,"
Yawatawa da idanun su yakaka da yagana suke yi cikin mamakin ganin yawan jama'ar da suke ta hada-hadar su a wurin duk kuwa da cewa hantsi ne bai wuce karfe tara da rabi zuwa goma na safiya ba ,"
Toh ku zo mu tsallaka titi kun ga chan ita ce kasuwar monday market maiduguri ( ita ce babbar kasuwar da take ci a kullum cikin birnin na maiduguri )
kolo ke yi musu wannan bayanin .
Ba ƙaramin ɗauki ba daɗi aka yi cikin turƙa-turƙa kafin su yakaka suka iya tsallaka babban titin na Ahmadu bello da yake daura da kasuwar ta monday market ba ,"
BAYAN AWA ƊAYA
Duk wani zagaye sun gama shi amma basu yi dacen samun gurin da zasu yi aiki ba a zagayen har ma da ainahin cikin kasuwar , kama tun daga kan masu tuwo-tuwon da suke ciki da wajen kasuwar har zuwa kan goge-goge koh jiran shago , hasalima wurare da dama da suka je korar kare aka yi mu su ,"
Yagana , yakaka , kun dai ga yadda aiki ya gagara samuwa a gare ku a cikin kasuwa , hakan ya sa ya zama dole ku shiga cikin unguwanni ku kutsa koh gida-gida da wuraren sayar da abinci na cikin gari koh Allah zai sa ku dace , ni yanzu gaskiya rana ta riga ta ɗaga aƙalla yanzu sha ɗaya da rabi ta kusa kun ga na riga na makara zuwa gidan aiki na , duk da dai cewa daga nan zuwa cikin unguwar da nake aikin babu nisa amma yakamata ace tun tuni ina bakin aiki kamar yadda na saba , saboda haka ni zan tafi idan ya so anjima da yamma mu haɗu a tasha inda mota ta sauke mu ɗazu , amma kafin nan ita falmata yakamata ta samu wurin zama domin yin barar ta domin kuwa babu inda ya kai bakin kasuwa samun sadakha , dan haka mu matsa daga chan wurin gefen bankin chan ta tsaya ko ta zauna a wurin har zuwa lokacin da zaku dawo , ina mai tabbatar muku da zata samu kuɗaɗe sosai ,
Duk kalma guda da take fitowa daga bakin kolo dai-dai take da ƙaruwar luguden da zukatan su yagana ke yi , wannan fa shi ake kira " anyi gudun gara an tadda zago " toh su kuwa ina zasu fuskanta cikin wannan turmutsutsu da taron jama'ah ?
Ta ina zasu fara dilmiyar da kan su cikin gari alhalin basu da tabbacin zasu iya gane hanyar da zata dawo da su nan mahaɗar ta su , wanda a zahiri cikin zagayen awa ɗaya jal da kolo tayi da su a tsukin kasuwar , a halin yanzu koh tashar da mota ta sauke su baza su iya komawa ba saboda kan su ya riga ya juye , ina ga batun kutsawa cikin gari cikin unguwanni , ai wannan zancen ma bai taso ba ,"
Kusan a tare su ukun suka haɗa baki gurin fara magana ," amma sai yakaka da falmata suka saurara domin bawa yagana damar faɗin abun da ke nata bakin duba da cewa ta fisu kusanci da kolo ɗin ,"
Kolo mun gode sosai da dukkanin dawainiyar da kika yi mana amma a gaskiya daga ni har yakaka babu wacce zata iya tunkarar cikin garin da nufin neman aiki ba domin kome ba kuwa dan gudun bacewa mu rasa hanyar komawa a matsayin mu na baki ," jaan numfashi tayi lokaci daƴa tana mai sake marairaicewa , dan Allah kolo ki idasa taimakon da kika yi niyyar yi mana ki yadda mu biki zuwa unguwar da kike yin naki aikin idan ya so sai mu shiga gidajen cikin unguwar mu nemi aikin koh Allah zai sa mu dace ?
