Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
sanar da Suleiman da kan sa , sai ko bayan auren , sai dai yadda ya matsa masa da tambaya yana nuna damuwar sa a fili ya sa shi sanar da shi cewa "aure zai ƙara da ƴar Innar sa da aka ba shi , " Wani sasakai Doctor suleiman yayi yana kallon Hamza , kafin ya wani kwashe da dariya , sai da yayi dariyar ta ishe shi , Doctor Hamza bai ce masa ƙala ba illa ma rubuce-rubucen sa da ya shiga yi , yana jin yadda ransa ke ɓaci da dariyar walaƙanci da suleiman ya sanya shi a gaba yana yi . " Ka ce dai alƙadarin Safiya ya karye , zaka yi wani yunƙuri dan ganin ka fara tara naka zuri'ar , lamari yayi kyau haka ake son Namiji to amma nayi mamaki ina kuma kan yi ko yaya zaka yi da mata biyu ? Da wutsiyar ido Doctor hamza ya dube shi , ba tare da ya bar abunda yake yi ba yace , " Su masu mata biyun me suke yi da na su ? Wata dariyar Doctor Suleiman ya sake kwashewa da ita kafin ya ɗora da cewa , " wataƙila jera su suke suna ado da su a gidajen su , ya ɗora da cewa watanni nawa aka sa lokacin bikin ? Banda abunka abokina to menene abun damuwa ? Ai hurhuɗu ya kamata ma mu ajiye , domin ko nima ba domin tafiyar nan da na ɗan yi ba da yanzu batun auren mu yayi nisa da Aminah ta , wataƙila ma sai dai mu haɗa ayi rana ɗaya tunda kuwa ita ma ƴar Maidugurin ce , wata nawa aka sa ? Muryar Doctor Hamza can ƙasa yace , " kwanaki goma kachal suka rage har da yau da muke ciki , Tsumu Doctor Suleiman yayi yana kallon sa wannan karon kamar bai yadda da abunda yace ba , ganin haka yasa Doctor Hamza cigaba da cewa , " tare za'a haɗa da na ƙanwata Rahima , saboda ayi a huta , tarewar kuma sai yadda hali ya min wataƙila ta kai watanni huɗu a maidugurin ko ma fiye da haka kasan dai kome daki-daki ake yin sa . Da fara'a sosai a fuskar sa Doctor Suleiman ya shiga taya shi murna yana taya sa shi da fatan alheri cikin raha ya ɗora da tsokanar sa , " kace ciwon so kake ciki mana tare da kewa , shiyasa duk ka wani zama haka , babu shakka wannan ƙanwar tamu mai sa'a ce , to sabon shiri kenan zamu fara dan angwanci ya same mu da rana tsaka ba tare da mun shirya ba , amma duk da haka ma ɗan yi wasu tsare-tsare a gurguje me da me za'a yi na biki ? Kallo mai kama da harara Doctor Hamza ya masa , kafin yace " Dan Allah zan roƙe ka Alfarma Suleiman, kar ka ƙara min damuwa , duk garin nan bayan kai ba wanda na faɗawa zancen nan , ko ita sofiya bata san da zancen ba dan haka ka ma bar maganar wani biki zancen ya tsaya kawai a tsakanin mu , bayan kai da daman zaka je bikin Rahima babu wanda zan gayyata . Da wani irin yanayi Suleiman ya dube shi kafin yace " ko meyasa ? " kawai ra'ayina ne , mu ba yara bane da za'a yi wani raye-rayen biki ina ma muka ga lokutan ɓatawa ?. Gƴaɗa kai Suleiman yayi cike da shakku yace " to shikenan tunda kace haka Allah ya kyauta . " Amin nagode abokina , Doctor Hamza ya amsa masa , domin ya sauƙaƙa yanayin rashin daɗi da ya hango a tare da Suleiman sai yace , " ina aka kwana kan batun lamarin ita Aminar taka ? ko idan muka je Maidugurin za'a yi wani motsi mai ƙarfi ne ? kasan fa kun jima da yarinyar nan ya ci ace anyi auren nan . Cike da zaƙuwar