Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ga fuskar ta da yalwatattacen murmushi dasashin ta a waje , wanda hakan yake tasiri matuƙa wurin bayyana ƴan ƙananun kyaun ta wanda hasken da take da shi ya fi jaan hankalin mazan da suka fara ƙaraƙaina akan ta fiye da kyan nata ," Zuwa lokacin samy baby ta fara jaan ɗamarar wanke yakaka daga dauɗar datti gami da ƙazantar ƙauye a cewar ta yakaka haja ce me matuƙar tsada , wacce sayan ta sai alhajin da ya rufu ya tada kai , " sai ya so zama tamkar gasa a tsakanin ta da madam saly wacce ita ma take bada sumfurin tata kulawar ga yakaka domin ta farga gaba kaɗan yakakan zata zame mata hanyar samun arziki ,dan haka ta fara kokarin janye ta daga wurin samy baby da ta lura tana son kawo mata tsaiko domin kuwa ga alama so take ta fanɗarar da yakaka ta sanar da ita daɗin ƴancin kai kamar yadda ita take da nata ƴancin a hannu domin samy baby ba'a ƙarƙashin kowa take ba cikin magajiyoyin gidan , da karfin ta ta shigo bariki da kuma nawin aljihunta tare da gatan ta domin ba kukan yunwa koh na rashin wurin kwana koh kuwa na neman kuɗin zuwa asibiti zubda ciki ne suka kawo ta bariki ba , ƴar cikin ƙwaryar gari ce da gatan ta da kome iyayen ta ma manyan mutane ne sanannu , uwa uba bata da duhun jahilci domin kwalin digiri ke gare ta ," sha'awar rayuwar barikin take tare da taimakon matar uban ta wacce take sake ingiza ta , uwa uba shaiɗan da yake tsakiyar kan ta yana buga ganga , Gidan kakaf ba wata tsohuwar kilaki da take shakka , sai ma su da idan jarabar su ta busa sigari koh afa ƙwayoyi suka motsa , kuma suka laluba lalitar su suka ji wayam , su je wurin ta neman ƴan kuɗaɗe sanin da suka yi kaf cikin karuwan gidan ba wacce ta kai ta kama kuɗi , da kuma kyauta domin hannun ta a sake yake bata da rowa ," Ranar wata litinin da safe yakaka ta wayi gari da wani irin matsanancin ciwon mara wanda tun kwanaki biyu da suka wuce take jin sa kaɗan kaɗan amma ta daure , Har zuwa yanzu da take kan hanyar ta ta zuwa ɗakin samy baby domin ta gyara mata ɗakin ,bayan ta gama kintsa na madam saly kamar yadda ta saba kafin su duƙufa aikin sana'ar su ," A dudduƙe da jaan ƙafa ta ƙarasa cikin ɗakin samy wacce take kwance tana sharar bacci daga ita sai ƴar ficiciyar rigar bacci kan gadon duk a hargitse kayayyakin ta tun daga kan rigar mama da ɗan kafai duk a wurge a kan gadon , tayi ɗai-ɗai da kafafu gashin dokin da yake kan ta ya baje akan filon da tayi matashin kai da shi ," idan da sabo yakaka ta saba tadda ta a haka kullum . Tana shiga ɗakin ta zube akan shimfiɗar kafet ɗin ta kwanta gami da dunƙulewa wuri guda tana murƙususu , dunƙulewar da tayi ta haɗe guiwar kafafun ta da kirjin ta sai ya sa taji rangwamen kartawa tare da murɗar da marar ta ke mata har ɗan wani bacci ta fara ji yana figarta saboda rashin bacci da tayi daren jiya a sakamakon ciwon cikin ," bata ankara ba bacci mai karfi ya fisge ta , ta sake jiki sosai tana baccin ta , Samy baby ce ta farka bayan da taji baccin ya soma gundurar ta , ta daina jin dadin sa , doguwar hamma ta hangame baki ta jaa babu neman tsari daga shaiɗan babu salati , ta gantsare bayan ta ya bada sautin ƙaƙas , tana zira ƙafar ta ƙasa ta sauke akan yakaka wacce baccin ta yake kai mata karo har tsibirin keemala na ƙasar