ilmin sa da bincike akan sashin da yake da ƙwarewa ta fannin sa na tsawon sati shiddan
, duk a ƙoƙarin sa na son ganin ya yakice duk wata damuwa da Yakaka ta ɗarsa masa cikin ran sa domin kuwa bai san yana son ta har haka ba , bai san son da yake mata yayi masa mugun kamu , ya kafu yayi rassa a cikin ran sa ba ,
sai cikin kwanakin da suka biyo bayan gudun da tayi ta bar shi , ya kuma gano duk wata rufa-rufa tare da yaudarar da tayi masa , kullum da tunanin abun yake rayuwa cikin ran sa ,
ko kaɗan bai jin sa dai-dai kewa tare da tsantsar tsanar ta da ya cusawa kan sa na barazana ga walwalar sa ,
aikin sa da kan sa ya fara samun tsiko a cikin sa , bai tare da kwanciyar hankalin da ake buƙatar irin sa cikin aikin sa , hakan ya sa ya rubuta Annual leave na dole , kuma a karo na farko cikin shekaru shida da fara aikin sa ," bai taɓa rubuta hutu ba sai fa wannan karon da So ya jefa shi a damuwa ,!
Dan haka ya zaɓi yayi ɗan nisa da inda ta taɓa zama da duk wani abun da ya shafe ta na ɗan wani lokaci ko zai samu ya danni zuciyar sa ya yakice ta baki ɗaya daga cikin tunanin sa ya fuskanci rayuwar sa ta gaba , cikin taka tsantsan da duk wani lamari na mata , haka yake fata haka yake buri.
Ya gama tanadar kome da mahaifan su zuwa ƙannen sa zasu iya buƙata na kimanin watanni biyu a gaba , gefe guda bai ƙi ba , bai ɗauke kai ba , bai kuma yi fatali da marayun da yakaka ta wofantar ba duk da cewa ya so yin hakan da farko amma tausayi da ya riga ya zama bangare mafi kyau a cikin jerin halayen sa ya sanya shi gaza yin ko oho da lamarin Falmata da baby mama ,
toh meye laifin su ? me suka yi masa ,? basu da laifin kome basu kuma yi masa kuskuren kome ba, su ɗin Raunana ne abun a taimakawa
Duk da cewa ya ɗauke ƙafafun sa daga cikin saboda kiyaye zuciyar sa da tuno masa da yakaka da take yi , amma cikin tanadin da yayi akan tafiyar da zai yi bai manta Falmata da mama ba su ma ya tuna da su ,
Ya sayi Cartons na madarar baby mama zuwa daiper , wiper , da tarin kayan jarirai himili guda , Falmata kuwa cikin kuɗin da ya danƙawa Rahima yace ta raba uku ta bada kashi ɗaya ga Fatima ,
Bayan ya kammala haɗa duk wasu abubuwan da zai buƙata Zama yayi akan kujera ya miƙe ƙafafun sa aƙasa tare jingina kansa da fuskar kujerar ya ɗaga kan sa sama , "
Tunanin da bai so shi ya fara , kafin kunnuwan sa su fara jiyo masa kukan ta char-char -char tana yi babu ƙaƙƙautawa , shiru yayi yana jin yadda tausayin ta ke lulluɓar sa , yasan ba kukan kome take ba illa kukan rashin jin ɗumin jikin uwa ,
Lumshe idanun sa yayi yana jin sunan da wani sashi na zuciyar sa ya ƙira yakaka da shi ,"muguwa ,"
Ji yayu kukan ya tsawaita , kuma kasantuwar dare ne tamkar a gaban sa take yi , har cikin ran sa yake jin kukan nata , dan haka ya mike cikin rashin kuzari ya sanya takalmun sa ," gami da yiwa cikin gidan tsinke ,
A tsaye ya tarar da su su uku , Falmata Rahima , Da kuma hajja mai wurya ," Baby mama tana rungume tsam a kirjin falmata hajja mai wurya da Rahima sunyi sunyi ta basu ɗiyar su gwada rarrashin ta taƙi , sai faman jijjiga ta take tana hura mata kunne , idan ban da kuka da mimmiƙewa babu abunda jaririyar take yi ,"
Meye same ta ?
