Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Samy Baby ta kashe wayar ta . Tana wani murmushin mugunta ta buɗe gidan sim ta zare sim card ɗin ta gutsittsira shi da haƙorin ta ta watsar a gefen hanya ajiye wayar tayi a gefe kafin ta ɗaura seatbelt a hankali ta daga glass na motar kafin ta tayar da motar da bala'in gudu ta cilla ta a titi . Yadda take gudu a titi ba'a ce Mace ce ke jaan motar ba har dai tayi nisa da ainashin garin Abuja tana tuƙi tana bin waƙar da take tashi ta sifukun motar ran ta fes a dai-dai lokacin ji take duniya ta mata daɗin da bata taɓa jin makamancin sa ba ta samu duniya abunda ya rage kawai sai ta miƙe ƙafa domin cin ta . Kafin kamar walƙiya ta ga ɓullowar wasu motoci biyu da gudu da suka yanko daga cikin daji suka yi banga-banga akan titi da yasa ta cikin matsanancin tashin hankalin da ya maye gurbin nishaɗin da take ji ta taka birki ƙuuuuuuu da ba domin Allah ya kiyaye ba da babu abunda zai hana motar tayi ƙundumbala da ita . Samy Baby bata tabbatar yau ita ce rana mafi muni a tarihi rayuwar ta ba sai lokacin da ta fahimci hannun ko su waye ta faɗa' Masu yin garkuwa da mutane ne kidnappers  da take jin labarin su wai-wai sune yau take ganin su a gaban ta kamar a mafarki . Kwakwalwar ta taƙi samun kwanciyar hankalin yin tunani ɗaya kamar yadda idanun ta suka ƙafe ƙaf daga samun damar zubar hawaye duk wasu kalmomi kuma suka ɓace suka shafe daga bakin ta har zuwa lokacin da suka ɗora mata bakin bindiga suka tasa ƙeyarta bayan sun kwashe kome da yake cikin motar suka nausa da ita cikin daji . *** Sofi ji tayi farin-cikin da take ciki ya mata yawan da bata jin za ta iya jurar sa bata ɗan wataya ba dan haka ta ɗau wayar ta da sai lokacin ta lura da saƙon Doctor Hamza . Wani tsallen jin daɗi ta sake yi jin cewa ba zai dawo ba ma a yau sai nan da wasu ƙarin kwanaki wanda hakan duk alamun nasara ne a gurin ta domin kuwa dama ce ta sake samuwa a gare ta . Kiɗa ta kunna a wayar kafin ta buɗe wata 'yar karamar loka da take jikin gadon ta ta fara zaro kwalabe da sauran kayan mayen ta ' Sai da ta tara su jibgi a gaban ta sannan ta shiga ɗaga su ɗaya bayan ɗaya tana tuttulawa a cikin ta tayi ha'in tana jin ta tamkar tafi kowa farin-ciki a duniya tana tangaɗi ta shiga juya jikin ta tana rawa . Daga can ɗakin Yakaka da ta ji shiru babu alamun motsin sofi a falon sai ta lallaɓa ta fito kai tsaye ta tafi kitchen saboda yunwa da ta fara sasuƙar ta har jiri-jiri take ji . Cikin awa guda ta gama irin girkin da take jin sha'awar ci ta kwashe ta kai ɗakin ta ba tare da ta rufe ƙofar ba sai kawai ta faɗa banɗaki tayi wanka ta ɗauro alwala saboda azahar ta gabato. Tun tana wanka take jin ana ta ƙiran wayar ta har sau uku dai-dai da fitowar ta wayar ta sake ɗaukar kiɗa da sauri ta ƙarasa ta ɗaga ta lokacin da ta ga sunan mai ƙiran Falmata ce . "Hello Falmata na kina lafiya ko ? Ko haihuwar ce ? Ko kin haihun