Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
zuciyar ta ke ciki , Miƙewar shima yayi ya ɗan wara hannu kafin ya nuna mata nasa jikin da yake jiƙe shima , yace " ku ji ta kamar ba ke kika ruɗani ni ba kika sa na jiƙa jikina , raguwa kawai kin sa yanzu dole na sauya kaya . Kewaye ta yayi ya fita kai tsaye wardrobe ya nufa ya zaro wata jallabiyar ya tuɓe ta jikin sa yana warware ɗayar Yakaka da ta matse ruwan jikin kayan ta ta murɗo ƙofar a hankali ta fito , Da fitowar ta da hango shi ba riga da komawar ta cikin banɗakin ta rufo ƙofar da ƙarfi duk cikin abunda yake ƙasa da minti guda ta yi su , Doctor Hamza da duk abunda tayi akan idanun sa , har A'uzubillah da tace kafin komawar ta cikin banɗakin duk ya ji ta , Ɗan wani guntun murmushi yayi lokacin da wani tunani ya gifta masa nan take , rigar da yayi niyyar sawa ya ajiye a gefen gadon , a nutse ya nufi ƙofar banɗakin , ba tare da ya taɓa ƙofar ba yace , " ki fito ki tafi kar a gaji da jiran ki . Daga ciki ta ce " to ka gama shiryawa ko ? Dan Allah kayi haƙuri ɗazun ban san kana shiryawa bane , Ɗan mitsitsin murmushi ya kuma yi yana cije leɓensa na ƙasa a taƙaice yace " eh na shirya ki fito . Kan ta a ƙasa ta fito , a ɗan sace ta ƙyallo sa ,ta gan shi yadda yake a ɗazu da sauri sake juyawa sai dai kafin tayi wani yunƙuri ya naɗo ta ta cikin jiƙaƙƙen Hijabin ta ya haɗa ta da jikin sa , A ruɗe Yakaka ta fara ƙoƙarin ƙwacewa , bakin ta ya gaza furta ko kalma guda , matsera kawai take nema , " Meye kike haka , kamar wacce bata saba ganin Maza a tuɓe ba ? Kar ki min kinibibin ku na mata . Doctor Hamza yace haka laɓɓansa ɗauke da murmushin da yafi kama da na mugunta , cikin zuciyar sa yana sake haƙaƙewa da abunda yayi niyya , ya juyo da ita da ƙarfi ya ɗago fuskar ta da idanun ta ke runtse , hasken da ya haske fuskar shi ya bashi damar ganin hawayen da suka jiƙa mata fuskar ta , Shagala yayi da kallon kowanne ɗigo na tudu da ƙwarmin da yake fuskar ta , kallo yake mata irin wanda bai taɓa yi mata irin sa ba , a idanun sa kome na fuskar ta tsararre ne da ya dace ƙwarai da muhallin da Ubangiji ya ajiye mata shi . Zuciyar sa take buɗuwa tare da tashin tsikar jikin sa, bai san lokacin da ya haɗe tazarar da bata wuce tudun yatsa guda da yake tsakanin fuskokin su ba , ya haɗe fuskokin su waje guda , tare da ratsa hannuwan sa ya kewaye ta da su sosai , Da wani irin yanayin da ya zarce yadda yake da nufin yi , ya shiga yin abubuwan da zuciyar sa ta raɗa masa da ya yi a matsayin gwada Yakaka ya ga ko kalaman Suleiman gaske ne Yakakar kamilallar mace ce , tsautsayi tare da kaddarar rayuwa ce suka faɗa mata ? Sai ga shi ya gaza tantance Yakaka yake son gwadawa ko kuwa martabar sa ta ɗa Namiji yake aunawa ? Domin kuwa a tsakanin lokacin jin sa yake kamar wannan ne lokaci na farko da gangar jikin sa ya fara raɓar na wata ɗiya Mace . Yakaka da ake yiwa gwaji ita ta yunƙura ba tare da tayi amfani da ƙarfin kirki ba , ta zare jikin ta daga na shi , bata tsaya ba kamar yadda bata yadda ta bari idanun su sun haɗu ba ta taka da gudun gaske ta fice daga ɗakin da sashin nasa ma baki ɗaya , Bata tsaya daga gudun da take yi ba sai da ta tabbatar ta bada tazara mai ɗan yawa daga sashin sa . Zama tayi akan wani ɗan tudu tana mayar da numfashi harabar