ta ga tahowar hannun Yakaka ta buɗe baki ita kuma ta jefa mata ƙulin ,
" Da Baa kike kama Falmata sak ma kuwa kawai tsawon sa ne baki samu ba , ni kuma da Maman mu nake kama sak kawai ban kaita haske ba ,
Ƙurus-ƙurus ku-rus , Yakaka ta taune ƙulin da ta jefa a nata bakin , ta cigaba da cewa
" Daman an raba , ni da Bulama kamar mu ɗaya ke kuma da Baana kuma kamar ku ɗaya (sulum fut ) baƙaƙe siɗik , ta ƙarasa zancen da sigar tsokana ,
Yamutsa fuska Falmata tayi , kafin ta ce ,
"Amma ai Baa kullum yana cewa fararen mutane basu da ƙarfi da dauriya , mu baƙaƙe mun fi ku , Yakaka kin tuno da karon mu da Biri a gonar Baa ?
Wata sassauƙar dariya suka kwashe da ita lokaci guda , Yakaka wacce ta fi Falmata dariya muryar ta cike da amon dariyar da take yi ta ce cewa za kiyi ranar da kika sumar da ni a garin dukan Biri ,
Wannan karon hatta Hajja da take kallon su sai da ta murmusa , sannan ta ce tayaya ta sumar da ke Yakaka daga dukan Biri ??
Siririyar Muryar Falmata cike da dariya ta fara cewa ,
"Hajja lokacin girbi ne Baa ya kai mu gonar sa domin muyi masa gadi , muna zaune yin gadi da rana tsaka , sai wani ɗan Biri ya shigo gona , Yakaka ita ta gan shi ta dunga binsa da wata sandar da Baa ya bamu tana son doke shi amma Birin nan sai tsalle-tsalle yake yana gudu yaƙi barin gonar , ƙarshe dai yayi tsalle ya hau kan Yakaka char ya tsaya atsakiyar kan ta , Sai yakaka ta ce
"Falmata nace "Na'am ,tace Birin nan yana tsaye akaina ga sandar nan zan wurga miki , inda kike jin muryar ta za ki doke ta sama kaɗan ki buga masa da ƙarfi ɗan iskan Biri ɓarawo ,
Nace "to Yakaka , ta kuwa wurgo min sanda na ɗauka ,
"Hajja na faɗa miki da na ɗaga sanda kin san dai ba gani nake yi ba a lokacin, na ɗaga ta da ƙarfin gaske , lokacin da. naji Yakaka tana cewa kai-kai-kai amma na riga na wulwula sanda sai kawai na rafka a zatona alama take min na inda zan bugawa sandar watau a kanta ,
Ɗif na ji Yakaka tayi shiru ,
"Hajja ashe Yakaka na rafkawa sandar Biri kuwa tuni yayi tsallen sa , Yakaka kuma ta some ,
Ta ƙarasa bada labarin tana sakin shisshiƙar dariya tare da kwanciya bisa kujerar da take kai , ba Yakaka ba hatta Hajja , dariya take yi sosai ,
Yossouf da yake tsaye ta bakin ƙofar falon saboda hankalin sa da ya kasa kwanciya a zaman sa a falon sa , cikin duk daƙiƙa guda zato yake yi Yakaka zata sanar da Falmata kome ,
Da shi kuma ko kusa a yanzu bai shiryawa tarɓar tashin hankalin da zai iya biyo bayan hakan ba .
