Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Bai kula kowa ba duk kuwa da gaisuwar ban girman da suke yi masa ta hanyar ƙamewa su sara masa , Kai tsaye ya shiga bayin sa ya ɗauro alwala , ya dawo cikin tantin sa ya sauke farillar sallar asubha da take kan sa , Yana idarwa baiyi ƙasa a guiwa ba ya ɗauko alqur'anin sa ya buɗe murya cikin nutsuwa ya fara tilawa , A hankali nutsuwa tare da amincin da suke tare da alqur'ani suka fara ratsa shi tare da yin tasiri ga wannan yanayin da yake tunzura shi ,' Jingina kan sa yayi da jikin karfen tantin nasa lokacin da yaji wani irin bacci mai nawi yana son fusgar sa ,' Ƙiran wayar sa shi yasa shi buɗe idon sa daga son yin bacci da yake ,' Ami Tafeêdah Shine sunan da ya bayyana à fuskar wayar !  Da rashin kuzari biyamuradi ya amsawa tafeedah sallamar sa, bayan nan suka ɗora da tambayar lafiyar juna ," ?   Ɗan ouwa da dama kou ? meke damun ka ? lalle cikin yanayin ka akwai damouwa yi gaogawar sanar da ni ? Shiru youssouf yayi , yasan tafeedah yayi masa farin sani , yana kuma iya karantar kowanne irin yanayi yake ciki ," to amma baya jin zai iya faɗa masa damuwar sa, toh yace me wai ??   Ya sake dulmiyewa cikin alfasha bayan wanda tafeedan ya san yana aikatawa, ya ƙara da wata ??    Ɗan ouwa bani jin daɗin jiki na ne kawai , ciwon kai na damu na ,!   Babu kome ka ɗaure abokina idan har ka cigaba da ƙaurace mata a hankali ahankali duk wasu yanayi masu wuya da kake shiga idan baka sha ba zaka ji ka daina jin yanayin , sannan ka sake dagewa da addu'a . Uhum ita ce kawai kalmar da youssouf ya furta     Da ace tafeedah ya san abun da ya aikata da babu abun da zai hana abotar su ta samu tangarɗa Nagode ! Cewar youssouf Daga haka suka ɗan yi hira sama-sama , ganin youssouf ɗin bai tare da nutsuwar sa sosai ya sa suka yi sallama tare da sake ƙara masa ƙarfin guiwar gujewa burkutu ! Yadda youssouf ya ga rana haka ya ga daren yau ," tsafi gaskiyar mai yin sa ne ," Da ita yake son kasancewa a yanayi irin na daren jiya , rashin samuwar hakan a gareshi ya haifar masa da masifaffan ciwon ciki da amai bayan masifar da yake ji a ruhi da ƙwaƙwalwar sa , ji yake kamar ya zura da gudu yayi ta gudu har ya tadda ta , ko kuwa dai yayi fiffike ya sauka gare ta a cikin daren ," Shajaran majaran ya wayi garin a halin jikkata , da ya sanya tilas likitocin da suke abokanan aikin su suka shiga bashi taimakon gaggawa , ƙarin ruwa zuwa magunguna ," ba laifi lafiyar jikin sa a zahiri ta dai-daita amma shi kaɗai ya san halin da yake ciki a ruhin sa , Zuwa azahar ya ɗan ji karfin jikin sa , dan haka yayi wanka ya ɗau shiri , zuciyar sa ta gama samun galaba akan sa tare da taimakon shaiɗanin da yake tare da shi yana bibiyar sa tare da ingiza shi , Karfe biyar na yammaci tayi masa dot a ƙofar su yakaka ,' Kan sa tsaye ya shiga gidan yana mai fatan cin karo da ita kawai su tafi , sai dai kuma inda gizo ke saƙar shine , shi fa bai wani tantance da kamannin yarinyar nan ba ," alhali kuma ya gama shawartar kan sa akan ya tsaya tare da ita kawai ta dunga biya masa buƙatar sa tun da shi ne mutum na farko da ya fara sanin ta ," shi kuma zai ɗauki duk wasu hidindimun ta har sai zuwa lokacin da ya fita a masifar da ya faɗa ,' Da wannan tunanin ya