ga kamata yayi a ce ki rabar da ita ga mabaratan da suke bakin masallacin juma'ar unguwar nan kin ji ko ?
To ummi tace tana saɓar taɓaryar ta fara daka ,
Lubna wacce take zaune a gefe kusa da ita kan ƴar darduma tana yankar ƙumba , ta ɗago kan ta fuskar ta da murmushi ta sanya hannu cikin faffaɗan kwanon silver da aka ajiye guntun dafaffiyar furar da ba'a kai ga daka ta ba , ta gutsuro wata ƙatuwa ta sake jefawa cikin turmin da yakaka ke daka ,
Yauwa ƴar ummi yi maza ki daka, na ɗebo madara na fara damu ni ce ta farkon sanya Albarka a result ɗin nan kin sani ko ?
Ummi kina ganin ta fa ? Tana ƙara min wata bayan na kusa gama dakan
Lubna maza ajiye nails clipper nan ki karɓi dakan nan ki taya ta ,
Ta furta hakan tana gyara zama gilashin idanun tana cigaba da karatun ta .
Ummiii , dan Allah ni lokacin da nayi nawa dakan futar gama makarantar ta taya ni Haba ummi dan Allah,
Wallahi na taya ki kin manta ranar ....
Yanzu aikin samun ladan kuke yiwa haka ?
To shikenan duk ku bari ni zan zo na ƙarba nayi tunda da alamu ku lada yayi muku yawan da ya sa har kuka fara gudun sa ,
Da sauri lubna ta zaburo tana ƙoƙarin karɓe taɓaryar hannun yakaka ita kuma yakakar ta riƙe gam ta hana ta ,
Dan Allah ki bar ni na taya ki kin ji sahiba ta.
Tare da marairaice murya
Naƙi ɗin , nima zan daka kaya na duk na mulmula na ɗau abuna a kai naje na rabar , kin ji sahiba ta .
Wayar lubna da ta ɗau kiɗa ita ta raba musu gardama
Cikin sauri lubna ta ɗau wayar ta ta yi hanyar falo tana satar kallon ummi wacce bata nuna alamun ta san duk abunda suke a wajen ,
Yakaka ta bi bayan ta da kallo tana murmushi
Ta kai gaf da shiga falon ta ɗaga murya tana cewa ,
A gaishe min da yayan namu da kyau da kyau kin ji sahiba ta ?
Da gudu lubna ta ƙarasa shigewa falon tana dariyar jin kunyar ummi .
Ƙarfe biyu dai-dai da idar da sallar juma'a yakaka da lubna sun kammala ɗaura fura guda uku uku a cikin farar leda tare da kindirmo me ɗan dama shima a ƙulle a leda daban , suka haɗa su suka zuba a ƴar bakar leda daban daban , ba laifi dayawa ,
Yakaka ta jaa hijabinta saka lokacin da ta gama saka socks ɗin ta a kafa ta zura hijabin tana kallon lubna wacce take ƙoƙarin ɗaura niƙaf ɗin ta ,
Sahiba dan Allah muyi sauri kar mabuƙata su watse ,
Taku biyu tayi ta ɗauko niƙab ɗin ta ruwan madara , mahaɗin hijabin ta ta fara ƙoƙarin ɗaurawa a fuskar ta ,
Da sauri lubna ta riƙe niƙaf ɗin ,
Haba sahiba ta ? Ina mun yi cewa kin daina saka niƙab ɗin nan haka sai bayan kin yi aure ??
Hararar ta tayi
Shiyasa na ga ai kema yanzu da za ki fita babu naƙib ɗin a fuskar ki , ni dan Allah sakar min mahaɗin kwalliya ta , cikamakon martaba ta ,na sanya abuna ,
Amma ai ni kin san dai an riga an sanya rana , babu sauran wani ɗa namiji da zai sake cewa yana so na na kula shi ,
Ok to maza yi min gorin aure sahiba ,
Ta furta hakan muryar ta babu alamun wasa .
A hankali ta sakar mata niƙab ɗin , Allah ya baki haƙuri sahiba ba manufata ba kenan . Mu tafi .
