Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
hukunci me tsanani a gare ki dai-dai da yadda doka da shari'a ta tanadar ga masu yin ƙage da sharri , wanda kin riga kin san haka . Daga haka ya juya ya fara tattaki domin nufar wurin mahaifiyar sa "cikin zuciyar sa kuwa cike taf da bakin ciki da baci rai ! Akan labarin da jakadiya ta zo masa da shi game da ɗan uwan sa muhamadou .'mamman" Muhamadou shine ɗa na huɗu a ɗakin hajiya mama "kuma shine ɗan ta ɗaya tal namiji . ****************** Dai-Dai ya sanya kan shi cikin ɗan madaidaicin wurin "da yafi kama da dakin hutawa " ita ma ta kawo kai kiris ya rage su ci gware cikin sauri ta ɗago kai da niyyar buɗe baki amma ganin wanda yake tsaye a gaban ta ya sanya a take ta diririce "tare da yin ƙasa da sauri ta kai gwiwowin ta ƙasa cikin ƴar siririyar murya tace "ina kwana hamma youssouf " , kallon ta yayi na daƙikan da suke gaza da biyar ya ɗauke kansa tare da sake yin kicin-kicin da fuska daga bisani ya wuce yana me amsawa ciki-ciki da lafiya lau " bayan sa ta bi da sassayan kallo daga bisani ta miƙe daga durƙusan da tayi tana me kakkabe gefe da gefen fara sol ɗin rigar da take ɗore bisa kan kayan ta , gyara zaman farin gilashin idanun ta tayi " da saboda firgitar da tayi kiris ya rage ya subuto daga kan siririn karan hancin ta ", Cikin sassarfar yake taku fuskar sa ɗauke da yalwataccen murmushi da yake bayyana ƙatuwar wushiryar da take tsakanin fararen hakoran sa na sama" har ya ƙarasa gefen dardumar da farar dattijuwar take zaune hannun ta riƙe da wani ɗan ƙaramin littafin addini tana dubawa "zama yayi tare da miƙa hannun sa ya kamo nata hannayen da suke ciƙe da awarwarayen zinare da suke ta faman haske idanun me kallon su , ɗaga hannuwan nata yayi dai-dai fuskar sa ya sumbancin bayan hannuwan nata ɗaya-bayan-daya kafin ya sarƙafe dogayen ƴan ƴatsun sa cikin nata yatsun da suke ƙawace da adon jaan ɓakin lalle da yake ta faman sheƙi tare da tashin sassanyan kamshi " Fuskar ta ɗauke da tattausan murmushi take bin duk wani motsin sa da ƙwarar idanun ta zuciyar ta fal! Cike da ƙaunar gudan jinin zuciyar ta "ina kwana ummana kin tashi lafiya ? Yaya fama da jama" ? Allah ya ƙara miki nisan kwana da hakuri da mu umma " cikin murmushi take shafar baƙar kwantatciyar sumar kan sa tana me amsa addu'ar sa da Ameen kafin ta ɗora da tambayar lafiyar sa shima sannan ta ƙara da tambayar sa yayi karin kumallo ? Ƴar dariya yayi sannan "yace umma na makara sai naje officie zan sha café " tana shirin yin magana ta sake shigowa palourdes (falo ) " Bakin ta ɗauke da ƴar siririyar sallama "Budurwar da suka kusan yin karo da biyamaradi ce " Tare da kulawa hajiya umma take kallon ta kafin ta ce yaya kuma kika dawo SIYAMA ? Ke da kike ta mitar kin yi latti , 'cikin inda-inda tare da satar kallon biyamaradi da ya ciro wayar sa yake dannawa "da alama kira yake shirin yi " tace "umm daman umma kamar nayi mantuwa ne , cikin sauri ta juya gami da nufar wata ƴar kofar da take tsakankanin kofofi huɗun da suke cikin wurin "bayan ta hajiya umma tabi da kallo cikin ran ta kuwa tausayi-kauna gami da soyayyar siyama ce taf take kai kawo" Tana shiga ta tura kofar gami da dafe kirjin ta bayan ta jinginu da jikin ƙyauren kofar " a hankali ta juya tare da zamewa ta durƙusa gami da sanya fuskar ta a dai-dai saitin ramin ɗan mukullin kofar , nan take idon ta ya ƙƴallo mata fuskar sa yana hirar sa da mahaifiyar sa hankalin sa kwance in da yake sanar mata da zancen tafiyar sa a cikin kwanaki uku masu zuwa "idan mai martaba ya amince" ɗan jim hajiya umma tayi sannan ta ɗora da cewa wai kou yarona (bata kiran sunan sa saboda sunan surikin ta ne ) shi tahia bisa aykin ba'a iya yin sa ne tare da amre "abun nuhi bai yuwuwa mutun ya tai tare da iyalin sa " ? ... [6/24, 9:49 AM] +234 701 013 7848: Fikrah writers association *MAFARI .........