ne ? Ta jero mata tambayoyin ba tare da ta ajiye numfashi ba saboda koyaushe cikin bin haihuwar Falmatan take a rai musamman da yake ita ta taɓa haihuwa ta ɗana ta ji yadda haihuwar ke da zafi duk sai take jin tausayin ƙanwar ta kullum cikin addu'ar sauƙa lafiya take mata musamman da cikin na Falmata ya kusan shige kwanakin haihuwar sa da hakan sabon abu ne a haihuwar fari . "Hello Falmata kina jina kuwa ? Ta sake furta hakan cikin damuwa Dariyar da Falmata ta cika mata kunne da ita yasa ita ma ta murmusa tana sauƙe ajiyar zuciya ta ce "meye abun dariyar kina jina ina miki magana wallahi duk kin ɗaga min hankali ganin yadda kike ta ƙirana ina wanka na zo kuma na ɗaga kin yi shiru. "Yakaka bani nake ta ƙiran ki ba wallahi ni yanzu nan na ƙira ina ƙira kuma kika ɗauka . Ɗan jimm Yakaka tayi "to waye yake ƙirana ? Ta tambayi kan ta , sai bata wani damu ba kawai ta zauna a bakin gado suka shiga hirar su ita da Falmata . Sun ɗau tsawon lokaci suna hirar da take sanya su duka biyun a farin-ciki tare da sake ƙaunar juna ' Kafin kamar daga sama Yakaka ta ji an damƙi kafaɗar ta da yasa ta matuƙar tsorata ta saki wayar ta ta faɗi . Jikin ta yana rawa ta miƙe tsaye tana kallon Sofi wacce take tsaye kiƙam hannun ta ɗaya a ɓoye a bayan ta. An-anty Sofi in-ina wuni. Wata irin shashashar dariya Sofi ta saki da hatta Falmata da bata kai ga katse wayar ba ta ji ta . Zuciyar ta ta fara sauya bugu daga lokacin da ta fara saurarar duk wasu zantukan da Sofi take yi cikin maye murya sama-sama . "Kin yi zaton na kyale ki ko ? A tunanin kin shaa da ni kenan ? Ƙaramar kwakwalwar ki ta baki tunanin kin yi nasara ?  Ni Safiya na bari ki rayu da Mijina ki haihu ? "Wacce irin cusashiyar ƙwakwalwa ce da ke ? Ta kifi ? Kin taɓa ganin an yi haka ? Ba zai yiwu ba , ba zai faru ba ba zai taɓa faruwa ba ki zo ki gina rayuwar ki a kan tawa Hamza nawa ne ni Kadai. "Dole na rusa rayuwar ki a duk lokacin da na so , dole ki mutu Yakaka tunda kin ƙi fita a rayuwa ta to zaki Mutu zaku mutu tare da ke da abunda ke maƙale a cikin ki . Wuƙar da take ɓoye a ɗaya hannun ta ita ta zaro wata kakkaifar wuƙa ce sabuwa fil da alama ita ce mafi girma a cikin jerun set ɗin wuƙaƙen ta . Lokacin da Yakaka ta ɗora idanun ta akan wuƙar ta kuma ji abunda Sofi take cewa jikin ta gaba ɗaya sai ya saki kamar an zare mata lakka wani yanayin da ta kasa tantancewa da shi ya shiga bin gaɓɓan jikin ta idanun ta kuma suka kafe akan wuƙar a hankali ta ji kunnuwan ta na toshewa . "Amma kafin na kashe ki zan so na miki ƙarin bayani kan dalilin mutuwar ki zan faɗa miki irin faɗi tashin da na dunga yi dan na auri Mijina da irin son da nake masa , da nasan ke kan ki za ki iya min uzuri akan kashe ki da zan yi . "Tun ranar farko da na gan shi na kamu da son sa , haka na dunga faɗi tashi alhalin ina korar masoyana har nayi nasarar da aka min tsafin da yasa ya fara kulani a matsayin