kai ta asibiti ,
Da sauri Youssouf ya waigo tare da sunkuyowa kan falmata ya tabbatar dai bata numfashi nan take ya sanya hannu a aljihun sa yana ƙiran direban sa , lokaci guda fuskar sa na bayyana ruɗanin da yake ciki yake cewa
Daman bata da lafiya ne Baba ??
Prof bai amsa masa ba ,
Direban youssouf shi ya fara shigowa dan haka rahima ta fara ƙoƙarin ɗaga falmata sai dai ta kasa , saboda tayi mata nawi ,
Baby mama Youssouf ya miƙawa Rahima ,
Lokaci guda ya sanya hannunwan sa biyu ya ɗaga falmata wacce take sume ya fice da ita wajen motar su , direban sa ya buɗe gidan baya ya shimfiɗe ta ,
Ya karɓi baby mama daga hannun rahima tare da yi mata umarnin ta shiga su tafi ta gwada musu asibiti mafi kusa da zasu kai falmata ,
tafiyar mintoci biyar suka isa wani asibiti mai zaman kan sa , inda nan take likitoci suka rufu akan falmata suna ƙoƙarin dawo da numfashin ta dai-dai ,
Hankalin Youssouf baki ɗaya a tashe yake ya kasa zaune ya kasa tsaye , sai zirga zirga yake tsakanin kofar ɗakin da Falmata take yana rungume da baby mama , tsoron sa ɗaya kar yarinyar nan ta mutu a sanadin raba ta da yace zai yi da ƴar sa , idan haka ta faru bai san inda damuwar sa zata kai ba , " ko kusa bai san haka take ƙaunar ƴar sa ba ,
ya kasa kintata yawan ƙaunar da ke tsakanin ta da yayar ta wanda yake da tabbacin son da take mata ne ya shafi ƴar ta , idan kuwa haka ne lalle falmata abar a tausayawa ce , ƙwarai ya kamata yayi adalci ya kuma duba anya idan ya raba ƴar sa da ita ya kyauta kuwa ?? Anya bai so kan sa dayawa ba kuwa ?
mintoci arba'in da shigar da ita ɗakin suka fara jiyo gunjin kukan ta , tana surutai ,
Da sauri Biyamuradi youssouf ya ƙarasa gaban ɗakin dai-dai da fitowar babban likitan ,
Mun samu numfashin ta ya dai-daita kamar yadda muke zaton kun sani tana da asthma , toh ta samu attack ne , yakamata a dunga kiyayewa da duk wani abu da zai iya kawo mata wahalar numfashi , yanzu ku shiga akwai wanda take son gani a tsakanin ku , nan da ɗan wani lokaci kaɗan ma zaku iya tafiya gida ko awa ɗaya haka nan gaba !
Biyamuradi youssouf ne a gaba sai Rahima biye da shi , suna shiga rahima ta ƙarasa ta rike hannun ta , tace ga ita
Ki daina kuka haka fatima , ai ga baby nan ba'a tafi da ita ko ina ba ,
Tana ina ??
Tace tana lalube da hannuwan ta biyu idanun ta har sun rine tsabar kuka ,
A hankali biyamuradi youssouf ya tako zuwa gaban gadon ya ɗora mata baby mama a cinyar ta tare da cewa
Ungo ta ! karɓe ta fatima daina kuka , ke ai uwa ce a gare ta ,
Chak ta ɗauke ta ta rungume ta tana ajiyar zuci tare da shafa bayan baby mama tana ɗan bubbugawa ,
Juyawa yayi ya fita yana jin yadda tsananin tausayin ta yake ratsa kowanne saƙo da lungu na zuciyar sa yana samun mazauni , ji yake kome yana neman kunce masa , tausayin ta kuma yana neman yin tasiri akan sa , mafita yake nema ,
Zuwa yayi ya biya kuɗin magungunan da aka mata ,
Daga nan ya sake ganin likitan da ya bata taimako , ya sake yi masa bayani tare da sake jaddada masa a kula da lafiyar ta, nan ya rubuta musu sallama zasu iya tafiya daga zarar an sake duba yanayin numfashin ta ,
A bakin ƙofa ɗakin ya tarar da rahima tana zaune ,
Da sauri ya tura ƙofar ya shiga idanun sa suka sauƙa akan ta , har yanzu tana zaune rungume da jaririyar da take ta bacci abin ta ,
waye anan ? Tace tana sake rungume ƴar ,
Fatima ,
ya ƙira sunan ta muryar sa babu amo ,
Ƙwalla ce ta sake kawo mata a ido , ita dai wannan mutumin ya fi ƙarfin ta ,
Dan Allah , Dan Allah ka bar min ita , kar ka raba ni da ita ,
Shiru yayi yana kallon ta , idan har yace zuciyar sa bata yi laushi ba akan tausayin yarinyar ya faɗi ƙarya ,
Fatima za ki bi ni mu tafi ?? Za ki bi ni na tafi tare da ku ke da ɗiyar ki ?? ?
