Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
mukulli , Kallon kallo suka yi tsakanin ta da gnala , kafin ta ratsa ta tsakanin su tana wucewa kan ta a ɗage bakin ta ɗauke da ɗan siririn murmushi ta fara rere waƙar da ta zo kan harshen ta a dai-dai lokacin   Aiki yayi kyau , tunda gida ya gyaru tsaf-tsaf ?    Allah kawo ran albashi mui fatantamawaaa . Na ku nawa ne ?  nawa kuka ɗauka a wata ɗaƴa ? In an bincika in an bibbiku da ɗai ɗai , har ma'aikatan zaria har ku na fi kowa ,  ɗan ɗan ɗaraɗanɗan .........   Da kallo suka bi ta tsaurin idanun Rakiya ba sabon abu bane a wajen su duk kuwa da cewa su sun fita daɗewa a gidan domin ita sabuwar ƴar aiki ce da ubbo ta kawo wa siyama tun daga jahar kanon nigeria .    Bata da kunya , bata kuma da tsoro ko kaɗan fallalliya ce ta ƙin ƙarawa . **** Fuskar ta babu walwala ta zuzzuba masa duk abincin da yake wajen akan wani ɗan faranti me ɗaukar ido , ta tanadar masa duk wasu abubuwan da ta san zai buƙata a wajen cin abincin ta mike tana barin wajen bata bi ta kan yumna ba wacce ta ɗau murfin wani ɗan kwano tana miƙa mata tare da yi mata gwarancin ta na yara , ta wuce ta tana nufar sama ,....    Ta ƙasan ido ya bita da kallo , ganin fushin ta a duk lokacin da maimounatu tayi masa aike ya haka ba sabon abu bane a wajen sa , siyama tana da zafin kishi shi da kan sa ya san haka , saɓanin maimounatu wacce tarin hikimar ta tare da wayo ya sa bata saurin bayyana kishin ta a fili har a fahimta ,   Shi da kan sa yana mamakin yadda ake maimouna take sanin zuwan sa maraɗi tun kafin ya iso gida ,Ko da kuwa bai sanar da kowa zuwan nasa ba , ya haka da yayi zuwan bazata , zai zo ya tarar tayo shirin tarɓar sa na musamman kamar daman ya sanar da ita zuwan sa ,  hakan ya sha faruwa ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba maimouna tana iya sanin duk wani motsin sa a cikin maraɗi , wanda shi ya ɗau hakan a matsayin tsantsar kulawa , to ina laifin wanda ya kula da lamarin ka ??      Cigaba yayi da cin abincin sa cikin nutsuwa , yana jin yadda hoton fuskar falmata ke yawo a ran sa har ya hana shi jin daɗin cin abincin so yake ya sake kallon ta, dan haka ya sake ɗaukar wayar sa ya buɗo hoton , yana sake kallo lokaci lokaci yana cin abincin sa tare da sanyawa yumna a nata bakin . Abuja Yau garin an tashi da hadari bakikkirin kafin zuwa hantsi ruwa ya fara sauƙa kamar da bakin ƙwarya , Yakaka ita kaɗai ce a gidan ƙwal , saboda samira bata kwana a gidan ba tun jiya da yamma suka fita tare da Alhaji Gali . Gaba ɗaya bata jin ɗaɗin yanayin da ta ke ciki , gidan yayi shiru dayawa duk da dai ba shi da girma sosai , zaman shirun ya sa tunaninnika yi mata dirar mikiya , cikin kwanakin nan tunanin falmata da mama ya matsanta mata , ko dan karatun da ya ɗan tsagaita mata ne ? Amma koyaushe cikin tunanin su take ,    Yaya suke ? , ta san duk sun girma Falmata yanzu shekaru ishirin ne da ita babu ƴan watanni yayin da mama ta haura shekaru biyar , Tana begen ganin su duk da cewa samy baby tana tabbatar mata da lafiyar su , a cewar ta suns waya da Rahima wacce take sanar da ita halin da suke ciki , har ma ta ce yaya doctor ya sa su a makarantu , sai dai duk da haka tana son jin ko da muryar su ne amma anty samy