budurwar sa . "Kar kiyi zaton ke ce rai ta farko da na kashe a kan Hamza ke ce ta uku na farkon jariri ne lokacin da aka bani tabbacin idan har ba'a yi mummunan aikin da aka raba tsakanin jaririya da uwar ta ba to babu shakka uwar jaririyar ita ce matar da Hamza zai aura ba ni ba idan kuwa har aka raba tsakanin su za'a kaɗa uwar wani waje mai nisan gaske ni kuma cikin shekarar Hamza zai aureni hakan ne kuma ya kasance . "Na sha wahala kafin na samu wani ɓangare na daga zuciyar Hamza wanda a ƙarshe sai da aka min aikin da aka kashe wani Mijin da zuciyar sa ta mutu a ƙauna matar sa a can ƙasar india bayan duk na sha wannan wahalar ina zaman daɗi da Mijina za ki ratso rayuwar mu ? "Ya kike tunanin ba za ki zama ta uku ba a cikin jerin Mutanen da za su mutu ba ? Dole ki Mutu dole ki zama mutum ta farko da zan kashe da hannu na akan Hamza . Wasu kauraran hawaye ne suka zubo mata kafin ta cigaba da cewa "kin ga laifi na ne ? Ki duba yadda na lalata jikina saboda kawai na burge Hamza na lalata Mahaifata saboda kawai muyi rayuwar hutu da Hamza bana son ko 'ya'yan cikina su ratsa tsakanin mu . Juyowa tayi ta wani irin fisgo Yakaka da daman tuni alhinin Mutuwa ya safko mata bata da wani sauran ƙarfi . Ta gwara kan ta da bango kafin tayi majaujawa da ita a tsakiyar ɗakin ta yasar da ita da wani azabar ciwo ya sarƙe Yakaka yasa ta saki ihun da ya daki dodon kunne Falmata wacce duk take jin abunda Sofi ke cewa.. Ita ma ihun ta saka da ya amsa sashin ta gaba ɗaya da ƙarfi ta miƙe tsaye lokacin da take sakin wayar hannun ta ta faɗi ƙasa tunanin ta yana tabbatar mata da cewa Sofi ta kashe mata Yakaka a yau . Da gudu Hajja da wasu bayun ta biyu suka shigo waɗan da ihun ta ya je har kunnen su Hajja tana shigowa ta gan ta a durƙushe tana murƙususun ciwo tare da ihun ƙiran sunan Allah da na Yakaka cewa take "Yakaka na ta mutu Sofi ta kashe Yakaka dan Allah ku kaini Nigeria . Hajja wacce kallo ɗaya ta yiwa Falmata ta ga alamun haihuwa a tare da ita ita kuma cewa take "To Alhamdulillah abun yau yazo kenan fatan mu Allah ya raba lafiya sannu Uwarɗakina sannu kin ji daure kowacce Mace da haka ta zama uwa daina iface-ifacen nan ikon Allah ke kuma taki naƙudar da ƙiran sunan 'yar uwar ki ta zo miki o wannan ƙauna ta ku ta girmama . Kafin mintoci goma sha biyar labari ya je wa Hajiya Umma kan cewa Falmata na naƙuda nan take ita da kan ta ta taso zuwa sashin . Ƙarƙashin Umarnin Sarki aka fita da ita zuwa asibiti da kawo lokacin Falmata ta daina surutai saboda ganin idon Hajiya Umma sai dai ruwan hawaye da suka ƙi daina zuba mata a zahiri ciwon da take ji a cikin ranta na rashin 'yar uwar ta yafi ciwon da take ji a sassan jikin ta na buɗuwar ƙasusuwan ta sakamakon abunda yake cikin ta da ya shiryawa fitowa duniya a yau . *** Ciwon da ya turnuƙe Yakaka daga ƙasa ya riƙe mata mara shi yasa ta kasa yin wani yunƙuri na kwatar kanta har lokacin da