bankok,"     Da farko ta firgita da ganin mutum kwance a gaban gadon ta sai dai fahimtar wacece a kwance ya sa ta ƙewaye ta gami da nufar kofar banɗakin da take ta cikin ɗakin nata , a ranta tana raya cewa gajiyar aiki da rashin bacci ne suka sa yakaka ta bingire anan ta na bacci , tare da sake aiyana niyyar taimakon yakakan har ta samu karfin tsayuwa da kafafun ta muddin yakakan zata yadda ta bi hanyar da zata ɗora ta ," yo ina ma zata ƙi ?? Ai duk wanda ruwa ya ci shi idan aka miƙa masa takobi sai ya kama ,"    A firgice yakaka ta farka lokacin da samy baby take tashin ta , "cikin inda-inda ta fara bata haƙuri bayan ta gaishe ta,  tare da faɗa mata cikin ta ne yake ciwo amma yanzu ya lafa ,"ta daina jin ciwon sa sosai , sai dai lema-lemar da take ji ta ƙasan ta ya sa ta gaza miƙewa sai faman muskuɗawa take cikin ran ta tana Allah ya sa dai ba fitsarin kwance tayi ba , toh amma ai ita bata fitsarin kwance tun da ƙuruciyar ta bare yanzu da ta zama ƴar budurwa , Tunanin ta ya katse lokacin da samy baby tayi mata umarni bayan ta miƙa mata kuɗi akan ta sayo mata soyayyar   indomi da ƙwai tare da shayi haɗin murtuku ya ji sugar sosai ," A sanyaye yakaka ta miƙa hannu biyu ta ƙarba tana mai taraddadin tashi kar samy baby ta ga yadda ta jiƙa mata kafet ," amma ba yadda ta iya haka ta miƙe tare da nufar bakin kofa Bin bayan ta da kallo samy baby tayi tana tunanin me ya sanyayar mata da jiki ?ko cikin ke damun ta saboda ta san a wurin aiki da aike yakaka bata da sanya ," karaf idanun ta suka sauka a bayan yakaka inda shuɗin siket ɗin yadin da take sanya da shi duk ya baci ,"   Ke yaks dawo nan wai ke me yasa kin cika gidadanci ne ?? Yanzu har yau baki yi wayewar da zaki saka pad a jikin ki idan kina menses ba ? Haba mana yaks meyasa kullum ina kai ki kina dawowa , yanzu ba dan na gani na ƙira ki ba da kenan haka zaki fita ?? Ta ƙarasa zancen tana balla mata harara ," Ƙasa da kan ta yakaka tayi tana me satar kallon wurin da ta tashi domin ita duk bata wani gane kalmar pad da menses ba , ga zaton ta faɗa samy baby take yi mata akan fitsarin da ta saddaƙar shi tayi a kwance "ɓacin rana" , sai dai ga mamakin ta wurin da ta tashin ɗan alamun danshin kaɗan ne kuma bai wani fidda kala ba saboda kafet ɗin ruwan kunkumadi ne ita ma da kƴar ta hango danshin toh akan me samy baby take mata faɗa ?? Tunanin ta ya katse lokacin da ta ji samy baby ta ce ,"       Ki buɗe ƙaramin akwati na ki ɗauki sabon pant da pad ki shiga banɗaki ki gyara jikin ki nan gaba kar ki sake zama babu pad alhalin kin san lokacin yin menses ɗin ki yayi kusa kina jin alamar sa ki tanadi pad idan ma baki da ita ki zo na baki koh kuma ki yi ƙunzugu da tsabatatatcen tsunma kin ji koh ,?? Da sauri yakaka ta gyaɗa kai tana rarraba idanu , domin ita har ga Allah ba wani fahimtar dogon bayanin samy baby tayi ba , koh ta so fahimta ma kalmomin da ta jefo guda uku da turanci sun hana ta gane kan maganar , dan haka kawai sai ta je ta durƙusa a gaban akwatin tayi zugui ," Fahimtar da samy baby tayi yakaka fa bata fahimce ta ba ya sa ta tashi ta zo ta buɗe akwatun ta tare da ciro sabon pant fil sai tashin ƙamshi yake  ( ku sani mata tsabtace undies tare da wanke shi da kuma goge shi wani babban sirri ne na sanya nishaɗi a gangar jiki tare da bada kariya na musamman daga kamuwa da cututtukan da suke addabar mata daga ƙasan su a zamanin yanzu ,ki kasance kullum cikin wanke tare da goge panties ɗin ki bayan kin shanya su a rana sun yi a ƙalla awanni shidda a rana ) da kuma ledar pad mai guda takwas ta danƙa mata," ki shiga banɗaki ki gyara jikin ki ," Da sauri yakaka ta amsa da toh ,    Kin iya amfani da shi koh ?    