ka isso lafiya ?
Lafiya mun same ku lafiya ? Yaya Yumna ?
Ga ta tana lafiya ,
Ɗan shiru suka yi kafin ya katse shirun da tambayar ta
Ina kuke da noufin zouwa da hantsi hakka ??
A ɗan ruɗe tace , zamu shiga fada gaishe da hajiya umma ,
Baza ku fita yanzou ba umma na tare da jama'a da wannan lokacin bani son idanun jama'a bisa ga kan ɗiya ta , ko dai ki bar ta ki tahi ke ɗai , ko kuwa ki bari da sanyin la'asar kun tahi tare .
Ko kusa baza ta so ƴar ta ta gifta ta kurkusa da shigifar gimbiya moumuna ba bare har ta taka ƙafafun ta cikin wani al'amari da ya gifta a tsakanin su me girma , wanda ya tarwatsa takaitatcen zaman daɗin da suka fara gudanarwa a tsakanin su , daga nan aka yi walƙiya kowa ya shaida kowa , yayin da daga lokacin ta fara bin irin takun gimbiya moumuna da nazari , nan ta fahimci dayawa daga cikin boƴaƴƴun fuskokin ta masu cike da abubuwan al'ajabi tare da sarƙaƙiya da baki yayi kaɗan wajen furta su ga wani har sai idan wannnan mutumin ya ga kome a idanun sa .
Hakan ya sa ta rufe kome ta haɗiye a cikin ta , ta kuma killace kan ta da ɗiyar ta daga gimbiya moumuna da ƴan barandar ta doumin ita ɗin ai gubba ce ga rayukan alhalin masarautar maraɗi !
Da sauri ta miƙa hannu tana ƙoƙarin amsar ƴar ta daga gare shi
Mun hakure zouwa yammaci kamar yadda ka faɗi mouna Biyamuradi .
Janye yumna yayi ya hana ta ɗaukar ta , a hankali ya kamo hannun tare da sarƙafe ƴan yatsun sa a cikin nata hannun yana jin yadda taushin hannun ke tado masa da yanayin da yake ta dannewa tsawon satika , " muryar sa tafe da amo marar ƙarfi yace
Mu tai ki ciyar da ni abounci na taho tare da yunwa me tsanani .
Ƙoƙarin zare hannun ta take tana satar kallon sashin gimbiya maimouna ,
Cikin sa'a idanun ta ya sauƙa akan gnala shugabar bayin sashin gimbiya moumuna ta na abunda yake goge gilashin falon gimbiyar ta ciki a zahiri , wanda tashin farko siyama ta fassara abunda take da ɗaukar rahoto
Toh Biyamuradi , amm...
Shitt
yace mata lokacin da yake jan hannun ta zouwa sashin sa kai tsaye da yumna saɓe kan kafaɗar sa ta dama tana ƙoƙarin ɗauke hular kan sa ,
Suka fara taku tare da masaniyar yau wajen ta ya kamata ya kwana a tsarin ƙwanakin girki .
Gimbiya moumuna wacce tun isar sa fada ta samou labarin zuwan sa , inda bata yi ƙasa a guiwa ba ta tashi shirin tarɓar sa ,
Ta tashi hankulan bayun ta da aikin gyara gida wasu kuma na haɗa mata ruwan wanka tare da fidda mata kayan da zata sanya a jikin ta ,
Zuwa shigowar sa gidan ta fito daga wanka ta fara shiri , yana dosar gidan saƙo ya iso mata , hakan ya sa ta miƙe daga gaban mudubi ta ƙarasa gaban babban window na ɗakin ta dake sama ta raba labulen biyu daga inda take ta hangi kome da ya wakana tsakanin sa da siyama .
Wani irin tuƙuƙi take ji yana taso mata daga cikin rai har tana jin ɗacin sa a maƙogoro .
Meyasa ne wankin hula ya kai ta ɗare har tsakiyar sa ?? Lamarin da suka yi hasashen yiwuwar sa a watanni zuwa
Shekara bayan zuwan ta masarautar maraɗi , sai ga shi shekaru har sun fara ƙoƙarin haurawa kirgen yatsu biyar ?? Wacce iriyar mummunar rashin sa'a ne gare su haka ?? Wanne sirri ne da yake boye cikin duhu da ya zamto shamaƙin da ya shiga tsakanin ta da cikar burin ta ?? Menene shi da ya wuce tasirin ƙarfin su ??