sanya kai cikin rumfar madam saly , ya tadda babu mutane dayawa mafi yawa suna wurin chasun da ya gitta a yayin shigowa ," Wuri ya samu daga gefe ya zauna , zuciyar sa na fatan ganin ta kamar yadda yake yawata idanun sa akan ƴan matan da ke kai kawo ta gaban sa , baki ɗaya bai ga fuskar ta ba acikin su , Ina take ? Ya san fara ce tas , bayan haka babu abun da zai ɗorar na daga suffar ta ,' Yagana ce ta ratso ta cikin rumfar cikin shirin tafiya gida, yakaka biye da ita da nufin yi mata rakiya ta dawo ta ƙarasa aiyukan da take kaiwa har dare tana yin su daga wannan zuwa wancen ! Tana sanyo kai ta ji ƙamshin sa ,' tabbas wannan ƙamshin "bature kam silum " ne , a take bugun zuciyar ta ya sauya tare da wata kewar sa mai tsanani da ta taso mata Ina yake !  Tambayar zuciyar ta Tun da suka bullo ya gan su , a take zuciyar sa ta shaida ta tabbas ita ce abar kwaɗayin sa ita ya zo nema ,! Hankalin ta ya rabu biyu ɗaya yana ga hirar da yagana ke yi mata ɗaya yana ga son gano inda yake , dan haka bata samu nasarar ganin sa ba har suka zo giftawa ta gefen sa ," Ganin zata wuce shi ya sa shi miƙa hannu ya kamo hannun ta ," Da sauri ta juyo domin ganin waye ne ,"duk da cewa an saba yi mata haka ," Idanun su suka sarƙe cikin na juna kowannen su ya gaza ɗauke idanun sa , a yayin da suke fassara kallon da suke yiwa juna a zuciyoyin su ," Kallon da yakaka ke bin biyamuradi kallo ne na nayi kewar ka , na kuma yi farin cikin sake ganin ka , Yayin da take fassara kallon da biyamuradi yake jifan ta da shi a nufin.!    Gani na dawo ki sake taimaka min .,'     Zan taimaka maka ta ƙudurce cikin ran ta ,!   Har yagana tayi ɗan nisa ta waiwaya bata ga yakaka ba dan haka ta dawo da baya nan ta tadda ta suna kallon juna da wani mutum da bata kai ga sanin sa ba , da ido ta bi hannayen su da yake manne ,! Dafa kafaɗar yakakan tayi ganin irin shagalar da tayi ,bata san ma ta zo wurin ba Da sauri yakaka ta zame hannun ta daga cikin na biyamurdi ," Ina zuwa ,' tace da shi ! A bakin kofar shigowa ainahin gidan ta dogare yagana  zan koma daga nan kin ga ana jira na ! Da ido yagana take bin ta cikin ranta tana mamakin farin ciki tare da murnar da yakaka take yi wanda kafin fitowar su a ɗazu babu shi,' A karo na huɗu ta sake tambayar ta Wai yakaka sai tambayar ki nake kin share ni waye wannan ɗin ko ƴan uwan ku ne ? Bature kam silum ne ,    Ɗan uwan mu ne Daga haka ta juya da sauri har tana haɗawa da ɗan gudu ta koma ciki , Ta bar yagana da mamakin ta fal cikin rai , " bature kam silum' ta maimata sunan ,! sashi guda na zuciyar ta yana shakkun ambaton sa da tayi da ɗan uwan ta , kai wannan daga gani ba yaren mu bane ! Da murmushi akan fuskar ta ta ƙaraso gaban sa ,   Ki kimtsa ki taho mu tafi ,kadda ki ɗau lokaci Ya furta hakan yana mai ɗauke kan sa daga kallon ta ya mayar ga agogon hannun sa ," Kalmar kimtsawa tai mata tsauri wurin fahimta , amma da yake tana jin sa cikin zuciyar ta , sai ta kintata ta  hasaso abun da yake nufi , dan haka ta shige ciki ,"     Ƙasa-ƙasa ya bi takun kafafu da kallo wanda yake halin sa ne kallon ƙasan ido ,"         nan ya hango dauɗa tare da taron kursashin da yake danƙare ƙasan kafafun ta . Cikin sauri ya ɗauke kan sa ! A gurguje ta shiga ta ɗibi ruwa tayo