Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
min kishiya da wannan ƙazamar kuchakar Yarinyar ? Kuma ma wai har ka ɓoye min Doctor ka ƙi sanar da ni tun wuri da na yiwa tufka hanci . Kwantar da murya yayi yace " Sofiya wallahi ba ni nace zan aure ta ba Baa da Amnee ne suka haɗa lamarin nan , ki bari zan miki bayani sosai idan mun zauna, yanzu ki bar kukan da kike muje cikin ɗakina ki wanke fuskar ki , kin ga magariba ta gabato bana so na rasa jam'i , Juyawa tayi maimakon ta ɗau hanyar cikin gidan sai ta kama hanyar sashin Prof , a tsorace ya sha gaban ta wannan karon fuskar sa babu alamun wasa yace " Ina za ki ? Ita ma da wata irin faffaɗar murya tace " wajen sa zan je naji dalilin da zai sa ya mun haka , sannan kuma na roƙe shi dan Allah ya warware wannan mummunan ƙullin da yake son yiwa rayuwata , Muryar sa a dake da bayyanuwar ɓacin rai yace " Sofiya ki nutsu ki shiga hankalin ki , iyayena fa ba abun wasan ki bane , naga duk irin haukar da kika yi a gaban Amnee dan na miki uzuri dalilin cewa ke ma an miki kuskure ba hakan ne zai sa ki dunga yin duk abunda kika ga dama ba akan su , ki nutsu nan gaba zan iya ɗaukar mummunan mataki akan ki muddin kika nemi cin zarafin iyayena , Daga haka ya wuce ya bar ta a wajen , wajen famfon dake zubar ruwa ya nufa yana daura alwala , Da saurin da ya wuce ƙima Sofiya ta tasamma ƙofar gidan ta fita tamkar zata kifa , Zuciyar sa babu daɗi ya bita da kallo , wannan tashin hankalin yake gudu daga gareta yasa tun farko ya kasa sanar da ita , sam shi ba mutum bane mai ƙaunar hayaniya . Yana kammala Alwala ya shiga motar sa ya tayar aka buɗe masa ƙofa , yana fita kafin ya dai-daita kan motar a bisa titi ya hango motocin su Doctor Suleiman tare da na wasu abokan sa su huɗu , motoci biyar kenan , a sarari yayi tsaki kafin yace " wannan kuma Uban 'yan didimar sai da ya min gayyar da na ce bana so . Hannu kawai ya ɗaga musu tare da matsa ham , ya bi bayan sofiya wacce ya hango har ta kusa titi . Da kyar ta yadda ta shiga motar ya miƙa ta gidan su , sai dai ko ficewa a layin gidan nasu bai yi ba ita ma ta sake fitowa a cikin motar Momy kori da gudun gaske ta ɗau hanyar gidan gogaggen Malamin ta da ta yadda da shi ɗari cikin ɗari aikin sa na ci , aifa zama bai gan ta ba . Matar mutum bata zama ta wanin sa , washegari da misalin ƙarfe goma na safe taron jama'ar da suka cika suka tumbatsa suka shaida ɗaurin auren Hamza Mustapha Dilmari tare da Amina Muhammad Kalama . Bayan ɗaurin Aure walima ta biyo baya , abokan Doctor Hamza da suka tasamma su ishirin sun sanya shi a tsakiya gami da sauran dangi , bayan fara'a babu abunda yake kamar ba shi bane ya sha ɓacin-rai da jin labarin auren , Shi da kansa bai san takamaimai me yake bashi nishaɗi ba illa yasan wani ɗan tsiron farin-ciki ne daga can saƙon zuciyar sa da ya zata ya mutu tun-tuni yake sabunta kan sa a yau . Ɗan gefe guda Suleiman ya jaa shi bayan ya gama tsokanar sa yadda ransa ke so a ƙarshe yace masa ya kamata Amarya ta fito su gaisa saboda su anjima kaɗan zasu juya . Baya so ko kaɗan Suleiman ya fahimci akwai wani abu marar daɗi a tsakanin sa da ita saboda ko babu kome ita a yanzu wata ɓangare ce ta rayuwar sa ba zai so ya zubda mata da ƙima