* ( _HARGITSIN RAYUWA_ ) *Umm'muaz* 3 Gyara zama Biyamaradi yayi kafin yace " A zahiri ummana ba wai ba'a tahia akan hidimar aiki tare da iyali bane sam-sam sai dai duba da irin wurin da zan tai ba kasa ta bace ba ,kuma zan tai ne domin kwantar da tarzoma sannan zan jagoranci mutane sama da dubu ɗaya ne ,ni ne shugaba gare su ina bukatar tattara hankalina kachokam na ɗora bisa aykina tare da kula da mutanen da suke karkashi na " Numfasawa yayi daga bisani ya ɗora da cewa kuma"ummana ki yi duba da irin ita Maimuna ɗiyan sarki ce wacce du inda zata ta zauna sai tare da bayun ta masu yi mata hidima , shin ya kamata daga amren mu na douke ta zuwa wata ƙasa a bakin ayki na wurin da babu tabbacin zata samu irin gatan da take samu a gidan su da kuma wanda zata iya samu da ace anan ta zauna da auren mu ? Ummana a duba lamarin nan da kyau ,? Sauke numfashi "hajiya umma" tayi duk zance ɗan nata gaskiya ne aykin sa me tattare da hatsarin rasa rai ne , ayki ne na sadaukarwa ga ƙasar sa ,shi ya sanya tun farko bata so ba youssof ya zaɓi da ya zama soja , so tayi yayi ta karatu me zurfi har ya zama alkali ta yadda du ranar da ya zama shi ne bisa gadon sarauta mulki ba zai taɓa yi masa wahalar gudanarwa ba , Sai dai duba da yadda shi youssof ya ɗage ya tsaya kai da fata kan ra'ayin sa , ya sanya daga karshe ita da mai martaba suka tsaya masa wurin ganin cikar burin sa bayan kammala karatun jami'ar da ita ma da rarrashi da ban baki youssof yayi "domin da farko so yayi yana kammala karatun gaba da primary ya fada makarantar horar da sojoji " sai dai mai martaba yayi masa jaan ido sosai sannan ya yadda yayi karatun jami'a inda ya karanci fannin sociologue" yana fitowa kuwa ya miƙa takaddun sa ga neman shiga soja , nan take kuwa aka ɗauke sa "kasancewar sa ɗan manya" cike da so da kaunar aikin sa gami da nuna tsantsar ƙwazo ya fara aykin wanda hakan ya jawo nan take ya fara taka matakan nasara hawa hawa , sau biyu ana sawa da shi a cikin zaɓaɓɓun sojijin da ake turawa kwantar da tarzoma a kasashen ƙetere "kasar Somalia da Libya " cikin ikon Allah kuwa duk tawagar da yake jagoranta lafiya suke dawowa cike kuma da tarin nasarori " hakan ya bashi ɗaukaka a cikin ƙanƙanin lokaci har ta kawo sa ga matsayin da yake kai a yanzu wanda a karo na uku sai ga shi an sake tura shi ƙasar Nigeria domin yaƙi da ƴan tawayen Boko haram " Cikin yanayi marar daɗi yake kallon fuskar mahaifiyar sa wacce da alama tayi nisa cikin tunani "shi ya san daga mai martaba har umma basa son aikin sa "kuma da yana da iko tabbas da ya haƙura da aikin amma toh shi yaya zai yi ne shi ya tabbatar haka Allah ya halicci zuciyar sa da ƙaunar aikin soja "domin baya mantawa tun yana shekaru biyar yake ƙwalafaci tare da mararin ganin sa riƙe da bindiga sanye da kakin soja haka ya tashi ya tsinci kansa kullum wayewar gari da mafarkin ya zama soja "abun a jinin sa yake " Muryar sa ce ta doki dodon kunnuwan ta tare da dawo da ita daga duniyar tunanin da ta lula "ummana a cigaba da yi mana addu'a kamar