Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
na bayyana mamakin ta tace  " Dan Allah fa Tabawa? A mamakance ta cigaba da cewa "yo ina kuwa muka sani muna zaune bonono , ai tsayuwa bata ganni ba dole na yi hanzarin komawa ciki, ke dai tabawa nagode miki. A zaune ta tarar da Falmata tana mammatsa yatsun ƙafafun ta da suke mata tsiko , ba tare da ta ɗago kai ba ta amsa Sallamar Hajja wacce ita ma kai tsaye ta zarce banɗaki ,bata tsaya yi mata dogon bayani ba  . ruwa mai zafi ta tarawa Falmata ta tuttula duk turarurrukan wanka da ta tarar da su a guri na musamman a jere da wasu ma ƙila ba na wanka bane ita dai Hajja ta zuba ƙamshi gum kuma ya cika banɗakin ya ratsa har waje . "Fatima tashi ki je kiyi wanka maza-maza zama bai gan ki ba 'yar nan . Hajja tace haka lokacin da take dawowa cikin ɗakin Falmata da ta riga ta saba da subaɗaɗin Hajja ta ɗan dubi Hajjan tana komawa ta kishingiɗa a ƙasa tace "Hajja duk yaushe nayi wanka da safe ? Sannan kuma wanka da tsakar ranan nan ƙarfe ɗaya saura Hajja lafiya dai ko ? " lafiya lau sai Alheri 'yar nan domin kuwa yau Ubanɗakina ke dawowa Babban soja Baban Mama yau amaryar ki kike uwarɗakina wankan taryar miji za kiyi . "Da gaske Hajja ? . Falmata ta tambayeta tana miƙewa  zaune fuskar ta ɗauke da yanayin da tashi ɗaya ba'a ba shi matsayi ba . bata jira Hajja ta bata amsa ba ta cigaba da cewa " Amma kuma ba wanda ya faɗa mana ko Maman Yumna ma bata faɗa min ba anya Hajja da gaske ne ? wa ya faɗa miki ? . " mts , ahaf ai ga irinta nan ke wa ya faɗa miki kishiya tana zama abar dogaro ɗari cikin ɗari ? Wa yace miki ana bada amanna da Amana baki ɗaya ga kishiya ? Ni daman daga ganin yadda take miki nan-nan nasan tsagoron kissa ce da kilbasa ai kin ga ga shi da tasamu labarin dawowar mijin ku ɗif ta ɗauke ƙafa tana can ta duƙufa shirya kan ta , ta bar ki baki sake , "Yanzu kiyi maza ki tashi ki gyagiije dan waɗannan ƙananun muri-mirin kowacce mai ciki sai tana yin su basu isa hana kome ba ai ciki ba cuta bace , kiyi azamar yin wankan ki fesa ado irin na shiga gasa ki tafi gaida Mahaifiyar sa daga nan ki zauna a falon ciki wajen ta , ta yadda daga ya sanyo kai falon zai gan ki tunda kuwa dai daga ya iso gidan gaishe da ita shine abu na biyu da zai yi bayan gaishe da Mahaifinsa , kin ga ita Siyamar take ko wa ? Da take miki ƙafar ungulu kin riga ta ganin sa , tashi maza uwarɗakina ba'a bori da sanyin jiki ... "Hajja ni dan Allah ki rabu da ni , kina ganin dai yadda koyaushe muka je gaishe ta ɓata rai take yi dakyar take ansawa sannan ..... Kafin ta ƙarasa Hajja ta katse ta "banda abun ki uwarɗakina faɗan da ya fi ƙarfin ka ai mayar da shi wasa kake , idan ta amsa yau da kyar watarana da fara'a zata tare ku ke da 'yan jikokin ta kiyi haƙuri kin ji  inda ba'a son ka anan arziƙin ka yake ke dai gwada mata ɗa'a sai ki ribaceta da kyawawan ɗabi'u kin san su saraki ne sai ana musu bangirma kin jii ko?  . Turo baki Falmata tayi da cigaba da cewa "  sannan Hajja shi ma ɗin ai bai ma san mun zo ba tunda kin ga fa bai taɓa neman mu ba gaskiya ni ba zan kai kaina wajen sa ba idan shi ya zo shikenan idan bai zo ba ma ni..... Wannan karon a hasale Hajja tace "to ai shikenan zauna kiyi ta jiran sa anan shi da yayi yi jinyar ya zo ya gaishe ki Iya-gwamma , tunda ni dai ba ki ɗaukeni bakin kome ba a zaman mu ban isa baki shawara ba ai shikenan . Daga haka tayi ficewar ta Bayan fitar Hajja a ɗakin sai duk jikinta yayi sanyi , tunda take da Hajja bata taɓa ganin tayi fushi ya haka ba duk sai ta ji ba daɗi dan haka ta miƙe a hankali ta shiga banɗakin Bayan fitowar ta da daga banɗakin da ta kwashi wajen mintoci talatin a ciki tana wanka. jikinta ba kuzari ta zauna a kujerar gaban gadon , har yanzu Hajja bata shigo ɗakin ba , tunanin da yake nuƙurƙusar ta sake yawaita yake yi "da gaske yau yake dawowa amma bai neme ta ba ? Tun rabuwar su har yau bai taɓa jin kewar ta ba kenan ? Shiyasa bai neme ta ba , tunda Aicha tace suna yin magana a waya kuma ko bayan dawowar su maradi rannan da kunnen ta taji suna waya da Aicha , kenan ita ce bai nema saboda baya buƙatar ta ko me ?  to meyasa ita kuwa zata damu kan ta da tunanin sa ? Har Hajja zata matsa tayi wani shiri na musamman a domin taryar sa . Har ruwan jikinta ya bushe bata shafa Mai ba , agogon ɗakin ta duba ƙarfe biyu har da kusan rabi dan haka ta miƙe ta sake komawa banɗakin tayi Alwala ta zo tayi Sallar azahar bayan ta idar bata miƙe akan sallayar ba ta cigaba da zama akai tana istigfar lokaci-lokaci tana murza idanun ta da suke mata mil-mil tunda tayi wanka da alama sabulan da tayi amfani da su wajen wankan sunfi ƙarfin lafiyar idanun ta . Tana zaune har aka ƙira la'asar bata jinkirta ba tayi Sallar kawo lokacin rashin jin motsin Hajja ya fara damun ta dan haka ta miƙe ta buɗe Babbar wardrobe bango guda da aka zube mata suturunta ciki ta dauko wata doguwar baƙar riga ta sanya a jikin ta ba tare da ta shafa ko hoda ba sai ɗan mai da ta mutsiƙa a fatar ta . Dawowa gaban Babban mudubin tayi ta tsaya tana duban kan ta cikin ta da ya ɗan tasa ya bayyana a sarari ta cikin rigar ta tsirawa ido. "Kunyar fita a haka ana gane mata cikin ya kamata ta . "Mts shi cikin nan ma duk ya bi ya hana mutum sakewa . tayi mitar haka lokacin da take cire rigar jikin ta ta zaro wata doguwar riga har lau launin ruwan zuma mai duhu da ya ɗan sirka da zane a tsai-tsaye launin farar ƙasa , rigar faffaɗa ce da take da rufaffen wuya sannan tana da ɗan nawi kaɗan a can Rochester ta taho da ita , lokacin da ta Sanya a jikinta ita da kan ta sai da ta ɗan murmusa saboda yadda rigar ta amshi zubin jikinta na dirarriyar mace mai matsakaicin tsawo da 'yar ƙiba kaɗan sai cikin nata ya ɓuya a rigar Rigar bata da mayafi dan haka ta ɗau wani babban mayafi launin farar ƙasa da aka masa adon duwatsu ta yafa akan ta ya rufe mata jiki kirif , har zata matsa daga gaban mudubin idanun ta suka kai kan 'yan kunnayen ta da tunda ta taho da su daga Maiduguri ta cire su ta ajiye ana,  su ta kai hannu ta ɗauka 'yan gajeru ne ta maƙala su a kunnuwan ta a hankali ta sanya ɗan yatsa ta lakaci mai ta shafe siraran labbanta marasa tudu . Takalmanta masu kama da silifa 'yan madina amma wannan daga Rochaster ta zo da su su ta zira a ƙafar ta ta fito bayan ta shafe jikinta da Humra da kamshin ta ke tashi kaɗan-kaɗan . Boyayyar ajiyar zuciya tayi lokacin da ta fito falon ta ga Hajja zaune daga gefe da alama Salla ta idar . Da fara'ar jin daɗin ganin ta ta matsa kusa da ita kafin tace " Hajjata anan kike ? Ɗan waigowa Hajja tayi kamar bata san da fitowar ta ba tace " uhm anan nake . " to sannu da hutawa Hajja nima yanzu na gama shirin zan shiga na gaishe su yadda kika ce . . Wannan karon Hajja ta ɗan saki fuska jin Falmatan