Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yarima yake ko wa ? Ban san inda yake ba abokin sa nuhu da kan sa bama tare , dan haka dabara kawai nayi miki tare da aiki da ILMI NA , dayake ke wawiya ce kika yadda kika amince wani ɗan sarki wai yana ƙiran ki , Ɗan sarkin da kuka yi tarayyar kwanaki kaɗan domin samun muradin zuciyar sa kaɗai , ɗan sarkin da ya miki ciki ya jefar ki kan titi ya yi tafiyar sa ya bar ki ba tare da ya sake waiwayar ki ba , ɗan sarkin da dake da babu duk ɗaya ne a wajen sa , ya ma jima da mantawa kin taɓa wanzuwa a rayuwar sa , wanda yayi watsi dake tsawon wannan lokacin amma shine kika yadda wai yana ƙiran ki wai yana ƙiran ki a hakan nan naki ,!     Ta ƙarashe tana nuna ta da ɗan yatsa kafin ta kwashe da dariyar walaƙanci ,"      Kin san meye yaks , idan zaki tafi Ban hana ki ba ga hanya ki fita amma ki sani nan Babban birnin tarayya kike Abuja , cike take da mutane mabanbanta wanda masifar da take tare da wasun su ta kai girman da ya zarta tunanin ki , abune mai sauƙi a sace ki a ɓatar da ke ɓata na har abada ,"    Zaɓi ya rage gare ki ki zauna tare da ni ki gina kan ki ta yadda watarana zaki koma ki ɗauko ƴar ki tare da ƙanwar ki ki musu rumfa ki zama gatan su , ko kuma ki fita da nufin komawa masu amfani da mutane wurin yin tsafi suyi gaba da ke su hallakar ki , Wataƙila ki samu nasarar komawa garin maiduguri kije ki auri doctor Hamza,  sofi ta taso bisa kan ki a ƙarshen ƙarshe ki hallaka a hannun ta , masifar sofi bazai tsaya iyakacin kan ki ba , har makauniyar ƙanwar ki tare da ƴar da kika haifa sofi sai ta ɗau fansar raɓar mata doctor da kika yi ,"    taku ta fara yi tana barin falon bakin ta na sake furto kalmar ,shawara ta rage gare ki BANZA WAWIYA JAHILA , Kalma-bayan-kalma kalaman samy baby ke yin dawurwura cikin kunnuwa suna zarcewa ga kwakwalar yakaka , sai dai fassarar su sun gagari ƙarfin tunanin yakaka ,    Meye tace ne ? Me take nufi wai ? Anty samy tace ni wawiya ce jahila amma ai bata ce ni mahaukaciya bace , alhalin kuma ni nasan na haukace ne ,"    Zamewa tayi ta kwanta a tsakanin kujerun gurin tare da curewa ta duƙunkune cikin hijabin jikin ta , fata take a mata wani mummunan mari , ina ma fankar da take juyawa a sama zata faɗo ta daki kanta ko zata samu ta farka daga mummunan mafarkin ido biyun da take ,"     Wai Anty samy duk daman ƙarya take mata , wai Anty samy yaudarar ta tayi , wai daman ashe Bature kam silum ya jefar ta ne ba tare da ya taɓa neman ta ba , ashe ya manta da ita , ita ke dakon soyayyar sa , wai ashe ashe an raba ta ne da Doctor hamza mai taimkon su ita da ƙanwar ta , tuno da shi tayi da tashin hankali tare da tausayin da ta hango ɓaro-ɓaro cikin ƙwayar idon sa lokacin da take cikin magagin ciwon naƙuda , ajiyar zuciya ta fara saki da sauri da sauri tana jin yadda tsokar jikin ta take ƙarƙarwa sakamakon wani mugun sanyi da taji yana lulluɓar ta ,"     ME NAYI WA ANTY SAMY DA TA JEFA RAYUWA TA A WANNAN MASIFAR ?? Tambayar da ke yawo cikin zuciyar ta kenan lokacin da take rufe fatar idanun ta da ko ɗiris babu ɗigon ƙwalla , "wani tashin hankali yafi gaban kuka ,"       Sai yamma liƙis samy baby ts fito ta sha wankan ta ta haɗe cikin wata diguwar rigar roba mai bin jiki , kasantuwar ta ƴar chas-chas sai tayi kyau a cikin kayan ," bata ga yakaka a falo ba dan haka sai ta leƙa ɗakin da ta mallaka mata nan ma har cikin banɗaki ta leƙa babu alamun ta shiga cikin sa dan haka ta fito da sauri da nufin leƙa waje ko dai ta fita ɗin ne da gaske ???      