Baya yayi yana dariya da haƙoran sa kwarai labarin wannan ƙatoɓarar da Falmata ta yi ya bashi dariya ,
Yana shiga Falonsa wayar sa da take ajiye akan kujera ta sake ɗaukar kiɗa sunan Tafeeda ne ke yawo akan fuskar wayar ,
Ji yayi damuwowin sa sun sake yi masa rubdugu , zama yayi daga kan kujera ya ɗau wayar ya riƙe , ya akayi ma Tafeeda yasan dawowar sa, ? duk ƴan mintoci kenan da sanya layin sa na nan a waya ,
Shi a yanzu baya buƙatar ƙarin wasu damuwowi , yasan Tafeeda ƙudirinsa shine ya raba shi da Falmata da shi kuma ba shiryawa hakan yayi ba , ba kma ya jin zai taɓa shiryawa har abada,
Danna wayar yayi ya sa a silent saboda Mama da ta samu bacci kar ƙaran waya ya tadda , tagumi ya rafka da hannunsa biyu yana jin yadda cikin sa ke ƙugin yunwa amma ba damar cin abinci ,
Bayan sun tsagaita daga dariya , Hajja ta kallesu tana nazarin tarin ingantatciyar ƙaunar da ke ga junan su , a hangen ta irin na manya ta fuskanci kowaccen su tana ƙokarin binne damuwar ta ne daga 'yar uwarta saboda zallar ƙaunar da suke yiwa juna , idan kuwa hakane Madallah da irin wannan ƙauna ta tsakani da Allah ,
Miƙewa tayi tare da cewa ,
"Yakaka yayar Falmata zo muje daga ciki ki ga irin 'Ya'yan itatuwan su na nan Niger ba irin namu na Nigeria ba ,
"Uwarɗakina Falmata a kaiwa Mama abincin kadda yunwa tayi mata lahani , tana sashin Baban ta ai kin san hanyar ko ? Kin kuma san kitchen ɗin ga shi nan ,
"nasan Hanya Hajja ,
Falmata ta furta hakan tana jin son ta tafi ga Mijinta ta ga halin da yake ciki , sannan ta fuskance shi ko zata iya ganin wani sauyi a tare da shi na daga zallar ƙaunar da yake nuna mata muddin suna tare , a sanadin bayyanar Yakaka ?
Yakaka bata ce ƙala ba ta bi bayan Hajja , har ta ɗan gifta Falmata , sai ta ji ta ƙira sunan ta ,
"Yakaka nyei
Juyowa tayi fuskarta da Murmushi
"Na'am Falmatan nyei
"Yanzu zan zo da Mama tayi miki hira duk da bata da lafiya sosai , amma ta iya hira sosai , zan kawo miki ita .
Murmushi kawai Yakaka tayi ta juya tana ƙarasa barin wajen ,
Suna shiga ɗakin ta cewa Hajja ,
"Hajja ina 'ya'yan itatuwan ? Mu ga irin su ?
Kallon tsakar ido Hajja ta yi mata ,
"Yo ina kuwa wasu 'ya'yan itatuwa nan ? Kin tsare yarinya kin hana ta kaiwa mijinta tattattun 'ya'yan itatuwa tayi aikin lada ubangiji ya samar mata da lambun 'ya'yan itatuwa a Aljanna , ke haka ake yi yanzu tsakani da Allah ? Haba Babba uwar Mama .
Kallon Mamaki Yakaka tayi mata , ta samu waje ta zauna daga gefen gadon dake ɗakin
"kenan Hajja dai ba gaskiya kika faɗa min ba wayo kika min dai ko ?
Hajja bata dube ta ba ta fara ninke gyalen ta , ta bata amsa da
" to kuma dai , karo ɗaya ai ko da ƙwai da dutse a yi sa .
Shiru Yakaka tayi bata ce kome ba , cikin ranta damuwarta ce ta dawo sabuwa fil akwai wani alamu da ta hango tare da Falmata wanda bata fatan tabbatuwar sa ,
Falmata bayan ta jera abincin su da ta tarar a rurrufe cikin mazubi , sai ta ɗauka ta nufi sashin Youssouf da ta san yana ta harabar gidan duk kuwa da cewar bata taɓa zuwa ba , sannu-sannu take tafiya saboda duhun dare da ya fara shigowa daf ake da ƙiran sallar Magariba , tare da taimakon hasken fititulun da suke girke a harabar gidan da suka kunna kan su , ta iso Bakin babar ƙofar ta tsaya tayi sallama ,
daga ciki Youssouf wanda tuntuni yake kai kawo a cikin falon ya taho da saurin sa jin muryar ta ya buɗe mata ƙofar
Tunda ta shigo falon Biyamuradi yake binta da kallo mai wuyar fassara , so yake ya tantance yanayin da take ciki , amma ya gaza gano wata alama, maimakon haka sai ya shagaltu wajen kallon tsarin kyakkyawan jikin ta da take sanye da doguwar rigar roba da ta bi jikin ta lafe , koyaya ta motsa sai wani sashi na jikinta ya ɗau hankalinsa .