ta hana a cewar ta ji daga garesu zai iys kawo tsaiko ga harkar karatun ta , zata yi rauni ta gaza maida hankali ga karatun ta , da jin hakan ya sa ta haƙurewa jin su , Ta bari har sai bayan kammaluwar karatun ta da samy baby ta mata alƙawarin zasu tafi maidugurin tare kamar yadda ta ɗauko ta ƙafa-da-ƙafa , ta je ta taya ta wanke kan ta a wajen falmata , yaya doctor , rahima da ma baba , ƙarshe kuma ta rungumi ƴar ta da ƙanwar ta su dawo tare nan .! Duk da cewa a farkon zaman su da samy baby ta kasa sakin jiki da ita ganin irin yAudarar da tayi mata ta rabo ta da maiduguri da ƴar uwar ta , sai ta kasance cikin ɗari-ɗari da ita tana tunanin ko zata yi yunƙurin cutar da ita sai dai abunda ya sa ta saki jiki bai wuce yadda lokaci yayi ta tafiya ba tare da ta ga wani sauyi na gallazawa , tilastawa ko ɓatanci daga samy baby ba ,sai ma hidima da take yi da ita tare da kyautata mata fiye da zaton ta , Tsawon shekaru biyar da suka yi tare samy baby ke ɗauke da nawin duk wasu buƙatun ta na yau da kullum , cin ta shan ta suturar ta kuɗin magani da na karatun ta duk ta dalilin samy baby ta same su kuma masu kyau masu inganci da suka taimaka mata ƙwarai ta fannin yin rayuwa me cike da inganci da isasshiyar lafiya tare da nasarar kammala karatun ta , Dan haka a sannu sannu samy baby ta mantar da ita girman laifi tare da yaudarar da tayi mata , a ƙarshe ta sake shirya mata sabuwar ƙaryar cewa suna waya da rahima , falmata da mama suna lafiya , wanda a zahiri ba gaskiya bane , hasalima rabon ta da shiga maiduguri ita ma ya doshi shekaru huɗu , kuma bata tare da number rahima , ba ta ma sake biyawa ta kan rayuwar bayin Allah biyun da ta raba su da garkuwar su ba , Ta tsara haka ne saboda yakaka ta sau jiki ta zauna tare da ita , yadda gaba zata cimma manufar ta hankali kwance ba tare da yakaka ta sake tayar mata da bori ba ! Sai dai kamar yadda suka alƙawarta lokaci ya zo da zasu maiduguri , idan ya so bayan dawowar su sai ta shiga jami'a kamar yadda samy baby ta sake ƙwaɗaita mata a cewar ta jami'a shine mataki na gaba da ya dace da yakaka , duk a ƙoƙarin ta na son janye ta zuwa kan turba irin ta ta , da take ganin fa a yanzu lokaci yayi . Ƙofar da ake bugu da ɗan ƙarfi ya sanya ta firgita ta dawo daga nisan tunanin da ta tafi . Duban agogo tayi ta ga ƙarfe goma sha biyu na rana ,   Fitowa tayi da nufin zuwa ta buɗe ƙofar da take hasashen dawowar samy baby .    Har lokacin ana yayyafi yif-yif da alamun yau yinin na marka-marka ne .      Da ɗan gudun ta ta ƙarasa bakin ƙofar ta zare sakatar ƙofar ba tare da ta waiwaya ba ta juya da gudun kar ruwan sama ya taɓa ta tana cewa    Sannu da zuwa anty samy .    Sai da ta tsallaka kan Balcony tukun ta juyo ,      A tsorace ta kai duban ta ga mutumin da yake tsaye a maimakon samy baby ,     Saurayi ne dogo wankan tarwaɗa yana tsaye ya zura hannun sa cikin wondon jikin sa , idanun sa sakaye cikin wani kwafcecen baƙin gilashi da kallo ɗaya za'a masa a fahimci rangwamen mutumcin dake tare da shi .    Juyawa tayi da sauri ta tura ƙofar falon ta shiga sabods tunowa da tayi da riga da wondon da suke jikin ta na bacci da duk da cewa basu kama ta ba ko kaɗan amma kaya ne masu tsantsi.    