Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
cikin sassarfa ta juya gami da nufar cikin gidan ," koma meye dole zata magance mata matsalar ta saboda ita kam duniya bayan mahaifan ta bata da kamar mahaifiyar siyaman har abada baza ta mance da ƙaunar ta ba ,"                          _____     Karfe huɗu da rabi na asubahi agogon niamey jirgin su biyamuraɗi youssouf ya ɗaga Daga "Diori Hammani international airport " zuwa nigeria ,inda karfe shiddah da mintuna arba'in suna cikin tashar jirgin sama na "Nnamdi Azikiwe international airport Abuja Nigeria ",...... Naso chapter nan tafi haka yawa, "amma ban samu dama ba, "kuyi manage da wannan din insha Allah mai yawan yana tafe, " Koh kun San comments din ku suna kadan? 😕ku Kara ku yunkuro a tattauna ku fada min ra'ayoyin ku akan abun da yake faruwa, da ma Wanda kuke hasashen zai faru a nan gaba, Domun nishadin ku nake yi. 😍 #vote #comments #share #son so #fkrh [6/24, 9:59 AM] +234 701 013 7848: Fikrah writers association *MAFARI........* ( _Hargitsin Rayuwa_ ) *Ummu'muaz* 9 Misalin karfe biyu na rana ya kammala da kome da ya shafi sabon wurin da zai fara aiki inda aka tura su shi da sojojin dake ƙarƙashin sa chan tsakanin bodar da ta haɗa nigeria da niger ta cikin jahar borno ," Karfe huɗu jirgin su na sojoji ya ajiye su a cikin garin maiduguri inda zasu kwana zuwa washegari su wuce inda suka nufa ," Tun isar sa babbar hedkwatar soji na birnin na maiduguri , hankalin sa ya tashi da ganin irin taron mutane maza da aka gaggarƙame cikin ɗakunan horo , a galabaice matuka , cikin azabobi da horo mai tsanani wanda a gaban idanun sa ma yaga an fidda gawarwakin jama'a daga cikin ɗakin horon da azaba ta kashe su ," Duk da cewa a matsayin sa na babban soja hakan ba bakon abu bane ,toh amma zuciyar sa ta taɓu da yaji daga bakin wani sojan nigeria cewa waɗannan mutanen , mutane ne waɗanda aka kama akan zargin suna da hannu wurin tada tarzomar boko haram da ba'a kai ga tabbatar da laifukan nasu ba ,sune a jibge a garƙame cikin horarwa da azabtarwa , yunwa da ƙishirwa ,rashin isashen muhalli ta yadda wasu a tsaye suke wuni , wasu a tsugunne ,wasu a tanƙware , wanda yawan su ya tasamma dubunnai ," Gagara samun nutsuwar zuciya yayi bayan ya koma masaukin sa ,zuciyar sa sai kai kawo take da tunanin san samar da mafita ga waɗannan bayin Allah waɗanda a zahiri akwai zalinci cikin irin wannan ajiyar da ake musu ,kamata yayi a miƙa su ga kotun ƙasa ta yankewa kowa hukuncin sa dai-dai da shi waɗanda basu da laifi a sake su , wannan hukuncin ajiye su ana gana musu azobobin da suke kai su ga rasa rayukan su yayi tsanani da rashin dacewa ," Har gari ya waye bai sake marmarin fita ba sai da suka tashi barin ainahin cikin garin maidugurin zuwa bakin bodar da ta haɗa nigeria da niger ta cikin jahar borno , a tare da shi da tawagar sojojin su na niger da kuma ƙarin wasu sojojin nigeria , zuciyar sa cike da tausayin al'ummar da sanadin boko haram ta ɗaiɗaice suka bar ainahin cikin garin na maiduguri . ******* Cikin kwanaki biyar ɗin da su yakaka da falmata suka ƙara cikin sansanin su basu tsinci kome ba sai tarin wahalwalun da suka sake jikkata gangar jiki da ruhin su ," Domin zuwa yanzu karfi da yaji su yakaka sun zama ƴan aikin matayen nan da aka haɗa su rayuwa a ɗakuna ɗaya da su," Ta bangaren yakaka matar da suke kwana tare wacce ake kira "fanne" ta