Sofi ta ƙaraso inda ta jefar da ita tana mata wannan kallon da salon murmushin da zuwa yanzu ta san manufar ta ta kuma gane dalilin da yasa take jin matsanancin tsoron Sofi ashe dan ta ita ce ajalin ta Ɗaga wukar Sofi tayi da iyakar ƙarfin ta ganin  haka ya sa Yakaka kare fuskar ta da tafukan ta biyu tana maimaita kalmar shahada a cikin ran ta kamar yadda take jin kome da ya shafi duniya yana shafewa daga ƙwaƙwalwar ta lahira na maye gurbin sa . duhun da yake da alaƙa da tsanantar gudun jinin jikin ta da aikin da ya wuce misali da zuciyar ta ke yi ya safko yana mamaye ganin ta ya koma dusu-dusu take iya hango abunda yake faruwa ta tsakanin yatsun hannunta Ba zata iya tantance mafarki ne ko ido biyu ba lokacin da ta ga kamar an ɗaga Sofi anyi cilli da ita gefe . Doctor Hamza take Iya gani ya gifta ya ɗago Sofi da ta faɗi a gefe. Mari ya shiga ba ta a fuskar ta dama da hagu kafin ya ji cewa marin bai gamsar da shi ba ya shiga ƙoƙarin zare belt ɗin dake kunkumin sa da muryar da ba tayi kama da ta shi ba yake cewa "Sofiya ashe haka kike ? Haka kika min Sofiya ? Haka za ki min ?  Kisa kike ?  daman Sofiya kisa kike yi ? . Ta ko'ina yake zuba mata belt ɗin a jikin ta kafin ya fisge ta su ka fice daga ɗakin ya tunkuɗa ta ta bugu da bango jikin ta gaba ɗaya ya farfashe yayi shatin belt . Ragwab ya zauna akan kujera kamar kuma ya zauna akan ƙaya sai ya sake miƙewa gaban ta ya dawo ya tsaya yana kama goshin sa da hannun sa ɗaya muryar sa na karkarwa yace "Sofiya duk abunda na ji kina faɗa da bakin ki gaskiya ne ? Gaskiya ne ? Kin yi kisan kai kina kuma yunƙurin sake yin wani a cikin gidana duk kuma a dalilina ? Fisgota ya sake yi a inda take yashe tana wani wuri-wuri da ido ko ɗigon ƙwalla babu a idanun ta illa wani irin ƙuna da ran ta ke yi ganin kome take kamar a mafarki . Fisge jikin ta tayi muryar ta a hargitse tana sarƙewa bata cikin hayyacin ta tace " Duk abunda ka ji nace na aikata a ta dalilin ka nayi kuma a shirye nake da nayi abunda yafi haka Wallahi ni Sofiya a shirye nake da na kashe kowa akan ka , idan kuma aka nemi raba ni da kai ta ƙarfi zamu Mutu tare ni da kai zan kashe ka na kashe kaina .....' Wani marin ya daɗa bata kafin ya fisgota Yana tunkuɗa ta hanyar barin gidan yake cewa , "Na sake ki Sofiya Ni Hamza na sake ki saki Uku ki fita daga gidana kar ki sake nuna min fuskar ki har abada na tsane ki . Chak! Sofi ta tsaya ta tirje taƙi tafiya lokacin da kalmomin sa ke mata amsa kuwwa a kunnuwan ta suna zama kamar ɗigon ruwan narkakkiyar dalma a kogon kunnen ta . Zata silale ƙasa ya ɗago ta da ƙarfi ya ƙarasa tunkuɗa ta waje ya rufo ƙofa a fuskar ta da har sai da ƙofar ta bugi bakin ta ya fashe . Wani ihu tayi ta shiga buga ƙofar kamar zata ɓalla da yasa makofta fara leƙowa wasu ma daga sama suke buɗe windows suna leƙen ta . Lokacin da ta fahimci ta zama mahaukaciya sai ta tashi da gudu ta nufi bakin titi ta