Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
tafi , sai ya miƙe a hankali bayan ya mata bankwana ya fito daga falon , baya sanin takamaimai ina yake jefa ƙafarsa ya nufi shiyar gidan sa , Sashin Siyama ya tasarwa ba tare da ya haƙiƙance meye zai je ya sanar da ita ba , Da shigar sa Yumna ta taso da gudunta daga inda take wasa a tsakiyar falon da tarin kayan wasanta ,   Da sauri ya sunkuya ya ɗauke ta yana matse ta a cikin jikin sa kewar Mama marar adadi na taso masa ,    "Papa ,    ta ƙira shi da ƴar muryar ta , "Yumna , ya amsa yana ɗora idanunsa akan Siyama da ta miƙe tsaye daga kan kujerar da take kishingiɗe Rakiya na mata tausar ƙafafunta , Da sauri Rakiya ta miƙa gaisuwar ta kafin ta bar falon zuwa can waje sashin su na ma'aikata , A hankali Siyama ta tako gaban sa bayan ta ƙirkiro wani guntun murmushi akan furskar ta , "Sannu da zouwa Biyamuradi,  da fatan ka iske mou lafiya ?   Tana ƙarasowa ta kama hannun sa guda , kafin ta cigaba da cewa ,     " Mu tai kayi wanka Baban Yumna kafin a samar da abinda zaka taɓa , Yanayin rashin kuzari bai bar shi ba ya bi bayanta zuwa sama ɗakinsa , Bayan ya yi wanka ya shirya , cigaba yayi da zama akan kujerar ɗakin ya zurfafa cikin tunanin umarnin Hajiya umma , da kowacce daƙiƙa guda tashin hankalinsa daɗuwa yake , gefe guda ga rashin sanin takamaimai halin da ita kanta Fatima ke ciki tare da ɗiyansa dake maƙale a marar ta ,    Ƙarar wayar sa ya sanya shi janye tagumin da yayi ya ɗau wayar ganin mai ƙiran nasa daya daga cikin manyan kwamandojin sojin su ne na yankin Diffa , Magana suka sake yi kan tsaron da zasu daɗa a tsakanin boda saboda motar da take ɗauke da matarsa da zasu bi ta Boda zuwa Nigeria , bayan ya gama wayar da bai ɗau lokaci yana yi ba ya ajiye wayar a gefe yana baya da kan shi ya ɗora kan bisa  allon kujerar ya ɗora dogayen ƙafafunsa akan ɗan teburin gilashi da yake gaban sa , Idanun sa ya runtse yana jin yadda kansa  ya ke sara masa musamman ta goshin sa ,    Siyama wacce ta ji shirun sa yayi yawa bayan ga abinci ta haɗa masa a shiyar cin abincin su , sai ta miƙe ta hau saman , cikin ranta kuwa ƙoƙari take tayi aiki da shawarwarin da Rakiya ta bata na danne kishinta daga barin bayyana shi a sarari , Tana murɗa ƙofar ɗakin ta hango shi a kujerar ya dafe kan sa da hannunsa guda , wani irin yanayi na zallar tausayi da ake samu ga abunda ake ƙauna ta gaskiya , shine ya tsigar mata , babu shakka a tun shigowarsa ta fahimci tsananin tashin hankalin da yake ciki . Bai ji shigowarta ba har zuwa zaman ta a gefen sa , sai da ya ji hannunta mai tsananin taushi ta ɗora akan nashi hannun da ya dafe goshinsa da shi ta janye shi ,   "Baban Mama , ta ƙira sa , ɗas ! Zuciyarsa ta buga da jin sunan Mama da ta masa inkiya da shi da Falmata kaɗai ke ƙiransa da sunan ,  sai ya dawo da ganin sa kanta ,bayan ya gyara zamansa yana jin wani irin yanayi mai tasari matuƙa ,    "Baban Mama ina miƙa ta'aziyyata kan rashin da muka yi na ɗiyar mou , Allah shi jikan Mama shi sa ta ceto mou . Sai tayi shiru tana neman dai-daita nutsuwar zuciyar ta daga tarin baƙin-cikin da yake bijiro mata na zallar kishin Falmata , ta ɗora da cewa ,    " Ina ƙamnata Fatima ? Da fatan ka baro ta lahia ? Da wani irin yanayi ya matse hannunta dake cikin nasa , cikin muryar dake cike da rauni yace     " nagoude sai dai a halin