kuwa bata karɓu ba domin kamar yadda ya zata dai Baba Prof ne da kan sa yake ƙiran sa.
Cike da ladabi ya ɗaga kiran suka gaisa kafin ya tsinkayi Baa yana masa maganar da yake gujewa tsawon sati guda .
"Hamza ka kuwa je kun taho da iyalin taka ?
Shiru yayi saboda ya san kawai ya tambaye shi ne ba wai dan bai san cewa bai je ba sai dan ya ba shi damar shigar da uzurin sa.
"Ban tafi ba Baa amma yau dai nake son na je Insha Allah .
"To ka daure dai ka je saboda kullum sai Mahaifiyar ta ta ƙirani bana son kayi wani abunda zai taɓa mana zumuncin mu na dai faɗa maka ina kuma sake maimaita ma shi aure daman haƙuri ke jagorantar sa sannan ba zaka gina gidan ka ba sai ka zama jajirtatcen Namiji tsayayye sannan gidan ka zai zama yadda ake so .
"Ina umartar ka da kaje anjima ka dawo da Matar ka ka kuma cigaba da haƙuri da su su duka biyun aure ibada ne .
"To Baa insha Allah zan je Allah ya ƙara girma.
"Madallah Allah ya muku Albarka baki ɗaya.
"Amin
Ya amsa yana sauƙe wayar ya kashe.
Ba sai ya faɗa mata ba daga cikin maganganun sa ta fahimci akan me ake zance da lokacin da ta fahimta ba ƙaramar juriya tayi ba wajen ɓoye razanar ta ta juya tana ƙoƙarin zuba musu abincin a farantin da ta ɗauko .
"Wafaa ya ƙira sunan .
"Na'am ta amsa tana ƙin kallon sa .
Ɗan jimm yayi yana juya zancen da yasan dole ya taɓa mata rai kafin ya tattaro juriyar sa yace .
"Baa da Amnee sun ce Sofi ta dawo , dan haka anjima zan je mu dawo tare.
Wata 'yar fara'ar da take tsakanin laɓɓa ta sakar masa da 'yar dariya tace "Yeehh Anty Sofi Oyo-yo gaskiya naji daɗi Yaya Dacta .
Matso ta yayi yana mata rumfa fuskar sa babu walwala yace "me kika ce ?
"Cewa nayi naji daɗi .
Ta sake faɗin hakan da siririyar murya ganin yadda ya haɗe fuska .
"Ba wannan ba da wanne suna na ji kin ƙirani yanzu ?
Dariya tayi tana tura shi baya ta ce "Anty zata dawo sunan ka na baya ma zai dawo..
Abincin da ta fara zubawa shi ya hana ya sake riƙe ta amma muryar sa bata ɓoye halin da zuciyar sa take ciki na rashin jin daɗi ba yace "Wafaa kar ki rage ko ɗigo na daga yadda muka saba al'amuran mu dan wai Sofi za ta dawo idan kika yi hakan za mu ɓata ni da ke , umarni ne wannan nake ba ki .
Bai sake cewa da ita ƙala ba ya fita daga kitchen. zuciyar ta taji ta ƙuntata "to ita meye laifin ta dan ta ce zata janye sunan da take ƙiran sa da shi a gaban matar sa ? Ita a ganin ta kiyayewa take son yi sanin da tayi Sofi tayi nisa a fagen kishi.
Hawayen da suka cika gurbin idanun ta ne suka zubo , wani irin tsoro take ji kan dawowar Sofi ko yaya zaman su zai sake kasancewa ?
Jikin ta duk a sanyaye ta gama zuba abincin ta ɗauko ta nufi falon , a kan kujera ta hango shi kafin ta ƙaraso ya taryo ta ya karɓe farantin hannun ta , sai ta koma kitchen ta ɗauko masu kayan sha da ta haɗa .
Ɗan shiru ya ratsa tsakani kafin lokacin da ta fara zuba musu haɗaɗɗiyar Maqluba da ƙamshin ta ya ɗau wajen ya tado wa da Doctor Hamza muguwar yunwar da yake ji .
