Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
na sauke ki gida . A motar ma share hawaye yakaka take sosai take jin ciwon barin ta da zai yi , yace wai ta manta da shi , anya ? Ita ta san baza ta iya mancewa da shi ba ," ya samu wani irin gurbi mai girma ya kafa kan sa cikin zuciyar ta ,"  kiran wayar sa shi ya katse shirun su , samun waje yayi ya tsayar da motar a gefen hanya , " nan ya amsa wayar     Kira ne na gaggawa ake yi masa daga sansanin su na soji ! Da sauri ya buɗe murfin motar da hannu yake yiwa yakaka alama na ta sauƙa masa a mota ," Jikin ta a sanyaye ta sauƙa tana gama ficewa a motar ya ja murfin da ƙarfi ya harba motar bisa titi a guje .' tsumu ta tsaya a gefen hanyar tana sake kallon kuɗin hannun ta ," kome bai mata daɗi wani irin ɗaci take ji daga ƙasan ran ta yana taso mata ,   Matsawa tayi jikin wata mota da take tsaye a gefe ta jingina jin da tayi tsayuwa na neman gagarar ta ," kuka take son yi so take ta samu wuri tayi ta kuka ko zata ji saukin abun da take ji a ran ta , da gaske ya tafi bazai dawo ba ? ko wasa yake yi mata ? Tun kafin ya tsallako titin daga ɗan shagon da ya tsaya ya saya kayan marmari a gefen titin ,  hasken ta ya dalle masa idanu , amma kasancewar sa mai tsananin kamun kai da nutsuwa babu ruwan sa da harkar mata (irin yadda samarin yanzu suke )  ya sa yayi saurin ɗauke kan sa , Har ya ƙaraso jikin motar da take jingine da take mallakin sa ce bai sake kallon inda take ba ," Murfin motar ya kama zai buɗe sannan ya juyo ya dube ta ,"     Baiwar Allah zan ɗauke motar daga wurin ,!     Ko gizau bata motsa ba   Ɗan tsaki ya ja marar sauti , wasu matan dai basu da kamun kai dubi wannan yadda ta zo ta dogare a bakin titi duk masu wucewa idon su akan ta . Ya sake maimaitawa da ɗan karfi ,    Zan ɗauki motar nace baiwar Allah a hankali ta juyo da fuskar ta inda take jin tashin muryar sa , kamar ta san muryar ,!    Kallon juna suka yi ido cikin ido , Tsai yayi yana kallon ƙwarar idon ta , shin ita ce ne ko ba ita bace ? Ƙwarar idanun ta suna tabbatar masa ita ce wacce ya shafe fiye da watanni biyu yana neman ta tsakanin sansanin su da zagayen kasuwa ,wacce a karshe ƙawar ta tace sun gudu sun bar garin ," sai dai kuma yanayin shigar ta da gogewar da ya hango tare da wannan suna ƙarya ta masa ita ce , wacce ya sani ai ƴar ƙauye ce ƙazama , wannan kuwa ƴar birni ce wayayyiya kuma ƴar gayu ," kai sai dai kamanni , ," da sauri ya saita kan sa daga ruɗanin da ganin kamar wacce yake bulayin nema ce ya sanya shi ,"   Ya ɗaure fuska gami da maimaita maganar sa ta farko cikin ƙosawa ," A hankali ta janye jikin ta daga motar , "     Ta gane shi sarai shine likitan da ya sha taimakon ta tun farkon zuwan ta garin ,"! Sai dai halin da zuciyar ta ke ciki a yanzu babu damar da zata tsaya yin magana da kowa ko da kuwa kalmar gaisuwa ce , domin tana buɗe baki kukan da take yi a zuci ne zai fito fili , dan haka ta ɗauke kan ta ,' ta matsa bakin titin sosai domin tarar adaidaita ya kai ta gida tayi jinyar gangar jiki da ruhin ta da tun yanzu suka fara kewar bature kam silum ," Tana matsawa a jikin motar ya shiga gami da jan motar sa , a cikin ran sa yana mamakin al'amarin hatta