yanzou Fatima ta gudou ta barni zuwa kan hanya mai matuƙar haɗari , Hajiya Umma kuma ta min oumarni na sau amren Fatima , ki min addu'a Siyama lamura agareni sun tsaurara , kowa ba shi fahimta ta bisa jarabawa ta rayuwa . Ƙwalla ta ji sun tara mata a ido , tunda take bata taɓa ganin Biyamuradi cikin halin ɗimuwa tare da rauni makamancin haka ba , sai fa yau ta dalilin ɗiya Mace , babu shakka wagga ɗiya Fatima ta kai ayi gangamin tafiya kallon ta . Gagara cewa kome tayi illa kanta da ta kwantar bisa ɓarin jikinsa , cikin tausayin kai tace , " kayi haƙouri da ikon Allah lamura zasu dai-daita maka a tsakanin hakka nayi Alƙawarin taya ka da addu'a , Allah shi dawo maka da Fatima-zahra . Hannunsa duk biyu ya sa yana rungumeta tsam a jikin sa , ransa cike taf da ƙauna ta musamman gami da ƙarin ganin ƙimar ta a idanunsa , babu shakka shi masoyi na gaskiya abun riƙo da hannu biyu ne . " Nagoude ƙamnata kouma Matata , ya furta hakan yana sumbatar kan ta ,     Idanunta ta runtse da hakan ya bawa ƙwallar dake cike a gurbin idanunta damar zubowa , tana sauƙa akan kirjin sa . Kanta take tausayawa yadda zuciyarta ta afu ga son maso wani irin haka , ta san zafi da raɗaɗin rashin abun so dan haka take tausaya masa babu shakka ita bata da makaman yaƙin tunkarar ko wacece wannan Fatima da ake ta ƙiƙi-ƙaƙa akan ta da ta sanya Mijinta ya ɗimauce tare da jan ɗamarar yaƙi da duk wasu masu son shiga tsakanin sa da Abar son sa , labarin kome da ya faru tuni ya iske ta ta bakin Ubbo , Da tundaga lokacin tayi kuka tare da jimaminta ta har ta kusa faɗuwa jinya da taimakon Mai aikinta Rakiya da ta riƙa tamkar ƙawar shawarwarin ta , ta samu dawowar nutsuwar ta da Rakiya tayi ta bata shawarwari masu inganci tare da kwantar mata da hankali . " Baban Yumna mu tai ka ci abincin ,   " Bani jin Yunwa yanzou sai ko anjima kaɗan ,   Bata ƙara cewa da shi kome ba ta miƙe , tana barin ɗakin , zuciyarta baza ta juri ganin sa haka cikin ciwon son wata daban ba . Haka Youssouf ya ɗebe awanni cikin yanayi na bacci-bacci ido biyu , ( yayi likimo😂 ) Zuwa gefen la'asar ya sake yin wanka tare da shiri ya tafi Masallaci. *** Nan ya cigaba da zama yana addu'o'i tare da karatun Alkur'ani har zuwa shigowar lokacin Sallar magariba , da idarwar sa ɗan sako ya zo masa cewa Maimartaba yana son ganinsa a can turakar sa ta ganawa da baƙi . Da azama ya miƙe ƙarƙashin jagorar ɗan aiken suka cimma turakar Maimartaba , inda ya tarar da shi , shi kaɗai . Bayan sun sake gaisawa yayi shiru a zaune , daga ƙasa gaban kujerar da Maimartaba yake zaune , An ɗauki lokaci Maimartaba yana kallon shi baice da shi ƙala ba , yana nazarin tashin hankalin da ya bayyana a suffar sa , sai bayan wasu ƴan mintoci yayi gyaran murya   "Youssoufa , ya ƙira sunan sa ,    "Na'am ranka shi daɗe , yace yana sake ƙan-ƙan da kai ,    "Matso kussa Youssouf ka samrari abounda zan ce da kai , Da sauri ya muskuɗa ya dawo kusa sosai da ƙafafun Maimartaba, Cikin muryar da take cike da ilhama tare da tarin ilmi maimartaba yace ,"Youssoufa  sa'ad da Ubangiji ya tsawatar maka ka mai da hankali sosai, ka kuma yarda da gargaɗinsa, Ubangiji yana tsawatar wa waɗanda yake ƙauna. Kamar yadda mahaifi yakan tsawatar wa ɗan da yake fa'ariya da shi, "Kada ka zurfafa wajen biyewa tunani tunane-tunanenka mafarin rai ne kansa, ka kiyaye su abin mallakarka