maida ta baiwar ta wacce take yi mata bauta nata da na ƴaƴan ta , tun daga kan wankan yaran biyu har zuwa wankin bargunan su da kullum ta Allah sai yaran sun zabga fitsari , wankin ƴan tsirarun kayan yaran da koyaushe ba'a rasa shi da guntun kashi da fitsari wanda yakakan take shan wahala wurin wankin saboda rashin isashen ruwa da sabulun wankin ,uwa uba rainon yaran da suke kusan yini goye bisa bayan ta duk wata jigila da su take yi suna ɗane a baya , ta sauke wannan ta goye wancen ,uwar su kuwa tana chan cikin yaran mata tana zuba hira da ɗinkin hular ta ,"bata chas bata ass , Ga falmata kuwa duk da kasancewar ta miskiniya amma hakan bai sa ajus ta ɗaga mata kafa daga sanyata ayyuka ba ," tun farar safiya idan ta tashi daga kan shimfiɗar da a yanzu ita kaɗai ke kwana a cikin gidan sauron sakamakon irin azabar da take ganawa falmatan cikin dare ya sa ta hakure ta samawa kan ta salama daga ,zagi hantara ,hauri , mangari da mintsinin da ajus take buwayar ta da su cikin dare , ta bar kwana a gidan sauron ta komo bakin kofa tana shimfiɗa zanen ta tana kwanciya bisa ," amma duk da hakan ita ke lalubawa ta naɗe gidan sauron ta kuma ninke kayan shimfiɗun da ajus ɗin ta kwana a kai , bata bar ta haka ba kullum ita take ɗebo mata ruwan wanka a bokiti da na tsarki a buta , daga bakin famfo inda anan suke samun damar haɗuwa ita da yakaka wacce ita ma take zuwa ɗibo ruwan hidimar fanne da ƴaƴan ta , famfon baki uku ne rak da shi kuma idan aka tayar da injin bada ruwan karfe biyar na asubah zuwa karfe bakwai na safe ake rufewa sai kuma lokutan sallah da shi ma na ɗan kalilan ɗin lokaci ne sakamakon rashin man tada injin tare da rashin wutar lantarki  ," dan haka yaƙi ne tukuru yake tashi wurin kokowar ɗibo ruwan wanda mai karfi ke ture na ƙasa da shi ya samu ya ɗiba ,"ire-iren su yakaka kuwa da kƴar da suɗin goshi da faɗawa cikin dagwalo tare da jin ciwo take samu ta cikawa falmata nata kayan ɗiban ruwan "da yakakan take tsaida ta a gefe ta hana ta shiga turmutsutsun ɗibo ruwan"  ta kuma ɗibo nata , wanda mafi yawancin lokuta ake kashe injin bada ruwan akan bokitin ta ," hakan ya sa har yau da suke cika kwanaki shidda wanda yake dai-dai da kwanakin su bakwai da barin mahaifar su ,fatar jikin su bata ga ruwan wanka ba sai dai ɗaurayar kafafu da hannaye zuwa fuskokin su da suke yi da ruwan alwala ," dan haka duk suka bi suka sake hautsinewa tare da ficewa daga kamannin su ,suka zama yarkace yarkace tamkar sabbin mahaukata. Ɗan dama-daman yagana ce wacce daman ita ta ɗan fi su wayewa da buɗewar idanu saboda ta tashi a alkaryar da take da wadatuwar wayewa , dan haka bata yadda kowacce mace ta nemi taka ta, bata yadda tayi aikin bauta ga kowa , sannan kuma abokiyar kwanan ta ma yarinya ce budurwa sa'ar ta dan haka suke yin chanjaras daga ta nemi kawo mata wargi ," damuwar ta yanayin rayuwar da take gudana ne a wurin da yanzu ta tabbatar ba gidan gwamnati bane , wuri ne na kazo na zo rayuwa ce irin ta daga ƙwari sai gwaiwa ,kowa kan sa ya sani rayuwa ce ta nafsi-nafsi ,uwa uba rashin wadatatcen abinci ,da ruwan sha ba'a maganar kayayyakin gudanar da rayuwa irin ta yau da kullum kamar su sabulan wanka da na wanki ,suturu da sauran su ," wanda tun zuwan su bata ga alamun za'a taimaka musu da waɗannan ba ," ga fatara da ta addabe ta saboda rashin koh kwandala da take matsayin mallakin ta ," gefe