, saboda sun san muddin ya tafi Maradi sai ya saki auren Falmata ba zai yiwu ya bijirewa iyayensa ba bayan tarin laifin da yayi masu muni .
Basu bi ta kan su Falmata ba bare su yi musu Sallama suka fita a gidan cikin motar Tafeeda , suka bar Youssouf shi ɗaya tal a ƙofar gidan ,
Matsawa gefe yayi ya samu waje ya tsugunna , kewar ɗiyar sa tare da ciwon rashin ta suna taso masa ,
kwanakin da suka biyo bayan mutuwar ta basu zo masa da sauƘi ba sanin da yayi bata raye a duniya yana murƙushe duk wani kuzarinsa ,
baya iya bacci daga ya rufe ido fuskarta ke yi masa gizo muryarta na amsa kuwwa a kunnuwansa ,
baya son doguwar magana da zata katange shi daga yin addu'o'i , ko abinci sai yunwa ta kai masa maƙura yake iya tsakura ya ci .
Ƙaunar Mama dabance a wajen sa ko cikin abubuwan da yafi so a duniya tana a sahun farko , yasan a cikin 'ya'ya ba zai samu ya ita ba a samun zallar so da ƙauna daga wajen sa tayi zarra , sai ga shi tafiya bata miƙa ba , mutuwa ta shafe tsakanin su , ta ɗauke masa sanyin idaniyar sa .
'yar da silar ta ya haɗu da Fatima zahra har tayi sanadin ƙulluwar aure a tsakanin su ta wanzu tsawon lokaci tana ƙulla kusanci a tsakanin su , har sai da ta sa bai farga ba ya faɗa tsundum cikin ƙaunar innar ta ,
Tunanin Falmata ya zo masa , a tun ranar mutuwar Mama rabon da ya sanyata a ido ko ya ji muryar ta , ya san tana cikin halin ɗimuwa kwatankwacin wanda yake ciki tana kuma buƙatar lallashinsa ,
Sai dai ba shi da wani sauran dauriyar sake fuskantar wani tashin hankalin da zai iya tasowa daga gareta bayan sanin da tayi cewa shi da Yakaka sun rufeta akan alaƙarsu da haihuwar Mama , bashi da tabbaci kan yadda ta ɗau lamarin , Dan haka ya zaɓi ya bata iska ,
Kafin zuciyar sa ta gama yanke shawara kan hukuncin da yake son zartaswa a gobe .
***
Yakaka da Falmata sun yi kwanaki biyun cike da kewa da jin ciwo na rashin Mama ,
Koyaushe su na ƙule a ɗaki , basa fitowa falo wajen da su Ubbo suke bare su ga juna , Hajja ita ke kai kawon kula da lamuran gidan, ko abinci kai musu take har ɗaki , duk kuwa da cewa basa yi masa wani cin kirki ,
Wani irin zaman shiru suke yi marar armashi da tunda suke su biyu irin shirun mai kama da na tsakanin baƙi juna bai taɓa gifta tsakanin su ba , kowacce tana jinyar ruhinta
Yau bayan sun idar da Sallar Azahar, suna bisa sallayun su , Falmata ta dubi sashin da Yakaka take , ta ƙira sunanta a hankali ,
" Yakaka ,
Yakaka ta ɗago kan ta ,daga karatun da take yi , ta amsa ƙiran da tayi mata tare da tasowa ta dawo kusa da ita ta zauna ta riƙo hannun ta da irin kulawar da ta saba bata tun tasowar su ,
Falmata ta ƙure kallonta ga Fuskar Yakaka da take iya hango haskenta , tace
"Yakaka , ki faɗa min , ki bani labarin tsakanin ku ,
Tayi shiru kaɗan ,
"ki bani labarin na gaskiya tsakanin ku da Baban Mama , kuma ki bani labarin rayuwar da kika ki bayan haihuwar Mama Alhalin bakya tare da mu ? Ki bani labarin gaskiya Yakaka .
