Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
," tsurawa kofar ɗakin ido tayi tana ganin yadda walƙiya take haskawa tare da rugugin hadari nan take hankalin ta ya tashi tunowa da falmata da tayi koh a wane hali take ciki a ɗakin da take ? Ji tayi baza ta iya kwanciya ba idan bata ganta ba . A hankali ta ɗaga gidan sauron da suke ciki da niyyar fita dai-dai lokacin da aka yi wani tsawa da rugugin tasowar hadari da ya sa jaririn nan ya firgice tare da tsanyara kuka ," a daburce uwar sa ta farka gami da fara cewa ke ke keh kina ina ne kika bar shi yana ta irin wannan ihun ji min ƴar banzar yarinya ,"muguwa ,cikin sanyin murya yakaka tace wallahi yanzu na ajiye shi koh kwanciya ban kai ga yi ba , kuma ma da alama kamar yunwa yake ji ", ta furta hakan cikin fatan Allah yasa uwar ta ɗauke shi ,"mts ta jaa tsaki tare da surar ɗan jaririn kamar ta suri yaro mai shekaru biyu ," ta koma ta kwanta tare da shi tare da ciro abincin sa ta cusa mar a baki ,ɗif yayi shiru . Sauke ajiyar zuci yakaka tayi ganin uwar da ɗan sun koma bacci ,"ta siɗaɗa ta fita dai-dai lokacin da kakkarfan ruwan saman ya tsinke kamar da bakin ƙwarya ," gudu-gudu ta tsallaka ɗayan barandar ɗakin da falmata take ,'ba tare da ta damu da duhu tare da shirun da harabar wajen ya ɗauka ba ,ga ƙarar ruwan sama ," Tana shiga ta fara yawata idanun ta ," a hankali ta fara jin ƴar siririyar muryar ta tana kuka ,"ɗas-ɗas zuciyar ta ta buga tare da taruwar ƙwalla cikin gurbin idon ta,  cikin sauri ta fara taku tana kewaye gidajen sauron jama'ah tare da tsallaƙe su cikin taka tsantsan ," tana nufar inda take jin sautin ta domin bata son yin magana kar ta tashi mutane Cak ta tsaya da kukan jin takun sawayen ƴar uwar ta ,"yakaka ta furta cikin sanyin murya dai-dai lokacin da ta ƙaraso tare da durƙusawa a bakin "shingen"(gidan sauro) . Ƙasa-ƙasa tace falmata meye yasa ki kuka ? Me aka miki ," da shishiƙar kuka tace babu kome yakaka na tuno da su mama ne ,"yakaka cikin daren nan kika fito kuma ana ruwan sama ? Meyasa ?  ki koma ki kwanta dan Allah cikin ƙura ido tare da taimakon hasken walkiya ta fahimci a dandaryar ƙasa kanwar ta take takure a zaune ," cikin takaici ta maida duban ta ga ajus da take ajiye numfashi ɗaya bayan ɗaya tare da sake duƙunƙunewa cikin jin daɗin barcin ta ,take ta fahimci abun da yake faruwa ," Zuruf ta miƙe cikin cewa ina zuwa falmata ," bata saurari amsar falmatan ba ta fita , Jim kaɗan ta dawo tare da bargon ta a hannun ta zura hannu  ta miƙawa falmatan bargon,"ungo falmata buɗa shi ki kwanta akan rabi ki rufu da rabin duk da ma dai fitsarin yaron matar chan ya taɓa jiki amma ki kwanta a haka ," Jin falmatan tayi shiru yasa tace matsa na shinfiɗa miki kin ji ,"? Cikin rawar murya tace yakaka ke kuma ki koma ki kwanta akan me ? Shittt ," falmata lafiyar ki tafi min kome , bamu da kowa a yanzu daga Allah sai junan mu , menene amfani na idan har ban zamar miki garkuwa ba falmata ,"  tana furta hakan ne dai-dai lokacin da take gyara mata bargon tana shimfiɗa mata ," kama mata tayi ta kwanta ," Yauwa toh bari ruwan ya ɗan tsagaita sai na koma ɗakin mu kiyi baccin ki kin ji ? Gyaɗa mata kai tayi domin kuwa idanun ta har yaji-yaji suke mata tsabar baccin da ya cika su , Sauke sassanyan numfashi tayi , tare da share guntun hawayen da ya cika mata gurbin ido nisawa tayi tana tunanin ƙalubalen da suke a farkon sa yanzu wanda basu da sani akan iyakar sa ,karshen sa babu abun da yafi tsaya mata a zuci irin tausayin ƙanwar ta a yin rayuwa cikin wannan sansanin da ta lura kowa kan sa ya sani kan sa yake so "rayuwar daga ƙawri sai gwaiwa ",  zuciyoyin mutane cike take da mugunta da son kai .. Yaa Allah ga ni ga miskiniyar kanwata Allah ka taimake mu .                *Maraɗi jamhuriyar niger*  A karo na biyar ta kama ta sauko daga kan murfin sunduƙin yin "bahaya"( Toilet- Toilette ) da yake cikin banɗakin ta ," kai kawo ta shiga yi tare da duban agogon fuskar wayar ta " Yau har karfe biyu da mintuna arba'in biyamuradi bai dawo ba kamar yadda ya saba fita sha biyu da rabi na dare ya kuma dawo karfe biyun dare ," Meye ya tsayar da shi ? Jin motsi tayi kamar an taɓa kofar sirrin da take bangaren biyamuradin wacce kuma da ita yake amfani wurin fita da shigar sa gidan a dai-dai wannan lokutan da ba wanda ya taɓa sanin yana fita daga Allah sai shi sai ita ,  Cikin sauri ta sake ɗarewa kan sunduƙin tayi ƴar ɗage ta leƙa ta ɗan siririn huɗar da aka yi ta a can saman banɗakin domin ado wanda aka liƙa kwan lantarki a jiki, sai dai a halin yanzu babu ƙwan lantarkin sai dai huɗar da ta fito sarari ake iya ganin abun da ke waje ta wurin , Tar ta hango shi a cikin hasken lantarkin da ya ƙawata lambun bayan ɗakunan sa ," yana layi tare da tamɓele jikin farar rigar sa da shuɗin wandon jins ɗin sa dumu-dumu da abun da bata iya tantance shi daga inda take ," Ji tayi ruwan hawaye ya silmiyo daga gurbin idanun ta da gudu sun fara tsere akan siriryar fuskar ta ," Wani faɗuwar ƴan bori da yayi rigijib shi yasa ta kusa zamewa ta silmiyo daga kan toilet ɗin ,  da sauri ta ɗiro cikin gudu-gudu ta bullo ɗakin ta tare da fitowa cikin parlour kai tsaye ta nufi kofa ta kama mariƙin kofar ta murɗa , zuciyar ta tana zafi tare da ingiza ta , idanun ta suna hango mata faɗuwar da abun kaunar ta yayi . Sai dai turus ta jaa ta tsaya lokacin ta tuno da fitar ta a wannan lokacin zuwa bangaren biyamuradi zai jawo , me zata cewa masu tsaron gidan ? Wanda ta san basu san halin da yake ciki ba , basu taba sani ba , idan kuwa har ta fita war haka dole su sani . Hakan yana nufin fallasuwar mummunar fuskar masoyin ta , hakan yana nufin kunyatar masoyin ta , hakan yana nufin dasuwar bakin ciki cikin zuciyar uwar goyon ta , hakan yana nufin samar da wanzazjen bakin ciki cikin zuciyar uban goyon ta kuma kawun ta , hakan yana nufin tozartuwar ƴan uwan ta ,hakan kuma yana dai-dai da zubewar girma da mutuncin masarautar su baki ɗaya . Kamar walƙiya ta juya ta koma da sassarfa ta shiga ɗakin ta gami da murza mukulli lokaci guda ta nufi gadon ta gami da fadawa rubda ciki ta sanya kanta tsakanin filo gami da fashewa da wani irin kukan da ya tuƙo tun daga karkashin zuciyar ta , kuka ne irin wanda mutum yake yi idan bakin ciki yayi masa yawa . *Sorry this is a really short chapter koh? Kar ku damu insha Allah the next one will be longer and more action packed !* *Things are really starting to heat up now* 😜 *Please comment what you guys think of not just this chapter but every chapter . I really love hearing feedback on my work because these chapters are not easy to write .* *#Thanks* . *#son so* *#mafari Yanzu muka fara* [6/24, 9:58 AM] +234 701 013 7848: Fikrah writers association *MAFARI.......