bayan ya gama ganin hotunan ,
ya ɗora ganin sa ga Falmata wacce ba ganin hotunan ta yi ba illa labaran da ta tsinci wasu abubuwan da Musa yake faɗa ,
Amma fuskar ta yalwace take da Kyakkyawan murmushin da ya ƙara mata kyau da haiba ,
"hannun ta ya riƙe yana murza yatsun ta ,
Yace,
" Fatima watarana zamu raya daren mu a Bawe Zanzibar island , kina so ?
Murmushi mai bayyana haƙora tayi , a hankali ta gyaɗa kai
" ina so Baban Mama ,
Shafar kumatun ta yayi ,yana jin yadda ƙaunar ta ke sake mamayar sa , cikin tunanin sa yana hasko yadda zasu yi rayuwa a tsibirin Bawe gefen taku .
Bayan sati biyu
Cikin sati biyun da suka biyo baya Falmata ta cigaba da shan magungunan da aka ɗora ta akai cikin bin ka'idar shan maganin ,
Gefe guda sassanyar ƙauna na gudana sannu kan hankali a tsakanin su mai cike da girmamawa daga ɓangaren Falmata , tausayi da zallar nuna kulawa kuma daga Youssouf ,
Duk wani rashin sakewa da ɗari-ɗarin da take da shi ta rage , ta fara sakewa da shi , har ma tana iya bashi wasu daga cikin labaran da suka shafe ta , iyayen ta, 'yan uwanta da garin su ,
Jin ainahin haƙiƙanin labarin su ya ƙarawa Youssouf zallar tausayin ta , tare da tasowar mikin binnennan laifin sa ga Yakaka ,
Ya haƙiƙancewa kan sa a yanzu Falmata bata da wanda ya fi shi , dan haka ya ɗau alƙawarin kome runtsi zai bata kariya cikin kowanne hali iyakar ƙarfin sa , shi zai zama inuwar hutawar ta bayan gwagwarmayar Rayuwar da suka shiga .
Yau tun da suka tashi sallar asuba basu koma ba , zama suka yi yin addu'a sosai game da aikin da za'a yiwa Falmatan a yau da misalin ƙarfe tara na safe , suna fatan Allah ya sa ayi aikin a sa'a .
Sai da gari yayi haske misalin bakwai , Mama ta farka ta fara neman abin karyawa ,
Kamar koyaushe Youssouf shi ya yi musu abun kari da shi da Falmatan sama-sama suka ci saboda rashin nutsuwa tare da Fargaban da suke ciki .
Takwas da rabi na safe ya yi musu a ofishin likita ,
Bayan gaisuwar da suka yi , likitan ya ƙara musu da kalmomin karfafawa ganin kamar suna tare da damuwa ,
A ƙarshe ya yi musu umarnin da su taso ya musu jagora zuwa ɗakin yin aikin inda sauran likitoci suke jiran su ,
Har bakin ƙofar dakin yin aikin da take iyakar sa ya raka ta ,
"kiyi ta addu'a Fatima , nima zan yi ta yi kin ji kou ? Ki roki Allah ya sa ayi aiki bissa sa'a , ki samu lafiya ,
Kai ta gyaɗa ,
Ba tare da ta furta kalma ba ,
Fuskar ta ya riƙo cikin tafukan sa ya Sumbaci goshinta ,
" ki shiga Fatima da Ambaton Allah , Allah shi baki lafiya ,
"Amin
Ta amsa idanun ta na kawo ruwa , haka kawai take jin fargaba gani take tamkar zata iya rasa ran ta a garin neman lafiyar ido ,
Ɗaya daga cikin nurses ɗin da suke cikin ɗakin ta taho ta kama hannun Falmata zuwa ciki ,
Labulen da yake tsakanin su aka yaye , ya zama Youssouf yana iya hango Falmata ta tsakanin gilashin da yayi ƙawayan ga ɗakin da take ciki ,