yadda aka saba da iznin Allah babu abun da zai faru da mu sai Alkhairi sannan shekara kamar kwana ce tamkar yau zaki ga ɗan ki ya dawo , ya karashe zance yana dariyar tsokana ". Ƴar dariya itama tayi kafin ta ce addu'a muna kan yin ta yarona kuma insha Allah zamu cigaba fatan mu Allah ya kiyaye tare da shiryar mana ku a duk inda kuke da sauran ƴaƴan musulmai baki ɗaya , to yaya ita ɗiyar tawa da fatan ka sanar mata da batun tafiyar duk da cewa ma nasan idan har tafiyar takasance mai martaba da kansa zai tada ɗan aike zuwa Birnin Agades ɗin " ta ɗora da sake tambayar sa, yaya ɗiyar tawa ta aminta dai kou batare da ta tayar da hankalin ta ba ? Gimtse fuska biyamaradi youssof yayi kafin ya ɗora da mun gama magana kuma ta fahimta , cikin ransa ! Kuwa mamakin yadda wannan lamari zai tafi a haka karfi da yaji yana namiji umman sa ta dunga nunawa da lalle ne ya yi abun da maimouna take so , Sau tari hakan ya sha faruwa hatta akan tsarin ginin gidan sa da aka yi duniya guda daga can Babban filin da yake karshe a cikin masarautar maimouna ita ta zaɓi irin ginin da take so kuma irin sa sak aka yi , ya rasa gano dalilin haka , Shi shine namiji shine shugaba tayaya za'a dunga gwada masa sai abun da matar da zai aura ta zaɓa shi zai yi ? Miƙewa yayi yana me duba agogon hannun sa cikin sauri yake yi wa umma sallama "Ummana ni zan wuce ina ga yau zan iya kaiwa cikin dare kafin dawowa ta sabadda yau zamu fara zuwa bakin bodar da ta haɗa mu da Nigeria domin duba irin tsaron da za'a fara ajiyewa ta wurin" , Bin sa da ido hajiya umma take "tana lure sarai da sauyin da aka samu akan fuskar sa tun da ta ambaci sunan maimouna "cike da so ta fara kwarara masa addu'a tare da sake jaddada masa ya kula da kan sa sosai , har zuwa lokacin da ya karasa ficewa daga wurin da take ", Sauke ajiyar zuciya tayi a lokacin da ya bacewa ganin ta ,lokaci daya ta ɗauke fuskar ta daga jikin bulin makullin kofar tare da miƙewa tsaye ta juyo fuskar ta wacce take " ɗauke da wani tattausan murmushin da a zahiri yake nuna zuciyar ta na cikin annashuwa " dan tsalle tayi tare da juyi kafin a hankali ta motsa laɓɓan ta cikin cewa " za'a ɗaga bikin auren hamma youssouf har zuwa nan da wata shekarar me zuwa ,' taku ta fara yi a hankali da ya dangana ta da jikin katafaren gadon da yake rufe ruf da kyakyawan labulen da iskar da take busowa daga jikin tagar ɗakin yake ɗan kaɗa shi a hankali " janye labulen tayi tare da zama a bakin gadon " ɗan rangwaɗa kan ta tayi cikin cewa "ɗaga ranar bikin hamma youssouf yana nuni da nasarar da na kan iya samu ,hakan yana iya yiwuwar samun wata sabuwar dama a gareni "., Lokaci ɗaya ta gimtse fuska domin tunowa da tayi da nisan da hamma youssouf ɗin zai yi mata wanda ya sanya ba shiri ta ji hawaye ya cika gurbin idanun ta ","hamma youssof zai tafi Nigeria har na tsawon shekara , zan rabu da ganin sa na adadin kwanaki ɗari uku da sittin " bazan iya ba " zuciyata zata iya samun matsala kafin cikar adadin kwanakin nan ya zama dole na samowa kai na mafita " ., zabura tayi jin ana ƙwanƙwasa mata kofa ,' Cike da jin haushi ta ce "waye a nan ? Cikin ladabi hadimar da take durkushe ta bakin kofar tace '"Allah ya huci zuciyar uwargijiya ta sako ne daga " Babbar uwa (hajiya umma ) tace a sanar da ke lokaci yana tafiya " ., ɗan jim tayi kafin ta amsa kina iya tafiya gani nan fitowa ., ki fito lafiya ranki ya dade,' Miƙewa tayi tana me jin duk fitar ta yau ta fice mata