saurari kansa bare waninsa burin su kawai su isa wajenta ,
Kuma a tsakanin Falmata da Yakaka babu wacce ta nufi motar Youssouf da ya shiga ya tayar dukkanin su biyu kai tsaye mafitar gidan suka nufa ,
Suna fita ya sha gabansu da Motar ,"ku shigo ,
Yace da wata irin murya
Dukkanin su a lokacin ganin Mama shine burin su , dan haka suka shiga motar ya jaa da gudun gaske ,
A lokacin hawayen fuskar Yakaka da Falmata sun ƙafe kamar yadda yawun bakin su ya ƙafe ya daƙile fitowar wata kalma daga gare su , bayan addu'o'i babu abunda kowannen su yake yi a zuciya
Suna ficewa daga layin gidan motocin da suka yi jerin gwano su kimanin guda biyar suka shiga layin .
Gudun da yake yi ya wuce ka'idar tuki , kiyayewar Allah kaɗai ta kai su asibitin , ba inda ya kamata ya ajiye motar ya ajiye ba , bai ko lura da securities da suke masa magana ba , ya fito daga motar sauƙar ƙarfar sa akan titin da ya ɗau zafin rana shi ya ankarar da shi cewa fa ko takalma babu a ƙafafunsa ,
da gudu-gudu suka nufi ɗakin da suka san Mama tana ciki suna rige-rigen kutsa kansu ,
Turus suka yi ganin babu kowa akan gadon nata , da sauri ya fita suka bi bayansa , ma'aikaciyar jinyar da ya fara cin karo da ita zata wuce ya tambayeta ,"ina ɗiya ta ?
Ta san shi sosai a saboda yadda suke yawan zaman asibitin da kuma kasancewar sa babban Mutum , sai ta nuna musu ɗakin da aka mayar da Mama wanda yake daga ciki sosai ,
Bai saurari me zata sake faɗi ba ya nufi inda ta kwatanta masa da sassarfa ,
Bankaɗa ƙofar ɗakin yayi ya danna kai su Yakaka suna bin sa ba tare da sun bi ta kan Hajja wacce take tsaye daga bakin ƙofar tana sharar hawaye da gefen mayafin ta ba ,
Shigar su ya zo dai-dai da lokacin da likitan yake zare trach tube ɗin da yake fuskar Mama ,
Da gudu Youssouf ya ƙarasa ya ratsa ta tsakankanin Likitocin da suke zagaye da ita , fuskokin su cike da Alhini ,
Ya tarairayo ta bayan ya zauna a bakin gadon ya ɗagota lokacin da take jaan wani irin numfashi mai tafe da gurnani ciki-ciki , idanunta a buɗe akan fuskar sa ,
Hannun sa ya kai yana goge mata tsinkakken yawun da yake zuba a bakin ta , muryar sa tana karkarwa yake kallon likitocin yana cewa,
" Doctora yaya hakka ? Kuyi wani abu mana , Mama tana hakka alhalin kuna tsaye ?
"Mama, kar ki barni ki dubeni Mama ,
ya ƙira ta da wata irin muryar yana jijjigata a jikinsa ganin yadda idanunta suka yi sama , numfashin da take kokawar riƙewa kuma ya ƙarasa barin jikinta , dukkanin wasu jijiyoyin jikinta suka tsayawa aiki , kamar yadda zuciyarta ta tsaya chak daga barin bugawa na har abada .
Da gudu Yakaka ta ratsa tsakanin su ta kai hannu tana riƙo hannun Mama da yayi wani irin sanyi ƙalau ya sake ,
"Mama tashi mana , me ya same ki haka ? Innalillahi wa inna ilaihi raji'oon .