Gƴaɗa kai ta yi sai kuma ta sake girgiza shi ," Samy baby wacce ta fara zowa wuya da gidadanci tare da jahilcin yakaka tace ,"     Buɗe baki zaki yi kiyi magana ba ki dunga gƴaɗa min kai ya kadangaren gobara ba , kin iya amfani da shi koh na gwada miki ??    A sanyaye ta amsa ban iya ba ," Karɓa tayi tare da nuna mata yadda ake amfani da shi ta ɗora mata da ,"ki wanke siket ɗin naki a banɗakin zan miko miki wasu kayan ," Ƙiris ya rage yakaka ta kurma ihu lokacin da ta ga yadda jikin ta ya ɓaci da jini ,"tashin hankali na shiga uku na lalace fitsarin jini na fara shikenan nima zan mutu na bi su abba wayyo Allah falmata waye zai kula min da ke ,"  wannan shine tunanin da yakaka take yi lokacin da take wanke jikin ta da kayan ta , tana yi tana sharar hawaye ," Ido jazur ta fito bayan ta shirya kan ta cikin kayan da samy baby ta miƙa mata na wata koriyar atamfa riga da siket , sun zauna mata ɗas kasancewar ita ma samy baby ƴar madaidaiciya ce tamkar ta ," Sumi-sumi ta wuce tana share guntun hawaye ta nufi wurin aiken da aka mata ,' samy baby ta bi bayan ta da kallo tana me jin tausayin yarinyar na zaunawa cikin ranta , ta fahimci yau ne ta fara tsintar kan ta a yanayi na al'ada saboda tashin hankali da damuwar da ta gani tare da yakakar wanda ba kome ya jawo hakan ba illa jahilcin addini da na boko saboda da tana zuwa makaranta kowacce daga cikin ta boko koh ta islamiyya a shekarun ta da take sha shidda da ƴan watanni ya ci ace ta san me wannan jinin yake nufi saboda ana wayar da kai a makarantu ," nan take ta ji tana son tayi yunƙuri domin ganin yakaka ta ɗan samu ilmi ko kaɗan ne domin ita kan ta harkar da take son ɗora ta akai idan kana da ilmin boko kafi samun kasuwa wurin manyan wayayyun mutane irin wanda take yi wa yakakar yangen su , domin su basu cika harka da jahila ba ," zamani ya zo da kome zaka yi domin cigaban kan ka sai kana da ilmin zamani ilmi shine gishirin rayuwa ," Tana tafiya tana rarrakaɓewa ta jikin gini tafiyar kan ta ba yadda ta saba take yin ta ba tana tafe tana mammatse kafafu domin ji da take tamkar ƴar audugar da take jikin ta zata faɗo wacce rashin sanya ta a dai-dai ya sa take jin hakan ," cikin ranta kuwa kalmomin wasiyyar da zata barwa falmata take haɗawa ," Yaks baby , yaks baby , ke yaks ji mana wai yane ina miki magana kina wani ƙara wuta tamkar baki ji na , zo mana magana za muyi ," Muryar babasho mai sayar da wiski da su matallah , zuwa kan taba sigari da sauran kwayoyin sanya maye a cikin ɗan shagon da yayi da tsoffin kwanukan rufi da katako ,ta katse mata tunani , babasho yayi masifar maƙalewa yakaka , yana bala'in son ta kamar zai yi hauka ,sai dai samy baby ta kasa ta tsare ta hana ya samu damar koh ɗan zantawa da yaks , duk kuwa da cewa kullum sai ya je rumfar saly baby ya sai burkutu dan kawai ya samu ya ga fuskar yaks ," samy baby ta kan faɗa mata ," ta wuce ajin babasho fintinkau , me zata yi da wannan sauran tabar ? Da duka-duka idan aka haɗa jarinsa da shagon nasa ba zai fice dubu goma ba ,??  