tace zata yi yadda ta sa ta dan haka ta ce " to Madalla ko kefe fa uwarɗakina ? Maza je ciki ki zauna idan son samu ne ma ki samu wajen da yake fuskantar ƙofar shigowa ki zauna kin ji ko ? . " to Hajja Falmata ta amsa cikin ran ta tana gujewa rigimar Hajja ne amma idan ba haka ba ita ba wani niyyar zama tayi ba . Da kallo Hajja ta bi bayan ta cikin ran ta kakkabin wannan rigar ta Falmata take yi taɓe baki tayi kafin a fili tace " ana yi yafi ba'a yi tsarkin mahaukaciya da kunu , idan ba haka ba wannan riga da kika sako ai bata da maraba da buhu . A ɗarare Falmata tayi sallama a bakin  falon da daga inda take tana jin tashin hayaniya da dararrakin mutane da alama akwai wasu baƙi masu ɗan yawa a ciki . Ɗan jim tayi jin babu wanda ya amsa mata duk kuwa da tasan ana jin ta,  sake sallamar tayi a karo na uku sannan ta tsinkayo muryar wata daga ciki ta amsa , dan haka ta sanya ƙafafun ta ciki a hankali  . Da ɗai-ɗaya suke mayar da hankalin su kan ta tana tahowa har ta ƙarasa daga gefe kaɗan tayi ɗan gurfano tana gaishe da Hajiya Umma wacce tunda ta shigo ta rage fara'ar da take yi , kamar yadda ta saba amsa mata gaisuwar ba wata kulawa haka yanzun ma ta amsa tana janye ganin ta daga kan ta zuwa gefe kafin ta yunƙura  tana barin wajen baki ɗaya zuwa wata ƙofa daban . A hankali ta waiga tana ɗan kallon sauran matan da suke wajen biyu daga cikin su kawai ta gane "Ubbo da Ammi sauran mata ukun bata gane su ba amma dai suna mata yanayi da su Ubbo , cikin nutsuwa ta gaishe su a kunnen ta Ammi ce kaɗai ta amsa da mutunci sauran matan sama-sama suka amsa ita kuwa Ubbo ko amsawar ma bata yi ba . Fitowar Siyama daga ɗakin Umma yasa ta ɗago kan ta " sœurs wannan fa ? Kamar ya fi zama a jikina kou ? Ta ƙarasa zancen tana ɗan yin juyi cikin dakakiyar Shadda "Boo" da ta sha aiki aka mata ɗinkin doguwar riga , nan take wajen ya ɗau ƙaramar sowa suna yaba kyaun da tayi . cike da burgewa Falmata take kallon ta tana murmushi sosai ta yi mata kyau kwalliyar ta kuma ta ƙayatar da ita . " kin yi kyau Maman Yumna , muryar Falmata ta ratsa wajen . Da sauri Siyama ta waiga inda ta ji tashin muryar ta da farkon fitowar ta wajen bata lura da wanzuwar ta ba . Tana murmushi ta ƙarasa kusan ta kafin tace " Fatima nagoude sosai, yaushe kika shigo ? "Yanzu na zo . Ta amsa mata a taƙaice Murmushi tayi kafin ta ɗan yi ƙasa da murya yadda Falmatan ce kaɗai zata iya ji tace " Yau Yarima Biyamuradi ke dawowa , da fatan kin masa shiri ? Da yanayin ta na rashin magana sosai falmata ta girgiza kan ta kawai tana janye ganin ta daga kan Siyama ta sunkui da kan ta ƙasa duk jin ta take a takure sakamakon  kallon ƙasƙancin da ta lura matan wajen na jifan ta da shi . Muryar Ubbo ta ratso wajen da take cewa " Siyama kiyi maza ki shirya mana kin tsaya inda bai dace ba , kin san fa Mijin ki na daf da shigowa , kin kuma san ke tauraruwa ce  ba tururuwa ba , ke tauraruwa mai hasken alkhairi ce ba tauraruwa mai wutsiya ba . Cikin sanyin jiki Siyama ta juya fuskar ta ɗauke da yalwatatcen murmushin jin ɗadin yabo mai kama da ƙirari da Ubbo tayi mata sai dai gefe guda tana jin wani iri da shaguɓen da ta lura Ubbo ta yiwa kishiyoyin ta . Har tayi taku biyu ta waigo Falmata wacce kanta ke sunkui har lokacin ba tare da ta iya haƙaƙe halin da take ciki ba , ta saita muryar ta sama kaɗan kafin tace " Fatima taho mu tai ki sauya