* ( _Hargitsin Rayuwa )_ *umm'muaz* 7 Juyi ya sake yi a karo na barkatai bisa makeken gadon nasa na alfarma, tare da runtse idanu yana mai sake jin yadda kan sa yayi masa mugun nawi har baya iya buɗe idanun sa sosai , ɗan ƙaramin tsaki ya jaa da yayi sanadin juyowar Tafeedah wanda yake zaune bisa doguwar ƙawatatciyar kujerar da take gaba ƙadan da gadon . Cikin takaici yake duban biyamuradi yousouf ɗin , kafin ya ɗan yi gyaran murya ! "cikin kowanne daƙiƙa ɗaya da yake wucewa yana sake nisanta ka da lokacin sauke farillah " tafeedan ya furta kalmomin masu nuni da tunasarwa , cikin nuna halin ko in kula ga biyamuradi yousouf , wanda koh kafin tafeedah ya idasa bayanin sa ya buɗe idanun sa tarwai da jijiyoyin cikin suka yi jaa , kammala bayanin nasa ya zo dai-dai da miƙewar sa zumbur daga kan gadon . Bai yi wani jinkiri ba ya fara taku cikin sassarfa lokaci ɗaya yana sauke idanun sa akan tagar ɗakin sa wanda hasken rana ya riga ya hudo ta tsakanin labulen . Bayan tsawon mintoci fiye da talatin da biyamuradi youssouf ya ɗauka yana addu'a da neman gafarar mahaliccin sa bayan ya idar da sallah , sadda kansa ƙasa yayi yana me jin kunyar ɗago kansa ya dubi aminin nasa wanda ya tabbatar idanun sa a kafe suke a kan sa , yayin da sashi guda na zuciyar sa yana me son tuno da wani abu . A firgice ya dago kan sa a sakamakon tunowa da yayi dawowar sa daren jiya da faduwar da yayi a harabar lambun sa wanda daga nan bai sake sanin inda yake ba a sakamakon kakkarfan baccin da yayi awon gaba da shi a wurin a yashe , da hakan baya rasa nasaba da sabuwar sumfurin dahuwar burkutun da ya sha a jiyan wanda gaba ɗaya ta hargitsa masa ƙwanya . Aina ka tarar da ni ? Shine kawai tambaƴar daya jefawa tafeedah bai koh kula da irin kallon da tafeedan ke jifan sa da shi ba mai cike da tarin ma'anoni . A jefa a inda kaga yafi dacewa da kai cikin kuma irin yanayin da ka zabarwa kan ka ."amsar da tafeedah ya bashi kenan " yana me miƙewa cikin yanayi na nuna alamun tafiya yake da niyyar yi ," Wani boyayyar ajiyar zuciya biyamuradi youssouf ya sauke a sakamakon fahimtar da yayi cewa tafeedah ne ya kawo sa ɗakin nasa ," Da misalin karfe nawa ka shigo gidan ? Su wa ka tarar a haraba ta ina nufin ma'aikata na sun yi chanji ? Mts! Idan kasan kana gudun zubewar mutuncin ka me zai sa ka jefa kan ka cikin rayuwar da kake youssouf ," tafeedah ya furta hakan cikin ƙufula yana me komawa ya zauna a inda ya tashi ," Cigaba yayi da cewa karfe uku na asubah na shigo sashin ka bayan tasowata daga wurin taron mu (meeting) ,inda masu tsaron gidan suka tabbatar min kana ciki tun farkon dare ," Amma abun mamaki nazo na gama neman ka ƙasa koh sama baka nan har nayi niyyar fita na sanar da masu tsaron ka , sai nayi tunanin zagayawa har cikin lanbu inda na tarar da kai kwance a ƙasa , da farko na tsorata amma daga baya na fahimci abun da ka min alkawarin ka daina sha kayi min rantsuwa da Allah akan baza ka sake sha ba ita ka sha youssof , ƙarin abun takaicin ma a cikin gidan nan , bayan ka san duk cikin ahalin gidan nan babu wanda ya taɓa sanin kana ta'amali da barasa ," kafi kuma kowa sanin masifun da fallasuwar wannan mummunar ɗabi'ar taka zata iya jawowa a garemu baki ɗaya ,"haba youssof , haba youssof , duk cikin tarin ababen zubda mutunci da jawo tozarta ka rasa wanda zaka zaɓa sai BARASA ? Bayan kasan itace shugaba ummul'aba'isi na jaan ɗan adam ga aikata kowanne irin sabon ubangijin mu ," tsagaitawa yayi lokacin da yaji muryar sa ta fara karkarwa alamun gaf yake da fara kuka sakamakon ƙona masa zuciya da wannan ɗabi'ar ta abokinsa ,amininsa kuma ɗan uwan sa youssouf da ya jefa kansa a ciki tun yana da ƙarancin shekaru sosai domin shi da kan sa ba zai iya