Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
duk dadbare-dadbaren datti ,ga manyan tsagun faso da datti ya samu mazauni na dindin-din wanda idan aka kwatanta da kafar samy baby da take a wanke a goge sumul-sumul tashin farko za'a fahimci baiwa ce da uwargijiyar ta , dan haka yayi tunanin yakakan wani laifi tayi wa samy take hukuntata ," sai dai duk da haka yaji haushin samy saboda shi mutum ne wanda sam baya son zalinci ," take yaji ya tsane ta , Ɗago idanun sa yayi ya sauke su akan fuskar samy baby wacce idanun ta da hankalin ta baki ɗaya yake kan "ɗan itaciyar ta nuhu "😁 da sauri yakakan ta wuce lokacin da ta ji samy ta janye kafar ta tare da yin gaba ,"  Kichibis tayi da madam saly wacce ta sawo kai kallon ta sama da ƙasa madam.saly ta jefa mata," yanzu yaks dan ubanki ban baki kayayyaki nace ki daina yawo cikin waɗannan shegun tsunmokaran ba , ace tsawon sati kenan yau da kuka fara zuwa min nan amma shegu ƙazaman banza kullum da daƙalkalallun kaya ɗaya? Kalen ku dunga sa min kostomomi amai ? Kuna yawo yarkace yarkace uwa sabbin  mahaukata ? A haka waye zai karbi abun hannun ki ya shaa ? Aaa ah ku ji min shegiyar yarinya zata min kashin kasuwa ta janyo min hasara ? Toh dan uwarki wuce maza ki je ki sauya kayan nan kamar yadda ƴar uwar ki ta sauya nata ,'idan ba haka ba a bakin aikin ki kin ji ko baki ji ba ? Da sauri yakaka take gyaɗa kai daga inda take rakaɓe ," Sake ɗaga kayan yakaka take tana jujjuya su tare da ɗora su a jikin ta tana gwada tsawon rigar wacce take ƴar ɗigil da kaɗan zata rufe mata cibiyar ta da ƴan guntayen hannu maƙale hammata , tare da ɗan siririn siket ɗin da ya shaa tsagu a gefe da gefen sa har fiye da rabin tsawon siket ɗin , Niyyar ta ta kaiwa falmata a ɗinke mata wuraren da suka yayyage a tunanin ta ," sakamakon ganin kayan ƙanana ne tunanin ta sun ɗangale mata ,  dan haka ta yanke shawarar kaiwa ƙanwar ta ," duk da tayi tunanin kayan zasu matse falmata kasantuwar ta ɗan fi ta kaurin jiki ," gefe guda na zuciyar ta tana jin zata fi samun farin ciki idan falmata ta samu sauyin sutura fiye da karan kan ta ," Zabura tayi tare da fara kokarin zare kayan jikin ta sauya , jin motsi da tayi yana nufo ɗakin da yake zaman mallakin ƴan aikin madam saly a nan masu kwana a gidan suke kwana su kuma da suke yini su tafi anan suke cin abincin su , ita da yagana da suke duddungura sallalolin su suyi sallah a ɗakin ," domin bayan su babu wacce ta damu da sallah cikin sauran ma'aikatan manyan su da yaran su da tsoffin su ," Juyowa tayi bayan ta sanya rigar a zaton ta madam saly ce ta leƙo ta ga koh ta shirya ," Karaf suka haɗa ido da ɗanliti wanda ya ɗaga labulen bayan ya tokare hannayen sa da jikin kofar yana ƙare mata kallo da jajayen idanun sa da suke cikin maye ," A firgice yakaka ta rarumi chukuikuyayyen hijabin ta ta suturta jikin ta ", tsaki ɗanliti ya jaa tare da ƙarasa shigowa ɗakin .,'    Aikin banza da wofi toh yarinya meye zaki boye min iyee ? Baya koh gaba ?? Baya dai kin san nima ina da shi , gaban ma idan naƴi niyya zan taso su ehe ,"     Jin tayi shiru ya sa ɗanliti buga tsaki dai-dai lokacin da yake zama a gefen wata yamutsatsiyar tsohuwar katifar da take yashe cikin babban ɗakin ,"     Ƙwaila ma irin ki me zan gani a wannan busasshen jikin naki da bana zaton koh nonon kirki kina da shi ," duk abun da zan gani na riga na gani a jikin jigajigan manyan mata ƴan uwana ," ya ƙarashe zance yana