Yakaka wacce bata furta zancen da wata manufa ta daban ba daga cikin ran ta sai domin ta samu lubna ta sakar mata niƙab ɗin ta da take neman ƙarfi da yaji ta hana ta sawa a cewar ta shi yake hana samari kula yakakar tunda ba ganin fuskar ta suke ba , duk sai ta ji ta ba daɗi da ta ga kamar zancen ta ya sa aminiyar ta a damuwa .
Tafe suke akan hanyar su ta dawowa daga rabar da furar suna tafe suna hirar su hankali kwance irin ta shaƙiƙan ƙawayen da halin su da ra'ayoyin su suka zo ɗaya suke kuma ƙaunar juna domin Allah ,
Motar da take tahowa daga bayan su sannu a hankali saboda ruwan sama da ya kwanta bisa kan kwaltar , wacce ta fito daga layin gidan su yakaka ,ita ce ta matsa musu hon ,
Su biyun suka haɗa ido , yakaka ta janye hannun lubna , da nufin ko Suna bisa hanya ne sun matsa daga hanyar ,
Maza biyu ne a cikin motar wanda kallo guda za'a musu a gane cewa ba ƙananun samari bane , mazaje ne waɗanda suke kan ganiyar shekarun su na 40 cif , wayewa tare da gogewar da ta bayyana kan ta a jikin su ita take nuni da tarin ilmin da yake jibge a ƙwanyar su , ɗaya yana mazaunin direba yayin da ɗayan yake daga gefen sa ,
Na gefen ya kai hannu a karo na biyu da nufin sake danna hon , na gefen nasa ya tare hannun nasa ,
Suleiman meye hakan kake kuma ?
Yace yana kai kallon sa gare shi ,
Dan Allah abokina yi parking ka bani mintuna biyu zan fita ,
Bai ce masa ƙala ba saboda yanayin sa da bai tare da nishaɗi ya sa baya buƙatar doguwar magana , ya gangara daga gefe ya tsayar da motar ,
Da sauri suleiman ya fice daga motar ,
A hankali yayi musu sallama cikin nutsuwar da take halittar sa tun ƙuruciya ,
Tana jin muryar sa ta gane shi , shine dai maƙalemata manne matan da ya liƙe mata tsawon shekaru uku yana bibiyar ta ba tare da ta taɓa saurarar sa ba ,
Matsa hannun lubna da yake cikin nata tayi , ta mata alama da kar ta kula sa , sai dai irin nutsuwa tare da kamala da ƙwarjini na musamman da lubna ta hango a gare shi ya sa ta fahimci ba irin sa ne mazan da mata ke gwatsalewa ba dan haka taƙi amfani da umarnin yakaka ta ja ta tsaya tare da amsa sallamar sa
Baiwar Allah naji daɗi da ki ka tsaya kika amsa sallama ta domin nasan da ta ƙawar ki ce baza ku tsaya ba , dan kuwa tsawon shekaru kusan uku kenan ina bibiyar ta amma bata taɓa tsayawa ta saurare ni ba,
Da sauri lubna ta kai kallon ta ga yakaka wacce ta yi gaba kaɗan ta tsaya tare da ɗauke kai daga barin kallon su .
Dan Allah kayi hakuri,
tace da shi , girman sa na sake cika mata idanu
Babu kome duba da cewa a yanzu bisa titi muke ba darajar mu bace yin magana anan dan haka ki sanar da ni adireshin da zan same ki ko kuma number ta wayar ki saboda ina son yin magana da ke game da ƙawar ki idan kin bani dama ,
Da sauri lubna ta ba shi number wayar ta , tana jin farin ciki na ratsa ta , a karon farko yau wani namiji ya nuna yana da ra'ayi akan yakaka , namijin ma gangariya irin wannan ai kuwa yau ummi na da farin labari .
Bayan ya karɓi number yayi mata sallama ya juya wajen motar su , da ƴar dariya a fuskar sa ya dubi abokin sa da hankalin sa ke gefe guda da alama yayi zurfi cikin tunani .