Kai tsaye ta shiga ɗakin ta ta fara bincikar hijabin ta ,    Sai dai hannun da ta ji ya sauƙa a ƙafaɗar ta ya sa hantar cikin ta kaɗawa ,   Da sauri ta jaa baya har tana gwaruwa da jikin wardrobe ,   Idanun ta ya shiga cikin na saurayin da ta bari a waje ,     Anty samira bata nan ta furta haka , muryar ta na karkawa , lokacin da take ƙoƙarin zira hijabin da ta samu nasarar ɗauka ,    Riƙe hajibin yayi da hannun sa ɗaya , yayi amfani da ɗayan hannun sa wajen zare gilashin idanun sa , mitsitsin jajayen idanun sa da suka sake shigewa ciki-ciki suka bayyana , yana bin ta da wani shu'umin kallo    Da muryar sa irin ta mashaya , yace   Wa yake ta samira tsahuwar guzuma ?    Ga kamar ki gorgeous , ya ƙarasa zancen yana kai hannu zai taɓa kumatun ta ,    Da ƙarfi ta make hannun sa gami da saurin zura hijabin ta ,    Ni ba ƴar iska ba ce kar ka sake taɓa ni , ka fita min daga ɗaki ,   Ɗan baya ya jaa yana yarfe hannun sa da ta buge bakin sa a ɗan buɗe alamun mamaki ,    Baby har da duka ?? Bata kula shi ba ta haura ta kan gadon ta ta dira tana nufar ƙofa , sai dai taku biyu kawai tayi ta ji ya kamo ta ta baya ya haɗa bayan ta da ƙirjin sa ya ɗaga ta ciɗak , ya shiga juyi da ita ,     To tunda wasan tsale tsalle kike so bari na miki hajijiyar ƙauna .     ya furta haka yana ɓaɓɓaka dariya . Tun ƙarfin ta ta fara ihu tana wutsil-wutsil da kafafu tare da ƙoƙarin son ɓanɓare hannun sa da ya zagaye cikin ta da shi , A guje samy baby da tun a tsakar gida ta fara jiyo ihun yakaka ta ƙaraso cikin ɗakin .     Kai kamal meye haka ?  kayi hauka ne ?? Dallah sauƙe ta .    Ba tare da ya sauƙe ta ba ya ce   Ke dallah kauce ki ɗan sakayo mana ƙofa zamu buga ƙwallo ne ni da wannan me zafin kan da tayi gigin duka na .   Ƙarasowa tayi ta jaa hannun sa ,    Kamal kar muyi haka da kai dan Allah ka sauƙe ta , ƙanwa ta ce fa , yaushe muka fara ƴar haka da kai mutumina ??   A hankali ya sassauta rikon da yayi mata kafin ya sake ta tana jin ya ajiye ta ta fita a guje , ƙafafun ta ko takalmi babu ,   Kallon baka kyauta ba samy baby ta wurga masa kafin ta ja ƙaramin tsaki , Kai dai kamal anyi tantiri ɗan iska , to bari na faɗa maka wannan haja ce me matuƙar tsada ba irin taku ba ce domin kuwa sabuwa ce fil , ba'a riga an shiga kasuwa da ita an daka mata wawa ba ,    Ba ta wasa bace na san a ɗan abunda ya shiga tsakanin ku a yanzu kaɗai ,laushin fatar ta da ka taɓa ya isa sanar da kai irin maɗuɗan da zasu taho ta hanyar ta muddin ta shiga kasuwa .      Ƙafar sa ɗaya dake sanye da wani ƙwamemen takalmi sau ciki ya ɗaga yana tokare ta da jikin gadon yakaka . Ni kuma kin san maƙudan da kike faɗa ba matsala ta bane , ko ruwan su kike so nayi miki kin san zan iya , muddin zan mayar ƙwaɗayi na akan wannan nunanniyar gwandar , nawa kike sa mata kuɗi ??   Two Million Naira    Ta furta cikin gatsali Bani account number da zan zira miki su ,      A ɗan jirkice ta dube shi cikin ran ta tana son ƙure shi , domin kuwa duk da sanin da tayi wa kamal na shahararran ɗan masu hali da iyayen sa suka gama gurɓata tarbiyyar sa , ya zama tamkar ɗan taure wajen bibiyar mata , manya da ƙanana kyakkyawa da mummuna shi baya zaɓe kawai dai idan ran shi ya biya ya samu ya maida mugun yawu shikenan kuma bai ƙara bi ta kan mace , bata zaton wasan sa da kuɗi ya kai ya haka .    