a wajen wasu nasa ba dan haka yace ," Abokina mu je daga sashi na a ƙira ta ta gaishe ka kai kaɗai amma sauran sa haɗu watarana kawai . " Ayi haka kuwa abokina ? Doctor Suleiman yace da ɗan shakku , hannun sa Doctor Hamza ya jaa tare da cewa "ai anyi ma , suka fara tafiya zuwa sashin sa yana ƙiran Amnee a waya , bayan ta ɗaga yake sanar da ita buƙatar sa na son a turo Yakaka sashin sa zasu gaisa ita da Suleiman . Cike da murnar da tunda aka ɗaura auren lafiya yake mamaye ta , Amnee ta miƙe daga bakin gadon ta da take suke zaune ita da wasu ƴan'uwanta suna tattaunawa ta nufi ɗakin da ta bari a ɗazu Hajje Nadiya tana shirya Amaren a ciki , Tana tura ƙofar idanun ta suka yi farin gani da kyakkyawar farar fuskar ta da yau hasken ta ya ninku har wani sheƙi take , tana ɗaukar idanu iyakar kyau Yakaka tayi sa cikin farar Lafayar da aka naɗa mata mai adon ƙananun flowers baby pink da ash color akan sissilkan yadin da aka mata siririyar doguwar riga da shima launin baby pink , kan ta an naɗa mata ɗaurin ɗankwali simple an soke mata shi a gashin ta . Rungume ta Amnee tayi ta sumbaci goshin ta kafin ta kamo hannuwanta da suka sha ƙunshi irin zanen ƙunshin mutan chadi jazur da su sun yi gwanin sha'awa , da manyan awarwarayen zinaren da Amnee ce ta bata su , suka daɗa fiddo martaba da kyaun hannunwan nata . " da hannu ta yafito Falmata wacce take tsaye daga bakin window da alama akwai abunda yake taɓa ran ta a dai-dai lokacin , taƙi yadda a mata makeup sai yar hoda da man baki masu kyau aka shafa mata a cewar ta idanun ta basu cika lafiya ba bata son makeup , ita ma shirye take cikin wani pink ɗin leshi da aka mata ɗinkin Buba da zane tayi kyau fes da ita an mata ɗaurin ɗankwalin da ya fiddo zagayayyar cikakkiyar fuskar ta da ta sake yin tuɓus-tuɓus tana sheƙi sakamakon gyaran Hajje Nadiya da fatar ta ta karɓa . Haɗa hannuwan su waje ɗaya tayi , tana cewa Falmata ," ki je ki raka Yayar ki sashin Yayan ku Babba zata gaisa da baƙi , idan sun gaisa ki tabbatar kin dawo min da ita hannu na yadda na ɗanka miki ita kin san yau ita tafi lu'ulu'a daraja . Ƴar kyakkyawar dariya Falmata tayi kafin tace " an gama Amnee watau yau ni ce ƴar jagora ba ni za'a jagoran ta ba kai Alhamdulillahi Allah mun gode maka da ka nuna mana wannan ranar, Amnee tana dariya ta roko su har ƙofar sashin ta ko'ina suka gifta ana ga Amarya ga Amarya ana bin ta da kallon sha'awa har da masu yi mata hoto , Falmata ita ta fara yin sallama a ƙofar falon , da aka musu iznin shiga ma sai da ta kai kusan minti guda a ciki kafin Yakaka ta saɓile takalman ta ta sanya ƙafafun ta ciki kan ta a ƙasa ta samu gefe zata zauna daga ƙasa , da sauri Falmata ta riƙo ta dai-dai lokacin da Doctor Suleiman ma yake cewa " Kai kai Amarya ya za ki zauna a ƙasa ? Tashi-tashi ƙanwata yau ai ranar ku ce kamata yayi ma a dunga miki yawo da kujera ta musamman dan zaman ki kin san yau ke da sarauniyar England matsayin ku kai-da-kai yake . A hankali ta ɗago kanta bayan ta zauna akan kujerar da Falmata take kai suna gaisawa da Doctor Hamza jin muryar sa raɗau tayi mata kama da na wanda ta sani , shima Doctor Suleiman yana ƴar dariyar tsokanar ta da yake sauran Kalaman bakin sa suka maƙale masa a maƙogoro