wani jijjiga da girgiza gwangonin kirjin sa da yake a bushe ƙaranbau," Raɓar jikin bangon yakaka tayi bayan ta sunkuya ta ɗauki tsohuwar rigar ta da sabon siket ɗin , ta suɗaɗa ta fice a ɗakin tare da nufar bayan gida domin ta sa siket ɗin ," Bayan ta ya bi da kallo ,"    Wai sunan wata kalma", Luwai ," yau naga ƴar kauye da lafiyayyar farar fata luwai-luwai,"ji yadda fatar ta take sheƙi da wani ɗan uban su fari na ainahi babu algus irin na su madam saly ," yarinyar nan idan ta samu hutu tabbas zata jaa gayu ahaayyee ,"gwara da babu ni a harkar ƴan maza ai da ganin da nayi wa bayan yarinyar nan da ace ina harkar maza da yau babu zaman lafiya,." Da raɓe-raɓe ta fito daga banɗakin tana tafe tana sake sauke siket ɗin ƙasa-kasa sakamakon tsagun sa da yake har ya zarta gwuiwar ta , Wurin karɓar burkutun suka haɗu ita da yagana da tun safe madam saly ta sata gyara mata cikin ɗakin ta ,"amma tsabar shirgin da yake cikin ɗakin bata samu damar kammala gyaran ba sai yanzu ," Kallon kallo suka yi da ita da yagana wacce ita ma take tsuke cikin sabuwar shigar da madam saly ta bata na wani chasasshen wondon jins da yake a ɓarƙe ta wurin cinyoyin sa da wata ƴar ɗangalalliyar riga mai siririn hannu ," fuskar yagana ta kalla kawai ta fahimci ita ma tirsasa ta madam saly tayi ,ta sa ta sanya kayan a dole kamar yadda tayi mata ," Ba wacce tace ga ƴar uwar ta ƙala suka ƙarbi manyan farantan silver da larki da hema suka ciccika musu ruwan burkutu a kofuna tare da jerawa akan farantan ," Tana shigowa ƴar rumfar ta doshi gurin da ɗazu wasu mutane biyu suka bukaci ta kawo musu burkutun dayawa ," Turus ta yi lokacin da ta tadda kujerun da ta bar su akai wayam babu kowa ," Ɗan waiwayawa tayi tana dube-duben wurin da zata hango su ,ga zaton ta kou sun sauya waje ne ," Sai dai jajayen idanun mazan da taci karo da su suna kallon ta ya sa nan take ta diririce saura kiris ta saki farantin hannun ta ,"fiye da rabin maxan wurin kallon farar doguwar yarinyar da take sanye cikin jaan yadin da ya sake fidda kyau tare da hasken fatar ta suke," giyar da suka shaa suka yi tatil tana sake ƙawata musu tare da girmama musu sassan halittar jikin ta daga yar ƙanƙanuwar yarinya zuwa cikakkiyar babbar budurwa ," nan take suka fara kawo mata wawura da chafka cikin tamɓelen su na mashaya,"  Zilliya da zamiya ta haɗa Allah ya bata ikon tsalleke farmaƙin da suke kawo mata , " dan haka gudu-gudu ta maida tiren burkutun tare da shaida wa larki, masu neman burkutun sun tafi . Ganin lokacin tashin su ya riga yayi "karfe biyar tayi " ya sa ita da yagana suka nufi ainahin cikin gidan inda anan ɗaki da falo gami da banɗakin madam saly yake ," Suna isa kamar kullum iwar haka suka tadda cikin falon nata a cike da manyan ƴan matan da suke ji da kan su ire-iren su samy baby ," sai karta suke da cha-cha suna yi suna haɗiyar ƙwayoyi tare da kora ruwan maganin mura da yake mahaɗin ƙwayar da suke sha ," Madam saly tana daga gefe zaune tsakanin wasu manyan Alhazawa biyu da alama wata magana mai muhimmanci suke yi ," Ɗan rakuɓewa suka yi daga bakin kofar a durkushe sannan suka sanar da madam saly lokacin tafiyar su gida yayi ,"   Kallon hadarin kaji madam saly ta watsa musu kafin ta balbale su da masifar basa ganin tana tare da baƙi ne ? Su waɗanne irin wawaye ne ? Hakuri suka bata tare da cigaba da tsugunno nan bakin kofar suna jiran ta ta kammala da bakin nata ," Sai da aka kwashe fiye da mintuna