Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da yayi mata da ta saka masa da tarin butulci ,? Da har kuma yanzu zata ɗebo ƙafafu ta zo gidan su to a matsayin wa take ? Kuma gurin wa ta zo ? Har ta gama barikin ne ta gaji ta dawo ? Zaton ta nan matattarar karuwai ne ?  Ko kuwa har auren nasu da uban ƴar ta ta ya ƙare ne ? Dole ta bar gidan kamar yadda tayi a baya,  tayi nesa da shi da dangin sa domin mumini ai baya sanya hannun sa a ramin Macijiya sau biyu . Ba zai taɓa saurarar ta ba , ita ɗin zantukan bakin ta ai duk ƙarya ne , da yaudara , kirkin baka ne da ita tare da ladabin banza . Runtse idon sa yayi yana tura ƙofar sashin sa da ƙarfi , ɓacin ran ganin ta yana sake hauhawa a ran sa hatta yunwar da yake ji tayi ƙaura . ,"Rahima dole na tafi tunda Yaya Dakta ne da kan sa ya kore ni kin manta shi ne ya fara kawo mu ? Dalilin sa muka zo gidan ku Rahima bani da ikon cigaba da zama ," Yakaka ta furta hakan tana shiƙar kuka lokacin da take jawo jakankunan kayan ta , Kukan ta daga ƙasan ran ta yake , kukan tausayin rayuwar ta tare da nadama ,   ina zata je ? Tun zamantowar su 'yan gudun hijira nan gidan ne kaɗai mafakar da suka tsaya cikin ta ba tare da ƙalubale ya cisgesu ba har sai da ita da ta sanya kafafun ta da kan ta ta bar mafakarta , Tayi zaton kome zai zo mata da sauƙi zaton ta zai yi saurin yafe mata , tayi tunanin zai tare ta da yawan ƙaunar nan tare da tausayin da ta san yana gwada mata can baya , har ma tana sanya ran cigaba da samun kulawar sa kamar farkon fari , Ashe dama ta riga ta kufce mata , ta riga ta ɗibga kashi a inuwar da ta huta , ashe ita ɗin yanzu wulaƙantattace a wajen sa ? Ashe yanzu ita abun kƴamata ce da bata wuce a kore ta ba ? Babu shakka ba'a ɓari a kwashe du , hangen hadarin nesa kuma ya sanya ta damal-malewa cikin kashi . Ɗauki take nema , so take ta samu wanda zai dube ta ya fahimce ta ba tare da ya aibata ta da laifin da ta riga ta aikata ba ,  ba tare da wani hukunci yayi tsalle kan ta ba sakamakon abunda ta aikata da bai wuce Kaddarar da zata iya hawa kan kowanne ɗan Adam ba . Malama Maryam ita ce ɗaya jal wacce ta sani da tashin farko bayan sanin laifin da ta aikata ta tausasa mata , a yanzu kuma bata nan , tayi komawar ta garin su tun kwanaki biyu da suka wuce . Shin Mutane ba za su mata uzuri ba ? Ashe haka halli  'yan adam yake ?? Da wanne zata ji ? Ita kenan haka guguwar Rayuwa zata cigaba da walagigi da ita ? Yanzu ina zata ? "Kar ki tafi Yakaka  tsaya ina zuwa . Rahima ta katse ta bata tsaya jiran amsar ta ba ta fita da ɗan gudun ta , bata tsaya ba , ta cigaba da jan  baccon ta da yafi ƙarfin kinkimar ta , tana yi tana rera kuka da murya mai ban tausayi . " Yakaka , Yakaka ki tsaya , kar ki tafi nace ki zo Baba yana ƙiran ki .' Kanta a ƙasa tana sharar ƙwalla ta shiga falon Prof , da ta tadda shi kamar koyaushe a zaune , muddin zai miƙe tsaye sai da sanda mai ƙarƙo . Muryar ta tana rawa ta gaida shi , ya amsa yana nazarin ta , ," Me ya faru zaki bar gida 'yata ,?  