jin an masa susa inda ke mar ƙaiƙayi Doctor Suleiman yace ," bari kawai abokina wannan yarinyar ko yau aka kawota gidana ta walashe ni , gyara zancen nan ka ma , saboda ai ni na jima ina son ta ba wai mun jima a tare ba , domin kuwa ai ita har yau bata wani bani dama ba , ni kaɗai ke fama , Ya dubi fuskar Doctor hamza da yayi kasaƙe cike da takaicin yadda ya zauna gotai-gotai da shi 'yar yarinya ƙanƙanuwa na masa yawo da hankali wajen shekaru uku , sai kace ƴa gwal ? Doctor Suleiman ya katse zancen da Doctor Hamza yake son ɗorawa ta hanyar cigaba da cewa , " kar ka ga laifina Abokina , Amina ta cancani da kowanne ɗa Namiji yayi sha'awar ajiye mace mai nagartartun halaye da Addini haɗi da nutsuwa irin ta , wallahi ko kai da kan ka idan na baka labarin irin rayuwar da yarinyar take yi mai cike da tsantsanin kiyaye kan ta duk kuwa da cewa inda take rayuwa ƙazamtatce ne , halayyanta na ƙwarai nake kwaɗayi ba kome ba , saboda na sha gwada ta ba sau ɗaya ba , na kuma sa mutane wasu daban ma sun gwada ta amma ko sau ɗaya ban taɓa kamata da wani laifi saɓanin zahirin ta da take bayyane kullum cikin kamala da nutsuwa ba . a yadda kake ƙyamatar halayen wasu matan nasan zaka yi mamakin nagartar da ita take da shi , kuma zaka bada goyan baya ɗari bisa ɗari akan na auro ta , musamman idan ka ji irin hali na tausayawa da suka riski kan su a ciki ita da ƴar uwar ta , Cike da gajiya da yadda ya zauna yana yabon wata wacce har yau shi da kan sa bata bashi darajar da za ta saurare shi ba , bare kuma su abokan sa Doctor Hamza yace " to Allah ya tabbatar da Alheri abokina . Kamar yadda suka yi alƙawari ana saura kwanaki biyar ɗaurin Aure Mutanen N'Djamena suka iso ,sun tasamma mutane ishirin da ɗoriya , domin sun kusan cika falon Prof da anan suka fara ssuƙa , bayan an gaisa murnar sake ganin juna ta kachame a tsakanin su har da 'yan koke-koke , banda yaren su na larabaccin Chad babu abunda ke tashi a wajen , Zainab , Hafsa da suka iso tun jiya , har Rahima haɗi da Yakaka da Falmata , a tsakanin su duk babu wani mai jin yaren har sosai , dan haka sai suka tsaya kallon su fuskokin su ɗauke da murmushi , Bayan sun ɗan nutsu sun sha ruwa da lemu , sai Matan suka shiga ciki inda za'a musu masauƙi , Mazan kuma suka tsaya anan Sashin Prof . A ciki Amnee ta sake gabatar da Yakaka da Falmata , nan aka fara rungumar su ana sumbatar kumatun su da goshi , cike da nuna zallar ƙauna , daga baya kuma aka sake sabuwar gaisuwa har da su Hafsa da mafi yawa sun riga sun san su , su Yakaka ne baƙi . Ba'a kwana ba Hajje Nadiya tare da tawagar ta mata huɗu da ta taho da su domin su taya ta suka buƙaci da su fara aikin da ya kawo su na gyaran Amare . Tun ana saura kwanaki biyu ɗaurin Aure Sofiya ta iso Maiduguri , amma sai ta ƙi ƙarasawa gidan su Doctor Hamza tayi zaman ta a gidan su tare da Mamar ta Hajja kori , da ita ta zuga ta tace tayi zaman ta sai ana gobe ɗaurin auren da Yamma sai su tafi tare , ba dan kome ba kuwa sai dan rashin shirin da yake tsakanin su da Amnee da Khaalty Rahima . Da ko kusa basu so Auren Amnee da yayan su ya sake ƙulluwa ba , kuma duk yadda suka so hana tabbatuwar lamarin fir Prof