Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ganin ta kan Sofi wacce ta jirkita sosai kan kafaɗun Doctor Hamza kirjin ta daf da fuskar sa , fiye da rabin cinyar ta na kan jikinsa ,  kan ta a ɗage sai shan ƙamshi take , ko ƙala bata cewa Hajja ba , "ah to wacece ita 'yar aikin zata gaisar ? Ƙanƙan da ido Hajja tayi , " Yau ina ganin taɓara maigida da kukan tsarki , mene haka wata shaɓatartar da ke kin wani ɗaɗɗane ɗan mutane ƙin kalmashe shi ? O ni hauwa'u inda ranka ka sha kallo , ikon Allah 'ya'yan zamani , mu lokacin mu ina muke iya ɗaga ido mu dubi miji a gaban mutane ? Cike da 'yar kunya doctor Hamza ya miƙe bayan ya ture Sofi daga jikin sa ,  yace , " Rahima bata nan ko Hajja ? A ɗan sama mana abinda zamu ci please ina tare da yunwa , " Rahima bata nan likita , bata ƙaraso ba daga Makaranta , to babu laifi yanzu kuwa za'a samar da abinci ,sannun ku da hanya , Wani banzan Kallo Sofi ta jefawa Hajja tana bin bayan mijinta , cikin ranta cike da haushin kalaman Hajja , cikin ran ta tana cewa , "ji min tsohuwar nan da kinibibi ? Ko ina ruwanta da ni ," ? Idan har ta ce zata shiga harka ta kafin na bar gidan nan sai na ratsa mata tarbiyya ,' " Mts   Hajja ta saki tsaki bayan barin su falon , "abun haushi Nama na jan kare ,  me ake da mace marar kunya da kamun kai ? Kunya ai ado ce . Murnar labarin da Falmata ta bata na samun warakar ta ya taso yayi awon gaba da takaicin da sofi ta bata , ***** Washegari bayan Doctor Hamza ya shirya kai tsaye ya nufi yin abunda ya kawo shi garin . Bayan ya je sun gaisa da Prof shi da Sofi , daga bakin mashigar sashin Prof ya dakatar da ita daga binsa , " Sofi ki koma ciki , ni fita zan yi sai na   dawo , Zunɓur-ɓur ta turo baki ,    Cikin salon da koyaushe take amfani dashi idan tana gaban shi na ƙoƙarin ta nuna masa ƙuruciyar ta da a zahiri ta riga ta yi mata adabo ,         A shagwaɓe tace "Haba mana Doctor please zan bika mu tafi tare naga gari , ka ga fa irin yanayin gidan shiru ba... "please Sofi kar ki ɓata min lokaci a banza ai kin san yanayin gidan babu abokin hira kika dage sai kin biyo ni , kuma ni wajen aiki zan tafi ba yawo a gari ba ,   Juyawa yayi ya ƙarasa ga motar sa ya shige ciki bai ko sake waigowa ta kan ta ba ya tada motar yayi tafiyar sa , " jagale ! Tayi a tsaye ranta cike da ƙuna ,     "so take ta san meye Doctor yake ƙullawa a garin da yake ta zirga-zirga a tsakanin Maiduguri da Abuja , Cikin wata guda wannan ne zuwan sa na uku , ita fa duk wani abu da zai sha gaban ta , ya mata katanga kome ƙanƙantar sa da Doctor Hamza yaƙi take yi da koma menene , Ko aikin sa dan bata da ikon hana shi ne amma da tuni ta shata layi tsakanin su , so take koyaushe ya zama bashi da uzuri sai nata , A fusace ta juya ciki , **** Kai tsaye gidan Amne ya nufa , ya taddata tana karin kumallo da Fankaso da miyar gandar ƙafar sa , Ya gaishe ta cike da ladabi , ta amsa tana mai farin-cikin ganin sa , Tambayar sa tayi ya safiyya ? Ya shaida mata ai tare suka zo garin . "Shine kuma baka kawo min ita mun gaisa ba ? Ta furta haka lokacin da take zuba masa miya akan fankason da ta zuba masa , "Amnee fita zamu yi tare zuwa wani waje , Ya furta haka lokacin da yake kai lomar farko bakin sa. " ina kuma zamu ? Allah yasa dai Lafiya . "lafiya lau Amne sai Alheri , cikin nutsuwa ya gama cin abincin sa , Bayan ya wanke hannu , yace "Amne zamu iya tafiya yanzu ko kina da