arba'in har duhu ya ɗan fara shigowa karfe shidda ta gabato , zuwa lokacin kuwa har kafafuwan su sun sage duk sun muzanta tsabar gajiya .," Sai da suka kammala maganganun da su basa iya jin me suke faɗi daga inda suke a sakamakon hayaniyar da take sake cika illahirin da'irar wajen ," basu ankara ba suka ji ta watso musu kuɗin aikin nasu ,"   Ga shi nan ,' ku tabbatar gobe kun zo akan lokaci sannan ku tabbatar baku dawo min nan wajen da waɗannan shegun tsunmokaran kayan naku ba ,"  idan kuwa kuka yadda kuka doso min nan wajen da wannan shigar taku uwa masu kwana akan bola toh kuwa a bakin aikin ku ," ni bana son ƙazanta ,"ta karashe zancen tana jawo wata jakar bagco ta tura musu a gaban su ," ga kaya nan kowaccen ku shiga bibbiyu da su nake so na dunga ganin ku ," kun ji koh baku ji ba ???   Cikin sauri su ka amsa da toh ! Sauri-sauri suka haura tudu tare da barin unguwar suka tadda falmata wacce har ta fara gundura da jiran su tare da fara jin tsoron rashin dawowar su har zuwa yanzu da take jin hayaniya ta ragu a bakin kasuwar alamar an watse domin tun ɗazu baba modu ,"mutumin da take zama a gefen rumfar sa ," ya tattara kayan sa tare da sauke rumfar ta sa yayi mata sallama ya wuce gida ," Ajiyar zuciya ta saki a take fuskar ta ta yalwatu da murmushi sakamakon jin muryoyin su yakaka ,"    Yakaka yau kun daɗe a wajen aikin da fatan dai lafiya ? Dan har na fara tsorata . Kamo hannun ta yakaka tayi tare da sarƙafe yatsun su cikin na juna,   Lafiya lau falmata uwarɗakin mu ce yau tayi baƙi shiyasa bata sallame mu ba da wuri , kin ci abincin rana dai koh falmata ?   Naci gƴaɗar naira ashirin yakaka ," ta furta hakan tare da miƙa mata ɗaurin bakar leɗar da take tara kuɗin barar ta a ciki  ,"     Wannan karon yagana ce tace ,"    Gyaɗar naira ashirin ba abinci bace falmata ina ma laifin ki sayi koh ƴar awarar hamsin ,"ki daina zama da yunwa kullum muna faɗa miki ,ai yunwa tana daga cikin dalilin da yasa muka fito nema , toh me yasa zaki sake zama tare da yunwar bayan kuma akwai kuɗin sayan abincin a tare da ke ,"    Shiru falmata tayi ba tare da tace ƙala ba cikin ran ta kuwa tana sake kuɗurce niyyar cigaba da tara kuɗin barar ta , har sai ta samarwa da yakaka iya adadin kuɗin da zai isa ta jaa jarin kowacce irin ƙaramar sana'a ce da zasu iya dogara da ita ba tare da yakaka taje tayi aikatau ba ," Yakaka kuwa da ita ma bata ce kome ɗin ba idanun ta ne yake bisa kan wata mata da take soya doya da kwai daga gefen bakin tashar ," sakin hannun falmatan tayi ba tare da ta amsa tambayar da falmatan take yi mata ba na "ina zata" ? Ta nufi me sayar da doyar , ta miƙa naira ɗari daga cikin kuɗin aikin ta ɗari uku ,"ta ce a bata doya ," Kamo hannun falmatan tayi tare da zaunar da ita akan wani ɗan fasasshen buluk ta tsugunna ta buɗe ledar doyar tare da ɗaukar yanka ɗaya ta nufi bakin ta da shi ,"buɗe bakin ki kici zaman ki tare da yunwa barazana ce ga kwanciyar hankalina falmata , babu amfanin wuni da nake ina aikayau idan har ke zaki wuni tare da yunwa , alhalin kina zaune a bakin hanya cikin rana kina bara , na kasa baki kulawar da ta dace , rashin amfanina zai yawaita a gare ki falmata idan har ya zama na kara miki da yunwa daga yau kar ki sake zama da yunwa duk kuɗin da aka baki na sadaka ki daina ajiye ko sisi duk ki sayi abinci ki ci , ki  ƙara girma ki zama ƙatuwa ko bakya so idan mama ta gan ki ta ji daɗi tare da yaba min akan na kular