ganin fuskar ta ɗauke da kwalliya da sheƙin Amarci bai hana shi ya gane ta ba duk kuwa da cewa ganin sa da fuskar tata sau biyu ne rak , amma ta riga ta zanu a zuciyar sa mafarkin ta a yanayi ya irin haka a gaban sa abune da ya jima yana yi , Sai dai a wannan karon zahiri ita ce a bayyane a gaban sa amma ba a matsayin ta sa ba da kullum yake hari , a matsayin matar aminsa na ƙud da ƙuɗ take , cike da ruɗanin da ya gagara ɓoyewa bayan ta ɗauke ido daga kan sa da sauri , yace " Abokina daman wannan ce Amaryar ta ka ? Daga Yakaka , Youssouf har falmata sai da zuciyoyin su suka sauya bugu da mabanbanta tunaninnika da ya musu dirar mikiya , Ɓangaren Doctor Hamza a take ɓakin-cikin sa ya nemi dawowa sabo abunda yake gudu kenan tun farin farko da kuma ya sashi tsanar ta , cuɗanya da tayi ta yi da mazaje . Da sautin da shima bai ɓoye ɓacin-ran sa ba a daƙile yace " eh ita ce , ki gaishe shi mana ku koma ciki . Muryar Yakaka na maƙyar-ƙyartar da ta ƙarawa Doctor Hamza tabbacin rashin gaskiyar ta ta gaishe da Doctor Suleiman da gumi yake tsattsafowa a goshi , yana share gumin ya amsa da " lafiya lau Aminatu , nayi muku murna kin ji Allah ya sanya Alheri . A ɗan kaikaice Doctor Hamza yake kallon sa lokacin da Yakaka da Falmata wacce jikinta yayi sanyi laƙwas da yanayin da ta gani a tare da su biyun suka fice daga falon . Kafin Doctor Hamza yayi wani yunƙuri Doctor Suleiman da ya miƙe tsaye cikin wani irin yanayin da yake bayyana alhinin da zuciyar sa ke ciki yace " Hamza ka min shigar sauri , why ? Amina da nake baka labari ita ce wannan Abokina ita ka Aura . Da sauri Doctor Hamza shima ya miƙe , kafin yace kome Doctor Suleiman ya sake katse shi cikin yanayin da yafi na ɗazu rauni , ya cigaba da cewa , " Na taya ka murna Abokina babu shakka Allah ya arzuta ka da kamilar Mace mai nagartattun halaye , ina taya ka murna sosai ina kuma yi muku addu'ar samun ɗorewar zaman lafiya babu shakka matar mutum daga gare shi take ... Katse shi Doctor Hamza yayi a mamakance yake cewa ," kana nufin wannan Aminar ita ce Amina , Amina da kake bani labarin ta ? " ƙwarai da gaske ita ce . Shiru su biyun suka yi baƙon yanayin da ya ziyarce su yana samun damar mamayar tunanin su , muryar Doctor hamza ta sake ratso wajen da yake cewa " Abokina Dan Allah ka bani labarin haɗuwar ku da duk wani abunda ka sani game da Amina . Bayan komawar su Yakaka cikin gida gaba ɗaya sai ta rasa sukuni sarai ta gane ko wanene abokin Yaya dakta , shine mutumin da ya dunga bibiyar ta da sunan soyayya tsawon shekaru wanda har Malama Maryam da Lubna sun san shi , sai yau ta tuno rana ta farko da ta fara ganin shi a duniya ranar da suka fara haɗuwa da shi da kan sa Doctor Hamza tare ta fara ganin su , shine wannan abokin nasa da ya ji tausayin su a lokacin da Doctor Hamza yake hora su kan fitsarin da Falmata ta yi masa a office har ma ya basu kuɗi yace su sayi hijabi su suturta jikin su . Sai yau ta gane shi gaba ɗaya , amma yanayin da ta hango a fuskar Doctor hamza kafin barin su falon bayan Suleiman ya nuna ya san ta ya bata tsoro , sanin da tayi daman ita a wajen sa abar tuhuma da zargi ce , tsoronta ya ninku lokacin da tayi hasashen kar Suleiman ya sake dasa zarginta a zuciyar