gefe guda Mamakin kansa yake yi yadda yarinya karama take mamaye tunaninsa a duk lokacin da suke tare ko ya koma gida. Akwai wani abu game da Fatima Zahra da ya kasa fasaltawa a ransa da a farko yake yawan sakawa a ransa cewa saboda irin kulawar da take yiwa 'yarsa ne.
Sai dai zuwa yanzu ya hiƙaƙancewa kansa cewa ƙaunar Fatima ɗarsuwa tayi a cikin ransa tun a ranar da ya soma ganinta , alhalin lokacin bai san cewa ma zata zam mariƙiyar ɗiyar sa ba .
Akan ɗan teburin dake tsakiyar falon ta ajiye farantin hannunta wurin da yake zaune ta waiga , cikin kwantatciyar murya tace
"ga abinci".
Shiru taji kamar babu kowa waigawa tayi sai dai duhun da yake falon tare da rashin ƙarfin ganin ta sun hana ta damar hango shi , wanda yana sane ya rinka tafiya a hankali ,
Ji tayi kamar abu na nenam rufeta ta baya ta dan ja jikinta kadan sai kawai taji tayi karo da mutum. Gabanta ne yayi wata irin faduwa ta rikice tana neman hanyar barin wurin saboda tsintar kanta kawai tayi da kasa sakewa da shi yadda suka saba , shi kuma yaki matsawa sai ma hannuwa da ya saka ya zagaye kunkumin ta tare da haɗa bayanta sosai da ƙirjinsa
"Hankali Zahra" yace da wata irin murya a daidai kunnenta har tana jin saukar numfashinsa.
"Uhmmm zan wuce ka matsa" ta hado kalaman ta furta a hankali.
"Baki zuba min abincin ba zaki tafi?" Ya ce yana karewa kyakkyawar fuskarta kallo, bayan ya juyo da ita ya kamata suka zauna ,
Turo baki tayi tana jin kanta a takure
"ni da kasan bana gani sosai idan dare yayi ?" kuma ai kasan ban iya zuba abinci ba .
Ya dage gira daya "yau kuma? Na dauka Zahra ta iya komai ashe da sauranta tunda bata iya zubawa miji abinci ba." Ya sake matsawa kusa da ita daga zaunen da suke ,
Sai dai bai bari jikinsu ya hadu ba saboda ko kadan bai yarda zai iya mallakar kansa ba a yadda yake ji ba , saboda shi da kansa buƙatar inda zai sanya kansa a rarrashe shi yake ,
da kuma ya tabbata Fatiman tasa a wannan gaɓar bata isa bashi kulawar da yake so ba ,
"gashi yau da hannunki nake so ki bani"
Yace mata yana murza ƴan yatsunta da ya riƙe cikin hannunsa
Yana kallon yadda idanunta suka kara girma kirjinta yana hawa da sauka cikin sauri da firgicin da bai san dalilin samuwar sa ba a dai-dai lokacin ,
"me zan baka?"
Tace muryar ta na ɗan rawa ,
"Abinci mana yadda kike bawa Mama"
Bata san lokacin da tace "kai alanguro Yarima" cikin wani irin amon murya mai nuni da tsoro da mamaki ba.
Murmushi yayi , tare da kai hannunta bakin sa ya sumbata ,
"me kika ce ? Aina kika ji wannan sunan ? Sake ƙira muji kamar naji kince wata kalma ta daban me kalmar ke nufi ?
