Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
," uwa uba tashin hankalin da zuciyar sa ke ciki , wanda duk wata ƴar sakewa da yayi suka ɗan taɓa hira da abokan tafeedan kawai ɗaurewa yake , sam bashi da nutsuwar zuci , tafeedan da kan sa ya fahimci hakan . Duk yadda yaso janye tafeeda su bar gidan ƙi yayi a cewar sa shi tsarin yanayin al'adar su ta burge shi dan haka zai ɗaukar wa mairamar sarki hotunan su haɗi da videos ya je ya nuna mata ,"    Da ace ya san kan garin ko kuma shi ya tuƙo kan sa ya zo , da tuni yayi tafiyar sa daga wajen , domin a halin yanzu ma chan gefe ya samu ya tsaya yana faman ciccin magani ,da ginshirin su irin na sarakai ,"  '"ah toh yarima anan wa zaka yiwa ?? Gani yayi gurin bai masa ba saboda yadda hankalin ƴan mata dayawa yake kan sa , dan haka kawai sai ya bi wata ƴar hanyar da ya gani daga gaba da inda yake tsaye kaɗan ," ba tare da ya san ina bane , sai dan gani da yayi akwai alamun rashin mutane ta wajen ,"   Ƴar siriyar hanyar ya shiga inda yake hango wani ɗan tudu da zai iya zama akai , sai da ya isa wajen ya lura da tsayuwar wata yarinya daga gefe a raɓe da jikin bango tana fuskantar ciki ,"   bai kula da wanzuwar ta ba ya zaro wayar sa ya shiga dubawa bayan ya zauna ,"   Tun takun sa na farko a wajen ta ji shi , ta cigaba da jin tahowar sa kafin daga baya ta ji an zauna a ɗan nesa da ita ,  jin shiru ya sa ta waiwayo ba domin tana son ganin wanene ba sai domin ta fargar da wanda ke wajen samuwar ta a wurin ,"   sun jima a haka shi ya manta ma da ya ga mutum a farkon zuwan sa wurin ,      Kamar ance ya ɗago kan sa , karaf ya sauke akan ta tana nan a inda ya gan ta tun farkon zuwan sa wajen ," idanun ta fes akan sa bata ko kifta su ,"    Shima kallon ta yayi sosai , ya ga dai ta tsare shi da manyan idanun ta da yake iya hango girman su da sheƙin da suke a sauran hasken ranar da take gaf da faɗuwa , " kamar shi take kallo kamar kuma ba shi ɗin take gani kai tsaye ba ," Yarinya ce a idanun sa bata wuce mairamar sa ba , a idanun sa ma sai ya ga tana yimar yanayi da mairamar yanayin yadda ta tsaya daga jikin bango alama fushi tayi taƙi fita zuwa wajen bikin nasu ,"        ɗan murmushi yayi tunowa da yayi da rigimar mairama yana jin kewar ta na taso masa ,"   Tsintar kan sa yayi da son yayi mata magana tun da ta rasa mai rarrashin ta ta huce,"    Ƙanwa ta ke baki gajiya ne da tsayuwa ??    Wara idanun ta tayi lokacin da ta ji tashin muryar sa , wannan ba doctor hamza bane ,toh WANENE ??? Da sauri yakaka take ratsa mutane tana son fitowa daga cinkoson gurin da ya sake ruɗawa da buɗa haɗi da sowa ana ɓarin kuɗi sakamakon shigowar ango da amarya cikin filin rawar ,"   dakyar ta samu fitowa ta nufi hanyar sashin doctor hamza , duk hankalin ta yayi kan falmata , bikin ya ɗauki hankalin ta har bata san ta ɗauki lokaci haka ba sai da ta ga duhun dare ya fara shigowa ta farga ! GAN,GAN ,GANNN ! GA ƁARAWO GA MAI KAYA , ƘAƘA TSARA ƘAƘA ??? DAFATAN ZAKU BAIBAYENI DA RUWAN RA'AYOYIN KU , GAME DA WANNAN SHAFIN , ME KUKA HANGO ME KUKA FAHIMTA ME KUMA KE SHIRIN FARUWA ?? KAI ABUBUWA DAYAWA FA , GA SUNAN DAKI-DAKI . BAN SAN KO KUN GANE BA ??? BARKA DA SALLAH ONCE AGAIN ! 