meye dalili ? Muryar ta na rawa tace "Yaya dakta ne yace na tafi  . Ya gane wanda take nufi dan haka ya ɗan yi jim cikin ransa yana sake ganin dai-dai kan ƙudirin sa . "Ki koma ciki , nan gidana ne ba na wasu ba , dan haka babu wanda yake da damar korar ki , kin ji ko ? ',To Baba , nagode ," ", Madallah ku koma ciki ,' Bayan tafiyar su ya ɗau wayar sa tare da ƙiran Doctor Hamza wanda tunda ya shiga sashin nasa ya gaza aikata kome illa kai-kawo da yake yi , zuciyar sa na cigaba da tafasa , Bayan ajiye wayar sa , sashin Prof ya tasamma , inda ya tarar da shi yana  tsimayen sa , bai saurari gaisuwar da yake yi masa ba , ya fara da tambayar sa fuskar sa na nuna ɓacin rai "Me yarinyar nan tayi maka zaka kore ta ? Da sauri ya ɗago kan sa yana duban Baba , a zaton sa yau ta zo , sannan Baba bai ma san da zuwan ta ba , ashe ba haka bane . Shin ƙarar sa ta kawo ? Babu shakka babu kome a bariki sai darussan da ke koyar da tsaurin ido tare da rashin kunya , Shiru yayi , ganin yayi shiru ya sa Prof  sake jefa masa wata tambayar "Ko kuwa ta aikata wani abu da ba dai-dai bane ? Ko tana kan aikatawa da ta cancanci kora ? Shiru Doctor Hamza ya sake yi , kai tsaye ba zai ce ga abunda ya hana shi ya ce kome ba , Bazai ce ga dalilin da yasa ya gaza bayyana laifin ta da yake sirri ne a gurin sa wanda yake tunanin a iya tsakanin su biyu yake,  da kuma can inda tayi rayuwar bariki , sai dai hankalin sa yafi tafiya akan ya rufawa ƙaryar sa da yayi a baya asiri ne,  sanin da yayi Ƙarya wata mummunar ɗabi'a ce da iyayen su suka wanzu suna hanin su da aikatawa , "Idan baka da wani dalili ,kar ka sake korar ta , ita ɗiya mace rauni ne da ita a koyaushe , a kuma ko'ina tana buƙatar matallafi ne cikin rayuwar ta , ' " Wanda daga zarar ta rasa mai tallafar ta zata iya faɗawa kowacce irin mummunar rayuwa  , yan gudun hijira su ma mutane ne kamar kowa walaƙanta su abune marar kyau , ka kiyaye . "Zan kiyaye Baba , *** Yakaka tana komawa cikin gida bayan Rahima ta kama mata kayanta sun mayar su ɗakin da cikin sa suka  zauna ita da Falmata tun farkon zuwan su gidan , muryar ta a ɗan dishe ta ce   " Rahima yaya Dakta fa yunwa yake ji , da farko da ya shigo yace ki masa girki ,   Zama Rahima tayi a bakin gado tana ɗan riƙe kanta ,   "Yakaka wallahi kaina ciwo yake ba kaɗan ba , yau nasha yawo a School ( makaranta ) taimaka ki ɗan dafa masa ko ƴar indomie ce . Bata ƙarasa zancen ba yakaka ta nufi ƙofa , tana amsawa da "To yanzu zan yi ," Bayanta Rahima ta bi da kallo cikin ranta tausayi ne me tarin yawa , Yakaka mai kirki ce kaddarar Rayuwa ce ta faɗa mata ta dalilin raunin Ilmi da wayewar ta . Ita da aka ce ta dafa indomie sai ga ta ta zage damtse wajen girka lafiyayyar jalloup ɗin Spaghetti da ta sha niƙaƙƙen nama da kayan ɗanɗano , cikin sauri da azama take aikin dan haka bata ɗau ɗogon lokaci ba ta kammala , ta tafasa shayi ( tea ) da ya buƙata ta adana su a mazubi me kyau ta ɗora bisa ɗan faranti , Zuwa tayi ta samu Rahima tana bacci , bata son tashin ta domin kar ta ƙara mata ciwon kai . Dan haka ta fita daga ɗakin ta koma kitchen tayi tsumu a tsaye hankalin ta ya rabu kashi biyu , tunanin Dakta da yace yana jin yunwa da kuma tsoro da take ji na kai masa abincin , Tayi tsayuwar kusan mintuna uku ta gaza ɗaukar abincin kafin daga baya ta gyara zaman hijabin ta ta ɗau tiren tare da nufar sashin nasa da ba baƙo bane a wajen ta , Cikin sanɗa take tafiya lokacin da ta shiga sashin nasa a yunƙurin ta na son ta shigar masa da abincin ta fita ba tare da ya san ita ta kawo masa ba , Ta zo dai-dai ƙofar tayi tiris ganin ƙofar shiga falon nasa a