tare taxi . Tana zama ta faɗi inda zai kai ta kafin ta cigaba da Sambatu cewa take " wallahi ban saku ba Hamza ƙarya kake ni da kai mutu ka raba ahaf ai daga aikin karnataka ya fara ci nan da gobe ma zan dawo gidana Kashe Yakaka kuma ban fasa ba wallahi sai na kashe ta wallahi sai ta mutu.. Ƙiiii mai taxi ya ci birki abinda kawai ya iya cewa shine "Hajiya Dan Allah sauƙa na fasa yin Area da kika faɗa . Haka ta sauƙa bayan ta cusa masa zagin rashin tarbiya da turanci shi kuwa ya jaa motar sa da ƙarfi ya buɗa mata ƙura ' Haka ta taka da ƙafa tana tafe tana surutai a dai-dai lokacin ba wanda zai gan ta ba tare da ya mata ganin mashahuriyar Mahaukaciya ba . *** Lokacin da Doctor Hamza ya koma ɗaki inda ya bar Yakaka anan ya tarar da ita yana share guntun hawayen idanun sa ya ɗago ta ya rungume ta tsam a jikin sa yana jin yadda bugun zuciyar ta ke sassarfa da yasan hakan hatsari ne ga lafiyar abinda ke cikin ta . Nan take ya fara ƙoƙarin bata agajin gaugawa sai dai bisa tilas ya shirya ta suka nufi asibiti saboda fahimta da yayi cewa dole abinda ke cikin ta da bai yi ƙwari ba sai ya fita saboda bakin mahaifar ya riga ya buɗe jini ya fara sauƙa. A can babban asibiti na ƙasa da yake aiki suka mata abinda duk ya dace kafin a mata allurar bacci na ɗan wani gajeran lokaci da ana sa ran idan ta farka firgicin da take ciki ya bar ta . Zama yayi akan kujera yana riƙe da hannun ta ya zubawa fuskar ta ido a can cikin ransa kuwa lamarin Sofi ke daɗa sanya shi a ruɗani a bayan kowacce daƙiƙa yadda yake jin kome kamar a mafarki Wai Sofi ta aikata duk abubuwan da ta lissafa da bakin ta.? Ga kuma ƙwaƙƙwarar shaida nan tana yunƙurin kashe masa Mata da ba domin Allah ya kawo shi ba da babu shakka Wafaa bata raye yanzu a duniya . Sake runtse hannun ta yayi a cikin nasa yana jin ciwon rashin gudan jinin sa da yayi wanda har ƙaunar sa ta fara yaɗo a cikin ransa "Safiya Annoba ce da ya dace ɗan Adam ya nemi tsari da mata ire-iren ta . Maradi Duk yadda likitoci suka yi kokari tare da son ganin Falmata ta haihu da kanta abu yaci tura gaba ɗaya ta gaza yin yunƙuri yadda ya kamata saboda firgicin da ta kasance a ciki ya tafi da duk wani ƙarfi nata . Mafi munin abun shine jinin ta da yake daɗa hauhawa a bayan kowacce minti talatin . Ba hajiya Umma kadai ba har Maimartaba ma ya shiga zullumi da yasa yake ƙiran waya bayan duk ƙaramin lokaci . Dole tasa ya sanar da Biyamuradi Youssouf da bai kai ga sanin Matar sa na asibiti ba saboda a da so suka yi sai ta haihu kawai sai a sanar masa amma a yanzu da lamari ya yi gardama dole aka sanar masa sannan kuma aka shiga addu'a fiye da wacce ake a baya sannan aka ɗaura tukwane domin yin abinci a bayar sadaƙha duk dan Allah ya sauƙi Gimbiya Falmata Matar Yarima Youssouf lafiya . Ganin lokaci zai tafi tare da shiga hatsarin rasa Baby ko uwar yasa likitoci suka nemi da wani makusanci ya sa hannu a shiga da