"Wow what a delicious ? a complete meal containing, carbs, protein, fats, fibre, essential vitamins and minerals.
Da murmushi take kallon sa lokacin da ya kai loma ta farko ya haɗiye ya sake ɗiban wata yana lumshe ido ya cigaba da cewa .
"Wafaa do you know Basmati rice has higher fibre content and is a great option for various meal plans, prevents against Cancer cell formation and prevents constipation against heart health risk.?
Tana ɓoye dariyar ta ta ɗan girgiza masa kai alamun bata sani ba.
Kazar da ya ɗauka ya gutsira ita ya nufo bakin ta da sauran .
Noƙewa tayi tana dariya tace " ni fa ba kaza zan ci ba kawai shinkafar raina ke so.
Wara ido yayi yana mata kallon mamaki kafin yace "Come on ki ci kaza Wafaa chicken is a great source of lean protein and has abundance of selenium, phosphorus, niacin.
Haka ba dan ta so ba ta gutsiri kazar ta ci kafin ya cigaba da bata abincin Suna cikin ci tace "Habibi kai baka cin tumatir Sosai ni kuma shi nafi so ka dunga bani sosai.
Bayan ya haɗiye abincin bakin sa yace "eh kuma kina da gaskiya domin shi tomato is a great source of vitamin C, potassium, vitamin k1, folate which are great for normal tissue growth and cell function.
Dariyar da take ta riƙewa tuntuni ita ce ta kufce mata ta shiga ƙyalƙyalawa har tana kwanciya a jikin kujera , shiru yayi yana kallon ta da murmushi a laɓɓan sa daman burin sa kenan ya ga fara'ar ta farin-cikin sa yana tare da walwalar ta.
****
Kamar yadda Doctor Hamza ya alƙawarta A daren ranar bayan Sallar isha'i ya tafi gidan su Sofi domin su dawo tare lokacin da ya ɗora idanun akan ta sai da ya razana saboda ramar da yaga tayi cikin 'yan satika.
Yadda yake zaton za ta masa hauka sai ya ga akasin haka sai nan-nan take yi da shi daga ita har Mahaifiyar ta da hakan yasa dole shi ma ya sau jiki suka ɗan taɓa hira da Momy kori kamar kome bai faru ba.
Inda ya ɗan ga alamun sauyi daga wurin su bai wuce lokacin da suka kawo masa girke-girken da aka shirya musamman domin shi sannan su ka matsa kan sai ya ci.
Shi kuwa ya riga ya ɗebi girkin Yakaka ya ɗora da lafiyayyen kunun aya da ta musu dan haka cikin sa a cike yake ha'in babu masaka tsinke , dan haka ya kafe kan cewa shi babu abunda zai iya sake sanyawa a cikin sa sai kuma gobe.
Nan ya ga yadda Sofi tayi kicin-kicin bai bi ta kan ta ba yace tayi sauri ta shirya ta zo su tafi.
Ga tunanin sa Momy Kori zata ajiye Sofi a gaban sa ta mata ko da 'yar nasiha ce tunda Baban su baya ƙasar yayi tafiya amma ga mamakin sa ko addu'a Momy Kori bata musu ba .
Mamakin sa bai ƙaru ba sai ma lokacin da suka ta shi tafiya yaga Momy Kori ta sa an kinkimi Manyan kulolin abincin nan ta ce wai a kai masu mota su tafi da abincin idan ya so gobe da safe sai Sofi ta ɗumama masa yayi breakfast .
Mamakin sa bai ɓuya ba yace "Momy ɗumamen abinci kuma.? Da Allah a mayar da abincin nan a bayar ga masu aiki .
Momy Kori za tayi magana Sofi tayi saurin katse ta "eh Momy a mayar da abincin nan Doctor fa baya cin abincin da ya kwana .