wani uzurin da zaki yi ? "ba abunda zan yi , amma tukun wai ina zaka kai ni ? Kaƙi sanar da ni . "kiyi haƙuri Amnee mu je ki gani , "to bari na yafa mayafi na , Tare suka fito shi da ita ya buɗe mata gidan baya na mota ta shiga ya rufe , gami da zagayawa ya shiga ya tada motar yana barin unguwar , Ya riga ya gama tsara hanyoyin da zai bi domin ganin ya dai-daita lamarin iyayensa , wanda daman burin sa ne tun ma kafin bayyanuwar Khaalty Rahima a gare shi , Bayyanar ta ya sauƙaƙa masa lamarin , ya kuma ji daɗi domin yasan dawowar ta a dai-dai lokacin matakin nasarar gyaruwar kome ne wanda hargitsewar kome yake da nasaba da ita , Bayan duk lallamin da yayi mata akan  ya mayar da ita gida , amma taƙi amincewa , Cikin dogon nazarin da yayi ya yanke shawarar haɗa su kitsumun , ba tare da sanin kowaccen su ba . Dan haka a yanzu da ya ɗau Amnee kai tsaye ya nufi gidan da Khalty Rahima take ba tare da ya sanar da kowaccen su game da 'yar uwarta ba . Suna 'yar hira shi da Amnee har suka iso ƙofar gidan , ya fita a motar ya nemi iznin shiga gidan daga maigadi inda ya amince nan take har ma yake sake jaddada masa , ai kuwa Mamar Bulama tana , Tare da Amnee suka shiga wacce take cike da mamakin ina Hamza ya kawo ta ? Gurin wa suka zo ? Allah dai ya sa lafiya , Shi ya fara shiga sashin da Khaalty Rahima take , daga bakin ƙofa ya dogare ,  yana fuskantar Cikin gidan daga inda yake yana hango Khaalty Rahima wacce ta duƙufa yin wanki daga gefe , Babu Alamun ta san da tsayuwar sa a wajen , "Bissmillah Amnee shigo , " Assalamu Alaikum , Amne ta ce lokacin da ta shigo filin gidan , Dai-dai da ɗagowar Khaalty Rahima wacce sautin Hamza ya ankarar da ita tsayuwar shi a wajen , Zuciyoyin su suka buga da wani irin yanayi mai girma , daga ƙasa har sama Amnee take kallon ta , Kowanne irin jirkituwar halitta ce ta samu Rahima ƙanwar ta , ba zai sa ta gaza gane ta ba , "Rahma,  Rahmatullah , Ta ƙira ta da wani ɗan guntun sauti , "Rahmatullah hal hdha haqiqiun lak 'Yaa ukhtee ? ( shin dagaske ke ce 'Yar uwata ? ) A hankali ta saki rigar hannun ta da take wankewa  , Da hannu biyu Amnee ta rufe fuskar ta lokacin da hawayen farin-ciki ya fara zarya akan fuskar ta , Bata jira ƙarasowar Rahima ba wacce take tahowa da sassarfa , ta taka da sauri ta tadda ta , Rungume juna suka yi hawayen murnar ganin junan su na sauƙa , Khaalty Rahima bata san haka take cikin maricin tare da kewar 'yar uwar ta , yayar ta , madadin uwa agare ta ba sai yanzu da ta gan ta tsaye a gaban ta bayan tsawon shekaru fiye da ashirin da suka kwashe basa tare . Hannu biyu Amnee ta sa ta riƙe fuskar Rahima , "ke ce wannan Rahimatullah ? Meyasa kika tafi kika barni ? Kina garin nan Rahimatullah duk tsawon shekarun nan bakya nema na ? Meye na miki mai girma haka Rahimatullah  ? "Rahimatullah wacce irin Rayuwa kike yi tunda kika barni ? Nan ne gidan ki ? Kin yi aure ne ? Ina maigidanki ? ki min magana mana ƙanwata Muryar Doctor Hamza ta ratsa tsakani , shi da kansa ƙwalla ta taru masa a ido , irin ƙaunar da yake hangowa a fuskar kowaccen su ga 'yar uwar ta , ta masa yanayi da na yaran nan biyu 'yan gudun hijira . "Amnee ki kwantar da hankalin ki , Khaalty Rahima ta gamu da larura tana jin magana amma bata iya mayarwa , Sabon Kuka Amnee ta fashe da shi , "Rahimatullah ce ta kurunce ? Meye haka ya faru da ke Rahimatullah ? Cikin ruɗani ta waiga ga Hamza " mu tafi