yaƙi saurarar su , ita kanta zuwan ta wajen sa biyu da zummar yi masa famfo amma bata samun fuska dan haka ta haƙura . Babu abunda yafi ƙara basu haushi irin dawowar Khaalty Rahima da suka fi tsana gidan wannan karon har ma da marayun 'ya'yan ta kamar yadda labari ya iske su Dan haka suka tsara zasu janye jikin su daga sabgar gidan sosai , sai ranar juma'a da Yamma lis , ana tsakiyar yin sakun lallen Amare tukun suka iso , ba su kaɗai bane ƙungiya suka yi da ɗan yawan su domin baki ɗayan ƙannen Prof matan sai yanzu suka zo tare da wasu daga cikin ya'yan su mata , sauran dangi kuwa mafi yawa sai gobe zasu zo . kai tsaye iyayen suka yiwa sashin Prof tsinke ba tare da sun bi ta kan jama'ar sauran Jama'ar Amnee ba mutanen N'Djamena da su Malama Maryam wacce ta iso jiya da Yamma . Suma kuma basu kula su ba , suka cigaba da gudanar da sakun lallen da aka tsara shi cikin irin Al'adun su na mutanen Chad , Kota'ina ƙamshin turaren wuta ne ke tashi da ake zuba shi ta kowacce kusurwa na filin wajen , haka Sofiya tare da wasu daga cikin yaran mata 'yan uwansu suka ratsa taro zuwa ainahin inda amaryar take zaune Abunda ya ɗaure musu kai bai wuce ganin Amaren su biyu ba tare da wacce su sauran basu kai ga sanin ko wacece ba ? ko ita Sofi sai da ta bar yatsine-yatsinen da take yi ta nutsu sosai tukun ta iya shaida Farar balarabiyar da take zaune daga gefen Rahima da aka musu ado iri ɗaya cikin jar lafaya , tundaga kan su har wuya da hannuwa zuwa ƙafafun su adon sarƙoƙi ne masu ruwan gwal irin wanda shuwa arab ke adon bikin su da shi , ( baki ɗayan kayan gudummawa ne daga Hajje Khalsum ) Muƙut ,! Sofiya ta haɗiye busasshen yawun da ya mata saura a baki , kafin ta ɗora da ɗan siririn tsakin da ya bayyana fili . Da ɗan sauri ta matsa kusa da Hafsa zuciyar ta na ƙara ƙarfin bugun da bata san dalili ba , " kamar nasan wannan kuma Bikin biyu ne wai ? Ta ce tana nuno Yakaka a walaƙance , Murmushin yaƙe Hafsa tayi sannan tace " ƙanwar mu ce 'yar Auntien mu Rahima , Da sauri ta sake cewa , " Ok daman wannan yarinyar ita ce ƙanwar taku da aka ce an tsinto su ? Kuma bikin ta itan ma ake yi na gan ta anan kusa da Amarya ko duk shisshigi ne da cusa kai ya bawan gado ? Wata daga cikin ƴar dangin su da ta zo ta jaa hannun Hafsa ɗin tana bata saƙon Amnee na ƙiran ta , ita ta hutatce Hafsa daga bada Amsar da take ƙoƙarin harhaɗowa cike da zullumi . Zare hannuwanta tayi daga cikin na Sofiya ta bar ta nan a tsaye , Ji tayi sam ba zata iya tsayuwa a wajen ba tana kallon Yakaka wacce sai ƙirƙiro ƴar fara'a take a tsakanin ƙawayen Rahima da suka zama kamar nata sai zuwa suke ana yin hoto , tare da yi mata fatan Alheri Bata sake bi ta kan kowa ba ta zare jiki ta nufi sashin Amnee inda ta tarar ba yawaitar mutane a falon , mutane basu wuce huɗu ba ƙawayen Amnee , kai tsaye ta nufi ɗakin Amnee da take jiyo muryoyin su daga ciki , Amnee da Khaalty Rahima haɗi da Hajje Khalsum duk shiru suka yi daga tattaunawar da suke suka bita da kallon ganin yadda ta shigo musu ɗaki bagatatan babu neman izni . samun waje tayi ta zauna kafin ta fara gaishe da Amnee , da ƴar fara'a Amnee ta amsa , daga haka shiru tayi tana latse-latsen