Doctor Hamza . An cigaba da shagalin biki zuwa Yamma aka fara shirye-shiryen tafiya Dinner da dangin Mijin Rahima ne suka shirya saboda su nan Baa baya son ire-iren bidi'o'in baya yarda a kama waje a tafi biki kome za'a yi a harabar faffaɗan gidan ake yi , sai dai fa idan dangin miji ne suka shirya abunsu ko kuwa bayan an miƙa amarya gidan ta ayi ta can . Shiri ake ta yi sosai saboda har Amnee da Khaalty Rahima ma zasu su a karon farko saboda ta roƙi Baa yau ɗaya tal ya bari su tafi tare har da Yakaka da Falmata tunda shi yaƙi yadda a shirya ayi daga Aljihun sa . Albarkacin farin-cikin da yake ji na wannan ranar bai jaa gardama sosai ba yace su je amma a kula a kuma dawo da wuri . Ana gaf da tafiyar bayan isha'i Doctor Hamza ya shigo gidan da tunda ya fita raka abokansa bai dawo ba ya zarce gidan su sofiya wacce tunda aka ɗaura auren take ƙiran sa a waya daga ya ɗaga sai ta fashe da kuka tana ihu tare da cewa sai ta kashe Yakaka , Tun abun na ba shi dariya har ya fara damuwa sosai tausayin ta ya tsirga masa , shi shaida ne akan irin son da take yi masa yana tsoron kar wani abu ya samu ƴar mutane ta dalilin haka dan haka da yayiwa su Suleiman rakiya suka rabu cikin raha da barkwanci sai ya kama hanyar gidan su Sofi Kacha-kacha ya tarar da ita tayi manƙas cikin ƙwayoyin da ta dunga afawa , tun lokacin da labarin ɗaurin auren ya zo ma bayan a jiya sai da ta bi malamai kusan biyar akan lamarin duk kuma suka tabbatar mata kan cewa za'a yi aikin da zai sa a fasa auren a daren kafin gari ya waye , sai dai ga shi babu wanda aikin sa ya ci sai asarar kuɗi da ta tafka . Tun kuma a jiyan ta dunga ƙiran layin Samy baby amma bata samun ta , damuwar ta ta ninku ba adadi . abunda ya mummunan kaɗa masa ƴan hanji bai taɓa sanin Sofin sa na shan kayan maye ba , ashe duk ihun da take masa a waya bata cikin hayyacin ta ? Kwayoyi ta fara sha a sanadin ƙarin auren da yayi ? Ƙwalla ne suka tarar masa a ido yana jin takaicin uwa irin Hajja Kori da baza ta iya tanƙwara ƴar ta ba , tayi ko ta bari , da ya shigo gidan ma bai ganta ba ko tana ina ? oho Haka da kyar ya sha kokuwa da ita tana doddoke shi tana zagin Yakaka wasu lokutan har da Amnee da Baa , haka dai ya daure ya sa tayi wanka ya taya ta shirya yana yi yana rarrashin ta , ya rubuta Allurar da yake son yayi mata ya bawa maigadi ya sayo ya kawo ya danna mata , bayan ya haɗa mata tea ta sha kaɗan tayi bacci . A gajiye liƙis ya baro gidan , zuciyar sa cike da tunanin maganganun da Suleiman ya faɗa masa game da Yakaka yana zakwaɗin samun tabbacin sahihancin su . Bayan ya zauna akan kujerar falon sa a kasalance ya ɗau wayarsa tare da ƙiran layin Amnee Khaalty Rahima ce ta ɗaga ƙiran saboda Amnee ta shiga wanka , bayan sun gaisa yace da ita " yunwa yake ji dan Allah a samar masa da abinci ," Abincin sa na musamman da daman yake kitchin ɗin sama a ajiye can ta hau ta ɗauko masa tana saukowa suka yi kichiɓus da Yakaka wacce ta fito daga ɗakin su zata shiga ɗakin Amnee , Da sauri ta ƙarasa ta karɓi tiren hannun Mamar su tana mata sannu , cike da jin daɗi Khaalty Rahima ta amsa , kafin ta ɗora da cewa yauwa Yakaka ga abincin yayan ku ɗauki ki kai masa , banda ma shirmen ki kina nan kina ta kai kawo mijinki