😍🙏             [6/24, 10:59 AM] +234 701 013 7848: Mafari .... ( Hargitsin Rayuwa ) umm'muaz 26 Ji tayi an riƙo hannun ta ta baya , tana daf da ƙarasawa sashin doctor hamza , fuskar ta da murmushi ta juyo ga zaton ta rahima ce ,"     Rahima , Falmata nake son na duba , kin ga dare ya fara yi bana son .....    Sauran kalmomin ta maƙalewa suka yi a fatar bakin ta lokacin da tayi arba da fuskar samy baby a maimakon rahimar da take zato ,     An-anty samy  ke ce ??   Ba tare da samy baby ta saki hannun ta ba ta fara tafiya tana nufar cikin gidan da ita sashin su rahima , ba musu ta bita tana waiwayen hanyar sashin doctor hamza , da fatan ko zata hango falmata , yayin da ran ta yake cike taf da fargaban abun da samy baby zata bijiro mata da shi ," Waye ne a anan ? Falmata ta furta hakan tana mai sake wara ƙwayar idanun ta ," Shiru youssouf yayi  tare da kafe ta da ido ,   Watau dai ita mace kome ƙanƙantar ta mace ce ," ji wannan ƴar yarinyar ma wai dan kawai nayi mata magana shine har zata min gwalangwaso da fi'ili ta nuna ma bata ma ganni ba sam.,"  tsaki ya jaa gami da mayar da hankalin sa kan wayar sa , Sarai ta ji tsakin da yayi mata kasantuwar ta mai nisan ji , ko yaya abu yayi motsi tana iya ji tun daga ƙasan ran ta ," jikin ta taji yayi sanyi ," koma waye bai gane bata gani ba , " ba laifin ta bane ," Dan haka ta juya a hankali tana laluben jikin bango da nufin komawa ɗakin doctor hamza ," Kiran wayar sa da Tafeedah yayi shi ya sanya shi miƙewa bayan ya ɗaga kiran inda yake sanar da shi ya zo su tafi masallaci daga chan kuma su wuce masauƙin su sai kuma gobe su dawo ɗaurin aure ! Da sassarfa ya bar gurin da daman jin sa yake tamkar akan ƙaya ! Tsumu yakaka tayi a gaban samy baby wacce ta tsare ta da tarin tambayoyi wani kan wani ," Sake ɗagowa tayi a karo biyu ta dubi samy baby kafin ta muskuta cikin yin ƙasa da murya tace :    Antƴ samy a gidan nan muke da zama ni da falmata , kuma yaya dakta shi ya kawo mu ,"    Wanene yaya doctor ? Kina nufin likita yayan su zainab ? Gyaɗa kai tayi   Shi ne ! Daman ya san ku ne ? Ko ƴan uwan ku ne ??   Kawai ya taimake mu ne bamu san shi ba amma tun farkon zuwan mu garin nan tun muna sansanin mu yake taimaka mana !   Jimm samy baby tayi tana aunawa tare da juya zantukan Yakaka cikin ran ta ,"    Meye tsakanin ku da shi ? Ya taɓa cewa yana son ki ne ? Da sauri ta girgiza kan ta   A ah ni baya so na ! Bai tambaye ki akan cikin jikin ki ba ?  Me kika ce masa game da cikin ? Cewa yayi waye ya min cikin ? Ni kuma ban faɗa masa ba , tun daga ranar bai sake tambaya ta akan cikin ba , sai ya kawo mu gidan su nan , yace mu zauna , yana kula da mu sosai ni da falmata , har asibiti yake kai ni ayiwa baby photo dan Allah kar ki sa su kore mu anty samy bamu da wani wajen da zamu je a yanzu da ya fi nan ,    Ta ƙarasa zancen hawayen da take tarawa a ido suna silmiyowa ," Guntun murmushi tayi   Ni bazan sa su kore ku ba yaks , ki daina kuka ,!      iyeeh watau har hoto aka yiwa baby ? kice dai kin shirya zama uwa sosai yaks    jaan numfashi tayi kafin ta sake  wurgo mata wata tambayar da ta sa zuciyar yakaka tsalle ,"    Ya labarin yarima uban cikin jikin ki ko har kin haƙura da neman na shi kin daina son shi saboda kin samu gidan hutu ?   