Yace da su lokacin da yake ƙarasowa inda suke ,"
Da sauri Falmata ta nufi inda taji tashin muryar sa ,"
Muryar ta tana karkarwar kukan da ta riga ta fara yin sa tun tuni , tace
Yaya dakta Dan Allah duba min Ita meya same ta ko bata da lafiya ne ? Tun ɗazu taƙi shiru ,
Bani ita yace yana karɓar ta daga hannun ta ba musu ta sakar masa ita , ta kafe inda take jin tashin muryar sa da ido , "
Jujjuya ta yayi a hannun sa , kafin yace ungo ta hajja rage mata waɗannan dogayen kayan ,
Zuruf Falmata tace kawo ta yaya dakta na iya cire mata , kuka take yi baza ta tsaya a cire mata a hankali ba , kar hajja ta ji mata ciwo ,"
Sakin baki hajja tayi cikin hasken falon ta dallawa falmata harara ,
Zata yi magana Dakta hamza yayi mata alama da hannu tayi shiru ,
Miƙewa falmata baby mama yayi,
Ga mamakin sa tsaf ta cire mata kayan jikin ta ta barta da diaper tana ta sharar ƙwalla , ta miƙa masa ita dudduba ta yayi ya tattaɓa cikin ta inda nan take ya gane cikin ta ne ya kumbura ,
Ɗaura ta a kafaɗa yayi a hankali ya shiga shafa mata baya yana ɗan jijjiga ta , ba'a fi mintuna huɗu ba ta fara fitar da iskar da ta cika mata ciki , a hankali kuma kukan ya fara lafawa , kafin mintuna goma ƴar jaririyar tayi bacci abin ta ,
Sauƙe ta yayi ya rungume ta a ƙirjin sa , yana kallon ƴar zagayayyar fuskar ta da take ruwan hoda dan fari , gashin da ya kwanta a gaban goshin ta har ya haɗe da girar ta , ,"irin na maman ta ya aina cikin ransa ,"
Da sauri ya miƙawa Falmata ita
Ungo karɓe ta Fatimah , nan gaba idan zaki bata madara ki tallafo kan ta , sannan bayan kin gama bata ki ɗora ta akan kafaɗar ki ki dunga shafa bayan ta kar ki kwantar da ita sai kin tabbatar tayi gyatsa , sannan kar a bata madara da ya zarce ka'idar da aka umarta a bata ,
waye ke hada madarar ?
Ita take haɗa mata cewar Rahima
Ita kuma ? Tayaya zata auna ? Meyasa ke bakya haɗa mata ?
Kafin tayi magana Hajja mai wurya tayi wuf tace ,
Yo wannan yadda take ƙwalafacin ƴar nan da wa ta yarda ? Ko fa ɗaukar ƴar bata yarda ayi , koyaushe tana ƙunshe a hannun ta kamar lalle ,!
Cikin siririyar murya falmata tace ina ganewa yaya dakta , idan na ɗibo madarar a cikin ɗan ludayin ɗibar madarar sai na shafe kan sai na zuba a robar bata madarar, sai nasa ruwan ɗumi dai-dai zanen layin na biyu ko ?
Hakane , haka zaki cigaba da yi mata
yace , yana kama hanyar barin wajen ,
Yaya dakta
Ta ƙira sunan sa .
Chak ya tsaya kafin ya waiwayo ta
Na'am Fatima
Mun gode da kome , Mun gode da taimako, Allah ya ninka maka ya saka da Alheri,
Jim yayi kafin yace mata
Ameen Fatima , gobe zan yi tafiya ki min addu'a
Allah ya kiyaye hanya , Ya dawo da kai lafiya , Allah ya baka sa'a
Ameen Yaa Rabb
Yace yana ƙarasa barin falon , cikin ran sa wani irin yanayi yake ji na taso masa , Ina ma ? Ina ma ? Kai ina ma daga bakin ta waɗannan kyawawan addu'o'in ke fitowa ?
Washegari
Ƙarfe bakwai na safe Doctor Hamza yayi wa mahaifin su Sallama bayan doguwar hirar da suka yi tun bayan sallar asubah , duk wata nasiha da yakamata tare da tunasarwa sai da yayi masa ,
A ƙarshe da ya miƙe zai tafi ya bishi da addu'o'in tsari da fatan samun nasara suka yi sallama , ya shiga motar sa yana barin gidan ɗauke da niyyar biyawa yayi sallama da Amne kafin ya ɗau hanya !