Falmata ɗakin fiɗa . Maimartaba sarki Abdoul-azizou shine da kansa ya zo har asibitin ya sa hannu aka shiga da Falmata ɗakin fiɗa. Anyi aiki cikin nasara an fitar da ƙatuwar jaririyar da ba'a ce ɗiyar fari bace saboda girma zabgegiya da ita jajir mai tarin suma akai kamar an kifa mata hular gashi dan har sai da likitan da ya ciro ta ya sanya almakashi ya yanke mata gashin ta gaban kan ta sannan ta iya buɗe ido . Babu wanda yasan da tahowar Youssoufa kawai sai ganin sa aka yi a asibitin lokacin har an gama aikin an tura Falmata recovery room. Duk suna tsaye suna jiran a fito da ita zuwa ɗakin da zasu Iya shiga su gan ta ɗaya daga cikin manyan malaman jinyan ya fito ya nemi son yayi magana da Youssoufa . Nan yake shaida masa Falmata ta farka amma kuma sai surutai take tana kuka tana ƙiran sunan wata . Ana buƙatar idan zai yiwu waccan ɗin ta zo ko kuma a ƙira ta a waya a haɗa ta da Falmata suyi magana dan kar kuma wata matsalar ta ɓullo . Tare suka koma cikin ɗakin da take abunda ya bashi Mamaki bai wuce nunawa da Falmata tayi ita ba shi take son gani ba Yakaka yayar ta take nema . Shi ba shi da layin wayar Yakaka amma yana da ta Baba Prof , Amnee da Mamar su da yake ƙira akai-akai yana gaishe su da baya zaton ma kawo yanzu sun san Falmatan ta haihu  Dan haka kawai sai ya ƙira Amne Bayan sun gaisa a gurguje ya sanar da su halin da ake ciki na haihuwar Falmata bayan an mata fiɗa da kuma halin da take ciki a yanzu na neman Yakaka . Yanayi biyu ne ya chakuɗuwa Amnee na farko farin-cikin haihuwar Falmata tare kuma da fargabar halin da aka ce Falmatan na ciki bayan fiɗa da aka mata aka cire mata 'yar . Nan take ta tura masa number Yakaka da bai jinkirta ba ya fara ƙiran layin sai dai sau biyar yana ƙira ba'a ɗauka hankalin sa duk ya daɗa tashi ganin yadda har lokacin Falmata bata bar kuka ba . Dan haka ya sake ƙiran Amne lokacin da ta ɗauka ma suna tsakiya da tattauna da khaalty Rahima kan haihuwar da kuma halin da aka ce tana ciki hankalin su duk bai wani kwanta ba. dan haka sai ta haɗa su da khaalty Rahima tayi masa barka ta kuma sake tambayar jikin Falmatan ? Nan yace har yanzu tana kuka kuma Yakaka take nema sannan ita kuma bata ɗaukar wayar . Jin yadda hankalin sa ke tashe sannan ita ma tana iya jiyo kukan Falmatan da take surutai sai ta ce to bari ta tura masa layin Mijin Yakaka ya ƙira shi wataƙila suna tare amma bari a fara sanar da shi Lokacin da ta ƙira Doctor Hamza dawowar su kenan daga Asibitin da yaga ƙiran Amnee ya ɗauka har labarin abunda ya faru ne ya je musu dan haka yayi hanzarin ɗaukar wayar sai dai bayan sun gama gaisawa sai ya ji Amnee ta ɗaura masa da wani batu kan Falmata da ta haihu da kuma halin da take ciki na kuka da neman Yakaka.' Yana jin haka ya fahimci cewa Falmata tana da sani kan abunda ya faru da hakan ne yasa ta firgicin da take ciki a halin yanzu . Amnee ta cigaba da faɗa masa cewa " idan