Cin karo tayi da ita kwance a inda ta bar ta tun safe , ta Ƙudundune daga kan ta har ƙafafun ta , wani irin tausayin yarinyar ta ji ya taso mata , ita da kan ta ɗazu ta jima bata yi bacci ba da ta kwanta tana ta saƙawa da warwarewa , ganin laifin kan ta take , akan ƙaryar da tayi mata ta zo da ita ba tare da Aminccewar ta ba yayin da wani sashi marar  ƙarfi kuMa ke ganin ai daidai tayi taimako tayi kamata yayi ta Gode mata , Sunkuyawa tayi tana tashin ta a hankali ,"    Yakaka , wacce daman ba bacci take ba ta janye hijabin ta ɗago kan ta tana fatan ta buɗe ido ta ga kome mafarki ne , ta gan ta a ɗakin su da Doctor hamza ya mallaka musu , tare da ƙanwar ta , baby mama kuma tana fatan taji motsin ta a cikin cikin ta ,   Ganin samy baby ce ke tashin ta cikin gidan da ta tabbatar nan ƙaddara ta jeho ta rayuwa cikin sa , yasa ta ji zuciyar ta na yadda da abunda tunanin ta ke tabbatar mata cewa ba mafarki bane , kome ya faru ne a zahiri , ita yakaka a duniyar da take yanzu ita kaɗai ce jal , babu Falmata babu abunda ke cikin ta babu kuma Doctor Hamza mai taimakon su , duk tayi musu bara'a ta tsallake su bisa jagorar wawancin ta tare da jahilci da suka biyo ta kan mummunar rufa-rufa tare da gadar zaren da samy baby tayi mata , da taimakon ta ta aikata babban kuskuren da baza ta taɓa yafewa kan ta ba ,"    Kallon samy baby take kamar yadda ita ma samy baby ke bin ta da kallon tausayi ,    yakaka ki tashi haka Dan Allah ki je ki ci abinci kiyi wanka ki gasa jikin ki , kin san fa jego kike ina miki tsoron kar jikin ki ya lalace ,    Toh tace tana mai yunƙurawa ta mike , da sauri  samy baby ta kama ta kai tsaye banɗaki ta kai ta tare da sake haɗa mata ruwa mai zafi tace tayi wannan sosai ,"   Toh     ta sake amsa mata ," cikin daɗin ran fara samun haɗin kan yakaka samy baby ta nufi ɗan kitchen ɗin da taje da shi a gidan domin dafawa yakaka ɗan wani abu mai sauƙin dahuwa da zata iya ci ,    Nan da nan ta dafa mata indomie ruwa-ruwa da soyayyen ƙwai guda biyar ta haɗo da ruwa ta kai mata ɗakin , nan ta tarar da ita zaune akan tiles ɗin ɗakin ta har lau tayi wanka ta maida kayan jikin ta da hijabin da ta cire     Yakaka kul ki daina zama haka a ƙasa jego kike ba'a son mai jego tana zaman ƙasa tashi ki koma bakin gadon ga abinci ki ci , zan kawo miki wani kaya ki sauya kafin ki warware muje ayi miki sabbin ɗinki kin ji ?   Toh Tace tana miƙewa ta zauna a bakin gadon kamar yadda tace .    Wasa-wasa cikin sati guda da samy baby tayi tana gida kullum tana kula da yakakar , ta lura tamkar yarinyar ta koma shiru-shiru , wacce ta samu taɓin hankali bata un bata un'un kome tace mata kawai "toh" take cewa    Hirar duniya wacce take bukatar bada amsa samy baby tayi wa yakaka amma yakaka taƙi cewa uffan , iyakaci idan ta bata umarnin yin abu take zata yi babu gardama,    Ranar da ta cika sati da kawo ta gidan ta shiga ɗakin yakakar da safe , cikin ran ta tana aiyana idan har ta tabbatar yarinyar nan ta samu matsalar taɓin hankali ne , sauri zata yi tasan yadda tayi ta maida ta inda ta ɗauko ta , ah to ita ina zata iya rainon mahaukaciya ?     