Ai sama tayi wa yaro nisa tsakanin ta da ire-iren su babasho sai dai ta kira su ta aike su ,"amma ita kalar manya ce kalar hamshaƙan da suka ci suka tada kai da naira , ," kar ki kuskura ki kula shi yaks bashi ma da isasshen hankali idan ya sha ta kai masa karo yana iya shaƙe ki ya kar ki ya kar banza atoh kiyi hankali," Ga yakaka kuwa ita ba ma babasho ba da take jin mugun-tsoron sa saboda chukurkuɗaɗɗan gashin sa da ya tara akai baya wani kula da shi duguzum-duguzum ya fenta kan kalar jaa shuɗi da kuma yalo , uwa uba faranta hannunsa zaƙo-zaƙo da suke cike taf da annakiyar dauɗa suna tsorata ta har su sanya ta hasashen yadda zai kafa mata farce a wuya idan ya shaƙo ta kamar yadda samy baby take faɗa mata , ita gaba ɗaya maza ma ƙarƙashin ranta tsoron su take , babu wani ɗa namiji da ta taɓa jin sa cikin ranta idan aka ɗauke dakta hamza wanda shi ma ta ɗauki tunanin sa da yake faɗo mata jifa-jifa a zuwan tana tuna sa ne domin taimakon da yayi a gare su ita da ƙanwar ta , bayan shi babu wani ɗa namiji da yakaka take ɗaga kai ta dube shi iyakar ta da su harkar cinikayyar su ta burkutu su , su zo saya ta je ta kawo musu ta karbi kuɗin ," bata taɓa buɗe baki tayi tsiwa koh rashin kunya ga kowa ba duk kuwa da yadda suke kai mata wawura tare da maganganun banza da ita bata ma kai ga fahimtar wasu kalmomin su na batsa ba ,"ita dai ba'a raba fuskar ta da tsadadden murmushin ta , dan haka yanzu ma da babasho yake kwala mata kira koh kallo bai isheta ba haka ta cigaba da tafiyar ta ,' shi kuwa ya bi bayan ta da kallo yana lashe leɓe tare da lanƙwasa ƴan yatsun sa cikin ransa yana fatan Allah ya kai damo ga harawa koh bai ci ba yayi birgima,", Karo taji tayi da mutum wanda zurfin da tayi a tunanin ta ya sa bata ga tahowar sa ba ," da sauri tayi baya ,tare da durƙusawa ta ɗauko masa makullin motar sa da ya faɗi a hannun sa ta sanya bakin gyalen ta ta goge ƙasan jikin ɗan makullin bakin ta ɗauke da kalmar ban hakuri ta miƙa masa mukullin ba tare da ta ɗago kan ta ba ,      Miƙa wankakken hannunsa mai ɗauke da wankakkun fararen farata ƙal yayi ya karbi makullin agogon hannun sa na ta ɗaukar ido ,"hannun ta bi da kallo wanda kyaun sa da gogewar sa a tsafta irin wanda bata taɓa gani ba ya ɗauke hankalin ta , muryar sa ce ta dawo da ita daga shagalal da tayi cikin hausar sa ta bamarɗe yace ,"   ", Ai ni ke da laifin ina gaugawa ban lura da ke ba yi mini afouwa ," Da hanzari ta ɗago kan ta jin muryar sa da ta yi kamar ta san ta , tana ɗagowa yana gifta ta sai tashin mabuwayin ƙamshin sa da ta shaƙa wanda ya sa ta jin tsaftar sa ta burge ta har ta waiwaya tana bin takun sa da kallo ," Har ta je ta amso aiken da aka mata tana jin ƙamshin turaren sa cike taf da hancin ta ," bayan samy baby ta ci indomie da soyayyen ƙwai ta cika cikin ta har ta barwa yakaka sauran ta cinye tas tare da wanke kwanon , ta tashi da niyyar fara gyaran ɗakin , samy baby ta dakatar da ita tare da cewa ta bata hankalin ta ," nan tayi mata bayanin jinin haila da ta fara da yadda ake wankan sa , ta kuma jaa kunnen ta akan ta kula kar ta yadda wani ɗa namiji ya ɗirka mata ciki kar ma ta kula