Ban - ban daina son shi ba anty samy kullum yana raina inason sake ganin sa , ban san yadda zan yi na gan shi ba ne ,! Ko kin samu labarin inda yake ? Murmushi tayi    Nasan inda yake yaks ! Zuruf ta miƙe tsaye batare da ta ji nawin cikin jikin ta ba ta matsa ta kamo hannun samy baby ta riƙe gam.,    Aina yake anty samy dan Allah ki kaini wajen sa , wallahi ina son shi , ina son na gan shi ki taimake ni ! Koma ki zauna yaks ba abun gaggawa bane , ki nutsu akwai maganar da nake so muyi da ke , amma....    Shigowar sofi ta katse abun da samy baby take nufin cewa ,    Da wani irin hargitsatsen kallo ta bi yakaka , kafin ta juya akalar hararar ta ta kan samy baby ,"    Ke kuma me ya haɗa ki da wannan koɗaɗɗiyar ƴar gudun hijrar ?? Ko wani aiki zata miki ? Nifa na tsane su yi sauri ki sallame ta duk ta cika mana  wuri da tsami da hamami ,"   Ba tare da samy baby ta amsa mata ba tace ga yakaka Ta shi ki tafi abin ki , Cikin sanyin jiki yakaka ta miƙe tana satar kallon sofi ,haushin ta na cinkushe mata rai ," sam ran ta bai so ba da zata bar gurin ba tare da taji wani ƙwaƙƙwaran bayani game da bature kam silum ba ,"  ta so ta ji ina yake da zama da babu abun da zai hana gobe ta je ta gan shi ko da kuwa da kwatance ne! Dai-dai tazo barin ɗakin ta waiwayo suka haɗa ido da sofi wacce take bin ta da kallon banza ," bata yi ƙasa a guiwa ba ita ma ta galla mata harara tana mai ƙarasa barin ɗakin ," Duka samy baby ta ɗakawa sofi a cinyar ta wacce take ta faman baloƙoƙo akan hararar da yakaka tayi mata sai faman zagin ta take tamkar zararriya    Ƙawata ke fa banza ce yanzu akan wannan ƙanƙanuwar yarinyar kike ta ɗaga murya haka ?  Alhali ma tayi tafiyar ta ," ko dai haushin kaza kike huce akan dami ," hala shi autan mazan ya miki abunda ya saba ?   Cisge ɗankwalin kan ta tayi jelar gashin dokin da tayi manyan kitson ghana suka watsu akan kafaɗun ta," Bari kawai kawata wannan ɗan tahalikin yana son ƙure gejin hakuri na akan sa , " bai san cewa akan sa kaɗai sashin zuciyata mai mutunci take iya tasiri ba , amma tunda yaƙi ta  mutunci toh fa ko da tsiya -tsiya wallahi sai ya so ni kuma ya aure ni , sannan na juya shi yadda na so a lokacin da na so , Naga shege ko shegiyar da ta isa yin min katanga da cikar burina , wallahi ko gyatumin sa sun yi tsororo !  Hamza nawa ne ni kaɗai , Da kallo samy baby ta bita tana nazarin kalaman ta tare da ɗauko kulawar da hamza yake bawa su yakaka tana haɗa su tare da yin dogon nazari , ita tasan wacece sofi tasan bala'i da kaidin sofi , bata fata ko kusa ko kaɗan ace wani sha'ani na adawa ya ratsa tsakanin ta da yakaka , wacece yakaka ? Bata tunanin ko uwar yakaka ta isa karawa da sofi akan abun da take ƙwalafacin so bare yakaka , tana tausayin yakaka da gaske baza ta so ba ta faɗo hannun sofi ta wannan mummunar hanya , ta sani sarai cikin ƙanƙanin lokaci sofi zata ɓatar da yakaka daga doron ƙasa ," Tunanin ta ya katse lokacin da ta ji sofi tana cewa    Wai kin kuwa san ma me yayi min ? Bata jira amsar samy baby ba ta ɗora ,    Tsawa fa ya min a bainin nasi , dan kawai na nemi ya tsaya muyi hoto ,"    Ta ƙuta , ai wallahi bashi ya ɗauka , zai kuma biya da tsada lokacin da ya shigo hannun na ,    Ta miƙe tana mai nufar bathroom , Da kallo samy baby ta bita ,"  ya zama dole tayi wani yunƙuri domin ganin ta hana wannan yaƙin faruwa tsakanin ƙaramar yarinya yakaka da