wajen babu mutane alama dake nuna an riga an tafi Dinner an bar ta . Kalaman Doctor Hamza ta tuno ," me yake nufin da cewa ta saba ganin maza a tuɓe ? Kenan nufin sa ita wata ƙasurgumar karuwa ce da ta saba cuɗanya da Maza , shi yasa ya mata abunda ya yi mata yanzu . Hawayen ɓakin ciki ya zubo mata , tayaya zata yi rayuwa da mijin da yake zargin ta irin wannan mummunan zargin ? Da jaan ƙafa ta nufi cikin gida , kai tsaye ta zarce ɗakin su inda ta tarar da Falmata ita ɗaya ƙwal tana kwance lamo akan gado Bata ce mata ƙala ba kamar yadda ita ma Falmatan bata nuna alamun ta san da shigowar ta ba , ta cire jiƙaƙƙun kayan jikin ta sauya da wasu , a hankali ta zo bakin gadon ta zauna , ta ɗan dubi Falmata da jikinta yake bata ba bacci take ba ƙoƙarin haɗiye damuwar ta take lokacin da tace , " Falmata baki tafi wajen Dinner bane ? Ba tare da ta motsa ba muryar ta can ciki tace " Ban tafi ba Yakaka Amnee tace na zauna nima tunda ke ma Yaya Dakta ya hana ki tafiya , kuma ma bana jin daɗin jikina bayana ciwo yake min . Shiru su dukkanin su biyun suka sake yi , zuciyar kowaccen su na sake ƙuntata da damuwar dake cin ta a rai , can ta tsinkayi muryar Falmata tace , "Yakaka yau kwanan mu ishirin da ɗaya da dawowa daga Niger ko ? Ɗan waigowa Yakakar tayi ta dube ta , ba tare da ta bata amsa ba tausayin ta ta ji ya kama ta , babu shakka tasan damuwar Falmata ba zata wuce akan Youssouf ba da shima yake gwada nashi walaƙanci a zaton ta ta hanyar yin shaƙulatin ɓangaro da ƙanwar ta . Washegari duk baƙi na nesa suka fara watsewa ciki har da Malama maryam da duk wasu dangi na nesa suka yi tafiyar su bayan Amnee ta cika su da kayan biki fal . Zuwa yammaci gidan ya rage sai su isu 'ya'ya da dangin Amnee , lokacin ne kuma Baa ya aika aka ƙira masa Doctor Hamza , bayan sun gaisa nasiha ya shiga yi masa mai ratsa jiki tare da tarin tunasarwa akan nawin da ya ƙaru akan sa , da kuma wuyar da yin Adalci yake da shi wanda kuma dole ne ya tsayar da shi a tsakanin matansa muddin yana son dacewa da samun Rahamar Ubangiji . Bayan ya gama masa nasiha da hannu ya masa nuni da saitin akwatuna biyu da adadin su yake kai ɗaya kawai launi da sumfurin su ne ya shabanba , kowanne guda takwas , ya ɗora da cewa " Wannan lefen Matan ka ne ɗayar ka kaiwa Safiya da hannun ka , ɗayan kuma na Amina ne , kamar yadda muka yi da kai nan da ƙasa da watanni biyu nake so ka samarwa da matar ka wajen zama a kusa da kai , idan ma kuma wajen zaman ya samu a yau ko gobe ne ka dawo ka ɗauke ta ku tafi abun ku Allah ya bada zaman lafiya . Godiya Doctor Hamza ya dunga yi ƙaunar Mahaifinsa na daɗa ratsa shi tare da ƙarin ganin ƙima da darajar sa , har ya miƙe zai tafi Baa ya sake dakatar da shi wata ɓakar leda da take nannɗe ya miƙa masa "wannan kuma wasu kuɗaɗe ne da aka bani na baka a matsayin gudumawa , ka ƙara wajen kula da gida , Da sauri Doctor Hamza ya noƙe hannun sa ," Baa ka bar su ayi amfani da su anan , ni ina da kuɗin da zasu isa nayi kome da su Nagode Baa nagode . Da murmushi a fuskar sa yace" karɓi mana ai ni na baka . Ƙarfe biyun rana Doctor Hamza yayi Sallama da iyayen sa zai koma Abuja a yau ɗin saboda gobe yana da tarin aiyuka a office da bashi da damar ɗaukar musu uzirin jinkirta yin su . Dangin Amnee ma ya musu Sallama