kowa a yanzu idan lokacin fara harkar ta yayi ita da kan ta zata kaita a bata maganin hana ɗaukar ciki ta yadda zata ji daɗin cin kasuwar ta ba tare da wata fargabar yin ciki ba , nan dai suka ɗauki lokaci samy baby tana mata huɗuba wanda mafi yawan su ba na kirki bane , idan aka cire wankan hailar da ta koya mata a taƙaice babu wani abun kirki cikin sauran shawarwarin da ta bata ,'    Ki lura da kyau da lissafin kwanakin menses ɗin ki domin ta haka ne idan kin fara harka zaki gane lokacin da kike danger ɗin ki dan ki kiyaye harka a waɗannan kwanakin duk da dak zamu je a miki ƴan dabaru amma kau da bara sai ana haɗawa da zamiya ,"kin ga yau ɗaya ga wata kika fara duk inda wata ya kai shidda  takwas zuwa goma zaki iya gamawa toh kwanaki bakwai da zasu biyo bayan kwana uku na kammala jinin al'adar ki sune ranaku mafi hatsari gare ki idan kin fara harka domin tabbas kina iya samun ciki idan kika sake kika yi koh da wasa da lawurjen namiji ne ehee ,sai ki kiyaye kin ji koh ? Ba tare da yakaka ta fahimci mafi akasarin bayanan samy baby ba ta amsa da "toh" hankalin ta ya fi karkata ga son sanin wacce harka ce zata ɗora ta akai wacce har akwaj hatsarin samun ciki ?? Ita fa tana tsoron zancen ciki kowacce irin harka ce zata iya hakura da ita idan har zata iya yin ciki , toh amma tayaya ma ake samun cikin ?????? ( ta miƙa tambayar ga masu karatu 😂) Cikin sanyin jiki ta koma bakin aikin ta inda duk take a takure domin gani take kamar kowa ya san tana fitsarin jini bini-bini ta leƙa ta kalli bayan siket ɗin ta ,kou kuwa ta shiga bayi tayi tsarki , duk a matse take jin kan ta , sai dai tata damuwar ta kau koh kuwa ace ganin damuwa kwance ɓaro-ɓaro akan fuskar falmata ya sa ta daina jin ta ta sai wani sabon tashin hankali tare da damuwar da ta fi ta farko da taji ya mamaye ta , sam bata ƙaunar ganin falmata cikin damuwa   Falmata nah ! faɗa min menene ?? wani ne ya zage ki ? Koh baki da lafiya ne , yunwa kike ji ?? Koh kina son wani abu ne ?? Koh jiya ɗan liti ya miki wani abun da ya ɓata miki rai ne  ? Gaya min dan Allah menene     Ɗan guntun murmushin da daga ganin sa na ƙaƙale ne shi falmata ta ɗora a fuskar ta ,"     Yakaka ni babu wanda ya min kome kuma lafiyata ƙalau , bana  jin yunwa ,"       Toh meye ne koh kin tuno da su mama ne ??    Da sauri falmata ta gƴaɗa kai tana me rushewa da kukan da tuntuni yake cin ta , sakamakon abun da ya faru da ita a wurin wani mutum wanda ɗan liti ya ɗauke ta jiya ya kai ta a matsayin shine ubanɗakin sa wanda yake bashi kayan daɗin da yake kawo mata tana cika cikin ta da shi ," Ita dai bata san ina ɗan litin ya kai ta ba domin a mota suka tafi ,    Duk da cewa ba gani take ba amma ta fahimci gidan da ɗan liti ya kai ta gidan me hali ne , domin maɗaukakin sanyin da ta ji a parlour da suka tadda mutumin har zuwa kan lallausar abun da aka zaunar da ita akai kujera zata kira abun koh gado ?? Ita dai bata taɓa zama a makamancin abu mai taushin sa ba ga wani fitinannen ƙamshi da ya cika wurin , bata ji ta fara tsorata ba sai da ɗan liti ya ɗibo wani abu mai matsanancin sanyi ya cusa mata a baki da ya umarce ta da ta buɗe bakin ta zai bata wani abu wai shi "ice cream" anan ta ji ta tsorata domin kuwa dawo da abun tayi ta tofar da shi saboda bata taɓa shan abu