Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Baban Mama , Mijin Falmata . "Amma kamar na ga fa mutum yana yawo a ciki Hajja ko shi ɗin yana nan ne ? "wa ya sani ko Fatalwar sa ce kika hango , saboda shi dai kam baya gari , sai dai in kuma binbinin sa kike a zuci  abunda ni dai nake so da ke ɗaya ne , " ki kama kan ki , saboda kin ga dai yanzu a matsayin sirikin ki yake , ke kuma a matsayin Fatalwa kike a wajen sa , "Dan haka ki kame ki dunga nuna halin surukutaka, ki manta da mu'amalar ku ta baya da ta riga ta shuɗe muddin kina son nuna dattaku ato . Jikin ta a sanyaye ta kama yin sharar da take da nufin yi , kalaman Hajja suna mata yawo a zuci , duk da ta sha  faɗa matan hakan yafi sau shurin masaƙi daga ranar da ta ƙudurci niyyar biyo ta , amma kalaman basu taɓa huda zuciyar ta irin na yanzu ba ko me yasa ? Ƙarfe goma direban da ya kawo su yazo , gaisawa kawai suka yi da Hajja tace yayi tafiyar sa anjima su da kan su zasu kasuwa , Ransa ya nuna ba haka ya so ba , amma ba yadda ya iya haka ya tafi yana muzurai . Rochester New York Tun bayan bayyanuwar cikin jikin Falmata laulayi ya sako ta gaba , laulayi take irin mai wahalarwa , kome ta ci amai take , ga kasala da rashin ƙarfin jiki , kusan kwance take yini , Youssouf ke yin kome na daga aikin gidan da bai cika yawa ba . Ga ranta da yake a dagule saboda batun komawar su gida , so tayi Mama ta warke kafin komawar su wacce cikin kwanakin nan jikin nata yake yawan matsanta mata . Sai dai duk yadda ta so Baban Mama da ya yarda ya ɗage komawar su gida saboda a yiwa Mama akai tunda ga damar ta samu , ita ta amince a yi amfani da jinin abunda ke cikin ta a yi Mama aiki , Amma yaƙi amincewa , hankalinsa yayi gida , har saɓani suka kusa samu a ƙarshe ya ce ba zai amince ba da abunda yake cikin ta da Mama duk ɗaya suke a wajen sa , hakkin su ne ya kare lafiyar su , su duk biyun ba zai yi abunda zai iya sa abunda ke cikin ta a hatsarin da zai salwanta ba , kamar yadda ba zai so rasa Mama ba , Su haƙura su bar kome zuwa lokacin da za'a haifi abunda yake cikin nata ya girma zuwa munzalin da shi ko ita da kanta zata sadauƙarwa da 'yar uwar ta/shi ɓargon ta . Falmata tayi kuka akan wannan batun , a ganin ta Baban Mama baya tausayin Mama , yaya zai ce har sai Mama ta jira shekaru kusan ishirin nan gaba tana fama da wannan ciwon ? Wannan ya ƙara mata damuwa duk ta rame sai haske da ta ƙara yi da ƙyalli irin na mata masu ɗauke da ƙaramin ciki , Ana gobe tafiyar su bayan sun dawo daga ganin likitan ta , inda ya bata tsawon watanni goma nan gaba da zata sake dawowa a duba idon saboda  sanar da shi batun komawar su gida da suka yi , Sannan babu wata sabuwar matsala da ta taso akan idanun nata sai ma cigaba da ake samu kaɗan-kaɗan ganin nata yana ɗan sake ƙarfi duk da dai har yanzu bata gani tar-tar . Yossouf ya dubi Falmata wacce ta rungume Mama akan cikin ta suka yi lamo akan kujerar ta naɗe musu jiki da babban bargo ɗaya , duk kuwa da cewa sanyi ya ragu sosai ƙasar . "Fatima nace ki daina ɗaura Mama bissa ga cikin ki , kada ta miki ciwo ko kuwa abunda ke cikin ki .' Ɗan murmushi tayi bata ce kome ba illa sake rungume Mama da tayi wacce take taɓa ƙailula saboda rashin jin daɗin jikinta , Ba tare da ya janye idanun sa daga kan su ba ya cigaba da cewa , "dagga