Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ta ƙasan ta ya sa ta gaza miƙewa sai faman muskuɗawa take cikin ran ta tana Allah ya sa dai ba fitsarin kwance tayi ba , toh amma ai ita bata fitsarin kwance tun da ƙuruciyar ta bare yanzu da ta zama ƴar budurwa , Tunanin ta ya katse lokacin da samy baby tayi mata umarni bayan ta miƙa mata kuɗi akan ta sayo mata soyayyar   indomi da ƙwai tare da shayi haɗin murtuku ya ji sugar sosai ," A sanyaye yakaka ta miƙa hannu biyu ta ƙarba tana mai taraddadin tashi kar samy baby ta ga yadda ta jiƙa mata kafet ," amma ba yadda ta iya haka ta miƙe tare da nufar bakin kofa Bin bayan ta da kallo samy baby tayi tana tunanin me ya sanyayar mata da jiki ?ko cikin ke damun ta saboda ta san a wurin aiki da aike yakaka bata da sanya ," karaf idanun ta suka sauka a bayan yakaka inda shuɗin siket ɗin yadin da take sanya da shi duk ya baci ,"   Ke yaks dawo nan wai ke me yasa kin cika gidadanci ne ?? Yanzu har yau baki yi wayewar da zaki saka pad a jikin ki idan kina menses ba ? Haba mana yaks meyasa kullum ina kai ki kina dawowa , yanzu ba dan na gani na ƙira ki ba da kenan haka zaki fita ?? Ta ƙarasa zancen tana balla mata harara ," Ƙasa da kan ta yakaka tayi tana me satar kallon wurin da ta tashi domin ita duk bata wani gane kalmar pad da menses ba , ga zaton ta faɗa samy baby take yi mata akan fitsarin da ta saddaƙar shi tayi a kwance "ɓacin rana" , sai dai ga mamakin ta wurin da ta tashin ɗan alamun danshin kaɗan ne kuma bai wani fidda kala ba saboda kafet ɗin ruwan kunkumadi ne ita ma da kƴar ta hango danshin toh akan me samy baby take mata faɗa ?? Tunanin ta ya katse lokacin da ta ji samy baby ta ce ,"       Ki buɗe ƙaramin akwati na ki ɗauki sabon pant da pad ki shiga banɗaki ki gyara jikin ki nan gaba kar ki sake zama babu pad alhalin kin san lokacin yin menses ɗin ki yayi kusa kina jin alamar sa ki tanadi pad idan ma baki da ita ki zo na baki koh kuma ki yi ƙunzugu da tsabatatatcen tsunma kin ji koh ,?? Da sauri yakaka ta gyaɗa kai tana rarraba idanu , domin ita har ga Allah ba wani fahimtar dogon bayanin samy baby tayi ba , koh ta so fahimta ma kalmomin da ta jefo guda uku da turanci sun hana ta gane kan maganar , dan haka kawai sai ta je ta durƙusa a gaban akwatin tayi zugui ," Fahimtar da samy baby tayi yakaka fa bata fahimce ta ba ya sa ta tashi ta zo ta buɗe akwatun ta tare da ciro sabon pant fil sai tashin ƙamshi yake  ( ku sani mata tsabtace undies tare da wanke shi da kuma goge shi wani babban sirri ne na sanya nishaɗi a gangar jiki tare da bada kariya na musamman daga kamuwa da cututtukan da suke addabar mata daga ƙasan su a zamanin yanzu ,ki kasance kullum cikin wanke tare da goge panties ɗin ki bayan kin shanya su a rana sun yi a ƙalla awanni shidda a rana ) da kuma ledar pad mai guda takwas ta danƙa mata," ki shiga banɗaki ki gyara jikin ki ," Da sauri yakaka ta amsa da toh ,    Kin iya amfani da shi koh ?    Gƴaɗa kai ta yi sai kuma ta sake girgiza shi ," Samy baby wacce ta fara zowa wuya da gidadanci tare da jahilcin yakaka tace ,"     Buɗe baki zaki yi kiyi magana ba ki dunga gƴaɗa min kai ya kadangaren gobara ba , kin iya amfani da shi koh na gwada miki ??    