kaya akwai Boo irin ta jikina da tai min yawa nasan zata iya miki dai-dai tunda kin fini ƙiba kuma launin zai amshe ki'... " ahir ɗin ki da arawa kishiya sutura solobiya hala ita batta da sutura ta ratayo wagga tsumma a jikin ta ta taho muna nan tana barin mouna tsamin gwanjo ? . " ko da shike ba laifin ta ba nan gurin ta ƙurewa kenan , talaka daman yaushe yunwar ciki nashi ya lafa bare ya san suturar da ta amsa sunan sutura ? Bar ta cikin tsummokaran ta da shi yafi dacewa da itta .. "s'il te plait Adda amm Dan Allah . Da yanayi na rashin jin daɗi tare da chakuɗuwar tausayi Siyama ta juya ga Falmata lokacin da take mikewa tsaye ,  tayi saurin riƙo hannun ta tana cewa " kiyi haƙuri ƙamnata mu tai na miki le maquillage ki sauya kayan kin ji kou ? Idanun ta cike da ƙwalla wannan karon cikin wani irin yanayi ta zame hannun ta daga riƙon da siyama ta mata , tana ƙoƙorin danne hawayen da suke neman ɓallowa tace " Nagode Maman Yumna sannan ba sai na sauya kayana ba na jikina ma masu tsarki ne kuma kyauta ce daga Mijina masoyina ,dan shi na saka dan ya gani yaji daɗi ba domin na zama tauraruwa ba ina so ya ganni da su rataye a jikina dan yasan cewa na yaba da kyautar sa . Dan murmushi tayi kaɗan tana mayar da gani. ta kan su Ubbo daga inda take tana hango ɓacin rai akan fuskokin su da take iya gani dusu-dusu . " Nagode sosai Maman Yumna , ta sake faɗin haka lokacin da take barin wajen . Dusu-dusu take ganin hanya saboda idanunta da suke cike taf da ƙwalla ga kuma zogin da suke mata. bata tarar da Hajja inda ta bar ta ba , tana zaton tana ɗakin su a yadda zuciyar ta take yanzu so take ta samu waje ta ɓuya tayi kuka , ciwo ke sasuƙar rarraunar zuciyar ta da daman tana kusa jiran kiris take . Dan haka a karon farko tun zuwan su gidan ta fito ta ɗau hanya ba tare da tasan takamai-mai ina ta nufa ba bata kuma damu da bayun da suke binta da kallo har  wasun su na yin ƙus-ƙus ba so take tayi nesa da mutane ta samu maɓoyar yin kukan ta masha'in ' Can wani sashin da ta lura da ɗaukewar ƙafa ta shiyar nan ta nufa ,lokacin da ta doshi mashigar sashin tun kafin ta ƙaraso masu gadi biyu suka dakatar da ita , tambayar ta suka yi wacece ita ? Ta basu amsa da ita ce Fatima , suka ce daga ina take ? Tace daga Maiduguri Nigeria . Juyawa suka yi gefe suna ƙus-ƙus Cike da gundura ta juya da nufin fasa shiga ta nemi wani wajen saboda gaba ɗaya cikin gidan ne bata son komawa sai ta tsinkayo ɗaya daga cikin bayun yace " Ranki shi daɗe uwargijiyar mu afouwa muke biɗa ki maouna sassauci rashin sani ya sanya mu turjiya ga oumarnin ki baa in miki jagora ƙofa a buɗe take ga Iyalan Yarima Biyamuradi.. Sai suka buɗe mata ƙofar gidan daga inda take tana iya hango ƙawatuwar harabar gidan da shukoki masu furanni da bata ga irin su ba a kan hanyar ta ta zuwa nan , dan haka sai ta sanya ƙafar ta a hankali cikin harabar gidan ƙamshin furanni tare da na sabon fenti da wankin da aka yiwa gidan ya sanya ta lumshe ido ta fara taku tana jin yadda sanyin wajen yake ratsa ta shirun wajen yana samar mata da wata nutsuwa ta musamman sai kawai ta miƙa hanya ba tare da tasan inda zata je ba . Bakin wasu manyan gine-gine uku ta bullo tana ƙare musu kallo gini ne mai matuƙar kyau da tsari , ta tafi a hankali kan barandar ginin da yake fuskantar ta a tsakiya ta zauna daga bakin barandar ba tare da ta damu da shirun da ya