Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
tare da wasu nurses da wasu securites ,       Kuyi haƙuri sir , a fara duba gida ko suna chan , domin tare da ƴar uwar ta suka fita ,"    Wata kakkarfar tsawa doctor hamza ya yiwa likitan ,    Ka daina cewa tare da ƴar uwar ta suka fita , "    Ga ƴar uwar ta nan , ya juya yana nuno musu Falmata wacce ita ma ta miƙe tsaye tana rarraba ƙwayar idanun ta da son sanin meke faruwa?   Ita kaɗai ce ƴar uwar ta , ya zama dole ku nemo ta  , ba gudu tayi ba sace ta aka yi , Yakaka baza ta gudu ta bar Fatimah ƙanwar ta ba baza ta gudu ta bar baby mama ba , noorie baza ta min haka ba , ya ƙarashe da rawar murya yana jin yadda zuciyar sa ke cika da tsoron tabbatuwar hasashen mutanen asibitin ,"    Sir kayi haƙuri amma matar ka ba sace ta aka yi ba ita da ƙafafun ta suka fita tare da wacce tace sister nata ce , bayan tafiyar ka matar ta zo , tanan muka wuce da ita , wannan yarinyar da kace ita ce ƴar uwar ta tana zaune a wajen bata nuna ta san yarinyar ba basu mata magana ba su duka biyun , sai da muka je ɗakin , suka yi magana , kuma lokacin da nake fitowa da baby domin kai ta wurin mamar ta naga bayan wasu mata biyu suna fita , ina hasashen su ne , domin su ne kaɗai matan da aka ce an gani sun fita da hijabi tsukin awannin nan ," ka zo ma na nuna maka shaidar flask ɗin ruwan zafin da matar ta kawo , har yanzu yana ɗakin !,    Cewar wannan nurse ɗin da ta kai yakaka ɗakin hutuwa ," Bai ce ƙala ba ya bita a baya zuwa ɗakin , anan ya tadda flask ɗin da ta ambata tare da wata ɓakar leda da sauri ya ɗauki ledar ya buɗe ,    Babu kome a ciki sai hijabin yakakar wanda ta zo da shi asibitin ," hajabin da yayi wa farin sani domin shi da kan sa ya saya mata su guda biyar mabanbantan launika .     Shiru ne ya ratsa ɗakin ,"    Doctor hamza yayi shiru kan sa a sunkuye da alama ya zurfafa cikin tunanin me yake shirin faruwa ne ? Da gaske ta gudun ne ? To meyasa zata yi haka ?Anya tana cikin Hankalin ta ? Ko dai gida suka koma tare da RAHIMA ? Idan ba haka ba yaran wa suka sani ? Ina za ta ? Basu da kowa ƴan gudun hijira ne .    Ina baby ??   Da sauri babban likitan yace a je a zo da baby , yana fatan Allah ya sa wutar masifar da take son kunnuwa masa a asibiti kar ta kai ga ruruwa har ta ɓata masa sunan asibiti .    Nurse ɗin ta dawo tare da Baby wacce ɗumin tsaftatatcen ruwan da aka cika mata ciki da shi ya sa ta fara bacci ,"    Miƙa masa ita aka yi ya karɓe ta , bai ce ƙala ba ya jiyo ya fito daga ɗakin ,"    Wajen da ya bar Amne da Falmata nan ya dawo    Mu tafi gida yace da su ,! Ita Yakaka ta koma gida ne  ?  Meyasa ta tafi ta bar baby wanne irin shirme ne wannan ?       cewar Amne ,   Yaya dakta Ina yakaka ɗin ? Bata da lafiya ne ?     Shiru yayi bai amsa musu ba , ya tsinci kan sa cikin ruɗani ,    Kai tsaye gidan Amne ya nufa da su , Amne riƙe da jaririya tare da Falmata suna baya a zaune shi kuma yana jaan motar ,"     Takamaimai bai san tunanin me yake ba , abu ɗaya ne yake fata , shine ya je gida ya tadda ta tara da Rahima sun koma gida , wani tsoro-tsoron tabbatuwar bata gidan ya sa shi kin ɗaga waya ya ƙira rahima yafi so yaje gidan da kan sa ,"   Ku shiga gida Amne zan je na duba ta wataƙila sun koma gida ita da Rahima , ya furta hakan ba tare da ya bari sun haɗa ido da Amne ba wacce take kallon sa     Wai me su likitocin suka ce maka ne ? Cewa suka yi sun tafi gida ita da rahima ?      