Tace da kuka a muryar ta ,
"Mama ,
Falmata ma ta ƙira ta lokacin da ta ƙaraso gurin idanunta basa gani sosai Amma tabbas a yau tana iya hange gefen Fuskar Mama tar-tar , shafa kanta tayi da yake rungume a kirjin Babanta
"Mama meye ya same ki ? Ki tashi Mama , kin ga fa Mamar ki ta asali ta dawo zata rayu da ke , Mama baki ko mata magana ba , bata ji muryar ki ba shine kuma za ki zama haka ? Mama ki tashi ,
Ta ƙarasa maganar tana jijjiga su ita da Youssouf ,
Kafaɗar Youssouf Babban likitan ya dafa , yana cewa
" Innalillahi wa inna ilahi raji'oon , kuyi hakuri duk wani ciwo na safiyya ya warke , ta komawa ga Ubangijinta , dukkan wani mai rai mamaci ne kuyi haƙuri , kuyi haƙuri , kuyi addu'a
Baya yayi a hankali yana kaucewa ganin tashin hankalin da yake ƙwarar idanun su su ukun ,da suke kallon sa zuciyar sa cike da tsantsar tausayi , tabbas mutuwar abunda ka haifa akwai ciwo , ciwo kuwa mai raɗaɗin gaske , ɗaya bayan ɗaya likitocin suke ficewa daga ɗakin suka bar guda biyu kawai a tsaye ,
Jikin Youssouf babu inda baya rawa , ya zaro Mama daga ƙirjinsa yana kallon fuskar ta yadda kan ta ya tafi galau ,
Ya sa kukan da yake riƙewa fisge masa , sai ya fashe da kuka mai ƙarfi ya mayar da ita ƙirjin sa da yake wani irin bugu da matsewa tamkar ana daure masa jijiyoyin dake gudanar da jini ta cikin sa ,
amon kukansa ya sa Hajja shigowa ɗakin , cikin ranta tana aiyana inda ake gudu nan aka zo aka tsaya , Mama ta rasu ,
Tun-tuni ta ga Alamun mutuwa a tare da yarinyar tunda jikin ya birkice daman ranta yake kai-kawo , Allah sarki mutuwa bata a shekaru , bata barin ƙarami ta ɗau babba domin wai ta jinkirtawa girman sa , ita lokaci kawai take jira , ko ɗan da yake cikin mahaifiyar sa tana ɗauka ,
Falmata wacce hankalinta ya kasa amincewa da mutuwar Mama kamar yadda likita ya faɗa , ƙarasawa tayi ga Yakaka wacce ta zube guiwar ta biyu a ƙasa ta kifa tafukanta biyu akan fuskarta , kuka take marar sauti , illahirin jikinta rawa yake sai ta kai hannu ta dafa ta , a lokacin da Hajja ta nufi wajen Youssouf , da muryar dake bayyana tsoro da tashin hankalin da me ita yake ciki tace ,
"Yakaka , ki tashi , ki tashi ki karɓi Mama mu tafi , mu tafi da ita Yakaka , ko kin manta da Alƙawarin da muka mata tun tana ciki ? Cewa ni da ke zamu kula da ita Yakaka , zamu bata kariya yaya kuma kina gani Mama zata tafi ta bar mu , ?
Alhalin ...Ya.Yakaka ki tashi nace kin san fa mu uku ne kaɗai a duniya Dan Allah kar Mama ta mutu , Mama kar ki barni mana , yaya za ki min haka Mama ? Bayan nayi alƙawarin zaki warke Mama .