Zaune ta tadda yakakar tayi jigum tana kallon windown ɗakin ,"    yaks ya kike jin jikin ki yau ? samy beby ta tambaye ta ba dan tana sanya ran samun amsar yakaka ba , ga mamakin ta sai ta ga yakakar ta juyo da kallon ta kan ta , cikin wata muryar dake fitowa da sauti marar amo tace     ANTY SAMY KI KAINI MAKARANTA , KI SAKA NI A MAKARANTA INA SO NAYI KARATU INA SO NA SAMU ILMI. Wata irin dariyar murna samy baby tayi tana mai zama gefen gadon ta riƙo hannayen yakaka ,    Yaks , yaks ko kefa ? Kin fara fahimta ta ko yaks ? A yau yau zan sanya a fara nemar miki makarantar da za'a sanya ki , nayi alƙawarin karatu sai kin gaji yaks , Ilmi ai shine gishirin rayuwa bari ki ga ina wayata ?  Bari naje na ƙira Alhaji Gali , makaranta sai wacce kika zaɓa yaks , tace tana ƙarasa barin ɗakin har da ɗan gudun ta , Da ido yakaka ta bita cikin ran ta tana sake ɗaura ɗamarar goge kalmar JAHILCI daga gare ta da tafi bada tabbacin kome da ta aikatawa kan ta da wanda wasu mutane suka wanzu suna aikata mata , ya faru ne ta dalilin Jahilcin ta , Kalmar wauta kuwa a cikin satin ta fara nesanta kan ta da ita , domin a ɗamarar ƴakin da ta ɗaura bata da buƙatar tafiyar tare da wannan kalmar ta wawanci da aka danganta ta da ita , " Bata sani ba ko zata iya , ko burin ta zai kai ga cika , ko watarana zata cimma manufar da ta lulluɓe cikin ranta a tsawon sati guda da ta wanzu babu dare ba rana tana saƙawa tare da kuncewa cikin ran ta , tana matse zuciyar ta tana ƙwanƙwasar ƙwaƙwalwar ta har ta samawa kan ta mafitar da take ganin zata iya kaiwa gaci ta hanyar ta , bata sani ba shawarar zata kai ta inda take so ko kuwa zata ɗora ta ne kan wani kuskuren , bata sani ba ta raba kan ta ne da kalmar wawanci ko kuwa ta sake tafiya ne bisa jagorancin wani wawancin ? Ko ma meye ta bar kome ta janye hankalin ta daga kan kowa da kome ta ɗaura ɗamarar yin YAƘI DA JAHILCI ."   Maraɗi Niger Tafeeda ne zaune a gaban hajiya umma ya tanƙwashe ƙafafun sa babu kowa a falon ta na ciki daga shi sai ita ,      Ka tafi zouwa nigeria ka zo min da bayani mai gamsarwa a game da abokin ka. Tabbas yana cikin wani yanayi wanda yake boyewa daga gare mu , kayi gaggawar taryar sa a chan a magance matsalar tun kafin ya samu isowa da ita zouwa cikin gidan nan , kasan dai duk wata matsalar da ta shafi yarima idan har ta shigo gidan nan ta shafi mutanen cikin masarauta ne baki ɗaya ,"  Toh ranki ya dade cikin yardar ubangiji a gobe zan fara neman iznin tafiya daga shugaba na wurin aiki , zouwa ƙarshen sati na kan iya samun iznin tafiya , ki kwantar da hankalin ki , babu abunda zai faru ga Biyamuradin maraɗi Allahu shi sa haka , haka muke fata , Allah shi muku Albarka baki ɗaya ya kare ku daga faɗawa tarkon Maƙiya , kana iya komawa yaro na ," Ameen Ameen yake amsawa , ya miƙe kan sa a sunkuye yana faɗin ki tashi lafiya ranki shi daɗe ," shiru hajiya umma tayi tana nisawa cikin tunanin meke faruwa ga yarima youssouf haka mai girma da yasa take jin damuwa har a cikin amon muryar sa , ?? Jikin ta yana bata wani abu ya faru ko yana shirin faruwa gare ta ita kan ta kyakkyawa ko kuma akasin sa , koma menene tasan yana da alaƙa da youssouf ɗin ta domin akan sa kaɗai wannan soyayya mai girma take bayyana tasirin ta a kaf cikin ƴaƴan ta !      