Waigowa yayi ya dube ta , da hannun ya nuna mata Falmata tare da yi mata Alamun roƙon tayi shiru ta bar maganar tukun , " duba da yadda a halin yanzu ma Falmatan duk a hargitse take tunda suka hau motar bata ce uffan ba sai faman share ƙwalla take tana jaan hanci ,"   Fita yayi ya buɗe mata kofar motar ,   Amne bata sake magana ba ta kamo hannun Falmata suka fito tare da jaririyar zuwa cikin gidan ta ," Komawa yayi cikin motar ya zauna ya ɗora hannuwan sa bisa kan Steering motar yayi shiru , zuciyar sa na kai kawo ,"    Ƙwanƙwasa gilashin motar da aka yi shi yasa shi ɗago kan sa ya sauke akan matashiyar yarinyar da ke tsaye a jikin motar sa ,"     Murmushi tayi masa ya ga lokacin da bakin ta ya motsa alamun gaisuwa ,"    Gyaɗa kai yayi kafin ya juyar da kansa ya fara ƙokarin tashin motar ,"   Zaton sa irin ƴan matan unguwar ne take gaishe sa ,"   Ƙara ƙwanƙwasa motar tayi da ɗan ƙarfin ta , tana masa magana ,"   Tsaki ya jaa mai sauti kafin ya sauke gilashin motar ,"       Kalaman ta suka doki kunnuwan sa da yasa ba shiri ya zuro kafafun sa wajen motar gami da miƙewa tsaye ,"    Me kika ce ?    Ɗan matsawa tayi baya kaɗan tana wani guntun murmushi tace    Yakaka ce ta aiko ni , tace na sanar da kai ita ta tafi Abuja wajen Baban Ƴar da ta haifa domin a ɗaura musu aure , dan haka kar ma ka sha wahalar neman ta bayan auren su nan da watanni kaɗan idan sun gama moneehmoon zata dawo kuma tace wai......      Marin da ya kwashe ta da shi ya hana ta ƙasara zancen ta ,sai da tayi taga-taga ta sunkuya , tana ɗagowa ya sake ƙara mata wani ,"      Shoƙo gelen wuyan ta yayi ya maƙure ta , "    Ina kuka kai ta ? Ke da su waye kuka haɗa baki kuka sace ta ? Zaki nuna min inda take ko sai na sada ki da jami'an ƴan sanda sun lallasa ki ,"    Idanun YAGANA sun fiirfito tace wallahi gaskiya nake faɗa , yakaka ƴar uwa ta ce tare muka zo garin nan , tun a sansani muke tare , cikin shege tayi madam ɗin da muke yiwa aiki ta kore ta , shine yanzu bayan ta haihu suka haɗa baki ita da uwarɗakin ta ta gudu zata koma wajen shi suyi aure ,"    Angaje ta baya yayi ,"   Ƙarya kike yi ,"ƙarya ne noorie ƙaramar yarinya ce bata isa shirya wannan wasan ba , ban yadda da ke ba , dole zaki faɗi gaskiya idan kika ji duka a wajen hukuma , wayar sa yake ƙoƙarin zarowa lokacin da ya ji tace ,"    Idan ƙarya nake bari na ƙira uwarɗakin nata ka ji muryar yakakar ma wallahi ,"    Bata saurari amsar da zai bayar ba ta danna ƙiran number samy baby bayan ta saka wayar a hands free , wacce daman jiran ƙiran yagana take , "     Dan haka ta rage gudun motar tare da gangarawa gefen hanya tayi parking sannan ta ɗauki wayar ,     Hello Doctor tace da shi , bata jira amsa sa ba ta juya harshe zuwa turanci ,"inda take cewa    Nasan zaka yi mamakin yadda abubuwa suka faru , wanda a zahiri ba wani abu bane na ban mamaki duba da yadda idanun ka suka makance basirar ka ta toshe , zuciyar ka kuma ta mace akan son yarinya yakaka , ita ma haka tata zuciyar ta mace , ta samu toshewar basira tare da makancewa cikin son wanda zuciyar ta ta zaɓa har ma ta daɗe da mallaka masa ruhi tare da gangar jikin ta baki ɗaya , " ba wani bane wannan illah uban ƴar ta wanda soyayya ta sa ta bashi kan ta , har kuma ta zaɓi rabuwa da ƴar ta tare da ƙanwar ta saboda ta tsira da shi , kana mamaki ko ? Ko kuwa zato kake ƙarya ne ," tunanin ka shiri ne koh ?  