akan tekun rairayin saharar tenere da yake boda tsakanin Niger da Chad ta yankin Bilma dake ƙarƙashin jahar Agades.
An kashe mafi yawa daga cikin ɓarayin manya daga cikin su kuma sun gudu , ciki har da shugaban su da ba'a kai ga sanin cikakken sunan sa ba amma bayanai sun tabbatar da cewa ɗan asalin ƙasar Mali ne .
Kalmomin yabo iri-iri suka dunga yiwa Biyamuradin maraɗawa , bayan sun gama tsinewa ƴan fashi da makamin suna kuma fatan Allah yasa a kai ga samun nasarar kashe sauran da suka rage ko Al'umma sa yi kai-kawo a tsakanin ƙasashe cikin kwanciyar hankali ,
Ita bata wani ji abun burgewa ba , idan ba lalacewa ba me yakai ɗan sarki Yarima a yadda ta ji sun faɗa , yin aikin soja bauta ?wannan ai shine a aiki kare ya aiki wutsiya .
Miƙewa tayi tana nufar wajen da ɗakin kwanan ta yake sai dai kafin ta ƙarasa ta ji wayar ta na kiɗan shigowar ƙiran Ghaddafi , cike da ɗoki ta daga wayar tana ajiyar zuciya tamkar wacce tayi gudu .
Cikin abunda ke ƙasa da mintoci goma sha biyar tayi shiri cikin doguwar ɓakar rigar ta ta rufa hula baƙa a kan ta tare da rufa ɗankwalin rigar da ta kare rabin fuskar da shi tundaga kan ta , ta nufi babban wajen hutawar da Ghaddafi ya sanar mata yana jiran ta a wajen ta je ta same shi .
Yadda ta gan shi duk a firgice da ƙananun raunika a fuska da hannuwan sa da suke sarari ya duƙushe tasirin farin-cikin ganin sa da tayi , sai ta shiga tambayar sa kan ko hatsarin mota yayi ? Ko kuwa ƴan fashi ne suka tare sa akan hanya ,?
Bai bata takamai-mai ɗin amsa ba a madadin haka wata sabuwar sallama ya shiga yi mata cikin sanar da ita sabuwar tafiyar da yake da nufin yi a yau zuwa France , da yace yana iya kaiwa watanni biyu zuwa uku ,
Da wani irin yanayi na tsoro take kallon sa , yaya zai tarki yin tafiya haka mai nisa bayan yasan suna mataki na ƙarshe ne na gaf da cikar burin su me hakan ke nufi ?
Duk yadda ta so ta masa rigima yaƙi bata dama , dole ta yadda suka yi sallama ,cikin kwantatciyar muryar sa ya cigaba da rarrashin ta kafin wayar sa take danƙe a hannun sa tayi ƙarar alamun shigowar saƙo , yana karanta saƙon ya miƙe a ɗimauce yana raba ganin sa a da'irar wajen hankalin sa baki ɗaya ba'a kwance yake ba ,
da ido ta bi shi ƙwalla na taruwa mata , yadda ya juya bai ko saurare ta ba , ya taɓa mata rai babu shakka akwai abunda yake faruwa da shi da bata kai ga sani ba , taku biyu yayi ta ƙira sunan sa , a hankali ya juyo yana ɗora ganin sa akan ta tsayayyun idanun sa na bayyana wani irin yanayi na tsoro .
" Ghaddafi , kada ka manta da ni zan jira ka koume tsawon lokaci , ta furta hakan tare silalowar hawaye daga kwarmin idanun ta ,
Daga inda take ta hango yadda laɓɓan sa suka motsa ko da kunnuwan ta basu iya jiyo mata amon sautin kalmomin sa ba ta fahimci cewa cewa yayi ,
" Maimounatou ina son ki .
Ƙarar harbin bindiga da ya gifta ta kunnen ta shi yasa ta kusa hantsilawa daga kan kujerar da take zaune , kafin ta farga harbe-harbe sun yawaita a sararin wajen da nan take mutane suka kaure da guje-guje , akan idanun ta Ghaddafi ya ɗaga kafafunsa ya taka da gudun gaske yana barin wajen kamar fitar kibiya .
Ta miƙe tsaye amma ruɗani ya sa ta koma da ƙarfi ta sake zama tana toshe kunnuwan ta biyu , ta gaban idanun ta takun ƙafafun sa da suke sanye da manyan takalman sa na soji ya wuce da gudun gaske ya dafa baya akan hanyar da Ghaddafi ya bi .