rufe , ajiye tiren tayi , tana tunanin yadda zata yi ? Wata dabara ce ta faɗo mata , dan haka ta ɗan sauƙe ajiyar zuciya kafin ta kai hannu ta ƙwanƙwasa ƙofar da ɗan ƙarfi , tayi wuf ta juya da saurin ta , garam ! ta ji tayi karo da mutum . Da sauri ta ɗago kanta ganin fuskar sa a murtuƙe yana jifanta da mummunan kallo ya sa ta haɗiyar yawun tsoro , ", Un- um daman Yaya Dakta abincin ne , Un Rahim.. ,"Wuce ki bar nan bana so na sake ganin fuskar ki . Yace da maɗaukakin sauti , Sum-sum ta ratsa ta gefen sa da yayi banga-banga yaƙi matsawa tamkar mai shirin jibgar ta ta bar wajen har tana haɗawa da ɗan gudun ta bayan matsanancin bugu da zuciyar ta ke yi . Sanin darajar abinci ya sa shi ɗaukar abincin da ta kawo masa ya shigar da shi falon nasa ya zauna tare da ajiye ledar da ya sayo abinda zai ɗan ci , Dafadukar shinkafa ce irin wacce aka cika mata ƙaƙale da launi ruwan ɗorawa shar ,  da ya taka takanas zuwa shahararren gurin sayar da abinci da ake ji da shi a garin ya sayo . Loma ɗaya-biyu yayi yaji abincin bai masa yadda yake so ba , sam shinkafar ma bata dahu sosai ba a bakin sa , shi yafi son yaji abinci ya dahu sosai ko shinkafar ce yaji ta suɓut-suɓut tuɓus-ɓus daɗin tauna , ba irin wannan dahuwar ƴan gayun ba,  da yake hasashen rabin shinkafar sai dai ta ƙarasa dahuwa a cikin sa . Rufe abincin yayi ya ɗan ture gefe , yayi jugum a zaune , yana tunanin matan zamanin gaba kamar nan da shekara hamsin anya za'a iya cin girkin su ? Ko Amne da take ba tsohuwa tukuf ba salon girkinta ya banbanta dana yaran mata irin su Hafsa, zainab ,Rahima a bar batun Safiyya wannan ba abunda tafi ƙwarewa akai irin Kwaɗon ganyen salad da take cin sa kamar me . Ɗan satar kallon girkin da Yakaka ta kawo yayi ta wutsiyar idon sa , tsaki yayi tunowa da yayi duk kanwar dai ja ce da girkin su Rahima da na wannan da ya raina dahuwar tasa  . kasa jure yunwar da take sasuƙar sa yayi dan haka cikin yanayin,  ya na iya ?  Ya ɗauko tiren abincin zuwa kan teburin gaban shi , Sai dai Yana ɗora ido akan abincin ya haɗiye yawu , da sauri ya ɗau chokali yayi bismillah ,gami da kai lomar farko bakin sa , Bai saurara ba cikin nutsuwa ya dinga aikawa hanjinsa haƙƙin sa har sai da yaji cikin sa ya samu dai-dai da buƙatar sa sannan ya sarara , a fili yace ", Alhamdulillah wannan ko wacce irin pasta ce haka Rahima ta dafa ? Wataƙila ta zallar Alkama ce ba surki . *** Bayan Yakaka ta idar da sallah tayi addu'o'in da ta saba yi duk bayan sallar ta , Ta waiga ga Rahima wacce ta farka daga bacci "Rahima yaya ciwon kan naki ? Kin ji sauƙi ko ? " Ya ɗan sake ni Yakaka thanks , "Yakaka yawan ibadar ki na burgeni ga yawan addu'o'i da kike yi kin fa kusa mintoci ishirin kina addu'a , Yakaka me kike roƙa haka mai yawa ? Ko dai har da shi ake yiwa addu'ar , Ta ƙarasa zancen tana ƴar dariya tare da kashe idonta ɗaya na ɗabi'a . Ɗan zaro ido Yakaka tayi sai kuma tayi murmushi , "Rahima , Bawa baza'a tambaye shi me yake nema a wajen Ubangijin sa ba , Duk abunda nake roƙa bai wuce neman gafara da samun Rahamar Ubangiji ba gare ni da iyayena da 'yan uwa na ,   Jim tayi kafin ta cigaba da cewa , ,"Ummin mu , Rashin sanin a wanne hali mamana take tsakanin Rayuwa da mutuwa yana matuƙar tayar min da hankali Rahima , kullum roƙon Allah nake ya ƙaddara haɗuwar fuskokin mu , idan kuma ita ma ta rasu kamar Baban mu , ina tsawaita musu addu'ar samun gafara a wajen Allah . Hawayen da ya tsatsafo a idonta ta goge cikin ranta ciwo take ji na rashin iyayen ta . Cikin tausayawa Rahima tace , "kiyi Haƙuri Yakaka , babu shakka abune mai ciwo naka ya ɓata har gara ma ace mutuwa yayi kaga gawar sa aka yi jana'iza aka binne , kowa ma jiran mutuwa yake , " Muma akwai Auntie na takwarata ce sunanta aka sa min , ita ma ɓata tayi tun ma kafin a haife ni , "Amne tana bani labari lokacin tana da ciki na ,  Khaalty Rahima ta bar gida tana yarinyar ta yadda Amne ke bani labari bata ma kai mu shekaru a yanzu ba  , " tundaga lokacin Rayuwar gidan mu bata sake zama dai-dai ba , duk da bansan Ƙhaalty Rahima ba amma labarin kirkin ta da yadda Amne ke ƙaunar ta yasa nima ina sonta sosai , ina kuma so ta dawo wataƙila rayuwar gidanmu ma ta dawo mai daɗi , " Cike da jimami da tausayi Yakaka tace ,    " Allah sarki Khaalty Rahima Allah ya bayyana ki daga yau zan dunga saka ta cikin addu'o'i na .   " Nagode Yakaka , duk ranar da muka je gidan Amne tare zan sa ta nuna miki hoton Khaalty Rahima . Cikin zumuɗi Yakaka tace "  yaushe zamu je Rahima ? Ina so naje na gaishe da Amne . "Weekend ( ƙarshen sati ) insha Allah . " Allah ya kaimu , Rochester New York City Tafe Biyamuradi Youssouf yake akan titin 3rd Ave, jikin sa sanye da kayan sanyi daga ƙafa zuwa kansa da ya ɗora hular da take da laɓɓa biyu da suka rufe masa kunnuwa elmer fudd da aka fi ƙiranta da Trapper hat   . Hannun sa ɗaya riƙe da 'yar jakar takarda da ya sayo ( Hot chocolate ) mai dauke da tambari tare da sunan kamfanin chocolate and Vines a jiki , domin su ɗumama cikin su ɗumin hot chocolate ya ratsa musu gaɓɓai kafin su fita zuwa cikin asibiti nan da awa ɗaya mai zuwa , Cikin kwanaki biyar da suka biyo bayan zuwan su ƙasar Amurka zuwa ganawar su da likita da duk wasu bayanai da suka samu game da Cutar dake tare da Mama . Daga Biyamuradi Youssouf har Falmata sun rasa karsashi da nishaɗin su , musamman Falmata wacce tundaga wannan ranar take cikin damuwa da tunanin hanyar da zata iya bi domin ganin ta samar da abunda zai zama sanadi na samun warakar cutar Mama da sanyin ƙasar tare da sauyin ruwa suka haɗu suka sa ta ɗan fara kukan ciwo , Sai dai kasancewar nan Amurka ba kamar ƙasashen Africa da basu cigaba bane ta fuskar kula da lafiyar ɗan Adam . Cikin ƙanƙanin lokaci a rana ɗaya aka bata magunguna tare da duk wani taimakon da ya dace a ƙarshe likitan ya gargaɗe su akan kiyayeta daga wannan sanyin mai tsanani , dan haka ciwon bai tsananta ba ya lafa  . Kwanaki biyu Biyamuradi yayi yana tsara abunda ya dace na daga sabon kuɗirin sa , da tunda ya samu gamsassun bayanai daga bakin likitan Mama , Ya dangana da nema mata lafiya a yanzu domin babu damar yi mata dashen ɓargo ko juyen jini da zai iya bata waraka , dole zasu cigaba da haƙuri tare da kula da ita , tana shan magungunan ta har zuwa wasu shekaru nan gaba da za'a samu wani cikin 'yan'uwan ta da zai isa sadauƙar mata da ɓargon sa .   