A ɗage ta karanto masa account number da suna , cikin abunda bai gaza mintuna biyu ba sai ga wayar ta dake cikin jaka ta ɗau ƙara , Jikin ta na mazari ta fiddo wayar ta duba ,    Alert  ne na adadin kuɗin da ta buƙata cif .     Ɗan wara ido tayi da sigar mamaki , sai kuma ta kaɗa idon cikin yanayi na shanye mamakin ta irin na gogaggun matan bariki .     Babu shakka ka ɗau haja me girma , kuma na san baza ka yi wadarai da ita ba , yaushe kake buƙatar ta ?    Haɗe fuska yayi kafin ya watsa hannu    Ka duba wannan da wata maganar iska ? Irin waɗannan kuɗaɗen da na cire har sai kin min iyaka da ita ? Ai yadda ta sani haɗiyar mugun yawu dole daren yau na fanshe kuɗi na , daman ga gari ya ɗau sanyi yanayi ne na shiga daga ciki da sauri . Ta saki Wata dariyar da take bayyana farin cikin ta akan kuɗaɗen da ta samu da dama tana tsakiya da buƙatar su ,    Alhaji kamalu ,  to baka da damuwa ,  yanzu ka tafi , sai ka aika mun address ɗin da kake son na kai maka ita ni da hannun na zan miƙa maka ita anjima da dare ,   Kasan na faɗa maka sabuwa ce bata harkar nan to sai na maka yaƙin shawo maka kan ta , Ɗaga kafaɗa yayi cikin nuna halin ko oho ,      Ni dai ki tabbatar kin mata Wankan irin yadda ya kamata    Ya ƙarasa zancen yana kashe mata ido ,     Alhaji kamalu , kar ka ji kome .daren yau na kai ne a sama . Yakaka wacce take zaune dirshan a cikin ruwan sama ta jikin bangon ɗakin ta ta baya  ,   Ta kai hannuwan ta duk biyu ta toshe bakin ta a ƙoƙarin ta na hana kukan da take fitowa sarari kar su samy baby su ji , kamar yadda duk zantukan su ya ratsa kunnuwan ta .   Ashe daman anty samy yaudarar take akan kome , ashe burin ta ta tsundumata cikin irin rayuwar da tunda ta fahimci girman saɓon da ake aikatawa ta hanyar zina take yi mata addu'ar Allah ya sa ita ma ta tuba ta daina , Manufar ta ashe ta mayar da ita ga aikata zunubin da tayiwa ubangijinta Alƙawarin ta daina baza ta sake ba ! Ƙuka take da hawaye wani na korar wani , tana jin yadda tsoro ke mamaye ran ta , tsoron kowa da kome , tsoron sake yin zina ta hanyar tirsasawa , Takurewa tayi ta sanya fuskar ta tsakanin ƙafafun ta , sanyin ruwan da ya ɗan sake dawowa da ƙarfin yana ratsa ta ta hanyar jiƙa kayan jikin ta . Assalamu Alaykum . Gaisuwa tare da fatan Alkhairi a gare ku baki daya! Nagode.                  Fikra writers association MAFARI ( Hargitsin Rayuwa) umm'muaz 34 Fiye da awa ɗaya Samy baby ta kwashe tana shirya Yakaka , wacce ta sha fama da kanta kafin ta iya tsayar da hawayenta batare da bari Samy baby ta fahimci cewa ta san manufar ta ba , Wacce ta shagaltu wajen shirya ta tana jaan ta da hirararrakin da suka shafi jin daɗin duniya , wankan da kansa so tayi ta wanke ta sai dan ganin ba fuska ya sanya ta tsayawa daga bakin ƙofar banɗakin tana sake jaddada mata ta fa yi wankan nan siral ta fita , domin inda zasu tafi waje ne na manyan ƴan gayu kar ta sake tayi abinda zata jawa kan ta raini ,   Daga cikin banɗakin nan ta ci kukan ta a ƙarshe ta tattara duk wani tunani nata da Allah ya mata baiwar sa ,ta matse ƙwaƙwalwar ta, ta haɗa kai da bango akan tunanin hanyar da zata bi ta samarwa da kan ta mafita . Ƙarfe baƙwai na dare suka