waya bata da niyyar gaishe da sauran mutanen , dan haka fuskar Amnee ta ɗan sauya daga fara'ar da take tace , " Safiyya baki ga 'yan uwa na bane ? Wannan ƙanwata ce wannan kuma matar wana maza ki gaishe su . Yanayin ta na bayyana rashin jin daɗin yadda Amnee ta disga ta a gaban mutane kamar wacce aka toshewa baki tace " Sannun ku ina wuni ? Fuskar Khaalty Rahima ɗauke da murmushi sosai ta amsa mata har tana ƙarawa da tambayar ta Mamar ta ? Bata bata amsa ba ta mayar da kan ta ga fuskar wayar ta , Sun cigaba da tattauna yadda wasu al'amuran da suka shafi bikin zasu kasance , kafin su tsinkayo muryar Hajja kori da take ƙwalawa Amnee ƙira tundaga ƙofar falo , A kusan tare suka miƙe da sofi wacce ita ma tashin hankalin da ta ji a muryar Mamar ta ya firgita ta , Suka fito falon a tare kichiɓus suka yi da tawagar su Hajja kori tare da sauran ƴan uwan su na kurkusa da suka zo tare , Kamar zata cukumo Amnee haka ta tsaya a gaban ta tana huci , sannan tace " Amina baza ki taɓa sauyawa daga mummunar zuciyar ki mai cike da baƙin-hali ba ke da wannan Annamimiyar ƙanwar taki , da daga dawowar ku ke da ita shine kuka haɗa kai kuka maƙalawa ɗan mu auren Shegiyar ƴar da .... A tsawace Amnee ta katse ta bayan ta matsa baya kaɗan tace , "Hajja kori ki dakata , ya isa kar ki sake ki ce za ki tozartani ko ki tozartamin 'yar uwa ta , wanda kuka yi a da can ma ya isa wannan masifar taku da bala'in a yanzu bazan ɗauke shi ba domin kuwa kunne ya sake ƙaho ya girma . aure kuma tsakanin Yakaka da Hamza babu wanda ya isa ya hana ƙulluwar sa muddin ni na tsugunna na haifi Ɗana nayi ɗawainiyar sa sai ya auri Amina Yakaka , idan kuma a wannan karon ma za ku hana ne to Bismillah sai mu gani . Ƙara matsowa Hajja kori tayi jikinta har tsuma yake tace " tsohuwar kilaki haka kika ce ? Babu shakka dole kice ƙaho ya girma saboda kin gama yawon banzan ki a bariki kin dawo za ki laƙawa.... " Momy kori ki saurara haka nan Dan Allah duk abunda za kiyi kada ki aibata min uwa da mummunan ƙazafi , Muryar Doctor Hamza a kausashe ta ratso falon wanda sauƙar sa kenan a garin ya nufo gida yana faka motar sa bai ko gama tsayawa ba Hafsa ta ƙira shi hankalin ta a tashe tana shaida masa rigimar da ƴan uwan Baa suka zo su nayi musu . Cikin takun sa na nutsuwa ya ƙaraso wajen , yana zuwa ya shiga tsakanin su yana fuskantar Amnee , hannuwan sa duk biyu yasa ya dafa kafaɗun ta , cikin kwantatciyar muryarsa marar amo yace , " khaalas Amnee , Dan Allah kar kiyi hayaniya ki bawa kan ki stress kiyi haƙuri kin ji ? Ganin ta ta sauƙe akan sa idanun ta cike da ƙwallar ɓacin rai , jin irin mummunan ƙazafin da Hajja kori ta yi mata a gaban jama'a , zata yi magana ya katse ta " Kiyi haƙuri Ummii mu je ki huta . Hajja kori wacce ta ƙulu da yadda ya juya mata ƙeya yana rarrashin uwar sa alhalin ita tudu biyu take ci a wajen sa na babar sa kuma surukar sa , a fusace tace " Kai Hamza ƙaramin marar kunya munafikin maza , tare da kai watau aka haɗa baki aka munafunce mu kana sane , watau kai gaka mai uwa ko ? To ka tabbatar da cewa sai ka zaɓa tsakanin 'yata da wannan koɗaɗɗiyar shegiyar yarinyar da ake shirin aura maka , ƴar da ba'a san