A shirye ya hangota tsaf, da taimakon nurses ta kwanta akan gadon da yake tsakiyar wasu fitilu masu matsanancin haske ,
Ba ɓata lokaci Manyan likitocin suka matso gaban gadon suka yi ƙawayan yayin da wasu suka shiga jona mata wasu na'urori a kai , wasun su na shirya kayan aiki ,
Aikin da ya ɗauke su tsawon awa guda da mintoci arba'in , da Youssouf ya ji lokacin tamkar tsawon shekara ,
Ɗaki na musamman aka mayar da Falmata bayan an gama yi mata aikin inda zata zauna tsawon awanni arba'in da huɗu kafin a kai ga mataki na gaba ,
Nan suka nemi Youssouf da ya tafi gida zata kasance cikin ƙarƙarshin kulawar su ,
Ya so yayi gardama saboda hankalin sa da yake tashe da son sanin halin da Falmatan ke ciki ,
Sai da Likitan ta ya yi masa bayani mai gamsarwa tare da kwantar masa da hankali ,
Ya sanar da shi allurar da aka mata zata sake ta nan da wasu mintoci , sai dai sun fi son kasancewar ta ita kaɗai , a wannan ɗakin da take zasu cigaba da bata duk wata kulawar da ta dace ,
Hankalin sa bai kwanta ba sai da ya yi masa jagora zuwa bakin ɗakin inda ya hango Falmata a kwance kan gado , an naɗe mata idanun nata da farin ƙyalle , da alama bacci take ,
Sanin da ya yi Mama bata cika lafiya ba ya sa dole ya bar asibitin tare da ita ya nufi gida da zummar dawowa zuwa anjima domin ba zai iya yin har tsawon wasu awanni masu yawa ba tare da ya gan ta ba , ya san halin da take ciki ba ,
Ko da suka dawo gida daga shi har Mama gidan bai musu daɗi ba ,
Mama kaɗai ya soyawa ƙwai tare da kifin gwangwani , ita ma bata wani ci na kirki ba ta ɗauke kai , Alamun ta ƙoshi ,
"Mama ki ci abinci sossai mana ,
Girgiza kai tayi tana ƙwalan-ƙwalan da ido ,
"Papa mu tafi wajen Mama yanzu ,
"zamu tafi idan kin ida cin abincin ki kin ji kou ?
Shiru tayi tana kallon sa ba tare da ta buɗe baki ta karɓi abincin da yake miƙa mata ba ,
Gajiya yayi da riƙe chokalin , ya ajiye gami da miƙewa yana jin yadda zuciyar sa ke cike da kewar ta , baki ɗayan hankalin sa na kan ta ,
Ya daɗe a zaune yana mata addu'a akan sallayar da ya idar da Sallar Azahar ,
Shafa kan Mama yayi wacce tayi bacci a gefen shinfiɗar sallar sa ,
Cikin ran sa yana aiyana irin yawan kewar Mamar ta da tayi wanda ya duƙusar da walwalarta
Ɗaukar ta yayi ya kaita ɗaki ya kwantar tare da rufe ta da bargo , ya zauna daga bakin gadon ,
Wayar sa ya ɗauka ya latsa ƙiran layin Tafeeda da ya yi ƙiran sa a ɗazu lokacin da ake yiwa Falmata aiki , bai samu damar ɗaukar kiran nasa ba
Bayan sun gaisa , tare da Tambayar lafiyar juna Youssouf ya ɗora da tambayar sa Leila matar sa da ɗan su Imran , ?
" duk lafiya suke ɗan'ouwa , Yarima kana ji na kou ?
"ina jin ka da kyau ɗan'ouwa ,
" Yarima kou kana da labarin mutanen da ka baro shekarun baya a Nigeria ?
Da ace Tafeeda na gaban shi a lokacin da zai iya hango firgicin dake zane ɓaro-ɓaro bisa fuskar sa ,
"waɗanne mutane Tafeeda ke magana kan su ?