Wani kallon yatsutsu Momy Kori tayi mata kafin ta kaɗa kai ta ce "to ai shikenan kowa rai ya yiwa daɗi bayan mai shi kai kuma My Son ka bar daɗi tunda baka cin ɗumame sannu ka ji baƙin bature .
Daga haka tayi juyawar ta cikin gida su kuma suka shige mota .
A hanyar su ta komawa gida Sofi sai shisshige masa take tare da bayyana masa zallar ƙewar sa da tayi .
A can-can yake amsa mata saboda ba wai ya huce bane gaba ɗaya.
Bai ankara ba ya ji ta faɗo mai jiki gaba ɗaya ƙiris ya rage kan motar ta kufce masa yayi saurin gangarawa gefen titi.
Ransa a matuƙar ɓace ya waiga yana kallon ta "Sofi wanne irin shirme ne wannan ki...
Bata ba bar shi ya ƙarasa abunda yake son cewa ba sakamakon haɗe fuskar ta da tayi da ta shi.
Sun ɗau lokaci a haka kafin ya zame fuskar sa bai ce ma ta kome ba ya fara ƙoƙarin tada motar yana dai-daita nutsuwar sa '
Ba sabon abu bane a wajen sa Sofi ta nema shi da kan ta amma yau sai ya ji sam bata wani burge shi ba kamar baya , har ji yayi tana ɗan ba shi haushi-haushi , ya fara sabo da yadda ake ɗan jaa masa aji yana nema ana ɗan nan-noƙewa ana zille masa hakan yana ba shi nishaɗi tare da sa shi ya ji cewa lalle fa shi Namiji ne .
"Sofi ki bari nayi driving please kar ki sake taɓa ni.
Bata amsa masa ba illa wani shaiɗanin murmushi da take jifan sa da shi tana wani kashe masa ido ɗaya .
Lokacin da suka ƙarasa gida Sofi ta riga Doctor Hamza sauƙa a motar dan haka ita ta riga shi takawa zuwa wajen ƙofar kai tsaye ta miƙa hannu ta ƙwanƙwasa ƙofar da ƙarfi
Yakaka wacce take zaune zaman jiran su zuciyar ta ta doka da ƙarfi dan sanin bugun ƙofar ko na waye .
A hankali ta miƙe ta ƙarasa gaban ƙofar kafin ta buɗe sai da tayi addu'a sannan ta miƙa hannu a hankali ta buɗe ƙofar .
Kallon-kallo aka yi a tsakanin su kafin Yakaka ta ƙalato murmushi ta ɗora akan fuskar ta dai-dai da ƙarasowar Doctor Hamza ta ce "Anty Sofi sannu da zuwa .
Sofi wacce fuskar take ɓoye yanayin halin da zuciyar ta take ciki ta miƙa hannunwan ta duk biyu ta rungumo Yakaka.
"I miss you so much Lil how are you?
Ta furta hakan kafin kuma ta sake ta tana mai tura ta baya ta samarwa da kan ta hanyar shiga gidan ta wuce kai tsaye ba tare da ta sake kallon Yakaka ba.
Yakaka bata dawo nutsuwar ta ba sai da ta ji sanyin hannun Doctor Hamza ya riƙe nata hannuwan "Wafaa mu shiga ciki .
Cikin wani irin yanayi Sofi take bin gidan da kallo kamar an sauya mata shi ta ko'ina ƙamshi ne ke ta shi shiru falon sai ƙira'ar kur'ani da ke fitowa ta sifuku .
Akan kujerar da ta saba zama nan ta zauna tana harɗe ƙafafu ta miƙa hannu ta ɗau Remote tana ƙoƙarin sauya tasha .
A ɗarare Yakaka ta zauna a kujerar da take kusa da ƙofa shi kuma Doctor Hamza kai tsaye ya wuce ɗakin sa .
"Anty Sofi ina wuni.? Ya Su Momy ?
Yakaka ta furta hakan tana kallon Sofi .