daga kai "tana da tabbacin yau bata iya tsinana wani abun kirki a wurin aykin ta "saboda chakuɗuwar farin ciki tare da bakin ciki ! A lokaci guda cikin ran ta ,' Sake ɗurkusawa tayi har ƙasa tana me daɗa yin sallama da hajiya umma wacce ta kafe ta da ido tana me yin nazarin ta ", har ta miƙe da shirin tafiya ta ji hajiya umma ta sake kiran ta "yaki nan ɗiya ta ', dawowa tayi tare da sake durkusawa ", babu dai wani abun da yake damun ki koh ? Da murmushi ɗauke akan fuskar ta ta ɗago tana me kallon fuskar mariƙiya gareta matar da a da take mata ganin mahaifiya tun tasowar ta domin bata taɓa cin karo da wani abu wanda zai sanya ta kokonto akan zaman hajiya umma mahaifiyar ta ba ,' har sai da lokacin da ta shekara goma sha bakwai(ta kammala makarantar gaba da primary ) a lokacin ne hajiya umma ta shaida mata hakiƙanin gaskiyar matsayin ta a wurin ta "hakan kuma ya samo asali ne dalilin ƙin amincewa ta bi mahaifin ta na ainahi da tayi ," da ya nemi son tafiya da ita wurin sa tayi hutun kammala karatun gaba da primary da tayi ", yazo da buƙatar tafiya da ita gidan sa domin ta ga sauran ƴan uwan ta da ya haifa tare da matar da ya aura bayan rasuwar zainab ", Sosai a ranar tayi kuka ,kukan maraicin ta kafin a hankali ta hakura ," ta bi mahaifin ta , ta kuwa ji daɗi sosai da wannan hutun da tayi tare da kannen ta da matar mahaifin ta da ta kasance matar kirki ,' Sai dai tun bayan dawowar ta daga gida (daga wurin mahaifin ta ) ta tarar da hamma youssof shima ya dawo daga jami'a inda ya kammala karatun sa ,' Rana ɗaya ta tsinci yanayin ƙaunar da take masa a zuciyar ta tana sauya muhalli ,daga so irin na ƴan uwan taka zuwa wata irin zazzafar soyayyah ,' ta aure wanda take jin idan har bata mallaki hamma youssof a matsayin mijin auren ta ba zuciyar ta kan iya samun babban raunin da zai iya dangana ta da kushewar ta ", Gyaran murya hajiya umma tayi bayan ta gama nazarin ta sosai ta ce "siyama ki kasance me tsananta addu'a a koyaushe akan dukkanin lamuran ki kin ji koh ? Gƴaɗa kai siyama tayi ,' to maza tashi ki je ɗiyar Albarka Allah ya tsare min ke ya dawo da ke lafiya ," cike da jin daɗi da wata irin kakkarfar soyayyar mariƙiyar ta siyama take amsawa da Ameen "umman mu" Alherin Allah ya isar miki umman mu" , Tsaf hajiya umma ta gama gano abun da yake nuƙurƙusar zuciyar ɗiyar ta siyama ,'domin tun ba yau ba dai take lure da duk wani motsin Siyama akan youssof ɗin ," a kuma bangare guda na zuciyar ta lamarin sosai yayi mata daɗi ganin yadda yayi kicibus da tsohuwar niyyar da ke kulle a cikin zuciyar ta akan siyama da youssof ɗin tana da tabbacin baza ta samu matsala daga bangaren siyama ba". Damuwar ta akan youssof ɗin ne wanda tun farko ta lura youssof ɗin bai wani cika kula lamarin siyama ba tun suna yara "kusan ma za ta ce jinin sa bai ɗauki siyama ba domin tun suna yara kullum faɗan sa da yayar sa 'ubbo' akan siyama ne ,' yana dukan siyaman kasancewar ta yarinya me tsinannen rawar kai a lokacin kuruciyar ta ,"shi kuwa youssof mutum ne marar son hayaniya hakan yasa garin sa bai jiƙuwa ƙoƙo guda da na siyama 'nan take zai bige ta ' wanda hakan yake haɗa sa faɗa da yar tasa domin duk duniya idan aka ɗauke hajiya umma da mahaifin siyama na ukun su a ƙaunar siyama ubbo ce ,sam bata ƙaunar abun da zai taɓa siyama ,' sosai take gwadawa siyama soyaƴyah da gata fiye da ƴan uwan ta da suke ciki guda ma, ' har dai zuwa lokacin da ubbo tayi aure a birnin Niamey