yana can zaune da yunwa ,ki sauya wannan ɗabi'ar tun wuri dan naga alamar duk jaan kunne da nasihar da ake miki ba ganewa kike ba ki sa hijabin ki ki kai masa . Saƙare Yakaka tayi tana kallon Mamar su , so take ko yaya ta samu ƙafar zillewa amma babu dama , ji tayi ta cigaba da cewa " ki kai ki dawo yanzu idan kuma ba haka ba a tafi a barki na ga ma ko gama shirin baki yi ba . Ɗaki Yakaka ta koma ta saka dogon hijabin ta akan doguwar rigar da take jikin ta mai guntun hannu da fitowar ta kenan a wanka ta zira ta a jikin ta ta fito ɗaukar kayan ta a ɗakin Amnee shine wannan tsautsayin ya gifta mata , " ah tsautsayi mana haɗuwar ta da Yaya dakta ai ita tsautsayi ne a wajen ta mutumin da babu wanda ya tsana ya ita ? Cikin takun rashin kuzari ta nufi sashin nasa riƙe da tiren da aka jera abincin akai , tana taɓa ƙofar ɗakin da nufin ƙwanƙwasa ta ƙofar tayi baya a buɗe take , Sai ta shiga a hankali siɗak-siɗak ta ajiye abincin aka ƙasa , zuciyar ta ta ɗan yi sanyi ganin baya falon , tana ɗaga ƙafa da zummar barin wajen ta tsinkayi muryar sa a ɓakin ƙofar ɗakin sa , " Yace " ina ruwa ? Dan Allah a kawo min ruwa , ruwan cikin Fridge na ya ƙare . Bata juyo ba tace "akwai ruwa a ɗaya cooler ɗin , Jin muryar ta ya sa shi ɗago kai da sauri daga goge kan sa da yake yi da towel fitowar sa kenan daga wanka jikin sa sanye da jallabiya , Da sauri ya dakatar da Yakaka wacce ta ɗaga sawu tana son ɓacewa daga falon , " zo ki zuba min , yace da sauti marar ƙarfi , kanta a ƙasa ta juyo ta ɗau daya daga cikin plate biyu da suke kan faranti ta fara ƙoƙarin zuba aɓincin , Da sauri ya dakatar da ita , " kar ki zuba , chak ta tsaya zuciyar ta na harbawa , jinsa tayi daf da ita ya kai hannu a hankali ya zare plate ɗin daga hannun ta , banɗakin sa ya koma ya ɗaureye plate ɗin tare da chokula biyu , ya dawo ya miƙa mata, ta miƙa hannu biyu ta karɓa , da ido ya bi hannun ta da ya sha ƙunshi . " Ya isa yace , lokacin da ya ga tana ƙoƙarin cika masa Plate har ya tunbatsa , kan ta a ƙasa ta miƙa masa , ya karɓa yana kallon fuskar ta , kafin tayi wani yunƙuri yace mata " ki dakata na gama ci kar ki tafi , A ɗarare ta zauna daga gefe a ƙasa ta sunkui da kai , yana daf da kammala cin abincin Amnee ta ƙira wayar sa , yayi hanzarin ɗauka ," tambayar sa tayi ina Yakaka ? Ka turo ta yanzu ta gama shiri kowa ya shirya ita ake jira har wasu sun tafi , Cike da nutsuwa da kwantar da kai yace " Amnee wani wajen za'a tafi ne ? A gaggauce ta amsa masa da " eh wajen Dinner ɗin Rahima zamu tafi tare baki ɗaya , ta ƙarasa da cewa " ka turo ta yanzu kaji ko ," "Amnee , amm Amma kuma zuwa dinner har da ita ? Da dai ita ta zauna a gida Amnee ba wani amfanin fitar ta a daren nan tun... Muryar ta a ɗan sama Amnee tace "kai kar ka min tsarin wofi ka turo ta mu tafi yau dai ɗaya tal taje , tunda ita ba'a shirya mata nata bikin ba . Zai sake yin magana ta kashe wayar tana cigaba da yiwa Khaalty Rahima mitar meyasa ta aiki Yakaka sashin Doctor Hamza ? Ga shi zai kawo mata wani iyayi irin na shi . Murmushi kawai Amnee tayi tana mamakin rigimar Amnee marar tushe , mutum da matar sa a hana ta yi masa hidima ? Hankalin sa kwance ya ƙarasa cin abincin sa , cikin ran sa neman hanyar da zai