Wani irin ɗago kai Sofi tayi ta tsattsare ta da ido tsawon daƙiƙai fiye da hamsin irin kallon da take mata ya kaɗa mata ciki har yasa ta nemi diriricewa .
Wani mummunan tsaki Sofi ta jaa da Yakaka ta ji shi har tsakiyar kan ta .
Lokaci ɗaya ta ɗauke kan ta a fusace tana kaɗa kai.
Nan take ta tunanin kama kan ta ya faɗo mata dan haka bata sake cewa ƙala ba sai ta ɗau wayar ta .
Zaman shirun da yake cike da ƙosawa daga ɓangaren su duk biyun ne ya miƙa suna jiran fitowar Doctor Hamza wanda sai da ya shafe fiye da mintoci talatin dan kuwa bayan wanka da yayi sai da yayi sallolin sa na shaf'i da watir .
Sannan ya fito falon ya same su kamar wasu gumaka , ita Yakaka kan ta yana ƙasa tana amfani da wayar ta ita kuwa Sofi sai sauya tasha take , bayan ya musu Sallama bai ɗau lokaci ba ya musu 'yar gajeruwar nasiha da ƙare ta da gargaɗi tare da hannuka mai-sanda ga Sofi kan cewa babu shakka shi ba zai sake ɗaukar raini ko rashin kunya tare da neman fitina ba dole ne kowaccen su ta zauna da 'yar uwar ta lafiya a ƙarshe ya sake musu batun rabon kwana inda ya tabbatar da yin ƙwana ɗai-ɗaya a matsayin ranakun girkin kowaccen su '
Bayan gama nasihar sa da dukkanin su suka nuna Amincewar su tare da ɗaukar gargaɗin sa ita Yakaka miƙewa tayi bayan ta musu Sallama.
Taku ɗaya tayi shi ma Doctor Hamza ya miƙe , yana yin taku ɗaya ya riƙo hannun ta da yazo dai-dai da jin sauƙar hannun Sofi da yayi a cikin ɗaya hannun nasa.
Yakaka tana juyowa idanun ta suka sauƙa akan hannun sa da Sofi ta riƙe wani abu ta ji ya soki zuciyar ta da yasa da sauri ta zame hannun ta daga cikin na shi .
Ba tare da ta sake juyowa ba ta nufi ɗaki tana shiga ta murɗa ɗan makulli ta rufe .
Jikin ta kamar babu lakka ta samu wajen zama a bakin gado .
Bata ankara ba kuka ya taho mata ta kai hannun ta biyu ta toshe bakin ta .
Ta kasa sanin dalilin da yasa zuciyar ta ke ƙonewa bayan kuma ba yau ne ba rana ta farko da Sofi ta fara riƙe Doctor Hamza a gaban ta amma a baya bata taɓa jin irin yadda take ji yanzu ba ko me yasa ?
Kukan ta chak ya tsaya lokacin da ta ji ya taɓa ƙofar cikin kwantatciyar muryar sa yake ƙiran sunan ta .
Shiru tayi ba tare da ta amsa ba "Yau lokacin Sofiya ne Yakaka kar ki aikata abunda idan aka aikata miki ba za ki so ba.
Zuciyar ta ta mata gargaɗi mai kama da tunasarwa , dan haka taƙi yarda tayi ko da ƙwaƙƙwaran motsi haka tana jin sa ya ɗan yi mintoci biyu zuwa uku yana taɓa ƙofar kafin ta ji takun sa yana barin wajen .
Silalewa tayi ta kwanta ruwan hawayen idanun ta na hagu na shiga cikin na dama .
****
Washegari da safe lokacin da Doctor Hamza ya sauƙo daga ɗakin Sofi a kitchen ya tarar da ita tana aikin ta hankali kwance duk yadda ya so ya hango wani sauyi a tare da ita bai ga ko alama ba daga yadda take masa bata sauya ba .
Sai ya ji ta saƙe ƙima a idanun sa ƙaunar ta kuma ta sake ninkuwa a zuciyar sa babu shakka managarciya ce tana kuma da dattaku.
