Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
na jikinta , Idanunta da hancinta suna tsiyaya ta dunƙule jikinta waje guda tana karkarwa , A cikin ran ta ta haƙiƙance rayuwar ta  ta zo gangara , ashe ita kuma irin tata sanadin mutuwar kenan sanyi  ? **** Biyamuradi Youssouf tunda ya fita saɓe da Mama , yayi ɗan tattaki cike da rashin sani takamaimai ina zasu ?? Ya zaɓi ya fita ne saboda yana da yaƙini zuciyar sa ba zata jure ganin fushin ta ba , da shi kuma a wannan gaɓar bai yarda yayi wani yunƙurin ds zsi fallasa halin da zuciyar sa ke ciki ba a kan ta bai so ta gano lagon sa tunda wuri haka , Cigaba yayi da tafiya har ya cimma babban titi , nan ya hango wani shagon sayar da coffee , Bayan ya ƙarba musu coffee me zafi ya zaunar da Mama a kujerar da ke fuskantar ta shi , Juya ɗan chokalin hannun sa yake yi ya gagara shan coffee ɗin , damuwa tayi masa ƙawanya duk wata walwalarsa ta kau , Ko kusa ba zai iya duban ta ya fayyace mata lamuran da suka auku tsakanin sa da 'yar uwar ta ba , yana jin kunya , yana kuma tsoro . Meyasa ta kasa fahimtar barin abunda ya riga ya wuce a muhallin shuɗaɗɗan lamari shi yafi alheri fiye da tone-tone . ? Duban sa ya kai ga Mama wacce tayi shiru ta lanƙwasa kai fuskar ta bayyane da damuwa , Tausayin ta ya ji domin ya san damuwar ta ta samo asali ne ga abunda ya faru tsakanin sa da Falmata , da shima zuwa yanzu nadamar ihun da yayi mata yake yi , Bai yi hakan da wata manufa ba illa ruɗanin da ya tsinci kan sa a ciki da ya sa bashi da wata hanyar daƙile yunƙurin ta tare da kawo ƙarshen maganar idan ba ta hakan ba . Tashi yayi ya zagaya ya ɗauki Mama suka fito daga Coffee Home ɗin ba tare da ya sha coffee da ya saya ba , Sake nusawa yayi bakin titi yana tafe sannu kan hankali har ya tadda ɗan wani killacaccen wajen yin sallah , nan yayi sallar la'asar tare da Mama a gefen sa  , Bayan ya idar hankalin sa ya kai kan wani fili gaban wasu gidaje da matasa da yara suka taru suna wasan ƴar zamiya akan dusar ƙanƙara Tobogganing , kama hannun Mama yayi suka ƙarasa wajen , Ya zauna daga gefe kan kujerar gefen hanya tare da ɗaura Mama a cinyar sa , Sosai wasan ya ɗau hankalin Mama ganin yara ƙanana sa'o'in ta nata faɗuwa da tashi cikin dusar ƙanƙara , nan take ta shagala da kallon su har tana taya su dariya idan wasun su sun faɗi , Ganin walwalar Mama ya bashi damar zurfafa a tunani , sashi guda na ran sa na shawartar sa akan idan ya koma gida ya faɗa mata gaskiya ksn abunda take son sani , yayin da sashi mafi rinjaye ke ƙwabar sa tare da tsoratar da shi abunda faɗa mata gaskiyar zai iya haifarwa , Abunda ya haƙiƙancewa ba zai iya jurar fushin ta da damuwar ta ba domin kusa take sosai da ruhin sa , Bai ankara ba har duhun dare ya fara shigowa , dan haka ya sake komawa wajen da yayi sallah , ya sallaci Magarib  ,  Yana idarwa ya kamo hanyar gida bayan ya saɓa Mama a bayan sa da tayi laushi tuɓus , Ta gaban manyan shagunan sayar da kayan ƙele-ƙele na mata ya zo wucewa , idanun sa suka kai kan wata 'yar kyakkyawar sarƙa da take ɗaukar ido tare da taimakon hasken lantarki da ya haske cikin gilashin da sarƙar take . Murmushi yayi lokacin da idanun sa suka hasko masa sarƙar a cikakken wuyan Falmata , Da hanzari ya shiga shagon ya sayi  sarƙar da take ta farin zinare ƙirar ƙasar Amurka suka zare kuɗin su ta katin sa tare