yawaita a wajen ba bare ta ji tsoro sai kunnuwan ta da suke tarwai tana jin sauƙar kukan tsintsaye . Tana zama ta ji ƙuntatciyar zuciyar ta ta fara warwarewa lokacin da kuka mai ƙarfi ya zo mata , ta dunga tuno yadda baki ɗayan 'yan uwan Youssouf basu son ta ciki har da Mahaifiyar sa kan ta . Sannan shi ɗin ma da ake kome domin sa bai damu da ita ba a halin yanzu ma bata san matsayin ta ba a wajen sa . A hankali ta kai rigar jikinta hancin ta ta shinshina lokacin da take tuno da kalaman Ubbo da tace duk ta cika musu waje da warin gwanjo , ita bata ji warin da rigar take yi ba sai ma ƙamshi irin na tsadaddun kayan da aka sayo su daga manyan shagunan da suka amsa sunan su da ya chakuɗu da ƙamshin humrar ta yake bada wani irin launin ƙamshi mai sanya shauƙi' Ajiyar zuciya ta sauƙe cikin ran ta tana tambayar kan ta ko sai yaushe ne su zasu huta daga gorin mutanen duniya ? Sai yaushe ne za'a fara musu kallon mutuntawa ? Hawayen ta ta shafe da hannun ta tana jin damuwar ta tana raguwa da tayi kukan , daga gefe ta hango bakin fanfo ta yunƙura a hankali ta nufi wajen wanke fuskar ta tayi kuma ta tari ruwan da tafukan ta ta sha , ta kulle fanfon ta dawo ta zauna inda ta tashi . Wasu kyawawan duwatsu farare kal-kal ta gani daga gefe a ɗan gurin da aka killace domin yin shuke-shuke ta sa hannu a hankali ta tsinto su , ta zube su a gaban ta tana kallo cikin ran ta tana tunanin me ake yi da su kuma ? Jingina kanta tayi da jikin barandar tana rintse idanun ta saboda iskar wajen da take jin ta mata yawa kamar tana ƙara mata ciwon idon . Da ta rufe idon sai taji daɗi sannu kan hankali taji zaman ya fara mata ba daɗi saboda bayan ta da ya fara ƙagewa , bata damu da ta buɗe idanun ta ba da daman tafi sabawa da duhun dake cikin su. sai ta kishingiɗa kaɗan da nufin bawa kanta hutu na wani lokaci ,  sassanyar iskar wajen haɗi da shirun da wajen yake da shi da kuma yanayin jikin masu ciki yasa bata jima ba baccin da bata san yaushe ne ya kawo mata ziyara ba ya ɗauke ta a wajen . Lokacin da Biyamuradi Youssouf ya iso baki ɗayan Masarautar sai ta ɗauki murna da kiɗe-kiɗe tamkar wanda ake gagarumin biki . Da kyar ya samu ya zille daga fada nan ma domin uzurin da Tafeeda ya shigar ne na cewar da yayi ya kamata ya samu hutu tunda bai cika lafiya ba har yanzu . Da ya shigo gida sashin Hajiya Umma nan ɗin ma a cike ya tarar da sashin da katafainin 'yan uwansa waɗanda dai suke cikin ƙasar kama daga waɗanda suke ciki ɗaya har 'ya'yan Hajiya Mama da suke gidan tuni sun yi zangon a ɗakin mamar su labarin tabbatuwar shigowar sa yasa suka yi ɗango zuwa sashin Hajiya Umma. Haka ya dunga gaisawa da wasu wasu na rungume shi wasu har 'yar ƙwalla suke na jin dadin sake ganin sa a tsaye kyam bisa diga-digan sa irin taryar da suka masa ya sanya shi jin hawaye bai taɓa sanin haka yake zakara a cikin 'yan uwansa ba sai yau , babu shakka da mutuwa yayi da ya bar musu miƙin da bazai gogu ba a zuci . Daga can lungu ya hango Siyama ita ma ƙwallar farin-cikin ganin sa take tare da tasowar ciwon kewar sa da take yi , ɗan bakin nan nata yaƙi rufuwa daga murmushin da take kamar yadda ta kasa janye idanun ta daga kan sa. da hannu ya yafice ta yana 'yar dariya tare da jin raguwa ciwon da yake ji a cikin ran sa kan abunda ya same shi yana yin ƙasa da kusan kaso 50% ganin soyayyar 'yan uwan sa ya ishe shi farin-ciki . Tana murmushi ta ƙaraso zata tsugunna daga gefen sa ya sa hannu biyu ya ɗago ta ya matsa tare da yi mata wajen zama daga gefen sa da fara'a cikin sautin sa yace " Mata ai geufen Mijinta take da mazauni ƙaƙa za ki ɓuya bayan Aicha kina leƙe na ?  