A sanyaye ta amsa ban iya ba ," Karɓa tayi tare da nuna mata yadda ake amfani da shi ta ɗora mata da ,"ki wanke siket ɗin naki a banɗakin zan miko miki wasu kayan ," Ƙiris ya rage yakaka ta kurma ihu lokacin da ta ga yadda jikin ta ya ɓaci da jini ,"tashin hankali na shiga uku na lalace fitsarin jini na fara shikenan nima zan mutu na bi su abba wayyo Allah falmata waye zai kula min da ke ,"  wannan shine tunanin da yakaka take yi lokacin da take wanke jikin ta da kayan ta , tana yi tana sharar hawaye ," Ido jazur ta fito bayan ta shirya kan ta cikin kayan da samy baby ta miƙa mata na wata koriyar atamfa riga da siket , sun zauna mata ɗas kasancewar ita ma samy baby ƴar madaidaiciya ce tamkar ta ," Sumi-sumi ta wuce tana share guntun hawaye ta nufi wurin aiken da aka mata ,' samy baby ta bi bayan ta da kallo tana me jin tausayin yarinyar na zaunawa cikin ranta , ta fahimci yau ne ta fara tsintar kan ta a yanayi na al'ada saboda tashin hankali da damuwar da ta gani tare da yakakar wanda ba kome ya jawo hakan ba illa jahilcin addini da na boko saboda da tana zuwa makaranta kowacce daga cikin ta boko koh ta islamiyya a shekarun ta da take sha shidda da ƴan watanni ya ci ace ta san me wannan jinin yake nufi saboda ana wayar da kai a makarantu ," nan take ta ji tana son tayi yunƙuri domin ganin yakaka ta ɗan samu ilmi ko kaɗan ne domin ita kan ta harkar da take son ɗora ta akai idan kana da ilmin boko kafi samun kasuwa wurin manyan wayayyun mutane irin wanda take yi wa yakakar yangen su , domin su basu cika harka da jahila ba ," zamani ya zo da kome zaka yi domin cigaban kan ka sai kana da ilmin zamani ilmi shine gishirin rayuwa ," Tana tafiya tana rarrakaɓewa ta jikin gini tafiyar kan ta ba yadda ta saba take yin ta ba tana tafe tana mammatse kafafu domin ji da take tamkar ƴar audugar da take jikin ta zata faɗo wacce rashin sanya ta a dai-dai ya sa take jin hakan ," cikin ranta kuwa kalmomin wasiyyar da zata barwa falmata take haɗawa ," Yaks baby , yaks baby , ke yaks ji mana wai yane ina miki magana kina wani ƙara wuta tamkar baki ji na , zo mana magana za muyi ," Muryar babasho mai sayar da wiski da su matallah , zuwa kan taba sigari da sauran kwayoyin sanya maye a cikin ɗan shagon da yayi da tsoffin kwanukan rufi da katako ,ta katse mata tunani , babasho yayi masifar maƙalewa yakaka , yana bala'in son ta kamar zai yi hauka ,sai dai samy baby ta kasa ta tsare ta hana ya samu damar koh ɗan zantawa da yaks , duk kuwa da cewa kullum sai ya je rumfar saly baby ya sai burkutu dan kawai ya samu ya ga fuskar yaks ," samy baby ta kan faɗa mata ," ta wuce ajin babasho fintinkau , me zata yi da wannan sauran tabar ? Da duka-duka idan aka haɗa jarinsa da shagon nasa ba zai fice dubu goma ba ,??  Ai sama tayi wa yaro nisa tsakanin ta da ire-iren su babasho sai dai ta kira su ta aike su ,"amma ita kalar manya ce kalar hamshaƙan da suka ci suka tada kai da naira , ," kar ki kuskura ki kula shi yaks bashi ma da isasshen hankali idan ya sha ta kai masa karo yana iya shaƙe ki ya kar ki ya kar banza atoh kiyi hankali," Ga yakaka kuwa ita ba ma babasho ba da take jin mugun-tsoron sa saboda chukurkuɗaɗɗan gashin sa da ya tara akai baya wani kula da shi duguzum-duguzum ya fenta kan kalar jaa shuɗi da kuma yalo , uwa uba faranta hannunsa zaƙo-zaƙo da suke cike taf da annakiyar dauɗa suna tsorata ta har su sanya