Ba zata iya sanin iyakar adadin mintocin da tayi durƙushe a gurin ba, zuwa lokacin da harbin bindugogin ya tsagaita , lokacin ta samu damar miƙewa daga durƙuson da tayi a ƙasan teburin gaban kujerun wajen .
Ba tare da ta tantance yanayin da take ciki ba ta fara taku da sauri da niyyar ficewa a wajen , can gefen zuciyar ta na son sanin halin da Ghaddafi ke ciki , sai dai bata saurara ba domin tana buƙatar nutsuwa mai tarin yawa a dai-dai lokacin .
Kamar ance ta ɗago kan ta lokacin da ta ɗaga ƙafa tana barin wajen , idanun ta suka sauƙa kan dogon sojan da yake sanye da kakin sa da jini ya ɓata gaban rigar , har yana ɗiga ta wajen hannun sa , yana tafe da takun sa na jarumta a hankali ta sauƙe ganin ta ƙasa inda ya riƙo ƙafar mutumin da ya harbe yana jaan sa tamkar kayan wanki , idanun ta suka sauƙa kan fuskar Ghaddafi da jinin da ya ɓata fuskar sa zuwa ƙirjin sa bai hana ta gane shi ba ,
Duk wasu jijiyoyin jikin ta ne suka tsayawa yin aiki , jinin ta ya daskare , kamar yadda kunnuwanta suka toshe , numfashi kuma ya fara kokawar kufce mata , ƙafafun ta taji suna mata girgiɗi.
" Ya kashe min Ghaddafi , Ya kashe min Ghaddafi .
Sune kalmomin da suka ƙwanƙwashi ran ta suka farkar da ita daga suman zaune da tayi , wani irin ihu ta sa mai sauti da ya jawo hankulan tsirarun mutanen da suka rage a wajen da zuwa lokacin daman ma'aikatan wajen ma korar jama'a suke .
Babu wanda ya saurari kukan da take yi da ake zaton na firgici ne aka tisa ƙeyar ta zuwa wajen park ɗin .
Mutuwar Ghaddafi bata zowa Maimounatou da sauƙi ba domin tamkar hauka tayi , surutai kawai take yi tana sambatun da ba'a wani fahimtar me take cewa , bata rubuta jarabawar ta ta ƙarshe ba hukumar makarantar ta turawa da Maimartaba mummunan saƙon rashin lafiyar ƴar sa ,
Nan take aka tado da mutane ciki har da manyan yayun ta suka zo Niamey suka ɗauke ta zuwa gida Agades .
Kowa ya ga yadda take yi a lokacin cewa ake gamo tayi , aljannu ne suka taɓa ta, dan haka aka shiga magungunan iska ba ji ba gani ,
Ganin ana ta banka mata hayaƙi babu gaira ba dalili , ya sa ta rusuna ta bar surutai da ƙiran sunan Ghaddafi , sai ta koma ba un ba un'un , bata iya ci bata iya shan ruwan kirki wanka ma bata yi ,
Ba'a tsahirta da magunguna ba , aka cigaba da kawo magani iri-iri , na wanka da na sha da na turare , kai har da na shafawa da shaƙawa ,
Mafi yawa zubda su take yi , ta kuma kasa sanar da kowa dalilin tashin hankalin ta , to cikin iyayen ta biyu wanene ya san Ghaddafi ?? Ya san Alaƙar su ? Babu .
Tsawon wata guda ta fara dangana sai kuma rashin lafiya Mai tsanani ya taso ta a gaba , ciwon ciki mai tsanani duk ɗan abunda ta samu ta ci sai tayi aman sa , ga zazzaɓi mai zafi tare da ciwon kai ,
Kasancewar ta wayayyiyar ƴar jami'a ita da kan ta ta fara bincikar kanta game da sauyin yanayin da take ji a jikinta , a sirance ta aiki Gnala ta sayo mata abun awun tabbatar da samuwar ciki .