mai tsananin sanyin irin sa ba ,"    Mutumin da suka tara a falon ya buɗe ƙatuwar muryar sa marar daɗin sauti kamar fasasshiyar  gangar  ya dunga tuntsira dariya ɗan liti yana taya sa harda shewa ,"     Watau kachallah bai taɓa shan ice cream ba ?? Ai kuwa daɗi ya bar ka , toh liti bashi gasasshiyar kaza ya ci nasan dai koh daga kan dutse ya sauko ya san nama , Wata ƙatuwar cinya ɗan liti ya fisgo ya damƙawa falmata a hannun ta bayan ya miƙa mata kwalin lemun ,"five alive" a ɗaya hannun ,     Maza ɗan kachallari ci kaza ka sha lemu yaro ai ka zo gidan arziki duk wasu kayan daɗi da nake kai maka kana ci kana lashe baki "ya tsohon kare nan ne tushen sa kaɗan ne daga cikin ire-iren kayan maƙulashen da suke jibge a gidan nan yaro saki jiki ka ci arziki ka bar shi a inda ka gan shi ,"     Cikin sanyin jiki falmata ta kai cinyar kazar bakin ta ta gutsuri kaɗan tana taunawa ," zaƙin kayayyakin ɗanɗano irin na alfarma tare da zaƙin naman kazar suka haɗu suka sa kunnen falmata motsi har bata san lokacin da ta cinye wacce ɗan liti ya bata ba ,     tana tanɗe baki ,  ɗan liti wanda suke kus-kus da wannan ɗan tsurut ɗin mutumin shi ya lura da ita ya sake fisgo ɗaya cinyar ya ɗangwala mata a hannu ,"       ungo maza cinye har ƙashin ka tauna ka haɗiye , yau ta shiga ranakun tarihi a wurin ka ɗan kachallari ," Miƙewa ɗan liti yayi bayan sun gama kitsa abun da suka kitsa ,"     Ɗan kachallari ni zan ɗan je na dawo nan kusa ka jira...    Koh kafin ya ƙarasa abun da yake nufin cewa falmata ta miƙe zuruf ta dangwarar da sauran naman hannun ta '',       Ah ah mu tafi tare nima zan bika ," Haɗa ido ɗan liti da wannan mutumin suka yi , mutumin ya yiwa ɗan liti alama da ido akan ya tafi kawai zasu yi waya ,"    Saɗaf-saɗaf ɗan liti ya fita ya jaa musu kofar wanda ƙarar rufe kofar ya sa falmata wacce take tsaye tana jiran amsar ɗan liti ta farga da barin ɗan liti wajen ,"      Kuka ta sa tare da fara taku tana nufar hanyar da ta ji motsin rufowar kofar da ɗan liti yayi lokaci ɗaya tana jera kiran sunan ɗan litin ,"   Dariya ta ji mutumin ya kwashe da ita  kafin ta ji ya fara tahowa inda take yana cewa haba ɗan kyakkyawan yaro kachalla menene abun kuka yi shiru yanzu ɗan liti zai dawo aiken sa nayi , kafin ya dawo zo muyi wasa ,"kafin ta ankara ta ji ya sure ta sama yana cewa ," A ɗaga sama anyi wa wada kwace 😂 ,"   Na so na baku ya fi haka , sai dai yawan cewa kuna jira da kuke yi , yasa na dakata anan kuyi manage da wannan sai mun hadu a shafi na gaba cikin yardar Ubangiji," A kan karo mutunci #umm'muaz #vote #comments #share with your Family and friends. [6/24, 10:59 AM] +234 701 013 7848: *© Fikrah Writers Association* *MAFARI* (hargitsin rayuwa) *Umm"mu'az* *18* Tuƙuru ɗan tsamurmurin mutumin nan yake son danne falmata , sai dai lamarin ya faskara domin daga ya samu nasarar cillata kan gadon kafin yayi wani yunƙuri ta zabura ta mike , babu abun da ya fi fusata shi da har ya kai shi ga danna mata cizo a kafaɗa irin ihun da ta buɗe maƙogoro tana yi tun karfin ta , wanda hakan ba karamin tada masa da hankali yayi ba sanin da yayi matar sa tana nan a sashin ta da yake maƙotan nasa , zata iya jin ihun falmata kuma duk irin manyan alfashan da yake aikatawa matar tasa bata kai ga sanin

Chapter 19 of 111