Shiru Yakaka tayi cike da zullumi sai dai ta san abune da tasan da faruwar sa ,tun gabannin ta tambaye ta dan haka ya zama dole ta sanar da ita dukkanin wata gaskiya da ta nemi da ta sani ,
Muryar ta babu kuzari ta fara bata labarin tun daga Rana ta farkon haɗuwar su da Youssouf , har zuwa ranar rabuwar su ta ƙarshe , ta ɗora da cigaba da sanar da ita irin gadar zaren da Samy Baby ta haɗa mata tun kafin zuwan ranar haihuwar Mama da a ƙarshe tayi nasara ƙarƙashin jagorancinta da mummunar huɗubar ta tayi tasirin rabata da rayuwarsu ita da Mama 'yan mintoci kaɗan bayan haihuwar ta ,
dakatawa tayi tana jin tashin hankalin yadda Falmata ta zare hannunwanta dake cikin nata , ta ɗago kai tana kai kallon ta ga fuskar ta ganin yadda hawaye suke zuba daga gurbin idanun Falmata ya ruɗa ta ,
Sai dai bata da wani zaɓi illa cigaba da sanar da ita gaskiyar kome kamar yadda ta alƙawarta , bata tsahirta ba ssi da ta gama tas da bata labarin rayuwarta a garin Abuja gidan samy baby , taimakon da Malama Maryam da ƴar ta Lubna suka yi a rayuwarta , har zuwa komawarta gida Maiduguri wajen Prof .
Ta ɗago kanta tana nazarin Fuskar Falmata wacce tayi ƙasa da idanunta ya zuwa yanzu ta daina hawaye , riƙe hannunta ta sake yi muryarta na rawa ta cigaba da cewa
" Falmata na san ni mai laifi ce a wajen ki , amma dan Allah kiyi haƙuri ki yafe min , nayi kome ne gurin ƙoƙarin na baku rayuwa mai kyau bansan cewa ace na kama hanya ne na rusa mana rayuwa ba , ki yafe min ki zo mu koma Nigeria wajen Baba prof shine kaɗai mutumin da ba zai kore mu ba , ki rabu da Rayuwa da Youssouf kamar yadda Mama ta bar mu , shi ɗin ba kowa bane da ya wuce Maƙaryaci Mayaudari da ......
Miƙewar da Falmata tayi ita ta hana Yakaka ƙarasa zancenta , da kallo ta bi ta lokacin da ta nufi ƙofar banɗaki ta tura ta shiga ta rufo ƙofar ba tare da ta waiga gareta ba , zama tayi cikin wani irin yanayi mai cike da rashin madafa , nadama na sake lulluɓar ta , ko Falmata bata buɗe baki tace mata kome ba ta fahimci tana fushi da ita , fushi kuwa mai tsanani , da ya sa taji tsoron sake yin wani yunƙuri domin tana gudun faruwar wani abu marar daɗi a tsakanin su ,
Fiye da minti talatin ta kwashe a zaune tana jiran fitowar Falmata daga banɗakin da tunda ta shiga bata jiyo motsinta ba , har ta fara tsorata tana tunanin tashi ta ƙira ta , sai ta ga ta murɗo ƙofar ta fito , daga fuskarta har tufafin jikinta a jiƙe suke , sai tayi kasaƙe tana bin ta da kallon tsoro , ganin yadda idanunta suka kumbura alamun kuka tayi mai tarin yawa ,
Kayan jikinta ta sauya ta zo ta janye sallayarta da take gaban Yakaka ta matsa gefe guda ta fara sallah ,
Gaɓɓan jikinta baki ɗaya sun daɗa sanyi Shirun Falmata kuma ya sa ta ɗeɓe tsammani , cikin zuciyarta sai ta fara tunanin mafita ,