Shi ya taya ta suka ƙarasa aikin kafin a gurguje ya shirya kafin ya gama shiri ta haɗa musu abin karyawa .
Yana gaf da kammala Breakfast Sofi ta sauƙo yau dai da alama ta ji faɗan Doctor domin doguwar riga ce a jikin ta mai faɗi wacce bata ƙarasa ƙasa ba ta tsaya gaba kadan da guiwar ta sai hula da ta sa ta rufe kan ta .
Kadaran-kadahan ta amsa gaisuwar Yakaka kafin tace mata "zuba min abincin na ga ko zan iya ci .
Da sauri Yakaka ta ɗau faranti ta zuba mata abincin butter chicken ne tare da khubsa.
Tun Sofi tana ci tana wani gatsine-gatsine har dai ta sau jiki daɗin girki ya kwashe ta ta buɗe baki tana wurga loma bayan loma .
"Doctor wannan Butter Chicken ɗin kamar daga HH Continental aka yi order ko? Dan naji irin dandanon girkin su ne.
Ta gefen ido ya dube ta dai-dai lokacin da yake miƙewa ya ce "Ni da nake da Mata kamar Wafaa yaushe zan tafi yawon gidan sayar da abinci ai wannan ya zama tarihi sofiya .
Hannun Yakaka ya kama "Wafaa mu je ki min rakiya ni zan tafi .
Sofi tana son miƙewa amma daɗin abinci ya danne ta dole tana ji tana gani Yakaka ta tafi raka Doctor Hamza ita tana kai lomar girkin Yakaka.
Bayan ta dawo daga rakiyar sa ta tarar Sofi ta gama cin abincin ta bar kome a wajen ta koma kan kujera ta hakimce .
Bata gaji ba ta tattara kwanukan ta kai kitchen ta wanke .
A ɗarare ta dawo falon ta zauna akwai wani series ne da take son kallo da bata samu damar gani ba jiya ta san suna maimaitawa da safe .
Tana zama ta ji Sofi ta jaa wani ƙaton tsaki.
A hankali ta miƙa ɗaga idanun tana kallon ta irin mummunan kallon jiya shi ta hango a idanun Sofi .
Har ga Allah tsoron yanayin kallon take domin kallo ne irin na hatsabiban mutane mugaye , kallo ne da yake ɗauke da saƙonni masu zafi tare da ƙaƙƙarfan gargaɗi .
Ciɗak¡ ta miƙe bata tsaya ba sai ta wuce ɗaki tana jin lokacin da Sofi tayi wata ƙwafa mai ƙarfi .
Tana shiga wayar ta ta ɗauka ta ƙira Amnee suka gaisa wacce ta dunga mata nasiha tana kwantar mata da hankali kan dawowar Sofi a ƙarshe ta miƙawa Mamar su wayar .
Suka gaisa kafin su yi 'yar hira da rabin ta labarin diramar Bulama ne wanda aka kai shi makarantar kwana ta firamari amma ya gudo da kukan sa da kome a cewar sa ba zai iya barin Mamar Bulama ba .
Yakaka ta yi ta dariya tana jin ƙauna tare da tausayin ƙanin ta wanda ba su wani shaƙu da juna ba.
A ƙarshe suka yi Sallama tana sauƙe wayar ta ƙira Falmata nan ma hirar suka sha sai dai a cikin muryar Falmatan ta iya jin tana da damuwa da nan take hankalin ta ya tashi dan haka ta matsa mata kan sai faɗa mata me yake damun ta ? Ko haihuwar ce ta zo ?
Falmata bata ɓoyewa Yakaka kome nan ta faɗa mata irin matsananciyar damuwar da take ciki kan barin ta da Youssouf yayi ya tafi wajen aiki ta ɗora da cewa "kuma fa Yakaka sau uku kawai muke waya a rana kuma sau biyu kawai muke Appel vidéo a rana kafin ya tafi kuma ba haka ya min alƙawari ba cewa yayi kawai koyaushe yana tare da ni .