mun koma gida zan kai Mama école ko doumin ta huttashe ki , ki yi fama da kan ki kadda ta kawo matsala ga Baby ,  Da sauri ta katse shi , "Baban Mama a yanayin wannan jikin na Mama zaka kai ta makaranta , da dai ka dauka mata mai koyarta darussa a gida , makaranta yara zasu doke ta ko kuwa ta yi tsalle-tsallen da zai iya kawo tashin ciwon ta , ga.... Shima katse ta yayi cikin taushin murya , "Fatima ciwon Mama ai bai hana karatu , baki da labarin masu ɗauke da irin cutar ta har suna kaiwa ga matakin kammala jami'a har ma suyi aikin bautama ƙasa , al'umma kouma ta ci moriyar su ? "Mama zata tai ecole inshaAllah , ki dunga ƙarfafa mata a matsayin ki na ouwa gareta , wataƙila watarana ita ma ta zam likita , Ya ƙarasa zancen zuciyar sa cike sa burin son Allah ya gwada masa wannan ranar , "Allah ya sa Baban Mama , Allah ya raya mana Mama mu kai zuwa ga wannan ranar . Ta amsa fuskar ta ɗauke da murmushin da ta kwana biyu bata yi irin sa ba , *** Washegari bayan sun kammala duk wasu shirin su , sun haɗa kayan su da suke son komawa da su gida a cikin manyan Jakankunan su da suka zo da su alhalin babu kome a cikin su , a yanzu cike suke da tarin suturu , magunguna , zuwa kan kayan buƙatun su na yau da kullum da suke son tafiya da su . Sauran tarkacen da bashi yiwuwa su kwasa Youssouf ya zubda a babbar shara , bayan sun gama tattara kome nasu , Youssouf ya zare katin kuɗin sa da ake cirar kuɗin ruwa da na wuta tare da gas da suke amfani da shi tsawon lokacin , Suka jawo jakankunan su waje , inda suka tarar da waɗanda suka basu hayan gidan suna jiran su , miƙa ƴsn mukullin gidan ya yi , Suka yi musaba tare da godewa juna , ya matsa kusa da Musa da Ramlat wanɗanda suke tsaye , Fuskar su cike da alhinin rabuwa da zasu yi a yau bayan ɗan takaitatcen zaman jin daɗi da mutunta juna gami da shaƙuwar da ta fara shiga tsakanin su , suka gaisa Basu wani jinkirta ba suka shiga mota baki ɗaya da kayan su Musa ya jaa su kai tsaye zuwa Airport inda jirgin da zai sada su da ƙasar su kai tsaye daga nan harabar tashi da sauƙar jiragen sama na birnin New York zuwa harabar tashi da sauƙar jiragen sama na Niamey . *** Ƙarfe huɗu na agogon Niger jirgin su ya dira , inda daman direban sa na musamman yana jiran sa , ba wanda ya ke kai Falmata makaranta da daukota ba wanda shine yake kai Hajja Maiduguri , Wannan direban sa ne musamman daga wajen aikin sa , da daman sun san da isowar sa , Gidan sa ya nufa da shi duk cewa Falmata ta so su zarce asibiti saboda Amai da Mama ta dunga yi tun a cikin jirgi , jikin nata ba daɗi sosai , Har cikin gidan direban sa ya shiga da motar , ya buɗe musu ƙofar motar suka fito , Youssouf ya riƙo hannun Falmata da ita ma ba wani jin daɗin jikinta take ba ɗauriya kawai take yi amma baki ɗaya zuciyarta hautsinawa take dan haka ne ma ta ƙi cin kome , yunwa kuwa sai sasuƙar ta take yi , Ya ɗauki Mama a kafaɗar sa wacce take kukan zafi tana son a cire mata kaya masu ɗan nawin da suke jikinta saboda sauyin yanayi . Kai tsaye suka doshi cikin gidan sojan da ya ɗauko kayan su yana bin su a baya , bakin su duk ɗauke da Sallama suka shiga , shiru babu wanda ya amsa musu domin babu kowa a falon . Da shigar su falon Yossouf ya zaunar da Mama bisa kujera , gefen Falmata ta sanya hannu ta jawo Mama jikinta , Shima zagayawa yayi ya zauna daga ɗaya sashin kusa da ita , Bayan direban ya gama shigo da kayan Youssouf ya yi masa iznin tafiya , Ƙarasa haɗe sararin tsakanin su yayi , tare da riƙo hannun ta da duk ya saki , "Fatima me zaki ci ? Hajja zata dafa miki , ina ga ma bata san mun dawo ba , "Mama ki je ɗakin Hajja kice mun dawo , Duk da cewa ba ƙarfin jiki ta cika ba sai ta miƙe , "to Papa , "Baban Mama bari na ƙira ta da kai na, Riƙo ta yayi ya ɗorata baki ɗaya akan jikinsa , yana jin yadda jikin nata ya ɗau ɗumi , "ki bari Mama ta ƙira ta zata iya , kar ki wahalshe min da kan ki , shafa saman idanun ta yayi da suka ɗan shiga ciki , kin zauna da yunwa Fatima meyasa , Ƙarasa narkewa tayi a jikin sa tana jin daɗin irin riƙon da ya yi mata , "Nagaji da irin abincin su ne , " To me zaki ci Hajja ta dafa miki yanzu  ?   " Ƙuli-ƙuli mai sugar raina yake so , Ɗan zare ido yayi sai kuma ya saki sassauƙar dariyar da har ta isa ga kunnuwan Mama wacce take ta faman tura ƙofar ɗakin Hajja ta gagara buɗewa , Ita ma dariya ta sanya jin sautin dariyar Babanta , tana sake tura ƙofar ta ga an buɗo , a hankali ta ɗaga kai tana kallon farar matar da take tsaye a gaban ta da bata kai ga taɓa ganin fuskar ta ba , Yakaka wacce fitowar ta kenan daga wanka ta ji ana taɓa ƙofar ta zo da saurin ta ta buɗe ga zaton ta Hajja ce wacce ta tafi kasuwa sayo kayan miya tun da ta idar da Salla , Fuskar da ta ci karo da ita a zahiri ta sa zuciyar ta sauya bugu , tamkar a mafarki ta gan ta a gaban ta duk kuwa da cewa tana da masaniyar dawowar su a tsakanin yau zuwa gobe a cewar Hajja ,. Bata san lokacin da tayi durƙuso ba a gaban ta , ta miƙa hannuwanta biyu ta tallafe kumatun ta bayan ta dai-daita tsawon su , "Mama , Ta ƙira sunan ta da wani irin sauti ciki-ciki , rungumeta take nufin yi sai taji yarinyar ta janye jikinta a hankali ta yi baya-baya , Kafin ta juya da ɗan gudun ta tana ƙiran "Papa , Mama , watta ce cikin ɗakin Hajja , Da sauri ta yunƙura ta bi bayanta saboda ji da tayi gaba ɗaya zuciyar ta ta afu ga 'yar ta , wani irin shauƙin so da ƙaunar 'yar ta ke kwaranyowa a zuciyar ta , Da taka kafafunta a falon Falmata ta ɗago kan ta , daga ƙirjin Youssouf , tare da chanjin bugun zuciyar ta , a take ta bijiro mata a cikin rai Yakaka, ta ambata a zuci , Tare suka ƙaraso da Mama da ta tafi da gudu ta hau kan jikin Babanta da Falmata ta ɗaga , Turus tayi , idanunta ya sauƙa akan su  , da wani irin yanayi ta dubi ƙwarar idanun Youssouf da suke cikin nata da yanayin firgici ɓaro-ɓaro a cikin su , Cikin daƙiƙa kaɗan ta janye idanunta daga kansa ta mayar su ga Falmata , wacce take ware idanun ta da suke hango mata dusu-dusun farar mace sol a tsaye , wacece wannan ? Hajja kenan ? Girman da Falmata ta yi tare da gogewar da tayi basu jirkita mata kamannin 'yar ƙanwar ta ba , so take ta taka taje ta rungumeta , sai dai wanda ta hango ta jingine da jikin sa ya mata tarnaƙi . Bata motsa ba daga inda ta ci birki , illa Muryar ta da ya ratso shirun da wajen ya ɗauka ta ƙira sunan ta "Falmata na , Muryar ta ta sauƙa da ƙaƙƙarfan sautin da ya wuce yadda ita ta yi maganar a kunnuwan Falmata , Waigawa tayi sashin da Youssouf yake a daskare , muryarta na rawa tace ' Baban Mama muryar Yayata nake ji ta ƙirani , Muryar Maman Mama , Muryar Yakaka na , yan yién . Yakaka wacce Hawaye ya fara sauƙa daga gurbin idanun ta tace , "Falmata umaa yammana3 , umaa bangie3 , are3 nayie3 Falmata , Falmata are3 nayie3 , are3 Falmata kiramie nyie . Sai ta miƙe a hankali daga gefen sa tana jin wani ƙaƙƙarfan yanayi na kusancin su na ingizata yana cire mata duk wani tsoro da shakku daga ran ta , Yakaka ai wata sashi ce na daga tsokar jikinta babu shakka wannan Yakaka ce tsaye a gabanta , wannan farar inuwar da take gani ba kowa bace illa Yakakar ta  , 'Yar uwar ta , Ashe Yakakar ta na raye , ashe bata mutu ba ? ??? Yakaka bata jira ta ƙaraso inda take ba ta tafi ta rungumeta , zuwa lokacin su dukkanin su biyu kuka suke da sauti , Kukan da kowaccen su ta jima tana neman 'yar uwa da zata taya ta yin sa , kukan kewar junan su , kukan tausayi da ƙaunar junan su , kukan tunowa da farkon fari , mafarin faruwar walagigin su , Mama wacce tayi lamo a jikin Baban ta ɗago kan ta tana kallon fuskar sa , "Papa qui est cette femme étreignant ma mère? qu'est-ce qui les fait pleurer? ( Papa wacece wannan matar da ta rungume Mamana?  Meyasa suke kuka ? ) Tamkar wanda ya farka daga bacci haka ya firgita da tambayoyin Mama , kallon ta yayi kafin ya mayar da ganin sa kan su da suka ƙarasa zama a ƙasa har yanzu suna kuma rungume da junan su tamkar idan ɗaya ta bar ɗaya ɗayar zata gudu ko ta ɓace . Motsa laɓɓan sa yayi da nufin yin magana sai dai ko kalma guda ta gaza fiddo da kan ta , wani irin zullumi mai tafe da tsananin firgici ke samun matsugunni a ƙarƙashin ran sa , "Yakaka bata mutu ba ta dawo ?? Wani  irin sarawa kansa ya yi lokaci guda , take gumi ya shiga tsattsafo masa tunanin makomar auren sa da Falmata yana kassara masa duk wani guntun ƙarfin sa . Assalam Alaikum masu karatu , Da fatan duk kuna lafiya ? Ina miƙa sakon gaisuwata a gareku da fatan alheri a duk inda kuka yi bigire . za ku ce ya ta rage hannu ?? 😜😂  Ban san ko kun fahimci MHR ya fara naɗe kayan sa ba ?  Me zai hana kafin lokaci ya gwada mana ƙarshen MHR dukkanin masoyan MHR na fili da na ɓoye su yunƙuro , kuyi ɗango ku gwada min ƙaunar ku ga MHR ta hanyar bayyana ra'ayoyin ku tare da danna ɗan tauraron nan , da ni kuma na gwada muku irin tawa bajintar ta hanyar ƙure muku ......................ɗan..ɗan...ɗanliti😂🏇 ƙur-ƙet , ah to meye ? Ya wuce na dunga yin update kullum har a gama ?? Ƙurunƙus 🙅🤓 Nagode. [11/23, 7:08 PM] +234 706 503 6187: MAFARI ( Hargitsin Rayuwa ) Umm'muaz 41 Shigowar Hajja ita ta tsagaita kukan Yakaka da Falmata, Da girmama juna suka gaisa ita da Biyamuradi Youssouf wanda ya samu da kyar ya iya harhaɗa kalmomin amsa gaisuwar Hajja , saboda jin sa da yake gaba ɗaya a birkice a gigice, tamkar babban mai laifin da yake jiran hukunci daga Alƙali , da yana da dama da tuntuni ya ɓace ɓat . Hajja ta mayar da ganin ta gare su sai tayi saƙare tana bin su da kallon Al'ajabin yadda suka ƙaƙwume juna suna shiƙar kuka , " ku kuma yaran nan lafiya kuke kuwa ?  