Kuka ne ya ci ƙarfin ta har tana shiɗewa numfashinta ya fara yin sama-sama
Da sauri Yakaka ta rungumeta kukan ta yana daɗuwa ta riƙe fuskar ta ,
"Falmata kiyi addu'a , kice innalillahi wa inna ilahi raji'oon , mu da Mama duk Allah ne ya yimu , ya bamu rai da muke rayuwa da shi , kuma shine ya hallicci mutuwa ya sa ta zama mai zare rayukan mu idan lokacin da ya kayyade mana na rabuwar mu da ruhin mu yayi , da ni da ke da Baban ta duk Allah ya fi mu sonta kiyi mata Addu'a Falmata ,
Da ƙarfi Falmata ta rungume Yakaka wacce ƙarfin hali ne kawai take yi domin kadda Falmata tayi rauni dayawa ,ita abunda take ji bata taɓa jin makamancin sa ba wani abu take ji mai ɗaci yana kai kawo a tsakanin zuciya da maƙogoron ta , gaba ɗaya ranta cike yake da duhu da take iya ganin duhun har ga idanunta ,
Hajja tana ƙarasawa ga Youssouf ta shiga bada baki da tunasarwar da ake yiwa wanda aka yiwa mutuwa , itama sharar hawaye take zuciyarta cike da tausayin su , tana kimanta irin zogin da zuciyoyinsu ke ciki kan mutuwar ɗiyar su ,
Sun ɗau mintoci kusan goma a haka cikin halin ɗimuwar jin zafin mutuwa kafin likitocin biyu su nemi da ya basu Mama zasu zare duk na'urorin su da suka riga suka jona mata ,
Bai dube su ba kamar yadda bai ce kome ba illa bakin sa da tun-tuni yake motsawa da alamun addu'a yake yiwa ƴar sa ,
Shi da kan sa ya raba jikinta da duk wasu na'urorin su ba tare da ya ajiye gawar ta ba ya jaa farin mayafin su na asibitin ya rufe fuskarta zuwa jikinta da shi , bayan ya shafe fuskarta da tafin hannun sa .
Cigaba yayi da zama a wajen yana riƙe da ita tamkar wanda ya samu ɗaukewar tunani .
Ganin haka ya sa likitocin da suka rage su biyu suka fita , Hajja ta ƙarasa wajen su Yakaka tana ba su baki , da har yanzu basu bar kuka ba .
Turo ƙofar aka yi Tafeeda ya shigo tare da shi dattijo ne wanda yana sanya ƙafa a ɗakin ƙamshinsa ya gauraye ɗakin da ya sa Youssouf ɗago kansa suka haɗa ido ,
Maimartaba Sarkin Maraɗi Abdoul-azizou Baskore , ya taka ya ƙarasa gaban gadon da Youssouf yake zaune riƙe da Gawar ƴar sa ,
"Youssoufa ,
Ya ƙira sunan sa .
Ɗago da kansa yayi a karo na biyu , laɓɓan bakin sa na karkarwa da kyar ya fisgo kalmomin da a tun farkon samuwar Mama yake tsoron Furta su ga Maimartaba a tsa-tsan idanun sa , a yau neman tsoron ya yi ya rasa a lokacin da Mama ta ƙare ta zama Babu .
" Baaba , ɗiyata ce , wannan Mama ce , ɗiyata ce , ta rasu , Mama ta rasu ta barni Baaba .
Kuka ya sake fashewa da shi idanun sa na zubar hawayen da suke ɗiga akan gawar Mama ,
Maimartaba sai ya zare gilashin idanun sa , da bayyanuwar sabon yanayi akan fuskar sa saɓanin wanda ya shigo da shi ,
Yayi tsumu ! yana kallon Youssouf da yake cigaba da kuka marar sauti , zuciyarsa ce ta rau-rawa saboda dalilai biyu da suka haɗe mar a lokaci guda .
a hankali ya kai hannu ya dafa ƙafaɗar Youssouf ɗin, cike da tausasawa a muryar sa mai ƙwarjini yace ,
"Youssoufa kayi haƙuri dukkanin mai rai Mamaci yake , Rayukan mu kuma ababen aro ne a gare mu da babu shakka masu komawa ne ga Ubangijin da ya bamu aron su a domin mu bauta masa , Ka dogara ga Ubangiji da zuciya ɗaya, kada ka dogara ga abin da kake tsammani ka sani , a cikin dukan abin da kake yi, ka tuna da Ubangiji, shi kuma zai nuna maka hanyar da yake daidai , Sam, kada ka yarda ka ɗauki kanka kai mai hikima ne fiye da yadda kake, kai dai ka ji tsoron Ubangiji, ka rabu da aikata saɓo , Idan ka kiyaye wannan, zai zamar maka kamar magani mai kyau, ya warkar da raunukanka, ya kuma sawwaƙe maka azabar da kake ciki ,
"Miƙata ga Tafeeda ka taso mu tafi ga yi mata sutura zuwa miƙata ga kabarinta ,Allah ya jiƙanta , Allah shi sa ta zama dalilin samun afouwar Ubangiji a gareka .