asibiti a duba min ita yanzu Rahimatullah Amana ce a wajena , Da sigar rarrashi khaalty Rahima ta jijjiga hannun Amnee da yake cikin nata , Waigowa tayi tana kallon ta , Murmushi tayi mata , ta kai hannu ta goge mata hawaye tana girgiza mata kai , ƙoƙarin taro ta Amnee take lokacin da ta ga tana ƙoƙarin tsugunnawa , tare suka durƙusa , Khaalty Rahima ta rubuta mata a ƙasa cikin yaren su , "ki daina kuka , murna yakamata muyi da sake ganin junan mu Yaa Amina . Bayan Awanni biyu Doctor Hamza , tare da Amnee da Khaalty Rahima da Bulama suka kama hanyar komawa gidan Amnee. Ga mamakin Hamza Khaalty Rahima bata yiwa 'yar uwarta irin tirjiyar da tayi masa kan komawa gida ba , Ko daman dan bata ga 'yar uwar tata bane a gaban ta ? abunda ya ɗan riƙe su a gidan shine batun tafiya da Rahima da ɗan ta da suka yi wanda da farko matar da khaalty Rahimar take yiwa aiki bata Amince ba . sai da suka bata gamsassun bayanai tare da ƙwararan hujjoji ta kuma ga shaida tare da Amincewar ita kanta Khaalty Rahimar tukun ta yarda ta sallami Rahima tare da yi mata fatan Alheri . Da shigar su gida Amnee ta shiga hidimar Khaalty Rahima , kama daga shirya mata wajen zama na musamman har zuwa gyara mata shimfiɗar da zasu kwana ita da ɗan ta. Abunda ya sake bawa Hamza tausayi shine duk inda Amnee ta gusa , Khaalty Rahima zata matsa kusa da ita tana yunƙurin karɓe aikin da take yi , Amnee taƙi sakar mata , banda murmushi mai cike da tarin ƙauna da tausayi babu abunda suke yiwa junan su . Sai da Amnee ta gama gyara musu waje tsaf sannan ta dawo ta zauna kusa da Rahima , ta riƙo hannun ta tace , "Rahimatullah ina son jin labarin yadda kika yi rayuwa bayan barin ki gida , amma babu dama a yanzu , inshaAllah daga gobe zaki fara ganin likita , Gyaran murya Doctor Hamza yayi , "Amne Ya ƙira sunan ta , a hankali ta waigo gare shi , "Amnee ina son dan Allah yau ki bani labarin abunda ya faru da rayuwar ku ke da Baba da Khaalty Rahima ? Dan Allah kar ki ƙi , ki ban labarin a matsayin tukuicin dawo miki da Khaalty Rahima da nayi . Shiru tayi na wani ɗan lokaci , kafin ta sauƙe ajiyar zuciya , *** "Labarin ba wani mai daɗi bane da kake naciyar sanin sa , "Kamar yadda ka sani ne mu 'Yan asalin ƙasar Chad ne daga Babban birnin N'Djamena , inda aka haife mu , iyaye da dangin mu baki ɗaya.  "Mahaifin mu sajjan ne ( mai gadin gidan yari )  a babban alsijn na ƙasar mu , albashin sa bai cika yawa ba dan haka mai ƙaramin ƙarfi ne sosai , dangin sa duk talakawa ne ,  haka ma mahaifiyar mu ta fito daga gidan talakawa sosai , sana'ar iyayenta sarrafa gishiri daga bakin teku su kawo cikin gari su sayar , ni ce Babbar  'yar su sai ƙanne na maza huɗu "Salihu , Mohammed , Usman da Jamil  sai ƙaramar mu Rahimatullah . "Rahimatullah tana shekaru biyar ni ina da goma sha shida Mahaifiyar mu ta rasu , inda ba'a ɗau lokaci ba bayan mutuwar ta Maifinmu ya sake yin aure , ya auri wata mata mai 'ya'ya huɗu daga ƙabilar N'gambaye mabiyar Adinnin Christian ƴar ainahin ɗarikar Roman Catholic . "zuwan "Aichawa rayuwar mu shi yayi sanadiyyar faɗawar mu ƙunci domin Aicha irin mugayen matan nan ce marar imani , babu irin aikin wahalarwa da bata sanya mu , Su salihu sun zame mata masu nemo mata kuɗi , inda ni kuma na zama baiwar ta mai yin duk wasu aikin cikin gida, hatta Rahimtullah da take ƙanƙanuwa bata tsallakewa izaya daga hannun Aicha ba . "shi da kansa Mahaifin mu bai tsira ba daga bala'in ta dan a wasu lokutan har duka take yi masa , idan ta nemi kuɗi bai bata ba, hakan ya sa yake masifar tsoron ta ba shi da kataɓus , ya auro jaraba . "mugun neman kuɗi irin na Aicha ya sa nima ta sama min aikin goge-goge a babban ofishin jakadancin ƙasar mu tun a wancen lokacin da ba'a cika barin 'ya'ya mata fita neman kuɗi ba , "karatu ma alokacin iyakata primary ban ci gaba ba .  "da murna na fara zuwa aikin saboda ganin zan huta daga masifar Aicha da wahalar aikin gida , sai dai kuma tunanin Rahimatullah da zan dunga bari a gida ya rage min karsashi , " ganin cewa aikin nawa shara ne da goge-goge sai na nemi iznin na dunga zuwa da Rahimatullah tana zama a gefe ni nayi aikina , saboda nasan idsn na bar ta a gida azaba za'a dunga gana mata , cikin sa'a aka amince min . "Tafiya ce miƙaƙƙiya a ƙafa daga unguwar mu zuwa wajen aikina , amma haka nake goyon Rahimatullah daga alfijir ya keto mu ɗau hanya , kafin lokacin da muke isa gari ya waye sosai , "Haka zan yi aikina Rahimatullah tana ƙiriniyar ta , "Rahimatullah irin yaran nan ce masu son wasa , hakan ya sa sai ina aiki ina kaffa-kaffa da ita kar ta yi musu ɓarna dan wani lokacin ma sai na neme ta na rasa ta shige ƙarƙashin tebura ko tayi wani wajen , "Amne ta tsagaita tana duban fuskar Khaalty Rahima wacce take murmushi , "Ashe Bulama ba a ƙasa ya tsinta ba gado yayi ,   Doctor Hamza ya kitsima hakan a ransa , Amnee ta cigaba da cewa , "Na ɗau tsawon watanni shida ina aikin goge-goge a ofisoshin guda biyar kafin a rage min yawan su zuwa kula da ofishi biyu rak , na wata mata Basudaniya ( Sudanese )"Mademe Laura , da kuma na wani jakadan ƙasar Nigeria "Al-Mustafa Dilmari . "tsakanina da su Gaisuwa msi cike da girmamawa ne idan sun iso ofis sun tarad dani a bakin aikina , "wata alaƙa bata taɓa gifta tsakanin mu ba sai Ranar da Rahima tayi wata mummunar ɓarna a ofishin Ambassador Mustapha , inda ta yayyaga wasu takardu masu muhimmanci da ya mance ya tafi ya bar su a ofishin sa ba tare da ya adana su ba , "Ranar na shiga tashin hankali domin kuwa faɗa sosai ya dunga yi min , bai tsagaita ba sai da Rahimatulla wacce take goye a bayana , saboda zamu tafi ƙiran sa ya cimmin , ta leƙo da kanta cikin harshen larabci ta ce da shi yayi haƙuri ya daina yi mana faɗa irin yadda Aichatuwa take yi mana kullum ai ita ta yaga takardun tana so ta yiwa ƴar tsanar ta kaya , "Ban san dalili ba sai naga ya sassauta fishin sa , a ƙarshe yace mu tafi kawai , "tun daga ranar sai naji tsoron sake zuwa da Rahima domin kar tayi wata ɓarna sa zata sa a kore ni daga aikin wanda albashin sa a lokacin da shi nake yi mana hidimar yau da kullum  ni da ita duk kuwa da cewa kaso uku Aichatuwa take raba albashin ta ɗau kashi biyu da rabi ta bani guntun , "daɓ dole nake barin ta a gida tana kuka , wani lokacin nima har ta saka ni ƙwalla , nake tafiya na bar ta , "ba'a yi sati guda ba wata safiya har na kammala aiki zan tafi , Ambassador Al-mustapha ya ƙira ni , zuciyata cike da tsoro na je na ɗauks batun laifin Rahima ne bai wuce ba ko kuma ni ce na sake yin wani laifin . " ga mamakina sai naji yana tambayata ina ƙanwa ta take meyasa na daina zuwa da ita ? " na ce masa tana nan , inajin tsoron kar ta sake ɓarna shiyasa na daina zuwa da ita , " sai ya umarceni da mu cigaba da zuwa tare amma na dunga lura da ita kar ta dunga yin ɓarna , "shikenan Tun daga