Tambayar da zuciyar sa ke yi ya bayyana kan harshen sa ,
Jim! Tafeeda ya yi yana nazartar firgicin da yake iya jiyowa daga Muryar Youssouf ɗin ,
"wannan ɗiya da tsautsayi yassa ta samu a duniya , nace kou ka sake waiwayar ta ? Tafiya ta kama ni zouwa Nigeria shine nake biɗar izni kan na tai na gan ta ko da ba kai tsaye ba ne na....
Cikin sauri Youssouf ya katse sa muryar sa a ɗan sama kaɗan ,
"Tafeeda ban ma izni ba , batun wannan ɗiya ai mun jima da ajje shi ghefe kou , ka kyale kawai wani lokaci idan Allah ya ida nufi ni naje da kaina na duba ta ,
Ajiyar zuci Tafeeda yayi ,
"tou babu kome 'dan ouwa Allah shi gwada mouna lokacin da lafiya , Allah kouma shi ƙara rufa asiri ,
'Amin Amin 'dan ouwa ,
Shiru ya gifta tsakani sakamakon tunani mai zurfi da kowannen su ya faɗa ,
Babu shakka Tafeeda yana da wani dalili da ya sanya shi bijiro masa da zance Mama a dai-dai wannan lokacin da tsawon shekaru wajen shidda bai taɓa tambayar sa game da lamarin ta ba sai fa yau .
a daddafe ya iya kaiwa bayan la'asar a gida , ya sake shirya Mama da ita ma duk ta damu da son su koma wajen Falmata ,
Ko da ya isa asibitin har lau bai samu damar shiga ɗakin da Falmatan take ba .
Haƙuri likitar da take da Alhakin kula da ita ta bashi , akan ba zai yiwu ya shiga inda take a yau ba sai ko zuwa gobe da yammaci
Haka suka ƙaraci zama daga gefen ɗakin da take ciki har duhu ya fara shiga, dan dolen sa ya miƙe da Mama ya ƙarasa jikin ƙofar ɗakin da take ,
Ya yi mata addu'a , kafin su bar asibitin zuwa gida ,
Daren ranar bai zo masa da sauƙi ba , baki ɗaya sai juye-juye yake yi ya gaza yin baccin kirki , bai san da haka ƙaunar ta ta rarake masa zuciya ba sai da ya gaza bacci saboda damuwa da son sanin halin da take ci gami da kewar ta mai tarin yawa ,
Abunda bai taɓa jin kwatankwacin sa kan kowacce ɗiya mace ba , ko da kuwa Maimounatu ,
Salon ƙaunar da yake yiwa Fatima daban ne da yake tafe da wani irin yanayi mai tasiri sossai a gare shi ,
Sai gefen asuba bacci ya ɗauke shi cike da mafarkai iri-iri , da har ya sanya shi makara wajen yin sallar asubahi .
Tara na safe suka samu isa asibitin , inda kuma cikin sa'a ya samu damar shiga ɗakin da Falmatan take ƙarƙashin jagorancin likitan ta ,
Da takun ƙafar su ta san da shigowar su ɗakin da take da ita ma ta kwana cikin kewar su duk kuwa da zogi da idon ke yi mata lokaci zuwa lokaci , amma ta fi damuwa da ta san a wanne hali Mama da Baban ta suke ?
"Mama , Maama
Suka haɗa baki wajen ƙiran sunan junan su ita da Mama wacce da shigowar ta ɗakin ta hango Falmata , ta tafi da gudun ta ,
Ɗago ta Falmata tayi ta rungume ta a jikin ta , tana jin yadda sanyin ƙaunar ta ke ratsa zuciyar ta , babu shakka ƙaunar Mama magani ce ga ta ta zuciyar ,
Da murmushin samun nutsuwa ya ƙaraso bakin gadon ,
"Fatima yaya jikin naki ? Babu inda ke miki ciwo kou ? Baki cikin damuwa kouma ?