Ɗan jim kolo tayi cikin nazari a zahiri bata son su yakaka su bita su ga irin aikin da take yi sanin cewa ta boye musu gaskiyar aikin nata , amma ita sosai take tausayawa musu musamman yagana wacce take da wani boyayyen buri akan ta , "
Toh shikenan ku biyo ni amma da sharaɗi ," kamar yadda kuka ce kun fito neman aiki ne dan haka baku da wani zaɓi akan irin aikin da zaku yi ,"domin unguwar da nake aikina ta sha banban da sauran unguwanni ," nan ne gaba kaɗan tsallaken titin nan ta karashe zancen tana yi musu nuni da wata hanya da ta gangara kwari ta miƙe sosai daga gaban su ,"
Ke kuma ta juya ga falmata muje ki zauna akan dutsen chan ki ɓuɗe hannun ki ki fara bara , kar ki motsa koh nan da chan zuwa yamma zamu dawo mu same ki ,",
Cikin rashin kuzari yakaka take taku domin raka falmata wurin zaman ta inda gefen titi ne daf da bakin kwalta kuma ta baya jikin bangon kasuwa ne da yake kewaye da shagunan saide-saide, gefe da gefe duk masu saide-saide ne na kayayyaki iri daban-daban wasu sun yi kashi-kashi akan buhu da algarara wasu a wulbaro wasu akan tire ,wasu kuwa ƴan tebura ne da su ,yayin da gaba kaɗan kuma wani babban gini ne mai kama da ma'aikata ( banki ) ,"
Dai-dai gefen wani ɗan tsoho mai sayar da kayan gwari suka cewa falmata ta zauna kan wani ɗan dutse ,'
Cikin nutsuwar da take halittar ta ta laluba ta ɗosana duwawun ta ,",
Durkusawa yakaka tayi akan guwowin ta gami da kamo hannunwan falmatan tace ,"
Falmata dan Allah ki kula da kan ki kin ga inda muka ajiye ki ɗin nan ki zauna kar ki motsa koh nan da chan ,
"ɗaga kan ta tayi ta dubi sama taga akwai rangwamen hasken rana sakamakon manyan giza-gizan da suke yawo suna kare ranar ,
" idan kin ji kishirwa ga wannan",
ta kunce bakin zanen ta ta ciro wata tsohuwar naira goma wacce ita falmata bata san inda ta samu ba ,"
ki sayi ruwa da shi ki sha idan kuma Allah ya sa kin samu sadakha idan kin ji me tallar abun sayarwa ki sayi wani abu ki ci ,
sake damƙe hannun falmatan tayi tana me jinjina hannunwan su da suke haɗe da na juna ,
falmata kar ki je koh ina ki jira ni dan Allah , kuma ki kula min da kan ki ,"
Yakaka ni fa sauri nake da Allah ki taso mu tafi ,"
cewar kolo cikin gundura da doguwar maganar da yakakan take yi da ƙanwar ta ta , wanda ita da yagana ba jin abun da take faɗa suke ba sakamakon ƙasa da muryar ta da tayi ,ga kuma hayaniyar motoci da ta muryoyin jama'ah ,"
Yunƙurawa tayi ta mike tare da cewa '" yi hakuri kolo mu tafi ,
idanun ta akan fuskar falmatan wanda a zuwa yanzu ta kasa fahimtar a wanne yanayi zuciyar falmatan ke ciki ,"
Tayi taku biyu ta ji hannun falmatan ya sarƙe a cikin nata ,"
", Yakaka dan Allah kar ki ɗaɗe kuma ki lura da kyau da wurin da kuka ajiye ni kar ku manta wurin , sannan kuma kema ki kula da kan ki , Allah ya baku sa'a kije ki dawo ina jiran ki anan yakaka ,"
Daga haka ta zame hannun ta daga cikin hannun yakaka ta buɗe zazzaƙar muryar ta tare da ware hannuwan ta biyu ,ta fara rero kalmomin bara ,"
Alaro sadakah fisabilillah
Alaro sadakha fisabilillah
Gurbin fararen idanun ta cike taf da hawayen da suke sheƙi a cikin hasken ranar , zuciyar ta kuwa ta jima tana kwararar da hawayen maraici da wata irin kewa maɗaukakiya ,"
Juyawa yakaka tayi cikin sassarfa tana mai bin bayan su kolo waɗanda har sun riga sun soma tafiya ," lokaci guda tana mai share ambaliyar hawayen da suke shatata akan farar fuskar ta , "zuciyar ta kuwa wani irin raɗaɗi da zogi suke yi mata tana jin kamar baza ta iya tafiya ta bar ƙanwar ta anan ba , tana jin kamar idan ta bar ta wani abu zai taɓa ta , " tana jin kamar ta kasa bata kariyar da ta kamata ," sai dai sashi guda na zuciyar ta yana mai karfafa ta da cewa ta tafi ai ZATA DAWO TA SAME TA ,' kuma a yanzu wannan hanyar ce kaɗai mafitar su domin tallafawa kan su .," da haka suka tsallaka babban titin da ya raba su da sashin kasuwa ,"
Dai-dai zasu gangara gangaren (kwarin) unguwar da zasu neman aikin ta sake waiwayawa a karo na barkatai tana me sake kallon bigiren da ta ajiye ƙanwar ta ta , chan ta hango wata mata ta miƙa mata wani abu da take kyautata zaton sadakha ce aka fara bata ," nan take fuskar ta ta yalwatu da kyakyawan murmushi har haƙoran ta suna masu bayyana cikin ran ta tana me yin hamdala ,
,"lokaci guda ta sanya kafafun ta tare da tattare zanin ta suna masu sauka cikin kwarin unguwar da ake kiran ta da ,"BULABURIN", unguwar da tayi ƙaurin suna a birnin na maiduguri gurin tara lalattun mutane , kama tun daga kan ƴan shaye shaye , karuwai da ƴan daba ," .