Inda take jin sautin muryar sa ta saita idanun ta tamkar tana ganin sa ,
Muryar ta ƙasa-ƙasa , ta juya tambayar kan sa ,
Za ka yadda na bi ka , ? Idan na bi ka za ka bar min baby a tare da ni ??
Idan za ki bi ni zan bar ki miki ita har abada a hannoun ki , babu mai raba ku ,!
NA YARDA ZAN BI KA ,!
****
ƙarfe huɗu suka dawo gida , numfashin falmata ya samu daidaito , tana maƙale da ƴar ta tsam , lokaci zuwa lokaci tana ɗan jijjiga ta saboda kukan yunwa da ta fara ,
Suna shigowa prof wanda tunda suka tafi yake ƙiran rahima ya ji halin da suke ciki , ya ji hankalin sa ya kwanta da ya ga falmata ta warware ,
kai tsaye falmata da rahima suka wuce cikin gida domin su haɗawa baby madarar ta ,
Shi kuma Biyamuradi ya shiga wajen prof ,
Cikin nutsuwa youssouf ya yiwa prof bayanin yadda suka yi da falmata akan amincewa da tayi zata bi shi , ya ɗora da cewa
Na ɗauki Alƙawarin zan kula da ita tamkar yadda zan kula da ɗiya ta , da yardar Allah ,
Gyaran murya prof yayi bayan ya gama jin sa ,
Ɗana ka so kan ka dayawa , kuma a wannan gaɓar inada ikon yin hani , saboda yarinya amanar Allah ce a hannu na , shi ɗa na kowa ne , abunda baza ka so ya samu ɗan ka ba idan kana da ikon hanawa kar ka bari ya samu ɗan wani ,
ni a matsayina na wanda wannan yarinya take a ƙarƙashin iko na a yanzu , bazan amince maka ka ɗauke ta ka tafi da ita ko ina ba , tana matsayin ƴa mace , kai ko namiji ce bazan yadda ba bare ƴa mace , to a wanne dalili ? Ka tafi da ƴar ka wannan ƴar ka ce ,kana da iko da ita amma fatima kam baza ta bi ka ko'ina ba !
Shiru youssouf yayi kan sa a ƙasa , shi tausayin falmata yake ji matuƙa , sannan yana da kyakkyawar niyyar sauke ƙudirin sa na tun farko da ya so cikawa akan yakaka , a yanzu da bata nan zai so ya tallafi falmata , ko da babu baby mama zata samu taimakon sa sanadin yakaka ,!
Baba ayi haƙuri a duba da kyau dai ita ɗiyar nan idan an raba su da jaririyar nan matsala ce babba zata auku , lafiyar ta abun dubawa ce ,
Babu alamun sassauci a muryar prof ya ce idan ka ga na bar ka , ka tafi da fatima , to ka ɗauke ta ne ƙarƙashin amincewar shara'a
amincewar shara'a ?
Youssouf ya maimaita
Ƙwarai ina nufin igiyar AURE ta ƙullu a tsakanim ƙu , ta zama halalin ka , ta maye gurbin ƴar uwar ta a gurin ka , to a lokacin kana da ikon da zaka tafi da ita tare da ƴar ka duk inda kake so cikin duniya ,bazan hana ba, idan kuwa ba haka ba ka janye batun zuwa da ita ko'ina idan Allah ya kai mu gobe ka zo ka ɗau ƴar ka kamar yadda ka ce , na gama magana !
Ɗago kan sa yayi yana kallon prof tamkar sassaƙen mutum mutumi ,
AURE ?