To bari ka ji kasan daman waƙa a bakin mai ita yafi daɗin sauraro ," Juya harshe tayi ta dawo hausa , Yaks , Yaks ,    Ke yaks    A hankali ta ɗago kan ta da yake bala'in sara mata ta kalle ta da idanun ta da suke cike taf da hawayen tausayin kai ," duk da daman tana jin ta tana waya da turancin da ba fahimtar sa take ba , ba bacci take ba ,    Na'am anty samy ," Ga Yariman naki ko kuwa me ma kike ƙiran masoyin naki ??    Cikin sanyin muryar tace Bature kam silum ?   Eh shine akan wayar riƙe kuyi magana ,"    Anty samy kice masa kawai ina zuwa zan zo wajen sa zaki kawo ni , bana jin yin dogon magana , zuciya ta ciwo take min ban san a wanne hali Falmata take ciki ba ,"      Cije baki samy baby tayi tana hararar yakaka da ta lura tana son ɓata mata shiri ,"    Bana son kinibibi bake kika yadda zaki wajen nasa ba ko na mayar ki ne ?    Shiru tayi bata ce e ba ko a ah   Karɓi wayar ki masa magana ya ji ki ,"    Alo Bature kam silum , gani nan zan zo wajen ka , anty samy zata kawo ni , amma gobe nake so mu dawo mu ɗauki su Falmata da mama , sai muyi aure mu zauna tare da su Dan Allah bazan iya zama babu su ba ina son ku ku duka sosai ka yadda koh ?      Ƙarɓe kan wayar samy baby tayi tana murmushin nasara , ta koma turanci     Sauran ƙarin bayanin da zai iya gamsar da kai yana cikin kayan ta tare da wayar ta da ta bari a gidan ku , da fatan zaka rungumi haƙuri , ka nemo matar da zata iya mallaka maka ruhin ta tare da sadauƙarwa irin wanda yakaka tayi ga masoyin ta ," idan kunne yaji .... ? Tace da shi tana sauke wayar a kunnen ta tare da latse ta ta kashe ta tada motar tana fincikar ta da ƙarfi ..    Tun kafin ta gama furto zantukan ta yake jin wani abu mai kama da hayaki yana lullube masa zuciya wani irin ƙaƙƙarfan kishi da tsanar yarinyar suka tarwatsa masa rai da ya sa jin kan sa na juyawa , tabbas ta yaudare shi , yaudara mai girma , ta ha'ince shi ta kuma butulce masa ," Amma anya , toh Anya gaskiya ne anya ba tursasa noorie aka yi ba ,! Anya tana da wayo tare da hikimar yin mummunar yaudara irin haka , sashin zuciyar sa da soƴayyar ta tayi ƙarfi ta kafa rassa ke son kawo uziri ke son bata kariya ke son wanke ta , ke son fidda zargi a tsakani , Bai bi ta kan yagana ba ya faɗa cikin motar sa ya jaa da ƙarfi gami da nufar gida domin ganin shidar da aka ce akwai , Gyara gelen ta tayi wanda ya cukurkuɗe , kafin ta ce     Wannan Banzan har mari na yayi akan wata banzar sokuwar yakaka , oho dai a yau zan yi kwanan farin ciki sanin cewa yakaka tayi nisa da garin maiduguri baki ɗaya , " babu ranar dawowa !   