Tattare labulen tayi ta cukuikuye shi a tafin hannun ta tana jin kamar tayi girgiza ta fasa bango ta dira a sashin yarima youssouf ta kaddamar da manufar ta ..
Ranki ya daɗe kƴakya.....
Bata bari gnala ta ƙarasa kalmomin ta ba wacce ta shigo ta durƙusa daga bayan ta ,
Da hannu ta dakatar da ita ,
Ayi gaugawar shiryawa Biyamuradi abincin sa a aika da shi shiyar sa .,
Ke zaki miƙa abincin da kan ki daga nan kin kawo mi ni labari na lamarin da ya auku gaba gare ki .
Allah ya huci ran gimbiya ƴar sarkin nahiyar mu maigirma oumarnin ki shine abun bi .!
da shigar su sashin nasa da yake me matuƙar girma , da tsari tare da wadatar tsaftar da ta haifar da kyakkyawan yanayi a wajen ,
Ya zauna bisa ɗaya daga cikin kujerun falon nasa , yana sauƙe yumna kan kafafun sa ,
siyama wacce ta saɓule mayafin ta ta ajiye a gefe ta sunkuya tare da yin gurfano a gaban sa , cikin nutsuwa ta kai hannuwan ta tana kunce masa igiyar takalmin sa tare da zare masa shi a hankali ,
Ɗan kiɗan da wayar sa ta yi dake nuna alamun shigowar saƙo ya sa shi zaro wayar daga aljihun sa ,
Lokacin da take ƙoƙarin karɓe hular sa dake hannun yumna ta ƙi bada hular ,
Ki bar mata hular mana , kin ka sani ko ɗiya tayi gadon baban ta ?
Da murmushi bisa fuskar ta ta wuce sama domin ajiye masa takalman sa , ta zo ta fara yi masa shirin girki .
Saƙon gimbiya maimouna ne mai ɗauke da tsararrun kalamai na barka da zuwa ƙarshe take sanar da shi ta bada saƙo a kawo masa ,
Fita yayi daga wajen adana saƙon yana shirin ajiye wayar hoton da ya ɗauke su ɗazu ya bayyana a fuskar wayar,
Ƴan yatsun sa ya sa ya jawo hoton ya cika wayar ya na nutsar da idanun sa kan fuskar ta me ɗan haske kaɗan da take ɗauke da wani sirri me tasirin da ya zarce a ƙira shi kyau ,
fatar ta suɓul-suɓul babu wasu ƙurarraji bare tabbuna manyan idanun ta da yankan su yake a tsaye da ƙwayar baƙi na cikin su me girma ne sosai , suna da ɗaukar hankali ta yadda ko yaya ta juya su sai mutum ya gan su , har kullum yana dogon tunani akan son sanin me ya makanta su ??
A hankali yayi ƙasa da hoton zuwa kan bakin ta da haƙoranta suke a buɗe tana dariya ,
Tsintar kan sa yayi da murmusawa, ya kai babban ɗan yatsan sa yana shafar fuskar wayar daidai zagayen ɗan bakin nata ,
lokacin da ya tuno da yadda take haɗe fuska ta tsuke bakin , duk idan ta ji motsin sa a waje , ta takura kan ta ta gaza walwala ,,
Kiyi haƙuri fatima ni ma ba zaɓi na bane irin rayuwar da muke gudanarwa a tsakanin mu a matsayin ki ta iyalina ,girman laifi na ya sa na gaza yin wani yunƙuri , ni ɗin me laifi ne a gare ki da duk ranar da gaskiya ta bayyana wataƙila baza ki yafe min ba , hakan ya sa na jinkirta miki har zouwa lokacin da kome zai bayyana agare ki , da na tabbatar ranar ta na zouwa , lokacin kike da zaɓi na zama da ni ko bari na bisa ra'ayin kan ki ,
Kiyi haƙuri Fatima zahra ina jin kunyar ki .
Ƙwanƙwasa ƙofar da aka yi ya sa shi kai duban sa ga ƙofar tare da mayar da wayar sa cikin aljihu
Daidai da ƙarasowar siyama wajen wacce kalaman sa na ƙarshe suka sauƙa cikin kunnuwan ta ,
Suka yi sanadiyyar harɗewar takun kafafun ta tare da sa zuciyar ta yin tsalle .