cewa ga lokacin da youssof ɗin ya fara shan barasa ba , kawai dai ya farga ya gane ne shi da kan sa a saboda kusancin da suke da shi da juna ta yadda wasu lokutan dayawa zai taradda da youssouf ɗin cikin maye ," wanda tun yana ƙaryata kan sa cewa youssouf giya yake sha ,a dalilin tsawaita bincike da yayi bai taradda alamun barasa ba a duk inda youssouf ɗin yayi bigire da kuma boye masa tare da waskewar da ya dunga yi , har dai ya zo ya yadda, kuma yayi amanna aminin sa mashayin giya ne , ya kuma tabbatar lokacin da ya bi shi har zuwa wani tsohon kuchakin gidan saida burkutu wanda yake chan tsakiyar unguwannin talakawan gari inda anan youssouf yake zuwa yayi tatul , amma baya guzurin ta . A ranar yayi kuka har kan sa yayi ciwo ,kuma ya girgiza matuka musamman da yayi duba ga matsayin youssouf a garin na kasancewar sa ɗan sarki mai jiran gado , wanda ake sa ran watarana shi zai jagoranci dubannan al'ummar yankin ya zama shugaba a gare su abun koyi , Yaya hajiya umma (mahaifiyar sa) da mai martaba ,haɗi da ƴan uwan sa zasu ji a lokacin da suka farga , uwa uba yaya al'ummar gari zasu dubi lamarin yayin da labarin ya bazu ga kunnuwan su , haƙiƙa maƙiƴan sarari da na boye zasu ji daɗi suyi murna , sannan kuma da akwai yiwuwar subucewar samuwar mulkin jahar maraɗi daga hannun sa domin rashin chanchantar sa ta wannan fuskar ! Wane irin mulki ake zato ga mashayin sarki ???? Tun daga lokacin tafeedah ya nuna cikar amintakar dake tsakanin su da biyamuradi youssof ta hanyar yi masa faɗa da nasiha mai tsanani a kullum, gami da boye masa sirrin sa tare kuma da toshe duk wata hanyar da zata iya sa asirin youssof ɗin ya tonu , sosai yake koƙarin kare masa martabar sa da mutuncin sa , ta inda har ta kai yasamu nasara a wani dare shekaru biyu da suka wuce ,biyamuradi youssouf ɗin yayi masa alkawarin daga ranar ya daina shan barasa bayan fada da suka yi kacha-kacha inda tafeedah har yayi wa youssouf ɗin barazanar daina shiga sabgar sa idan har ba zai daina ta'amali da barasa ba . Farin ciki tare da kwanciyar hankali suka wadata ga tafeedah bayan jin alkawarin da youssof yayi masa ",cikin rashin sanin tuban muzuru youssouf ɗin yayi ya kuma ninke sa a baibai domin daga ranar ya sauya lokutan shan barasar sa muddin yana cikin garin maraɗi , ta yadda ya maida tsakanin sulusin dare lokacin fitar sa ya sha abar sa , yayin da idan yana wata ƙasar koh wata jahar a duk lokacin da ya samu sarari yake zuwa ko'ina ne ya nemo barasar gargajiya da aka fi sanin ta da " *BURKUTU* " zazzafa ya sha iya shan sa babu abun da ya fasa . Janye idanun sa da suka ciko da ƙwallar takaici tafeedah yayi , cikin rashin kuzari ya sake miƙe jin youssof ɗin ya rasa abun faɗa , toh me ma zai faɗa masa ? Soke hannayen sa yayi cikin wondon sa ,"ni zan shiga na gaishe da hajiya umma daga chan zan wuce ,sai kuma Allah ya kaddara saduwar mu , ina mai fatan Allah ya kiyaye ka ya baka nasara akan waɗanda zaka tunkara ," Daga haka ya sanya kan sa gaba da sauri youssof ɗin ya miƙe daga kan dardumar da ya idar da sallar sa ,"Jira ni nima babu abun da zan yi da wuce wanka sai mu fita tare ," bai jira amsawar sa ba kamar yadda shima tafeedah bai tsaya domin saurarar sa ba ya sanya kai yana me ƙarasa barin katafaren ɗakin youssouf ɗin . Yana shiryawa yana tunanin maganganun aminin sa tabbas duk wasu kalmomin da ya ɗauki shekaru yana furtawa agare shi gaskiya ne ," kuma shima a karan kansa yana mai bakin cikin halin da ya wayi gari ya