Kai kuma marin nan wallahi bashi ka ɗauka , zan rama shi ta wata hanyar da baka yi zato ba a kuma lokacin da baka yi tsammani ba ,     Wucewa tayi ta kutsa cikin unguwar da daman take ta su , tana hararar gidan Amnee inda take da tabbacin ciki jinin Yakaka suka yi bigire ,"     Cikin ran ta ta fara saƙa da mummunar zaren da zai iya zargewa har da ita ,"      Kusan da gudu-gudu ya shiga sashin su Rahima bai ko tsaya rufe ƙofar motar sa ba ,"    Rahima , Rahima , Rahima yake ƙwalawa ƙira ,   Da gudu ta fito daga ɗakin ta tana ƙoƙarin ɗaura ɗankwalin ta ta shirya tsaf domin zuwa asibitin wajen su Yakaka , jin shirun yayi yawa tun hantsi har ga shi ƙarfe uku ta ƙarato.ta tabbatar zuwa yanzu ta haihu ," Na'am big bro , ina su Yakaka ya jikin nata ? Ta haihu ,? Me muka samu ? Ina wajen kayan su yake ?  Yace da ita haka idanun sa sun kaɗa ,"   Kayan su wa ?   Fatima .   yace da ita Wani abu zan ɗauko maka ?  Me zan ɗauko maka big bro ta haihu ko ? Me ta haifa ? Ina wajen kayan su nace miki , ya daka mata tsawar da ta firgita ta ,   Da hannu ta nuna masa ɗakin su Yana cikin wardrobe ,   Kayan yayar fatima nake nufi Duk kayan su a haɗe suke big bro , ta furta hakan tana karya wuya , ran ta cike taf da jimamin abun da ya hatgitsa musu ɗan uwa haka ,"      Watsi yake da kayan su yana hautsinawa , har zuwa lokacin da idanun sa suka sauka kan ɗan ƙaramin hoton tare da agogo haɗi da damin kuɗin niger da suke chan ƙasan kayan ta ,"    Zuciyar sa na bugawa ya ɗauki ƙaramin hoton fasfo ɗin gami da kai idanun sa kan fuskar kyakkyawan bamarɗen ingarman saurayin da bai fi sa'an sa ba jikin sa sanye da kakin soji na ƙasar niger , hoton a zamunance yake babu wani alamun tsufa ,"   Tabbas shine ba tantama kome gaskiya ne , ya aina haka cikin ran sa lokacin da yake sake jujjuya agogon da rannan ya gan shi a hannun ta , tace masa na BABAN ta ne , tunowa yayi da ranar da ta nace ya kai ta bakin kasuwa , tace cikin kayan ta akwai hoton BABAN ta , ashe duk ƙarya take masa , ashe yaudarar sa take , ashe ganin yarinya ƙarama yake mata ita kuma tana masa kallon soko ?   Sakin hoton yayi tare da agogon suka faɗi ƙasa kan suturun ta da ya saya mata ya fara taku da nufin barin ɗakin    Lokacin da ya ji kafafun sa sun sauka akan ƴar ƙaramar wayar da take jefe a ɗakin , sunkuyawa yayi ya ɗauka ,    Ya kunna ta ,   Call logs ya shiga nan ya ci karo da number da aka rubuta HUBBY BB a jikin ta ,    Bi ya dunga yi yana ganin yadda suke ƙiran juna ita da number kusan kullum sai sun yi waya , " tun wajen wata guda da ya wuce , " ji yayi idanun sa na shirin kawo hawaye , a sarari ya furta ta yaudare ni , BATA SO NA BATA TAƁA SO NA BA ,"   Jefar da wayar yayi yana barin ɗakin cikin ran sa yana tunano irin baya-baya da take yi da shi a tun haɗuwar su , yadda take janye jiki daga mu'amala da shi , yadda baya ganin fara'ar ta , bata sakin jiki tayi magana da shi , bata ɗaukar sa da wani muhimmanci , ashe bata son shi ne , ashe tana da wanda take so suka yi soyayya mai girma da har ta kai su ga aikata zina , ashe shiyasa take son cikin jikin ta kamar ba shege bane , soyayyar uban cikin ne ta shafi ɗan , ashe son da take yiwa wannan mutumin ya wuce son da take yiwa ƴar cikin ta tare da ƴar uwar ta ?? Tunowa yayi da kalamar ta ta ƙarshe inda tace TANA SON SU SU DUKA ," ji yayi duk wani jijiyar da ta kafa so da ƙaunar ta cikin ran shi tana tsinkewa , son ta da ƙaunar ta suna mutuwa ,"   Bai san ina yake taka ƙafafun sa ba saboda yadda zuciyar sa ta shiga ruɗani , sai tsintar kan sa yayi a tsakiyar falon Baban su ,    Ɗago kan sa professor Mustapha Dilmari yayi ya dube ɗan nasa , tashin hankali da damuwar da ya hango a fuskar ɗan nasa ya sanya shi ajiye doguwar jaridar "daily trust" ɗin da ke hannun sa ," yace da shi    Doctor yaya yarinyar nan ta sauka lafiya ?     