Waigawa tayi sashin da take jin tashin muryar sa ,
"Baban Mama ina kwana ? Yaya Mama ta kwana ? Bata yi ciwo ba ko ?
Ɗan tsayirtawa tayi , kafin ta ɗora da cewa
"bana jin damuwa ko ciwo mai tsanani , amma ina son a warware min idon nawa wannan abunda suka rufe min ido da shi yana damuna ,
"likitan da duk yana jin abunda take faɗi tare da taimakon na'urar kunnen sa ,
Ya matsa yana sake rarrashin ta tare da yiwa Youssouf bayani kan cewa kafin su warware mata idon zuwa gobe anfi buƙatar idon ya zauna a rufe haka , har sai bayan awanni arba'in ,
A cikin ɗakin suka wuni tare , sau biyu Gimbiya maimounatu na ƙiran wayar sa , ya gaza ɗaukar ƙiran .
Bai san dalili ba amma can cikin ran sa ya gujewa yin hira da maimounatu ne saboda gudun ɓacin ran Falmata .
Washegari kamar yadda suka sharɗanta , awanni arba'in da huɗu da 'yan mintoci ,
Misalin ƙarfe goma na safe likitocin suka yi da'ira , a kan ta ,
Babba daga cikin su wanda kuma shine ainahin wanda ya yi mata aikin , shi ya warware mata idon ,
Bayan sassauta haske tare da sauya launin hasken zuwa marar kaifi , cike da fatan nasara likitan ya umarci Falmata da ta buɗe idanun ta ,
Babu karsashi ta fara wara idanun da suka mata wani irin nawi , hasken da ta ji kamar ya chaki idon shi yasa ta saurin runtse idanun ta kai tafukan ta biyu ta rufe fuskar ta ,
Cikin sauri likitar da ke gefen ta ta sauke hannunwan nata ,
Rarrashi da kalaman ƙarfafawa suka shiga yi mata cikin kwantar da murya , suna umartar ta da ta buɗe idon ta zata ga duniya ,
Sannu kan hankali ta ware idanun da suke rawa kaɗan-kaɗan , baƙon yanayi ne ya ziyarci ƙwaƙwalwa zuwa gangar jikin ta lokacin da raunanan jijiyoyin idanun ta suka fara ɗaukar jirkitattun hotuna suna aikawa da shi zuwa cikin ƙwaƙwalwarta da sauri ,
Wajen ya ɗauki shiru , likitocin suna ƙure ganin su akan ta da take gwale idon cike da burin son samun ƙarin ƙarfin ganin da tare kuma da son fahimtar abubuwan da take iya ganin hotunan su duru-duru , shin wannan shine hasken duniyar ? Haka kuma suffofin mutanen yake a zahiri ?
A sama ta tsinto muryoyin su lokacin da suka cigaba da yi mata magana , dusu-dusu take iya ganin kusantowar motsin wani abu kafin ta tsinkayi muryar likitan yana tambayar ta ko tana iya ganin alamun motsin sa ??
Bata amsa ba illa kan ta da ta gyaɗa ,
Hannu ya kai yana ɗaukar wani baƙin tabarau mai haɗe da 'yar na'ura na musamman wanda cikin awanni arba'in aka yi shi domin Falmata ,
Ya sanya mata a fuska tare da daidaita mata shi , ya miƙe tsaye da murmushi a fuskar sa cike da burin nasara , ya tambaye ta ko tana iya ganin sa ?