tsinci kan sa a ciki sannan yayi iyakacin kokarin sa dan ganin ya daina shan burkutu amma hakan ya gagareshi duk kuwa da addu'o'in da yake yi a koyaushe yayi sallah akan Allah ya yaye masa, amma abun kamar tiri , ji yake idan bai sha burkutu ba a kowacce rana , yana iya rasa numfashin sa , burkutu ta zama jinin jikin sa , mahaɗin rayuwar sa kuma abar dake samar da nutsuwa da farin ciki a rayuwar sa ( a ganin sa kenan ) Ajiye matajin hannun sa yayi bayan ya kammala taje ƙwantatciyar sumar sa wanda yake yawan yi mata saisaye luf-luf da ita ," yayi yawo da idanun sa a ɗakin cikin son gamsuwa da bai bar wani abun sa mai muhimmanci ba ,"duk da cewa tun a daren jiya sojan dake kula da shirye-shiryen tafiyar tasa ya kammala haɗa masa kome cikin umarnin sa da yake zaune a gefe yana gwada masa abubuwan da yake bukatar tafiya da su ,"ya shirya su tsaf tare da kai su motar da aka shirya zai yi tafiya zuwa Niamey inda daga nan zasu daga zuwa Nigeria. Cikin takun sa na ƙasaita wanda yake bayyana cikar jarumtar sa irin na gwarzon soja , jaan tunga yayi ya tsaya "ɗan mitsitsin murmushi yayi ganin tafeedah da yayi a zaune cikin ɗaya daga cikin kujerun falon fuskar sa kadaran kadahan ya dago ya dube shi gami da miƙewa tsaye yayi gaba ," da sauri ya bi bayan sa suka jera . Cikin nutsuwa suka yi sallama a babban falon hajiya umma , da ya jawo hankalin siyama da merama aisha da suke zaune bisa wadatattciyar darduma suna ƙarin kumallo ," gefe guda masu hidimar zuba musu abincin da tsaftace wurin ne suke durƙushe zaman jiran su kammala , zumbur aisha ta miƙe Da ɗan gudu da tsalle ta ƙaraso gare su dai-dai lokacin da suke yiwa kan su mazauni akan jerun kujerun falon ,"zama tayi a gefen biyamuradi gami da ɗaura kan ta bisa kafaɗun sa ",barka da safiya hamma nah , nayi kewar ku sosai na same ku lafiya . ? Shafa kan ta yayi lokaci ɗaya fuskar sa tana sake faɗaɗa da yalwatatcen murmushin da yake bayyana tsananin  ƙaunar sa ga ƙanwar tasa yace ", lafiya lau meramar mai martaba yaya karatu ? Yaushe kika zo ? anyi muku hutu koh ? Anyi hutu hamma jiya da yamma nazo . Ɗan gyaran murya tafeedah yayi , Murmushi ta sake yi tana me sunne kanta a jikin hamman nata tace ,"ina kwana hamma tafeedah na same ku lafiya ," ?     Bazan amsa ba tunda abun ma wariyar launin fata ce ,"     Leƙo shi tayi ta bayan biyamuradi tana ɗan murmushi tace yi hakuri hamma tafeedah kasan nayi kewar hamma na watanni uku fa ,"     Kallo yake mata me kama da harara amma kuma fuskar sa ɗauke da sassayan murmushi wanda sai shi ya san ma'anar sa , sai kuma ita da duk lokacin da yayi mata irin wannan murmushin da kallon take tsintar kanta cikin wani irin yanayi na fargaba da mutuwar jiki ," Cikin sanyin jiki siyama ta ɗago idanun ta tana mai sauke su akan abun ƙaunar ta ," hamma youssof antashi lafiya ,? Hamma tafeedah barka da asuba ,? Ciki-ciki ya amsa mata da "lafiya" saɓanin tafeedah da suka gaisa sosai cikin sakewa har ma yake tambayar ta akan lamarin aikin ta inda ta tabbatar masa da ta ɗauki hutu na tsawon sati uku ," cigaba tayi da satar kallon biyamuradi da aisha wanda suke hirar su ƙasa-ƙasa cikin tsantsar shaƙuwa da kulawa da junan su da alama wata matsala ce da aishan wanda ta ƙagautu ta haɗu da yayan nata ta faɗa masa kasancewar ta rainon sa kuma abokin shawarar ta , cikin nazari take kallon sa bata samu ƙwanciyar hankali na sosai ba sai da ta fahimci faɗuwar sa ta jiya da dare bata haifar masa da wani rauni ba ,"ta sauke boyayyar