da zura masa akwatin sarkar cikin 'yar jakar da take ɗauke da tambarin Manns jewelry . Cike da fargaban halin da zai riske ta ciki ya nufo gidan , zuciyar sa na aiyana masa wataƙila tayi ta kuka ,?wataƙila kuma ran ta ya sake ɓaci da shi, koma menene zai bata haƙuri ys rarrashe ta ta bar maganar nan , Da Sallama ya tura ƙofar gidan ya shiga , Shiru ya ji bata amsa ba , Ya lalubi wutar falon ya kunna , Idanun sa akan ɗan wajen kunna witar ɗumama ɗakin da har wutar ta mutu , hakan ya sa ɗakin ya ɗau sanyi cikin ran sa babu daɗi  , Ya zaunar da Mama akan kujera , yayi tsaye yana saƙe-saƙe , jikinsa gaba ɗaya yayi sanyi da barin ta da yayi ita ɗaya , Takawa yayi ya ƙarasa bakin ƙofar ɗakin ya ɗan ƙwanƙwasa , " Fatima , mun dawo Ya furta haka da sauƙaƙar murya , Shiru ya sake ji babu alamun motsi , Sai ya murɗa hannun ƙofar ya shiga ɗakin , cikin 'yan daƙiƙai ya fahimci bata ɗakin , da sauri juyo , kai tsaye ya leƙa cikin ɗaya ɗakin , babu alamarta Tamkar an safure shi haka ya dunga bin kowanne lungu da saƙo na gidan yana neman ta tare da ƙira sunan ta , A ƙarshe ya hiƙanƙancewa kansa tabbas bata gidan , ta fita ne ? Ko an sace ta ? Shikenan shi kam ya shiga ukun sa , ta shi kuma ta same shi . Da gudu ya sunkuci Mama ya fito , dusar ƙanƙara na sauƙa a kan su yayi tirus a harabar wajen , ina zai fara nufa neman ta ? Wa zai dosa ya tambaya akan ta ? Gidan da yake maƙwaftan na su ya nufa da sauri ya danna musu ƙararawar neman iznin shiga gidan , Zuciyar sa na ayyana masa wataƙila ta shiga gidan , Tunanin sa ya katse lokacin da aka buɗo ƙofar wani mutum magidanci yayi tsaye yana kallon sa , Da harshen turanci ya gabatar masa da kan sa a gurguje kafin ya ɗora masa tambaya kan ko matar sa ta shigo gidan su ? Da harshen larabci mutumin ya miƙa tambayar ga matarsa da take daga bayansa a tsaye , Nan suka tabbatar masa da babu wacce ta shigo musu , Har ya juya sai kuma ya dawo , Rokon su yayi akan su taimaka su riƙe masa 'yar sa zai je neman matar sa , Basu musa ba suka karɓi Mama da tayi rau-rau da ido tana shirin kuka ganin Babanta zai tafi ya bar ta hannun waɗanda bata kai ga sanin su ba , Bai kula ba ya juya da sassarfa mai haɗe da gudu ya kama doguwar hanyar da tayi cikin unguwar sosai yana tafe yana dube-dube da waige-waige , hankalinsa yayi ƙololuwar tashi , maƙogoran sa ya bushe , idanun sa har raɗaɗi suke yi masa , "Yaa Allah Fatima ina kike ? Yaya za ki min hakka Fatima , ? Meyasa kika fita ? Ya furta hakan muryarsa na karkarwa , bayan hannun sa ya sa ya goge fuskar sa da iskar dusar ƙanƙara ta watso masa , Ganin har ya kusan ƙure unguwar bai gan ta ba ya sa shi komowa baya , yana cigaba da neman ta , addu'o'i iri-iri yake yi , Zai iya cewa tunda yake bai taɓa shiga tashin hankali irin na tsuƙin lokacin nan ba , bai taɓa sanin ita wata kadara ce mai maɗaukakiyar daraja a wajen sa ba sai a wannan gaɓar da yake gaf da rasa ta , bazai yafewa mummunar zuciyar sa ba idan har wani abun cutarwa ya same ta , Sakin hanya yayi ya nufi wata doguwar hanyar da tayi gefe a tsakankanin dusar ƙanƙara Fatima , Fatima , Fatima Yake ƙwala ƙiran sunan ta , Ya ƙure hanyar bai ko ga alamun sawun ta ba sai zunzurutun sanyin a yake ratsa sa , Dawowa yayi da baya ya sake kama wata hanyar ta daban nan ma yana tafe yana kiran sunan ta , Durƙushewa yayi a gefen hanya yana jin tamkar ya ƙwala ihu ko ya ji sauƙin tashin hankalin da yake ciki , Kamar a sama ya fara jin amon Murya ta daga nesa , tana ƙiran sa Da gudu ya nufi inda yake jin tashin sautin ta , A gefen hanya zaune cikin dusar ƙanƙara ya hango ta , Hannuwan sa duk biyu ya sa ya ɗago ta , ya riƙo kumatun ta dama da hagu , "Fatima meyasa kika fito ? Ina za ki je ?  