Assalamu Alaikum ina miƙa sakon gaisuwa ta ga masoyan rubutuna a duk inda kuke , tare kuma da baku hakurin jinkirin cigaban labarin da ake samu wanda a zahiri ba a son raina bane, face hali irin na rayuwar ɗan adam wacce take tafe da cuta da lafiya ," duk tsawon lokutan da kuka ji ni shiru , shirun ya faru ne a sakamakon rashin lafiyar da nayi fama da ita , amma a halin yanzu Alhamdulillah da sauki .,
Nagode
#vote
#comments
#share
#fikrh[6/24, 9:59 AM] +234 701 013 7848: Fikrah writers association
*MAFARI........*
( _Hargitsin Rayuwa )_
*umm'muaz*
11
Fuskar ta ɗauke da murmushin da ya zarce zuwa dariyar da ta bayyana ƴan gajerun jerarrun haƙoran ta ,take shafa tare da sunsuna tarin kuɗaɗen da ta samu ta hanyar barar da ta shafe awanni fiye da uku tana zaune tana yi , wanda bata kai ga sanin yawan adadin kuɗaɗen ba ,"
Sake runtse kuɗaɗen tayi cikin tafukan hannayen ta ,lokaci guda kuma ta fara lalubar leɗar da ta saya awara taci ɗazu domin ta kulle kuɗaɗen nata a ciki ganin cewa kuɗaɗen sun taru a hannunta ,
zuciyar ta kuwa ƙwal kuma cike da farin ciki a rayuwar ta yau ne karo na farko da ta riƙe kuɗaɗen da suka kai haka yawa nata na kan ta , nan take taji ta sake gamsuwa tare da samun karfin gwaiwar cigaba da yin bara har sai yadda hali yayi , "
Gefe guda kuma tana Allah-Allah su yakaka su dawo ta nuna mata irin ɗinbin alherin da ta samo musu ,"
Soke kuɗin tayi a cikin zanen ta bayan ta ƙulle su a cikin leɗar , ɗan saurarawa tayi tana mai jin yadda rugugin hadari yake bada amo bisa ga dukkan alamu garin gangame yake da hadari ,duba da yadda ta ji rangwamen zafin rana da yake nuni da cewa hadari ya kare ranar ," ,
Ji tayi hankalin ta yaɗan soma tashi sanin cewa a sararin Allah take ba cikin rumfa ba ,ita kuma bata shiri da dukan ruwan sama mummunan zazzabi da ciwon kai gami da tari yake samar mata ,"
Ɗan matsawa tayi ta gurin da take jin muryar dattijon nan wanda tun da ta zauna a wurin take jin sa yana hada-hadar saye da sayarwar sa ,"
Baba dan Allah ince koh hadari ne sosai haka a garin naji sai cida garin yake ?
Ƙwarai kuwa ƴata hadari ne gashi nan ya shata bakikkirin a sama ," ya kamata ma kiyi haramar komawa gida ,'domin duk jama'a ma shirin tafiya suke ga la'asar ta riga ta gabato ,"
Tsugudi falmata tayi cikin fargaba tare da taraddadin rashin dawowar su yakaka har yanzu ,"
Tunanin ta ya katse ne lokacin da taji wata mummunar ƙara da tafi karfin a kira ta da rugugin hadari domin gabadaya sai da ta ɗimauce ,"lokaci guda ta miƙe a zabure gami da tsayuwa akan kafafun ta da take jin ƙasa na girgiza ,"
Waige waige ta fara yi lokacin da ta tsinkayo hayaniyar muryoyin mutane sun ƙaru tare da takun kafafun su da alama guje-guje aka fara ,"
Cikin tashin hankali ta sake matsawa wurin dattijon nan da take jin muryar sa sama-sama da alamun tashin hankali ,sai dai rashin jin isashiyar hausa da kuma yadda ta firgice ya sanya ta kasa tsintar koh da kalma guda daga cikin kalmomin da take ji a bakunan al'ummar wajen bare ta fahimta,"
Ba-Baba dan Allah meke faruwa ne ƙarar menene haka naji ?