motsa bakin sa yayi maƙogoran sa na kai kawo , ya haɗa jimlar kalmar da ta tabbatu ta fito tun daga Ƙasan ruhin sa ,       TA MUTU innalillahi wa innaa ilaihi raji'oon , ta rasu ,? Wajen haihuwar ? Allahu Akbar , yi sauri ka sanar da jama'a a zo ayi mata sutura , ina abun da ta haifa ko tare suka tafi ,? "   An mata sutura a chan asibitin kamar yadda aka saba yiwa ƴan gudun hijira ƴan uwan ta idan sun rasu ba'a jiran mutanen su ,"ma'aikatan asibiti tare da sauran Al'ummar musulmai suke sallatar su a wuce da su makwancin su  ,,"    Daga haka ya miƙe ya bar mahaifin nasa yana jero addu'o'in da ake yiwa mamata ,    Bai jin yayi kuskure akan kalmar da ya furta ga mahaifin sa , ƙwarai ta MUTU  a cikin zuciyar sa kamar yadda cikin kowanne daƙika ɗaya yake sake yakice ta tare da nesanta ta da duniyar sa nisa irin na har abada , Shi yayi ƙarya ga mahifin sa da ƴan uwan sa , ya wanke ta ya rufa mata bargon asiri tare da kyautata mata zato da kyakkyawar niyyah, yanzu da kome ya bayyana gare shi ya fahimci wacece ita ,  dan haka ya sake yin wata ƙaryar da yake fatan ta zama babbar ƙarya ta ƙarshe da zai yi a rayuwar sa yayi amfani da ƙaryar ta hanyar zare ta daga rayuwar duk wani da ya shafe shi tare da shafe babin ta cikin rayuwar duk wani nasa domin ita ɗin bata chanchanta ba ... Shiru shiru Amne bata ga dawowar hamza ba da take tsumayen ganin sa tare da yakaka tayi ta ƙiran wayar sa shiru ba'a ɗauka Ga kuma baby da take ta faman tsanyara kukan yunwa duk da cewa tun shigowar su ta ɗaura ruwan zafi ta wanke jaririyar tas ta sauya mata kaya tare da diaper a cikin kayayyakin ta da suka zo da su daga asibiti , amma daga lokacin da aka haife ta tun hantsi zuwa yanzu la'asar sakaliya dole jaririyar ta ji mummunar yunwa , Gefe guda ƙarin damuwar ta na ga Falmata wacce tun tana kuka ƙasa-ƙasa , zuwa yanzu kuka take riris tana ambaton sunan yakakar babu tsahirtawa , tayi rarrashin duniyar nan Falmata taƙi shiru , taƙi ci taƙi sha , sallah ma sai da tace ta tashi tayi addu'ar Allah ya sa yakaka na a halin lafiya sannan ta tashi tayi , Ganin dare na neman yi babu abun da zata bawa ƴar jaririyar nan ya sanya ta rufe kai ta nannaɗe jaririyar da kyau ta ɗau kuɗi mai ɗan yawa ta fita nemo mata abinda zata ciyar da ita da shi ,"  kasantuwar a kusa da kasuwa unguwar tasu take , dan haka bata sha wahala ba wurin samun madarar jarirai mai kyau tare da feeding bottle a ɗaya daga cikin shagunan da suke jikin kasuwa wanɗanda basu kai ga rufewa ba ta saya , ta tsallako titi zuwa gida, Wurin da ta bar falmata nan ta tadda ta zaune kan ta haɗe da jikin bango ,    Bata bi ta kan ta ba kamar yadda falmatan ma bata nuna taji motsin ta ba , ta kwantar da jaririyar ta