Uwarɗakina Falmata ya daga zuwa sai kuka ? Ai ke yanzu kukan ki ya ƙare , farin-ciki ya kamata ki ta tayi  'yar nan , bari kuka Falmata . Falmata ta ɗago kan ta daga jikin Yakaka idanun ta da hawaye amma tana ɗan murmushi tace , " Hajja ke ce wannan ? Bata jira ta amsa mata ba ta ɗora da cigabada cewa , "Dole nayi kuka Hajja , wannan da take gabana yanzu ita ce Yayata da nake baki labarin ta Yakaka Mamar Mama , ta dawo ashe bata mutu ba , kukan murna nake Hajja , duk duniya a yanzu bani da wanda ya wuce ta . Hajja ta ɗan taɓe baki , tana satar kallon Youssouf da yake wuƙi-wuƙi da ido yana shafa kan Mama da take jikin sa tana bin Yakaka da kallo , " aifa na ganta , labari kuma ya iske mini tun muna can , ai tare muka zo , ina gida lokacin da ta dawo daga inda tayi mafakarta tsawon shekaru , " Uwarɗakina lafiya ta samu ko ? , wallahi nayi murna , nayi murna Allah dai ya sakawa Babban soja da dubun Alheri , samun mijin da ya wuce shi a wannan zamanin akwai wuya , ki kama mijin ki ki riƙe ƙam-ƙam , Allah ya barku tare ya baku zuri'a masu yawa da Albarka , Shiru falon ya ɗauka aka rasa mai ƙarfin guiwar Amsawa , Ga Yakaka mummunar addu'a ta danganta addu'ar Hajja da ita dan haka tace " ba amin ba, cikin ranta tabbas ta san da Hajja take wannan kankanbar bata san wanene Youssouf bane ,  A sanyaye Youssouf ya miƙe riƙe da hannun Mama da taƙi barin jikin sa , so yake ya kaucewa sake haɗa ido da Yakaka , yana buƙatar wani ɗan saƙo da zai shiga ya rakaɓe ya haɗa kai da bango ya yi kuka ko zai ji sauƙin tashin hankalin da yake ciki , fili da baɗini bai ji daɗin dawowarta ba , bai ji daɗin bayynuwar ta ba , ya so da ta cigaba da zama a matatciyar ta tulin addu'o'in sa na riskar ta , Taku ɗaya yayi yana ajiye na biyu , yaji sun ƙira sunan sa a kusan tare , "Baban Mama , "Yusuf , Hatta hantar cikin sa sai da ta kaɗa , da jin tashin muryar ta da kaushi a ƙiran sunan sa , A firgice ya waigo idanun sa cikin nata da yake iya hango ƙiyayya da tsana masu ɗinbin yawa , ji yayi kamar ya durƙusa guiwa biyu ya roƙeta kadda ta fasa sirrin dake tsakanin su a yanzu .  Da sauri ya mayar da ganin sa ga Falmata wacce ya ga ta sunkuyar da kan ta yana iya hango bayyanar wani irin yanayi a tare da ita , "Na'am Fatima yace , Falmata wacce ƙiran sunan sa da Yakaka tayi ya ankarar da ita tare da tuno mata da matsayin Youssouf ɗin Na asali ga Yakaka , jikin ta yayi sanyi da tasowar wani yanayi mai suffar tsoro-tsoro daga ƙasan ranta , cikin dabarbarcewa tace , " un daman nace ga Maman Mama fa ? Baku gaisa ba ? Zaka fita da Mama bata gaishe da Maman ta ba , Da sauri ya saki hannun Mama , bai yarda ya dubi fuskar Yakaka ba , yace " sannu dai , Da sassarfa ya ƙarasa barin falon Mama ta ƙara da gudu ta bi bayan sa duk ita zuwan Yakaka ya takurata , Kallon tsanar da Yakaka ta bi Youssouf da shi akan idanun Hajja wacce ta kasa ta tsare tana bin duk wani motsin Yakaka da ido , Moɗe baki tayi kafin ta ce , " ke Yakaka tashi mu shiga daga ciki , ita Falmata ta bi sawun Mijinta tunda dai bata bar shi shi kaɗai ba , wannan zaman naku na ke kuka ita juyayi baya haifar muku da ɗa mai ido ba , " Abunda ya wuce ya riga ya wuce a bar tuna shi ana koke-koke kun ji ko ? Daga Yakaka har Falmata babu wacce ta amsa mata saboda kawo yanzu hankulansu ya dawo jikin su daga ruɗanin murnar da suka shiga na sake ganin juna , Kowacce kuma ƙwaƙwalwarta ta fara aiki cikin gaggawa da fuskantar ƙalubalen dake gabanta , Ga Yakaka yadda zata tunkari Youssouf yaso ruɗata da ta ga ya ƙara girma da haiba , ƙwarjinin sa yana neman tsorata ta sai dai daga ta tuna shi da munanan ɗabi'un sa sai ta ji duk ya koma