tafiyar su iri ɗaya ya furta hakan a fili yana sake leƙen ta ta jikin madubin motar ,"  gefe guda na ran sa ƙaunar yarinyar da har yau bai ko kai ga sanin sunan ta ba yana tasowa , ya so ƙwarai ya nemo ta , domin a ranar da suka bar asibiti ita da ƙanwar ta ba ƙaramin damuwa ya shiga ba , so yayi ya ɗauke su ya kai su gidan sa inda yake zama tare da mahaifin sa da ƙannen sa ya ɗau nawin su ya inganta rayuwar su ita da ƙanwar ta , ya sha wahalar neman su da kwatance su a sansanin su dakyar aka samu wacce ta san su aka ce tare suka zo , tashin farko da ya tambaye ta game da su tace da shi YAKAKA DA FALMATA SUN BAR GARIN . Assalamu Alaykum  my dear sisters ! How are you guys doing today  ? I hope everything is well ? Please don't delete comments because I didn't reply straightaway . I hardly get time to come frequently , but I do dedicate some time every now and then to reply to y'all Insha Allah  ! I hope you guys enjoyed this chapter  ??  buckle up cause chapter twenty is going to be a sadness one!  LET ME KNOW WHAT YOU GUYS THOUGHT ,PLEASE  COMMENT , VOTE, AND SHARE WITH YOUR FRIENDS AND FAMILY.     THANK YOU .               [6/24, 10:59 AM] +234 701 013 7848: MAFARI ....... Hargitsin Rayuwa umm"muaz 20 Yakaka tana shiga gida Kai tsaye sashin samy baby ta nufa , ta ci sa'ar samun kofar ɗakin ta a buɗe kai tsaye ta danna kai cikin ɗakin idanun ta a rufe da ruwan hawayen da yake ambaliya ," Zube guiwar ta tayi a ƙasa tare da yin jifa da kuɗaɗen hannun ta suka tarwatse a tsakiyar ɗakin ,hannuwan ta biyu ta sa ta rufe fuskar ta lokacin da take sakin kukan da yake cin ta a zuci . Sautin kukan da yayi sanadiyyar tashin samy baby a firgice daga baccin tofon girar da take shaƙa ,"  Da sauri ta zo ta kama ta Yaks meye ya same ki ? Duka aka miki ? Ko meye ? Kusan ba a hayyacin ta ba ta riƙo hannun samy baby ,   Dan Allah ki ce masa ya dawo kar ya bar ni , idan bana ganin sa mutuwa zan yi , kin ga nan ,"ta ɗora hannun samy baby akan zuciyar ta ,"ciwo take min ina jin wani abu ya tokare ni ," INA SON SHI WALLAHI INA SON SHI," Kalmar ta ta ƙarshe ita ta sa samy baby kwashewa da dariya bayan fitar ta daga ruɗanin da kukan yakakar ya haifar mata shi da farko ,"    Shashashar banza yanzu ke yaks akan soyayya kike wannan uban kukan ? Kamar wacce aka cewa uwar ta ta mace ? To wai ma tsaya yaushe kika fara soyayya ban sani ba ? Duk kuwa da kashedin da nake yi miki ? Koh daga tafiyar da nayi ta sati biyun ce har kananan ƴan iskan nan da nake raba ki da su suka samu damar hure miki kunne ,ah lalle fa ga ki kuwa kin sauya kin yi lumui lumui kin cika kin yi clean , hala saurayin naki mai ɗan gwaɓi-gwaɓi ne naga ya wanke min ke , ah toh ai babu laifi tun da mai maiƙo ne ,"       shi ya baki wannan kuɗaɗen kenan ? ," ta furta hakan tana mai bin kuɗaɗen da kallo , " idanun ta suka sauƙa kan ɗan wani hoton fasfo wanda ga alama daga tsakanin kuɗin ya fito , ta kai hannu gami da ɗaukar hoton ,       Hoton sa ne sanye da kakin sa na soji daga kirjin sa zuwa fuskar sa ," kallon hoton tayi da kyau tabbas ta san shi abokin saurayin ta nuhu ne ,'bata manta ba nuhu ya bata ɗan takaitatcen tarihin sa a wani yammaci da taje bariki