Shiru Yakaka tayi tana jinjina rikicin Falmata a zuciyar ta kafin ta ce "Falmata waya har sau uku a rana ? Ga kuma vidieo call ? Sau biyar fa kenan kike jin sa bai yi yawa ba Falmata ?
Kin san fa tare da matar sa yake a can , sannan ita ma tana da hakki a kan sa bakya ganin za ki shiga hakkin ta dayawa idan ya zama koyaushe kuna tare a waya ? Ni dai fatana Allah yasa bakwa doguwar wayar dare Falmata abunda duk ba za ka so ayi ma ba kar fa ka yiwa wanin ka '
Tsit Falmata tayi daga can tana ɗan turo baki kamar Yakaka na ganin ta sai cewa tayi "to ai nima ina da hakkin ni ba barina yayi ba ma gaba ɗaya ya tafi da ita ba ? ina cewa kullum tare suke kwana ? Meye dan kawai mun yi waya ?
Yakaka tana danne dariyar ta ta ce "a ah wallahi da kome muddin aka ce za ki dunga ratsa tsakanin lokutan da ya kamata ace yana tare da ita to ba shakka kina shiga hakkin ta haba mana Falmata ban fa san ki da zalunci ba , dan Miji yafi son ki kar ki yadda ki biye masa ya dunga ƙuntatawa matar sa .
Ni yanzu da Yaya dakta yafi son Sofi akaina za ki so ya dunga min abunda babu daɗi akan ta ?
Girgiza kai Falmata tayi tana jin duk jikinta yayi sanyi ta ce "ki daina cewa haka Yakaka Yaya dakta yana son ki ba zai taɓa walakanta ki akan Sofi ba.
"Kuma nima ba wai so nake ya dunga walakanta matar sa akaina ba kawai dai.
Ɗan shiru tayi tana numfasawa kafin ta ce "Yakaka ina son shi ne dayawa zuciyata tana min ciwo idan har na tuno yana can tare da ita ni kuma ga ni nan da ciki himm ina fama.
"Ki rage kishi Falmata kowacce mace tana son Mijinta amma domin a zauna lafiya babu cutarwa sai a dunga sassautawa ana tausar zuciya kin jin ko Gimbiya Falmata., ke ce fa Uwargidan Sarki watarana uwayen gida da kawaici aka san su domin suke jagorar Gida .
Sassauƙar dariya Falmata tayi tana jin ranta na yin sanyi ƙaunar 'yar uwar ta na kawo mata
****
Kafin cikar sati ƙarfi da yaji Yakaka ta koma zaman ɗaki saboda yadda Sofi ta kasa ta tsare alhalin ta san Yakaka tana matuƙar shakkun ta .
Muddin ta fito falo to aiki za tayi ta bar wajen ko kuma idan Doctor Hamza yana nan wanda shi bai san yadda yinin su yake kasancewa ba idan baya gidan .
Babu abinda yafi daɗa tayarwa da Yakaka hankali irin ji da tayi Doctor Hamza a jiya da dare yace cikin kwanaki biyu masu zuwa zai yi tafiya zuwa jahar Kano za shi asibitin koyarwa na Kano yin wani aiki na kwanaki uku "kenan zai bar su daga ita sai Sofi a gidan 'yar sakewar ma da take samu tayi a cikin awowi ishirin da huɗun idan yana nan zasu zama babu .
Hakan ya daɗa sanyayar mata da jiki har wani ɗan zazaaɓi take ji yana kama ta bayan bugun zuciyar ta da take ji yana sauyawa a bayan kowacce sa'a ɗaya ga kasala da ta dirar mata .
Bayan fitar sa aiki da ƙyar ta iya lallaɓawa ta fito yin girkin rana da ta san Sofi za ta iya buƙata ba wai dan cikin ta ba saboda ita gaba ɗaya ma yau tunda ta tashi bata sha'awar kome dan ko da suka zauna karin kumallo bata iya cin kome ba sai ruwan shai da ta zubawa cikin ta.