fita a motar Samy baby dukkanin su sun ɗau kwalliyya ta gani a faɗa , Duk da fuskar Yakaka a tamke take da bayyanannen ɓacin rai hakan bai hana kyaun da tayi ratsowa ba , dai-dai tana karya kan motar ta fito kan titi sosai Samy baby ta dubi sashin Yakaka a kaikaice ,    Yanzu ke Yaks meye haka ? Dan asara akan na hana ki saka wannan uban barigizan hijabin naki shine kike wannan ƙuncin ? Mts! Ji wannan ƙatuwar jakar da kika ɗauko kamar wata wanzamiya na faɗa miki bata dace da ƙwalliyar nan ba , ƙwalliyar nan taki ba ta babbar jaka bace ta ƴar ƙaramar jakar hannu ce amma kin ƙi ji , ai daman ɗan ƙauye sai ya shekara hamsin a birni yake barin ƙauyenci da gidadanci , ke kika sani sautun mahaukaciya ! Ta danna motar da gudun gaske suka cilla kan titi cikin manyan unguwannin abuja da ko sau ɗaya Yakaka bata taɓa kai ƙafar ta bigiren ba tun zuwan ta garin . Bata cewa samy ƙala ba illa sake rungume jakar ta da tayi wanda a ciki ta saka hijabinta da niƙab ɗin ta , ƙwaƙwalwar ta a hargitse take da sabon tsoron da yake mamayar ta , Ƙofar wani tafakeken gida samy baby ta tsaya tare da zaro wayar ta ta latsa lamba , bugu ɗaya ya ɗauka Gamu mun iso tace tare da sauƙe wayar daga kunnen ta , ba'a yi mintuna uku ba sai maigadi ya buɗe musu ƙofar gidan , samy baby ta danna kan motar a hankali shigar su gidan yazo dai-dai da ƙaruwar firgici a fuskar yakaka , saboda girman gidan da ya wuce hankalin ta ga fitulu da suke a watse birjik a harabar gidan haske ya wadata tamkar tsakar rana , Gefen wasu tsirarun motoci da basu wuce guda shida ba samy baby ta ajiye motar ta , Muje Yaks , A tsorace ta fito tana bin gidan da kallo , ba tare da samy baby ta kula ta ba tayi gaba , cikin jaan ƙafafu ta bita a baya maƙale da jakar ta , suka dumfari katafaren ginin da yake tsaye a gaban su , Babu yalwar mutane a babban ɗakin hutawar da suka shiga ,  mata da mazan da suke harkokin su a wajen babu wanda ya kula su , Samy baby ta jagorance su suka zauna , basu jima da zama ba aka murɗo ɗaya daga cikin ƙofofin da suke ta cikin falon aka shigo , Kamal ne ya shigo yana ɗan gama hanya ya ƙaraso tare da sakin jiki ya faɗa kan kujerar kusa da yakaka , rigijib ! a tsorace ta miƙe tana raba ido .    Idanun sa da suka yi nawi saboda kayan mayen da ya ɗibga ya ɗaga ya watsa mata wani kallon ƙasƙanci , Ke wai ji mana , ya kike wani safurewa haka kina wani ƙoƙarin waskewa , ?  Kamar baki da sanin cewa na biya kuɗin ki , zo nan na fara  morar kuɗi na dallah Ya miƙa hannu ya fisgota ta koma da ƙarfi ta zauna , Ganin sa ya mayar kan Samy baby Yane to yawa kike fa,  Zaman me kike ?  Ko kina neman me tayi ne ? Nan duk suna da chicks ɗin su dan haka ki ƙara gaba ,.. Ke kuma zo muje ki fara tausa min gaɓɓai da waɗannan tausasan hannuwan naki tuɓus-tuɓus , wayyo laushi!      