Da zaton motsuwar kwakwalwar ta Gnala ta karɓi kuɗin ta sayo mata ,
Kamar yadda tayi zato gwajin farko ya nuna mata samuwar ciki a jikin ta ,
Ranar damuwa ta dawo mata sabuwa dal , tayi kuka irin wanda tun mutuwar Ghaddafi bata samu damar yin irin sa ba sai ranar ,
" ina zata da cikin jikinta tana ɗiyar Martaba ɗiyar Asali ɗiyar sarki ?? Ya zama dole ta rabu da cikin , ina ma da ace aure suka yi ita da Ghaddafi ta samu cikin nan ? Da zata fi kowa murna da samuwar sa ,
Ita da kanta ta saci hanya ta fita , wani babban ɗakin sayar da magani ta je , bayan ta wadata mai sayar da maganin da maƙudan kuɗaɗe ya ɗau maganin zubar da ciki mai ƙarfi ya bata ,
Tun da ta saya maganin sau uku tana yunƙurin shan maganin tana kasawa , cikin satin gaba ɗaya ta sake lalacewa ta rame tamkar wacce take tsananin ciwo ,
A karo na huɗu ta runtse ido ta haɗiye maganin , ta yi kamar yadda pharmacist din ya faɗa mata ,
Cikin ƙasa da mintoci arba'in kachal jini ya fara sauƙa mata kafin ciwon ciki mai tsanani ya biyo baya , jini kuma ya ɓalle mata ,
Kasancewar ta kulle ƙofar falon ta bayan ta kori bayun da suke kula da ita sai Gnala kaɗai ya sa babu wanda ya san irin wahalar da ta sha da irin zubar jinin da tayi daga ita sai Gnala ,
Da kyar jinin ya dai-daita ciwon cikin kuma ya lafa ta samu bacci ,
Sai zuwa la'asar ta farka ta ji ƙarfin jikinta duk wasu kasala da rashin ƙarfi irin na masu ƙaramin ciki ta rabu da jin su , dan haka tayi wanka ta shirya tana jin raguwar damuwar da take ciki da kaso goma cikin ɗari ,
Kai tsaye sashin Mahaifiyar ta ta yiwa tsinke , inda ta tarar da ita a babban falon ta tana kishingiɗe bayu na mata hidima , ganin ta ya sa ta miƙe zaune cike da jin daɗi ta rungume ta tana murnar ganin alamun samun lafiyar ta ,
Duk da cewa ta hango wasu yanayi da bata gane da su ba a tare da ita amma ta danganta kome da larura irin ta jinnu da babu abunda basa sawa .
Suna zaune aka hasko fuskar Colonel Youssouf Abdoul-azizou baskore a babban tv da yake kafe a gaban su , ana bayani akan ƙarin girman da ya samu sakamakon samun nasarar kawo ƙarshen gungun 'yan fashi da makamin nan da ake yiwa take da escouade de lions , inda bayan rundunar su ta tarwatsu su daga terene , ya samu nasarar kashe manyan huɗu daga cikin su , ciki har da shugaban su Ghaddafi Yacouba Dango .
Raba hoton aka yi biyu , gefe hoton gawar Ghaddafi ne , gefe kuma hoton Youssoufa ne yana dariya lokacin da ake masa ƙarin girma .
****
Gimbiya Maimounatou ta sanya hannuwanta biyu ta share hawayen ta , kafin tayi ƴar dariya da take nuni da tasowar miƙin ƙasan ranta ta cigaba da cewa
" Tun daga wannan ranar na kuɗurci aniyar ɗaukar fansa akan sojan da ya kashe Ghaddafi da hannun sa , nima so nake na kashe shi, so nake na ɗanɗana masa baƙin-ciki irin wanda ya samar a gareni .
" Ban damu da laifin da ake tuhumar Ghaddafi da shi da yasa aka kashe shi ba , a ganina Ghaddafi bai cancanci mutuwa a yanzu ba kome kuwa girman laifin sa , akwai sasauci hukuncin kisa yayi tsanani ga Ghaddafi , mafi girman sashi na raina ma ban yadda da laifin da aka danganta Ghaddafi da yi ba , saboda ni ban taɓa ganin sa yayi kisa a gabana ko satar kayan wani ba .
" daga lokacin na shiga bin hanyoyin da duk nasan zasu taimaka min wajen cimma nasara kan ƙudiri na , a ƙarshe kuma nayi nasarar sanyawa Youssouf so na da har ta kai ga ya amre ni sanin da nayi wannan ce hanya mafi sauƙi da zata kaini ga kashe shi ,
" ga jin daɗina lokacin da nake bibiyar rayuwar sa ina kafa masa tarko bayan auren mu , sai na fahimci ba ni kaɗai bace ba ke farautar rayuwar sa , ciki har da kai da Mahaifiyar ka Mammadou , babu ɓata lokaci muka haɗa hannu wajen ganin ƙarshen maƙiyin mu , kuma ga shi a ƙarshen ƙarshe mun yi nasara ,
Wata ƴar dariya ta sake yi tana tsare ɗan sanda da ido , tace " wai ya ƙarasa mutuwa ne ko kuwa har yanzu yana shan wuya ?