Kalaman Maimartaba sunyi tasiri ga duhuntatciyar zuciyar sa mai ciwo , dan haka sai ya sasssuta riƙon da yayi wa gawar Mama , ya miƙata ga Tafeeda zuciyar sa na tuno masa rana ta farko da ya fara karɓar ta da tafukansa , ya rungumeta a ƙirjinsa , sai ga shi a yau ya zareta daga jikinsa da hannunsa , zarewa irin ta har Abada , ji yayi tamkar bazai iya ba , tamkar wani sashi na ransa ne ya bar jikinsa .
A hankali Tafeeda ya samu damar zareta daga jikinsa , wanda shima tasa zuciyar tayi laushi tausayin Youssouf ɗin ya cika zuciyar sa tare da ƙarin tsoron Allah , da ya tuna irin ƙauna da tsantsar son da Youssouf yake yiwa wannan ɗiyar , da har ta kai ya zaɓe ta bisa ga kowa da kome nashi , duk a domin ya rayu tare da ita .,
Sai ga shi domin Ubangiji ya yi masa babbar jarabawa sai ya sanya mutuwa ta raba tsakanin su , a kuma lokacin da kome ya rinchaɓe masa a dalilinta , lalle wannan jarabawa ce maigirma ,
Mayafin da aka rufe mata fuska da shi ya buɗe lokacin da yake ɗaga ta , Maimartaba ya dubi fuskarta da tsantsar tausayi cike a ransa ,
"Ubangiji yasa ki zamto dagga ƴa'ƴan da zasu zam silar samun afouwar Allah ga iyayen su daga tarin zunuba su ,
"Amin Amin Amin,
Hajja ta amsa tana sharar ƙwalla ,
duba guda Maimartaba yayi musu ita da su Yakaka yayi wucewar sa , Tafeeda ya bi bayansa da gawar Mama , Youssouf ma ya sauƙa ya nufi ƙofar ficewa , ya zo ficewa ya waiga garesu da har lokacin suke ƙasa dirshen a zube , muryarsa a ciki yace
"ku tasso mu tai ku wanke ta ,
Shiru suka yi babu wacce ta amsa masa ,
Ganin ya fita yasa Hajja cewa ,
"ku tashi mu tafi Falmata , Yakaka kuyi haƙuri kun ji , haka Allah yake ikonsa uwa ta haifo ɗan da ta fi nisan kwana, kuyi haƙuri kuyi ta addu'a mutuwar Mama hutu ce a gareta , kuyi haƙuri .