guda na zuciyar ta tana tausayawa abokan tafiyar ta da a yanzu ta fisu ƴanci , ta kuma sha zama ta gwada musu yadda zasu ƙwaci ƴancin kan su daga hannun ƴan iskan mata azzaluman da suka maishe su bayin su , sai dai daga yakakan har falmata babu mai kumajin iya kwatarwa kan sa ƴancin saboda rangwamen wayewar kai tare da ƙarancin shekaru , ɗan gwara ma falmata idan ƙumu ta ƙuma mata kai ta kan iya yin hobbasa ta nemi matsera daga hannun ajus ɗin ta hanyan yi mata batar dabo ta gudu bayan ajujuwa cikin datti da guntun najasa tayi zaman ta ," amma ga yakaka babu fuss , akan ga ƙwanjin ta ne kadai idan aka taba mata sanyin idaniyar ta falmata a gaban idanun ta , amma akan kan ta kam raguwa ce ta kin ƙarawa ," Dan haka kamar yau da suke zaune su ukun turmus a cikin rairayin da ganyayyakin bishiyar darbejiya ya lulluɓe ,yagana ta dubi fuskar yakaka da take duk jirwaye da lollori "( abun ka da farar fata )     "Nikam yakaka wannan mawuyacin halin da muke ciki a sansanin nan namu ya isheni , domin ban hango ranar yankewar wahalar mu ba a haka muna zaune cikin rashin sanin makomar rayuwar mu ya kamata mu samarwa kan mu mafita tun kafin ta ƙure mana ,"  dan zunkuɗa goyon yaron da ke ɗane baƙe-baƙe akan bayan ta wanda iskanci ne irin na yara ya sanya shi sanya kukan sai an goya shi domin yana yawon sa da gudun sa ko'ina ,"    "Hmm yagana kenan toh wace mafita kike tunanin muke da ita , mu da bamu da kowa kuma bamu san ko'ina ba sai nan ɗin ? Ai ina ganin haka zamu cigaba da hakuri har zuwa lokacin da ubangiji zai sauƙaƙa mana domin nasan yana sane da mu ," ta karashe zancen tana mai kokarin maida ƙwallar da ta ciko mata a ido      Yangana ta nisa cikin kallon sashin da falmata take wacce gaba ɗaya ta maida hankalin ta ga gefen su tamkar dai idanun ta suna kallon wani wajen , da azahiri kunnuwan ta tarwai suke tana kuma sauraran tattaunawar tasu ,kawai bakin ciki da damuwa ne suke danƙare a kahon zuciyar ta      ",Amma ai kina ganin yadda wasu mutane dayawa a sansanin suke taɓuƙawa kansu wasu abubuwan ta hanyar kula da rayuwar su da ƴan kananun sana'o'in da suke , me zai hana muma mu yunƙura mu gwada sa'ar mu koh zamu samu damar taimskon kan mu da kan mu yakaka rayuwa a haka bazai yiwu ba ," Murmushin takaici yakaka tayi ganin yadda yagana ta hakikice akan batun neman sana'a       Yagana kin manta da ruwan ciki ake jaan na rijiya ? Ita kan ta sana'ar ai sai da jari ,mu kuwa bamu da ko sisi bamu da kadara toh aina kike tunanin zamu samu jari bare a kai ga batun fara tunanin sana'ar yi Nasan bamu da jari yakaka toh amma ai ga "kolo"(abokiyar kwanan ta ) ita ma bata da jarin amma tana bi tana neman aikin kwangilar yin ɗinkin hula ,ana biyan ta muma mai zai hana mu nemi kwangilar mu dunga yi koh zamu samu ɗan kuɗin biyan kananun buƙatu ? Jimm yakaka tayi cikin tunani a zahiri ita bata wani iya ɗinkin hula ba sai dai tana ganin bata da wata mafitar taimakawa kan su ita da falmata idan ba ta wannan hanyar da ƙawar kirki yagana ta zo da ita ba ," dan haka ta ɗago da murmushi dai-dai lokacin da falmata ta waiwayo su tana me kafe gefen da take jin muryar yakaka da ido ,"      Yakaka bata iya ɗinkin hula ba koh riƙe allura a soka bata iya ba, asalima a cikin wannan halin bautar da muke ciki ina yakaka zata samu damar da zata zauna ɗinkin hula , yakaka kar ki ƙarbi abun mutane ki zo ki ɓata musu abu