bayan ya bada kuɗaɗe masu yawa da yace ayi musu sayayyar duk abunda suke so kafin tafiyar su , sannan ya tsawaita godiyar sa a gare shi . Da Khaalty Rahima ma sallamar su ta musamman ce da suka keɓe suna yi ta inda ita ma ta ɗora masa 'yar nasihar ta a ƙarshe ta ba shi shawara kan ya lallashi Safiya sosai kar ya bari ƙarin auren da yayi ya ɓata zamantakewar su . Ƙannen sa mata ma duk Sallamar yayi da su har da Rahima amarya da ba'a riga an miƙa ta gidan mijin ta ba saboda iyayen sa ba 'yan nan bane 'yan ƙasar katsina ne , kuma a halin yanzu duk suma shirye-shiryen komawar su suke can ƙasar America inda suke rayuwar su a can , nan da ƙasa da sati biyu zasu tafi tare duk har da Rahima . Lokacin da ya gama Sallama da kowa da ya dace , ciki har da Falmata, sai ya shiga ɗan jefa ido waje-waje ya gagara tashi ya tafi , sai daɗa jaan hirar su yake shi da ƙannen sa . Hajja wacce ita ma tun a waje da ita ya fara cin karo tana tattara harabar gidan suka gaisa har ma ya mata sallamar tafiyar sa ta jero masa addu'o'in da yake jin daɗin irin su , Ita ce ta shiga tana ganin sa tace ," Babban likita har yanzu baka tafi ba ? Kai kuwa na ga baka saba tafiyar dare ba garin Abuja ai ba kusa ba , dan ma dai ku manya ne . " yanzu zan tafi Hajja , yace yana ƙoƙarin miƙewa , Hajja ta shige ɗakin ta tana cewa " Allah ya tsare hanya Babban likita . Tana shiga ɗakin tayi turus ganin Yakaka kwance akan katifar ta tana buga game da wayar Rahima , Salatin da Hajja ta ɗauka sai da ta dire shi da tafa hannuwa sannan ta ɗora da cewa " ni hauwa'u me zan ji me zan gani ? 'yar nan kan ki ɗaya ? Yakaka ta ɗago kai tana kallon Hajja , " me nayi Hajja ko dan na hau 'yar katifar ki ? to bari na tashi , ta ce tana miƙewa ta sauƙa daga katifar ,fatan ta shine Hajja tayi shiru kar a jiyo muryar ta a san tana nan . Hajja ta ɗora da cewa " tambayar ki nake kan ki ɗaya ? Yanzu ace Mijinki na can shirin ɗaukar doguwar hanya ke kina nan kina latse-latsen wofi ? Bawan Allah shi yasa mana ya gagara tafiya ashe ke ce baki masa abunda ya dace ba wanda zai ƙara masa kuzari da nishaɗin tafiya , tashi nace sakaryar mata , tashi ki fice min a ɗaki , ki fita ga mijinki can yana jiran ki kuyi sallama . Hafsa da zainab da duk abunda Hajja ke cewa daga ɗaki suna jin ta sarai saboda sama-sama take maganar sai suka haɗa ido kafin su duka ukun su kwashe da dariya , Falmata ma sai da ta ɗan dara , a ran ta tana aiyana wannan kaɗan ne daga halin Hajja , yadda aka san bata da wani aiki sai na faɗin yadda mace za ta farantawa miji Ho Hajja , ya dace a bawa Hajja shugabantar wata ƙungiya ta faɗakar da mata kan yadda ake tafiyar da Miji . Hafsa ita ta rage dariyar ganin yayan su na tsaye yana kallon su , ita ma sai ta ɗan ɗaga murya lokacin da take miƙewa tsaye tace , "Ƙanwata Amarya ki fito kuyi sallama big bro zai tafi idan kuma ma mu kike jin kunya , kun ga ku zo mu bar wajen tace da sauran 'yan uwan ta , nan take suka miƙe suka yi ɗaki suna ƴar dariya tare da sake yiwa yayan su fatan Allah kiyaye hanya , Doctor Hamza da yake tsaye hannun sa a zube cikin Aljihun rigar rigar jumfa jikin sa , ya ɗan gyaɗa musu kai da murmushi a fuskar sa , shi ɗaya ne ƙwal ya rage a falon . Ganin sa ya mayar kan ƙofar ɗakin Hajja lokacin da Yakaka ta buɗo ƙofar ta