fanko a idanunta , tafi shiga damuwa akan yadda zata fayyacewa Falmata gaskiyar kome , yadda ta hango nutsuwa a fuskar Falmata ta san zuciyarta zata yi baƙi idan ta san gaskiya wataƙila ma ta tsaneta ita da kan ta da ita kuma bata fatan hakan, ita yaya zata yi ne ?? Falmata kuwa wani irin tsoro ne ya cika zuciyarta tare da zullumi , bayan murnar dawowar Yakaka , zuwa yanzu abunda zai biyo baya takewa Fargaba . na farko tsoron rabuwa da Mama , Allah ya shaida bata fatan rabuwa da Mama ko na yini guda , sai kuma ga Allah ya dawo da Mahaifiyarta , ta san dole Uwar ta buƙaci 'yar ta , Yakaka zata rabata da Mama ne ko zata barta ta cigaba da riƙon Mama ? Tsoro take ji. Tare da zullumin rabuwar su da Baban Mama ,  mutumin da Alkhairin sa ya yawaita ya tunbatsa a gareta , mutumin da tarin Alherun sa da haƙurinsa da ita ya huda tattaurar zuciyar ta tare da kafa soyayyar sa a ciki , Mutumim da ya zama tsani na samuwar ganin haske a idanunta , mutumin da sanadin sa ta samu ilmin boko da na addini dai-dai gwargawdo,  mutumin da ta riga ta mallakawa gangar jikinta ya tarɓeta da so mai tsanani cike da tausayi da tausasawa  , mutumin da ta riga fara gina rayuwar ta da shi ,mutumin da wani ɓangare na jikin sa yake a cikin ta yana rayuwa , Wani irin narkewa ta ji dukkanin lakar jikin ta na yi , Lokacin da ta tuno yiwuwar rabuwar ta da shi , tunda daman rashin Yakaka ya kawo yiwuwar auren su har ta kai su da rayuwar aure tare yanzu kuma da ta dawo , dole ita zata matsa kenan  , zata tafi kenan , za su rabu kenan ina ma ina ma ? Sanyi ta ji ya fara kaɗa ta duk kuwa da cewa a zahiri zafi ake yi , Hannun ta da yake cikin na Yakaka ta dunƙule , jin haka ya dawo da Yakaka daga tunanin da ta nausa a ciki , da sauri ta riƙe hannun Falmatan , "Falmata kun dawo baku ci abinci ba ke da Mama ? Mun yi muku girki fa , kuma ma na kawo miki tsaraba ban san ko Mama ma zata iya ci ba , ƙuli-ƙuli ne mai sugar irin naki kina so  ? "ina so Yakaka kawo mun zanci , na daɗe ban ci ba , kamar kin san yana raina , yanzu na cewa Bab... Sai tayi shiru bata ƙarasa ba , ji tayi tana tsoron ƙiran sunan sa a gaban Yakaka ko me yasa ? Yakaka ta miƙe a hankali , ta nufi ɗakin da suka yi masauƙi , Hajja wacce tayi jugum a zaune tana binsu da kallon tsanaki , tace 'Uwarɗakina kar fa ki sanya kan ki cikin damuwar kome ko domin abunda kike ɗauke da shi a jikin ki damuwarki hatsari ne maigirma , da yardar Allah haƙuri tare da ƙaunar ki ta gaskiya da riƙo da zumuncin da kika yi basa bari ki tozarta ba , ke dai ki cigaba da yin kome domin Allah kin ji ko ? Gyaɗa kai kawai tayi , "nayi muku tuwon shinkafa da miyar kubewa , ga kuma farfesun dantsen sa , akwai dafadukar shinkafa 'yar uwar ki ta mata sarrafawar turawa a ciki wacce zaki ciki ? Ƙarasowar Yakaka ya sa bata amsa ba , hankalinta ya koma kan Yakaka da take tahowa , ƙewar 'yar uwar ta tare da wannan ƙaunar mai tarin yawan suna taya ta binne duk wata damuwar ta tare da ƙarfafa mata , "Yakaka ashe kina da tsawo haka sosai , ga ki kuma fara sol Yakaka mai kyau da ke tubarakallah ,  bani labarin kamannin Maman mu da Baban mu da wa ni nake kama a tsakanin su ? Yakaka wacce take sunce ledar ƙulin ta gama kuncewa ta ɗibo biyu a hannun ta , tana murmushi ta kai ɗayan bakin Falmata da

Chapter 74 of 111