Ta shiga bijiro mata da kome da ya wakana daki-daki tsakanin da Youssouf wanda tuni ta fahimci kason nata laifin yana neman zarta na Youssouf tun a farkon fari , ai ita ta fara bada kanta cikin salama , sannan ta cigaba da zama rakuma da akala wajen biye masa aikata zunubi , mafi girman laifin da ta aikata shine gudu da tayi ta ƙyale Mama da Falmata ,
wanda ta nan Youssouf ai ya fita amfanarwa ga Rayuwar Mama da ya haɗa su da ita da Falmata ya tallafa har ma ya zamto sanadin samun lafiyar idanun ta wanda tun akan hanyar su ta zuwa Niger Hajja ta sanar da ita samun lafiyar idanun Falmata , ranta kuma ya cika da farin-cikin da ta ƙi nuna shi a fili saboda kada ta nuna yabawa ga Youssouf bayan tarin laifin da take tuhumar sa da shi da kuma ƙudirin da take tafe da shi na son raba zaman su ,
Sai dai a yanzu da irin yanayin da Falmata ta nuna bata hango alamun zata samun haɗin kanta cikin sauƙi ba , ita kuwa ai bata da sauran ƙarfin zuciya , mutuwar Mama ta kwace mata duk wani karsashi nata ,
Jin an ƙira sallah ya sa ta miƙewa ta ɗaura Alwala ita ma ta tada sallar la'asar ,
Bayan sun idar gani tayi Falmata ta miƙe ta hau gadonta ta kwanta tare da jaan bargo har kai ta rufu , duk kuwa da cewa garin babu sanyi ,
Jugum tayi tana hangenta , kafin ta ce Falmata , garin ai babu sanyi meyasa kika rufu haka ?
Biris tayi da ita bata amsa ba , jikinta sai ya sake yin sanyin sanin da tayi cewa Falmatan tana jin ta sarai ƙin tankawa tayi ,
Sai ta miƙe ta naɗe sallayar , takunta ba ƙarfi ta fita ta ja mata ƙofar ɗakin bata yi taku uku ba ta ji ƙarar sanyawa ƙofar makulli da Falmata tayi ,
Sai ta waigo tana kallon ƙofar , tayi murmushi mai bayyana ciwon da zuciya ke yi , hawaye na taruwa a gurbin idanunta ƙwarai abunda ta fuskanta daga Falmata a yau ya taɓa ran ta , ɗakin Hajja ta koma bata sake bin ɗakin Falmata ba .
Daren ranar babu wanda ya ci abincin dare a tsakanin su Ukun Youssouf , Yakaka ,da kuma Falmata haka kowannen su ya kwana yana saƙa abunda yake ganin zai fissheshi ,
Ƙarfe huɗu da rabi da Hajja ta farka ta tarar Yakaka ta haɗa kayanta kaf , cikin ƴar jakar da ta zo da shi da tana zaune shiru ta jingina kanta da jikin bango ,
Tausayinta ya kama Hajja , bayan ta ɗaura Alwala ta fito sai ta zauna a gefenta ,
"Yakaka uwar Mama
Ta ƙira sunanta , bata amsa ba amma ta maida hankalinta gareta ,
" Ya naga kin ɗauko jakar kaya haka ?ko..
" Tafiya zan yi Hajja , yau zan koma Nigeria , daman domin na gansu na zo kuma ai na gansu , na ga mutuwar Mama a idanuna , babu sauran zama da zan sake yi zan tafi yau .
Ta ƙarasa zancen hawaye masu ɗumin gaske suna sauƙa daga idanunta
Kamo hannun ta Hajja tayi , muryar ta a tausashe tace
" kiyi haƙuri Yakaka dukkanin abunda kika ga ya faru ga Rayuwar Bawa tun gabannin a halicce sa yake a rubuce cikin kaddarar rayuwar sa , kar ki bari shaidan ya raba tsakanin zumuncin ku ke da ƴar uwar ki , kan abunda ya gabata ku duka uku kaddarar rayuwar ku ce ta zo a haka , ke kece Babba ki riƙe zumuncin ku ƙam kar ki bari kowanne mahaluƙi ya shiga tsakanin ku , ku biyu ne rak a duniya ko kuwa kuna da wanda ya wuce junan ku ne ??