ne mafi daraja, "Kada ka faɗi kowane abu da yake ba na gaskiya ba, kada wani abu ya haɗa ka da ƙarya, ko maganganun ruɗarwa, ka duba gaba sosai gabanka gaɗi, ba tsoro ka tabbata ka san abin da kake yi, duk abin da kake yi kuma zai zama daidai , Idan har kayi haka ? ba za ka ji tsoro, sa'ad da kake kwance a gadonka ba, za ka yi ta sharar barci a dukan dare, ba za ka damu da masifar da za ta auko farat ɗaya ba, irin wadda takan auka wa mugaye kamar hadiri , Ubangiji zai kiyaye ka. Ba zai bari ka faɗa cikin tarko ba jinkirtawa yayi ya nisa tare da gyara zama , ya kai dubansa ga Youssouf wanda  fuskarsa tayi jaa idanun sa suka ciki-ciki . Ya cigaba da cewa , " Kada ka yadda Mazinaciya ta sake ruɗar ka , kada kayi duba ga ƙilbasar ta ko kuwa daɗi na daga kalmomin hilatar da suke kan harshenta.    "Leɓunan matar wani, mai yiwuwa ne, su yi zaƙi kamar zuma, sumbace-sumbacenta kuma su fi man zaitun taushi , amma ka sani bayan an gama , duka ba abin da za ta bar maka sai baƙin ciki, da azaba , za ta gangara da kai zuwa lahira, hanyar da take bi hanyar mutuwa ce ba a kan hanyar rai take ba, tana ragaita nesa da hanyar, amma kai ba ka ankara ba , " kayi nesa da zina Youssoufa kada ka yarda ka sake kusanta kan ka da zina Idan kuwa ka ƙi girmamawar da ake yi maka za ta zama ta waɗansu , mazinata ba kome bane su face walaƙantattu ababen walaƙantarwa ,            "Ka iya rungumar wuta a ƙirjinka sa'an nan ka ce ba za ta ƙone tufafinka ba? Ka iya tafiya a kan garwashi sa'an nan ka ce ƙafafunka ba za su ƙone ba? Haka yake da mutumin da ya kwana da matar wani , duk wanda ya aikata wannan, zai sha wahala . "kuma ai a yanzu ka gani , ka ga bala'in dake cikin zina , kome na tsanani da ya sabko maka ka sani cewa kankarane na daga zunuban ka ,zunuban mutum tarko ne, komar zunubinsa ce take kama shi , kayi gaugawar tuba ga Allah kafin lokaci shi ƙure maka .    Zuwa lokacin hawayene ke sauƙa a idanun Youssouf , nadama marar iyaka ta sabko masa , daga can ya tsinkayi muryar Maimataba yana sake cewa ,    " ina ka baro ɗiyar mutane da kake amre ?     Muryarsa na rawa yace    "ta tafi ƙasar su , kouma a yau Umma tai oumarni da na sau amren ta , zan sake ta Ranka shi daɗe , Ɗan murmushi Maimartaba yayi kafin yace ,     "mata sai abar su da lamarin su na ƙarancin hikima da tunani , anya ana gyaran ɓarna da ɓarna ?  Tafeeda ya gwada muna duk wasu shaidu na ɗaurin Amren ku , mun kuma gamsu da su , " dan haka baka sau amren matarka ba Youssouf ,  yi aminci ga matarka, ka ƙaunace ta , ka amro ta ne domin kana ƙaunar ta Alhalin kana da damar hakka , kai Mijin mataye ne , "Saboda haka ka yi farin ciki tare da matarka, ka yi murna da budurwa da ka auro, kyakkyawa mai kyan gani kamar barewa , ka bari kyanta ya ɗau hankalinka, daga ɗauke gani bisa matayen banza ,  Bari ƙaunarta ta kewaye ka , daga kwaɗayin macen titi , ƙwarai kana da damar haka ita halaliyar ka ce ,   Wani irin sanyin daɗi ne ya fara tsartuwa a zuciyar Youssouf sai ya ɗago kansa kamar wani soko-soko yana duban Maimartaba da kokonto ko kunnuwansa gaskiya suka jiye masa ?    Ɗorawa Maimartaba yayi da cigaba da cewa ,       " Amma ka tsahirta har abubuwa su dai-daita Mahaifiyarka kuma ta sabko daga fushin ta daga nan sai ka tafi ka zo da matar ka , mafi girman lamari a gaba ka tsaida adalci  a tsakanin Matayen ka babu shakka Allah yana farin-ciki da adalai .    