mata da falmata mafi soyuwa agare ta cikin ƴaƴa ??", Tun da ta fara maganar take taunar doyar da ta sanya mata cikin baki tana murmushi , kammala maganar ta ya zo dai-dai da fitowar ƴar siririyar dariyar da tayi jin an ambaci kalma mafi daɗin sauraro agare ta watau " dawowar mahaifiyar su"      Nagode yakaka a kullum ina alfahari da yawan ƙaunar ki gareni ina kuma rokon Allah nima ya bani damar da zan nuna miki kulawa koh da bata kai yawan wacce kike min ba ,Allah ya bayyana mana mama tare da su baana cikin ƙoshin lafiya ,"   Su duka suka amsa da ameen har yagana da take kallon su cikin sha'awar yawan kaunar da suke yiwa junan su ," A gijiye likis suka dawo sansanin nasu amma hakan bai sa ,"fanna da ajus sun tsahirta musu ba domin tamkar jira suke su sanyo kafafun su cikin camp ɗin su tare su da lodin aiyukan su da ƙyuiya tare da sanin cewa akwai waɗanda suka maida bayun su ya sanya suka ƙi motsawa suyi aikin ," Da ɗibo ruwa da suka tadda an tada injin yamma kenan suka fara , kafin yakaka ta ɗora da wankin kayan yaran fanne na kashi da fitsari , ita kuma falmata ta tafi aiken da ajus tayi mata wurin saurayin ta wanda shi ma a cikin sansanin nasu dai yake amma yana ta bangaren maza da yake chan-ciki inda tantunan maza yake ," Wannan shine karo na huɗu da ajus take aiken falmata ta karbo mata kuɗi koh kuwa ta tambayo mata saurayin nata kou zasu samu damar haduwa a wannan ranar idan dare yayi ," wanda ita kuma sam falmata bata son zuwa wurin tantunan samarin saboda wani da bata kai ga sanin sa ba da yake biyo ta a baya ta tsakankanin manyan bishiyun darbejiyar yana taɓa mata jiki ," yana faɗin wai tsarin jikin ta tun tana ƙarama yana da kyau ," Sai dai tsoron ajus ya hana falmata tayi wani yunƙuri na samarwa kanta damar kaucewa zuwa aikin , Cikin sanyin jiki ta kama hanya bayan ta biya ta sanarwa yakaka wacce take ta faman gurzar wanki ta gefen ɗakunan su duk da duhun dare da ya riga ya shigo domin har an idar da sallar magariba ina shirye-shiryen yin isha'i amma su koh sallar magaribar ma basu samu damar yi ba kamar yadda a yawancin lokuta haka take faruwa sai dai su haɗa magariba da isha'i suyi tare , abincin dare kuwa ba kullum.suke samun damar ci ba saboda ana idar da magariba ake zubo shi a daka wawaso kamar yadda aka saba , su kuwa a mafi yawancin lokuta basu kammala aiyukan bautar da ake basu ba ,"dan haka zuwa yanzu sai rana ɗaiɗaiku suke cin abincin sansanin kuma basu wani damu sosai ba sakamakon suna da ƴan kuɗaɗen su a kulle ," kou yagana da take take da damar cin abincin ma bata cika shiga cikin turmutsutsun ayi kokawar ɗibar loma da ita ba , a cewar ta daman dole ne ta sa take cin wannan cinkusasshen abincin marar daɗin ɗanɗano ," Tafe take tana juya jikin ta a hankali kamar yadda yake halittar jikin ta , duk da ƙarancin shekarun ta  da yanzu ne ta fara fidda alamun budurci ," amma haka halittar ta take irin matayen da suke da maɗaukakin kyaun diri da ɗan madaidaicin tsawo ," tafiya take cikin nutsuwa baza a taɓa zaton makauniya bace ," saboda yadda take tafe babu ɗan jagora kuma babu sanda sai dai lokaci-zuwa-lokaci ta kan ɗan lalubi hanyar wanda hakan yake babbar baiwar da Allah ya yi mata , tana daga cikin makafin da Allah ya basu ikon gani da zuci , wanda kai tsaye baza'a kira hakan da gani ba domin ba ganin suke ba sai dai wata irin baiwa ce da ɗaukakar ubangiji da ya yi musu daga kwakwalwa zuwa zuciyar su ," Ta