asalinta ba . Bai juyo ba , yace " Momy kori kema kiyi haƙuri Dan Allah . "Amnee mu tafi ɗaki ki huta , yace yana juya kafaɗun ta suka fara taku , " Doctor , Chak ya tsaya lokacin da sautin muryar Sofiya ya doki kunnuwan sa ,da sassarfa kamar ana tunkuɗa ta ta ƙaraso ta zagayo ta gaban su , idon ta da suka firfito da ke bayyana tsantsar firgicin da zuciyar ta take ciki ta tsattsare sa da su , cikin wata irin murya tace " Da gaske za ka ƙara aure ? Kai ne za ka auri yarinyar nan Yakaka ? kuma wai gobe ne auren naku ? Ganin sa ya kai kan Amnee da take raba ganin ta a tsakanin su , fuskar ta na bayyana ciwon da ran ta ke ciki, muryar sa can ƙasa yace " Gaskiya ne Amma ki bar maganar nan daga baya zamu yi . Kewaye ta yayi suka wuce cikin ɗaki , Ukhtee Rahima da take tsaye daga bakin ƙofar ɗakin idanun ta cike da ƙwallar tuno da wata rana mai kama da wannan a cikin wannan falon lamari mai muni ya haka ya faru ta silar dangin Prof da sanadin haka ne rayuwar su ita da 'ya'yan da ta haifa suka faɗa a garari , sai ga shi a yau tarihi yana sake maimaita kan sa sun kuma gwada hakan akan 'yar ta, daga ƙasan ranta take tambayar kanta wai laifin me ta musu ne da suka tsane ta , tsana mai muni ya haka ? Juyawa tayi ta rufa musu baya suka rufo ƙofar . Wani irin zaman 'yan dabaro Sofiya tayi a ƙasa dirshan kafin ta ƙwala wani irin ihun da yasa Rahima da Yakaka hanzarin ƙarasa shigowa falon da suke daf da ƙarasowa daman . " Ƙarya ne , inaa no no wallahi ƙarya ne , Doctor baka isa ka min haka ba , Momy kice mafarki nake dan Allah ? Ta ƙarasa sambatun da take tana miƙawa Momy kori hannu daga inda take kamar 'yar yayen da take son uwar ta ta ɗauke ta, A fusace Momy kori ta ƙaraso wajen , ta fara jaan hannun ta tana ƙoƙarin ɗaga ta , bakin ta har kumfa yake lokacin da take cewa , " sai ki tashi mu tafi ai shugabar 'yan taurin kai marar zuciya , tun farko ai na faɗa miki akwai ranar ƙin dillaci muddin kika yadda kika auri ɗan wannan Annamimiyar matar , amma da yake kafiya ce da ke kika nace kika liƙe masa kika ƙi kowa kika zauna zaman jiransa shekara da shekaru . "to ai ga shi nan kin fara gani kishiyar rana tsaka ,baki da ko darajar da za'a sanar dake bare a miki abunda ake yiwa mata a al'adance idan aka tashi musu kishiya , idan baki bar gindin auren ɗan Amina ba kaɗan ma kika fara gani daga cikin irin ƙiyayyar da zata zuba miki , A haukace Sofiya ta warce hannun ta daga cikin na Momy kori , da ƙaraji a muryar ta tace , " ki bar ni Momy , nace ki bar ni wayyo Allah na na shiga uku Doctor meyasa za ka min haka duk irin kula da son da nake nuna maka irin sakayyar da za ka min kenan ? Wani mummunan tsaki Momy kori ta jaa a fusaace tace , " to kar ki tashi dan uban ubanki ki zauna kina kuka anan , kina sambatun wofi akan wani lusarin yaron da bashi da zaɓin kan sa , shegiya mahaukaciya zauna anan nace , Daga haka ta fice a fusace , wasu daga cikin dangi da suke 'yan kanzagin ta suka rufa mata baya , wasu kuma duuu suka yi kan sofiya wacce take ta rafsa ihu kamar wacce uwar ta da ubanta suka mutu a haɗarin mota . Yakaka wacce duk haukar da Sofiya take yi tana kallon ta , a hankali ta fara jaan ƙafafun