Wacece fatima ? Wanne matsayi ne gare ta da har Biyamuradi ke neman afouwar ta ? Shin laifin me ya aikata mata ?
Ruɗanin da ta afkawa ya hana ta tsinkayar kalaman da yake mata sai da ya ɗan ɗaga muryar sa da ƙarfi .
Siyama ki buɗe kofar nan saƙon maimounatu ne ya iso ,
Ba tare da ta amsa ba ta taka tana nufar ƙofar , cikin ran ta damuwa goma da ishirin ta san sarai saƙon ko na menene, abunda maimounatu ta saba yi mata ne a koyaushe , shine yau ma ta maimaita .
Tana buɗe ƙofar tayi arba da gnala tare da wasu bayu biyu hannuwan su riƙe da manyan farantai da aka rufe su da tumaƙasa irin na alfarma ,
Ajiye faranta suka yi tare da yin gurfano a gaban ta ,
Ranki ya daɗe barka da fitowa ! saƙo ne daga gimbiya tace a shigar da kaɓaki ga maigirma yarima .
Fuskar ta a ɗaure ta ce
Ki je sashi na yanzu yanzu ki ƙira min Rakiya ku zo tare !
Da sauri Gnala ta miƙe
Ba ke ba .
Tace da kaushin murya
Ciki sauri ta koma ta tsugunna
Ke tashi ki je ki taho da Rakiya
Tana nuni da ɗayar baiwar .
Cikin ƙasa da mintuna uku sai ga su tare da wata yarinyar mace da zata iya zuwa sa'a ga siyamar ,
Ranki ya daɗe uwargijiya ta .
Rakiya ki ɗauko waɗannan farantan ki biyo ni da su ,
Ta furta haka tana juyawa ciki Rakiya ta bita ɗauke da faranti guda , kafin ta dawo ta ɗau sauran da ɗai ɗaya ta shiga da su ,
Tana gama shigarwa ta fito gami da jan ƙofar , tana iya jiyo lokacin da uwargiyar ta ta murza ɗan mukulli ,
Kallon kallo suka yi tsakanin ta da gnala , kafin ta ratsa ta tsakanin su tana wucewa kan ta a ɗage bakin ta ɗauke da ɗan siririn murmushi ta fara rere waƙar da ta zo kan harshen ta a dai-dai lokacin
Aiki yayi kyau , tunda gida ya gyaru tsaf-tsaf ?
Allah kawo ran albashi mui fatantamawaaa .
Na ku nawa ne ? nawa kuka ɗauka a wata ɗaƴa ?
In an bincika in an bibbiku da ɗai ɗai , har ma'aikatan zaria har ku na fi kowa , ɗan ɗan ɗaraɗanɗan .........
Da kallo suka bi ta tsaurin idanun Rakiya ba sabon abu bane a wajen su duk kuwa da cewa su sun fita daɗewa a gidan domin ita sabuwar ƴar aiki ce da ubbo ta kawo wa siyama tun daga jahar kanon nigeria .
Bata da kunya , bata kuma da tsoro ko kaɗan fallalliya ce ta ƙin ƙarawa .
****
Fuskar ta babu walwala ta zuzzuba masa duk abincin da yake wajen akan wani ɗan faranti me ɗaukar ido , ta tanadar masa duk wasu abubuwan da ta san zai buƙata a wajen cin abincin ta mike tana barin wajen bata bi ta kan yumna ba wacce ta ɗau murfin wani ɗan kwano tana miƙa mata tare da yi mata gwarancin ta na yara , ta wuce ta tana nufar sama ,....
Ta ƙasan ido ya bita da kallo , ganin fushin ta a duk lokacin da maimounatu tayi masa aike ya haka ba sabon abu bane a wajen sa , siyama tana da zafin kishi shi da kan sa ya san haka , saɓanin maimounatu wacce tarin hikimar ta tare da wayo ya sa bata saurin bayyana kishin ta a fili har a fahimta ,
Shi da kan sa yana mamakin yadda ake maimouna take sanin zuwan sa maraɗi tun kafin ya iso gida ,Ko da kuwa bai sanar da kowa zuwan nasa ba , ya haka da yayi zuwan bazata , zai zo ya tarar tayo shirin tarɓar sa na musamman kamar daman ya sanar da ita zuwan sa , hakan ya sha faruwa ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba maimouna tana iya sanin duk wani motsin sa a cikin maraɗi , wanda shi ya ɗau hakan a matsayin tsantsar kulawa , to ina laifin wanda ya kula da lamarin ka ??