Shiru tayi tana murmushi ,
"to shikenan idan baza ki zuba min ba , bakya ƙara fita a ɗakin nan sai gobe ,
Bai rufe baki ba ta laluba ta ɗau farantin ,
Tana turo baki ta zuba abincin tana faman kunkuni "yaushe kaji nace ba zan baka ba to?"
"Afuwan nayi tunanin kin fada a zuciyarki ne"
ta dauki cokali ta ciko shi taf "bude" tace kamar tana magana da baby.
Cokalin ya kalla a tsorace "duk wannan a bakina Fatima?"
Tayi murmushin keta "ba irin na Mama kake so ba? Haka nake bata"
"Amma ni da hannu nake so"
Tunanin yadda za ta tsere takeyi ta ajiye ta diba da hannunta tayi sama dashi tana laluben bakinsa,Hannu taji irin na mazan da suke gwagwarmayar yau da gobe ya rike tsintsiyar hannunta
a hankali ya kai bakinsa ya ci kadan sai da ya hadiye ya kara sai a karo na uku taji yatsunta gabadaya cikin bakinsa. Ita kanta bata san yanayin da ta tsinci kanta ba bare kuma shi uban gayyar da yake jin inama bakin tsiwar ya samu haka ba yatsunta ba kawai,
"Ashh Alangubro zaka cinye min yatsu ne ?
" da zan iya haɗiye ki ma baki ɗaya da na haɗiye ki Fatima , da kuma hakan shine kaɗai zai fiddani daga zullumi
Bata ce kome ba sai murmushi kaɗan da tayi , cikin ran ta tana aiyana , "ina ma da zata iya shigewa cikin jikinsa ta fake wataƙila da rabuwar su baza ta kasance ba ,
Cigaba tayi da ciyar da shi abincin , kafin ta ji ya riƙe hannun ta ,
"na ƙoshi Fatima , buɗe bakin ki na baku ke da Baby ,
Bata musa ba ta buɗe baki ya shiga ciyar da ita , ita ma kaɗan ta ci tace ta ƙoshi ,
"kaɗan kika ci Fatima , ki ƙara saboda Baby ,,
"Na ƙoshi , ai kaima kaɗan ka ci ,
Bai ce kome ba , sai jawo ta da yayi jikinsa ya haɗe ta da ƙirjinsa tsam-tsam ,
Cikin kunnen ta yace
" ina sonki Fatima Zahra ,
Lumshe idanun ta tayi , wasu siraran hawayen da bata san dalilin sauƙar su takamaimai ba suka silmiyo suka sauƙa a fatar ƙirjinsa , runtse ido yayi yana jin tausayin ta mai tarin yawa yana mamayarsa a wajen sa babu abar tausayi sama da ita ,
Sun ɗan yi mintoci kaɗan a haka kafin ya zare ta daga jikin sa , "Fatima , magarib tayi muyi Sallah ,
****
Bayan sun idar da Sallah sun yi addu'o'i shiru ne ya ratsa tsakani kafin Falmata tace
" ina so na shiga wajen Yakaka ,
Shiru Youssouf ya yi bai ce ƙala ba , saboda har ga Allah bai son su dunga kaɗaicewa saboda bai san da wacce manufa Yakaka take tafe ba , sai dai koma menene yana fatan kar Allah ya bata damar fayyacewa Fatima kome .
Jin yayi shiru ya sa Falmata sake cewa
"zance wajen Yakaka muyi hira kaɗan , ga shi Mama ma tana ta bacci ba abun na tayar da ita ba ta je Maman ta ta gan ta ,
"ki rabu da ita , mu je na raki ki kiyi mousu sallama ki dawo nan ki kwanta ki huta , gobe kun yi hira ,
Youssouf yace haka yana kama hannun Falmata cikin zuciyar sa dan babu yadda zai yi ne , da ba zai bari ta fita ba ,
Tare suka shiga har falon , basa nan dan haka Falmata ta ƙarasa ƙofar ɗakin Hajja , shi kuma ya dakata daga tsakiyar Falon ,
Ƙwanƙwasa ƙofar tayi ,
"Yakaka , na dawo .