AURE TSAKANIN sa da wa ? Wannan ƴar ficiciyar yarinyar ? Ƙanwar yarinyar da yayiwa ciki ? Makauniya ƴar gudun hijira ? Marar gata marar galihu marar dangi ??
Wani irin yanayi yake ciki akan tunowa da yayi da wacece ita , ?
Bugu ƙirjin sa ya shiga yi gumi yana tsattsafo masa har yana ɗiga daga goshin sa duk kuwa da sanyin ac da ya wadaci falon , "
Youssouf mutum ne da yake jajirtatce mai kafiya akan cikar burin sa bai cika duban yadda gaba zata kasance ba idan yaso aiwatar da wani ƙudiri nasa , a yanzu tafiya da ƴar sa shine a gaban sa , so yake ya tsira da ƴar sa ba tare da ya bar baya da ƙura ba , ba tare da ya ci karo da wani abu da zai iya yi masa shamaƙi ba ,
raba fatima da baby mama wani abu ne da idan yayi , har abada baya jin zai iya mantawa kamar yadda ya riga ya san cewa tabbas idan ya tafi ƙasar su dawowar sa nigeria wani abu ne da yake gani da wuya ya kasance to ya dawo yayi me ?? Waye nasa a nigeria ? Ba shi da kome a nan , bai taɓa zuwa ba sai ta dalilin aikin sa ,
Kalmomin da zuciyar sa ta riga ta amince masa da hukuncin da ya yanke sune suka jero kan su suka fito ta tsakanin laɓɓan sa ,
NA AMINCE DA AUREN TA !
a take fuskar prof ta yalwatu da haske da fara'a
Masha Allah Masha Allah haƙar sa ta cimma ruwa ,
Ka amince zaka auri fatima ƙanwar matar ka ??
NA AMINCE ZAN AURE TA !
Assalamu Alaikum ! Masu karatu ,
Da fatan duk kuna lafiya cikin aminci ?
Ina sake miƙa godiya ta bisa ga tarin saƙonnin ta'aziyar ku da suka iso min kan rasuwar ƙani na , nagode ƙwarai Yaa Allah ya amsa addu'o'in da ku ka yi masa , ya kuma baku lada Ameen thumma Ameen
Nagode !
[9/3, 10:13 PM] +234 806 122 1116: Fikra writers association
MAFARI
( Hargitsin Rayuwa )
umm'muaz
30
Babu kowa a harabar barikin sai masu gadi da suke daga kowacce kusurwa , sakamakon dare da ya raba tsaka 2am , sai Biyamuradi youssouf da ke kai kawo a cikin hunturun sanyin da yake ratsa har ɓargon mutum gami da iska mai ƙura da take toshe ƙofofin hancin ɗan adam , a tsaye yake tsakiyar filin ya sunkui da kan sa jikin sa sanye da ƴar baƙar riga mai gajeren hannu da dogon wondon uniform ɗin su na soji ,
Ya zurfafa a tunanin makomar Auren da yake shirin karɓarwa kan sa nan da wasu ƴan awanni zuwa wayewar gari ,
Ina zai dosa da auren yarinyar ?? Yarinya ce ƙanƙanuwa , sannan kuma miskiniya , ta wacce hanya zai fara tallafar ta , domin ƙwarai take buƙatar matallafi cikin rayuwar ta da bata da kowa sai ƴar jaririyar sa ,
Me zai cewa iyayen sa su fahimce sa da dalilin sa na auren ta? Wanne irin hukunci maimartaba da hajiya umma zasu yanke masa idan suka ji ainahin abunda ya aikata da har ya kai shi ga auren yarinyar ?? Zasu su yi fushi mai tsanani da shi irin fushin da baya fatan ya gitta tsakanin sa da iyayen sa duk tsawon rayuwar sa ,
Me zai wakana tsakanin sa da gimbiya maimunatu lokacin da ta san ya auri wata mace kafin ita , Yana riƙe da auren wata bayan ita ? Zata iya yi masa kallon mayaudari kuma munafuki , a ƙarshe soyayyar su zata gurgunce da zai iya datse alaƙar su shi da ita , bai fatan haka saboda ya shaida irin tarin ƙaunar da zuciyar sa ke yiwa gimbiya maimounatu,
Kalaman prof ya tuno inda yake ce da shi ,
Madallah tunda ka amince da auren Fatima , ka zo da wakilan/waliyan ka, a gobe zan baka auren ta , daga nan idan kana buƙata a goben zaka iya tafiya da ita tare da ƴar ka ,
A lokacin ya amsa masa da
Toh na Amince
Har ya tashi zai tafi prof ya tsaida shi ,
To amma akwai wani lamari guda ɗaya , lamarin kuwa shine bazan iya ɗaukar yarinyar nan na baka ita , ka tafi da ita, ita kaɗai ba dole zan haɗa ka da mutum ɗaya wanda za ku tafi tare chan ƙasar ta ku domin a gano inda zaku zauna saboda sha'anin duniya , ta ka zo ta kan zo ko watarana wasu daga cikin dangin su zasu ɓullo su zo neman sanin inda ƴar su take , da fatan ka fahimceni da kyau kuma ka amince ?