ranar na cigaba da zuwa da Rahima , "a hankali sabo mai ƙarfi ya shiga tsakanin Ambassador Al-mustapha da Rahimatullah saboda 'yan kayan maƙulashe na yara da yake mata hasafin su , "kafin wasu watanni shaƙuwar su da Rahima ta shafeni wanda a ƙarshe cikin shekara guda tsakanin mu ya rikiɗe ya zama soyayya ce mai ƙarfi , "duk kuwa da tazarar matsayi da yake tsakanin mu hakanan Allah ya kulla auratayya a tsakanin mu , bayan rigin-gimu da suka taso daga dukkan ɓangarorin biyu , daga Aichatuwa , da bangaren iyaye da 'yan uwa Al-mustapha na jini , wanda suks tirje akan ba zai auri 'yar wata ƙasa ba wacce ba ƙabilar su ta kanurai ba , alhalin ga 'yar uwarsu wacce take dakon jiran sa suyi aure , "hakanan ɓangaren Aichatuwa wacce ta bi duk wata hanyar da zata iya bi domin ganin auren mu bai yiwu ba da Mahaifin ka , amma dayake shi aure Kaddara ce daga kaddarorin da Allah yake yi ga bayin sa . "A ƙarshe aka ɗaura Auren mu ni da Mahaifinka tare da Amincewar kakan ku wanda ya taka har ƙasar mu ya nemawa ɗan sa aurena cikin mutuntawa , bai duba ƙasƙancin mu da shi yake babban Attajiri a ƙasar su kuma mai ilmin addini da na boko tun a wancen zamanin . " Bayan auren mu mun zauna shekara guda a N'Djamena kafin aikin mahaifin ku ya ƙare da ƙasar mu , muka kuma fara shirin komawa ƙasar su , "a kuma tsukin wannan lokacin Allah ya yiwa Mahaifin mu Rasuwa sakamakon sukar sa da wuƙa da wasu ga cikin 'yan firsina suka yi a ƙoƙarin su na gudu daga gidan yari . "Mutuwar Baban mu ta gigita mu ganin cewa duk wani gatan da muke da shi ya ƙare , "a ƙarshe dole muka haƙura , riƙon Rahima kachokam ya dawo hannun mu da duk wasu ɗawainiyar ta Al-Mustapha ke yi , "Sauran ƙannena maza suka raɓu da gidajen 'yan uwa  , , "Ba mu jima ba bayan nan muka koma Nigeria tare da Rahimatullah da   kuma kai a lokacin kana ɗan jariri . "na fuskanci tsangwama da ƙiyayya iri-iri daga kakar ku , da dangin mahaifin ku da baki ɗayan su basa ƙaunar auren mu , idan aka ɗauke Salman wanda ƙani ne na uku ga mahaifin ku da shi babu ruwan sa da duk wasu lamura da suka shafe ni . "Haka shekaru suka yi ta tafiya tare da nasarar rayuwa , matsala mafi girma da ta zama sanadin rabuwar auren mu da mahaifin ku ya samo asaline daga lokacin da Soyayya ta shiga tsakanin Salman da Rahimatullah , "lokacin Rahima ta gama makarantar gaba da primary , kai kuma ka shiga makarantar kwana ta gaba da primary , "rikicin an ɗauki lokaci ana yin sa tun bayan bayyanuwar soyayyar su da suka yi shekaru biyu suna boyen ta a tsakanin su , "Salman ya doshi mahaifiyar su da sauran 'yan uwan sa da batun auren Rahimatullah , ƙaramin yaki aka yi a tsakanin su saboda lokacin kakan ku ya jima da rasuwa . "Lamari yayi tsamari da yasa har kakar ku ta ƙira mahaifinku ta masa kashedi kan muddin yana son Albarkar ta , ya zama dole ya raba tsakanin ƙanwar matar sa da ƙanin sa , "daga lokacin shima Mahaifinku ya fara nuna adawar sa da soyayyar tsakanin Salman da Rahima domin bin umarnin Mahaifiyar su , da hakan ya kawo saɓanin a tsakanina da shi domin ni ɗari cikin ɗari nake tare da su akan lamarin soyayyar su . "ana cikin wannan hatsaniyar uwar matar da aka so aurawa Mahaifin ku wacce take ƙanwar kakan ku ce ta zo da wani lamari mai yanayi da tsafi ko kuwa chanfi  , kan cewa muddin ba'a yi gaggawar raba tsakanin Salman da Rahima ba to babu makawa guda a tsakanin su zai mutu , domin Malamin