Fatima kar ki sake tafiya ki bar mu . Ta kifta idanun ta da suka bushe ƙemas saboda sanyi tace , "Baban Mama ku na fito nema , dan Allah kayi haƙuri kar ka sake tafiya ka bar ni , bazan sake yi ma laifi ba , Kamota yayi suka miƙe tsaye , yadda take rawar sanyi ya tashi hankalin sa , " Juyawa yayi yayi durƙuso "Fatima kama ni hau bissa bayana mu je gida , Duk da wahalar da take ciki , noƙewa tayi , muryar ta na rawar sanyi tace , "Baban Mama zan iya tafiya da kaina mu taf.... Bata ƙarasa zancen ba ta ji ya ɗaga ta ciɗak , ya ɗauketa , da sauri ta riƙo rigar sa , ya nufi gida da ita . Duk da tafiyar akwai tazara amma bai gajiya ba ko dan kasancewar sa ingarman sadaukin soja ne ? Yana ajiyeta akan kujerar falon su ya shiga haɗa wuta , Muryar ta can ƙasa tace masa , "ina Mama , " zan ɗauko ta tana gidan daura da mu ,     yace Da sauri ya dawo ya zauna a gefenta ya shiga zare mata safar ƙafafunta da suka ɗau sanyi , ya zarce da cire mata hular sanyin kan ta , ɗaki ya shiga ya ɗauko ƙaton bargo ya rufa mata har kan ta Ya kamo ta ya dawo da ita gaban wutar sosai , Hannuwan sa biyu ya shiga karawa a gaban wutar su ɗau zafi sosai sai ya cire ya sa mata a ƙafafunta , A karo na biyu ta sake cewa , "Baban Mama , Mama tana waje ko ? Kar sanyi ya tada hargitsin ciwon ta , Da ido yake bin kyakkyawar fuskar ta da kallo , yadda fuskar ta ke da kyau haka ma zuciyar ta , ya aina hakan cikin ran sa , duk laifin da yayi mata , duk wahalar da ta sha a sanadin sa , ita ta lafiyar 'yar sa take , "bari na ɗauko ta , ya miƙe Har ya kai bakin ƙofa , ya waigo "Fatima kadda ki matsa dagga gaban wuta , Bai jira amsar ta ba ya fita da sauri , ya shiga ya ɗauko Mama wacce har tayi bacci , Godiya sosai ya yiwa maƙotan sa da suke musulman larabawa , Kai tsaye ya wuce da Mama Kan shinfiɗar ta ya ƙwantar da ita a ɗaki tare da haɗa wuta a cikin ɗakin , Inda ya barta nan ya dawo ya tadda ta kamar yadda ya umarceta bata motsa ba , kamar yadda bata daina rawar sanyi ba "Zanyi Sallah tace da shi , Bayan ta idar da magarib ya ja su isha'i , Da suka idar kai tsaye ya nufi shayi me zafi ya haɗo mata , Da chokali ya ɗan sisita shi ya shiga bata a baki tana kurɓa kadan-kaɗan , yadda take rawar sanyi yana damun sa dan haka ya ajiye kofin hannun sa , ya kusanto da ita sosai cikin jikin sa , bayan ya rage kayan jikin sa ya rage 'yar rigar sa ta ciki ya ware bargon da lulluɓa da shi ya rufa musu su biyu , Hannun sa ta ji ya buɗe zif ɗin rigar sanyin jikin ta , kafin ta ankara ya zura hannuwan sa ya kewaye ta da su tare da ƙwanto da ita kan kirijn sa sosai , Ɗumin jikin sa tare da firgici suka yi tasirin da suka hanata ƙwaƙwararan motsi har zuwa lokacin da ya ƙarasa zare rigar sanyin jikinta da ta ɗau sanyi na ban mamaki yayi cilli da ita gefe , Habar sa a tsakiyar kanta ya rungume ta tsam a jikin sa tana iya jin bugun zuciyar sa da yake tashi sannu kan hankali , Wani irin yanayi mai cike da daɗi da nutsuwar zuci da gangar jiki suka tsinci