Ƴata bom ne ya tashi yanzu yanzu a post-office , maza maza ki kama hanyar gida domin kuwa kasuwar ma yanzu za'a rufe ta sojoji zasu zo ,ai yau gari sai yadda hali yayi bom a post-office matattarar mutane ? Kai Allah dai ya kawo mana karshen wannan masifa ,"
Kalmar bom da ta sojoji ita kaɗai falmata ta fahimta cikin dogon jawabin da dattijon nan yake mata ," a take wasu hawayen da bata san lokacin da suka samar da kan su ba suka fara sintiri akan fuskarta ," dai-dai lokacin da taji an kai mata wata bangazar da tayi sanadiyar zubewar ta a ƙasa da bata raba ɗaya biyu ƙaton da ya bangajeta gudu yake yi domin ya samu isa ga mafakar sa kafin zuwan sojoji koh kuma tashin wani bom ɗin ,"
Ji tayi dattijon nan ya sanya hannu ya ɗago ta lokaci guda yana me fada akan rashin imani na wasu mutanen ta yadda har wannan garjejen ƙaton ya bangaje ƴar ƙanƙanuwar yarinya kuma miskiniya amma bai koh juyo ba ,"
Ƴata ina abokan tafiyar ki da suka ajiye ki anan suke ?? Koh kuma ina ne unguwar ku ? Kiyi maza fa ki samu ki bar wajejen kasuwar nan dan nan da mintoci ƙaɗan kowa zai watse ,"
Yakaka , yakaka , itace kawai kalmar da bakin falmata ya furta ba tare da ta jira jin ƙarshen zancen dattijon nan ba , lokaci guda kuma ta fara jefa kafafun ta ba tare da ta san inda take sanya kai ba koh kuwa inda ta nufa ," ita dai burin ta ta sadu da yayar ta ,"
AWANNI UKU BAYA
Tun da suka gangara gangaren unguwar yakaka da yagana suka ware idanun su sosai suna masu kallon tun daga kan tsarin gine-ginen unguwar har zuwa kan mutanen da suke cikin unguwar da mafi akasarin su kallo ɗaya za'a musu a fahimci ƙarancin tarbiyyar da take tare da su ,"
Unguwa ce irin ta yaku-bayi talakawa mafi yawan gine-ginen unguwar sun shiga ƙasa kana iya ganin kan ƙwanukan ,ƙananan gidaje da suke manne da juna ,waɗanda kallo ɗaya za'a musu a fahimci mutanen cikin su na rayuwar rashin wadata,"
Mafi akasarin matasan da suke yawo a unguwar irin ƴan shaye-shayen nan ne masu rabin kai a aske ga kuma uwa uba rangwamen tsafa da ta bayyana sarari a gare su ,
,"duk tashin muryoyin su irin na ƴan maye ne da take tafe da amon kalmar arziki ɗaya ashariya goma ,"
Yaran su ƙanana kuwa kaso tara cikin goma yawo suke kafafun su babu takalma ,dauɗa ta samu mahallin zama na dindindin a jikin su da suturun su ,"
Ga Ƴan mata birjik waɗanda mafi yawa hannayen su zuwa kawunan su ɗauke yake da robobi zuwa bokitaye da fantekun ,ababen ci na sayarwa ," sun sha kwalliyar gazal da jar hoda ,laɓɓan su na ƙyallin jan baki 24 awa ,",
Duk ba wannan yafi girgiza zuciyar yakaka ba asalima ita bata hango wani aibu koh naƙasu a tare da mutanen unguwar ba idan aka ɗauke ashariƴar da suke amfani da ita cikin maganganun su wanda hakan yake bakon abu a wurin ta ,sai dai duk da haka ta ɗauki hakan a matsayin wayewa irin ta ƴan birni duba da cewa ita a wurin ta wayayyun mutane ne .,
Abun da yafi takura yakaka da firgitata shine yawan karnuka tare da ƙyanwowin da take ganin giftawar su a cikin unguwar tamkar dai yadda akuyoƴi da tumakai suke yawo a garin su wanda hakan babban barazana ne a gare ta kasantuwar ta ma'abociyar tsoron karnai , yakaka tana ƙin kare yadda take ƙin mutuwar ta koma fiye da haka , dan tabbas da tasan zata haɗu da karnuka irin haka da ko daga cikin sansanin su baza ta fito ba bare har ta ɗauko kafa ta shigo wannan unguwar ,",