Tun a washegarin ranar ya koma asibiti ɗauke da sabon ƙudirin sa bayan dogon nazari tare da kai komo a ƙarshe zuciyar sa ta amince ya haƙiƙance cewa zai kai Falmata ga Manyan likitocin ido dake Mayo clinic su duba ta , idan tana da rabon gani shi zai yi iyakar ƙoƙarin sa wajen biyan kuɗaɗen da za'a buƙata domin yi mata aiki zuwa kan magunguna domin  samun warakar ta . Babu shakka Falmata ta cancanci duk wata kulawar sa duba da yadda take nuna ƙauna ta haƙiƙa ga gudan jinin sa da yake da tabbacin ko mahaifiyar Mama baza ta so ta sama da son da Falmata take yi mata ba , Sannan akwai wani abu da shi yake ji game da Fatima da ya kasa fasaltawa a zuciyar sa sai dai yana yawan sakawa a ransa cewa saboda irin kulawar da take yiwa 'yarsa ne. Bayan haka Halin mutum yana zama tsani wajen samarwa da mutum Alkairi ko akasin sa , halayen Fatima mafi yawansu masu kyau ne , ƙwari yake yabawa da Yakanah tare da Nagartar dake gare ta .    **** Yau ne Alƙawarin sa da Sabon likitan da zai Fara duba Falmata wacce bata kai ga sanin ƙudirin sa ba , domin bai kai ga sanar da ita ba . Kasancewar ƙarfe uku na yamma shine lokacin da zasu ga likitan hakan ya sa shi fita sayo musu hot chocolate Su sha kafin fitar su domin zai taimaka wajen rage musu jin matsanancin sanyi . Da Sallama ya tura 'yar ƙofar ya shiga inda ya tarar da su a zaune yadda ya fita ya bar su , da ɗan gudu Mama ta taho gurin sa ",Bienvenue Papa, que m'as-tu apporté?  (sannu da zouwa Papa me ka kawo min ?) Rungumar ta yayi suka ƙarasa kan doguwar kujerar da Falmata ke zaune fuskar ta ɗauke da siririn murmushi , ", Sannu da dawowa Baban Mama ,   "Sannu da hutawa Maman Mama , yace da sigar zolaya yana kallon fuskar ta      Hot Chocolate ɗin ya ciro musu gami da sanya 'yan chokula ya sakawa  Falmata nata a hannu, Ya ɗauki Mama ya ɗora a cinyar sa ya shiga bata a baki tana kurɓa a hankali Shiru ne ya biyo baya , ɗumin shayin da aka yi shi da garin koko ( cocoa ) da damammiyar  Madara mai zafi yana ratsa sassan jikin su daɗin sa kuma yana basu nishaɗi , da yasa Falmata bata farga da tayi shan haɗama ba sai da ta ji 'yar robar hannun ta sakayau , ta kai chokalin baki , taji bata ɗebo kome ba . Biyamuradi Youssouf wanda duk idanun sa ke kan ta ya ga irin shan da tayiwa chakulan ɗin, ya kai hannu a hankali ya zare robar daga hannun ta tare da musanya mata da nashi wanda bai kai ga fara sha ba , ", Fatima bois ça aussi ( ki sha wannan ma )   " Baban Mama na ƙoshi fa , nagode .    Ta furta hakan tana jin kunya na taso mata , Murmushi mai sauti yayi , ganin yadda gefen bakin ta ya ɓaci , ya kai hannun sa kusa da fuskar ta , hannun sa na sauƙa a jikinta ta jaa baya da sauri tare da ajiye robar hannun ta ,    "Dakata Fatima , repérer zan ɗagga miki daga fuskar ki ,     Babban ɗan yatsan sa ya kai gami da goge mata gefen bakinta inda hot chocolate ɗin ya sauƙa bata sani ba . Kanta a ƙasa tace   "Nagode . bai amsa ba illa ɗibar chakulan ɗin da yayi ya kai bakin ta ,   " amshi lait au chocolat chaud , buɗe bakin ta tayi cike da kunya ta karɓa , "zan iya sha da kaina . tace masa muryarta can ƙasa , yayi kamar bai ji ta ba ,  tare da cigaba da bata a lokaci guda shima yana sha , bata sha dayawa ba tace da shi ta ƙoshi , cikin nishaɗi ya shanye sauran , yana ƙurewa fuskar ta kallo da take sumul babu ɗigon ƙwalliya , Bayan sun gama , yace mata   "Fatima zamou fita zouwa hospitalisé ku shirya yanzou ,   " Baban Mama zamu sake ganin wani likita daban ko ? Wannan bai ƙware ba sosai ya zai ce cutar Mama bata warkewa bace ? akwai ciwon da bashi da magani ne ?   