ya zo ya zama rigima da muguwar rawa gwamma ƙin tashi mu cigaba da addu'a Allah zai kawo mana mafita ," Falmara ta furta hakan karon farko tana me jin ciwon rashin idanun ta da babu abun da zai hana tayi ɗamarar karba kwangilolin ɗinkin hula har sai ta samar musu rayuwar da ta fi wacce suke yi yanzu inganci ita da yayar ta domin babu dare ba rana zata duƙufa soka allura da zarewa koh da zata tsire ƴan yatsunta da allura ," sai dai tana jin baza ta iya barin yakaka ta yi ba saboda sanin irin tarin ayyukan da  suke jibge akan yakakan wanda mafi akasarin su na wannan azzalumar matar ne fanne " idan dai ba tsakar dare yakakan zata tashi yin ɗinkin hular ba bata hango tana da lokaci ba , tsakar dare kuma da wanne haske zata soka allura a matsayin ta na ƴar koyo ? Su da basu da koh ashana bare tocila ? Zata fi so yagana ta zo da shawarar wata sana'ar da ita ma za'a iya haɗuwa da ita ayi . Shiru ne ya biyo bayan katse musu hanzari da falmata tayi ,kafin yakaka ta yunƙura cikin karfin zuciya      " zan iya falmata , yagana yaushe zamu samu kwangilar ɗinkin hular kuma aina zamu samu ? Wallahi zan yi koh da a tsaye koh a durƙushe ne zan kuma koya na kware cikin karamin lokaci ni dai fatana mu samu na kan mu ," ta ƙarashe zancen tana mai kamo hannun yagana wacce tayi shiru tana jimamin bahagon halin falmata , Toh bari mu fara tuntuɓar kolo koh zata shige mana gaba domin ita ta san masu bada kwangilar saboda ta fimu daɗewa a sansanin ,"        _____ Saɓanin tunanin su yakaka akan saukin samun kwangilar ɗinkin hula sai ga shi har yau da suke kwanaki huɗu da fara neman aikin kwangilar ɗinkin hular ,amma koh hula ɗaya ta gagara samuwa a gare su , daga ita har yagana ,saboda kowa shakkar basu ɗinkin hular sa yake domin gudun kar su ɓata masa dan babu wanda ya tabbatar da ƙwarewar su , kamar yadda ita kolo tayi suna wurin ƙwarewa da saurin ɗinkin hula hakan yasa take samun kwangila sosai," Har dai yanzu da suka gama hakiƙancewa baza su samu ba ,"kolo wacce ita ma ƙwarai ta so su samu ɗinkin koh dan ɗasawar da suke ita da yagana a yanzu ,"      Mai zai hana toh ku nemi wata hanyar neman kuɗin yagana ? Cewar kolo           Kolo kenan ina muka ga jarin neman kuɗi ? kina ganin aikatau ma mun gagara samu .inji yagana wacce duk mamakin halin mutane na rashin taimako ya cika ta,   Akwai hanyoyin neman kuɗi mana ba iyaka ma mu da muke cikin birnin maiduguri ," Tun kafin ta ƙarasa yakaka ta tari numfashin ta toh ai kolo bakya ganin mu a kulle muke cikin sansanin mu ba'a kuma fita sai da dalili mai karfi kamar idan kana saye da sayarwa koh kuwa ka nemi iznin zuwa ganin wani naka cikin gari ka ci sa'a an bar ka    Idan dai har kun tabbatar kuna son fita domin zuwa neman kuɗi cikin gari ni kuwa zan muku hanyar da koh kwanaki nawa zaku je kuyi ku dawo idan ma kuma zuwa zaku dunga yi kullum kuna dawowa duk zan taimaka muku , ku dai da farko yanzu kuyi tunanin sana'ar yi , idan kun fitan Cikin zumuɗi yagana tace toh ai ke kolo da kike fita cikin garin ke zaki fi mu sanin sana'o'in da zasu dace da mu kuma wanda zamu samu , ni dai ko ma meye zan yi , haka kuma nasan kawayena ma zasu yi ta furta hakan tana mai maida kallon ta ga yakaka wacce tayi shiru kamar ruwa ya cita , cikin ran ta wasi-wasin fitar su daga sansanin su take da fargabar abun da ka iya zuwa ya dawo a matsayin su na ɓaki da basu san ko'ina ba ,muryar kolo ta katse mata tunani Toh kun dai ga ana aikatau a gidajen mutanen gari ,"ana bara , ana aikatau a gidajen saida abinci idan baka tare da ƙazanta ,ana yin aikatau har a cikin kasuwanni , idan kana so tashi biya idan kuma kana so biyan wata yanzu haka nima ina wanke-wanke da shara gidan wata mata amma tashi biya muke , kullum naira ɗari biyu take biyana kuma na ci abinci nasha ruwan leda ga kaya kuma tana bani  , bata tsagaita ba ta cigaba da cewa tun da ku baku da naƙasa zaku iya yin aikatau ita kuma ƙanwar ku tayi bara a bakin kasuwa wallahi zaku yi mamakin kuɗin da zaku samu akalla ɗari bakwai zuwa dubu ɗaƴa a kullum banda kuma kwancen kaya da za'a dunga baku da sadakar ɗanyen kayan abinci , Cikin nazari yagana da yakaka suke kallon kallo yayin da falmata tayi jugum ta ƙurawa guri ɗaya idanu tana tunani ,"     *Toh mana bari mu ɗan huta koh* ?😁😍     *Mu bar su Yakaka/Falmata/Yagana su yi tunani cikin tsanaki*     #Comnents #Vote #Share #Fikrh [6/24, 9:59 AM] +234 701 013 7848: Fikrah writers association *MAFARI.......* ( _hargitsin rayuwa )_ *umm'muaz* 10 Shiri yakaka take sauri-sauri , tana yi tana taya falmata yin nata shirin , cikin mintocin da basu gaza goma ba har sun kammala , duk da dai kayan su na jikin su da suka cire suka sake mayarwa amma bisa ga dukkan alamu da su da kayan nasu sun ɗan samu tsafta domin sun ɗan yi haske , hakan kuwa bai rasa nasaba da wanka da wankin da suka samu damar yi tun a dare jiya bayan da suka tsaida shawarar fara fita neman na kansu cikin gari a ƙarƙashin jagorancin kolo da yagana , Kamar yadda kolo ta tsara musu shine su yakaka da yagana kowacce zata fita neman aikatau , yayin da falmata kuma zata zauna a bakin kasuwa tayi bara ," Da farko yakaka bata amince da yin barar falmatan ba , turjewa tayi sam tace sai dai falmata ta bita inda zata samu aikin ta zauna ta dunga jiran ta har zuwa lokacin da zata kammala ayukan sai  su koma tare , abun da duk ta samu tayi musu hidima tare , kuma abun da duk ta ci , ta bawa falmatan , Sai dai ga mamakin ta firr falmata taki ta amince da tsarin ta , ta tsaya kai da fata akan lalle ita ma sai ta nemi hanyar taimakawa kan su wanda kuma hanyar a yanzu ɗaya ce ita ce yin bara , idan har kuwa baza ta amince tayi bara ba toh sai dai tayi zaman ta kawai a cikin camp domin bata ga amfanin bin ta da zata yi kawai ta zauna ba . Ala tilas ta amince mata domin gudun bacin ran ta,  da kuma sanin cewa baza ta iya fita daga camp ɗin ta bar falmatan ba , toh ta bar ta a hannun wa ? Ga larurar da take tare da ita , amincewar ta shi ya zama dole sai dai bisa sharaɗin baza su nisanta da juna ba , dole a tsukin gurin da falmatan zata yi zaman barar ta anan ita ma zata nemi nata aikin .                                 _____ Yakaka , falmata ku fito mu tafi mana kar muyi rana , kolo ta riga ta gama magana da mai tsaron kofa            ,"yagana ke furta hakan dai-dai lokacin da take ƙarasowa bakin kofar ɗakin da su yakaka suke ,"         Gamu nan yagana mun gama shiri sai tafiya ,"                cewar falmata fuskar ta ɗauke da yalwatatciyar fara'a a karo na farko da yagana ta gan ta cikin farin ciki kwatankwacin wannan , wanda bata raba ɗaya biyu murnar zasu fara dasa harsashin cigaban su ne a karon farko cikin tsananin rayuwar da suka tsinci kansu ,"     Hannunwan su sarƙe da na juna suke sanya kafafun su domin