Cigaba yayi da cin abincin sa cikin nutsuwa , yana jin yadda hoton fuskar falmata ke yawo a ran sa har ya hana shi jin daɗin cin abincin so yake ya sake kallon ta, dan haka ya sake ɗaukar wayar sa ya buɗo hoton , yana sake kallo lokaci lokaci yana cin abincin sa tare da sanyawa yumna a nata bakin .
Abuja
Yau garin an tashi da hadari bakikkirin kafin zuwa hantsi ruwa ya fara sauƙa kamar da bakin ƙwarya ,
Yakaka ita kaɗai ce a gidan ƙwal , saboda samira bata kwana a gidan ba tun jiya da yamma suka fita tare da Alhaji Gali .
Gaba ɗaya bata jin ɗaɗin yanayin da ta ke ciki , gidan yayi shiru dayawa duk da dai ba shi da girma sosai , zaman shirun ya sa tunaninnika yi mata dirar mikiya ,
cikin kwanakin nan tunanin falmata da mama ya matsanta mata , ko dan karatun da ya ɗan tsagaita mata ne ? Amma koyaushe cikin tunanin su take ,
Yaya suke ? , ta san duk sun girma Falmata yanzu shekaru ishirin ne da ita babu ƴan watanni yayin da mama ta haura shekaru biyar ,
Tana begen ganin su duk da cewa samy baby tana tabbatar mata da lafiyar su , a cewar ta suns waya da Rahima wacce take sanar da ita halin da suke ciki , har ma ta ce yaya doctor ya sa su a makarantu , sai dai duk da haka tana son jin ko da muryar su ne amma anty samy ta hana a cewar ta ji daga garesu zai iys kawo tsaiko ga harkar karatun ta , zata yi rauni ta gaza maida hankali ga karatun ta , da jin hakan ya sa ta haƙurewa jin su ,
Ta bari har sai bayan kammaluwar karatun ta da samy baby ta mata alƙawarin zasu tafi maidugurin tare kamar yadda ta ɗauko ta ƙafa-da-ƙafa , ta je ta taya ta wanke kan ta a wajen falmata , yaya doctor , rahima da ma baba , ƙarshe kuma ta rungumi ƴar ta da ƙanwar ta su dawo tare nan .!
Duk da cewa a farkon zaman su da samy baby ta kasa sakin jiki da ita ganin irin yAudarar da tayi mata ta rabo ta da maiduguri da ƴar uwar ta , sai ta kasance cikin ɗari-ɗari da ita tana tunanin ko zata yi yunƙurin cutar da ita sai dai abunda ya sa ta saki jiki bai wuce yadda lokaci yayi ta tafiya ba tare da ta ga wani sauyi na gallazawa , tilastawa ko ɓatanci daga samy baby ba ,sai ma hidima da take yi da ita tare da kyautata mata fiye da zaton ta ,
Tsawon shekaru biyar da suka yi tare samy baby ke ɗauke da nawin duk wasu buƙatun ta na yau da kullum , cin ta shan ta suturar ta kuɗin magani da na karatun ta duk ta dalilin samy baby ta same su kuma masu kyau masu inganci da suka taimaka mata ƙwarai ta fannin yin rayuwa me cike da inganci da isasshiyar lafiya tare da nasarar kammala karatun ta ,
Dan haka a sannu sannu samy baby ta mantar da ita girman laifi tare da yaudarar da tayi mata , a ƙarshe ta sake shirya mata sabuwar ƙaryar cewa suna waya da rahima , falmata da mama suna lafiya , wanda a zahiri ba gaskiya bane , hasalima rabon ta da shiga maiduguri ita ma ya doshi shekaru huɗu , kuma bata tare da number rahima , ba ta ma sake biyawa ta kan rayuwar bayin Allah biyun da ta raba su da garkuwar su ba ,
Ta tsara haka ne saboda yakaka ta sau jiki ta zauna tare da ita , yadda gaba zata cimma manufar ta hankali kwance ba tare da yakaka ta sake tayar mata da bori ba !