ta hasashen yadda zai kafa mata farce a wuya idan ya shaƙo ta kamar yadda samy baby take faɗa mata , ita gaba ɗaya maza ma ƙarƙashin ranta tsoron su take , babu wani ɗa namiji da ta taɓa jin sa cikin ranta idan aka ɗauke dakta hamza wanda shi ma ta ɗauki tunanin sa da yake faɗo mata jifa-jifa a zuwan tana tuna sa ne domin taimakon da yayi a gare su ita da ƙanwar ta , bayan shi babu wani ɗa namiji da yakaka take ɗaga kai ta dube shi iyakar ta da su harkar cinikayyar su ta burkutu su , su zo saya ta je ta kawo musu ta karbi kuɗin ," bata taɓa buɗe baki tayi tsiwa koh rashin kunya ga kowa ba duk kuwa da yadda suke kai mata wawura tare da maganganun banza da ita bata ma kai ga fahimtar wasu kalmomin su na batsa ba ,"ita dai ba'a raba fuskar ta da tsadadden murmushin ta , dan haka yanzu ma da babasho yake kwala mata kira koh kallo bai isheta ba haka ta cigaba da tafiyar ta ,' shi kuwa ya bi bayan ta da kallo yana lashe leɓe tare da lanƙwasa ƴan yatsun sa cikin ransa yana fatan Allah ya kai damo ga harawa koh bai ci ba yayi birgima,", Karo taji tayi da mutum wanda zurfin da tayi a tunanin ta ya sa bata ga tahowar sa ba ," da sauri tayi baya ,tare da durƙusawa ta ɗauko masa makullin motar sa da ya faɗi a hannun sa ta sanya bakin gyalen ta ta goge ƙasan jikin ɗan makullin bakin ta ɗauke da kalmar ban hakuri ta miƙa masa mukullin ba tare da ta ɗago kan ta ba ,      Miƙa wankakken hannunsa mai ɗauke da wankakkun fararen farata ƙal yayi ya karbi makullin agogon hannun sa na ta ɗaukar ido ,"hannun ta bi da kallo wanda kyaun sa da gogewar sa a tsafta irin wanda bata taɓa gani ba ya ɗauke hankalin ta , muryar sa ce ta dawo da ita daga shagalal da tayi cikin hausar sa ta bamarɗe yace ,"   ", Ai ni ke da laifin ina gaugawa ban lura da ke ba yi mini afouwa ," Da hanzari ta ɗago kan ta jin muryar sa da ta yi kamar ta san ta , tana ɗagowa yana gifta ta sai tashin mabuwayin ƙamshin sa da ta shaƙa wanda ya sa ta jin tsaftar sa ta burge ta har ta waiwaya tana bin takun sa da kallo ," Har ta je ta amso aiken da aka mata tana jin ƙamshin turaren sa cike taf da hancin ta ," bayan samy baby ta ci indomie da soyayyen ƙwai ta cika cikin ta har ta barwa yakaka sauran ta cinye tas tare da wanke kwanon , ta tashi da niyyar fara gyaran ɗakin , samy baby ta dakatar da ita tare da cewa ta bata hankalin ta ," nan tayi mata bayanin jinin haila da ta fara da yadda ake wankan sa , ta kuma jaa kunnen ta akan ta kula kar ta yadda wani ɗa namiji ya ɗirka mata ciki kar ma ta kula kowa a yanzu idan lokacin fara harkar ta yayi ita da kan ta zata kaita a bata maganin hana ɗaukar ciki ta yadda zata ji daɗin cin kasuwar ta ba tare da wata fargabar yin ciki ba , nan dai suka ɗauki lokaci samy baby tana mata huɗuba wanda mafi yawan su ba na kirki bane , idan aka cire wankan hailar da ta koya mata a taƙaice babu wani abun kirki cikin sauran shawarwarin da ta bata ,'    Ki lura da kyau da lissafin kwanakin menses ɗin ki domin ta haka ne idan kin fara harka zaki gane lokacin da kike danger ɗin ki dan ki kiyaye harka a waɗannan kwanakin duk da dak zamu je a miki ƴan dabaru amma kau da bara sai ana haɗawa da zamiya ,"kin ga yau ɗaya ga wata kika fara duk inda wata ya kai shidda  takwas zuwa goma zaki iya gamawa toh kwanaki bakwai da zasu biyo bayan