Youssouf a lokacin ji yayi kamar ya tashi ya sungumi Maimartaba ya shiga shilla shi sama yana chafewa saboda tsabar daɗi da zumuɗi ,    " Nagode ranka shi daɗe, Nagode , nagode , nagode  kawai yake ta maimaitawa ,   " Youssouf kada ka manta kalmomin da na furta su gare ka zasu inganta halinka, su zama kayan ado kamar kyakkyawan rawani a kanka, ko kyakkyawan abin wuya a wuyanka, don su ƙara maka kyau ,     "Ban manta ba ranka shi daɗe , Allah shi saka da  Alheri Ranka shi daɗe ,    Gyaɗa kai maimartaba yayi " kana iya tafiya ga iyalin ka .     " to na barka lafiya ranka ya dade mu kwana lafiya .   Da tarin farin-ciki ya nufi sashin sa , da sassarfa ya shiga falon Siyama wacce ta ɗau kwalliya cikin ƙananun kaya riga da siket , jajaye da suka amshi fatar jikin ta mai matsakaicin haske. Da mamakin ganin sa a shiyarta da daren nan , Alhalin kuma yau ɗakin Gimbiya yake kwana , ta miƙe tsaye tana masa sannu da zuwa , Da sassarfa ya taka ya isa gareta ya rungumeta tsam a jikinsa yana shaƙar ƙamshinta mai sanyin daɗi , shafa bayanta ya yi a kunnenta ya ce da ita ,      " ki tayani farin-ciki ƙamnata Maimartaba ya yarda da aurena da Fatima , har ma ya min iznin nan ba da jimawa ba na tai na zo da itta , kwanan nan za ki ga ƙamnar ki . Murmushin yaƙe tayi tana rintse ido , muryar ta da ɗan rawa tace ,    " Alhamdulillah , Madallah da adali mai yawaita Adalci da kyautayi , nayi maka murna Biyamuraɗin maraɗawa ,   Zare jikinta tayi tana ƙin haɗa ido da shi saboda ƙwallar da cika taf a ƙwarmin idanun ta tana daf da kwaranyowa .   " mu tai ka ci abinci   ta ce da shi tana jaan hannuwan sa , Tare suka ƙarasa gaban teburin cin abincin da yake cike taf da kayan cimaka na alfarma . *** Zuwa lokacin Gimbiya Maimounatu ta kai maƙura wajen shaƙar baƙin-ciki , jin ya zo ya yini a gidan bai ko neme ta ba bayan irin laifin da ya aikata mai muni . Ta kasa zama sai kai kawo take , gaba ɗaya yau mummunar zuciyar ta ta ƙeƙeshe ita ke jagorar ta ,    Ko ƙwalliyar da ta saba yi domin taryarsa yau ta gaza , saƙa take da warwara , a ganin ta abunda yayi mata iyaka ne a cin fuska dan haka ta ɗau alwashin cimma manufarta a yau . Duban ta ta mayar ga gnala wacce ita ce ta zo mata da labarin sake shigowar Yarima Youssouf gidan da sake shigar sa sashin Siyama .   Da kaushin murya tace ,    Gnala ,    " na'am gimbiyar matar yari... a tsawace ta katse ta ,     " ki tashi ki tai ga shiyar matar can ki ce ina biɗar ganawa da Major Youssouf  Abdoul-azuzou Youssouf Baskore .   A ɗan firgice Gnala ta ɗago kan ta tana duban uwargijiyar ta , jin yadda yau ta ƙira sunan Yarima garan-gatsau babu wani sakayawa bare girmamawa , sai dai yadda ta ga fuskarta ta tsorata ainun , dan haka ta miƙe jiki na rawa ,ta fice tana cewa ,   "  Allah shi huci ranki Gimbiya ɗiyar Sarki . sanin da tayi bata da ikon shiga sashin Siyama kai tsaye , sai da kamun ƙafar Rakiya shugabar hadiman sashin da ita ce zata yi mata jagora , yasa ta ratsa dogayen bishiyoyi da shuke-shuken farfajiyar gidan ta cimma Rakiya a shiyar ƴan aiki ,   Da kallon banza suke bin junan su , tamkar kishiyoyin da suke zama bala'i,  kamar Mai ciwon haƙori Gnala ta buɗe baki da kyar tace ,    " saƙo dagga Gimbiya tace a shaidawa Matar Yarima , gimbiya na biɗar kaɗaicewa da shi .   