Zuruf Hajja ta miƙe daga kishingiɗar da tayi tana jaan chasbaha , ta buɗo kofar tare da leƙowa ,
"uwarɗakina ai Yayar ki tayi bacci tuni , ki koma kiyi kwanciyar ki ki huta kun haɗu gobe da safe ko kuwa ,
Murmushi tayi , "kai Yakaka har tayi bacci ikon Allah ,
Ɗan jim tayi sai kuma ta sake cewa ," Hajja to ko cikin dare idan ta farka ki faɗa mata na zo muyi hira tana bacci , ai ta ci abinci ko ?
"ta ci abinci sosai ta cika cikinta dam ,
"to Hajja sai da safe ,
" yauwa uwarɗakina maza a je ayi bauta a huta ,
Har ta juya sai kuma ta sake dawowa ,
"amma , un, un Hajja nace da dai kin taso ta ta koma ɗakina , ina da filo mai laushi irin wanda take so , Yakaka bata son filo mai tauri irin naki Hajja ,
Wani kallon yatsu-tsu Hajja tayi mata ,
"aifa Lalle , ita Yakaka jaririya ce kenan ? To ai wannan surutun da kike ba kai ba ƙafafu ya isa ya tayar miki da ita daga baccin da na lallaɓata da kyar take yin sa , ni wuce Dan Allah ki tafi Allah ya tashe mu lafiya ,
Ƴar dariya Falmata tayi jin yadda Hajja take yi mata shaguɓe akan Yakaka , juyawa tayi ta kama hanya cikin ranta ba haka ta so ba , so tayi su raba dare suna hira da Yakaka , bata so Yakaka ta ga kamar ta kyale ta ta maƙalewa mijin da bata da tabbacin cigaban zaman su ,
Youssouf da sauri ya taryeta a cikin ransa yana hamdala da rashin ganawar su ,
Hajja tana komawa ɗaki ta dubi Yakaka da take zaune akan sallaya riƙe da Alkur'ani tana karatun ta hankali kwance , duk zantukan Falmata a kunnen ta , tausayi gami da ƙaunar 'yar uwar ta suna bin jinin jikinta da gudu ,
Hajja ta mokaɗe baki , lokacin da take komawa ta zauna a wajen da ta tashi ,
"ai a wani ƙaulin irin wannan ƙaryar tana iya zama makaruhi , ko kuwa ba haka ba Babba uwar Mama ?
Yakaka bata kulata ba ta cigaba da karatun ta , can ƙasan ranta diramar Hajja ta fara bata dariya ,
**
Youssouf , Yakaka , da Falmata kusan kowannen su raba dare yayi bai yi bacci ba musamman Youssouf da ƙiran sallan farko na ƙarfe uku da rabi a kunnuwan sa a hankali ya zame Falmata daga jikinsa wacce itama bata jima da samun bacci ba , ya miƙe tare da shiga banɗaki ya ɗora Alwala , jallabiya ya zira yazo ya tada sallah
Nafila yayi tayi har zuwa lokacin da masallatan unguwar suka sa Assalatu , sai ya sallame ya miƙe ya ɗau turare ya fesa tare da ɗaura agogon sa ,
Fita yayi ya nufi masallaci , bayan ya ja ƙofofin gidan gabaɗaya ,
Yana bada baya , mutumin da yake maƙale da jikin katangar , ya siɗaɗa kansa tsaye ya shiga gidan ,
Yakaka wacce ta shiga banɗaki domin ɗaura Alwala sallah ta ga inuwar mutum ya gifta ,
Tsam tayi tana tunanin waye ?