ta tana yin baya-baya zuciyar ta kuwa cike da tsoron kar Sofiya ta gan ta , Ai kuwa bata yi nasara ba domin kamar ancewa Sofiya ɗago kan ki karaf ta sauke idanunta akan Yakaka , Wata irin zabura tayi ta miƙe har tana ture matan da suka taru suna rarrashin ta dayawa daga cikin su rayukan su a ɓace yake da irin cin zarafin da suke ganin an yiwa 'yar uwar su , yi mata kishiya ba tare da an sanar da ita ba , sai a wajen bikin ta samu labari babu shakka a wajen mata wannan shine iyakar cin zarafin da ɗa Namiji zai iya yi musu . Kukan kura tayi ta kaiwa Yakaka cafka , da gudu Yakaka ta kewaya ta bayan kujeru tayi ɗakin Amnee dai-dai da murɗo ƙofar da Doctor Hamza yayi ya fito daga ɗakin , Tana zuwa ta shige jikin sa ta ƙanƙame shi , a bazata ya ji shigar sa jikin sa , dan haka ya ɗago kai a firgice dai-dai tahowar Sofiya , a cikin ƙanƙanin lokaci ƙwaƙwalwar sa ta fahimci abunda ke faruwa dan haka ya juya baya da sauri , dukan da Sofiya ta kawo gami da chafkar da taso yiwa maƙogoron Yakaka ya sauƙa a bayan sa , Tun ƙarfinta ta shiga dukan bayan sa da ya yiwa Yakaka rumfa da shi , tana ɗura ashar tare da shan alwashin a kan sai ta kashe Yakaka , Da kyar ya ɓanɓare Yakaka daga jikin sa wacce ta shige masa jiki ta runtse ido gam zuciyar ta bayan bugu ba abinda take yi , addu'o'i iri-iri bata gama wata take kama wata . Ƙofar ɗakin Amnee ta murɗo ta leƙo , lokacin da yake zare Yakaka daga jikin sa , " Menene kuma hakan ? Amnee ta tambaya a tsawace , Yakaka tana jin muryar ta ta juya da gudu ta kutsa ta bayan ta ta tsaya tana kallon Sofiya , tsintar kan ta tayi da kwashewa da irin dariyar nan ta na tsira , da kuma ƙarin ganin yadda Makeup ɗin da Sofi tayi duk ya mata muzu-muzu a fuska ya kwaɓe mata , kamar wata dodo . Ganin Amnee bai sa Sofiya ta bar zage-zagen da take yi ba , sai ma daɗa zabura da take yi tana son kamo Yakaka , wacce har lokacin dariya take yi da gajerun fararen haƙoran ta , Dariyar ta ta shagaltar da Doctor Hamza wanda yake ta faman rirriƙe Sofiya kamar wata tunkiyar da take rawar turke , fuskar sa da ɓoyayyen murmushin da ya barranta da yanayin da yake ciki a zahiri a sace yake kallon Yakaka , yaƙi matsawa daga wajen kamar wanda aka dasa shi banda kokawa babu abunda yake da sofiya . Muryar Amnee ce ta dawo da shi cikin hankalin sa , inda take cewa , " ka jaa ta ku bar nan wajen nace bana son hauka da rashin kunya kana jina ko ? Da ƙarfi ya murɗa hannun sofiya , muryarsa cike da gargaɗi yace " ki nutsu Sofiya meye kike ne haka ? Ki zo mu tafi . Ta tsakanin Mata da yaran da suke tsaye carko-carko suka wuce yana riƙe da tsintsiyar hannun ta Sun zo kusa da sashin sa ta warce hannun ta da ƙarfi , muryar ta tana rawar kuka tace " Ka daina jana Hamza , ina wai za ka kaini ? so nake kawai ka faɗa min gaskiya , dan ni har yanzu ban yadda da abunda yake shirin faruwa ba . Matsowa yayi daf da ita yana satar kallon tsirarun mutanen da suke sabgogin su a harabar gidan yace " Sofiya kiyi haƙuri dan Allah muje ki nutsu na miki bayani.. Da ƙarin ƙarfin kukan da ta take yi tace " Bayani ? Bayanin me za ka min ? Doctor meye bana yi maka a zaman mu na aure da za ka

Chapter 88 of 111