Girgiza kai Yakaka tayi alamun a ah , sai kuma tace " Hajja Amma Falmata ta samu wanda ya fini tu.....
" kul kar ki bari zuciyarki ta miki mummunar saƙar da zata wargaza muku zumuncin ku , kiyi haƙuri ki maida kome ba kome ba , kiyi haƙuri da jarabawar Ubangiji Allah zai miki tukuici da mafificin abunda duk kika rasa kin ji ko ?
" to
Ta amsa tana share hawayenta , Hajja ta cigaba da cewa , "yadda kuka haɗu kuna murnar ganin juna kar ku rabu kuna zargin juna ku rabu da farin-cikin da zai ƙara danƙon zumuncin ku kin ji ko ?
" naji nagode Hajja ,
Shiru suka yi suna saurara lokacin da suka ji an taɓa ƙofar falon , sai dai basu kawo kome a rai ba ga zaton dukkanin su Falmata ce ta dawo daga turakar Mijinta ,
Hajja ta ɗora da cigaba da yiwa Yakaka nasiha tare da gwada mata girman zumunci. Da ya sa ta jin sabuwar ƙaunar 'yar uwarta na game mata jini ,
Lokacin da gari yayi shaa , sai ta fito falo da jakar kayanta tana jiran fitowar Falmata domin suyi sallama ta kuma sake neman yafiyarta , 'yan kuɗaɗenta kimsnin dubu goma sha uku a ƙulle a marar ta , sai ta ware dubu uku da ɗari hudu zata bawa Falmata kyautar su ita kuma ta san dubu goma zai sada ta da birnin Maiduguri har ƙwaryar gidan Prof .
Zaman fiye da mintoci goma ta yi lokacin da ta ji an shigo Falon a hankali ta kai ganinta kan sa yana shirye tsaf cikin kakinsa na soji , sai ta tuno da ganin da tayi masa a baya can ,
Da sauri ta ɗauke kanta ta mayar da ganinta ƙofar ɗakin Falmata ,
Shima a ɗarare ya ƙaraso falon fuskarsa babu walwala , a kusan tare suka furta kalmomin
"ina kwana ?
Shi ya riga ta amsawa da "lafiya ,
Sai duk suka yi shiru , shi bakinsa ɗauke yake da jawabi duk da cewa a yau ya hango sassauci daga gareta a karon farko ,
Ƙarasowar Hajja wajen ya sa shi zama akan kujerar da take kusa da shi , gaisawa suka yi tana sake yi musu ta'aziya su duka biyun , har ta miƙe sai yace
"Hajja ina Fatima ?
Hajja tace tana ciki Babban soja , a ƙirata ne ?
"eh Hajja a ƙirata ,
Hajja ta nufi ɗakin Falmata ,
Haka kawai Yakaka ta ji zuciyarta ta tsinke , a karo na farko ta ji tsoron kar Youssouf ya furta cewa ya saki Falmata da tun-tuni ta fahimci ta faɗawa son shi , tausayi take ji , ita ta san yadda raɗaɗin so yake , bata fatan Falmata ta ɗan-ɗana zogin rasa masoyi , a yanzu zata so Falmata ta tsira da masoyinta , abunda ke cikinta kuma ya rayu kusa da mahaifinsa ƙarƙashin gatan uwa da uba a lokaci guda ,
Dan haka ta yunƙuro da zummar yin magana ta shaida janyewar ƙudirinta akan sa ,
fitowar Hajja ya katse ta , inda take sanar da su Falmata bata ɗakin ,
"tana ina Hajja ?
Youssouf ya tambaya da ɗan shakku a muryar sa ,
"ban sani ba Babban soja kuma bata can sashin naka ?