Ina ɗiyata ban ganta a masu tarɓa ta ba . " tana bacci'  ta bashi Amsa tana sake riƙe hannun sa da yasa cikin nata a lokacin ji take kaf duniya ba wanda ya kai ta jin farin-ciki har wani narkewa take jin zuciyar ta na neman yi bata ƙi ba kowa ya watse a bar su tare . Wajen ya ɗau dariya wasun su na tsokanar Siyama suna cewa kunyar kinibibi take yi bayan tun ɗazu ta ishe su da leƙe-leƙe . A cikin su duk babu wanda ya tado da batun abunda Maimounatou tayi masa da wannan kuma umarni ne daga Maimartaba da kan sa da yace " kada a maida zancen labarin tattauna akai . Hajiya umma ta miƙe tana barin wajen zuwa cikin ɗakin ta a lokacin Allah kaɗai yasan Halin da zuciyar ta ke ciki tayi rauni bata taɓa zaton zai dawo haka ras da shi da lafiyar sa ba babu shakka Allah shine mai yin yadda yaso da bawan sa wani ɗan Adam can bai isa tasiri ba. Bayan Miƙewar ta bai fi mintoci uku ba shima Youssouf ya mike cikin ran sa ya fahimci Mahaifiyar sa na son ganawa da shi dan haka ya bi bayan ta zuwa cikin ɗakin . Bayan yayi Sallama ya tura kai ciki , bisa sallaya ya hango ta riƙe da Alkur'ani  , ta ɗago kan ta tana saita ganin ta a kan shi fuskar ta ɗauke da Murmushi ya ƙaraso daf da ita ya zauna yana riƙo hannuwanta baki ɗayan raunin da yake ji a lokacin shine ya taso masa " Umma Allah shi min dawowa ban mutu ba kamar yadda suka so . .. ya furta hakan hawayen da suka cika idanun sa na sauƙa , yana jin yadda zuciyar sa ke yin kuka. a take ita ma zuciyar ya ta karye tun faruwar lamarin yau ne rana ta farko da Youssouf ɗin yace wani abu yau ne kuma rana ta farko da ta ga kukan sa a tunda ya zama cikakken mutum. Kan shi ta ɗora hannun ta kafin tace " ka dawo Youssouf ita cuta ai ba mutuwa ba wani kuma bashi da tasirin datse rayuwar wani sai fa idan kwanaki sun ƙare ka yi godiya ga Ubangiji doumin shi ya baka kariyar da basu idda nufin su ba Allah ya sa hakan ya zama kankara na daga zunuban ka . " Amin-Amin Umma,  ya amsa yana goge ƙwallar sa da hannuwan ta duk biyu ta taya shi tamkar dai lokacin da yake ɗan yaron sa. " Kar ka yiwa maƙiya kuka kamar kai ba jarumi bane ? Hakan zai iya barantaka da matsayin da kake kai na Soja mazan Fama sannan kuma Yarima sarkin watarana jarumi bai yiwa maƙiya kuka idan sun kai shi ƙasa ya samu dama miƙewa yake ya gyagije a cigaba da fafatawa . " hakan ba kome bane da ya wuce ƙarin ilmi cikin zaman duniya ka lura ka gane ba kowanne so bane yake zama na gaskiya , ba kowanne murmushi bane yake zama na ƙauna wasun ai shiga suke irin ta burtu suyi aron halayya da kamanni domin cimma wata mummunar manufa tasu su idar da mugunta ka kiyaye Yossoufa . Kallon ta yake bai ko ƙifta idanun sa zuciyar dake ƙirjin sa ya buɗe yana ƙarbar duk wasu kalmomin ta yana musu adana saboda dayawa daga cikin zantukan ta  bai kai ga gane me take nufi ba a yanzu ? Har kawo yanzu cikin ruɗani yake mai yawa ' har kawo yanzu zuciyar sa bata bar nacin tambayar sa me yasa Maimounatou tayi masa haka ba ?  yana son ganin ta domin ita kaɗai take da amsar tambayar nan . Ga mammadou ya kasa amincewa kiyayyar da yake masa har ta kai ya kashe shi

Chapter 95 of 111