Ƙarfe tara ta sami colonel Youssouf tare da colonel Tafeedah a babbar headquarter na soji da ke garin ,"Giwa barrack ," inda bayan ƴar gutuwar mahawar tare da gabatarwa aka haɗa su da gungun sojoji kimanin su goma sha biyu akan su raka su , a je a kwaso mutanen da colonel Youssouf yace sun ɓoye masa ƙanwar sa ,"
Hilux biyu ta soji ɗauke da bindigogin su suka yiwa unguwar su madam saly tsinke ,.
Tunda suka doso unguwar matasa da ma wasu daga cikin magidantan da suke da tsoffin laifuka suka fara guje-guje , kasancewar unguwar kusan cike take da marasa ji ƙananu da manyan masu laifuka sai kawai aka hargitse da guje-guje , saboda sun san haka tsigau gungun sojoji basu kauce hanya su gangaro musu cikin unguwa ba shakka wani ne yayi wata ta'asar aka zo yin ram da shi ,
Basu kula kowa ba suka bi hanya ƙarƙashin jagoranci Conole Youssouf da yake hakimce gaban motar farko .
Tun daga nesa madam saly da Ɗan liti da suke zaune daga cikin rumfa kan kujeru suna jajantawa juna game da asarar maɗuɗai da suke jajen sun same su , suka fara jiyo jiniyar motar sojoji ,"
Gefe guda kuma ma'aikatan tane baki ɗaya kowa na aikin sa , masu goge-goge da share-share na yi , ta ciki kuma masu wanke-wanke da haɗa ruwan barasar nayi .
Ɗan liti da ke karkaɗa ƙafa yana tsuma yace
Hmm ai ke dai saly fara bar tuna min ,"cin kazar daren farko ," ban son ko tunawa da yadda waɗannan magudan kuɗaɗen da Bala manci yayi mana ta leƙo ta koma da su , ai ƙwaranƙwasa da mun kama su da mun tsalleke kogin talauci , naira dubu ɗari tara fa saly fara ? Kuma ke a ganin ki da mun biya masa buƙatar sa ba zai cikace mana ya zama miliyan bane ??
Kai dai bari liti wallahi ni sai yanzu nake jin takaicin gudun tsinannun yaran nan ƴan gudun hijira yaks da ƙanwar ta , ka ga wannan ƴar luɓu-luɓun ƙanwar tata ai ita ce irin wacce Bala ya nemi da mu kai masa , ƴar ƙwailar da take gaf da balallagewa , "
Uhun ni na tabbatar ke ce mai baƙar ƙafa saly dan duk wata harka indai ta kuɗi ce idan na haɗo da ke ban ganin falala a cikin ta , ƙwaranƙwasa da na sani da juwai me kala-kala na kaiwa harkar nan da yanzu tuntuni kuɗaɗe na sun nuna sun yi ligif a hannu na ,"dan nasan ko ramin kura ta shiga ta nemo irin wacce bala ya nema ,"
Wani kallon sheƙeƙe madam saly ta jefawa ɗan liti ,
Lalle kuwa liti , yo yaushe daren yayi nasa tuwo a ido ?? To idan ka fasa kaiwa juwai me kala kala harkar ka ta samun kuɗi nan gaba kai ba ɗan halak bane liti muna nan da kai zaka dawo da ƙafafun ka ni ɗuwawu ce dole a zauna da ni ,
Rama kallon banzan yayi ya murza yatsu,"suka bada sautin ," ɓas
Ni ce ma ke saly fara , nace ni ce ke , gaba asara baya asara ai wallahi , ki ji ni da kyau idan ido ya mutu kwalli bai tada shi , ke da kan ki dai kin san kome yanzu ba irin na da ba ne , anbar yayin 504 Yanzu 406 ce ke kada maza ahaayye ji min saly fara zata gwadan salon su na tsofin bariki ??