Cikin satin kamar yadda tafeeda yace ya gama shirinsa tsaf , yayiwa nigeria tsinke , Bai wani sha wahala ba yayi wa kan sa jagora zuwa garin maiduguri bayan da jirgi ya sauke shi a garin abuja , " sai da ya samarwa kan sa masauki international hotel ya huta , washegari ya bada kuɗi aka sayo masa layin nigeria ya cire layukan sa na niger ya sanya ns Nigeria , hajiya umma ya fara ƙira ya sanar mata da samuwar sabon layin nasa da zasu dunga magana ta hanyar sa sannan , ya kashe ya fara laluben number biyamuradi youssouf wanda bai kai ga sanin isowar Tafeeda nigeria ba rabon da suyi waya ma sun tasamma kwanaki goma abun da kusan hakan bai taɓa faruwa ba a tsakanin su sai fa yanzu da biyamuradin yake cikin wani hali na tsantsar damuwa tare da ƙarin zafafawa kan sa aiki da yayi ta hanyar rashin hutu ba dare ba rana yana zabarin rundunar dake ƙarƙashin sa suna matsa ƙaimi wurin farautar ƴan tawayen Boko haram ," duk a ƙoƙarin sa na son yakice tunanin damuwar sa daga cikin ran sa da kuma kusantowar lokacin da aka ɗibar ma su na kammala aikin su da nigeria yana gaf da ƙarewa tsakanin kwanaki arba'in masu zuwa nan gaba zasu cika shekara da aka ɗibar musu za kuma su koma ƙasar su ta haihuwa ,"......! Assalamu Alaykum kowa da kowa ! ina miƙa sakon gaisuwa ta ga masu karatu ,tare da fatan Alheri ! ku sani naji daɗi na kuma yaba muku a kan yadda kuka bayyana ra'ayoyin ku kan shafin da ya gabata ," ƙwarai ƙwarai na gode muku ," Zan kuma yi ƙoƙari ganin nayi amfani da wasu daga cikin shawarwarin ku/ƙorafin da kuka yi , da fatan nima zaku bani dama ku cigaba da bibiya ta ba tare da kun yi saurin yanke hukunci ba har ku ga inda na cimma matsaya da kuma manufa ta da inda labarin ya dosa , Da fatan zaku samu wasu ƴan dakiƙai daga cikin lokutan ku kuyi addu'a ga ƴan gudun hijira da igiyar rayuwa ta chukurkuɗe musu take kuma jaan su tana haɗa su da manyan ƙaddarori duk a sanadin rabo su da bigiren su mahaifar , su garuruwan su da annabor boko haram tayi , suka tsinci kawunan su a cikin matsananciyar rayuwar da ta zarce ta su yakaka da falmata a tasku tare da wahalarwa , Annobar boko haram gaskiya ne kamar yadda wani sashi na daga cikin labarin nan yake gaskiya ! Ina matan da suke makancewa cikin so , ?  tare da sarkarwa soyayya ragamar rayuwar su , har ta kai su ga aikata mummunan kuskuren da zasu wanzu suna danasani tare da nadama cikin rayuwa , Yakaka tace ahir kuma kul ! Ba kome da kake so kake samu ba ba kuma kowanne abunda kake so bane yake zama Alheri , Rayuwar da duk aka ɗaukaka soyayyar fiye da kome a cikin ta ba'a cika yin ƙarƙo tare da samun farin cikin rayuwa ba ,! Hannun ka mai sanda ne kuma Nasiha ce !    Nagode !   Af na manta    Yakaka tace I Love y'all ta gutsuro muku kaɗan daga cikin irin son da take yiwa bature kam silum, " Ah to meye So ne fa ??? 