Sai dai kamar yadda suka alƙawarta lokaci ya zo da zasu maiduguri , idan ya so bayan dawowar su sai ta shiga jami'a kamar yadda samy baby ta sake ƙwaɗaita mata a cewar ta jami'a shine mataki na gaba da ya dace da yakaka , duk a ƙoƙarin ta na son janye ta zuwa kan turba irin ta ta , da take ganin fa a yanzu lokaci yayi .
Ƙofar da ake bugu da ɗan ƙarfi ya sanya ta firgita ta dawo daga nisan tunanin da ta tafi .
Duban agogo tayi ta ga ƙarfe goma sha biyu na rana ,
Fitowa tayi da nufin zuwa ta buɗe ƙofar da take hasashen dawowar samy baby .
Har lokacin ana yayyafi yif-yif da alamun yau yinin na marka-marka ne .
Da ɗan gudun ta ta ƙarasa bakin ƙofar ta zare sakatar ƙofar ba tare da ta waiwaya ba ta juya da gudun kar ruwan sama ya taɓa ta tana cewa
Sannu da zuwa anty samy .
Sai da ta tsallaka kan Balcony tukun ta juyo ,
A tsorace ta kai duban ta ga mutumin da yake tsaye a maimakon samy baby ,
Saurayi ne dogo wankan tarwaɗa yana tsaye ya zura hannun sa cikin wondon jikin sa , idanun sa sakaye cikin wani kwafcecen baƙin gilashi da kallo ɗaya za'a masa a fahimci rangwamen mutumcin dake tare da shi .
Juyawa tayi da sauri ta tura ƙofar falon ta shiga sabods tunowa da tayi da riga da wondon da suke jikin ta na bacci da duk da cewa basu kama ta ba ko kaɗan amma kaya ne masu tsantsi.
Kai tsaye ta shiga ɗakin ta ta fara bincikar hijabin ta ,
Sai dai hannun da ta ji ya sauƙa a ƙafaɗar ta ya sa hantar cikin ta kaɗawa ,
Da sauri ta jaa baya har tana gwaruwa da jikin wardrobe ,
Idanun ta ya shiga cikin na saurayin da ta bari a waje ,
Anty samira bata nan
ta furta haka , muryar ta na karkawa , lokacin da take ƙoƙarin zira hijabin da ta samu nasarar ɗauka ,
Riƙe hajibin yayi da hannun sa ɗaya , yayi amfani da ɗayan hannun sa wajen zare gilashin idanun sa , mitsitsin jajayen idanun sa da suka sake shigewa ciki-ciki suka bayyana , yana bin ta da wani shu'umin kallo
Da muryar sa irin ta mashaya , yace
Wa yake ta samira tsahuwar guzuma ?
Ga kamar ki gorgeous , ya ƙarasa zancen yana kai hannu zai taɓa kumatun ta ,
Da ƙarfi ta make hannun sa gami da saurin zura hijabin ta ,
Ni ba ƴar iska ba ce kar ka sake taɓa ni , ka fita min daga ɗaki ,
Ɗan baya ya jaa yana yarfe hannun sa da ta buge bakin sa a ɗan buɗe alamun mamaki ,
Baby har da duka ??
Bata kula shi ba ta haura ta kan gadon ta ta dira tana nufar ƙofa , sai dai taku biyu kawai tayi ta ji ya kamo ta ta baya ya haɗa bayan ta da ƙirjin sa ya ɗaga ta ciɗak , ya shiga juyi da ita ,
To tunda wasan tsale tsalle kike so bari na miki hajijiyar ƙauna .
ya furta haka yana ɓaɓɓaka dariya .
Tun ƙarfin ta ta fara ihu tana wutsil-wutsil da kafafu tare da ƙoƙarin son ɓanɓare hannun sa da ya zagaye cikin ta da shi ,
A guje samy baby da tun a tsakar gida ta fara jiyo ihun yakaka ta ƙaraso cikin ɗakin .
Kai kamal meye haka ? kayi hauka ne ?? Dallah sauƙe ta .
Ba tare da ya sauƙe ta ba ya ce
Ke dallah kauce ki ɗan sakayo mana ƙofa zamu buga ƙwallo ne ni da wannan me zafin kan da tayi gigin duka na .
Ƙarasowa tayi ta jaa hannun sa ,
Kamal kar muyi haka da kai dan Allah ka sauƙe ta , ƙanwa ta ce fa , yaushe muka fara ƴar haka da kai mutumina ??