wurin nuhu ta tarad da youssouf ɗin , bayan tafiyar sa take tambayar nuhu  yaya ta ga launin uniform ɗin su ya banbanta ? Nan ya shaida mata youssouf sojin niger ne , ya ɗora da bata labarin sa kar ki gan shi haka anan fitattace ne a ƙasar su ɗan sarki ne , yarima ne mai jiran gadon birnin maraɗi ,babbar masarauta ce a niger ,"      Yaks wanene wannan ?? Ko shine masoyin naki ? Da sauri yakaka ta ɗago kan ta domin ta ga wanda samy baby take kira da masoyin ta ,     Idon ta ya sauka akan ƙaramin hoton biyamuradi , da sauri ta kaiwa hoton chafka !      Shine wallahi shine , ina son shi dan Allah anty idan kin san shi , ki kai ni wurin sa ,"    Cikin mamaki samy take yi mata kallon kan ki ɗaya ?    Ke yaks wannan ne saurayin ki ? Kar ki min ƙarya , gaya min ta yaya ya zama saurayin ki ?     Yakaka bata boye mata kome ba daga ranar haɗuwar su ta farko da youssouf zuwa yau ,"        Jinjina kai samy bby tayi bayan ta gama jin bayanin yakaka da ta tabbatar ba ƙarya bane ,! Domin ta san goge yaks a ɗan ƙaramin lokaci ta zama fes yadda ta gan ta sai mai kuɗi , Idan kuwa hakane babu shakka tayi farincikin ƙulluwar alaƙar sa da yakaka , daman irin namijin da take mata hange kenan wanda zasu tatsi arziki daga jikin sa  !tab , ai batun yace ya rabu da yakaka ma zancen iska ne , wasa tsakanin sa da yakaka yanzu aka fara , zata yi duk yadda zata yi taga mu'amalar sa da yaks ta ɗore , har sai ya gama wanke yaks ya zamar da ita mace mai aji yadda baza ta yi wahala ba wurin samun irin sa ko ma wanda ya fi shi koh da shi ya zo ya bar ta , ! Ai da ruwan ciki akan jaa na rijiya ,' idan yaks bata wanku ba ina zata samo masu attajirai irin wanda take buri???       Share hawayen ki yaks idan wannan ne na san shi abokin saurayi na ne , duk inda yake sai na nemo miki shi , kin ji ? Bai isa ba ya wurgar da ke bayan ya morewa ƙuruciyar ki , dole ya zo ya ƙarasa aikin da ya fara ," Cikin murna yakaka ta fara share hawayen ta , tana jin damuwar zuciyar ta fiye da rabi ta kau , jin cewar samy baby ta san bature kam silum har tayi mata alkawarin nemo mata shi ,"    A saboda murna tana tattara ƙudaɗen da ya bata , ta miƙawa samy baby ,"      Ga shi anty na baki gaba ɗaya ! Da murmushi samy baby take kallon ta , sa hannu tayi ta karɓi kudin ta ƙirga su dubu arba'in da shida ne ," Naira dubu goma ta zara a ciki ta miƙawa yakaka sauran ,"     Ki riƙe sauran kuɗin a hannun ki zasu miki amfani kafin na gama shirya yadda zan yi na dawo miki da yarima , wannan wanda na ware kuma , kafin ya dawo ku cigaba da harka dole zamu je asibiti a baki kariya daga samun ciki , kin sai dai ba'a cin moriyar bariki idan ana yi ana kwasar ciki .     Da sauri yakaka ta amince da shawarwarin samy baby , nan dai suka ƴar taɓa hira samy baby tana sake kitsawa yaks shawarwarin yadda zata riƙe yarima idan ya dawo ,     Falmata tayi jugum a zaune tana tunani, wata irin kewa take ji , tun da yakaka ta samu aikin da take yi yanzu  ya zama bata da lokacin ta irin da , duk da cewa dai idan tana gidan tana bata kulawar sosai da sosai bugu da ƙari ga cimaka masu kyau da daɗi da suke samu a yanzu , ga wasu ranakun ma biya yakakar take yi ayi aikin wanke-wanken