barin cikin sansanin su da suka wanzu a cikin sa tun ranar da suka shigo birnin na maiduguri , yayin da sashi guda na zuciyoyin su ke cike da fata tare da burin zuwa su nemo na kan su ,gefe guda na zuciyoyin nasu kuma fargaba ne tare da taraddadin yadda fitar ta su zata kasance ,      Sansanin su a bakin babban titi yake dan haka basu sha wahala ba wurin samun motar bus da take jigilar mutane zuwa kowanne sashi na garin ,       Kasuwa monday market         Kolo ta furta bayan ta tsaida wata kwaraɓabɓiyar motar bus da take ɗauke da mutane jingim a cikin ta ,"           Shiga muje         Cewar conductor ( karen mota ) wanda ya wangale musu kofar motar ,      Ni ɗaya ce zan zauna akan kujera su akan inji zasu zauna ,"           cewar kolo dai-dai lokacin da take shigewa cikin motar domin yi wa kan ta matsugunni ,"           Wata zamiya kondoktan yayi tare da zabura ya babbake kofar motar ,"         Nai gamma waɗannan ƙattin ƴan matan har su uku ne zasu hau kan inji  kut ? ,"       Kayi hakuri dan Allah yayana ka taimaka mana wallahi naira ɗari daya ce jal da ni , kuma ni zan biya musu domin su da ka gan su nan koh sisi basu da shi mu ƴan gudun hijira ne , " cewar kolo cikin marairaicewa da karya wuya ,"       Kai ina bazai yiwu ba malama waɗannan sun yi girma da hawa kan inji a jere su uku rus ,          ya karasa zancen yana me jifan su yakaka da kallon banza wadanda suka yi tsilli tsilli a tsaye cike da taraddadin ganin samu da rashi ,sanin cewar idan aka ƙi ɗaukar su toh fa babu su babu tafiya dole su koma cikin sansanin su .       Tsalle konduktan yayi ya ɗale motar gami da bubbuga murfin tare da cewa ",Muje oga,"       Tsaya tsaya nima zan sauka tun da baza ka ɗauke mu tare da ƴan uwana ba ,"  Burki direban motar ya jaa lokaci guda ya juyo cikin hargagi yake tambayar me ya faru ne ?       Konducto yayi masa bayani ," sake tambaya yayi akwai sarari ne akan injin ,"      Akwai sarari oga sai dai sun yi girma sosai mutanen da ke kan sit zasu takura sosai ,"      Wani banzan kallo direban ya wurga masa da jajayen idon sa ,"    Ganin hakan ya sa da sauri konducton ya sauka gami da buɗe motar , yayi wa su yakaka alamun kira da hannun sa saboda har motar ta ɗan gifta ,"          Miƙo kuɗin ku        Cewar karen motar lokacin da direba ya daidaita motar sa akan titi    Da sauri kolo ta miƙa masa tsohuwar naira ɗarin da ta gama shan wahala a hannuwan jama'a               Azabar zafin inji da zafin ranar da motar ta ɗauka suka haɗu suka sa su yakaka , falmata da yagana haɗa gumi kirshiɓ suna ta ɗiga , yayin da suka kasa zama wuri ɗaya akan injin sai mutsu-mutsu suke suna jin zafin ƙunar da injin motar yake musu a ɗuwaiwai , uwa uba yadda suka takura suka cure guri guda kamar "kifayen gongon" gefe guda ga warin da konducton yake wanda ya buɗe hannayen sa ya tokare ɗaya hannun dai-dai fuskar falmata wari da tsamin hammatar sa na barazanar sanya su haraswa ,"      Bayan tsawon lokacin da bai kamata ace sun yi shi ba daga tsakanin sansanin su zuwa bakin kasuwar , amma a sakamakon rashin kyaun motar ,tsufan ta da kuma tsayawa a sauke fasinja a ɗau wasu a hanya ,ya sa suka kusan shafe mintuna arba'in a kan hanyar da bai fi suyi mintoci goma zuwa sha biyar ba , "        Cikin jigata suka sauko daga cikin motar , fuskar kowaccen su na nuna wahalar da ta sha a yayin tafiyar

Chapter 11 of 111