Abokina ka taya ni murna ga alamu na sanya ƙafa a kasancewa mijin mata biyu , ramla ta kusan samun abokiyar zama , tsawon shekara uku da nake bin yarinyar nan tana yin biris da ni , sai yau nayi sa'ar haɗuwa da ƙawar ta ga alamu ita zata min tsani na samun ta ,
na rasa me yake fusgata akan ta alhalin sau biyu kawai na taɓa ganin fuskar ta ,
Da alama akwai rabo ne a tsakanin mu me ƙarfi ,
A hankali ya tada motar ba tare da ya bada muhimmanci a zancen nasa ba ,
To ai sai ka ɗau harama , takaicin matan duniya ne bai ishe ka ba , ko kuwa ma nace har yau baka san wacece mace ba da irin tarin abubuwan ƙi da yake tare da ita da ace ka sani da baza ka yi sha'awar ajiye su har su biyu kamar kayan ado a gidan ka ba ,
Wuce su suka yi a hankali ,
Lokacin da suleiman ke bashi amsa
Hamza kenan kai dai na rasa wanne irin tabo mace tayi maka a duniya kake musu irin wannan kuɗin goro , duk kuwa da yadda safiyya take tarairayar ka tare da lelen ka kamar wani jariri sabon haihuwa , bana jin ta taɓa saɓa maka a rayuwar zaman auren ku .
Ya ƙarasa zancen tare da dariyar shaƙiyanci .
Murmushin takaici doctor hamza yayi ,
Baza ka taɓa ganewa ba suleiman !
Ya maida ganin ga madubin motar sa , yana hango ta ta jikin madubin ƙwarai tafiyar ta ta ɗau hankalin sa , mace ɗaya ya taɓa gani da salon takun nan , wacce bai ko son giftawar tunanin ta cikin ran sa sai fa yau da ya sake ganin wata wacce fuskar ta take a rufe Bai kai ga ganin kamannin ta ba .
Yakaka ashe daman irin zaman da kike da ni kenan ??
Cewar lubna idanun ta na bayyana ɓacin rai ,
A kaikaice yakaka ta dube ta , kin ga sahiba bana ciki da rigima , daga kawai mutum ...
Hmm
Lubna ta katse ta ,
Wallahi sahiba abu ɗaya zan faɗa miki a matsayin ki na wacce na ɗauka ƴar uwa ,
Kar ki yadda kiyi wasa da damar da ta zo miki , idan har wannan mutumin da gaske yake ki bashi dama ku fahimci juna , aka yi bincike bashi da wani aibu wallahi ki bada dama kuyi auren ku shekarun mu sun fara tafiya ishirin da biyu mun rufa ta da uku muke hari ,wallahi wasa ba namu bane dama kuma sau ɗaya take zuwa a rayuwa ,
Shiru yakaka tayi
Kalmar ,"Dama," na maimaituwa a cikin kan ta , ita har tana da wata dama da ta rage mata kuwa ? Ai damar guda ɗaya da take da ita ta riga ta zo ta wuce tun a shekarun baya , " damar da mahaluki ɗaya ya bata wanda ta tabbatar baza ta taɓa samun makamancin sa ba, bata yi amfani da damar ba a maimakon haka ma sai tayi masa mummunan sakamo da har yau idan ta tuno shi kunya tare da nadama basa ƙasa a guiwa wajen danne ta ,
ina ma ina ma ina ma ?? Da ace dama zata dawo mata ? Da ace zai sake ba ta dama ko da gutsire daga irin damar da ya bata a baya ? Wataƙila da ta gyara kuskuren ta ta wata fuskar ,
, abunda ta sani shi ɗin ya riga ya mata nisa ita ta zama wata shuɗaɗɗɗan lamari da ya taɓa giftawa cikin rayuwar sa ,
Bata da wani shauƙi ko tunani mai armashi akan wani ɗa namiji har yau ta gaza sake son wani ɗa namiji , " zata iya cewa ta ƙi maza ," ƙi irin na wanda kunama ta taɓa harbin sa babu shakka idan ya ga gizo-gizo kakkaɓe shi yake , dangantakar nesa nesa ce ke tsakanin ta da maza ,
shiyasa har yau ta gaza samun saurayi ɗaya tak , ita ce bata saurarar su bata bada fuska , take boye kan ta tare da killace surar ta daidai da fuskar ta a rufe take , ta zaɓi hakan , ta kuma fi son tayi tsarayuwar ta a haka ba tare da wani ɗa namiji ya sake ratsa rayuwar ta , burin ta ɗaya ne shine tayi ilmi kuma tana godiya ga Allah tana godewa malama maryam tare da addu'ar Allah saka da alkhairi ga baki ɗayan zuri'ar ta ,
Ko da ko kusa bata sahun malumma amma kai tsaye a yau ta wuce a ƙira ta da jahila , ta nemi ilmi tana kan nema kuma zata cigaba da nema har.....