Zuciyoyin su a lokacin basa aikin da ya wuce na kuka da jin raɗaɗin mutuwar ƴar da suka shirya sadauƙarwa a domin ta sai gashi mutuwa ta ɗauketa a lokacin da kowaccen su take jin rayuwarta kachokam zata sadauƙar domin ta tsaya tare da ita ,
Suka miƙe ƙafafun su babu ƙarfi suka rufa masa baya , a motar da suka zo a ciki suka koma sai dai wannan karon wani ne ke jaan motar da basu kai ga sanin sa ba ,
Gidan suka tarar da yalwar mutane da suka wuce yadda suka barsu a farko yawa ,
Mutane maza da suke sanye da kaya mai launi guda , da kuma mata a falon nasu , Yakaka da Falmata ratsawa suka yi basu dubi kowa ba suka wuce ɗakin da yake na Falmata , suna shiga su duka biyun kuka suka sake sawa , a tsakanin su an rasa mai rarrashin wani ,
Shigowar Tafeeda ɗauke da gawar Mama shi ya dakatar da ƴan guna-gunin da ya fara tashi bayan wucewar su
Kai tsaye ya miƙata ga Hajja wacce take raƙube daga gefe tunda ta shigo babu wanda ya dubeta bare su amsa gaisuwar ta'aziyyar da take yi musu da basu kai ga sanin wa ya rasu ba , ganin sun yi biris da ita ya sa tayi shiru tana sharar ƙwallar ta ,
"Ki miƙata ga uwayenta sui mata wanka , su shirya ta yanzou za'a kawo likkafani ,
Sai ta ƙarbeta ta ratsa ta tsakanin su ta wuce ɗakin Falmata , zuwa lokacin hankalunsu baki ɗaya ya koma ga Tafeeda ,
Bai jira sun tambayeshi ba , ya ce
"Diyar Biyamuradi Youssoufa ce da Allah ya amshi ranta a yanzou ,
Daga haka bai ɗora kome ba ya juya ya fita ,
Shiru wajen ya ɗauka , kafin lokacin da Hamshaƙiyar matar da ita ce ƙwal ɗaya a bisa kujera ta motsa , fuskar ta da wani yanayi da kai tsaye ba'a iya fassara shi ba ta soma da cewa ,
"Allahu Akbar innalillahi wa inna ilaihi raji'oon , kaico yarinya wahalar ki ta ƙare kin kuma huttashe da wasu dagga samuwar baƙin-ciki sanadin duban ki , to Allah shi jiƙan ki , ta tabbata dai Youssoufa yana da ɗiya mai shekarun ya wannan da kuma Amre ko ba Amre ?
Bata tsaya ba ta cigaba da cewa , "Mutumin da ya ƙi faɗar gaskiya yana haddasa wahala, wautace babba a ɓatar da lokaci akan aikin banza , mutumin da ya ƙamnaci zunubi ya irin haka , ai ya shiryawa hukunci ne , zunubi da kunyata kuwa tare suke rungumar mai su, shiyasa asharari bashi da wata ƙima ,
Ta murza zoben hannunta , tana wani ɗan guntun murmushin cikar buri , ta ɗora
" gaskiya ita dawwamammiya ce ƙarya kuwa ai ƙurarriya ce , ɗan da ya jawo wa Mahaifinsa ɓacin rai ya haka ,? Ai abun baƙin-ciki yake ga Mahaifiyarsa , to wanne farin-ciki za'a yi da samuwar baragurbi cikin 'ya'ya ?
A hankali Adda Ammi ta ɗaga kai ta kai ganin ta gareta bayan gama jawabinta lokacin da ƙaramar jakadiya tace ,
" Babu shakka ko kokonto cikin kalamanki ranki ya daɗe , kowa ya aikata abunda ransa ke so zai ga abunda bai so a lokacin da bai so ba ,
Kallon-kallo aka yi tsakani Ammi da Ubbo da kawo yanzu suka rasa halin da zuciyoyin su ke ciki kan mutuwar ƴar ɗan uwansu da ake duk wani ƙiƙi-ƙaƙa akanta ,
Sai dai kalaman Matar da take mazaunin uwa agare su , Matar Mahaifinsu , da kuma ta wakilci Mahaifiyar su wajen wanzuwarta anan , da kalaman nata ke nuni ƙarara da tazorci gami da kausasawa ga ƙaninsu , ko kusa bai musu daɗi ba , duba da cewa wajen gauraye yake da bayun su ,waɗanda Youssouf shugaba yake a wajen su duk da laifin sa ,
sai dai su basu da ikon tankawa ,"Hajiya Mama uwa take kuma shugaba a gurin su
Ba'a ɗau lokaci ba Tafeeda ya dawo hannunsa riƙe da likkafani , ya miƙawa Ubbo ba tare da yace kome ba ,
Sai ta karɓa ta nufi ɗakin da ta ga sun shiga ta tarar da su su ukun suna kewaye da gawar Mama da take shimfiɗe a ƙasa ,
Yanayin da ta gansu ya taɓa ranta , bata ce ƙala ba ta miƙawa Hajja likkafanin ,
Ta juya , har ta kai ƙofa ta juyo , "kun iya wankan ? Ta tambayesu
Babu jinkiri Yakaka ta gyaɗa kanta , sai ta juya tayi ficewarta tana ɗauke ganinta daga kan hoton Mama da yake bangon ɗakin Falmata , tsananin kamannin da yake tsakanin Mama da nata ƴa'ƴan ya girgiza ranta .