fito kan ta a ƙasa fuskar ta kadaran-kadahan , ɗan matsawa kaɗan tayi ta bayan kujerar falon ta ɗan durkusa , " ina yini yaya dakta , Bata jira ya amsa ba ta ƙara da cewa " Allah ya kiyaye hanya , Bata yarda ta dubi sashin da yake ba bare ta san cewa ya matso kusan ta sai da ta miƙe tana shirin wucewa ta shige ɗakin su da yake kusa da ita , sai kawai ta ji ya riƙo hannun ta , A hankali ya jawo ta ya kusan haɗe jikin su , hannuwan sa yasa ya kewaye kunkumin ta , yana kallon fuskar ta da taƙi yadda ta ɗago kai , muryar sa ƙasa-ƙasa yace " haka ake yin sallama ? Babu addu'a ? Baki ji Hajja tace ki min abunda zai bani kuzari bane ? Da sauri ta ɗago kai , signal ya mata da duk girar idanunsa biyu , yana 'yar dariya da fararen haƙoran sa da suke da kyau sosai akan fuskar sa mai rangwamen haske . Ɗauke kai Yakaka tayi gefe can cikin ranta tana mamakin meyasa ta hango kamar sauyin mu'amala a tare da shi daga jiya zuwa yau ? muryar ta cikin sanyin tace " ai nace Allah ya kiyaye hanya na yi addu'a , Hannun yasa ya sake juyo da fuskar ta saitin sa , ya zarce da sanya ɗan yatsan sa ya shafa saman idon ta , da yasa Yakaka ta lumshe idanun ta da sauri , " Ya idanun ki sun wuce ko ? Basu sake damun ki ba ko ? Ya tambaye ta da ragwan sauti , gyaɗa kan ta tayi tana ƙoƙarin kautar da fuskar ta , amma ya ƙi bata damar haka sai ma hannuwan sa duk biyu da yasa ya tallafi fuskar ta yana shafa kumatun ta masu taushi yace ," to ina saurarar ki ki min Duas kuma ki min abunda Hajja tace ki min , ko bakya so na samu kuzarin tuƙin ne ? Sallamar wata baƙuwa ya sa Yakaka ta fisge jikin ta da ƙarfi da daman baki ɗaya a takure take damar gudu take ta son samu , Sai dai bai bata damar gudun ba ya riƙe hannun ta lokacin da suke gaisawa da matar ya san ta ɗaya daga cikin mutanen Amnee ce , ta zauna akan kujera. " Ba za ki min Duas ɗin ? ba yace yana jaan hannun Yakaka su fice daga falon , babu yadda ta iya ta bi shi sai dai suna fitowa suka hango Amnee na tahowa daga sashin Baa , " Yaa Doctor Allah ya kiyaye hanya ya kai ka lafiya , ya kare ka , ta harhaɗo kalmomin cikin sauri tana ƙoƙarin kwace hannun ta daga cikin nasa , kafin ƙarasowar Amnee ya sake ta da sauri ta taka tana komawa ciki , da murmushi ya bi bayan ta da kallo wani irin nishaɗi ne mai daɗi yake huɗa shi . Ƙarfe uku ya ɗau hanyar Abuja tare da sofiya wacce ya biya gidan su ya ɗauke ta dole bayan ya mata jaan ido tare da barazanar barin ta ta cigaba da zama a gidan su na wasu kwanaki da take son yi dai-dai yake da rabuwar su baki ɗaya , jin haka ba shiri ta tattaro ƴan kayan ta ta bi shi, ba tare da ta kula Momy kori sun yi wata sallamar kirki ba saboda haushin ta da momy kori take ji . ASSALAM ALAIKUM MASU KARATU DA FATAN KUNA LAFIYA ? INA GODIYA DA YADDA DAI HAR KULLUM KUKE HAƘURI DA NI . INSHA ALLAH SHAFI NA GABA SHINE ƘARSHEN LITTAFIN MHR DA ZAI BIYO BAYA NAN BA DA JIMAWA BA. NAGODE [1/17, 9:40 PM] +234 706 503 6187: MAFARI ( Hargitsin Rayuwa) Umm'muaz 49 MARADI-NIGER Kwanakin da suka biyo bayan bayyanuwar mummunan aikin da Gimbiya maimounatou ta aikatawa Biyamuradi Youssouf , tare da sa hannun Mammadou da Hajiya Mama , Masarautar maraɗi ta kasance cikin alhini mai tarin yawa , kusan kullum aka yi zaman fada da Waziri ne ke jagoranta ba'a da wani