da wani irin yanayi yake dubanta yadda take maganar cike da son samun warakar Mama ya taɓa ransa , ita bata da wani sauran buri ne a rayuwa da ya wuce lafiya tare da walwalar Mama ? Bata yiwa kanta wani shiri ko tanadi ? Bata da wani buri ne na gina tata rayuwar ? " Doctorat gasskiya ya faɗi Fatima , cutar Mama batta maganin waraka a yanzou sai fa kou ɗaya bissa hanyoyin da ya faɗi da kouma babu dama a yanzou , ba bissa lafiyar Mama zamou tafi hospitalisé ba , Shiru tayi ranta babu daɗi , yaya zai ce babu hanyar samun warakar Mama , shi baya irin tunanin da ita take yi ne  ? Meyasa bazai yi wani yunƙuri ba domin taimakawa gurin samar da yadda zasu yi su tsaretar da Mama daga wannan ciwon me azabtarwa , ?    So take tace masa akwai hanya mana ,  sai dai tana cike da tsoro , da jin nawi tare da zargin ko matsayin da take da shi a wajen sa bai kai wannan matakin ba , mafi girman lamarin ya tambayeta ƙarin bayani , to tace da shi me ? Ko a mafarki bata jin ta san amsar da zata iya ba shi . Cikin sanyin jiki ta tashi , da gudu mama ta sauƙa daga jikin Baban ta ta zo ta kama hannun Falmata , sannu kan hankali tayi mata jagora zuwa ɗaki  , Ajiyar zuciya ya sauƙe bayan shigewar su ɗaki , bai ji daɗin sanyin da jikinta yayi ba kan amsar da ya bata , Mayo clinic Doctor Omer Berat ɗan asalin ƙasar turkiyya ( Turkey ) da aiki ya kawo shi Amurka , shine ƙwararren likitan ido da zai duba lafiyar Idon Falmata , Bayan sun shiga wajen sa tare da taimakon na'urar fassara yare suka gaisa , Babu ɓata lokaci ya nemi da ya fara zantawa da marar lafiyar sa , A hankali Youssouf ya kamo hannun Falmata da take zaune a kujerar da take fuskantar ta shi yace ,   "Fatima ki saurara da kyau likita ke son yin magana da ke kan lafiyar ki . " Lafiya ta ko ta Mama ? "Lafiyar idon ki Fatima . Ya amsa yana sake tabbatar mata , Mayar da hankali tayi ga likitan lokacin da ta ji ya ƙira sunan ta , Ta amsa , tana mamaki daman ita ya kawo asibitin a yau ? Tambayoyi ne sosai Likitan yake yi mata da mafi yawan su Falmata bata da takamai-mai amsar su domin tambayoyin sun shafi asalin dalilin sumuwar rashin lafiyar idon nata da ita bata sani ba , amsar da ta bashi a ƙarshe ita ce   " Je ne sais pas, je viens de vivre dans la cécité , mes parents sont morts sans me dire à quel point j'étais aveugle . ( nima ban sani ba kawai na tsinci kaina cikin rayuwar makanta kuma iyayena sun mutu ba tare da sun bani labarin yadda makanta ta ta samo asali ba . )   Biyamuradi Youssouf da amsar ta ta taɓa masa zuciya , ya sake runtse hannun ta cikin nashi , yana jin yadda tausayin ta ya kawo masa . bayan ɗan guntun rubutun da likitan yayi ya umarci Falmata da ta zo kan ɗan wani gado da yake daga gefe a ofishin ya duba idanun nata , Har bakin gadon Biyamuradi ya kama hannun ta , ya kaita tare da kama mata ta hau gadon ta kwanta  , Doctor Omer ya haska ƙwarar idanun nata da penlight , ya ɗora da tambayar ta ko ta ga haske ? Tace ita bata ganin kome , Cigaba yayi da haska idon yana dubawa , a ƙarshe ya kunna slit-lamp ya dallare mata ido da haske , Wani irin kaifi ta ji ya soki idanun ta da ya sata kifta idanun da sauri tare da kai hannu biyu ta riƙe kanta da ya sara mata , "washh kaina . " Sannu ', ita ce kalmar da Youssouf ya furta da sauri yana riƙo

Chapter 66 of 111