Wani ƙaƙƙarfan marin da aka ɗauke ta da shi da ya sanya ta yin tangal-tangal tare da giftawar walƙiya a idanun ta ya sanya ta rufe bakin ta ruf ,
Da wani irin yanayi a muryar Tafeeda yace ,
" Babu shakka kin kasance mayaudariya , azzaluma ban yarda ke kina da ɗigon imani ba a ran ki , kamar yadda kika ce hukunci wanda yayi kisa ko ta yaya ne a kashe shi a irin naki ƙwaƙwalwar mai cike da duhun jahilci , da ke da duk wasu masu hannu cikin wannan mummunan aikin da kuka yiwa Youssouf muddin ya kai ga rasa ransa kamar yadda kuka so , wallahi baki ɗayan ku sai na kashe ku da bakin bindiga ta koda kuwa hukunci ya so muku sassauci , ni sai na kashe ku , sai na ....
Muryar sa ce ta sarƙe jikinsa har tsuma yake idanun sa sun koma ciki tsabar tashin hankali , ya juya da sassarfa ya fita zuciyar sa cike da ruɗani ashe masoyin ka da ka yadda da shi kan iya zama mai farautar ranka ? Da ya tuno irin tsananin son da Youssoufa ke yiwa Maimounatou sai hawaye ya sauƙa a idanun sa ,
wacce irin zuciya ce haka a ƙirjin Mammadou da Hajiya Mama da zai sa a haɗa baki da su wajen kashe mutum irin Youssoufa shin me ya taɓa yi musu da zafi da ya cancanci ƙiyaya irin haka ? Babu shakka mutum ya tsoraci maƙiyin sa da yake ƙin sa babu wani dalili bayan ta hassada , irin wannan ƙiyayyar mai zafi ce , tsawon zamani baya tasiri wajen goge ta .
Yana kai ga ficewa daga harabar ofishin motar su Maimartaba da kansa ta sawo kai dan haka yayi baya da tasa motar tare da sake kashe ta ya fito ,
Sama-sama suka gaisa da Maimartaba a tare da shi da mahaifin shi kansa Tafeeda , sai kuma Hajiya Mama su uku ne kawai tare da direba ,
Hajiya Mama tayi firi-firi da tashin hankali ta bi bayan su Maimartaba , Tafeeda ya dafa musu baya yana jin kamar ya shaƙe Hajiya Mama ,
A ciki kai tsaye suka nemi da a haɗa su da Maimounatou da Mammadou ,
Bayan shigar su inda suke da har lokacin kowannen su bai rusuna ba , Mammadou yana ganin iyayen sa ya fashe da kuka yana ƙaryata duk wasu kalmomin da Maimounatou ta yi , akan yana da hannu wajen kisan Youssouf ,
" Ranka shi daɗe wallahi ƙarya take min ban san kome ba , bani da hannu wajen mutuwar ɗan ouwana wallahi Abba ƙarya take min ,
Cike da nutsuwa Maimartaba yake kallon sa , kafin yace
" Mammadou , Youssoufa bai kai ga mutuwa ba , har kawo yanzou yana asibiti , zuwa nan nayi saboda na fidda kai ne daga nan muddin ta tabbata baka da hannu cikin lamarin nan , muddin kuwa aka kama ka da laifi ni bani da ikon hana mahukunta aikin su , zaka cigaba da zama a nan har zuwa yadda hali zata kasance ga Youssoufa tsakanin rayuwa da mutuwa , daga nan sai mahukunta suyi hukuncin su yadda ya dace .