ajiyar zuci , tana me Ƙwaɗaitawa a ranta ina ma ita ce maƙale da kafaɗun biyamuradin yana sauraren ta cike da kulawa da ƙauna kamar yadda yake yi wa ƴar ƙanwar ta sa ," lokaci zuwa lokaci suna sakarwa juna murmushin yaƙe ita da tafeedah da rabin hankalin sa yake kan wayar sa domin idan da sabo yaci ace ya saba da yadda yake zama saniyar ware a duk lokacin da biyamuradi da aisha merama suka haɗu . Da yalwatacciyar fara'ar ganin ƴaƴan nata ta ƙaraso falon , cikin hanzari bayun suka yi jerin gwano suna masu isar da gaisuwar su ɗaya bayan ɗaya , kafin cikar mintuna biyu sun cika babbar dardumar da suka shimfiɗa da kawatattun kwanukan abinci na alfarma ,ficewa suka fara yi ɗaya bayan ɗaya bayan sun sake kai gaisuwa . Da murmushi take amsa gaisuwar yaran nata tare da tambayar su yaya suke ," Umartar aisha tayi da ta zubawa yayun nata abinci ," ita kuma tuni siyama ta zuba mata abubuwan da take tunanin zata so ,"ta ɗebo ruwa a wani kyakkyawan mazuɓi tare da kamo hannun umma ta hau wanke mata su ," cike da so da kauna take sanya mata albarka ," tana me sunkui da kai take amsawa da ameen umman mu . Bayan sun kammala cin abincin ne tafeedah ya miƙe bayan amsa wayar da yayi wanda saƙo ya iso gare shi ana neman sa ," ƙarasawa gaban umma yayi tare da yi mata sallama addu'a tayi masa tare da ɗaurawa da nasiha ta ƙare da gargaɗin sa akan idan har yana cikin garin maraɗi kar ya yanƙe zuwa wurin ta kullum koh da bayan tafiyar aminin sa , Tare da ladabi yake amsa mata da yi mata alkawarin ba zai ɗauke ƙafar sa daga sashin ta ba koh da youssof baya nan , sallama yayi mata tare da miƙewa ya fice bayan sun yi musabaha da aminin nasa . Bin sa yake son yi domin ya shawo kan sa amma bashi da kuzari koh kuwa bai tanadi kalmomin da zai yi amfani da su wurin wanke fushin da yake hangowa a idon tafeedan ba , dan haka ya bar shi ya sarara zasu  shirya a waya , domin sanin da yayi cewa shi da aminin nasa basa iya wani dogon fushi da juna , duk saɓanin ra'ayin su bai taɓa jawo musu fushi da junan da ya wuce awanni ishirin da huɗu ba , dole daya zai nemi daya koh da ta waya ne koh ta hanyar sakon kar ta kwana su shirya ," kaunar junan su daga Allah take ," Cikin son fahimtar samun saɓani a tsakanin su umma take bin su da kallo har lokacin da tafeedan ya bacewa ganin ta ," tasowa biyamuradi youssouf yayi gami da dawowa daf da ita tamakar zai hau cinya ,"riko hannayen sa tayi tana me murmushi tace ,"yarona tun kafin ka tafi ka fara bani kewa ƙwarai zan yi kewar ka bani kaɗai ba har mai martaba ma jiya ya ɗauki lokaci yana mitar nisan da zaka yi mana alamu sun nuna kiris yake jira ya janye alfarmar da yayi na barin ka tafiyar nan ," Tare da tsananin ƙaunar iyayen nasa da yake taso masa yana kokarin dannewa yace "umma na shekara tamkar kwana ce kamar yau zaku ga Allah ya dawo muku da ni ,'kuma a jiya mai martaba ya sanar da ni cewa duk lokacin da yaga dacewa zai dunga tashin mutane daga nan musamman suna zuwa dubo masa ni ,ko da shi da kan sa bai samu damar zuwa ba ," umma na nima zan yi kewar ku ya karashe zancen sa yana me "ɗaga tafin hannunuwan ta ya sunbata tare da sanya kumatun sa a tsakanin hannun ta ,"ya cigaba da cewa addu'ar ku ita nafi bukata domin ita zata min jagora zuwa kan dukkanin wasu matakan nasara akan tafiyar da na sa gaba ," Murmushi tayi tana jin yadda kowacce ɗakika ɗaya take ƙaruwa da yawan kaunar ta ga gudan jinin zuciyar ta ", baza mu gushe ba muna masu yi muku

Chapter 9 of 111