Ya fisgi hannun Yakaka suka miƙe tsaye , Fuskar samy baby ta kalla , idanunsu suka gauraya cikin na juna ,   Ga mamakin samy baby ba kamar yadda ta zaci zata ga hawaye a idanun yakaka ba , saɓanin ta idanun ta a bushe suke ƙyamas ,ɗauke da wani irin yanayi wanda yayi tasiri ƙwarai wajen rage mata kuzarin tashi ta bar gurin kamar yadda aka mata umarni , Kallon da yakaka take mata kallo ne me kaifi da yake ɗauke da fasasarori da dama ,wanda ta gaza ɗaukar masa fassara guda ,  tana ganin lokacin da ta fisge hannun ta daga cikin na kamal ɗin ta nufi ƙofar da ta ga ya nufa da ita , ba tare da ta sake waiwayowa gare ta ba , A sanyaye ta miƙe cikin ran ta tana harhaɗa kalmomin da zata yi amfani da su wajen kalmaso kan yakaka ta rarrashe ta kamar yadda ta saba yi mata a duk lokacin da tayi mata wani gagarumin laifi , gefe guda tana tunanin ware wani kaso me ɗan tsoka daga cikin kuɗin da kamal ɗin ya bata ta danƙa mata su duk domin su taimaka wajen  shawo kan ta cikin sauki.   Da wannan tunanin ta faɗa motar ta bar gidan tana duban agogon hannun ta da yake nuna ƙarfe tara saura ƴan mintoci , sama ta haskaka da hadarin da yake haɗuwa da ke nuni da koyaushe cikin dare ruwa zai iya sauƙa . Kar ka kuskura ka sake taɓani , Ta ce da shi lokacin da take samun wajen zama bisa kan kujerar gaban tafkeken gadon ɗakin na alfarma .   Wata dariya ya kwashe da ita yayi sufa ya faɗa gadon rubda ciki .    Kai yarinyar nan salon ki na burge ni , wat....    Zan sha BURKUTU , Ya tsinkayi muryar ta ta katse masa kalaman sa , waigowa yayi yana daga kwance ya dube ta , fuskar sa na bayyana mamaki yace : Burkutu ? Eh tace da shi tana tsattsare shi da idanun ta , Ni bana shan giyar gargajiya ,"blue moon ," ita ce giyar da nafi ƙauna , yanzu ma ita na sha ƴar kaɗan , kin san tana da ƙarfi shegiyar giya ce , ko za ki iya sha na zubo miki kaɗan ki taɓa irin ta ? Kawo min ta ce da shi a taikaice . Miƙewa yayi ya fita Yana fita ta miƙe tsaye ta shiga kai kawo a ɗakin tana yarfe hannu , da tayi zaton zata iya , a zaton ta tana da ƙarfin zuciya , ya kome yake shirin kufce mata ? Me zai faru da ita idan har shirin ta bai tafi dai-dai ba , ??   Jin motsin taɓa ƙofar ya sa tayi saurin komawa ta zauna , Ya shigo hannun sa ɗaya riƙe da kwalbar giyar blue moon ɗaya kuma kofin gilashi da ya zubo ƴar ƙanƙara a ciki , Zuba giyar yayi ƴar madaidaiciya ya miƙa mata ,   Idanun ta na duba ƙasa ta ce da shi ka fara sha , Jim yayi riƙe da kofin sai kuma ya kai bakin sa ya ɗan kurɓa , Ya Sake miƙa mata , Ka cika min taf Tace da shi ba tare da ta bari sun haɗa ido ba , Keeeee hahaha , wannan fa blue moon ce ba'a mata haɗama yanzu nan za ki ji ki warwas kin gaza motsi, ba ta wasa bace wannan , ke kin san kuɗin ta kuwa ? Yafi jarin baban ki . Bana shan wannan , warin ta bai min daɗi ba ka kawo min wata idan akwai , nafi son wacce zata ƙara min kuzari ,   Ɓata rai yayi !  ya tsaya kallon ta  sai kuma ya kwashe da wata dariyar sakarci , Tunda ta ƙara kuzari kike nema bari na kawo miki Amstel kina shanta yau ji za kiyi kamar an miki allurar da ake yiwa dawakai ,    Ya ƙarasa zancen yana kafa kai ya sha fiye da rabin wacce ya zuba a kofin ya ajiye sauran ya fita yana gama hanya tare da jaan wani siririn fito irin na wanda duniya ta yiwa daɗi . Yana fita ta miƙe tare da murɗa ƙofar ta fito , ɗan yawatawa tayi da idanun ta cikin daƙiƙoƙi ta fahimci ɗaukewar ƙafar da ya ƙaru a wajen domin mutum ɗaya ta hango a zaune ya tasa kwalaban giya a gaban sa , Da sassarfar da take harɗe kafafun ta ta taka tana nufar ƙofar ficewa daga wajen bakin ta ɗauke da addu'o'i iri-iri ,    Siit ji mana , ? Numfashin ta ya

Chapter 60 of 111