batu da ya wuce na sake tattaunawa kan wannan mummunan lamari haɗi da yiwa Biyamuradi Addu'ar samun lafiya tare da fatan dawowar Maimartaba . Da har yau da suke cika kwanaki ishirin da ɗaya basu baro india ba , Amma ana saka ran dawowar tasu a yau ko gobe saboda saƙon yiwuwar dawowar tasu ya iso musu . Akwai labari daga majiya mai tushe cewar gimbiya Siyama tare da ƙanin Biyamuradi Youssouf , 'Bilal wanda shine mai binsa a haihuwa sun fara shirin tafiya India domin cigaba da jinyar sa da har kawo yau babu wanda yasan takamaimai a halin da lafiyar Youssouf ɗin ke ciki . Ta ɓangaren Hajiya Mama kuwa duk yadda ta kai ga sanyawa idanun ta toka ta mustsiƙe ta cigaba da yin harkokin ta yadda ta saba , amma ta gagara domin yadda labarin sa hannunta da na ɗan ta wajen yunƙurin kisan da Matar Biyamuradi tayi masa , ya bazu ba a bakin bayu da hadiman cikin masarautar Maradi kaɗai ba har jama'ar gari da na wasu jahohin labari ya kai musu . Ake kuma kucin-cina labarin tare da sake liƙa masa baƙaƙen sassa ana sake munana sa ba ƙaramin tasiri hakan yayi wajen kassara mata duk wani karsashi haɗi da ɗagawar da take tinƙaho da shi na kasancewar ta matar Sarki . Dan haka gaba ɗaya sai take neman zama mujiya , tsarguwa take da irin kallon da bayun gidan suke mata , gefe guda ga dumuwowi birjik da suka mata ƙawanya , wanda bata saba shiga makamantan su ba , mafi girman su halin da ɗan ta tilo namiji yake ciki wanda yake tamkar ga ƙoshi ga kwana yunwa a wajen ta , domin kuwa tasan muddin Youssouf ya rasa ransa, cikin hakan akwai yiwuwar shima Mammadou ayi masa huƙunci mai tsauri da ka iya kawo ƙarshen shima tasa rayuwar . Ga Maimartaba da bata san matsayin ta takamaimai a wajen sa ba , bayan tonon sililin da Maimounatou tayi mata a gaban sa , gefe guda kuma ga Mairamar sarki da take autar ta sannan mafi soyuwa a wajenta cikin 'ya'ya da tun bayan faruwar wannan lamarin da ta samu labarin kome bayan kuka bata wani taɓuka abun kirki , Rufe kanta take a ɗakin ta da yake sashin uwar-riƙon ta , ( Hajiya Umma ) ta ci kuka ,domin lamarin ya mata tsauri wajen ɗauka duka biyu a lokaci guda , dan kuwa bayan kasantuwar Youssouf yayan ta mafi kusanci da yawan ƙauna a tsakanin su fiye da duk sauran 'yan uwan ta , ta shaƙu da shi tunda ta buɗi ido ta ga kanta riƙe a hannuwan sa , shiga hatsarin rasa shi ba abune mai sauƙi a wajen ta ba . Damuwar ta tana sake hauhawa da hango rugujewar zancen auren ta , tare da ma guntilewar alaƙar su ita da masoyinta da suka ɗibi tsawon shekaru uku suna soyayya wanda yake yaya ne ga gimbiya Maimounatou , uwa ɗaya uba ɗaya gaf ma ake da yanke ranar auren su cikin watannin gaba kaɗan a sha biki , sai ga shi wannan mummunan lamarin ya shata layi a tsakanin su , domin kuwa ko ba'a sanar da ita ba ta san makomar soyayyar su ita da Khaalifa , sannan tun kafin a hana ta ita ya kamata ta fara zare soyayyar sa daga ran ta , bayan abunda ƙanwar sa ta aikata ga Biyamuradi ai babu wani sauran alaƙa mai girma da zai sake shiga tsakanin masarautun nasu biyu . Ba tun yau ba ta riga ta san wasu daga cikin munanan halayen Mahaifiyar su da ita koyaushe huɗubar ta tare da yunƙurin ta bai wuce na ganin ta raba kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin ta da uwar-goyon ta tare da sauran