Jim yayi a ƙarshe ya sake amsawa da
NA AMINCE
Waje ya samu ya zauna akan ɗaya daga cikin dakalin da aka yi su domin zama dake a watse cikin barikin ,
Da farko yayi niyyar idan ya ɗauke ta ya kai su Niamey gidan ubbo a matsayin ƴar gudun hijirar da ya taimaka ita da baby mama idan ya so su kasance ƙarƙashin kulawar ubbo tare da shi har zuwa lokacin da zai samawa kan sa hanyar da zai bi ya bayyana su ga dangin sa ba tare da abubuwa sun rinchaɓe masa ba ,
Sai dai batun haɗa su tafiya da wani ya rusa wannan nufin nasa domin ko kusa ba zai so a san wasu dangi nasa ba , ba zai so asan ko shi wanene ba saboda kar watarana kome ya bayyana , a biyo sawu ba tare da sanin sa ba , kome ya lalace masa a lokacin ,
Idan kuwa har ya nuna ƙin amincewar sa , hakan zai sa a dasa ayar tambaya akan sa , ayi masa zaton marar gaskiya , wanda zai iya sa pro ya tsananta bincike akan sa wataƙila a ƙarshe kome ya isa ga masarautar su , bai fatan haka ,
Idan kuwa haka ne dolen sa ya yarda ya tafi da su da me rakiyar su ,
Ƙaunar ƴar sa da Allah ya jarrabe shi da shi ya sa duk yana ƙoƙarin fuskantar duk wani ƙalubale , burin sa ya tsira da ita , dan haka a ƙarshen tunanin sa ya ture duk wani ƙalubale gefe ya amince da mallakar baby mama tare da uwar goyon ta a lokaci guda da me rakiyar su ,
Yana tsaye a wajen aka yi ƙiran sallan farƙo na karfe 3:30am , kai tsaye ya nufi babban masallacin cikin barikin ya ɗaura alwala da sassanyan ruwan da iskar hunturu ta gama hura sa ya shiga masallaci ya fara jero nafilfili , yana roƙon Allah ya bashi nasara akan manufar sa ya kuma rufa masa asiri ya kawo masa warwaruwar al'amuran sa a sauƙaƙe , "toh ameen,"
ALƘAWARIN UBANGIJI ( MATAR MUTUM DAGA GARE SHI TAKE )
Da misalin ƙarfe goma na safiyar ranar Alhamis ɗin karshen sati , ƴan tsirarun mutanen da prof ya ƙira na cikin unguwa da basu wuce goma ba tare da wasu ƙarin mutane biyar da youssouf ya kawo a matsayin wakilan sa wanɗanda a zahiri abokan aikin sa ne daga ƙasar su , suka haɗu suka shaida ɗaurin auren FATIMA DILMARI , tare da YOUSSOUF ABDUL-AZIZOU BASKORE , wanda ya sauya suna zuwa youssouf Garba Malbaza Uzine,
Bayan ɗaurin auren babu ɓata lokaci su abokan aikin youssouf suka yi komawar su domin ɗaura shirin tashin su zuwa Abuja inda zasu wuce ƙasar su ta jirgin sama a yau ɗin ,,
da shi kuma youssouf ya shigar da neman iznin a bada mota guda cikin motocin su na soji tare da direba da zai tuƙa su zuwa Niamey ta hanya , ba'a tsananta bincike ba aka bashi izni tare da shaida masa ya tabbatar ya samu isa niamey kafin ranar litinin inda za'a yi bikin dawowar su tare da yi musu ƙarin girma ,
Hajja me wurya," ita ce dattijuwar da prof ya zaɓa a matsayin wacce zata raka fatima ɗakin mijin ta daganan ta gano garin da zasu zauna a niger , kasancewar ita hajja mai wurya dattijuwa ce da a ƙalla ta tasamma shekaru hamsin , sannan kuma a halin yanzu bata da wani jigo cikin rayuwar ta iyaye duk sun mutu dangin kuwa kowa ta kai ta kai yake sannan tun asali bata da haula ɗan ta ɗaya ne tal da ta haife shi a shekarun girma bayan aure auren da tayi ta yi domin neman haihuwa ,