kwana uku na kammala jinin al'adar ki sune ranaku mafi hatsari gare ki idan kin fara harka domin tabbas kina iya samun ciki idan kika sake kika yi koh da wasa da lawurjen namiji ne ehee ,sai ki kiyaye kin ji koh ? Ba tare da yakaka ta fahimci mafi akasarin bayanan samy baby ba ta amsa da "toh" hankalin ta ya fi karkata ga son sanin wacce harka ce zata ɗora ta akai wacce har akwaj hatsarin samun ciki ?? Ita fa tana tsoron zancen ciki kowacce irin harka ce zata iya hakura da ita idan har zata iya yin ciki , toh amma tayaya ma ake samun cikin ?????? ( ta miƙa tambayar ga masu karatu 😂) Cikin sanyin jiki ta koma bakin aikin ta inda duk take a takure domin gani take kamar kowa ya san tana fitsarin jini bini-bini ta leƙa ta kalli bayan siket ɗin ta ,kou kuwa ta shiga bayi tayi tsarki , duk a matse take jin kan ta , sai dai tata damuwar ta kau koh kuwa ace ganin damuwa kwance ɓaro-ɓaro akan fuskar falmata ya sa ta daina jin ta ta sai wani sabon tashin hankali tare da damuwar da ta fi ta farko da taji ya mamaye ta , sam bata ƙaunar ganin falmata cikin damuwa   Falmata nah ! faɗa min menene ?? wani ne ya zage ki ? Koh baki da lafiya ne , yunwa kike ji ?? Koh kina son wani abu ne ?? Koh jiya ɗan liti ya miki wani abun da ya ɓata miki rai ne  ? Gaya min dan Allah menene     Ɗan guntun murmushin da daga ganin sa na ƙaƙale ne shi falmata ta ɗora a fuskar ta ,"     Yakaka ni babu wanda ya min kome kuma lafiyata ƙalau , bana  jin yunwa ,"       Toh meye ne koh kin tuno da su mama ne ??    Da sauri falmata ta gƴaɗa kai tana me rushewa da kukan da tuntuni yake cin ta , sakamakon abun da ya faru da ita a wurin wani mutum wanda ɗan liti ya ɗauke ta jiya ya kai ta a matsayin shine ubanɗakin sa wanda yake bashi kayan daɗin da yake kawo mata tana cika cikin ta da shi ," Ita dai bata san ina ɗan litin ya kai ta ba domin a mota suka tafi ,    Duk da cewa ba gani take ba amma ta fahimci gidan da ɗan liti ya kai ta gidan me hali ne , domin maɗaukakin sanyin da ta ji a parlour da suka tadda mutumin har zuwa kan lallausar abun da aka zaunar da ita akai kujera zata kira abun koh gado ?? Ita dai bata taɓa zama a makamancin abu mai taushin sa ba ga wani fitinannen ƙamshi da ya cika wurin , bata ji ta fara tsorata ba sai da ɗan liti ya ɗibo wani abu mai matsanancin sanyi ya cusa mata a baki da ya umarce ta da ta buɗe bakin ta zai bata wani abu wai shi "ice cream" anan ta ji ta tsorata domin kuwa dawo da abun tayi ta tofar da shi saboda bata taɓa shan abu mai tsananin sanyin irin sa ba ,"    Mutumin da suka tara a falon ya buɗe ƙatuwar muryar sa marar daɗin sauti kamar fasasshiyar  gangar  ya dunga tuntsira dariya ɗan liti yana taya sa harda shewa ,"     Watau kachallah bai taɓa shan ice cream ba ?? Ai kuwa daɗi ya bar ka , toh liti bashi gasasshiyar kaza ya ci nasan dai koh daga kan dutse ya sauko ya san nama , Wata ƙatuwar cinya ɗan liti ya fisgo ya damƙawa falmata a hannun ta bayan ya miƙa mata kwalin lemun ,"five alive" a ɗaya hannun ,     Maza ɗan kachallari ci kaza ka sha lemu yaro ai ka zo gidan arziki duk wasu kayan daɗi da nake kai maka kana ci kana lashe baki "ya tsohon kare nan ne tushen sa kaɗan ne daga cikin ire-iren kayan maƙulashen da suke jibge a gidan nan yaro saki jiki ka ci arziki ka bar shi a inda ka gan shi ,"     