tsakanin dattin ganyen bishiyar ta ratso har ta bullo a gaban tantunan da suke duk a rurrufe saboda ɗan sanyi sanyin damina uwa uba tsoron kar muggan ƙwarin damina su buwaye su , " Tsayuwa tayi a dai-dai bakin tantin da take hasashen nasu saurayin ajus ɗin ne tare da yin sallama cikin maɗaukakiyar murya ta kwala kiran sunan sa kamar yadda ta saba ," Daga ciki ya jiyo tare da shaida muryar ta nan take ya fito , nan ta isar masa da sakon ajus ɗin da take tambayar neman sanin kou yau zasu haɗu su zanta ? Inda shi kuma ya faɗawa falmata ta sanar da ita shi yau bai jin daɗi . Tana kammala jin amsar sa ta juya tare da nufar hanyar komawa , signal saurayin ajus yayi wa wani saurayi ɗan uwan sa da yake tsaƴe a gefe wanda kuma tare suka fito daga tantin ," shafa shukurkuɗaɗɗan daddauɗan gemunsa daya saurayin yayi lokaci guda suka yunƙura tare da rufawa falmata wacce ta ɗan fara nisa daga da'irar su ," Ta cikin takun su da yake sauka akan busassun ganyayyakin ta fahimci akwai mutane fiye da ɗaya a bayan ta wanda bata kawo hakan a zuwan wani abu ba cikin ranta ," Cigaba tayi da tafiyar ta , sai dai kome ya tsaya mata ne lokacin da taji anyi sama da ita an ɗaga ta cak lokaci guda ana me sanya hannu a toshe mata bakin ta , kafin taji an  zura da gudu da ita zuwa wani bigire da bata san ina bane duk kuwa da wuntsil-wuntsil da ƙoƙarin sauka da take daga kafaɗun wanda ya ɗaga ta da bata kai ga nasarar saukar ba  ,," sauke ta aka yi akan wani abu da tashin hankalin bai bari ta fahimci menene ba , kafin kuma tayi aune taji an fara ƙoƙarin raba ta da suturar ta alhalin bakin ta yana danne cikin hannunwan wani daban , an hana ta damar ihu , wani irin bugawa zuciyar tayi tamkar zata fashe lokacin da ta fahimci mummunan nufin da suke son aiwatarwa a gare ta ," Bugawar zuciyar ta ya zo dai-dai da na yakaka da tata zuciyar ta fara sauya salon aikinta tun daga barin falmatan gaban ta zuwa yanzu da zuciyar tayi mummunan bugawa, " zuruf ta miƙe tare da zare hannun ta daga ruwan wankin ta kai hannayen nata duk biyu ta dafe kirjin ta ,"......! #Fikrh #umm'muaz #son so [6/24, 10:57 AM] +234 701 013 7848: Fikrah writers association MAFARI ........ ( Hargitsin Rayuwa....) Umm'muaz 15 Dafe da kirjin ta da yake cigaba da bugu ta nufi hanyar da zata sada ta da ɗakunan kwanan mazan sansanin su , domin haka kawai ta ji hankalin ta bai kwanta ba da rashin ganin ɓullowar falmata har yanzu dan haka ta tafi domin ta taro ta su dawo tare,' Sai dai har ta cimma ɗakunan bata ga falmatan ba , sai tsirarun mutane da suke giftawa ta cikin duhuwar ," turus ta jaa ta tsaya saƙe-saƙe ta fara yi a zuci ,"    Toh ina falmata tayi ?    Koh dai ta koma ɗakin su ne wurin ajus ? Ganin bata ga koh alamar ta ba kuma ga shi babu wadatar kafafun mutane a wurin bare ta cigita , ga kuma duhun dare da take tsorace da shi , sai ta juyo gami da kamo hanyar komawa da nufin zuwa ta duba ɗakin su falmata , A sanyaye take taku saboda har yanzu zuciyar ta bata bar tsinkewa ba sai ma ƙara dukan uku uku da take yi ," Bata yi nisa ba ta tsinkayo wani rishi da alamun fitowar kukan da aka ƙi bada dama ya fito ,' kiƙam ta jaa ta tsaya tare da sake kasa kunne lokacin da ta sake jin irin rishin ," a firgice ta juya laɓɓan bakin ta suna furta sunan ,"Falmata" Tayi diri-diri cikin rarraba idanun ta a kewayen wurin ,tana neman inda zata gan ta domin tabbas kunnuwan ta muryar falmata suka jiye mata ," Cikin rashin