gidan ta shine wurin hutun siyama a duk lokacin da ta samu hutun makaranta ,har kuma yanzu da siyama ta kammala karatun ta a shekaru biyu da suka gabata daga Université médecine- medical school ( makarantar horar da likitoci ) in da ta karanci fannin likitar haƙora ( Dentiste-Dentist ) ta kuma fara aiki a asibitin gwamnatin tarayya ta ƙasa reshen jahar maraɗi watanni sha tara da suka wuce , siyamar bata da zancen da ya wuce wurin da zata rubuta hutu musamman ta je da ya wuce gidan addar ta ta ubbo ,wacce mijin ta a yanzu ɗan majalisar tarayyah ne na ƙasa baki ɗaya ," A lokacin da youssof ya zo tare da batun ya samu matar aure a shekarar da ta gabata "dai-dai lokacin da ita kuma take gaf da fiddo manufar ta na son haɗa youssof da siyama aure ta shaida ga mai martaba "wanda ta san zai fi kowa farin ciki da wannan lamarin sanin da tayi lokacin marigayiya zainab tana raye suna da kyakyawar mu'amala ita da mai martaba duk kuwa da cewa shi mai martaba ya girmewa kanwar ta sa da tazara sosai domin mutane uku ke tsakanin sa da marigayiya zainab " , sai dai kuma youssof ɗin ya riga ta tada maganar auren in da yazo da murnar sa yake sanar mata da samar mata da suruka da yayi,' tun a lokacin ta so ta rusa maganar ta kuma fiddo masa da ainahin nata ƙudirin na son haɗa su aure shi da siyama,' Sai dai jin wacce ɗan nata yake da zummar aurowa a matsayin surukar ta ya sanya ta yin laƙwas "ba wata bace wacce youssof ɗin zai auro illah maimouna ɗiya ga mai martaba sarkin AGAƊES , Maimouna ita ce ɗiyar sarkin agades mace ɗaya tal 'ƴar da ta samu gata da kulawa irin na bada kwatance .' Maimouna kyakyawar yarinya "ƴar buzaye" wacce ake kwatancen kyaun ta har ta kai sunan ta da kyaun ta ya shiga jerin abun kwatance a bakin al'umma " haka za'a ji budurwa idan ta ƙure wanka da gayu za'a ji masoyan ta na kururutata " wance kin kou ga kan ki sai kace gimbiya maimouna '? " ko kuwa idan budurwa ta cika feleƙe da yanga dan ita ɗiyar masu akwai ce nan za'a ji ƴan adawar ta suna faɗin" yo ai mu munga gimbiya maimouna ma karshen gata dai kenan" a taƙaice dai gimbiya maimouna ɗiyar gata ce gaba da baƴa , Sanin duk wani wanda ya kwan ya tashi ne cikin ƙasar Niger ", Sarautar birnin Agades shi ke da suna har karfin mulki fiye da dukkanin sauran manyan masarautun gargajiya da ke ƙasar Niger , sanin hakan da hajiya umma da mai martaba sarkin maraɗi suka yi ya sanya nan take zuciyoyin su suka cika da farin ciki ganin ɗan su zai auro ɗiya mafi soyuwa ga Sarkin agades ", wanda sun san hakan ba ƙaramin babban nasara tare da samun sabuwar ɗaukaka gare su da ma jahar maraɗi baki ɗaya ba ne ," Nan take hajiya umma ta ajiye zancen auren siyama da youssof a gefe wanda a da take jiran kammaluwar karatun ita siyama sai ta tado maganar kuma a wancen lokacin siyamar ta riga ta kammala karatun tun watanni biyar da sun ka wuce ", jinkirin da aka samu na son ta sake tsananta addu'ar neman zaɓi ne sai kuwa ga shi jinkirin ya zama Alkhairin da ya sa dole ta ture maganar siyama gefe ba kuma domin ta hakura ta janye zancen baki ɗaya bane "sawun giwa ne ya take na rakumi "sannan cikin ranta tana maimaita ai youssof mijin mace huɗu ne ", da wannan ta ajiye batun gefe , tare da bayyana tsantsar farin cikin ta da batun maimouna , Cikin satin mai martaba sarkin Maraɗi Abdoul-azizou Baskore ya tura da takardar neman aure ga sarki Usoumanu Ibrahim tounouss na birnin Agades , koh da sakon ya isa ga