Cikin sanyin jiki falmata ta kai cinyar kazar bakin ta ta gutsuri kaɗan tana taunawa ," zaƙin kayayyakin ɗanɗano irin na alfarma tare da zaƙin naman kazar suka haɗu suka sa kunnen falmata motsi har bata san lokacin da ta cinye wacce ɗan liti ya bata ba ,     tana tanɗe baki ,  ɗan liti wanda suke kus-kus da wannan ɗan tsurut ɗin mutumin shi ya lura da ita ya sake fisgo ɗaya cinyar ya ɗangwala mata a hannu ,"       ungo maza cinye har ƙashin ka tauna ka haɗiye , yau ta shiga ranakun tarihi a wurin ka ɗan kachallari ," Miƙewa ɗan liti yayi bayan sun gama kitsa abun da suka kitsa ,"     Ɗan kachallari ni zan ɗan je na dawo nan kusa ka jira...    Koh kafin ya ƙarasa abun da yake nufin cewa falmata ta miƙe zuruf ta dangwarar da sauran naman hannun ta '',       Ah ah mu tafi tare nima zan bika ," Haɗa ido ɗan liti da wannan mutumin suka yi , mutumin ya yiwa ɗan liti alama da ido akan ya tafi kawai zasu yi waya ,"    Saɗaf-saɗaf ɗan liti ya fita ya jaa musu kofar wanda ƙarar rufe kofar ya sa falmata wacce take tsaye tana jiran amsar ɗan liti ta farga da barin ɗan liti wajen ,"      Kuka ta sa tare da fara taku tana nufar hanyar da ta ji motsin rufowar kofar da ɗan liti yayi lokaci ɗaya tana jera kiran sunan ɗan litin ,"   Dariya ta ji mutumin ya kwashe da ita  kafin ta ji ya fara tahowa inda take yana cewa haba ɗan kyakkyawan yaro kachalla menene abun kuka yi shiru yanzu ɗan liti zai dawo aiken sa nayi , kafin ya dawo zo muyi wasa ,"kafin ta ankara ta ji ya sure ta sama yana cewa ," A ɗaga sama anyi wa wada kwace 😂 ,"   Na so na baku ya fi haka , sai dai yawan cewa kuna jira da kuke yi , yasa na dakata anan kuyi manage da wannan sai mun hadu a shafi na gaba cikin yardar Ubangiji," A kan karo mutunci #umm'muaz #vote #comments #share with your Family and friends.Cikin sati biyu da tarewar su yakaka a gidan madam saly ,sun zama ƴan gari a da'irar ta yadda yakaka ta san ɗakunan manyan kilakai da ƙananun karuwan da suke unguwar saboda aiken ta da madam saly take wurin su , a gefe ɗaya kuma ta zama ƴar ɗakin samy baby , wacce bayan dawowar yakaka gidan madam saly ta gama nazarin yarinyar tsaf , ta gane bata san ma mai kalmar bariki take nufi ba kamar yadda da tayi zaton yakakar ƙaramar karuwa ce , sai ta fahimci ashe yakakan neman abun sawa a bakin salati take tare da wajen da zata sanya haƙarƙarin ta , dan haka sai ta jaa ta a jiki ta maida ta mai gyara mata ɗaki tare da yi mata ƴan kananun aike da aiki , ita kuma tana bata ƴan kuɗaɗe bayan jibgin suturun ta da ta fitar ta bata kwance , tun yakakan tana ɗari-ɗari ganin abun da samy baby tayi mata a farkon haɗuwar su , har dai ta zo ta saki jiki da ita , sosai take kyautatawa samy baby da ta riƙa a matsayin uwarɗakin ta , wacce take samun alheri tare da sakewa a wurin ta, domin a lokuta da dama har ƴar hira samy baby take zama su yi da yaks , Aikin gidan madam saly kuwa tuƙuru yakaka take yin sa domin gwanintar da take nunawa ya faranta ran madam saly da take ganin ta a matsayin ginshiƙin su cikin duniya a yanzu , bata da wani lokaci nata na kan ta sai na aikin burkutu wanda ba'a sanya ba ma yi take kamar su wanke dawa , juya ruwan dahuwar burkutun da kuma tace shi wanke kayan madam saly da gyara mata ɗaki , tun safe idan ta kama aiki sai dare karfe sha ɗaya