Zuba masa ido tayi tana iya ganin shatin sa fiye da ɗazu , suffar sa ta mutum ta bayyana duk da ba tarwai take iya gani sa ba ,
a hankali ta juya ƙwayar idanun ta zuwa kan kome da yake sararin wajen daki-daki take ƙure musu kallo , duk da ba sosai take ganin abubuwa ba ba kuma fahimtar su take yi ba ,
A hankali likitocin suka dare , tare da bada hanya ga Youssouf da Mama da babban likitan ya yi umarnin su shigo ,
Hannun sa yana riƙe da Mama suka shigo ,
Kamar koyaushe takun Mama ya fara isa ga dodon kunnen ta ,
Dan haka take ware ido cike da buri , burin da ada ta ɗauka ta haƙura da shi ,
'yar ƙaramar halittar da ke kusantota ta ɗorawa ido ,
Ko ba'a faɗa mata ba , ko da cewa bata taɓa ganin wata halitta da idanun ta ba , ta san wannan ita ce Mama ,
" Mama ,
Mama ta ƙira sunan ta dai-dai da ƙarasowar ta gaban ta ,
Hannuwanta biyu ta sanya ta ɗago Mama , da wani irin yanayi ta matso da fuskar Mama daf da tata bayan ta ɗaura ta a cinyar ta ,
Ƙure mata kallo take yi , cike da son ganin ta fiye da yadda take iya hango ta dusu-dusu a yanzu ,
Runtse ido tayi ta buɗe a hankali
'Mama
Ta ƙira sunan ta,
Dariya Mama tayi tana ɗora 'yan hannuwanta akan hannun Falmata da take tallafe da kumatun ta ,
Ta ga hasken haƙoran Mama da fuskar ta , a yanzu ta yadda da cewa ta samu waraka , irin ganin da take yi dusu-dusu shine ganin da ta haƙiƙance kowanne ɗan adam yana yi ,
Irin haske marar ƙarfin da take gani shi ta aminta da cewa shine hasken duniya , ita kuwa mai zata yi da ya wuce godiya ga Allah da ya nufe ta da samun waraka ?
rungume Mama tayi tana faɗin kalmar Alhamdulillah , Alhamdulillah babu ƙaƙƙautawa ,
Raf-Raf-Raf likitocin da suke wajen suka ɗau tafi , cike da bayyana farin cikin su na samun nasara kan aiki ,
Youssouf wanda farin cikin sa bazai misaltu ba ya tako zuwa gaban gadon Falmata ,
" Fatima
Ya ƙira sunan ta , da amon muryar da take cike da shauƙi da zumuɗi ,
cike da ƙwaɗayin son ganin Fuskar wannan ma'abocin Alheri a gare ta ta ɗago kan ta daga fuskar Mama da take ta son sake gani tamkar mai son haddace kamannin ta a ɗan tsakanin lokacin ,
Dariyar haƙoran sa ta fara cin karo da su , kafin hasken farar fuskar sa irin na Mama da ta fahimci basu kai sauran mutanen wajen haske ba , ta bayyana mata ,
Kafe shi tayi da ido tana burin ganin kamannin sa ko da kuwa ace shine abu na ƙarshe da zata iya samun nasarar gani kafin hasken da ta samu ya koma duhu da har yanzu ta gaza yadda a zahiri ne ba mafarki ba cewa idanun ta suna ganin duniyar da ta rayu tsawon lokaci a cikin ta ,
Irin riƙon da ta yiwa fuskar Mama shi ta masa , ta kai hannun ta kan sajen fuskar sa ta tallafo fuskar tana kallon sa da irin ganin da ya sawwaƙa a gare ta ,
Dariya Youssouf ɗin ya cigaba da yi da haƙoran sa ganin yadda ta riƙe masa fuska ƙam-ƙam , kamar wanda zai ƙwace ya gudu , ko kuwa ya ɓace mata ,
Da ƴar dariyar mai tafe da amon da ke bayyana tsantsar farin-cikin ta , ta kai goshin ta ta haɗa da nashi , tsinin hancin su na gugar na juna ,
"Baban Mama nagode , nagode nago...