Ga bangaren yagana kuwa yanayin tsarin unguwar ne sam bai mata ba a zaton ta zata ga sun doshi unguwar hamshaƙan masu kuɗi ne ,"inda zata yi kallon birni sai take ganin su a wata ƙazamar unguwa wadda koh a garin su ba'a sanya ta cikin unguwannin arziki ba ,' duk sai ta ji tafiyar ta daina yi mata armashi .,
Sun ɗan yi tafiya mai nisa kafin su jiyo Kiɗan da suke ji sama-sama yana sake cika kunnuwan su a yayin da suke dosar wani wajen matattara jama'ah shi yasa suka maida hankulan su suna bin mutanen da suka fara cin karo da su a farfajiyar wajen da kallo ,"
Da farko rumfunan sayar da abinci ne birjik a wurin wanda aka kafa manya-manyan murhu aka ɗora manyan tukwane lamba talatin-arba'in an babbaka wuta a ƙarƙashin su da basa raba ɗaya biyu girki ake ,"
Daga gefe cikin wasu rumfunan kuma shimfiɗun tabarmai ne da suke cike da mutane a chakuɗe maza da mata , ba'a jin kome sai tashin muryoyin su da dararrakin su ,"
Daga gaban su nan ne wata babbar kofa take wanda kuma daga cikin sa wannan kiɗan kalangun ke tasowa ,"
Ɗaya daga cikin rumfunan sayar da abincin nan suka ga kolo ta nufa inda su ma basu yi wata-wata ba suka bi bayan ta zungui-zungui , daga bakin rumfar ta dakatar da su yayin da ita kuma ta shiga ciki inda suke jiyo tashin muryoyin wasu mata ,"
Kichibus kolo tayi da uwarɗakin ta ,wacce kallo guda za'a mata a ajiyeta a mizanin tatattun karuwan mcmc, duba da yanayin shigar ta na wata matsatsiyar doguwar rigar wani yadi da ya cire kowanne bangare na jikin ta kashi-kashi a sarari ,"uwa uba koɗaɗɗiyar fatar jikin ta da duk man sauya kalar fata ya maida ta dabbare-dabbare , sannan zaƙo-zaƙon faratan hannun ta da suka sha fenti ruwan ɗorawa zuwa gashin ɗokin da ta yaɓa a kan ta launin shanshanbale ,wanda bata samu koh da zarafin ɗaura masa ɗankwali ba ,"
Wata harara ta watsawa kolo da mitsi-mitsin idanun ta da suka sha koren fenti daga sama ," ta tauna cingam ya bada ƙarar bas-bas-tas ,"
Dan ubanki kolo yau sai yanzu kika ga damar zuwa ? Duba agogo karfe nawa yanzu ? Karfe sha biyu saura , toh bari kiji wallahi a kuɗin ki zan cire dan ni ba'a min iskancin banza idan kin gaji da aikin ne sai ki faɗa na maye gurbin ki da mai so ,"
Kiyi hakuri madam wallahi na tsaya taya ƴan uwa na neman wurin aiki ne kin gan su chan ma tare muka zo domin basu samu gurin yin aikin ba ma ," ta ƙarashe zancen tana mai nuno su yagana waɗanda duk abun da yake faruwa tsakanin kolo da uwarɗakin ta suna ji sarai daga inda suke .
Ɗan leƙawa madam ɗin tayi tayi wa su yakaka wani kallon sama zuwa ƙasa ,"
Ni dai na gaya miki zan cire kuɗin awa biyun da kika yi lattin su domin ni bana asara , " ki wuce ki kama aikin ki ," ku kuma "ta sake ɗaga murya yadda su yakaka zasu iya jiyo ta
Sai ku shiga daga ciki domin kun yi sa'a jiya-jiya sally fara ,ta bada cigiyar a ƙaro mata ƴan aiki biyu a madafar ta domin cikin tsoffin da da suke mata aikin ɗaya shekaranjiya ta mutu,"
Turus yagana da yakaka suka yi duk da cewa sun fahimci abun da ta sanar da su toh amma inane cikin ? Kuma wacece" sally fara " ?