falmata , amma duk hakan sun gaza samar da farin ciki mai daɗi ga falmata ,yanayin su na farko da ko yaushe suna tare yafi mata kome daɗi , bata da kowa bayan yakaka ,! Ga shi wannan aikin da yakaka ta samu yana neman raba tsakanin su , domin a yanzu duk zata iya ƙirga ƴan awowin da suke yi tare da juna a wuni , daɗewar da yakaka tayi yau bata dawo daga wurin aikin ba ya dagula ran ta , tana aunawa da zafin ranar da yake buso ta tare da kusancin ranar da take ji a jikin ta ta tabbatar yanzu rana ta fara kaiwa tsaka ! Ina yakaka take tun jiya da yamma har yanzu bata dawo ba ? A hankali wasu siraran ƙwallah suka silalo zuwa kan ƙuncin ta ,!   Bata ji zuwan ta wurin ba , sai saukar hannun ta taji ta share mata ƙwallar ,! Cikin ƙaruwar rashin kuzari akan wanda tafiyar youssouf ta jawo mata ganin hawayen falmata ya sake taɓa ranta , " ta zauna daga gefen falmatan        Falmata na ! Meyasa ki kuka ? Wani abun aka miki ? Ko baki da lafiya ne ? Yakaka yanzu kin rage kula da ni , bayan kuma kin san ke kaɗai nake da ita wacce take bani kulawa , " yakaka dan Allah nima ki yadda na dunga bin ki sabon wurin aikin ki nafi son koyaushe muna tare duk inda muke , bamu da kowa sai junan mu ,"    Kiyi hakuri falmata nima daga yau ɗin bazan sake zuwa ba !         Meyasa baza ki je ba ? Ni fa ba nace ki daina zuwa bane , toh shikenan na hakura ki dunga zuwa kin ji ,?    An dakatar da aikin ne wanda nake yiwa aikin ya tafi ,! Sai idan ya sake dawowa watarana ,"    Cikin rashin jin daɗi falmata ta karya wuya ,       Kai amma banji daɗi ba yakaka mutumin yana da kirki , tun da kika fara aiki a gidan su muke samun jin daɗi .,'     Uhum ,!      Cewar yakaka tana mai miƙewa Bari na sauya kaya na nazo kan aiki ,! Chan ƙasan kayan ta a kusa da kuɗaɗen niger da agogon sa da ya bata a haɗuwar su ta farko ta ajiye hoton tare da kuɗin hannun ta , a ran ta tana jin hoton sa da agogon sa zasu zame mata abun ɗebe kewar sa kafin samy baby ta dawo mata da shi kamar yadda ta alƙawarta mata ! Washagarin ranar samy baby ta samu yakaka , suka je asibiti ƙarƙashin jagorar wani nurse abokin hulɗar samy baby , tare da taimakon sa aka yiwa yakaka allurar hana ɗaukar ciki , ba tare da an tsawaita binciken ina mijin ta ba ?, tare da tunasar da ita dawowa sake yin wata allurar duk bayan watanni uku !   Yakaka bata ji ko ɗar ba sai ma farin ciki da take ji chan ƙasan ran ta a domin kan hanyar su ta zuwa asibitin samy baby ke sanar da ita a yau ɗin nan zata garzaya barracks wurin nuhu inda zata samu cikakken bayanin inda youssof yayi bigire idan ma ta kama har inda yake sai ta kai yakaka ! har ɗakin kwanan sa ,! Ah to meye bariki ce fah !  A haka suka tsaya . Sai dai tun dawowar su daga asibitin yakaka ta gaza tsinana wani abun kirki , saboda wani irin murɗawa da marar ta take ta sake , ga duhu-duhu da take gani a idanun ta ,! Gaba ɗaya jin ta take marar lafiya ,' dan haka ta zari nera dubu biyu cikin kuɗin ta ta bawa madam saly tace bata jin daɗi zata je ta kwanta ,"     Jiki na rawa madam saly ta warce dubu biyu tace ta je ta kwanta za'a yi aikin ta .!    