Ta buɗe baki da nufin maida masa martani suka ga ƙartin mazan da ke karta ta waje suna shigowa da gudu suna tsalleke katangar da take ta ƙarshen filin gidan, miƙewa su duka biyu suka yi , dai-dai da shigowar wani gabjejen ɗan busa hayaƙin da ya sha yayi manƙas da gudun ma da ƙyar yake wondan sa a hannu ,
kai idi meye ya faru na gudu ? Inji madam saly
Ta wajena ki arce kiyi ta kan ki idan ba gungun rundunar sojojin Nigeria kaf ne suke shigowa gidan nan ba ,"
Mts ɗan liti ya jaa tsaki yana komawa ya zauna ,
Zauna muyi hirar mu saly fara yanzu haka wannan na maliyan sha yayi tafi ƙarfin ƙwanyar sa , yazo yana mana subaɗaɗi , wai gungun sojojin nigeria ? Ahayyee asha ruwa ayi tamɓele .
Anya kuwa ɗan liti baka zuwa ka dubo mana ko ƴan sanda ne ? Kasan su fa matsayi ta ne ba mutunci ne da su ba yanzun nan sai su chafke mutum su sha janin sa ,"
Bazai wuce su," Corporal garuje " ne suka zo samame ba suna neman na shan matala Kin fa san wata yayi nisa kum...
Kamar ɗaukewar wutar lantarki madam saly ta ji ɗan liti ɗif,"
Kan ta ankara ta ga gungun sojojin da suke ɗurowa cikin gidan , " cikin ta taji ya murɗa nan take laɓɓan ta suka ɗauki rawa ta gagara cewa ƙala ,"
Na ƙale , wallahi na ƙale , nayi surrender !
Ɗan liti ya furta haka yana kai guiyoyin sa ƙasa bayan ya ɗage hannuwan sa sama
Kai tsaye sojojin suka dunga kutsawa ɗakunan gidan suna wurgo mutanen cikin ɗakuna waje ta ƙarfin tsiya , cikin mintoci kaɗan sai ga mutanen gidan rankatakaf a filin gida ,
Kowannen su ciki ya ɗuri ruwa, sai waige waige suke , suna bin sojojin da suka saita su da bakin bindigogin su da kallo ,"cikin son sanin meke faruwa ? Wanne laifi suka yi ? Amma ba halin tambaya soboda tsoro
Tsakiya colonel Youssouf ya fito cikin muryar sa mai amo da yake buɗe ta ya haka a bakin daga yace
Ina yarinyar da kun ka boye a cikin gidan nan ? Ina take ? Ina Kun ka kaita ? Kuyi gaugawar fiddo ta kafin harsashai su sauƙa a kawukan ku baki ɗayan ku ,
Cikin maƙyarƙyatar muryar da tsoro ya riga ya bayyana kan sa a ciki ɗan liti yace
Wallahi Tallahi ranku ya daɗe ni ban san kome ba , ni yanzu shigowa ta gidan ma karbar saƙo wallahi ko jinjirin kiyashi bazan iya cutarwa ba bare ɗan mutum , ɗan mutum ma irin wannan mai darajar dan ....
Dukan da sojon kusa da shi ya kai masa da ƙafa ya sa shi sakin ihu tare da zaman ƴan daɓaro a ƙasa ,
Matsowa Youssouf yayi , kan madam saly
Kin samo ta ko kouwa a ah ? Zaki fiddo ta ko kouwa sai kin ji ƙamshin mutuwa ,??
Idanun madam saly da suka sake shigewa ciki saboda tsoro suka kawo ƙwalla,
Wallahi ranka ya dade na duba , mun duba mun cigita , mun yi neman saƙo da lungu amma ko wanda yace ya ji ɗuriyar su ma ita da ƙanwar ta bamu ji ba , wallahi ranka ya daɗe ba ni na kori yarinyar nan ba raina yana son ta ina ƙaunar ta ita da abun....