tana tsakiyar fara cin moriyar ɗan nata da ya ɗan fara tasawa shekarun sa ishirin da huɗu , ƴan tawayen boko haram suka shigo har gida suka yanka mata shi , a cewar su yana zagin su tare da sukar akidar su , dan haka suka kawar da shi,
Tun daga nan rayuwa ta fara yi mata wahala , ƙunci da talauci suka dirar mata , zamani ne da kowa yake gudun wahala ba'a duban zuminci , tunda ta fahimci haka ta daina yin raragefe gidan ƴan uwa ta bazama neman na kan ta sanin da tayi da ɗan sauran karfin ta bata zama ƙarƙashin dangina ana zuba mata sharar walakancin ,
aikatau ta fara a gidajen saida abincin ,kasancewar ta gwanar girki iri iri ,musamman ma na ƙasar camaru da tayi farkon zaman auren ta a chan , amma sakamakon tsaurin ta da kuma tsayuwar ta kan gaskiya ya sa ba ta cika daɗewa a wajen aikin ake sallamar ta , saboda bata zuru duk ta ga zalau sai ta tsinka ,"
daga baya ta koma aiki a gidajen masu hali nan ma gida biyu tana barin aiki saboda yadda take gwadawa uwargida iyakar ta a cikin gidan ta idan har ta ga abunda bai dace ba, sai fa wannan karon da tayi dace ta samu aiki gidan Professor Mustspha dilmari
Allah ya tsawaita zaman ta a gidan da taimakon tarbiyyar yaran gidan da basu cika raini da walakanci irin na sauran ƴaƴan masu hali takwarorin su ba , babu kuma matar gidan shekaru biyu take nema da fara aiki a gidan a matsayin mai yin girki , musamman ma na shi prof .
A jiya da prof ya ƙira su ita da falmata ya faɗa musu hukuncin da yake ƙoƙarin yankewa har ma ya tuntunɓi ita falmata akan jin ra'ayin ta , ta amince zata auri baban ƴar da take riƙo su tafi ita da shi da ƴar chan ƙasar sa ko kuwa ??
Ga mamakin sa ba tare da shayin kome ba
Falmata ta amsa da ta amince zata auri baban baby ya tafi da ita tare da baby ,
Ƙwarai prof ya ji daɗin amsar Falmata domin da farko har yana fargabar ko yarinyar zata ƙi gatan da yake son yi mata na aurar da ita tunda ƙuruciyar ta , ga mutumin da yake iya hango nagartar sa a cikin yanayin sa da mu'amalar sa , yana hasashen mutum ne na ƙwarai !
A sarari ya nuna jin daɗin sa tare da yi mata addu'o'in samun nasara a rayuwa , sannan ya juya ga hajja mai wurya wacce ita ma take durƙushe daga gefen falmata ,
Hajja Alfarma zan nema a gurin ki akan ki raka fatima ɗakin mijin ta ki gano min wajen da zasu zauna ita da mijin ta a chan niger ɗin daga baya sai ki dawo. Da fatan zaki min alfarma ?
Dariya hajja me wurya ta sa !
Babu kome Alhaji zamu tafi tare , me zaman aure ma ta amince bare ni ƴar rakiya ?? Ai ko gaba da binnin sin ne Alhaji ba na ƙi raka ƴar marainiyar Allahn nan ba , kai shima dai wannan dogon balaraben nijar ɗin Allah yayi masa Albarka da duk da kyan nan nasa da cikar zati irin ta ɗa namiji amma haka ya runtse ido ya ce ya amince zai auri wannan murɗaɗɗiyar bahaguwar yarinyar , ai dole ayi masa godiya bawan Allah .