A hankali ya sassauta rikon da yayi mata kafin ya sake ta tana jin ya ajiye ta ta fita a guje , ƙafafun ta ko takalmi babu ,
Kallon baka kyauta ba samy baby ta wurga masa kafin ta ja ƙaramin tsaki ,
Kai dai kamal anyi tantiri ɗan iska , to bari na faɗa maka wannan haja ce me matuƙar tsada ba irin taku ba ce domin kuwa sabuwa ce fil , ba'a riga an shiga kasuwa da ita an daka mata wawa ba ,
Ba ta wasa bace na san a ɗan abunda ya shiga tsakanin ku a yanzu kaɗai ,laushin fatar ta da ka taɓa ya isa sanar da kai irin maɗuɗan da zasu taho ta hanyar ta muddin ta shiga kasuwa .
Ƙafar sa ɗaya dake sanye da wani ƙwamemen takalmi sau ciki ya ɗaga yana tokare ta da jikin gadon yakaka .
Ni kuma kin san maƙudan da kike faɗa ba matsala ta bane , ko ruwan su kike so nayi miki kin san zan iya , muddin zan mayar ƙwaɗayi na akan wannan nunanniyar gwandar , nawa kike sa mata kuɗi ??
Two Million Naira
Ta furta cikin gatsali
Bani account number da zan zira miki su ,
A ɗan jirkice ta dube shi cikin ran ta tana son ƙure shi , domin kuwa duk da sanin da tayi wa kamal na shahararran ɗan masu hali da iyayen sa suka gama gurɓata tarbiyyar sa , ya zama tamkar ɗan taure wajen bibiyar mata , manya da ƙanana kyakkyawa da mummuna shi baya zaɓe kawai dai idan ran shi ya biya ya samu ya maida mugun yawu shikenan kuma bai ƙara bi ta kan mace , bata zaton wasan sa da kuɗi ya kai ya haka .
A ɗage ta karanto masa account number da suna , cikin abunda bai gaza mintuna biyu ba sai ga wayar ta dake cikin jaka ta ɗau ƙara ,
Jikin ta na mazari ta fiddo wayar ta duba ,
Alert ne na adadin kuɗin da ta buƙata cif .
Ɗan wara ido tayi da sigar mamaki , sai kuma ta kaɗa idon cikin yanayi na shanye mamakin ta irin na gogaggun matan bariki .
Babu shakka ka ɗau haja me girma , kuma na san baza ka yi wadarai da ita ba , yaushe kake buƙatar ta ?
Haɗe fuska yayi kafin ya watsa hannu
Ka duba wannan da wata maganar iska ? Irin waɗannan kuɗaɗen da na cire har sai kin min iyaka da ita ? Ai yadda ta sani haɗiyar mugun yawu dole daren yau na fanshe kuɗi na , daman ga gari ya ɗau sanyi yanayi ne na shiga daga ciki da sauri .
Ta saki Wata dariyar da take bayyana farin cikin ta akan kuɗaɗen da ta samu da dama tana tsakiya da buƙatar su ,
Alhaji kamalu , to baka da damuwa , yanzu ka tafi , sai ka aika mun address ɗin da kake son na kai maka ita ni da hannun na zan miƙa maka ita anjima da dare ,
Kasan na faɗa maka sabuwa ce bata harkar nan to sai na maka yaƙin shawo maka kan ta ,
Ɗaga kafaɗa yayi cikin nuna halin ko oho ,
Ni dai ki tabbatar kin mata Wankan irin yadda ya kamata
Ya ƙarasa zancen yana kashe mata ido ,
Alhaji kamalu , kar ka ji kome .daren yau na kai ne a sama .
Yakaka wacce take zaune dirshan a cikin ruwan sama ta jikin bangon ɗakin ta ta baya ,
Ta kai hannuwan ta duk biyu ta toshe bakin ta a ƙoƙarin ta na hana kukan da take fitowa sarari kar su samy baby su ji , kamar yadda duk zantukan su ya ratsa kunnuwan ta .
Ashe daman anty samy yaudarar take akan kome , ashe burin ta ta tsundumata cikin irin rayuwar da tunda ta fahimci girman saɓon da ake aikatawa ta hanyar zina take yi mata addu'ar Allah ya sa ita ma ta tuba ta daina ,
Manufar ta ashe ta
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Chapter 110
Chapter 111
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 52 Chapter of 111