har yana tare da Yakaka to Mijin Falmatan zai ƙira yanzu sai ya haɗa su suyi magana . "To Ya amsa kafin yayi wani yunƙuri Amnee ta katse wayar ta.' Bai rufa mintoci biyu ba sai ga ƙira daga ƙasar Niger. Ɗan jimm yayi kafin ya ɗaga ƙiran saboda sanin da yayi ƙiran daga Biyamuradi Youssouf ne Baban Mama . Lokacin da ya ɗaga ga mamakin sa ba kamar yadda yayi zato ba sai ya ji muryar Youssouf ɗin faran-faran kamar ya san shi haka ya gaisa da shi dan haka shi ma sai ya daure zuciyar sa suka gaisa har ya masa barka . Daga nan sai Youssouf ya nemi da ya haɗa shi da Yakaka , Falmata ce ke son magana da ita. Cikin nutsuwa Doctor Hamza yace "ka kai mata wayar idan ka bata sai na haɗa su  . "D'accord . Youssouf ya amsa yana mai takawa ya matsa gaban gadon da Falmata ke kwance a hankali ya kara mata wayar a kunne cikin taushin murya yana shafa kan ta yace "Mon Bébé ga Yayar ki nan kuyi magana kiji sai hankalin ki ya kwanta ta ki daina kuka . "Hello Yakaka na tace tana shiƙar kuka.. Jin muryar ta yasa Doctor Hamza karawa Yakaka wayar a kunnen ta wacce duk abunda yake faɗa tana jin sa amma bata san da wa yake maganar ba . Jin sautin Falmata tana kuka yasa ita ma kukan ya zo mata sai suka dunga yi tare cikin kukan Falmata ke tambayar ta "Yakaka baki mutu ba ko ? Sofi bata kashe ki ba ? Ashe Sofi haka take muguwa azzaluma  ? Yakaka ki koma gidan Baa kawai idan Sofi ba zata bari ki rayu a gidan ba kin ji Yakaka Dan Allah ki koma Maiduguri kar watarana Sofi ta kashe min ke Yakaka idan ta kashe ki ni kuma ya zan yi.? Doctor Hamza shi ya fara ƙoƙarin hana kukan Yakaka muryar sa a ƙasa yace " Wafaa ki daina mata kuka ta haihu ana so jinin ta ne ya dai-daita a halin da take ciki kwantar da hankali take buƙata ki rarrashe ta . Kallon sa take yi kafin a hankali ta buɗi baki tace "Falmata kin haihu da gaske.? Me kika haifa muna ? Falmata tana goge hawayen ta da bayan hannu Youssouf na taya ta tace "eh Na haihu Yakaka amma ni ban san ma me na haifa ba ban gani ba ma Ya.. Da sauri Yakaka ta katse ta tana cewa "ina abunda kika haifa ? Ki sa a kawo miki ki ɗauki abinki ki riƙe a hannun ki ki rungume ki shayar da shi arziƙi ne babba yau Allah ya miki Falmata kin zama uwa a yau Dan Allah kar ki bari abunda ki ka haifa yayi kuka a domin rashin ki a kusa da shi sa a kawo shi Alhamdulillah Alhamdulillah . Wata irin nutsuwa kalaman Yakaka suka zo mata da shi cikin sanyi murya ta ce "To Yakaka zan sa a bani abunda na haifa yanzu amma Yakaka kina lafiya ko ? Sofi bata yi miki ciwo ba . "Lafiya ta ƙalau Falmata , ki sa a kawo Baby nan ki sa min naji sautin numfashin abunda kika haifa Falmata . "Ina Baby na ? Falmata ta cewa Youssouf haka , ɗan murmushi yayi yana jin daɗin yadda ta fara dawowa hankalin ta. "Riƙe telephoné na amsa miki ɗiyar mu ki ganta Fatima ' Fita yayi sai ga shi ya dawo rungume da jaririyar a hannun sa da shi ma

Chapter 109 of 111