Yakaka ita ta wanki gawar Mama da take rungume a jikin Falmata , ƙwarar idanun su bata huta ba wajen zubar hawaye ,
Tunawa Yakaka take tun daga ranar da suka ɗora ƙazamtatciyar alaƙa da Youssouf , har zuwa ɗaukar rainon cikin ta da ta samun ta ta haramtatciyar hanya , zuwa da ranar da ta haifeta , da ko fuskarta bata kai ga gani ba , ta tuno da ranar da ta zo irin kallon da tayi mata dake bayyana tsoro da rashin sanayya ,
' tsawon rayuwar da Mama tayi shekaru shida a duniya bazata ɗorar da kome na daga rayuwar yarinyar ba , ƴar da ta ƙi kallonta lokacin farko da ta fito duniya , ta kuma tafi ta barta bata ji tausayin ta tayi tunanin me zata ci ta rayu alhalin abincinta na jikinta ba , ina zata ji ɗumin jikin uwa irin wanda jariri ke buƙata a lokaci na hunturu ?
Babu shakka Samy Baby ta zalunceta da ta cisgeta daga cikin ƴar gajeriyar rayuwar ƴarta , ta yi mata yaudara mafi girma da ciwo , irin ciwon da ba zai rabu da ruhinta ba har ta koma ga Maliccinta ,
" Mama Allah ya jiƙan ki yasa kin samu hutu dawwamamme daga barin rayuwarki mai cike da jinyar gangar jiki , ki yafe min Mama , ki yafe min , addu'o'i ta cigaba da yi mata tana wanke ta .
Bayan sun shiryata suka fito da ita , Hajja ta fita ta ƙira Ubbo , zama tayi a ɗakin sannan ta ƙira Tafeeda ta sanar da shi an shiryata , babu jimawa suka shigo su biyu da wani , suka ɗau gawar Mama zuwa waje da za'a sallaceta ,
Falmata kasa riƙe kukan da yazo mata tayi ta fashe da kuka mai ƙarfin gaske , dake bayyana jin ciwon rabuwarta da ƴar da ta ƙwallafawa rai fiye da abunda ke cikin cikinta ,
Ƴar da ta so tare da sadauƙar da kome a domin ta , ƙaunar da ta mata ta fara daga ranar da ta rungumeta a jikinta bayan rashin mahaifiya da tayi , ta ɗau alwashin maye mata gurbin uwa da ta rasa , ta dunga tuno da yadda suka ƙaunaci juna ita da Mama , da bata san tana da wata uwa ba bayanta har ta koma ga mahaliccinta ita ce mahaifiyarta ɗaya tal, tabbas Mama ta bar mata gurbi a zucia sa babu ranar cikata shi .
***
Tamkar wutar daji haka labarin mutuwar ɗiyar Biyamuradi Youssouf/MaJor Youssouf da mutane basu san da wanzuwarta ba ya dunga kewaya ko'ina ɗauke da mummunan tambarin da Youssouf ya ƙi tabbatuwar sa ga rayuwar Mama sai ga shi bayan mutuwar ta labari ya bayyana an kuma ƙira ta da sunan da bai so ba .