Har suka kawo gida bata cewa lubna ƙala ba ,
Sai da suka shigo gidan ta ruga da ɗan gudun ta ta rungume malama maryam wacce take tsaye daga ƙofar kitchen tana amsa sallamar su .
Ni bazan yi aure ba har sai nayi ilmi na zama kamar ummi malama ta , sai ki san yadda zaki yi da mutumin da kika ba wa phone number .
Murmushi ummi tayi ,
Anya kuwa yakaka ? Aure ai shine cikar darajar ɗiya mace
Lubna wacce take zama akan kujera ta shiga bada labari tiryan tiryan tana yi tana hararar yakaka wacce take yanka musu cabbage da zasu ci abincin rana da shi .
Sosai malama maryam ta yiwa yakaka faɗa daga ƙarshe ta ƙarƙare da yi mata nasiha tare da faɗa mata fa'idojin aure da girman matsayin sa a addini .
Jikin yakaka yayi sanyi har idanun ta na tara ƙwalla , ta gaza cin abinci na kirki .
A ƙarshe ta jaa kunnen ta akan daga yau kar ta ƙara ƙin saurarar duk wani namijin da yake da kamala da ya nuna yana son ta , ta ƙoƙarta ta saurare shi na ɗan wani lokaci ta fahimci wanene shi , daga nan idan ta yarda da halayen sa na ƙwarai ta bashi dama ita ma tayi aure , ko kusa kar ta kawo aƙidar ƙin aure kusa da ran ta saboda wani shuɗaɗɗan dalili nata , .
A ladabce ta amsa mata da zata yi yadda ta faɗa mata .
Bata wani jima ba saboda yadda walwalar ta tayi ƙaura ta musu sallama tana barin gidan ƙarƙashin rakiyar lubna wacce duk ta damu da rashin walwalar ƙawar ta ta , sai faman jan ta da hirar raha take ,
Har ƙofar gida ta rako ta ,
Zata tura ƙofar gidan ta shige lubna ta riƙo hannun ta , ta waiwayo tana kallon ta da sakakkiyar fuska .
Sahiba idan baƙya son sa idan ya ƙira insha Allah zan faɗa masa dan Allah ki bar damuwa .
Murmushi yakaka tayi ,
Ni dai ban ce miki ba , kawai ....shiru tayi ,
Baza ki gane ba sahiba .
Zan gane dan Allah ki faɗa min meye ne ? Duk banji daɗi ba da naga ranki a jagule
Ni bana son kowanne ɗa namiji ilmi me zurfi nake da burin yi saboda ina da mummunan rauni a zuciyata wanda jahilci ne ya assasa min ina so na samu ilmin da zai warkar min da ciwon da na ji akan jahilci ,
A hankali lubna ta gyaɗa kai tana sakin hannun ta ,
na fahimta,
ta furta hakan ba domin ta fahimce ta da gasken ba , abunda ta daɗe da sani cewa yakaka tana da wani binannen ƙuduri wanda take dakon sa boye cikin ran ta da ita bata riga ta san wanne irin kuɗiri ne ba .
Daga cikin niƙab ta sake yin murmushi ,
Sahiba sai gobe zan zo ki bani labarin yadda kuka yi da ,"direba,"
Ta ƙarasa zancen da dariya cikin muryar ta , ko kafin lubna ta bata amsa wacce ta yamutsa fuska tare da ƙanƙance ido
Ta shige gidan da ɗan gudun ta tana jin lokacin da lubna ke cewa daɗin abun ma direban jirgin sama ne .
Da sallama ta shiga falon duk da cewa tayi ne ba domin tana sanya ran za'a amsa mata ba sai dan sanin muhimmancin sallama a musulunci da ta riga tayi .