wanke feeding bottle ɗin ta haɗa mata madarar dai-dai yadda aka ka'idance  da ruwan ɗumi , ta ɗan bar ta ta huce dai-dai yadda jariri zai iya sha ta ɗauke ta tayi bismillah , ta fara bata ,     Nan take kuwa ta kama bakin feeder tana jaa ,    Sannu sannu sai da ta sha fiye da rabi , bacci ya ɗauke ta , Ganin ta maida kan falmata bayan ta shinfiɗe jaririyar ,"   Tausayin falmatan ya tsarga mata , cikin ɗan zaman da tayi da yaran lokacin bikin zainab ta fahimci yadda yaran suka shaƙu da juna suke kuma ƙaunar juna tare da tattalin juna ,    Ɗan ƙaramin tsaki ta jaa lokacin da take ɗaukar wayar ta domin sake ƙiran Doctor Hamza ,    Ni ban san ina ya bar wayar ba haka , ina ta ƙira baya ɗauka ya bar mu cikin fargabar halin da yarinyar nan ke ciki bari na ƙira Rahima naji ko yana gidan ne ," Bugu ɗaya Rahima ta ɗauka ta ɗauka   Abnaty ina yayan ku ne ? yaya an san inda yarinyar nan ta tafi kuwa ?   Shiru Rahima tayi tana ƙoƙarin tsayar da ƙwallar idanun ta ,"   Yayan mu ya dawo tun ɗazu hankalin sa a tashe , ya shiga sashin sa ya kulle , sai yanzu da naje gurin Baba , yake sanar da ni wai ashe yakaka ɗin ta rasu ne wajen haihuwa ,"     Innalillahi wa inna ilahi raji'oon Amne ta ƙara da salati ,    Bata ce kome ba ta sauƙe wayar daga kunnen ta , tare da kai kallon ta ga falmata wacce tayi kasaƙe tana son fahimtar  menene ,:       Muryar ta ƙasa tace Amne wai me Rahima tace ? Wani abu ya samu yakaka ko ? Amne Dan Allah kar ki ɓoye min ni da yakaka bama boyewa juna kome , yakaka ita ce kome na , ita ce mama na , baba na yaya ta kuma ƙawa ta meye ya same ta ? Dan Allah ku kaini na gan ta ,      ta furta hakan tana me sake fashewa da wani sabon kukan da yasa hawaye silmiyowa bisa ƙuncin ta , tana jin wani tsohon miƙi makamancin raunin da zuciyar Falmata ke ciki yana ɗanyencewa cikin nata ran , amsa kuwwar kalmai makamanta wannan da suka fito daga bakin Rahimar ta yana maimaituwa a kunnuwan ta ,"   Sai ta gaza rarrashin Falmatan . Washegari Bayan fitowar doctor Hamza daga masallacin sallar asubah kai tsaye sashin mahaifin sa ya shigo kamar yadda ya saba , kan shi a ƙasa suka gaisa da mahaifin sa wanda yake nazarin ɗan nasa ba tun yau ba ya fahimci akwai wata ɓoyayyar manufa a zuciyar ɗan nasa game da yarinyar ya bari ne yaga iya gudun ruwan sa , amma tundaga yadda ya ɗau komen su da muhimmanci ya fahimci yana da ra'ayi akan ɗayar su ,"   Tausayin sa ya ji mutuwar yarinya da irin birkicewar da yayi ya sashi fahimtar wataƙila ita zuciyar sa ke ra'ayi Addu'a ya sake yi masa sannan ya ɗora da tambayar sa ina ƴar uwar ta ? Nan yayi shiru ,   Kafin yace Suna gidan Amne ita da jaririyar da uwar ta bari , Nan take fuskar professor ya sauya   Gidan Amina ?    Me kuma ya kai su gidan Amina ? Na kai su ne wai dan ta kula da su musamman ma jaririyar .   Ita Amina MACE ɗin ce za'a bawa kulawa tare da tarbiyyar yara mata har biyu ? ?  To ban amince ba maza idan gari ya gama haske kaje ka zo da su , tunda ka kawo yaran nan gidan nan ikon su ya bar hannun ka ya dawo ƙarƙashi na , ni nake da ikon kulawa da su , nima ina ƙwaɗayin samun ladan rikon marayu da marasa galihu , kan Ji na ko ?    Toh Baba Ya

Chapter 38 of 111