sofi , dole ta zare yakaka daga rayuwar hamza muddin ta gano yana da manufar soyayya da yaks ɗin kamar yadda ta hasaso , " ai idan ka ga kare na sunsuna takalmi ɗauka zai yi ," kuma banza bata kai zomo kasuwa ," 10:30pm Duk yadda Tafeedah ya kai ga son sanin meke damun Youssouf da har ya firgita shi ya zama barazana ga nutsuwar sa , Youssouf ɗin yaƙi faɗi masa , iyaka yace masa ya gaji ne da zaman nigeria yana son komawa ƙasar su , wanda shi Tafeedah ko kusa zancen bai shige sa ba , tayaya Youssouf masoyi ga aikin sa kuma jajirtatcen jarumi a fagen daga zaƙwaƙuri wurin bawa ƙasar sa kariya tare da sadauƙarwa zai ce ya gajiya ? Babu shakka akwai wani abu wanda yayi girman da yake neman jirkita masa tunanin aboki da shi bai kai ga sanin wannan lamarin ba ," Kallon sa ya mayar ga Youssouf ɗin wanda yake kwance bisa gado ya takure cikin bargo gami da bashi baya , ji yayi duk wani ɗan kuzarin da yayi saura a jikin sa yana barin sa , bayan tsawon watanni tara da rabuwa da ganin junan su , yau sun haɗu amma babu wani armashi a haɗuwar ta su kamar yadda suka saba ya haka idan aiki ya shataa layi ya raba su , toh fa duk ranar da suka haɗu kusan raba dare suke suna hirarraki da dararrakin su ta hanya bawa juna labarukan bayan rabuwar su , " Youssouf amini ne a gare shi ƙari kuma ɗan ouwan sa ne na jini , amintakar su mai ƙarfi ce ta yadda idan ɗaya ya kasance cikin damuwa ɗayan ya kan gaza sukuni har sai sun haɗu sun samarwa da kan su mafita , damuwar sa a yanzu bai wuce yadda Youssouf ɗin yake kokarin boye masa abun da ke damun sa ba , da hakan yake baƙon lamari a tsakanin su  sai dai ko ma menene zai bi a sannu har ya kai ga sani , Ga Youssouf ɗin kuwa damuwa ce ta yi masa katutu , kan ɓacewar yakaka , mafi girman lamarin shine cikin da aka ce tana tare da shi , tunanin sa idan ba'a kai ga samun ta ba har ya bar nigeria yaya zai yi ?? Shikenan zai tafi ya cigaba da rayuwa alhalin wata na nan ta wanzu tana aikata babban zunubi ana raba musu tare ?? Wannan lamarin ya girmama a gare shi danasani kuwa yayi ta yafi sau shurin masaƙi , a bayan kowacce daƙiƙa damuwa ke sake masa lullubi , ya ƙagauta gari ya waye ya sake komawa gidan madam Saly ya ji yaya aka kwana  ?  Yawan damuwar ita ta bayyana kan ta ga Tafeeda wanda a zahiri bai shirya ba baya kuma fatan wani nasa makusanci ya san irin ta'asar da ya aikata a rayuwar sa , duk da yasan Tafeeda aminin sa ne , amma bashi da karfin guiwar sanar da shi wannan auka-aukar da yayi , to ma me zai ce ? Ta ina zai fara ? Ko babu kome shi ɗan nasaba ne , ɗan sarauta , ɗan manyan mutane wanda wurin su ake hangen kyaun tarbiyya tare da nagarta har mutane suyi koyi , yana jin zuciyar sa na nawi a duk lokacin da ya tuno da matsayin sa tare da martabar sa ga idanun tarin wasu mutane YARIMA ne shi wanda ake sa ran bayan shuɗewar wani lokaci idan da rai ya zama SARKI , JAGORA kuma SHUGABA abin KOYI , Anya-anya shi bai faɗa cikin wata babbar musifa ba kuwa ?? Ya ɗauki tsawon lokaci a haka yana kwance ba kuma bacci yake ba har zuwa lokacin da ya tabbatar bacci ya ɗauki Tafeeda , sannan ya miƙe gami da shiga banɗaki ya ɗauro Alwala ya zo ya fuskanci Al-Qibla yana mai fatan Allah ya kawo masa mafita ya kuma yafe masa zuban sa ! Kewar da take binne cikin ran yakaka