Kamar yadda ta zata kuwa daga samira har hamshaƙiyar ƙawar ta da take haƙimce akan kujerar falon babu wanda ya amsa sallamar ta , hirar su suke cigaba da yi da take cike da shewa da dararraki irin na yaran matan da suke juya duniya a tafin hannun su .
Rage tsawo tayi ta ɗan durƙusa ,
Anty samy sannu da hutawa ,
Ke ke yaks wanne irin iskanci ne wannan ?? So nawa zan faɗa miki bana son kina shigo min gida da wannan maya-mayan yadikan da kike yawo da su a jiki , musamman ma na fuskar nan taki kamar wata korarriya daga makka ? To na faɗa miki yau ce rana ta ƙarshe .
A hankali yakaka ta kai hannu ta kunce niƙab ɗin fuskar ta , lokacin da sofi take kai ganin ta kan ta ,
Kiyi hakuri anty na cire .
To ya dai fi miki , yo Allah na tuba na sanya wannan mayanin a fuskata ai ya shaƙe min numfashi ya sheƙa da ni barzahu ban shirya ba ,
Kallon kallo suka yi a tsakanin su , kafin sofi ta janye idanun ta tana yatsina fuskar da ya zama halittar ta ,
Kirjin yakaka yayi dakan lugude , tsawon shekaru biyar bai isa a ce ta manta fuskar sofi ba matar da ganin farko haɗuwar su ta fari ta ɗau karan tsana ta aza musu ita da ƙanwar ta falmata , dan haka cikin hanzari ta miƙe tare da haɗiye kalaman gaisuwar da tayi niyyar miƙa mata , ta juya tana nufar ɗakin ta .
Friend wannan wacece ? Aina kika samo ƴar ƙwara ? Ko dai ko dai .... Ta ƙarasa zancen tana sakin wata shashashar dariya .
Ɗan murmushi samy baby tayi cikin ran ta bata mamakin rashin gane yakaka da sofi ta yi , ko ita da kan ta bata gajiya da kallon yakaka , wata irin fata ce da ita wacce bayan haske tana ɗauke da wani irin taushi tare da ƙyalli a idanu , ya haɗu da gyara tare da jimaka me kyau da take samu daga ita samy baby , haɗi da girma tare da cikar macen da take kan ganiyar ƙuruciyar ta , sai ta zama tamkar farin wata idan ta gifta dole ta ɗau hankali , ɗan tsararren jikin ta da yake a murmure kowanne irin kaya ta sanya masa kyau yake .
Ai ba domin tirjiya da yakakar take gwada mata ba da tuni maƙudan kuɗaɗe sun fara shigo mata ta hanyar yaks , amma wani ɗan lokaci kaɗan take jira wanda zata kammala aiwatar da nufin ta , ta kuma fara kwasar adashen da ta dunga zubawa a dalilin ta ,
Friend wannan wata haja ce da nayi tsintuwar ta a gari ,
Kalaman samy baby suka zo daidai da zaman yakaka a bakin ɗan gadon ta , daga inda take tana iya jin muryoyin su ,
Daɗi ta ji da samy baby bata jaa dogon bayani ta sanar da sofi ko ita ɗin wacece ba .
Taɓ kina nufin wanna ƙatotuwar budurwar kika bawa mafaka a gidan ki ? Ah lalle ,
ta ƙuta
Kawai dai dan ke ma ba miji ke gare ki ba , idan ba haka ba ina ke ina kawo annoba muhallin ki ?
Ai ni tsakanina da ire-iren waɗannan matan masu kama da barbarar yanyawa ko gaisuwar kan titi babu ,
Ai ko sama da ƙasa zasu haɗu bazan bar ido irin na yarinyar nan ya gauraya da na doctor na ba ,
Wai Allah har bugun numfashi na ya fara sassarfa bala'i .
Dariya samy baby ta kwashe da shi , daɗi na da ke freind akwai bala'in kishi ,
Sha kurumin ki sanya ranki a sassanyar inuwa tunda har kika mallaki doctor hamza a matsayin miji ke da kan ki kin san naki ne ke kaɗai mutuniyar ,
Wata sakaryar dariya sofi ta sake tare da ba wa samy hannun suka tafa .