wanka , ta dawo ɗakin su larki ta hau shiri ," falmata wacce take zaune shiru kamar yadda yake al'adar ta ce killace kan ta wurin da babu kowa tayi shiru ,"   Motsin da taji an taɓa musu jakar kayan su , ya sa takai hannu tana kamo jakankunan nasu ,"     Waye anan ? Yakaka wacce ɗoki ya sa bata ko yi sallama ba bare tayi wa falmatar magana , tace,           Nice fa falmata nah ," Aiyo yakaka na , to ai baki min magana bane ! Yau har kin gama aikin ne ? Ban gama ba falmata , Mutumin shekaranjiya ne ya dawo yana so mu je na sake taimaka masa ," Zuruf falmata ta miƙe nima zan biki yakaka ,! Tsam yakaka tayi ta bar ƙoƙarin sanya kayan ta da take yi , Ta taso ta zo ta kamo hannuwan falmata ,"    Falmata na kiyi hakuri ki zauna har naje na dawo , kin ga aikin da nake yi masa mai wahala ne baza ki iya ba , kuma yau bazan kwana ba , anjima kaɗan zan dawo kin ji ?    Da kyar ta shawo kan ta ta yadda zata jira ta tare da alƙawarin baza ta kwana ba zata dawo , da haka ta kammala shiryawa cikin wata atamfar cote d'ivoire ruwan zuma mai cizawa da aka yiwa ɗinkin riga da siket , duk cikin ire iren kayan da samy baby tayi mata kyautar su ne da basu sha jiki sosai ba ," wani turaren da samy baby ta bata lokacin da take menses ta ce ta dunga shafawa a jikin ta ,"shi ta ɗauko ta mutsittsika ,"    Fes tayi kyau ta ɗaura ɗankwalin ta shigen yadda ta ga samy baby na yi , bata sanya gyale ba domin bata da shi kuma ka'idar gidan madam saly ba'a yawo da mayafi .! Wannan karon a tsaye ta tarad da shi ya saka hannun sa ɗaya cikin aljihun wandan sa , da alama tsumayen ta yake cikin ƙaguwa ," Babu laifi a idon sa tayi kyau , duk da cewa shi ba wannan bane ya dame sa , Sai dai tana matsowa kusa da shi ya ji wani ƙamshi marar daɗi a hancin sa yana tashi daga jikin ta , sam ƙamshin  bai masa ba ,! Juyawa yayi ya fara taku ba tare da yace da ita ƙala ba ," Zungui-zungui ta bishi a baya , Duk yadda yaso ya Daurewa ƙamshin turaren dake tashi a jikin ta ya kasa , sosai yake jin wani yanayi marar daɗi a cikin ƙamshin  , shi mutum ne mai tsananin tsafta da ƙyanƙyami sam bai son wani abu da yake da alaƙa da ƙazanta ," Dan haka lokacin da suka daidaita akan titi ,ya ɗan juyo da ganin sa kan ta ,"     Ki gwouda mini hanyar les salons !     meye kuma Les salons, ?  ita hausar sa gaba ɗaya wahalar fahimta take yi ma ta ,"      A takaice ta amsa    ban san wajen ba ! Wani wuri ya samu a gaba kamar super market ya tsaya shaguna birjik a wurin , Mayuka tare da sabulai zuwa turaruruka na mata , masu kyau da tsada ya jida , Ya koma banagare kayan sawa ,"shi ba wani sanin size ɗin ta ya yi ba dan haka ya ɗauki dogayen riguna baƙaƙe biyu , A wurin biyan kuɗin ya tambayi Cashier wurin salons , nan ya masa kwatance na wani shahararren wurin gyaran jiki da yin kwalliya , TaTa saloons da yake kan titin danboa . Ya ajiye kayan a kujerar baya ya zo ya tada motar ba tare da yace da ita ƙala ba , ita ma kuma tayi shiru bata magana sai satar kallon sa , Tata salon babban wurin gyaran gashi , ƙafa da ƙumba , yin kwalliya da gyaran jiki ,  zuwa sayar da turarurrukan arabs masu kyau da ƙamshin sanyaya rai ,suna da gyalalluka na yayi masu matuƙar kyau da inganci . Hajiya ruma mamallakiyar shagon mace ce mai