Nan dai Alhaji ya sallame su yana sake musu godiya akan biyayyar da suka ma sa ,
Kan hanyar su ta komawa hajja mai wurya tana riƙe da hannun falmata tace
Ke ƴar nan Allah ya dube ki ya tarfawa garin ki nono , irin wannan zankaɗeɗen miji da Allah ya wanke ya ba ki ?? Ai ko ɗiyar masu mulki ba ta ƙi shi ba , to zan fara faɗa miki tun wuri tun yanzu , ki zubar da waɗannan hargitsatsun halayen naki tun a nan nigeria kar ki ce zaki tafi gidan auren ki da su , saboda wannan dai miji naki wallahi kin yi sa'a wanke hannun ka taɓa Allah dai shi sa yadda surar nan tasa take halin sa yafi haka kyau ,
Ai bazan bar gidan nan naki ba sai na ga kamun ludayin zaman naki da shi , ato sai ki shirya ni ɗin dai da kika tsana kike ƙin bani riƙon jaririya , nice dai me miki zaman ɗaki sai dai muyi wacce za mu yi mahaukaci ya ɗau rigar kurma ...
Zame hannun ta tayi daga cikin na hajja tayi gaba ta miƙa hanya , ƙalau tamkar me gani saboda yau da gobe ta fara haddace hanyar a ƙwaƙwalwar ta,
Sasakai hajja me wurya tayi
Au aikin banza kenan hanci ba ƙafa , to ki fi ruwa tafiya , nace ki fi ruwa tafiya , wannan yarinyar sai na dage kafin ta shiga hanya ta ɗau haske ta san me duniya take ciki kan ta hayaƙi yake ,!
Falmata ko sauraron ta bata yi ba hasalima ji tayi hayaniyar hajja me wurya ta hana kwakwalwar ta sakewa tayi tunanin da ya kamata shi yasa ta zame hannun ta ta rabu da ita ,
Aure da ita da shi ?? Wanene shi da yace baban baby ne ? Da gaske shine baban baby ? Wanne irin aure zasu yi ? Ina ne ƙasar ta su ? Idan suka tafi zasu dawo ? Bata son barin nan inda take , burin ta watarana dr hamza ya nemo mata maman su , to amma yanzu kuma ga shi zata tafi ta bar nan ɗin ,
Abun da ta sani zata yi kome , zata tafi ko ina zata kuma ta shiga kowannen wahala domin ta tsira da baby mama , domin ta tsaya tare da baby mama , domin baby mama kar ta sha wuya , naƙasun ta miskinancin ta , rashin idanu ,
da ace ita lafiyar ta ƙalau , bata buƙatar abokin tayi wajen gina rayuwar ƴar ta , da zata gudu da baby mama ta ɓuya wani waje tana kula da ita , to amma ita ɗin ma miskiniya ce dole ne ta bi baban baby da yace zai kula da mama ƴar sa ce !
Ƙarfe biyu cif aka fara fito da jakar bocco ɗin falmata wacce ta haɗe kayan ta da na yakaka kakaf a cikin babbar baccon yakakar , sai kuma kayan baby mama shima a cikin babbar jaka , duk aka zuba su a bayan dunƙulalliyar motar soji me ƙirar golf kofa biyu ,
Biyamuradi youssouf ya taka zuwa cikin gidan falon prof , suka yi sallama inda prof ɗin ya bi shi da kalaman godiya ya kuma ɗora da damƙa masa amanar fatima tare da roƙon sa akan ya kula da ita , ita ɗin abar a tausayawa ce ,
Nan youssouf ɗin ya amsa tare da ɗaukar Alƙawarin zai kula da ita ,
Yana zaune hajja me wurya da falmata rike da mama haɗi da rahima suka shigo , falmata tana shirye tsaf cikin sabuwar atamfar ta ruwan ganye da adon furanni farare, ta saka farin hijabi har guiwar ta ,
Daga gefe suka tsugunna , nan prof yayi musu addu'o'i tare da ƴan nasihu ya sake ɗanƙa amanar falmata a hannun hajja me wurya har lau ,
Daga ƙarshe ya
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Chapter 110
Chapter 111
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 45 Chapter of 111