Ya miƙe tsaye lokacin da yake cewa
"bata can ai Fatima batta je ga sashi na ba ,
su dukkanin su sai suka yi tsaye cikin ɗarsuwar sabon tashin hankali a rayukan su
Kamar haɗin baki sai suka bazama neman ta , lungu da saƙo na gidan , Youssouf da Yakaka suna haɗawa da ƙwalla ƙiran sunanta , amma ko alamu babu kurwar ta a gidan , dawowa suka yi suka haɗu a falon zuwa lokacin Yakaka kuka take yi , shi kuwa Youssouf idanunsa ne suka kaɗa jawur , da wani irin tasowar mummunan ɓacin rai lokacin da tunanin sa ya gama hasaso masa abunda ke faruwa ya dubi Yakaka da wani irin sauti yace
" Ina kika kai ta ? Ina kika ɓoye min Matata ? Kiyi gaugawar sanar da ni kafin ki riski fushina Yakaka ..
Yakaka ta zaro ido da maɗaukakin mamaki tana kallon sa ,
"ita Youssouf yake nufin ta sace Falmata ƙanwarta ? Wanne irin mummunar kalma ne wannan yake jifatan ta da su ??
Saɓon ɓacin rai ya bijiro mata .
Assalamu Alaikum masu karatu dafatan kuna lafiya ?
Wannan shafin kachokam ɗinsa sadauƙarwa ne ga duk wasu iyayen masu ɗauke da cutar Amosanin jini ,( Sickle Cell Disease)
Ku sani ya ƴan uwa Allah ya ɗora mana ne domin ya san zamu iya , wataƙila kuma domin hakan ya zamto hanyar samun Rahamar Ubangiji a gare mu mu iyayen da kuma su da suke ɗauke da cutar ( muna fatan haka )
Ku sani cewa cuta irin wannan mai wahalarwa baiwa ce da ba kowa Allah ke ɗorawa ba , dan haka muyi ƙoƙari wajen basu kulawa tare da haƙuri domin cinye jarabawar da Allah ya yi muna ta dalilinsu .
Kada mu danƙwafar da su , kada kuma mu banbanta su da sauran ƴan uwansu masu lafiya , ƙarfafawar mu tamkar ƙara musu lafiya da walwala take yi a gare su, saɓanin haka zai iya sawa suyi rauni su ji tamkar su basu da amfani a lokaci guda su ji sun gaji da duniya .
Cuta bata nuni izuwa ga mutuwa kamar yadda lafiya bata nufin tsawitar rayuwa ( nisan Kwana ) fatan mu Allah shi iyar muna , ya yi mana maganin abunda ya gagare mu , ya wadace mu da lafiya mai amfani .
Ina miƙa ta'aziyya ga dukkanin iyaye ,kakanni 'ƴan uwa na waɗanda suka rasa rayukan nasu ta sanadin ciwon Amosanin jini Sickle Cell Disease .
Jinjinar kuma ta tafi gare ku gawurtattun mayakan da Allah ya ratayawa cuta mai wahalarwa, Da ku nake ( sickle cell Warriors ) ku din ai JARUMAI ne da suka banbanta da saura , ku cigaba da nuna jarumta watarana akwai waraka zata zo inshaAllah .
Nagode .
[12/10/2019, 2:44 PM] +234 706 503 6187: MAFARI
( Hargitsin Rayuwa)
Umm'muaz
44
Cikin motar ƙirar Golf 2 Wagon da take shilla gudu akan titin da zai sadu da jahar Tahoua .