karamci wacce ta san harkar kasuwa dan haka take girmama abokan cinikayyar ta , ( Allah ya ƙara ɗaukaka ƴar ƙanwa ta ) Sun ci sa'ar tarar da ita da kan ta , inda tayi musu tarɓar girma tare da ruwan gora da lemun gongoni ," nan youssouf yace ayi wa yakaka gyaran jiki tun daga salons zuwa pédicure , kai har wanka ma ayi mata ,! . Aka sa masa kuɗi ya biya . Nan aka shiga da yakaka wani ɗan ɗakin da ya wadata da fitilun haske ,' Suka fara aikin su , goge nan wanke chan , dirza nan shafa wannan goge wancen , har dai suka samar da yadda suke so a jikin yakaka , duk da cewa su da kan su sun yi mamakin irin dauɗar da take danƙare a kowanne lungu da sakon jikin yakaka , ,misalin karfe takwas na dare suka fito da ita , tayi kyau ba kaɗan ba , ɗan nude makeup ɗin da suka mata ya sake fiddo da zallar manyan kyaun da take da shi , jikin ta sanye da ɗaya daga cikin dogayen rigunan da ya saya mata ,sun yi mata naɗi da gyalen rigar bayan sun tara mata gashin ta mai rangwamen duhu sai tsanananin laushi da tsawo a tsakiyar kan ta sun kama mata shi da roba ," , ita da kan ta jin kanta take kamar ba ita ba kamar an sauya ta , wani irin nishaɗi ne yake huda ta , ƙamshin da yake mamaye da sassan jikin ta yana bata wani irin farin ciki na musamman, tsafta tayi a rayuwa ," ita kuwa me bature kam silum zai biɗa a wajen ta da baza ta iya masa ba ? ai babu ! Da ido yake bin ta da kallo lokacin da suka fito , duk da cewa idanuwan sa sun saba ganin kyawawan mata daga bangarori daban daban na duniya , amma kwarai irin nata kyaun ya burge shi ," daga inda yake yana jin tashin ƙamshin ta ," Da hakan ya sa shi sakar mata murmushi da suka haɗo ido , a karo na farko da yakaka ta ga murmushin sa wanda yake ƙarawa fuskar sa haiba , nan take ta washe gajerun hakoran ta da suka sha wanki tana maida masa da martanin dariya , tsintar kan ta tayi da tambayar sa ,"      Nayi kyau ko ? Murmushin bai gushe ba akan fuskar sa ya haɗa yatsun sa biyu babban da mabiyin  sa ya mata alamu da kinyi kyau sosai ! Hannun sa ya miƙa mata ta ɗora nata akai ya ja ta suna mai ficewa a shagon   ma'aikatan shagon suka bisu da kallon sha'awar da suka basu ,"Cikin ran su suna aiyyanawa ma'aurata ne irin sabon auren nan har wata ƴar gaza gani daga cikin su ta tanka ," perfect couples" Kwanakin da suka biyo bayan wannan ranar biyamuradi youssouf da yakaka zama suke irin na masoyan ma'aurata , babu wata rana da ta tsallake musu da basu kwana tare ba . Yayin da biyamuradi yake fidda kuɗi yana mayar da yakaka irin macen da yake so , ƴar hutu ƴar gayu mai tsafta , tata salons ya zama wurin zuwan su , bai jin ƙyashin kashe mata kuɗi tare da bata farin kuɗin tsurar su domin ta biya wasu buƙatun , har ƴar ƙaramar waya ya saya mata , wanda yake amfani da ita wurin kiran ta idan ya zo ɗaukar ta ," a yanzu burkutu guzurin ta yakaka take yi masa , har ɗakin da suka mayar na kwanan su a garki Guesthouses , Yakaka kuwa sau da kafa take bin biyamuradi youssouf cikin dukkanin buƙatun da ya zo mata da shi bata iya kuya masa baya , tana bashin haɗin kai tare da juriyar ɗaukar bukatun nasa ," A yanzu aikin gidan madam saly ya ragu a kan ta , saboda yadda biyamuradi da ita kan ta yakakar suke sakarwa madam saly kuɗi , wacce a rana