😂    [7/9, 4:42 PM] +234 803 559 8589: Fikra writers association . MAFARI ( Hargitsin Rayuwa ) umm'muaz 28 Biyamuradi youssouf bai samu damar shigowa cikin garin maiduguri ba sai da Tafeedah ya samu kwanaki biyu a cikin garin yana dakon jiran sa ,"saboda yanayin aikin sa ," Kai tsaye hotel ɗin da tafeeda yayi masauƙi ya nufa , kasantuwa tsawon watannin da ya samu yana ɗan shigowa garin ya fara gane hanyar guraren da kafafun sa ke yawan zuwa ," Bayan sun gaisa cikin raha sosai irin ta aminan junan da suka shaƙu da juna , Tafeeda ya nisa yana kallon Youssouf ɗin tare da nazartar sa , ƙwarai ya fahimci har yanzu bai shirya sanar da shi damuwar sa ba , duba da yadda yayi ƙoƙari ya boye damuwar ta sa fiye da wancen haɗuwar tasu , cikin rashin sanin damuwar ɓaro-ɓaro ta bayyana kan ta a cikin ƙwarar idanun sa ," Kai tsaye Tafeeda ya doshi Youssouf da maganar da ta taso shi takanas daga ƙasar su ƙarƙashin umarnin hajiya umma , inda yake cewa   Ban san ba ko rabuwar mu ta ƴan watanni ta sauya alaƙar mu da kai ba ɗan ouwa , ta yadda har ta kai ka shiga boye min wani babban lamari da ya shafi rayuwar ka wanda ya kai ga tsunduma ka cikin damuwar da hatta Hajiya umma ta shina , ita ma kuma damuwar ta shafe ta ta kuma sanya ta a firgici , ka riga ka san kome na daga yanayin gidan da munka taso cikin sa , ka san kou kai wanene , kasan yadda hajiya umma ke takatsantsan da du wani lamari naka , hakan ya sa hajiya umma ta titsiye ni tana son san sani game da abunda yake faruwa gare ka , na shaida mata ko ɗaya bani da sani game da halin da kake ciki nan , sai  tayi gaugawar turo ni domun naji shin menene damuwar ka Yarima Youssouf ? Shiru ne ya ɗauki ɗakin , A haƙiƙanin gaskiya Youssouf yana kunyar buɗe baki ya sanar da wani mahaluki laifin da ya aikata tsakanin sa da ubangijin sa , laifi mai girma kuma irin wannan , to amma hajiya umma ita wata halitta ce mai girma gare shi bazai so ba ko kusa shi ya zamto silar samar da damuwa ga ruhin ta , abun zai masa yawa ," To amma wanne hali zata shiga idan ta ji dalilin shiga damuwar sa ? Wane alfanu sanar da ita damuwar sa zai samar ?  Idan ta ji laifin da ya aikata da har ta kai shi ga shiga halin da yake ciki ƙara mata damuwa zai yi daɗi da ciwon zuci ko kuwa ma hawan jini ," ! Kai anya ma kuwa zata yafe masa ?? Tunanin halin da zata iya shiga ciki kawai ya sanya gumi tsatsafo masa a goshi , hannun sa ya kai ya rufe fuskar sa da tafukan sa , ya goge gumin , Ɗan ouwa , nayi kuskure mai girma cikin rayuwa wanda giya ta zam sanadi , na haiƙewa ƴar mutane , nayi tarayya da ita har ta samu juna biyu , a yanzu haka mariƙiyar yarinyar ta kore ta ta shiga duniya . ɗan ouwa ka faɗa min ya zan yi ina zan tahi na same ta ? Yaya zan yi na gyara kuskuren da na aikata , ɗiyar mutane zata zama kilaki sanadi na , yaya rayuwar ni nawa ɗiya mata zasu ƙarƙe ?? Yaya nawa ƙanne zasu samu kariya , tayaya zan katange iyalina ? .... Kallon sa kawai Tafeeda yake idanun sa sun kaɗa jazir da ɗai bai taɓa jin zance mai munin wannan ba , ashe yarima bayan shan barasa har fyaɗe yake yiwa mata ? Har zina yake yi ?  Har ɗa ya samar ta hanyar haram ? Anya anya Yarima Youssouf ya chanchanta ?? Miƙewa yayi ya soma haɗa kayan sa ," baya so ya cigaba da kallon sa , ganin sa a halin yanzu zai ɗarsa masa tsanar sa , zai rushe amincin da suka faro tun ƙuruciyar su ," yana so ya tafi , yana so yaje ya lallashi hajiya umma da tausasan kalamai domin ita ɗin a yanzu abar a tausayawa ce , da ɗai bazai yadda kunnuwan ta su ji waɗannan munanan laifukan da ɗan da ta ƙwallafawa rai ya aikata ba , ɗan da hatta shi da kan sa yaci albarkacin samun tsaftatatciyar tarbiya daga gareta sanadin raɓar Youssouf da yayi amma sai ga shi , !  