Kafin azahar yakaka ta jigata saboda tsabar ciwon ciki da kwankwaso ta takure a guri ɗaya sai murƙususu take  , ! Larki ce ta shigo ɗakin ta tadda ta a galabaice ," nan take tambayar ta meye yake damun ta tace ciki da baya ,'         Cewa tayi ta bada kuɗi a anso mata magani ƙila ciwon cikin al'ada ne daman yana irin haka ,!    Da rarrafe ta jawo jakar kayan ta ta fiddo da duk kayayyakin ta zaƙulo damin kuɗin ta , ta fidda naira dubu ɗaya ta bayar a anso mata magani ,! Ta koma ta kwanta gami da runtse idanun ta !    Da kan ta larki ta je ta amso mata magungunan saboda ta hango moriya , ta kuma ƙulla abunda ta ƙudurta cikin ran ta ," Ta tsaya a wani ɗan shago ta sayo mata ruwan leda guda biyu ! Lamoo ! ta samu yakaka tana sauraran gangar jikin ta ,"    Ta taimaka mata ta zauna tare da ɓalla mata maganin ta miƙa mata ruwan ta kora , ta koma ta kwanta cikin wani sabon yanayin rashin kuzari da take jin kan ta a ciki . Larki ta ɗan saci kallon jakar kayan yakaka , ta gan ta a buɗe yadda ta bar ta bayan ta miƙo mata kuɗin ! Yaks bari na tattara miki kayan naki , ai ba'a bar kayan haka ba ko dan gudun masu dogayen hannu kin san ɗakin namu babu tsaro ,' , Idon ta a rufe ta ɗan gƴaɗa kan ta ,! Da azama larki tayi wa jakar kayan rumfa ta bada baya ga yakaka wacce idanun ta ke rufe ,"      Kayan ta fara mayarwa bayan ta wawuso kusan rabin kuɗin da yake cikin jakar ta chusa a lalitar ta ,"   A ranta tana cewa ! To meye ? Ta san yarinyar sabuwar hannun ce dan haka tana kan ganiyar ta , dan ƴan waɗannan kudaɗen ba kome bane a wurin ta , ƙila ma bata san yawan su ba daga ta shafa ta ji sun ragu , fita zata sake yi wurin masu bata ta sake samo wasu , Dan haka gwara itama ta samu ta wawushe nata , ko ta samu ta kashe wasu matsalolin ta,  ta kuma  farfaɗo da jarin ta na goro da taba ! Da wannan zancen zucin ta kammala maida kayan tsaf ! Ta juyo da kallon ta kan yakaka domin ta sanar da ita ," Sai taga bacci ma take da alama ta samu lafawar ciwon ! Tura jakar tayi inda suke ajiye ta cikin ranta tana ayyana ta samu hujjar da zata kare kan ta ko da ace yaks tayi cigiyar kuɗin ta ," cewa zata yi bata san wanda ya ɗauka ba ita dai ta gyara mata kayan ta fita ,! Sai bayan la'asar yakaka ta farka ! Daga baccin da yake cike da mafarkin biyamuradi da soyayyar sa da ta maƙale mata a zuci !  Watsa ruwa tayi tayo alwala , ta haɗa sallolin azahar da la'asar tayi su , Tsumu tayi a zaune kan ɗankwalin ta da ta shimfiɗa tayi sallah bisa ,  ta rasa abun da ke mata daɗi . Babu laifi taji sauƙin ciwon cikin sai dai sakayau take jin ta ga wani irin ƙuncin zuciya da take ji uwa uba kewa tare da ƙaunar youssouf da take tokarin ta a duk bayan daƙiƙa guda wanda ko da wannan aka bar ta kawai ya isheta cuta ! Ji take kamar ta shekara da barin ganin sa haka ta shafe tsawon daren jiya tana jin kewar sa ta gaza bacci sai juye-juye , Cikin sati biyu kachal da suka yi tare da juna ya mata mugun sabo da soyayyar sa mai tsayawa a zuci , duk da cewa soyayyar ba da baki yake ambato mata ba , a aikace yake idar mata , shiyasa gaba ɗaya take jin kewar sa hatta a fatar jikin ta da kowanne saƙo da lungu na jikin ta ,! Har gizo hannuwan sa ke yi mata a sassan jikin ta ,' ko yaya ta rufe idanun ta fuskar sa take gani tana mata gizo , shi ba ma'abocin murmushi agare ta bane , amma yanayin kamammiyar fuskar sa yana bala'in burge ta , babu shakka a rayuwar ta bata taɓa ganin mutum ɗan gayu mai kyau irin sa ba ! Yunwa take ji domin rabon ta da abinci tun karin safe ," sai dai kallo ɗaya tayi wa robar abincin ta da take ajiye a gefe wanda take da tabbacin wake da shinkafa ne a ciki ta ɗauke kai , ' abinci daddaɗa bakin ta yake kwaɗayi !    