ƴan uwan ta da suka haɗa uba ɗaya ba , da ita kuma ko kusa bata ganin aibun su , sannan duk wasu laifuka nasu da hajiya Mama ke faɗin sun aikata ko suna kan aikatawa , ita bata kai ga kama su da ko guda ba dan haka koyaushe take biris da huɗubar ta , tare da toshe kunnuwan ta , ƙaunar ƴan uwanta a jinin ta yake tana ƙaunar su kwatankwacin ƙauna tare da zallar kulawa da su ma suke nuna mata a matsayin ta na ƙaramar ƙanwar su , ga hajiya Umma kuwa ba zata ce kome ba da ya wuce fatan alheri tare da godiya ,riƙo ta mata na haƙiƙa ba irin riƙon ƴar kishiya ba , dan haka take jinta basu da wata maraba da Hajiya Mama , sau dayawa ma tafi kusanci da Hajiya Umma akan ita Hajiya Mama ,( goyo guba ) Amma ace sanadin son zuciya irin na Hajiya Mama duk ta rusa mata farin-cikin ta a lokaci guda ? Gani take kamar Hajiya Umma da sauran ƴan uwan ta duk zasu tsane ta akan laifin Mahaifiyar ta da ɗan uwanta , a tsakanin hakan take yawaita tambayar kanta anya kuwa tayi sa'ar uwa ??? An cigaba da tsare Gimbiya Maimounatou tare da Mammadou a Niamey , saboda rashin sanin halin da Youssoufa ke ciki ya hana a tura su ga kotu , kawo yanzu kuwa Mammadou iyakar nadama ya yita , ko abincin da ake ɗan kawo masa , baya iya ci duk ya lalace yayi duhu , bai taɓa zaton akwai wani lokaci da zai zo yayi danasanin zazzafar ƙiyayyar da yake yiwa ɗan uwan sa ba irin wannan lokacin da ya sarƙe cikin sharrin Gimbiya Maimounatou da ta tsaya kai da fata kan shi ya kawo mata gubar da ta ciyar da Youssouf da a zahiri ba gaskiya bane ba shi ya kawo mata ba ,ba shi kuma da wata masaniya akan haƙiƙanin me ya faru ga Youssouf a wannan daren , iyakar abunda ya sani shine yaje gidan Youssouf mintoci kaɗan bayan ƙiran sa da tayi saboda kusancin da yake tsakanin gidajen nasu biyu da wuri ya isa , ƙarƙashin jagorancin gnala da ta tare shi tun a babbar ƙofar gidan ya cimma har falon da Youssouf ke yashe a ƙasa cikin halin fitar hayyaci , a lokacin shi da kansa ya shiga ruɗani ganin halin da ɗan uwansa ke ciki , a ɗimauce ya shiga tambayar gimbiya Maimounatou " Ya mutu ne ? Da gaske Youssoufa ya cimma kushewa tai ? Bai gama tantance da abunda ke faruwa ba lokacin da suka tsinkayo jiniyar 'yan sanda , Kallon-kallo aka yi tsakanin su ukun , da ruɗani ya bayyana a fuskokin su sannan da wani irin sauti Gimbiya Maimounatou tace , " Mammadou ka shigo da ha'inci cikin lamarin mu amma kayi kuskure ka kuma yi shuka a idanun maƙwarwa , muddin kuwa baka yi wani yunƙuri ba tarkon da kayi na iy afkawa har da kai da makusantan ka , Cikin ruɗewa yace , "ki bar surutan banza ki faɗi wanne tanadi kika yi kafin ki aikata wannan aikin domin nayi gaugawar shafe girman laifin ki kafin lokaci ya ƙure miki , ko kin manta Yarima ɗiyan sarki kin ka kashe ? Kafin yin wani yunƙuri mai girma jami'an tsaron da bai kai ga tantance kakin soji ne a jikin su ko kuwa na 'yan sanda ba , suka dunga tururuwar shigowa falon kafin ya farga sun cika falon , bai shaida fuskar ko ɗayan su ba , sai fa Tafeeda da shi kuma tun shigowar sa ya rufu ga Youssoufa bakin sa ɗauke da sallalami gami da addu'o'i . Hanjin cikin sa ya kaɗa lokacin da ya lura jami'an tsaron wajen riƙe suke da bindigogin su da suke ɗane a saitin su shi da gimbiya Maimounatou , tsoro mai

Chapter 90 of 111