Marin da ya ɗauke ta da shi ya hana ta ƙarasa dogon labarin ƙanzon ƙuregen da ta kwaso ,"
Ku musu duka ku kai su mota mu wuce da su barrack , idan sun ɗanɗani azaba zasu faɗi inda take , " cewar Yaoussouf
Kamar jira suke suka fara ƙwallo da su nan take guri ya ruɗe da ihun matan banza da kururuwar ɗan liti da ya buɗe maƙogoro yana zurma ihu tamkar ana watandar tsokar jikin sa , ya buɗe muryar sa ta asalin garjejen namiji ,"
Kora su suka fara yi waje da shirin tafiya da su barikin su na soji ,"
Nan fa idanun Yagana ya fara raina fata wacce ta sha manyan bulalai huɗu ,
Ita tasan aka kai ta wannan barikin sojin sai ɗan buzun ta ," ta tsoraci soja ba kaɗan ba domin ta ga irin yadda basu ɗauki kisa a bakin kome ba ,
Bulalar belt ɗin da wani soja ya sake sauƙe mata a gadon baya yana tunkuɗa ta ita ta gigita ta ,"
Wayyo Allah bayana , fatar bayana ta sulluɓe , dan Allah ku tsaya wallahi na san inda take zan kai ku , zan kai ku Dan Allsh kuyi haƙuri kar ku tafi da ni ,
Matsowa gaban ta yayi ya bar chasa madam saly da ta riga ta fara galabaita da bulalar soji ,
Kin ka ce kin san inda take ? Tana ina ? Ki kai ni yanzu - yanzu idan kin ƙi zan harbe ki ,"
Muryar ta tana sarƙewa tace
Nasan inda take kuma ma ai ƴar uwa ta ce zan kai ku yanzu , Dan Allah kar ku ji min ciwo kar ku tafi da ni ,wallahi nasan inda YaKaKa take ,"
Finciko ta yayi ya miƙar ta tsaye , muje ki kai ni
Yace yana tunkuɗa ta gaba , kafafun ta ko takalmi babu ,
Ku cigaba da tsare su , idan mun same ta zan sanar da ku ta téléphone sai ku ƙyale su idan bamu same ta ba zaku zo mouna da su barrack ,
Ɗaya daga cikin motar suka hau , Yagana da Youssouf da Tafeeda ,
Ki gouda muna hanya," yace da ita
Ba'a yi wata tafiya mai nisa ba Yagana tace a tsaya ga gidan
Tana yi musu nuni da gidan Amne ,
Su suka fara fitowa shi da Tafeda suka tasa ƙeyar yagana kai tsaye suka sanya kai cikin gidan .
Amne tana kishingiɗe akan ƴar daddumar ta tana shan hantsi ta ga tsayuwar sojoji akan ta ,"
Miƙewa tayi zaune tana kallon su a tsorace ,
Wannan ce ta ɓoye su
Yagana tace haka tana nuna Amne da ɗan yatsan ta ,
Da sauri ta miƙe tsaye ,
Ranku ya daɗe lafiya ?
Wanne laifi nayi dan Allah ?
Yarinyar da kin ka boye zaki fiddo mana ita yanzu mu tahi da ita ,ƙanwa ta ce ,
Wacce yarinyar ?
YAKAKA
Yagana ta bata amsa tana matse ido
Zuciyar Amne ta buga da ƙarfi dan razana ƙwarai ta gane yakaka yarinyar da ta mutu wurin haihuwa , ƴan gudun hijirar da ɗan ta ya taimakawa yake riƙon su a gidan su , ganin jami'an tsaro suna neman ta yasa hantar cikin ta kaɗawa ,
anya baza su harbe ta ba idan ta gaya musu ai wacce suke nema ta mutu ?? Ko su tafi da ita barikin su na soji su wahalshe ta a banza , bata da mai karbo ta , ɗan ta yau-yau yayi tafiya , ya bar garin , dole tayi taka tsantsan kar ta ɗaure kan ta !
Mahaifin su Hamza babban mutum ne ba abu mai sauƙi bane a tozarta shi musamman ma da ta san basu yi wani mummunan laifi ba , tana da yaƙinin idan ta sada su da shi kome zai zo da sauƙi , shi zai iya musu bayani su fahimta ,
Ni ba nice mariƙiyar su ba riƙon kwana ɗaya jal nayi musu , a halin yanzu suna gidan mariƙin su , zan iya kai ku gidan na dawo ?
Ta ƙare jawabin ta da sigar tambaya ,?
Ki gouda mana gidan , idan har kin san gaskiya kin ka faɗi ,"
Gaskiya ne wallahi , muje na kai ku ,
Babu Ɓata lokaci Amne ta kai su har Unguwar su Doctor Hamza ta nuna musu gidan daga nesa ,
Kuna iya komawa muhallin ku Tafeeda yace da su, Youssouf zai yi magana , ya masa alama da yayi shiru ,"
Gudu-Gudu Yagana ta tare mai napep ta shiga ,
sansanin ƴan gudun hijira zaka kai ni ,"
tace da shi tana waiwayen bayan ta ,
Ta ɗan madubin gaban napep ɗin ya dube ta , wanne daga cikin sansanin ƴan gudun hijirar zan kai ki ??