sanin gaba zata yi ko baya ta taka da gudu tare da hawa kan barandar wasu tsoffin ajizuwan da suke gefe da ita waɗanda kou rufi babu a kan su ta wasu wuraren ma sun fara zaftarewa da alamun sun zama kango ," Da gudu take shiga cikin ajizuwan  tare da kwala kiran sunan falmata , sai dai bata tarar da kome cikin ajizuwan sai tarin bola tare da yanar gizo-gizo da tayi dafifi a ciki , cikin tashin hankali ta jaa ta tsaya daga karshen barandar da take daf da katangar makarantar , daddagewa tayi ta sake ƙwala kiran sunan falmatan , sai dai bata kai ga rufe bakin ta ba taji an ɗauke ta da wani kakkarfan mari , kafin ta farga taji an shatile kafufuwan ta , ta tafi ta baya ta faɗi ƙasa tare da bige ƙeyar ta da katangar  makaranta , zuruf ta miƙe bata koh ji alamun zafi ba lokacin da tashi sautin muryar falmata ya fito tar cikin wani irin kukan wahala tana ambaton sunan ta a kurkusa da ita ," Taku biyu ta ƙara ta ci karo da ita a kwance cikin tarin busassun ganyayyakin da ake sharewa a tara a wurin ya zamto tamkar bolar zuba ganye ," Ɗago ta tayi ta tarairayo ta tare da rungumo ta zuwa cikin jikin ta tana yi tana waige-waigen jin ta inda waɗan da suka bige ta zasu bullo wanda take da tabbacin sune suke shirin cutar mata da falmata cikin ran ta tana jin karfin yin ɗauki ba daɗi da ko su waye domin ta tseratar da falmata ," Tunanin ta ya tsaya chak ! Lokacin da ta ji gaba ɗaya kukan da falmatan take yi ya gauraye da wani irin numfashi tamkar na me shiɗewa , jijjigata ta fara yi tare da kokarin tayar da ita tsaye ,tana cewa        "sannu falmata me suka yi miki ? Duka ? Kin ji ciwo ne falmata tashi muje ki shaa ruwa ," Rinjayar ta falmatan tayi a domin ta gaza tsayuwa sakamakon numfashin ta da yake sarƙewa , su duka biyu suka zube ragwaf a ƙasa kafin falmata tayi baya lau ta tafi zata kwanta cikin sauri yakaka ta riƙo ta kwakwalwar ta na son fahimtar me ke shirin faruwa da ƙanwar ta ? Jijjigata ta fara yi cikin zubar hawayen da suka balle sakamakon tashin hankalin ganin falmatan a kwance bata motsi sai wani irin shiƙar numfashi take ,"   Cicciɓar falmatan take son yi amma ta kasa saboda tayi mata girma da nawi baza ta iya ba , kwantar da ita tayi ta taka da nufin zuwa ta kira mutane su taimaka mata , har ta yi taku biyu a gigice ta sake juyowa , zuciyar ta na bijiro mata da hoton gawar mahaifinta da ta bari a wuri makamancin wannan cikin "gona babu kowa ," Da gudu ta taho gami da sake durƙusawa tare da ɗago falmatan da dukkanin karfin ta , ta rungumo ta a kirjin ta , ta yunkura da kyar ta miƙe gami da ciccibar falmata da jikin ta yake a sake bata motsi , kiki-kiki ta fara kokarin jaan ta ta tafi da ita , sai dai kou taku uku mai kyau bata yi tayi tuntube da wani ɗan kankanin dutse ta baya kafar ta ta zame takalmin ta ya tsinke , suka tafi baki ɗaya suka faɗi ta baya kan falmatan ya bigi haɓar ta nan take hakoranta suka datse laɓɓan ta na ƙasa ya fashe ," Da hanzari ta sake sunkuyowa kan falmata hawayen ta na ɗiga akan fuskar falmatan ta ɗago ta ta fara jaan ta cikin sautin kuka ta fara ƙwalla kiran naiman taimako , domin zuwa yanzu ta fahimci mutanen da suka jefa ƙanwar ta cikin wannan mummunan yanayin da zuciyar ta taki aminta da falmatan ta mutu kamar yadda ta ga alamu , mutanen sun gudu basa wajen ," Da faɗuwa da tashi ta fiddo ta tsakiyar hanyar da ake wucewa , sunkuyowa tayi tare da tallafo kan falmata tana cigaba da

Chapter 15 of 111