Wani irin runtse ido Maimounatou tayi , tana son cewa wani abu sai dai cikar kamala da ƙima irin ta Maimartaba ya wuce ta yi wargi a gaban sa ,
Hajiya mama wacce ganin hawaye tare da tashin hankalin da ɗan ta yake ciki tare da kalaman da Maimartaba ya furta suka haɗu wajen ƙara mata tashin hankali kan wanda take ciki , ta zaburo tana cewa ,
" Ni nasani Mammadou ba zaka yi yunƙurin kashe ɗan ouwan ka ba , na san irin tarbiyyar da na yi maka , ni shaida ce akan irin ƙaunar da kake yiwa ɗan ouwan ka sai dai idan wannan makirar ce take ƙoƙarin samun abokin da zata raba laifin ta da shi , shine zata maka sharri , tsinannan ibilishiya ta Allah ba taki ba Youssouf zai tashi bai mutu ba ,
Ta ƙarasa zancen tana fashewa da kukan wanke kai ,
Kukan nata bai tsawaita ba ta tsinkayi muryar Maimounatou tana cewa ,
" Hajiya kenan, ai ibilisan muna da yawa , amma ke ce shugabar mu , idan kin ce sharri na yiwa ɗan ki akan gubar da na zubawa Youssouf dan an samu tangarɗar cikar aiki , asirin da kika yiwa Youssouf na shan giya da neman mata domin ya tozarta ya rasa damar samun sarauta shima sharri ne kenan ? Duk da cewa kowa ya shaida saboda har ɗiyar banza Youssoufa ya ajiye aikin ki kuma ya kai ga matakin nasara kamar yadda duk kika tsara Youssoufa ya rasa martabar sa a idanun Al'umma ,
Kukan kura Hajiya Mama tayi ta shiga dukan Maimounatou , tana cewa ,
" sharrin ki kaina zai dawo ? wallahi ranka ya dade ƙarya ɗiyar nan take min so take ta ga bayana , so take na tozarta shi yasa take faɗe-faɗen surruka masu nawi .
Maimartaba bai ce ƙala ba ya juya ya fita , yana fita , Maimounatou ta tunkuɗe Hajiya Mama da ƙarfi , cikin tsawa tace ,
" Saurara ɗiyar talakawa , mai gajaren asali ni nan da kike gani na ɗiyar sarki ce , sarkin da ya yafi duk wani sarki ƙarfin mulki a ƙasar nan , dan haka ahir ɗin ki da ki sake taɓa lafiyar fatar jikina , kiyi ta kan ki da ramin da yake gaban ku ke da ɗan ki, idan ku ka faɗa babu mai iya cire ku , ni kuwa kin ganni kome girman ramin da na faɗa daga Mahaifina ya ziro hannu zai tsamo ni .
Kamar wacce aka yiwa umarni Hajiya Mama tayi hanzarin barin ɗakin zuwa inda su Maimartaba ke tsaye suna sauraron muryar duk labarin da Maimounatou ta bayar ,da ƴan sanda suka naɗa a waya .
Bai jira karshen labarin ba Maimartaba yace su tafi kawai , jami'an tsaro su cigaba da yin aikin su duk ta yadda ya dace da ƙa'idar aiki ,
shi hankalin sa baki ɗaya yana ga Youssoufa da yake asibiti cikin mummunan yanayin mutu-kwakwai rai-kwakwai da a halin yanzu an gama shirin kome na fita da shi ƙasar India , lokacin tashin jirgin su kawai ake jira nan da awanni uku .
A gidan baya na motar da Hajiya Mama da Maimartaba suke zaune , banda raba ido cike da rashin gaskiya babu abunda take yi ƙwarai Kalaman Maimounatou a gaban Maimartaba suka shammace tare da ƙara mata tashin hankali , ganin kome na shirin kwaɓe mata cikin ƙanƙanin lokaci .
Muskuɗawa tayi tana kallon Maimartaba tayi ƙanƙan da kai ta fara cewa ,
" wannan ɗiya lamarin ta abun tsoro ne, dukkananin kalamanta cike suke da ƙarairayin....
Da hannu ya dakatar da ita ba tare da ya dubi sashin da take ba yace
" Su kalaman mutum suna iya zamar masa tarko su fallasa ko wanene shi , ita hanyar mugaye kuwa duhu ne baƙi ƙirin, kamar duhun dare , da har sukan faɗi a cikin turbar su amma ba su san abin da ya sa suka yi tuntuɓe ba , sukan manta da cewa ita mugunta rami ce mai zurfi da a ƙarshe da mai tonon ta take ruftawa ciki , ki adana kalaman ki akwai wajen yin su ba nan gabana ba .
Muƙut ta haɗiye busasshen yawun tashin hankali , ta san irin wannan zaurancen na masu hikima da mafiyawancin lokuta Maimartaba ya fi amfani da su cikin kalmomin sa .
Hasashen manufar kalamansa ya sa gumi karyo mata yana tsiyaya ta cikin jikin ta , " Babu shakka kwaɓarta tayi ruwa tsululu .
****
Ƙarfe biyu na ranar jirgin da zai tafi ƙasar India ya ɗaga da Youssoufa yana a halin rashin sanin ina yake ? A tare da shi da Maimartaba da kansa , da Hajiya Umma da kuma Tafeeda .