Mai martaba sarkin Agades shima ya bayyana farin cikin sa bayan da yaji ta bakin ɗiyan sa , in da ta tabbatar masa da amincewar ta tare da sake jaddada yawan ƙaunar ta ga biyamaradi youssofa, anan take mai martaba sarkin Agades ya bada tukuici mai yawa tare da takaddar jaddada amincewar sa ," Bayan dawowar ƴan aike daga birnin Agades a daren mai martaba sarkin Maraɗi ya gana da hajiya umma inda yake sanar da ita tayi magana ga ɗiyar ta siyama cewa a tare za'a haɗa bikin ta da na youssof dan haka ta tsaida guda cikin masoyan ta ," Anan hajiya umma bata yi ƙouron baki ba ta sanar da mai martaba haƙiƙanin shirin zuciyar ta tun daga farko ', Ɗan jim mai martaba yayi bayan kammala jin dukkanin kalaman uwargidan sa ," sosai yaji daɗin kyakkyawar niyyar ta sai dai yadda ta ture Al'amarin bayan bayyanuwar maimouna ya sanya shi jin wani iri tamkar dai akwai sautin son kai cikin lamarin nata ," sai dai yayi saurin kauda zargin daga ransa akan sanin da yayi a duniya idan ana kirga masoyan siyama hajiya umma tana daga sahun farko ƙwarai yana alfahari da ita akan irin kyakyawan riƙon da tayi wa ƴar kanwar sa , " dan haka yace idan har ita siyama ta amince da shi youssof ɗin ya zama dole ga youssof ya auri siyama a matsayin matar sa ta biyu shekara guda bayan auren sa da maimouna idan Allah ya yadda ", Nan take maɗaukakin farin ciki ya bayyana akan fuskar hajiya umma ,' tana mai sake jaddada masa da ƙaunar da ita siyama ta lura tana yi wa youssof ɗin tun shekarun baya ," nan dai mai martaba ya tsaida batun auren siyama da youssof sai dai ya nemi hajiya umma da ta bar batun nan a tsakanin su ,"saboda gujewa ƴan kai-kawo ', . *Mairambiri Borno Nigeria* Hasken ranan da ta ɗago ta fara ɗan zafi ita ta sanya ta fara motsi , kafin ta buɗe dogayen manyan idanun ta da suke farare tas tas , da sauri ta miƙe daga kwanciyar da take a cikin taɓon da ya cakuɗe da ruwan da ya kwanta a cikin ƙonanne ɗakin nasu wanda wuta ta riga ta ƙona azaran saman ɗakin ," da sauri ta fara lalube gefe-da-gefen ta , jin bata ji almun mutum a ɗakin ba ya sa ta miƙe tsaye ta fara laluben hanyar fita tare da kiran sunan ƴar uwar ta "yakaka "yakaka " santsi ne ya kwashe ta suuu ta tafi ta faɗi dabas a bakin kofar ," bayan ta ya bada ƙara ƙaƙas , " wani kuka ne ya taho mata a lokacin da wani mugun tsoro ya ɗarsu a ranta koh dai ƴan tawayen boko haram sun dawo ne jiya ? Sun tafi da yakaka ," tunanin hakan ya sa taji wani karfi ya zo mata ta yunƙura da karfin ta ," ta miƙe ta fara tafiya a cikin ruwan da ya cika tsakar gidan nasu da ƙasa bata kai ga shanye sa ba ', Cigaba tayi da ƙwalla kiran sunan yakaka ' yakaka ' yakaka , ruwan hawaye yana me cigaba da ambaliya akan fuskar ta da karfi take jefa kafar ta ba tare da tana laluben gaban ta ba burin ta kawai ta tafi neman ƴar uwar ta ɗaya da ta rage mata," ji tayi ta kaiwa bango karo tayi taga-taga ta tafi da baya ta sake faɗuwa," da gudu take jin takun tahowar mutum kafin taji sautin muryar ta itama cikin firgici tana ƙwalla kiran sunan ta 'falmata 'falmata falmata' Da gudu ta shigo gidan ,"wurgi tayi da ledar da take hannun ta tare da ƙarasawa gurinta zuwa lokacin ita ma kokarin tashi take tana mai sake kiran sunan "yakaka ', ɗago ta tayi tare da rumgume ta cikin jikin ta ,' itama kamkame ta tayi ," kafin su dukkanin su biyu su saki juna suna masu haɗa baki gurin tambayar junan su,' "Falmata baki ji ciwo ba koh ? Yakaka ina

Chapter 4 of 111