ta biyu da yakaka ta sake bin biyamuradi suka kwana alhalin bata gama mata aiyukan ta ba kusan raba dare tayi tana zagin yakakar tare da shan alwashin a gobe gobe zata kore su , Da hakan ya sa falmata kwana tana kuka ita ba kome yafi bata mata rai ba irin kalmar "ƙaramar karuwa sabuwar yar iska ," da madam saly ta danganta yakakar da shi ba ," cikin muryar kuka ta dunga maimaita kalmar    Yakaka na ba ƴar iska bace    Yakaka na ba ƴar iska bace Ƙasa-ƙasa yadda madam saly bata jiyo ta ,' tsaf ta gama kintsa musu jakar kayan su tana jiran gari ya waye yakaka ta dawo su kama hanyar su," Sai dai abun da ya ɗaure mata kai washegari bayan dawowar yakaka gidan tayi ta kasa kunne ta ji hayaniyar madam saly tana zagin su tare da kora kamar yadda tayi rantsuwa , " sai taji tsit , sai ma jin madam saly tayi ta zo har cikin ɗakin nasu tana bawa yakaka wani abu tare da shaida mata idan har ta sha shi da madarar ruwa ko nono , ba ƙaramar kyauta saurayin ta zai yi mata ba ƙila ma ya bata "mota ," Saurayi kuma yakaka ?   Wanne saurayi ? Tambayar da falmata ta jefawa yakaka kenan , bayan ta cika bakin ta da donut,  wacce ita ma yakakar ta toshe mata baki da kayan maƙulashen da biyamuradi ya ciko mata manyan ledoji da su ,lokacin da ta so tada bori akan kwanan da yakaka ta sake yi a waje ,!     Ba saurayi na bane wanda nake taimakawa ne ,"     Wai yakaka wane irin taimako kike yi masa da har yake baki kayan daɗi haka ? ga turare mai ƙamshi da kika ce ya baki har da su mai ," to kawai mu koma gidan su mana mu dunga yi musu aikin tare koh ba taimakon sa kike da aiki ba ? Cikin diriricewa yakaka ta ce,"     Ba-ba ba agidan su muke aikin ba a wani waje ne ,falmata kiyi zaman ki anan tun da ni ina zuwa nemo mana , kuma ina samo mana kuɗi , kin ga tunda kuɗaɗen dayawa idan suka taru har ɗaki zamu iya kamawa mu bar gidan nan , mu kama sana'a a hankali a hankali muna neman su maman mu ko ?  Take falmata ta hau murna jin za'a nemo maman su ," nan dai ta hakura zata dunga zama yakaka ita zata dunga zuwa sabon aikin da ta samu ! Haka kwanaki suka jaa har yau da suke kwanaki goma sha huɗu da fara tarayyar su , zuwa yanzu yakaka tayi nisa cikin makauniyar soyayyar biyamuradi bata ji bata gani wata irin mahaukaciyar soyayyah take masa da bata ƙi ba su tabbata har abada a tare , Ta bangaren biyamuradi kuwa shi tun farko babu batun so atsakanin sa da yarinyar , hasalima ya ɗauke ta ne kawai a matsayin mai bashi maganin cutar da yake ganin ta kama sa a kwanakin nan na jarabar mace , wanda a yanzu kuma yake jin ya fara samun sauƙi domin a ƴan kwanakin nan yanayin da yake ji mai tsanani a duk ranar da bai kusance ta ba ya ragu , dan haka zuwa yanzu ya fara jin zai iya daina harkar gaba ɗaya tunda daman dole ce ta sanya shi farawa ,( a cewar sa ) A yau yayi niyyar sallamar yarinyar da ƴan kuɗaɗe masu tsoka domin yau idan ya koma daji ba zai sake fitowa kwana kusa ba zai maida hankalin sa kachokam kan aiki , giyar da kan ta zai gwada barin ta na kwana biyu , Daga wanka ya fito jikin sa ɗaure da towel , kai tsaye ya nufi ƴar wadrobe ɗin da take ɗakin ya fiddo da mai tare da mataji ,( comb ) ya shafa mai tare da taje ƴar sumar sa da bata cika yawa ba ,  , ya jawo ƴar ƙaramar jakar matafiya