Falmata ce a zaune daga kujerar da take daura da Direban da bakinsa yake cike da goro , yana ta bin wakar Sa'adu bori mai taken 'soyayya abun yi ce ,da take tashi ta cikin sifikun motar kamar zai fasa mata dodon kunne , ta kare fiye da rabin fuskarta da ɗankwalin doguwar rigar jikinta da ta sanya hijabi a madadin sa
Ita ɗaya ce ƙwal mace a cikin motar sauran mazauna gidan baya na motar duk maza ne matasa majiya ƙarfi
***
Lokacin da ta samu isa tashar mota na birnin Niamey da misalin ƙarfe biyar da rabi na asubahi , babu yawaitar mutane a tashar da kyar ta samu wani dattijon ɗan kamasho inda ta shida masa Maidugurin Jahar Bornon Nigeria take son zuwa ,
A mamakance dattijon yake kallon ta , kafin yace mata ,
"kai tsaye Borno zaki tai dagga nan yarinya ?ko dai Sokoton Nigeria zaki tai dagga nan , a can kuma ki tai Borno ?
"Maiduguri zan tafi daga nan Baba, dan Allah ka kaini motar da zata tafi can .
ta bashi amsa tana share ƙwallar da taƙi tsayawa a idanunta ,
Da sauri ya tare ta da cewa ,
"a ah yarinya batun ba na kuka bane kin ga itta motar Borno dagga nan ai wahala take batta samuwa haka a sauƙaƙe , sabadda Borno daga nan tahiya ce miƙaƙaƙƙa ya ta mai yada shege , sai kin tai zouwa zender dagga nan ki shiga ta diffa kafin ki tsallaka boda ki shiga yankin Mobar ta jahar Bornon Nigeria , anya yarinya kina mace budurwa ɗanya shakaf kya iya wagga tahiya ta mazaje ?
" zan iya Baba , Allah zan iya , zan tafi ga taimaka min .
Tace , zuciyarta na sake haƙaƙewa kan tafiyar ita ce kaɗai mafita a gareta ,
" to babu laifi , bara shi malam Amadou gayu ya isso domin shi ɗai yake wannan dagon zagon Allah sa dai ƴan tangaran basu riga sun kama kujerun motar ba , dawo dagga nan ki zauna , nan ba da jimawa ba ike isowa ,
A ɗarare ta zauna akan wani ɗan dandamali ba dan ranta ya so ba domin a matse take ƙwarai da ta bar yankin ,
Zaman mintoci goma kawai tayi sai ga motar Ahmadou gayu , wata wankakkiyar golf wagon ce da ta ci uban dilken da ake yiwa tsoffin motocin da ake son tada musu da komaɗa tare da ɓoye musu tsufan su .
Tayi zaton za ta ga wani matashin saurayi jin ana masa inkiya da "gayu , sai ta ga wani dattijon da ya tasamma shekaru sittin amma ya ƙi sarewa daga yin gayu domin kuwa a tsuke yake cikin ƙananun kayan da suka ɗau guga , ya ci zanzaro , kan nan nasa da sanƙo ya cinye rabi rabin kuma gashi ne a tare himili guda da aka yiwa shamfo a taje tsaf-tsaf yana sheƙin Mai .
Da fitowar sa gurin ya ɗau ƙamshin ƙaƙƙarfan turarensa na 999 for male .
Bai jinkirta ba ya fara goge jikin motar da a zahiri babu wani datti sai ƴar ƙura da ba'a rasa ba ,
Ɗan kamashon nan shi yayi sauri ya samar mata wajen zama domin kuwa , kamar yadda yayi zato har an riga an kama kujeru huɗu na bayan motar ,wajen mutum ɗaya tak ya rage ,
Dan haka Falmata bata jaa ba lokacin da aka yanka mata adadin kuɗin da zata biya , ta ƙirga kuɗin daga ciki ƴar karamar jakar hannunta da ita ce tal abunda ta riƙa , ta basu ta shiga gaban motar ta zauna .
Sauran mutane huɗun da yake daman sun riga sun kama kujerar motar suna zuwa shiga suka yi ba ɓata lokaci ..
Ƙarfe shidda cif motar su ta bar cikin tasha ta ɗau hanyar da tafiyar da zata iya kai su kwanaki biyu kafin isar su Yankin jahar Borno Nigeria .