kan su , " Fatima , Ya ƙira sunan ta muryar sa ƙasa-ƙasa , "na'am Ta amsa masa a hankali , "Kar ki sake tafiya wani waje ke kaɗai ba tare da iznina ba kin ji ko ? Bata amsa ba illa kan ta da ta gyaɗa a hankali , Shafar bayanta yayi da hannuwan sa masu ɗumi , "Fatima ɗazu kin tsorata ni na shiga tashin hankali , kada ki ɓata a ƙasa irin US , " kayi haƙuri Baban Mama neman ku na fita sai kuma na kasa gane gida , " kan ta ya ɗago daga kirjin sa ya riƙe fuskarta ba domin yana ganin ta ba saboda duhun da yake cikin bargon , A hankali ya sumbaci goshin ta , "Na haƙura Fatima, ke ma kiyi haƙuri da faɗan da nayi miki ɗazu , kin haƙura ? " kan ta ta mayar cikin jikin sa ta sa hannuwanta biyu ta zagaye bayan sa cikin shauƙi tace "ni baka min laifin kome ba Baban Mama idan ma kayi min na yafe ma , Murmushi yayi da sauti , ya sumbaci kafaɗar ta , yana jin tilin ƙaunar ta da yake binne cikin ramsa suna tunɓuƙowa da wani irin shauƙi da yasa ya gagara mallakar kan sa a karon farko ya shiga gwada mata zallar ƙaunar ta da yayi raino tun wasu shekaru a baya da tsiron sonta ya fara ɗarsuwa a ran sa , ita ma bata ƙi ba , bata kuma bijire masa ba ta ɓuɗe tafukanta ta tallafi muradin sa , tare da miƙa masa abunda yake halalin sa .. daga falo ai sai aza room ko kuwa ??  Assalamu Alaikum Masoya ! Da fatan kuna cikin ƙoshin lafiya tare da ƙwanciyar hankali ? Ina mai baku haƙuri bisa ga jinkirin da ake samu wajen cigaba da rubutu , ajizanci ne irin na ɗan Adam. Nagode . [11/13, 7:04 PM] +234 706 503 6187: MAFARI.. ( Hargitsin Rayuwa ) Umm'muaz 38 Washegari sun tashi cikin farin ciki tare da walwala marar misaltuwa , musamman Biyamuradi Youssouf da yake jin kan sa tamkar yau ya fara angwancewa a tarihin rayuwar sa , Zallar ƙauna tare da tattali yake gwada mata da ita kuma take ta zille-zillewa tare da jin tarin nawin sa , gefe guda na zuciyar ta tsiron ƙaunar sa ya fara yaɓanya yana baza rassa . Da dukkanin daƙiƙa guda yana wucewa ne tare da tunanin sa dake manne cikin ƙwaƙwalwar ta duk kuwa da ga shi zaune zahiri a gaban ta . Yau ne Alƙawarin su da likita dan haka bayan sun kammala karin-kumallo , suka shirya cikin jibga-jibgan rigunan sanyin su rufaffu tundaga wuya, crew neck sweatshirt. Biyamuradi ya maƙalo hannuwan Falmata tare da ɗaukar Mama bisa kafaɗar sa , Ƴar tafiyar da bata cika yawa ba , mai cike da nishaɗi saboda 'yar hirar da ta gifta tsakanin su da ta ƙara musu shauƙin jin daɗin kasancewa da juna , Suka iso asibitin , babu ɓata lokaci suka haɗu da likita , bayan tambayoyin da yayi mata game da sabon cigaban da take samu kan  lafiyar ta , Cikin amsoshin da ta bashi da bincike-binciken da ya sake yi , ƙarshe ya shaida musu da cewa dole a kai ga matakin ƙarshe na yin aiki ga idon . Ba tare da ja ba Biyamuradi Youssouf ya amince , cikin lokaci kaɗan aka shigar da bayanai tare da ɗaura ta akan wasu magunguna daban da zata sha na tsawon sati biyu da za'a mata aikin idon . Sun baro asibitin zuwa gida , akan hanya Biyamuradi Youssouf ya cigaba da ƙarfafawa Falmata tare da kwaɗaitar da ita samun lafiyar idon ko da kuwa ace bata warke baki ɗaya ba . Maƙotan su suka tadda daga ƙofar su suna ƙoƙarin kulle na su gidan , Cikin mutunci Biyamuradi Youssouf ya matsa kusa suka yi musabaha da Maigidan duba da irin mutuncin da suka yi masa a jiya na riƙe masa Mama  , Balaraben da matar sa suka sake jajanta masa kan ɓacewar Falmata a jiya , Cikin jin daɗi ya sake matso da Falmata jikin sa , yana shaida musu cewa ita ce wannan , Nan ya gabatar musu da kan sa , Matar sa da 'yar sa , ƙasar da ya fito da dalilin zuwan sa nan . Inda shi ma Balaraben ya gabatar masa da kan sa , sunan sa Musa Adnan , matar sa kuma Ramlat , sai Yaran su mata biyu Hind da Zahira , Aiki ne ya kawo su nan ,  musulmai ne 'yan asalin ƙasar Kuwait . Da murna tare da ƙauna irin ta musulunci Ramlat ta matsa ga Falmata ta kama hannun ta tare da juya harshe cikin faransanci ta gaishe ta tana tambayar ƙarin lafiyar jikin ta ? , Da jin daɗi Falmata ta amsa mata ,tana riƙe hannun Ramlat da ke cikin nata , Babu ɓata lokaci Musa Adnan yayi musu tayin ko zasu bi su strong museum? Inda zasu tafi da 'ya'yan su domin shaƙatawa ? Ɗan Jim Youssouf yayi , cikin son yin nazari ,shi fa bai cika son tsawaita mu'amala da mutanen da bai wani san su sosai ba sai dai Musa ya katse masa hanzari ta hanyar bugun kafaɗar sa kaɗan , ya juya masa harshe cikin faransanci , "Allez, c'est l'un des meilleurs endroits pour emmener des enfants et des familles dans la région de Rochester am sure you'll enjoy the place. ( ka zo mu tafi , yana daga cikin jerin wurare mafiya kyau domin iyali da yara a garin Rochester na tabbatar zaka ji daɗin wajen )  Falmata wacce daman zaman waje ɗaya tsawon satika ya fara gundurar ta , ta ɗan kwanto da kan ta bisa kafaɗar sa , "BaBan Mama s'il vous plaît nous devons y aller, ( mu tafi mana ?  ) ta furta hakan tana yin ciki da muryar ta ,, Ganin sa ya kai kan zagayayyar fuskarta da take ƙyallin da ke bayyana shaidar yanayin wajen ya amshi fatar ta , Ya mayar da ganin sa ga Musa dake jiran amincewar sa ,    "Okay let's go. Cikin motar da Musa ke jaa da kansa suka kama hanya , akan hanya hira ta sarƙe a tsakanin su , inda Musa yake sanar da Youssouf aikin sa na cruise-ship worker da yake yi ƙarƙashin company jiragen ruwa na ƙasar amurka , ya cigaba da sanar da shi irin tarin ƙasashe da garuruwa gami da tsibiran da ya ziyarta wanda aikin sa ne ya bashi damar haka . Falmata da Ramlat ma suna ƴar hirar da bata cika tsawo ba saboda rashin nunan yaren faransancin a bakunan su duk biyun , yayin da ita kuma Falmata bata jin Turanci bata jin larabci yaruka biyu da Ramlat ta fi iyawa . Basu yi tafiya mai nisa ba suka iso bakin katafaren Museum ɗin , Musa shi ya yanka musu tikitin shiga ciki . Da sanya kafar su wajen ya ɗau hankalin Youssouf da yau ya taɓa zuwa , ƙwarai tsarin gine-ginen wajen suke da ban sha'awa , Mama kuwa tsalle ta fara yi ganin manya-manyan liluna da kayan wasanni irin na yara masu ɗaukar hankalin yaro har ma da babba . Da gudu ta saki hannun Falmata ta bi bayan su Hind da suka riga suka yi gaban kan su zuwa wajen kayan wasanni , Falmata tana ƙoƙarin riƙo ta , ta zille mata ,  hankalinta tashe ta shiga ƙiran sunan ta bata so ta gusa daga kusa da ita kar ta ɓata , Youssouf ya kamo hannuwanta , yana fuskantar ta , yace mata 'ki rabu da itta Fatima , kayan wassan yara ne dayawa a wajen su ta gani ta tafi wurin tare suke da sauran yara, "kar ta ɓata ko kuma ta ji ciwo Baban Mama da dai... "shitt yace yana ɗora mata yatsa akan bakin ta , "baza ta ɓata ba , zo mu tafii inda take , Yana riƙe da hannun ta suka nufi ciki , inda da ƙyar