hana fitar Yakaka zuwa wajen wani taron can daban yake , a haƙiƙanin gaskiya baya son ta fita da auren sa cikin wasu ƙattin wofi ,su gama ƙare mata kallo , wanda aka kalla a da ma ya isa , duk da cewa dai wasu maganganun da Suleiman ya faɗa masa sun saɓa sosai da zaton da shi yake mata . Yakaka ta durkusa ta tattara wajen ta haɗe kome yadda ta zo da shi , a hankali ta miƙe zata fita , cikin rashin sanin ta ta taka bakin dogon Hijabinta , saboda sauri da take ta bar inda yake , bata ƙarasa miƙewa ba Hijabin ya taɗile ta tayi ƙasa baki ɗaya farantin hannun ta ya bigi ɗan teburin gabanta , miyar da bata rufe sosai ba ta buɗu cooler ɗin yayi ɗan tsallen da yasa miyar tankwaɓewa ta fallatsuwa har cikin idon ta kafin ta kwaranye mata baki ɗaya a jikinta . Ɗumin miyar tare da zafin attaruhun ciki da ya shiga mata ido yasa bata san lokacin da ta saki wani ɗan ƙaramin ihu ba . A ruɗe Doctor Hamza ya miƙe yana jera mata sannu , amma azabar da take ji a idanun ta yaƙi barin ta nutsuwa bare ta ji me yake cewa , ihu ta shiga yi tana cewa " wayyo idona , Da sauri ya riƙo ta ya kama hannuwanta duk biyu zuwa cikin ɗakin sa ya zarce da ita cikin bathroom , gefen Bath ya zaunar da ita , duk a ruɗe yake da ihun da take yi ya kunna fanfo lokacin da ya ɗauki handle ɗin shower yana tara ruwa a hannun sa , ruwan ya kai ya wanke mata fuskar da shi ya sake cika hannun sa ya wanke mata , Yayi hakan sau kusan huɗu amma bata daina kukan da take yi ba , sai kawai ya juya shower ɗin ya shiga fesa mata ruwan a fuska yana haɗawa da wanke mata idon sosai da ma fuskar ta baki ɗaya , Hannun sa ta ture lokacin da ta ji raɗaɗin ya ragu sosai , ta fara ƙoƙarin buɗe ido , " ya ya ? Ya fita ? Ya tambaye ta cikin taushin murya bayan ya ɗan yi durƙuso a gaban ta yana leƙen idon nata so yake ya ga ta buɗe su , Tana buɗe idon ta runtse su da ƙarfi jin har yanzu da sauran raɗaɗi , bata ankara ba ta ji ya ɗago haɓar ta ya matso da fuskar sa daf ta ta , hannu ya sa ya tallafe ƙeyar ta ya fara hure mata idon a hankali Sassanyar iskar bakin sa tayi tasiri sosai wajen rage mata raɗaɗi , ta kuma taimaka wajen dawo mata da nutsuwar ta , har ma ta fahimci irin kusancin da yake tsakanin su , zuciyar ta ta ji ta buga ɗas! Da hanzari ta buɗe idanun ta da suka ɗan rine suka kunbura kaɗan , suka yi musayan kallo da ita da shi , nitsar da idanun sa yayi cikin nata yana yawo da ƙwarar idanun sa a tsakanin nata , ji yake tamkar wata dama yau ya samu na gano tare da tsamo abunda yake hangowa a cikin ƙwarar idanun ta da yake kashe masa jiki a duk lokacin da ya fiye kallon su , Tsintar kan ta tayi da gaza janye idanun ta , fuskar sa dake daf da ta ta take ƙarewa kallo , sajen da ya bari da yake ta sheƙi a hasken lantarki ya ɗau hankalin ta , kamar ta kai hannu ta taɓa , Ganin yadda ta shagaltu da kallon fuskar sa yasa shi hure mata ido , da sauri ta sake rufe idanun nata , Kamar an farkar da ita sai ta miƙe tsaye da sauri , ta ɗan matsa daga kusan shi sosai sai lokacin ta ankara da jiƙewar da kayan ta yayi sharkaf ,tundaga kan hijabin jikinta har rigar ta ta ciki . " shine ka jiƙa ni haka ? Yanzu ya zan yi ? Ta furta hakan muryar ta cike da shagwaɓar dake nuni da damuwar da

Chapter 89 of 111