***
Tunda suka kama hanya ta kwantar da kanta jikin gilashin , bayan ta rufe rabin fuskar ta , A zahiri ta ɗora idanun ta ne bisa kan titi da ƙura irin ta juyin yanayin shigowar bazara ke tashi daga kan rairayin hamadan dake gefen titin ,
Sai dai can cikin tunanin ta ruhi da ƙwaƙwalwarta sun zurfafa ne cikin tsinkayen makomar rayuwarta tare da rarrabe fari da baƙi ,
Tun a jiya da ta san haƙiƙanin gaskiyar kome take jin tamkar mafarki ne tayi ba ido biyu ba ,
Tayaya za'a ce Mutane biyu masu girman daraja a rayuwar ta sun yi mata irin wannan mummunan rufa-rufa ?
Ashe Baban Mama da ta ɗau duk wani aminci da yarda ta ba shi , ta riƙe shi a matsayin mafi nagarta cikin mutane ,
shi ɗin mayaudari ne , fasiƙi , yayi zina da yayarta , ya gudu ya bar ta da cikin , tsakanin rayuwa da mutuwa , sannan daga baya ya dawo yayi ƙarya ya aure ta , ? Shiyasa mana yake shiga gigita da ɗimuwa a duk lokacin da tayi yunƙurin sanin irin alaƙar da ta kullu tsakanin sa da Yakaka , ashe Azzalumi ne .
Yakaka ta cutar da ita tun farko da bata taɓa sanar da ita irin alaƙar da ta kulla har ta kai ga samar da Mama ba ,
Ashe son da Yakaka take iƙirarin tana yi mata bai kai nan ba , tunda har ta iya gudu ta bar su ita da Mama jaririya akan ɗa Namiji bata ko tausaya musu ba ,
ta tuno irin yadda fitar Yakaka daga rayuwarta ya jiggata mata rayuwa , ta tuna irin halin ƙunci da ciwon rai da tayi fama da shi , ta tuna da cikin kowanne irin yanayi na farin-ciki ko baƙin-ciki a rayuwarta tana yin su ne tare da tarin kewar Yakaka , bata taɓa sabawa ba da rashin ta , bata taɓa daina kukan mutuwar ta ba kamar yadda cikin duk wasu sallolinta bata tashi ba tare da tayi mata addu'ar samun rahamar Ubangiji ba , da yafiyar sa .
Amma ashe wai duk tsawon lokacin nan Yakaka tana raye cikin ƙoshin lafiya da kwanciyar hankali bata taɓa waiwayar su ba ?
kuma wai da son ranta ta bar cikin rayuwar su ? shin wanne irin so ne maigirma haka Yakaka take yiwa Youssouf ? Babu shakka tana iya tuno kaɗan daga cikin soyayyar da Yakaka take yiwa Bature kam silum ɗin ta ,
Dan haka tun jiya ta riga ta sulluɓe Youssouf daga ran ta , take kuma kankare duk wani ɗiso na ƙaunar sa daga ran ta , tana ƙenƙesawa zuciyarta Youssouf ya haramta a gareta .
Tunanin irin cutar da su biyun suka yi ga ɗiyar su Mama yana nuƙurƙusar ran ta tare da ƙara mata baƙin-ciki a duk bayan ƴan daƙiƙoƙi ,
Cikin ƴar taƙaitatciyar Rayuwar da Mama tayi babu shakka bata yi maraicin uwa ba , ta cikace mata gurbin da Yakaka ta bari ƙarƙashin son zuciyar ta ,
A ganin ta daga Youssouf har Yakaka bata su dace da zama Iyayen Mama ba , mutuwar Mama kuma hutawarta ne daga shan takaicin gori da aibatawan mutanen duniya ,
Ta zaɓi da ta tafi ta barsu tare tunda su biyun babu abunda suka sani sai tsananin son zuciyoyinsu , su zauna tare domin su biyun ai sun dace da juna ,
Ita zata koma Maiduguri , ta roƙi Prof kan
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Chapter 110
Chapter 111
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 79 Chapter of 111