Rakiya wacce take cin gyaɗa ƴar marau-marau , ta karkaɗa ƙafa bayan ta afa gƴaɗar ta a baki ,  ba tare da ta dube ta ba tace ,    " kin ga Gnala ki ɗaga sauti kiyi magana yadda zan iya ji amma kin zo kin tsaya akaina kina wani mui-mui da baki ,yo ce miki aka yi aka yi kunnen nawa zuƙo sauti yake ? Aikin banza .   Gnala ta ƙuta , cike da takaicin rashin mutuncin Rakiya. da ƙaƙƙarfan sauti ta ɗaga murya cikin faɗa-faɗa tana maimaitawa mata saƙon Uwargiyar ta ,    " ah ke saurara haka kar ki fasan dodon kunne ki fallasheni , kin zo kina min hargagi akai ya ruɓaɓɓan radi'o ,    " Naji , sai ki wuce mu tafi , tace tana miƙewa ta zira takalman ta ,   Da wani mummunan kallo Gnala ta bita kafin ta dafa mata baya , suna tafe Rakiya na rera waƙar Barmani mai coge "cikin waƙar ɗuwawai ," inda take cewa ,       A hayayye ɗuwaiwai dole a zauna da ku , to ko ana so , to ko ba' a ƙauna ,ko da sun tsiyaye ,  wayyo ladi ko a tsidau , kai koma cikin kwata ne . Daga bakin ƙofa ta nemi iznin shiga wajen Uwargijiyar ta ta hanya matsa mata ƙararrawar dake shaida isowar ta , Siyama wacce ta zuba abinci da zummar fara ciyar da Youssouf sai ta miƙe bayan ta ɗau izni daga wajen sa , fahimta da tayi wani saƙo muhimmi Rakiya take tafe da shi a dai-dai wannan lokacin . Da buɗe ƙofar ta ci karo da Gnala wacce take tsugunne a gaban ta , ba ɓata lokaci ta isar da saƙon Uwargiyar ta .   Murmushi Siyama tayi cikin ran ta tana aiyana " ai shi daman wanzami bai son jarfa ,   Da baya ta dawo tana sanar da Youssouf saƙon Uwargidan sa , jim yayi ," shi ba da gangan yaƙi zuwa wajen nata ba , rigimar ta yake gudu , baya son ta ƙara masa damuwa akan wacce yake ciki ,   Miƙewa yayi tare da yin baya da kujerar dake gaban teburin , tunda har ta sauƙe girman kan ta na ɗiya mace ta ƙira shi , duk kuwa da laifin sa , shi ya zama dole ya tafi gareta ,yayi aikin rarrashi da neman Afuwar ta tunda zuwa yanzu ai yana da ɗan ƙarfin jikin ɗaukar duk wani bore da zata iya yi masa ,   Sai da ya kai tsakiyar falon ya waigo ga Siyama wacce take tsaye jikinta a sanyaye  tana bin sa da kallo , dawowa baya yayi , a hankali ya rungume ta , tsawon wasu daƙiƙai , ya sake ta tare da sumbatar leɓɓan ta a tsanake ,     Daf da fuskar ta , ya kawo tashi fuskar cikin muryar da take tsakanin maƙoshin sa yace ,     " Nagode da kome Ƙamnata , je t'aime pour ça, tu es spécial pour moi seulement ,   Ya saketa a hankali ya juya yana barin falon ,    Tsaye tayi a gurin tana shaƙar ƙamshin sa da yayi saura a gurin , ta lumshe ido tana murmushi kaɗan cikin ran ta farin-ciki ne fal ,      " Da gaske yake da yace yana son ta ? Ita ɗin kuma ta musamman ce a wajen sa ? Ko dai duk farin-cikin kusantar dawowar masoyiyar sa ne ? **** Bayan shigar sa falon Gimbiya Maimounatu wanda yake da rangwamen haske sakamakon ƙasa da aka yi da hasken fitulun falon sosai a tsaye ya hango ta ta juyawa ƙofar baya , A hankali ya taka ya isa inda take tsaye , hannunsa ya sanya ya kewaye cikin ta tare da haɗa bayanta da ƙirjin sa sosai , Da sigar rarrashi yace ,       " Bana cikin Farin-ciki da ganin ɓacin ran ki princesse,  ina bakin-cik... Da wani sauti daban da wanda ta saba yi masa magana da shi ta katse shi ,         "  ya ya kake son samun farin-ciki lokacin da ka kwashi tsawon wasu shekaru kana assasa baƙin-ciki a zuciyar wasu mutanen  ? "  ka baranta da farin-ciki ba zaka yi farin-ciki ba har abada kai ma .     