Jakar ta ta jawo domin ta ɗauki kuɗi taje sayan abinci wurin su kolo Kallo ɗaya tayi wa kuɗin tasan an taɓa su , da azama ta fiddo su ta ƙirga ta ga dubu goma sha bakwai ne a maimakon dubu talatin da huɗu,! Jujjuya kuɗin take idanun ta sun ciko da ƙwalla , tana da buri akan kuɗin , so tayi ta kai falmata babban asibitin ido a duba ta domin kwana biyu idon yana ɗan matsa mata da ƙaiƙayi kuma suna yin jaa , cikin ran ta bata fidda rai watarana falmata zata gani da idanun ta ba , ji take watarana falmata zata ga hasken da yake wadace cikin sarari duniya , watarana zata ga fuskokin jama'a , zata ga fuskar ta kamar yadda kullum ita take ganin ta ! , sannan idan kuɗin ya rage ta jaa jari ta fara soya doya da kwai da yammaci zuwa dare , kafin dawowar bature kam silum domin ta ɗanɗani daɗin kuɗi da ƴancin da suke samarwa ga mai su ! Baza ta iya sake zama irin na tsananin talauci tare da walaƙancin da ake musu sanadin babu ba !  idan ya so sa dunga raba ribar tare da madam saly , ta san baza ta ƙi ba !, Amma shine wani azzalumin marar imani ya kwashe mata kuɗin ?! Tunanin larki ya faɗo mata arai , ko ita ce ta ɗauka ? Amma larki anya zata ɗauki kuɗin ta ? Koma waye na bar shi da Allah ! Ban yafe ba .    Ta furta hakan a sarari tana share guntuwar ƙwallar ta , ta zari naira dubu ɗaya , a ranta tana tunanin chanjin ta da ya rage hannun larki , bata ,  bata ba ko maganin na dubu ɗaya ɗin ne ? Ita dai baza ta tambaye ta ba idan ma ta cuce ta dan kan ta ! ¿ Kai tsaye ta wuce rumfar su kolo , ta miƙa kuɗin tace a bata tuwon shinkafa da miyar yakuwa , malmala biyu da nama guda huɗu , Kolo ta miƙo mata tuwon a naɗe cikin leda tare da miyar a wani ɗan kwanon roba bayan ta gargaɗe ta akan ta dawo musu da kwanon miyar  ! Kai tsaye wurin wanke wanken falmata ta wuce , ta tadda ta wanke-wanken sun taru tana ta faman wankewa ana ƙaro wasu , saboda yamma tayi lokacin ciniki ne kuma an kusa gama sayarwa ! Alamun gajiya ya bayyana a gare ta ,ga gumi da ta haɗa fiye da rabin zanen ta a jiƙe yake da ruwan wanke-wanken! Ajiye abincin hannun ta tayi a gefe ! Cikin ruwan kumfan ta sa hannu gami da zare soson daga hannun falmatan ,       Kawo nayi sauri na gama , kin ci abinci falmata ?? Da murmushi a fuskar ta ta cire hannun ta a ruwan gami da goge hannun ta a jikin rigar ta ,'     Ban ci ba yakaka , kin ga aikin yayi yawa wanke wanken ina yi ana ƙaro wasu ,"     Amma yanzu zan samu nayi sallah sai na ci ,"     Da ido kawai yakaka ta bita lokacin da ta matsa jikin fanfo ta fara alwala ,"    Ɗan kwalin ta ta shinfiɗa tayi sallar azahar da la'asar akai , bayan ta idar , tace yakaka ta bata abincin ta ,da ta rufe shi da faranti a gefe ,"    sai lokacin yakaka ta lura da yasashiyar robar abincin falmata da take

Chapter 24 of 111