tare da tsananin son biyamuradi youssouf sune suka yi toroƙo suka hana ta sukuni tun bayan rabuwar ta da samy baby , har ƙamshin sa ta dunga jiyowa lokacin da ta sanya kafafun ta cikin sashin doctor hamza wanda yayi mata jagora har zuwa cikin falo , illahirin tsukin wajen ya ɗauki kamshin kakkarfan turaren biyamuradi youssouf wanda yayi tasiri matuƙa wurin ƙarasa lugui-guita rarraunar zuciyar yakaka ta ƙarasa narkewa cikin so da begen biyamuradi , Hatta Falmata da Rahima sai da suka fahimci tana cikin damuwa , juyin duniya suka nemi sanin meke damunta ?? Tace musu babu kome a ƙarshe da ta ga sun damu ,musamman Falmata da ta gaza cin abinci dare na kirki , kamar yadda ita ma yakakar ta gaza ci , sai kawai tace kan ta ne ke ciwo , " nan ma dai wani sabon tashin hankali ne ga Falmata domin kuwa kalmar ,"sannu," bata yanke daga bakin ta ba har bacci ya ɗauke su ! Washegari  Misalin ƙarfe 8am Hamza ya ƙira Rahima a waya inda yake sanar da ita su buɗe masa ƙofa zai shigo ya shirya , "  daman sun riga sun jima da tashi dan haka.saƙon nasa kawai ta sanar ga su yakaka su dukkanin su suka miƙe , A bakin kofar sashin nasa suka haɗu da ladabi suka gaida shi ya amsa cikin gaggawa yana amsar ɗan mukullin sa da yake hannun rahima,'   Ku jira ni anan na gama shiryawa yanzu na fito , kar ku tafi ko'ina ,"  ya furta hakan yana shigewa ,"  har yayi ciki sai kuma ya kira Rahima suka shiga tare ,"      Hankalin yakaka ya kai ga manyan rumfunan da ta gan su a kakkafe a harabar gidan birjik wanda bata san lokacin da aka samar da su ba , ana ta faman shimfiɗa manyan dardumai da kilisai a ciki , babbar ƙofar gidan a wangale take ana iya hango kai kawon da ababen hawa suke akan titin da ya bi ta gaban gidan , wata mota ƙirar bus ce ta tsaya a ƙofar gidan , Manyan Mata ne su rai shidda suka fito daga motar sai kuma ƴan mata sun kai su biyar , dukkanin su suna yanayi da juna farare ne sol-sol dogaye , mafi akasarin su lafaya ce a jikin su wacce bata ƙarasa ƙasa ba iyakar sangalalen kafafuwan su, hannun su zuwa kafafun su da manyan zanen lalle , jazir " Manya-manyan jakar bacco sun kai guda biyar suka kinkimo zuwa cikin gidan , waccen da wannan sun kama wannan ma da waccen sun kama , uku daga cikin manyan matan ne basu sa hannu ba wurin ɗaukar kayan , Daga gefe suka tsaya tare da ajiye kayan hannun su , Ɗayar da ta tsaya biyan direban motar itace ƙarshen shigowa , Magana tayi musu kafin ta nufo sashin Hamza kai tsaye , su kuma suka dakata daga inda suke ,  duk abun da suke idanun yakaka yana kan su ta nacewa kallon su , yanayin su ya mata daban da na mutanen da ta saba gani , Idanun ta ya sauka akan matar da take nufo su , wacce ita ma hankalin ta ya kai kan su yakaka , sosai suke kallon juna ita da yakaka lokacin da take ƙarasowa gurin ," Da wata irin murya da ta fito da sauti sosai tace RAHIMA ,    Dai-dai da fitowar Rahima wacce jin sautin muryar da ko a mafarki baza ta mance ta ba tana ƙiran sunan ta ya sa ta ƙarasa takowa da gudun gaske ta rungume ta bakin ta na kiran ,   Amne ! Amnee !    Rungume Rahimar itama tayi idanun ta na nacewa kallon yakaka wacce ta sunkui da kai tare da riƙo hannun falmata , saboda wani irin yanayi da take hangowa a cikin idanun matar mai kama da idon wata wacce tayi wa farin sani ," A hankali ta zare Rahima wacce take ta murna tana dariya daga cikin jikin ta , Abnatay wacece wannan ?  