take samun hutu ," wanda hakan ke matuƙar farantawa madam saly rai har take ganin wautar kan ta da farko,  da ta so korar su ashe dai maganar ɗan liti dutse , Ga falmata ma sai sam barka domin kuwa har ɗan kumatu tayi ta sake mul-mul , sakamakon cika mata ƙundu da ɗan liti yake da cimar daɗi kullum dare kafin su kwanta bacci , ga kuma labaru masu sanya nishaɗi da yake bata har bacci ya ɗauke ta ,bata zuwa ko'ina daga ɗakin ɗan liti da yake daga wajen filin rawa sai cikin gidan madam saly da take aikin wanke-wanke kofuna tare da farantan aikin burkutu tsawon yini a cikin gidan , bata da wata matsala saboda duk lokacin da yakaka ta ɗan zagaya zata taho bakin fanfon da take zaune din-din a gefen sa ta shafi kan ta koh kuwa fuskar ta , ta kuma tambaye ta bata da wata matsala koh ? Nan zata amsa mata cikin farin ciki da ita bata da wata matsala , Haka zata sake komawa bakin aikin ta tana mai farin cikin sauyin rayuwar da suka samu , musamman farin cikin da take hangowa a fuskar ƙanwar ta wacce ɗan liti ya wadata ta da ƴan kayayyakin gonjo na ƴan matasan yara maza sa'annin ta fes-fes da ita hasken ƴar luwai ɗin fatar ta ruwan zuma yana bayyanuwa, Ranar da suka kwana huɗu a gidan ɗan liti yayi mata kyautar kayan wanda daga ita har falmata kyautar bata wani faranta musu ba , saboda ƴan rigunan basu da wani girma kayan turawa ne , su kuma sun san kayan nan burguza burguza da falmata ke sanye da su sune rufin asirin su a kasantuwar falmata namiji saboda kayan ya boye ɗan tudun kirjin falmatan wanda suka fara tasowa tare da bunƙasa ,  Da kƴar yakaka ta shawo kan falmata wacce da farko ta tubure akan shawarar da yakaka ta kawo na falmatan ta dunga sanya riguna biyu bayan ta tamke kirjin ta da ɗankwali ,saboda boye tudun tare da yi mata gargaɗi kada ta yadda ta sauya kaya a gaban ɗanliti duk juyin duniya , ta kan ce     Kiyi hakuri falmata har mu ɗan tara abun da muka tara anan ɗin zuwa lokacin kuma mun san gari sosai idan ya so sai mu koma wani wurin da babu ƴan iska mu raɓa ki koma saka kayan mu na mata , kamar kowacce mace ina nan ina ware miki kayan ki cikin kayan da nake samu ," Ranar da ta fara ɗaure kirjin ta yini tayi tana fama da ciwon kirjin , amma da ta kwana biyu sai ta saba ta daina jin ciwon , Bata taɓa yin wanka sai sun tabbatar da ɗan liti ya bar da'irar wajen sannan zata yi wankan a gurguje yakaka ta raka ta ta sauya kaya tare da sake gyara mata ɗaurin kirjin ta wanda ya taimaka ƙwarai wurin boye halittun kirjin ta , sai dai salon takun tafiyar ta tare da tudun bayan ta ke sa samy baby tana yawan tsokanar ta da "Kachallah me jikin mata ,"    tafiyar ka sai kace ta hamshaƙan mata , koh kuwa tace shege kachallah da kai mace ne da anyi manyan kaya a wurin ka ," Idan yagana tana wurin tayi ta sheƙa dariya ,wacce ita ma a yanzu sha'awar rayuwar su yakakan take , domin kuwa har kuɗi da suturu yakaka ta bata daga cikin wanda samy baby ta bata ," Haka kwanaki suka yi ta tafiya har suka samu wata guda da ƴan kwanaki a dafdalar wannan gidan , wanda zuwa lokacin yakaka tayi jazur wannan maɗaukakin hasken fatar ta ta ya sake bayyana dal tamkar fitila haka take a waje , ƴar kyakkyawar ƙaramar budurwa mai sanyi tare da yawan fara'a koyaushe cikin murmushi take , ko magana yakaka take haka zaka

Chapter 18 of 111