"Fatima ki godewa Allah da ya baki lafiya , ni ma shi nake godewa , da ya nufa aka cimma nasarar aiki ,
Zama yayi daga gefen ta a bakin gadon ,
Mama tana tsakiyar su ya sanya hannu sa ya kewaye su da shi ya rungumo su jikin sa , yana jin matsanancin farin-ciki na zagaya ruhin sa ,
Tamkar a ire-iren shuɗaɗɗun lokutan da suka wuce cikin rayuwar ta da Yakaka , sautin ta ya bijiro cikin tunanin ta tamkar a lokacin take furta mata ,
" Falmata na ina ji a jikina watarana za ki warke , za ki ganni kamar yadda nake ganin ki .
Hawaye masu ɗumi suka silmiyo ta ƙarƙashin gilashin idanun ta , kewa tare da ƙaunar ahalin ta suka bijiro mata , a sarari ta furta
" Allah ya jiƙan ku Baba , Mama , Yakaka, Bakura da Baana ,
'Amin
Youssouf ya amsa mata .
*****
Cike da tarin sabbin dokoki da sharaɗin ziyartar likita a duk bayan mako guda na tsawon watanni biyu ,
Suka samu sallama daga asibitin , tafiyar ƙafa suka yi zuwa gidan su , inda Falmata ta dunga bin titi da ganin ta marar ƙarfi ,
Murna fal cike da zuciyoyin su ita da Youssouf , kome ta hango shatin sa sai ta tambaye shi wannan abun menene shi ? Meye sunan sa ?
Shi kuma babu gajiyawa cikin jin daɗin tambayoyin da take masa yake bata amsa tare da faɗa mata sunayen abubuwan .
Ƙofar gidan Musa suka tsaya , farin cikin da zukatan su ke ciki ya tunbatsa so suke su yi ɗaukanin sa da wani , alhalin babu wani nasu makusanci tare da su , dan haka gidan Musa suka yada zango ,
Musa da Ramlat sun taya su murna sosai inda a ƙarshe har 'yar walima suka shirya musu nan cikin falon su,
Yana riƙe da hannunta suka shigo gida ,
Suna shiga tun kafin su zauna ta ce shi ,
"Baban Mama ka ƙira Hajja a waya na faɗa mata na warke nima yanzu ina gani ,
Yana murmushi ya zaro wayar sa daga Aljihun sa ya shiga lalubar layin Hajja ,
Ya san dole tana neman wani makusanci nata wanda zata raba farin-cikin ta da shi ,
Nigeria
Tsawon satikan da suka biyo bayan Rayuwar Yakaka tayi su ne wajen ganin ta cigaba da ƙokarin wanke laifin ta daga idanun jama'ar gidan Prof ,
Babu inda take zuwa kullum tana gida ita ke yin mafiya yawan aiyukan gidan ,
A hankali Hajja ta fara fahimtar kyawawan ɗabi'un Yakaka , na kawaici da gudun tashin hankali , sannan kuma me sakakkiyar fuska ce ma'abociyar murmushi ,uwa uba yawan ibadar da ya zauna mata .
Hakan ya sa ta fara sakar mata fuska har takan ɗan ja ta da hira a wasu lokutan ,
A yau ma zaune suke , suna 'yar hira Yakaka tana taya Hajja tsinke ganyen zogalen da zata yiwa Prof girki da shi
Wayar Hajja da take ajiye a gefe ta ɗau ƙara ,
Da sauri Yakaka ta ɗau wayar ta miƙa mata ,
"Ni hauwa'u waye ke ƙirana da wannan sanyin la'asar ɗin ? Allah jishe mu Alheri ,
ɗaga ƙiran tayi dai-dai da ƙwanƙwasa ƙofar falon da aka yi , Yakaka ta miƙe da saurin ta tana cewa
" Oyoyo Rahima .