Tamkar wutar daji haka labarin gubar da Matar Biyamuradi Youssoufa da ɗan ouwan sa Mammadou suka ciyar da shi ya shiga ratsa kowanne lungu da saƙon ƙasar Niger baki ɗaya ,
Cikin kwanakin duk wasu kafar yaɗa labarai zancen ake ana sake maimaita sa , har wani sashi na daga muryar Maimounato cikin labarin da ta bayar kan dalilinta ake sakewa ,
A halin haka labari ya shiga sauya salo da launi iri-iri dake ƙara munana sa , wasu ma cewa suke ai fasiƙanci Maimounatou da Mammadou suke yi , da kuma sanin ita uwar Mammadou ita ce ma ta bada gubar da aka ciyar da Youssoufa ita .
Tozarta da ɓacin suna irin wanda Hajiya Mama bata taɓa zaton afkuwar sa a gare ta ba , ita ce ta faɗa mata lokaci ɗaya ,
Tuntuni labarin irin auka-aukar da Maimounatou tayi ya iske kunnen iyayen ta , da hakan ya sa take jinin Maimartaba sarkin Agades ya hau , aka ciccɓe shi ranga-ranga zuwa asibiti .
Nan take wasu daga cikin dangi suka fara Allah wadarai da ita .
Assalamu Alaikum masu karatu da fatan kuna lafiya ?
Ina sane da haƙurin bibiyata da kuke yi , ina kuma godiya bisa yawan ƙaunar ku ga rubutuna nagode irin sosai ɗin nan , nima ina ƙaunar ku a duk inda kuke ina muku fatan Alkhairi .
Nagode
[12/26/2019, 9:58 PM] +234 706 503 6187: MAFARI
( Hargitsin Rayuwa)
Umm'muaz
47
Falmata tun tana zuwa ɗakin Hajja tayi ta zama ba tare da ta iya faɗin abunda ke kaita ɗakin ba ,
Har dai a kwanaki shida bayan zuwan su ta daure bayan sun gaisa da Hajja wacce take kishingiɗe akan ƴar katifar ɗakin ta , ba tare da ta yadda sun haɗa ido da Hajja ba tace ,
" Hajja daman zuwa nayi nace miki , un'un wai inji Baa , sai kuma tayi shiru ,
Hajja wacce ta tashi zaune , tace ,
"Uwarɗakina faɗi mana , me kike son faɗa min ?
"Daman nace Hajja idan kun yi waya da shi ki ce masa akwai saƙon da nake son faɗa mi shi inji Baa ,
Kallon tsanaki Hajja take yi mata kafin ta ce , " Shi wa fa ?
Ɗago kanta tayi ta saci kallon Hajja , tana sake gintse fuska tace , " shi Baban Mama ko ?
Salati Hajja ta sa tana tafa hannuwa , kafin tayi ƙanƙan da ido tace ,
" Ke Fatima ki fita idona na rufe ,nace ki fita idona , idan ba kin mayar da kanki wata bi ta can ba , har kya bani saƙo wajen Mijin ki ? Cewa nake ke kika fi kusanci da shi fiye da kowa a ƙasar nan ? To bari na faɗa miki daman ina cike da ke akan irin sakarcin da kika yi na gudowa daga ɗakin auren ki , akan wannan mummunar zuciyar taki mai ƙullaci da bauɗaɗɗan halin ki na miskilanci idan baki gyara kin nutsu kin san ina ke miki ciwo ba ke ce da Nadama marar amfani wataran , ni nagaji da nuna miki gabas kina daɗa bauɗewa,
Zunburo baki Falmata tayi , ƙasa-ƙasa tace " to ai ba komawa zan yi ba ,
Ashe maganarta ta shiga kunne Hajja , sai ji tayi tace ,
" Auho aikin kawai kike domin shima kuwa wannan karon kin kai shi bango da iyashegen ki , dan tunda muka taho yau kwana shida muna yini na bakwai bai biyo sawun mu ba ko da da ƙiran waya , ni kuma na ƙira layin nasa da nake da shi bai tafiya , ai kin ga sai ki zuba ruwa a ƙasa ki sha , idan zaman gidan daɗi ne ki zauna ga waje kiyi ta zama har mahadi ya bayyana .
Daga haka ta jaa bakin ta ta tsuke tana kawar da kai .
Rai a ɓace Falmata ta miƙe ba ko sai anjima ta fice a ɗakin , Hajja ta bi
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Chapter 110
Chapter 111
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 85 Chapter of 111