ta yace babu aure a tsakanin su , ' "Maganar bata ɗaga min hankali ba sai da naga kamar Mahaifinku ya yarda da batun inda har ya fara maganar ko dai Rahimatullah zata koma N'Djamena na ɗan wani lokaci , idan kome ya lafa ta dawo ,ranar nayi kukan Maraicin mu da rashin gatan mu  , " an yi haka bai fi da wata guda ba , Rahima ta gama shan kukan ta akan wannan batun , Babban Al'amari ya afku, "Ranar wata juma'a bayan Rahimatullah da Salman sun gama hira da rabin ta neman hanyar warwaruwar matsalar su suke tare da kaiwa ga cikar burin su , "ƙarfe biyu da rabi na ranar bayan sallar juma'a labarin Rasuwar Salman Dilmari matashin Saurayi, ya bazu tare da yin tambari a baki ɗayan birnin Maiduguri kasancewar sa matashin ɗan siyasa da ya yi suna a lokacin , "ya rasu a sakamakon mummunan haɗarin mota da yayi akan hanyar sa ta komawa daga masallacin juma'ah mintoci arba'in da rabuwar su da Rahima , " mutuwar data girgiza zukata da dama , ta kuma bar miƙi a zuciyoyin wasu da dama , Salman Mai Alheri ne , Allah ya gafarta masa , Shiru ne ya ratsa tsakanin su saboda kuka haiƙan da Rahima take yi , kukan tasowar tsohon miƙin dake zuciyar ta da ya tarad sabon ciwukan dake cin ranta a kullum kwanan duniya , Mutuwar  mijinta uban 'ya'yan ta da ta tarar da gawar sa a yashe cikin gona , haka kuma tana ji tana gani ta tsallake shi domin ceton ranta da na 'ya'yan ta ta tafi ta bar gawar sa a daji,  tare da ɓacewar manyan 'ya'yan ta da har yau bata da sanin haƙiƙani kan rayuwar ko mutuwar su ta ma fi haƙaƙewa akan Yakaka da Falmata sun mutu kamar yadda harsashi ya samu Baana yayar Bulama ta mutu akan cinyar ta , Bakin lafayyar ta Amne ta sanya ta sharewa Rahima hawaye sannan ta cigaba da cewa , "Fasalta irin halin da baki ɗayan zuri'ar Dilmari ta samu kanta a ciki bashi yiwuwa ,   "ai ka san lokacin kana da wayo sosai kana secondary School , gyaɗa kai Hamza yayi wanda idanun sa suka yi jaa , " Rahima ta shiga ɗimuwa marar misali domin har suma ta dunga yi , sai da Maigadin gidan ku na lokacin ya dunga yi mata rubutu , cikin sati guda da mutuwar sa Rahima ta rame tamkar majiyanciya , ni da kaina ƙarfin hali nake yi , nake hana kaina tunani saboda tsohon cikin Rahima ƙarama da nake ɗauke da shi . "abu mafi muni da ya biyo bayan mutuwar Salman shine takowa da 'yan uwansa suka yi har gida bayan kwana arba'in da mutuwar sa , suka ci mutuncin mu ni da Rahima , a ƙarshe suka danganta mutuwar Salman da cewa ni da Rahima muka lashe masa kurwa muka kashe shi , to waye ya san salsalar asalin mu ?? "Ni kuka Rahima kuka , sannan abun takaicin mahaifinka yana zaune ya gagara hana su ko ɗaukar wani mataki na ba mu kariya , wanda hakan ni kuma ya tunzuro ni , na yunƙuro domin maida musu martani a karon farko bisa duk abubuwan da suke min marasa daɗi , "Ga maɗaukakin mamakina sai mahaifinka ya hayyaƙo min ya takore ni daga yin magana har ma yace muddin nace wani abu kome zai iya faruwa ga igiyoyin auren mu , "bisa tilas nayi shiru sai hawaye da muke yi ni da Rahima suka gama zage mu tas har da dungurin Rahima da alama ma duka suke da niyyar yi mata sai ɗan uwansu ya rarrashe su , 'tundaga wannan ranar Rahima ta sake yin sanyi duk ta susuce firgici ya bayyana cikin suffar ta bata da aiki sai tunani   , "duk da ceqa ina bin duk wasu hanyoyi domin kwantar mata da hankali duk da cewa nima hankalin nawa a tashe yake domin

Chapter 71 of 111