Ni yanzu kin ƙi ki faɗa min sirrin friend wai tsakani da Allah wacce duniyar kika samu haka a Boston da har kika ajiye waɗannan manyan kayan haka ? Kin gan ki kuwa sofi cikin shekaru huɗu jal kin sauya ta jiki ,
ai wallahi wanda duk ya san ki a da da kike bulugari bazai gane ki ba a yanzu da kika koma wata katafila, ke ni anya kuwa doctor yana iya yin nisa da ke wannan irin abebaɗan more rayuwa da kika haɗa a jiki ahayye duniya gidan daɗi ɗan Allah ƙawata bani sirrin !
Kalaman samy baby na kusa da ƙarshe ya sa fara'ar fuskar sofi raguwa ,
Cikin jimami tace ,
Ai lamarin doctor ajiye shi gefe guda friend , kullum jiya iya yau ke wataran ma jiya ta fi yau ɗin domin ko yanzu kafin su kawo ni nan su ajiye baki ga yadda ya nemi min cin fuska a gaban abokin sa ba , akan sutura , wai kayan da na sa sun matse ni , bazan hau masa mota a haka ba sai dai na tafi na hau taxi shi babu abunda ya dame shi , ya dunga balbalin bala'i da daman ƙiris yake jira tun kafin mu baro US yake kumburi shi ɗaya uwa fulawar da yis yayi mata yawa, ina dai lallaɓa sa ne ,
Wallahi tsawon shekaru uku da muka yi a US da zan lissafa miki irin baƙin cikin bawan Allah nan da na ƙunsa sai kin ji tausayi na , gangar jikin sa kaɗai na mallaka , ruhin sa na wani waje wanda nake zaton ya min nisa duk kuwa ƙoƙarina akan kome nasa , ke dai kin san yadda daman aka yi auren nan namu , to duk da haka ban zauna ba malamai da bokayen yi nake na ƙarƙare miki ƙanƙat ɗin tsafi dai har india na je akan a min yadda zan yi na samu mazauni na dindin a gurin sa na amshi sararin zuciyar sa,
Zuwa na karnataka india ne ma fa da aka min wani mugumugun aiki aka min filla filla da tunanin sa na samu yake kula ni har muke iya haɗa shimfiɗa ,
A hakan ban zauna ba kullum ni ce a gyara saƙo da lungu na jikina tare da matso kyau , rana ɗaya na lura kamar
Yana son mace me manyan kaya , saboda bin wata mata da kallo da na ga yana ta yi a gidan cin abinci a boston , na dubi matar na ga idan banda himilin cinya da ɗuwawu bata fi ni kome ba , tun daga ranar na shiga faɗi ta shi ganin yadda zan yi nima na ajiye manyan kayan nan ,
magungunan ɗago ɗuwaiwai da ƙara faɗin cinya babu irin wanda ban afa ba , amma da yake jikin nan nawa marke ne , shiru maƙatau bulunbuƙui , jiya iya yau , na kasa haƙuri na faɗa miki tare da jagorar wata ƴar * ƙawa da nayi a boston balarabiya ce ƴar duniya ta ƙarshen ƙarshe , ita ta kai ni aka min aiki me ƙanƙat ,
aka tatso tare da ɗago tudun bayan nan da kike gani , azaba babu irin wacce ban sha ba a lokacin aikin nan da bayan gama yin sa ,
amma na shanye , kuma babu shakka ƙwalliya ta biya kuɗin sabulu , domin wasu cin kashin da yake min da yawan fushin sun ragu , duk da dai da farko ya tada ɓallin sai na faɗa masa me naje nayi jikina ya koma haka ya dunga bincikata , da yake lokacin aikin nan na karnataka na kan zafin sa , zancen bai yi nisa ba ya manta ya kuma haɗu da shima yana son manyan kayan ai hajiyata shiru kike ji malam ya haɗiyi shirwa !
Sai dai ki ga idan na gifta yana zaune yana haka da ido ,"ta wani yi ƙasa-ƙasa da ido tana kwatance , " yana bin abebaɗan da kallo , ni kuwa sai na sake jujjuya masa su da kyau yadda zan sake kamo sa , a raina ina "faɗin kai da abubuwan ka ai daman sakin jiki kayi ka ƙure musu kallo meye na wahalar satan kallo kamar ba
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Chapter 110
Chapter 111
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 50 Chapter of 111