Zaman makoki sosai ya kankama tun yammacin ranar da aka bizneta da kuma tun bayan jana'izar da Maimartaba sarkin Maraɗi da kansa yayi limanci , ya bar wajen tun kafin dawowar su daga maƙabarta ,
Ƙarƙashin rakiyar maƙarrabansa da suka zo tare suka koma , waɗanda mafi yawa manyan fada ne , masu faɗa a ji a harkar sarautar masarautarsu da amintattun manyan bayunsa , zaɓaɓɓu da aka aminta da Amanarsu
Da tafiyar tasu musamman ta samo asali ne kan zuwa su ganewa idanunsu inda Youssouf ɗin ya ɓoye yana rayuwar banza kamar yadda aka yi ta jita-jita a kwanaki zancen kuma ya dawo kunnuwansu Amma suka yi binciƙe basu samu shaida ba ko guda a wancen lokacin
Sai fa da yanzu shaida ta bayyana ta hannun Mouhammadou da yace shi ma fa bayani aka ba shi ,
Mafiya yawan masu zuwa ta'aziyyar abokan aikinsa ne da matan su sai kuma tsirarun mutanen gari da yake mutunci da su , daga masarautar su babu mutum guda da ya ƙiraye shi ko kuwa ya zo yi masa ta'aziyya tun bayan juyawar tawagar sarki da kuma ta su Hajiya mama ,
Tsakanin Hajiya Umma ko matansa babu wacce ta ƙira shi , haka ma 'ƴan uwansa idan aka cire Ubbo da Ammi da kawo yau da ake kwanaki biyu da mutuwar Kullum suna zuwa gidan nashi su yini a karɓi gaisuwa da su duk a ƙoƙarin su na son ganin sun rufa asirin ɗan uwansu daga mutanen da basu riga da sun san ta hanyar da ya samar da Mama ba ,
Sai dai a yau su ma sun kudurce cewa sun yi zuwan ƙarshe dan haka suka yanke shawarar yi masa magana ,
Har falon sa suka shiga suka tarar da shi , tare da Tafeeda da tunda aka yi mutuwar yana tare da shi , duk da cewa babu wata doguwar mu'amala ko da kuwa ta maganar baki ce da take shiga tsakanin su ,
A zaune suka tarar da su shiru tamkar kurame , shi Tafeeda yana aikin latse-latsen waya shi kuma Youssouf yayi tsumu irin yanayin da yake ciki tun bayan mutuwar Mama ,
Babu karsashi suka gaisa , bayanan suka yi shiru ,suna nazarinsa da ya sunkui da kansa , baki ɗaya yayi wani irin sanyi har ƴar rama yayi , ba kaɗan ba mutuwar ƴar sa ya taɓa rayuwar sa ,
Cikin taushin Harshe Ammi ta fara masa nasiha kan laifinsa na aikata zina da ta kai shi ga haihuwar Mama , har zuwa yin aure ba tare da sanin iyayensa ba , bayan haka ta tambaye shi tsakanin Yakaka da Falmata waye uwar Mama ?
Nan ya basu amsa da cewa Yakaka ce mahaifiyar ta ,
Ta tambayeshi kuma ta yaya yake auren Falmata alhai ƙanwace ga Yakaka kuma suna tare guri guda ?
Nan ya basu labari a taƙaice kan yadda aka yi ya auri Falmata da zaton cewa Yakaka ta mutu ne , sai kuma kwanakin da suka dawo daga USA ya ganta a gidan bashi da wani masaniya kan labarin da ya shafe ta .
Duk shiru suka yi , kafin ubbo tace
" to tunda Allah ya gwada karshen kome da ya zare wannan ɗiya a tsakani domin kawo maslaha a gare ka, sai kayi ƙoƙarin gyara duk wasu kuskuren ka ,
"tunda daman domin riƙon ita ɗiyar kake amren innar ta ai sai yanzou ka sau amren su yi tafiyar su , kai ma ka koma ga iyayenka ka biɗi afouwarsu , su yafe ma sabadda rayuwa tayi maka kyau Youssoufa , ka fuskanci aikin ka cigaban rayuwarka ka ji kou ?
Ba tare da ya ɗago kan sa ba yace
" to naji ,
Kallon rashin gamsuwa da amsar sa suka bi shi da shi , amma basu jaa zancen da tsawo ba suka rabu da shi
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Chapter 110
Chapter 111
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 78 Chapter of 111