Ta furta hakan tana nuna mata yakaka da hannun ta da ya sha awarwaro da jaan ƙunshi , Yakaka da Falmata ne , Su waye su ƴan uwan ku ne ? Da ɗan murmushi tace , " ƴan gudun hijira ne yayan mu ya kawo su ," ta ɗora da jawo hannun yakaka ,    Yakaka ga maman mu ," Nan take yakaka da falmata suka buɗe haƙoran su suna dariya kafin duk su kai guiwowin su ƙasa ,   Mama sannu da zuwa ina kwana , suka haɗa baki wajen gaishe ta ,"   Da sauri ta ɗago yakaka ,   Tashi - tashi yarinya ta babu kyau durƙuso a halin da kike ciki , sannun ku kuna lafiya ?    Lafiya lau duk su biyun suka amsa ," Ɗauke idanun ta tayi daga kan yakaka tana saita nutsuwar ta tace ga Rahima Ina yayan ku ?? Yana ciki ta bata ansa  Janye idanun ta tayi daga kan su falmata ,lokaci guda ta miƙa hanya zuwa ciki wajen Hamza ,  zuciyar ta na cigaba da kambama mata wasu kamanni masu karfi dake tsakanin yakaka da Rahimar ta , da a tashin farko da ta ɗaura idanu akan ta ta firgice , ƙewar  ƴar uwar ta na mamayar ta har idanun ta suna tara ƙwallar tunowa da ita a take taji gidan ya fara mata duhu , kome yana da sanadi kome yana da mafari , nan gidan , nan sashin shine mafarin kome , nan inda dugadugin ta ke takawa a yanzu shine mafarin tarwatsewar rayuwar Rahimar ta da yayi sanadin rabuwar su  , ko tana ina ?? Allah shi kaɗai ya sani .. sai dai jikin ta na bata Rahimar tana raye kuma zasu haɗu zata dawo gare ta , abu ɗaya ne fargaban sa ke guiguiyar ran ta kullum wayewar gari shine Rahimar zata dawo mata ne a matsayin Rahimar ta ƙanwar ta , ko kuwa zata dawo ne da ƙudirin ɗaukar FANSA  ,...... ? ****** Nan sashin Hamza , mahaifiyar sa tare da ƴan uwan ta da tsirarun ƙawayen ta , 'tayi bigire daga yau zuwa gobe da zasu yi tafiyar su ! tsakanin ta da dangin mahaifin su Hamza kallon nesa-nesa ne ko gaisuwar fatar baki bata haɗu su da kannen mahaifin su hamza ba ,tamkar ma gudun haɗuwa da junan su suke , saboda ta riga ta ƙullace su irin ƙullata mai tsanani domin tana musu ganin sune SANADIN KOME , kowanne daga cikin su su rai shidda yana da tabon sa a idanun ta idan aka cire UNCLE SALMAN wanda shi kuma a halin yanzu baya raye a duniyar ,... Su ma a ɓangaren dangin mahaifin nasu kowannen su ya ɗarsawa ran sa tsanar AMINA AL-ARABI SHUWA , saboda wasu manyan dalilai nasu ," Cikin awa ɗaya jal da haɗuwar ta da su yakaka , ƙaunar yaran ta gauraye zuciyar ta , dan haka bata jinkirta ba wurin tambayar su labarin su da na iyayen su , Cikin sakewar da suka yi da ita suka bata labarin su tirƴan-tiryan , kafin su gama tausayin su ya sa zuciyar ta tayi laushi , sau uku tana maimaita musu tambaya game da mahaifiyar su akan menene sunan ta ,    Amsar su ɗaya ce , su basu san ana kiran ta da wani suna ba bayan maman Yakaka , su kuma suna kiran ta Mama ,!      Ta jinjina da jin cewar mahaifiyar ta su kurma ce bata magana, ta kuma tausaya , sannan ta cire tsammanin da take ko yaran suna da wata alaƙa ta kurkusa da ita/da Rahimar ta , tasan Rahimar ta ba naƙasasshiya bace ba cikakkiyar lafiyayyar mutum ce , dan haka ta danganta kamannin da take gani na rahima tare da yakaka a matsayin kawai halittar ubangiji ," Karfe 10am

Chapter 35 of 111