suka lalubo yaran da suka nutse cikin kayan wasanni , Mama sai ihu take me yasa aka zaƙulo ta daga cikin shirgin da ta shige ? Musa shi yayi musu jagora zuwa shashi daban-daban na kayan tarihin wasannin yara tun na tala-taini , tare da tsoffin cartoons, Suna tafe har suka ɓullo gaban gidan sasemet street  , Ɗan murmushi Youssouf yayi yana ɗage girar sa , kafin su haɗa baki shi da Mama wajen cewa, "Sasemet street ? Dariya Musa da Ramlat suke yi ganin yadda Mama take tsallen Murna , tare da ihun ƙiran sunan toys ɗin da take gani na sasemate street a waya ko Laptop ɗin baban ta da koyaushe shine cartoon ɗin kallon ta , Wanda shima kuma favorite children's show ɗin sa ne tun yana yaro hakan ya sa ya koyawa Mama ma kallon sasemate street. "Elmo , Grover, Abby, cadabby , cookie-monster,  Big bird .. Ta ƙarasa jera ƙiran sunayen su tana rufe bakin ta da hannuwan ta biyu , da gudu ta taka zuwa wajen ƴar ƙofar gidan Elmo , Tana matsa ƙararrawar ding dong ditch , ga zaton ta Elmo zai leƙo ya buɗe mata ƙofa , Kara ƙunne tayi a jikin ƙofa cikin 'yar muryar ta take ƙiran " Elmo , Elmo ouvre la porte ( Elmo open the door ) Dariyar da wajen ya ɗauka tare da hasken camerorin da suke ɗaukar ta hoto shi ya ankarar da Youssouf yawan mutanen da suka tsaya kallon shirmen da Mama ke yi cikin Burgewa , Dariya yayi ya taka wajen ta yana ƙiran sunan ta , Ɗaukar ta yayi , "Mama Elmo il dort maintenant ne le dérange pas okay ?) , elmo yana bacci kar ki tayar da shi kin ji ko ? Gyaɗa kai tayi tana waiwayen ƙofar , daga step ɗin suka tsaya Musa ya ɗauke su hoto a camerar sa , Youssouf ya kamo Falmata suka tsaya a wajen Musa ya sake yi musu wasu hotuna , Haka suka cigaba da yawatawa a strong museum , tsawon lokaci kafin su yada zango a wajen wasan pinball , nan wasan ya koma na manya tsakanin Youssouf da Musa , an tuno ƙuruciya , cike da nishaɗi da dariya suka dunga buga wasan pinball , kafin daga bisani su koma kan wasan retro arcada . Sosai suka nishanɗantu , basu yi aune ba har lokaci yayi ta tafiya, wajen cin abinci suka yada zango, Kowa ya nemi a kawo masa abunda zai ci , sanin da Youssouf yayi har yau ba kome Falmata da Mama suke iya ci ba dan haka yayi musu order na abunda zasu iya ci . Daga can wani babban fili da yake a tsaftace suka samu waje gefe , Musa ya jagorance su suka yi sallah . Hira suka cigaba da yi nan zaune bisa kan dakalin da aka yi su da kayan wasan yara yayin da yaran suka tashi suna cigaba da wasannin su da hawa kan liluna , Cikin hirar su Musa ke basu labarin wani tsibiri daya da ya taɓa zuwa a yankin Africa , cikin ƙasar Tanzania , mai suna BAWE a yankin ZANZIBAR, "Bawe zanzibar yana ɗaya daga cikin tsibirai masu kyaun yanayi da namun ruwa masu ban sha'awa tare da tsirrai masu kyaun gani da taɓa zuciya da na taɓa gani  ,      Cewar Musa , ya cigaba da cewa ya yawata a ƙasar Tanzania sosai , ya ga manyan namu dawa a cikin dazuzzukan su , wanda duk duniya a yankin ƙasashen Africa kaɗai ake samun irin su , Ya ɗora da yi masu bayani kan tsibirin Bawe da ya ƙira da dausayin duniya , Har wasu daga cikin hotunan wajen ya nunawa Youssouf daga camerar sa, Karɓa youssouf yayi yana kallon wuraren da suka yi matuƙar tafiya da hankalinsa , ashe muna da irin waɗannan dausayin masu ban sha'awa a yankin Africa ? Miƙa masa camerar sa yayi

Chapter 69 of 111