Da ƙarfi ya juyo da ita yana laluben ganin fuskar ta , sai dai hasken wajen ya masa ƙaranci .       " kiyi haƙuri Maimounatu ni ɗin mai laifi ne a wajen ki na sani , Wani ɗan ƙaramin murmushi mai sauti tayi ,     " haƙuri , laifi ?     Ta ce da sigar tambaya , Dariya tayi mai sauti , dai-dai da shigowar ƙira a wayar sa ta cigaba da cewa ,    " Ai ni baka min laifin kome ba kan abunda ka aikata ma rayuwar ka ?  To ma menene dan ka rage dare da yaya ka kuma zo ka amri ƙamna ?  Ai babu wani laifi ga hakan ni dai ta ɓangarena , dan haka kada ka bani haƙuri bisa wannan ba damuwa ta ce ba .   Jiki a sanyaye Youssouf yake bin ta da kallo , sai yake ganin baki ɗaya ta sauya masa ,      Hasken wayarsa ya kunna tare da cewa ,     " Maimounatu meye ya samu fitilun sashin nan ne ? Hala sun mutu ?  Bari za'a sauya wasu ,     " fitilin sashin nan na taya Uwargijiyar su baƙin-ciki ne kamar yadda zuciyata tun-tuni ta kasance a cikin duhun da yake matsananci fiye da wannan , tun a  wata ɓakar-rana cikin ranaku da ka sanya bakin bindigar ka ka tarwatsa min fitilar zuciya ta ,    Wayar sa ya mayar aljihu bayan ya ssnyata a silent , da alama sai yayi da gaske da alama ran Gimbiyar ta shi ya kai ƙololuwa a wajen ɓaci , jin yadda take amfani da wasu kalmomin da ya gaza fahimtar su , Jawo ta yayi ya zauna tare da ita tana bisa cinyar sa ,      "  Duk ki bar waɗannan kalaman Maimounatu , Fatima-zahra ƙaramar yarinya ce , ba zata ƙi ku zauna lafiya ba sann....     katse shi tayi ta hanyar ɗora yatsanta manuni akan laɓɓan sa ,      "shitt , Yarima Youssouf nace kada ka damu ,    Miƙa hannu tayi ta ɗauko tatatcen ruwan 'ya'yan itatuwa da ta sarrafa da hannun ta , ta nufi bakin sa da kofin ,     Jimm yayi yana kallon sheƙin idanunta ta ɗan hasken wajen , dariya tayi yana iya ganin hasken haƙoranta kafin tace da shi     " Sha mana Yarima , abun shan ka ne mafi soyuwa , ni da hannuna nayi sa musamman domin kai .    Ƴar ajiyar zuciya yayi jin alamun ta fara sauƙowa , hannun sa ya ɗora akan nata ya kai kofin zuwa bakin sa , yayi Bismillah ya kafa kai ,     Ya sha sosai saboda ƙishirwar tare da yunwar da ya yini yana ji , ya kuma gagara cin kome sai fa yanzu da ya fara samun nutsuwar zuciya ,     Wata irin damƙa da cikin sa yayi masa kamar kiftawa ido bayan gama sha , shiyasa ya zame Gimbiya maimounatu daga jikinsa ,   Da sauri ya fidda wayar sa daga Aljihu da har lokacin ƙiran Tafeeda bai bar shigowa ba , da hasken shigowar ƙiran ya kai hannu ya ɗau kofin yana haska ciki . Da wata irin muryar yace ,     "Maimounatou menene cikin wannan juives din ?  Meye a ciki ? Meye..  Kasa ƙarasa magana yayi     Gumi ya shiga karyo masa saboda wani irin ciwo mai tsanani da ya ji ya turnuƙe shi tamkar ana filla-filla da kayan cikin sa , zamewa yayi daga kan kujerar bayan ya saki kofin hannunsa zuwa ƙasa ,   Cikin azaba ya ke duban Fuskar ta , yana iya hango wani ɗan guntun murmushin cikar buri da take yi , bata yi motsi ko kaɗan ba wajen ba shi wani taimako     Wani irin gurnanin nishi ya fara yi , ya miƙe a ƙasa yana murƙususu ,ciwon da yake ji bai taɓa jin makamancin sa ba , wani irin duhu mai tsanani yake ji yana sabko masa daga can wani waje mai nisa a kwakwalwarsa Alhalin kunnuwan sa sun samu ƙarin ƙarfin ji ,    Domin

Chapter 82 of 111