Kai kaicho Da sauri Youssouf ɗin ya miƙe yana riƙe hannun Tafeeda da yake harhaɗa ƴan abubuwan buƙatun sa cikin jaka , Warce hannun sa yayi da wani irin zafin nama     Kar ka taɓa ni Youssouf , babu wata sauran Alaƙa a tsakanin mu , manzon Allah yace mu guji munanan abokai, mu mu'amalanci mutanen kirki ," kai baka chanchanta ba Youssouf      Ƙwallar da ya kamata ta zubo tun watanni da suka gabata amma rashin samun damar kukan ya hana ta zubowa tare da taurin rai irin na soja gami da jin kai na jinin sarauta ita ce yau ta silalo ,      A hankali ya zauna a bakin gadon , bai yi aune ba ya fara kuka shaɓe-shaɓe da hawaye kukan nadama kukan tsanar kai kukan neman mafita ,"   Share shi Tafeeda yayi tare da cigaba da haɗa kayan sa tsaf ya ɗaura agogon sa gami da ɗaukar ƴar jakar sa na matafiya,      Kallon Youssouf ɗin yayi , Zuciyar sa ta raunana , ganin hawayen sa abune da tun zamanin ƙuruciya rabon sa da gani , kai zai iya ƙirga yaushe da yaushe ya ga kukan Yarima Youssouf tun a ƙuruciyar su , to ɗan sarki ne , ɗan gata yarima , da kowa tattalin sa yake ,  a yau ya san cewa zuciyar sa ta luguiguita matuƙa da har ya kawo zubar hawayen sa a karon farko cikin shekarun girman su ,     Ƙauna ta haƙiƙa irin ta shaƙiƙan aminai ta taso , ji yayi bazai iya tafiya ya bar shi ba ya zama dole ya tsaya su samar da mafita , kamar yadda suka saba tallafar junan su idan wata maysala ta riski ɗayan su kome girman ta ko ƙanƙanta,    Ina yarinyar take ?wanne hali take ciki ? Ina cikin jikin ta ? Gaba ɗaya martabar gidan sarautar maraɗi na cikin barazana , ! Dawowa yayi ya zauna a gefen sa gami da kautar da kai ,"      Sai ka faɗi wanne yunƙuri kayi wajen neman gafarar ubangiji gami da nemo yarinyar tare da wanke kan ka , ka fa sani Yarima Youssouf ɓacin sunan ka daidai yake da zubewar martaba da ƙimar mahaifin ka "Maimartaba," tare da gaba ɗayan masarautar mu ,"   A yau Yarima shi ya koma tamkar bawa da ake ba umarni babu ja ya shiga bawa Tafeedah labari tun daga ranar da kome ya fara wanzuwa a tsakanin su irin mawuyacin halin da ya shiga akan ɗiya mace a lokacin da yadda kome ya cigaba da gudana har zuwa ranar da ya tafi ya bar ta ," Tsumu Tafeeda yayi yadda yake zaton kome ba haka ya ji ba , tabbas ya san Youssouf bai yin ƙarya da garaje , yayi zaton da son ran sa ya aikata kome , amma a yanzu da ya saurati bayanin bakin sa idan kuwa gaskiya ne tabbas akwai lauje cikin naɗi ,"   Ya zama dole a nemo yarinyar nan tare da cikin jikin ta ," domin mu samu tabbacin abun da ke cikin ta bashi alaƙa da kai , domin kai ma baka tabbatar ba , bani fatan ya zam naka ne ,"   ya kuma zama dole ka gyara kuskuren ka ɗan ouwa kamar yadda kayi niyya nima ina goyon baya ɗari bisa ɗari ka taimaki rayuwar yarinyar nan son samu ...ka aurar ta ga wani !   Basu gushe ba suna tsara yadda lamura zasu musu sauƙi wajen samun ta har dare ya shiga , nan suka bar duk wani shirin su zuwa gobe ,"       ****    9pm Doctor Hamza ya kammala duk wani shirin sa da ya ɗau tsawon kwanaki goma yana yi kafin rubuta hutun ƙarshen shekara da yayi na tsawon sati shidda da zai fara daga gobe , Kamar yadda ya tsara a goben zai bar garin zuwa zaria inda yake so ya ƙare hutun nasa a chan Jami'ar Ahmadu Bello , sashin horas da likitoci inda ya ƙirkirawa kan sa wani guntun shiri na faɗaɗa

Chapter 40 of 111