Ba irin rarrashin da Doctor Hamza bai mata ba kan ta ci abinci amma ta gagara dan kan shi yayi shiru ya bar ta bayan ya gama nazarin ta.
Fitowar ta daga ɗakin ya zo lokaci guda da ƙwanƙwasa ƙofar gidan da aka yi dan haka ta ɗan saurara jin ana sake ƙwanƙwasawa yasa ta taho ta buɗe ƙofar .
Musayar kallo suka yi ita da wacce take tsaye a dokin ƙofar tana jifan ta da siririn murmushi mai tarin ma'anoni .
An-anty Samy .
Ta ambata a harɗe ,
"Yaks Amarya a gidan Doctor , matsa min hanya mana na wuce ko kuwa na koma ne ba'a maraba da ni ?
Da sauri ta matsa tana girgiza kai da 'yar fara'a tace "a ah ina maraba da ke mana Anty Samy sannu da zuwa .
Tayi gaba Samy baby ta bi bayan ta tana ƙare mata kallo .
Suna ƙarasawa tsakiyar Falon Sofi na sauƙowa daga sama wata 'yar shewa suka yi ita da Samy Baby kafin su taho su rungume juna suna 'yan ƙananun maganganun su na shaiɗana .
Samy baby za ta zauna Sofi tayi maza ta hana ta "friend me za ki zauna yi anan ? Ta shi mu tafi sama akwai muhimman maganganun da kin san nan ba muhallin yin su bane ba .
"Ok friend
Samy baby ta furta haka tana miƙewa tsaye ta ɗau jakar ta kafin ta mayar da ganin ta kan Yakaka wacce take rakuɓe a gefe wata 'yar iskar dariya tayi mai kama da shewa
"Hehehe Yaks kenan ka ga manyan amare masu harin miƙamin uwargida an gaishe ki Yaks da tsaurin ido .
Shiru Yakaka tayi bata ce ƙala ba gaisuwar da ta yi niyyar yi ma ta fasa jin yadda Samy Baby take mata ba'a sarai ta fahimta .
Kitchen ta koma su kuma su ka hau sama suna shiga ɗaki Samy Baby ta lailayo wata ashariya ta kwatsawa Sofi .
"Kina me Sofi ? Nace kina me har kika bari yarinyar nan ta samu sakewar da zata fara haramar ajiye ƙwai a gidan nan ? Na shiga uku Sofi ina mai tabbatar miki taki ta kusan ƙarewa a gidan nan .....
Sofi da lokaci ɗaya ta diririce idanun ta suka sake shigewa ciki da in'ina a muryar ta tace "me..me ..kika ce ban..ban fahimta ba wanne irin ƙwai kuma kamar wata kaza'
"Yo ai ga ki nan babbar kaza Sofi tunda har kika kasa gane Yarinyar nan Yaks tana da shigar ciki kike zaune baki sake baki ɗau kowanne irin mataki ba...
Bata ankara ba ta ji Sofi ta sakar mata Mari da yasa shiru ya gifta wajen .
Kafin ta tsinkayo muryar Sofi tana cewa "kar ki sake min wannan mummunan Fatan mummunan zancen ,
"kin yi hauka ne Sofi za ki mare ni ?
"A turu nake Samira ya za ki zo kina barazanar fasa min zuciya da mugun fata ki sa na faɗi na mutu tun kwanana bai ƙare ba .
Gyara fuska Samy Baby tana ƙoƙarin shanye fushin ta saboda tarkon da take son ɗanawa kar ya lalace ta sassauta muryar tace
"Wallahi tallahi I swear Sofi Yarinyar nan ciki ne da ita ki nutsu ki dawo hankalin ki tun wuri mu yiwa tufka hanci kafi....
Wani razanannan ihu da Sofi tayi da ya amsa gidan gaba ɗaya sai da yasa Yakaka wacce take kitchen ta zabura
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Chapter 110
Chapter 111
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 107 Chapter of 111