Na hanyar bulunkutu tace da shi ,
Cikin ran ta tana kitsima gara ta koma sansanin ƴan gudun hijirar inda samun ta zai yi wahala , zata ɓace a cikin dubunnan ƴan gudun hijira ƴan uwan ta domin ta san ta yarda ta bari wannan sojan ya san da haɗin bakin ta aka gudu da Yakaka har wani garin da ita kan ta ma baza ta ce ga sunan garin ba , bata da hanyar saduwa da samy baby , toh fa tasan ba abunda zai hana shi harbe ta har lahira ya kashe ta !
Tattaki suka fara suna nufar gidan da kowanne cikin su ke yiwa kallon sani ,
Kusan a tare suka ce da juna wannan ai gidan da munka zou biki kwanakin baya ,"
Babu shakka shine Yarima Youssouf ya amsa ,
Maigadin gidan ne ya tare su , cikin ladabi ya gaishe ya ɗora da tambayar su ina suka nufa ?
Suka shaida masa gurin maigidan suka zo ," nan ya shaida musu zai shiga ya sanar da shi zuwan su , har youssouf zai yi magana , Tafeeda ya sake dakatar da shi , bayan wucewar sa yace da shi ,"
Ɗan ouwa mu bi kome a sannu , kar muyi garaje .
Bai ce da shi kome ba , suna tsaye maigadin ya fito yayi musu iznin shiga gidan ƙarƙashin jagorancin sa ,"
Har cikin falon yayi musu jagora , prof yana zaune suka shigo bayan sun sunce ƙwafta-ƙwafatan takalman su daga waje ,
Da kallon rashin sani yake bin su bayan sun gama taƙaitatciyar gaisuwar da ta shiga tsakanin su ,"
Samari daga ina kuke ? Ban shaida fuskokin ku ba !
Ɗan jim suka yi suna tattaro nutsuwar su , kafin Tafeeda da shine ya tsara kome yace
Baba munzo neman watta ɗiya da anka ce kana riƙo sunan ta Yakaka , " wannan mijin ta ne ,
Ya ƙarasa zancen yana nuna youssouf
Ɗan jim prof yayi, wacece yakaka ? Ko dai yarinya ƴar gudun hijira ? ,'
Yaya kamannin ta yake ? Kuma a wanne yanayi take ,"
Doguwa ce fara , tana da tsago a fuskar ta , sannan , sannan kuma tana ɗauke da juna biyu ,
Youssouf ya ambata
Kaine mijin ta ? Prof yace da shi fuskar sa na nuna jimami ,"
Ni ne baba
Ya amsa
, cikin zuciyar sa yana fatan tambayoyin su tsaya iyaka nan , tare da zaƙuwa da son a ƙira masa ita ya gan ta , Allah sarki ashe ma ƴar hijira ce ,
Tunanin sa ya tsaya chak lokacin da yaji prof yace
Yaro ina baka haƙuri tare da tunasar da kai akan cewa duk wani mai rai mamaci ne , yarinya yakaka ƴar gudun hijira ta rasu a wajen haihuwa bayan riƙon su da muka yi a gidan nan tsawon watanni bakwai , ta rasu ta bar ɗiyar da ta haifa tare da ƙanwar ta da muke riƙon su tare ...
Ji yayi wani irin yanayi mai kaifi yana ratsa zuciyar sa wanda ya zarce kaifin tsoro ko firgita , tsintar kan sa yayi a hali na shuɗewar tunani na wucin gadi , jikin sa a take ya ɗauki rawa , da wannan yanayin ya watsa idanun sa kan Baba prof ,"
Yarinya yakaka ta mutu ? Ta mutu a wajen haihuwar abunda ke cikin ta ? Ta mutu bamu gana na nemi yafiyar ta ba ? Ta mutu ban gyara kuskuren da nasa muka aikata tare ba ? Ta mutu Alhalin ban nuna mata godiya ta akan irin taimakon da ita take tunanin ta mun ba ? Meyasa ta Mutu ta bar min nawi mai girma bissa kaina ni kaɗai ?
Tafeeda ne ya riƙo shi ganin yadda yake surutai kusan
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Chapter 110
Chapter 111
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 41 Chapter of 111