Ta nufi ƙofar ,
"Assalamu Alaikum Hajja ni ce Falmata ,
Muryar Falmata ta karaɗe kunnen Hajja ta cikin wayar ta mai maɗaukakin sauti ,
Yunƙurawa tayi ta miƙe tsaye ɗingis-ɗingis ta nufi ɗakin ta da yake gefe ,
"Lale Lale Marhabin da uwarɗakina Fatima mutan turai ,
Ta furta hakan lokacin da take ƙarasa shigewa ɗaki cike da son kar Yakaka ta san da wacce take waya ,
" Uwarɗakina ince dai duk kuna lafiya ? Ya Babban soja tare da 'yar rigima Mama , dafatan an samu nasara wajen neman magani ?
"Hajja Alhamdulillahi ki taya ni murna , na warke Hajja na samu lafiyar idona ,
"Da gaske Fatima kai Alhamdulillah nayi murna , nayi murna Allah Abun godiya kin warke Fatima ,? Buwayi gagara misali ,
Murnar Yakaka ta rikiɗe zuwa Fargaba lokacin da idanun ta suka sarƙe cikin na Sofi matar Yaya Dakta ,
Kallon-kallo na daƙiƙoƙi suka yiwa juna kafin ta tsinkayo muryar Doctor Hamza wanda yake tsaye daga bayan sofi ,
"Malama kauce ki bada guri mutane su wuce kin yi wani sanƙanƙam a tsaye kina zarewa mutane ido ,
Da sauri Yakaka tayi baya tana komawa falon ƙarƙashin rakiyar mummunan tsakin da sofi ta bita da shi .
Ɗan diri-diri tayi a falon rashin ganin Hajja yasa sum-sum ta nemi mafakar ta a can ƙarƙashin kafar benen da yake falon ta samu guri ta zauna ran ta duk a dagule .
"Me ya sake dawo da shi yau kuma ? har ma da matar sa ?
Daga inda take tana iya jiyo tashin Muryar su ,
Da Sallamar da Docto Hamza ya yi ,
Basu ko zauna ba Sofi ta fara faɗin
"Wannan kuma wacce jemammiyar 'yar aiki aka samu haka a gidan nan ? Sai tashin ƙarnin man masu bleaching take , Doctor ba dai ita take yin wanke-wanke ba , ? Dan bana jin zan iya riƙe ko chokalin da ta wanke ,
A kaikaice Doctor hamza ya dube ta yana samarwa kan sa mazauni akan kujerar falon mai cin mutum guda ,
Motsa laɓɓan sa yayi kamar zai ce wani abu sai kuma yayi biris da ita yana zaro wayar sa daga Aljihu ,
Hannun kujerar da ya zauna ,Sofi tayi matsuguni a ɗosane tana cigaba da cewa ,
"Ni kamar ma nasan Fuskar ta a wani waje ?
A hankali ya ɗago kai yana duban ta da ita ma ta karkato gare shi , fuskar ta ɗauke da wani irin yanayi na tsantsar ɓacin rai da bai kai ga sanin dalilin samuwar sa ba ,
" akan wa kike magana ne ?
" wannan yarinyar mai kama da farar kura , "
Ta furta hakan lokacin da tunanin ta ya gama tuno mata da inda ta taɓa ganin Yakaka a gidan Samy baby ,
Dariya ce ta so kama Doctor Hamza jin an kwatanta Yakaka da farar kura ,
" ko ina sofin sa ta san wannan gantalalliyar yarinyar ?
Ya tambayi kansa a zuci .
" okay ,
Yace a taƙaice yana mayar da hankalin sa ga fuskar wayar sa ,
"irin karuwan nan ce masu tsayawa a bakin hanya suna ne...
Fitowar Hajja cikin Murna ya katse mata zance da ta ɗauko yi ,
" a a' ah Babban likita kaine tafe iwar haka ? Sannu da zuwa sannu da zuwa ka sha hanya tun daga birnin tarayya,
Da 'yar fara'a Doctor Hamza yake amsawa Hajja gaisuwar da take masa ,
Hajja ta ɗora
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Chapter 110
Chapter 111
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 70 Chapter of 111