Haka kawai ta ji zuciyarta ta tsinke , sai ta juya da sauri ta fito , sannu-sannu take tafiya , hasken lantarki ya game ko'ina , gabaɗaya unguwar ƙiran sallah ne ta ko'ina ,
Mutum ta gani a tsaye ya bada baya yana nufar ƙofar falon Youssouf ,
"Waye ne ta ce
Idanunta ƙyar akansa ,
Chak aka tsaya ba tare da an jiyo ba ,
Matsawa tayi ta sake cewa waye ne nace ?
Ba'a amsa ba ,
Taku ta fara yi tana kusantar sa , ta zo kusa da shi bata ankara ba ta ji an kifa mata marin da ya gigitata ,
Tayi taga-taga tana jin wani tsuu a kunnuwanta saboda ƙarfin marin , ta ji takun gudunsa sai dai ta kasa watsakewa daga zafin marin da yayi mata dan haka bata yi wani yunƙuri ba ,
Lokacin da ta watsake babu kowa a wajen ,lokacin an idar da sallah gari har ya ɗan yi shaa ,
Yawatawa ta fara yi a wajen tana raba ido ko Allah zai sa ta ga azzalumin da ya mare ta haka ?
Ƙarar buɗe ƙofar gidan ya sa ta juyowa a tsorace , wanda ta hango ya shigo ya sa zuciyarta bugun uku-uku ,
Da sauri ta gyara zaman hijabinta , ta fara tattaro duk wata dauriya da ƙarfin halin da take da shi ta kuma shiga harhaɗa manyan kalmomi masu kaushi da take son yin amfani da su domin su taya ta tunkarar sa ,
Tirus , Youssouf yayi yana hangota , sarai ya gane ta , wani ɗan guntun yawu ya haɗiye lokacin da tunaninsa ya gama ba shi dalilin tsayuwar ta anan ,
Gyagijewa yayi a matsayin sa na soja bai kamata ya tsorata har haka ba .
Kai tsaye ya nufi ƙofar falonsa yana yin kamar ma bai san tana wajen ba ,
bai ƙarasa ba ya ji tashin muryarta ta ƙira cikakken sunan sa ,
" Youssouf Abdul-Aziz Baskore ,
Sai ya juyo a hankali ya fuskantota da takunsa mai girma , fuskar sa babu alamun ɗaukar wargi ,
"Gani
Yace da ita muryar sa a kwance tamkar fuskar sa ba a murtuke take ba ,
Cikin zallar ɓacin ran da yake tunkuɗo kansa daga ƙasan ranta da ta wanzu tana ɗauke da shi tsawon shekaru , ta ƙaraso daf da shi da taimakon hasken Alfijir da ya ƙeto ya dusashe hasken lantarkin wajen suke iya kallon fuskokin juna ,
" Nasan baka san wannan ranar zata zo ba , baka san cewa zan dawo ba , shiyasa har ka samu damar kutsawa cikin rayuwar ƙanwata, ka cuceni ka yaudareni , ka ɓata min rayuwa , ka lalatamin Asalin 'yata , ka sa rayuwata ta shiga garari kuma ka zo kana sake cutar min da ƙanwata , a karo na biyu kana sake gurɓata mata rayuwa , Allah zai saka mana abunda kayi mana , kai wanne irin marar imani ne macuci Azzalumi , Mayaudari kuma fasiƙi mazin ....
" KI MIN SHIRU .
Baisan lokacin da ya daka mata tsawa ba saboda kalamanta da yaji suna tayar masa da hankali , take jijiyoyin kansa suka fito ruɗu-ruɗu , idanunsa suka sauya launi , jikinsa har tsuma yake yi , irin tashin hankalin da yake ji , da akwai bindiga a hannunsa zai iya kai harbi .