da yake sako kayan sa a ciki shiga ɗaya idan zai shigo gari ya fiddo kakin sa na soji ya sanya ya fesa turare tare da ɗaura agogon sa , kayan jikin sa da ya cire wanda yake riga long-sleeved da dogon wando , ya ɗauka ya mayar cikin jakar tare da haɗo ƴan sauran tarkacen sa duk ya zuba a ciki , Ya samu wuri ya zauna a gefen gadon ya jawo takalman sa mahaɗin kayan sa yana ɗaurawa a kafar sa , Duk abun da yake yakaka wacce take shirye tsaf a kishingiɗe a gefen gadon tana bin sa da kallon so da ƙauna haɗi da burge ta da duk wani motsi na sa yake , " Tunani take ina ma ina ma ace wannan kyakkyawan mutumin da har yau bata kai ga sanin sunan sa ba duk kuwa da kusanci mafi girma da suka samu a tsakanin su , ina ma da zai AURE TA , ?    Da ita kuwa ta gama jin daɗin rayuwa tare da nasarar rayuwa , Ɗago kan sa yayi ya kalle ta , ɗan gajeren murmushi yayi mata     Yaya irin wannan kallo haka ƴan mata ? Kayi kyau bature kam silum ," amma ina ta tambayar ka meyasa kai kayan ka ba irin na sauran sojoji ba , baka bani amsa ,"  A  takaice ya amsa mata saboda ni ba sojin ƙasar ku bane ,"     To inane ƙasar ku ?      Wani wuri ne mai nisan gaske ! ,"ya amsa mata   Wallet ɗin sa ya ɗauka ya fiddo da dukkanin kuɗaɗen ciki , da suke sabbin ƴan dubu ɗai ɗaya , " ya tako ya zagayo ta bangaren da yakaka take ,   Kamo hannun ta yayi tare da ɗora mata kuɗin ,"   Ƴan mata ,( kamar yadda yake kiran ta tun haɗuwar su a zahiri ya manta sunan ta bai kuma taɓa damuwa ya sake tambayar ta sunan ta ba toh ina ruwan sa da sunan ta ? Amfanin me sunan zai masa ? )     Ni zan tafi yau kuma bazan dawo nan kusa ba saboda yanayin aiki na , ƙila na dawo cikin sati biyu masu zuwa ƙila sai cikin wani watan watakila kuma .... Sai ya ɗan yi shiru  tare da duban fuskar ta ," Wacce tunda ya fara bayani idanuwan ta suka cika da ƙwalla , wani irin bugu zuciyar ta take yi , Zame hannun ta tayi kuɗin suka sauka akan katifar ,"           "ka bar kuɗin ka bature kam silum ba sai ka biya ni ba , ni dai dan Allah kar kace baza ka dawo yau ba , ka dawo dan Allah ni ko baka bani kuɗi ba zan taimaka maka kamar kullum , akwai wasu sauran kuɗin da kake bani ma ina tara su duk zan dawo maka da su ni dai dan Allah bana so na daina ganin ka , idan bana tare da kai zuciya ta bata min daɗi , na saba da kai . tun da ta fara magana yake bin fuskar ta da kallo wacce kafin ta kammala ta jiƙe da ruwan hawaye , wani irin tausayin ta ne ya kama shi , tausayi mai tsanani , ya fahimci yarinyar ta faɗa a tarkon son sa , wanda shi kuma sam bai so hakan ba domin kuwa a zahiri bata da gurbi cikin rayuwar sa ko kaɗan , " shi kuwa ina zai kai ƴar talakawa marar galihu irin wannan yarinyar toh ya kai ta ina ? Masarautar su ? Ai auren ɗan sarki sai ƴar sarki idan kuwa ba ita ba toh sai fa ƴar manyan attajirai ," kai shi bai taɓa ɗaukar ta da wani matsayi ba ma da ya wuce macen da yake biya ta gusar masa da sha'awar sa , bata da wani banbanci da sauran karuwai !   Duba ƴan mata ," ni akan aiki na zo ƙasar ku , batta kasancewa kullum mu zauna tare , ki ɗauki kuɗin ki riƙe a hannun ki zasu miki amfani watarana , ni akan hanya nake ," ki manta da ni kiyi rayuwar gaba har yanzu ke yarinya ce kin ji kou ? Tashi mu tai

Chapter 23 of 111