Ganin yadda suka yi wiƙi-wiƙi suna kallon ta ya sa ta fahimci basu gane nufin ta ba ," ƙas-ƙas ta sake yi da cingam sannan tayi wani turanci ",
Idiyot buladiful marafoka waɗannan ajawos ɗin koh fahimtata ma basa yi ," ke kolo koh kuma ma ke zauna kiyi aikin ki ɗanliti zo tafi da waɗannan garorin ciki wajen sally fara kace ga ƴan aikin cikin madafa an samu ," kai ku bishi dallah kun tsaya sai wani kif-kifta idanu kuke yi kamar an shaƙe akuya a mayanka idiyot buladiful
Sum-sum su yagana suka bi bayan mutumin da aka ƙira da ɗanliti wanda tashin farko idan an hango shi yana tafe za'a zaci wata zarkaɗeɗiyar budurwa ce sakamakon shigar mata da yayi da yadda yake karairaya da lanƙwasa kamar tarwaɗa a cikin ruwa ,"uwa uba kwalliyar da ya rangaɗawa fuskar sa har da yari da ɗan kunne ,"
Suna shiga cikin babban harabar dodon kunnuwan su ya fara tsalle a sakamakon kiɗan gurmi da kalangu da suke tashi ," a babbar harabar da tafi kama da wata ƙaramar makaranta ," mata ne da maza waɗanda kallo ɗaya za'a musu asan mutanen banza ne suke ta kai kawo ,"
Wata ƴar hanya ɗanliti ya bulla da su sai ga su sun bullo a gaban wani waje mai kama da shagon cin abinci ga irin fararen kujeru da teburan su nan birjik a wajen ta tsakanin kujerun da duk babu kowa akai suka wuce suka fito wani babban fili wanda suka taras da wasu manyan murhu da Manyan yankakkun durum bisan su wasu mata na koƙarin haɗa wuta ,"
Wani wari da tsami kamar na ruɓaɓɓen abinci shi ya fara dukan hancin su kafin idanun su yayi tozali da wasu yamusassun mata ƙomaɗaɗɗu suna ta faman wanke jiƙaƙiyar ruɓaɓɓiyar dawa suna subda ruwan yana kwarara zuwa wata katuwar magudanar ruwa ,"
Larki , hema ,duduwa ina madam sally take ? Inji danliti ,"
Koh kafin su amsa masa sai ga wata koɗaɗɗiyar mace da take tsakanin shekaru arba'in da biyar zuwa hamsin ta fito daga wani lungu hannun ta riƙe da wani ƙaton luɗayin kunu da ya kai girman a haɗa kawunan yakaka da yagana ,"
Kai liti yaya anka yi ne eh ? Waɗanan ƙuya-ƙuyan kuma daga ina ?
Daman madam jumai ce tace a kawo miki ƴan aikin ga su nan su biyu an samu ," ya ƙarashe zancen sa yana farfari da ido tare da yarfe hannu ,"
Ta ƙundumo wata ashariya ta makawa madam jumai ," kafin ta ce
Waɗannan ƴan shilan ne zasu min aikin ciki ? Waɗannan ne zasu tuƙa min DURUM ƊIN BURKUTU ? Tirƙashi waɗannan ai basu wuce suna bayan uwar su tana tatsa musu nono suna sha ba ?
Wata dariya da ɗaya daga cikin matan da suke aikin wankin dawar nan tayi shi ya katse banbamin masifar da sally fara", take yi ,"
Kin ji madam sally da wani zance ai da rashin tayi akan bar arha da kuma rashin ƙira karen bebe ya bata , ban da abun ki ai gwada su zaki yi ki ga koh zasu iya ," bakya ganin kamar ɗaukar irin su ma yafi riba , zaki mori kuruciyar su da kyau kafin abar ta fara aikin ta , zasu daɗe suna yi miki bauta kina juya su sai yadda kika yi da su ? Ai madam kar ki bari wannan damar ta wuce ki ," ta ƙarashe zancen tana sakin wata sakaryar dariya lokaci guda kuma tana chafe amshin wakar ƙidan kalangun da yake tar-tar kamar a gaban su mai kalangun yake kaɗa gangar
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Chapter 110
Chapter 111
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 111