Tsawar da yayi ita ta farkar da Falmata wacce taji tashin muryar sa a tsawace , shafa ɓangaren da yake tayi ta ji baya nan ,
Sassauta murya Youssouf yayi yana kallon Yakaka da take masa kallon sheƙeƙe kallon tsana kallon baka isa ba , , zata yi magana ya sake katse ta ,
"Nace kiyi shiru ,
zuciyar sa ya ji tana kai kawo wajen tuno masa da girman kuskuren sa , girman laifin da ya yiwa Yakaka , sai ya shiga ƙoƙarin sassauta fushin sa tabbas kome Yakaka zata faɗa masa ya cancanta , shi ɗin ai ya cutar da its dayawa kamar yadda tace ,
"ki yiwa Allah kiyi haƙuri , kiyi shiru mu bar kome a tsakanin mu ko dan saboda Albarkacin Fatima da Mama , ki faɗa min duk abunda kike buƙatar nayi miki zan yi ,
Ya furta hakan muryar sa a ƙasa yana satar kallon ƙofar falonsa,
Cikin rashin sanin sa Falmatan tana tsaye daga jikin ƙofar ta bayan labule kalmomin sa na ƙarshe kuma sun cigaba da sauƙa a kunnuwanta tarwai .
"Abunda nake so shine kawai ka sakar min ƙanwata , ka sake ta Youssouf ka kuma bani 'yata , Falmata baza ta taɓa cigaba da zama matarka ba muddin ina raye , ka auri Falmata Alhlin babu sanina ba kuma tare da amincewar wani nata ba , ya zama dole ka saki Falmata , ka sake ta nace .
Ganin yadda ta birkice masa tana ɗaga sauti tamkar bata cikin hayyacin ta yasa Youssouf ruɗewa yana gudun kar Falmata ko Hajja ɗayar su ta ji maganar , dan haka cikin yanayi na lallaɓa yace ,
" to naji naji , zan SAKE TA ,
Wani irin kallon kar ka raina ni Yakaka tayi masa ,
" yanzu nake son ka sake ta anan idan kuma ba haka ba wallahi zan je masarautar maraɗi a yau ba gobe ba ,
Da tashin hankali Youssouf yake kallon Yakaka , wacce ta tsattsare sa da ido babu alamun shakku a tare da ita ,
Gani yayi gabaɗaya ta rikiɗe masa tamkar ba yarinyar nan da ya rainawa wayo , ya kuma yi wasa da rayuwar ta a shekarun baya ba ,
Falmata wacce hawaye suka riga suka wanke mata fuska kamar ruwan fanfo, ta sanya tafukanta duk biyu ta rufe bakinta ta hana sautin kukan da take yi fitowa , a hankali ta silale ƙasa ta durƙusa tana jin yadda marar ta ta wani irin curewa guri guda ..
Assalamu Alaikum masu karatu da fatan kun wuni lafiya ?😍❤
Wai-wai , kai-kakai , yau wacce rana ?? 🤓😂
Uhmmm ai idan har baku daina sakar min bama-baman Comments da likes din ku irin na jiyan nan ba ( ko ma fiye da haka ) Nima kuwa ba zan yi k
ƙasa guiwa ba wajen cigaba da sasukar rubutu ba, "Ah to meye? Ai tuwon girma miyar sa nama, sannan kuma yaba kyauta tukuici. ❤😍
Amma kuyi hakuri da yadda bana samun damar maida muku da martanin sharhin ku, idan nace zan dunga daukar waya ba zan kammala aiyuka na da wuri har na samu damar typing ba , duk da haka nayi alkawarin zan bibiyi comments din ku baki daya na bada amsa inshaallah .
Nagode.
Na manta ko da wacce take buƙatar hayar ɗan Biri saboda tsaro ?! 🐒😂[11/26/2019, 3:24 PM] +234 706 503 6187: MAFARI
( Hargitsin Rayuwa)
Umm'muaz
42
Wani ɗan kuka ciki-ciki da Mama ta fara daga can cikin ɗakin kwanan su mai haɗe da nishi shi ya sa Falmata miƙewa daga inda ta durƙushe tana rishin kuka ,
A duƙe ta ƙarasa ɗakin saboda
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Chapter 110
Chapter 111
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 75 Chapter of 111