Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
a ran sa! Tare kuma da jin takaicin me ya sa suleiman bai bar shi ya hora waɗan nan gidadawan ba son ran sa ta yadda gaba baza su sake gigin yin ganganci makamancin wanda suka yi a yanzu ba , yayin da wani bangare me rangwamen rinjaye yake jin wani abu me kama da bai fa kyauta ba , musamman a yanzu da ya kalli cikin ƙwarar idanun ta masu ruwan zaiba-zaiba ,sai ya ji wannan yanayin kamar yana sake ƙarfafa acikin ran sa ,! Tsaki ya jaa a lokaci guda yana mai kau da kan sa , Ga yakaka kuwa ,' lokacin da take kallon ƙwarar idanun sa baƙar shaida take yi masa tare da jin tsanar sa tana mamaye baki ɗayan zuciyar ta tana jin shine mutum na farko da ta fara tsana a cikin rayuwar ta , sakamakon rashin tausayi ƙarara da ya nuna a gare su uwa uba , shi ɗin ne mutum na farko da ya taɓa lafiyar ƙanwar ta abar ƙaunar ta akan kuskuren da ta aikata shi cikin rashin sani ,ba tare da ya dubi naƙasar da ke tare da ita ba ," ɗauke kan ta tayi lokacin da suke sanya kafafun su domin barin ofishin , Baku ji ba ," waiwayowa yakaka tayi lokaci guda tana me jin faɗuwar gaba ," a hankali ya ƙaraso hannun sa a aljihu , zare hannun sa yayi daga aljihun ya fiddo da sabuwar naira dubu ɗaya ," ungo ku sayi hijabi ku dunga sanyawa ," ganin basu ƙarba ba ya sanya yayi ƙasa da hannun sa dai-dai hannun falmata ya taɓa hannun nata da kuɗin cikin buɗe muryar sa yace ," Ƙarbi mana ,' duk da cewa falmatan ba gani take ba hakan bai hana ta juya fuskar ta inda take jin hucin numfashin yakaka ba ," da alamun neman izni bisa fuskar ta ," Mungode Allah ya saka da Alkhairi amma baza mu karbi kuɗin ka ba a wurin Allah muke neman taimako ta hannun gwamnati muna tunanin gwamnati ke da Alhakin ɗaukar nawin mu ,? Dan haka baza mu ƙarbi kudin ka ba mun gode sosai ," cewar yakaka daga haka ta jaa hannun falmata suka ƙarasa barin wajen. Ɗan murmushi suleiman yayi lokacin da yake bin bayan su da kallo , lokaci guda yana jin tausayin su yana ratsa shi , gefe guda na ran shi ji yayi kyakyawar tarbiyyar da ya ga alamun ta a tare da su ta burge shi , juyawar sa yayi bayan ya maida kuɗin sa aljihu ," Amma wallahi hamza baka kyautawa a wasu lokutan ,abun da kayi ga waɗan nan yaran sam bai kamata ba , baka ganin ƙauyawa ne ? Ya kamata ka dunga rage zafin zuciya tare da tausayawa na ƙasa da kai Dan Allah . Mts toh uba na idan ka gama min faɗan sai ka fita ka samo Cleaner ya zo ya goge wurin tun da ka sallami masu ɗauke da alhakin gyaran kaji koh waliyyin Allah ? Yakaka , Falmata wanka kuka yi ne naga jikin ku du a jiƙe haka ? Falmata meya ya same ki haka fuskar ki a kumbure faɗuwa kika yi a banɗakin ? Ganin sun wuce basu tanka mata ba ya sa yagana bin bayan su tana me sake ƙare musu kallo daga sama har ƙasa ," a ranta kuwa ta fara jin haushin irin halayyar da suke gwada mata a wasu lokutan ,' musamman ma dai falmata , Yagana meyasa kike yin ƙarya ? Tun muna yara maman mu ta nusar da mu rashin kyaun faɗar zancen da ba gaskiya ba ,meyasa kika ce mana can wurin banɗaki ne alhalin kin san ba haka bane ? Dubi jikina dubi jikin falmata kuma ki dubi fuskar ta ? Duk sanadin kin faɗa mana zancen da ba gaskiya bane kika jawo mana wannan masifar ya zaki ji idan mu ne muka tura ki cikin haɗari irin haka ,? Cikin nadama yagana take kallon fuskar yakaka wacce take bayyana tsantsar bacin rai a lokacin da take sanya sauran guntun ruwan da ta ɗibo tana wankewa falmata jikin zanin ta ," Kuyi hakuri yakaka na ɗauka banɗaki ne ganin wani mutum ya fito daga ɗakin yana gyara wondon sa da buta riƙe a hannun sa , A fusace falmata ta katse ta wacce ta zo har wuya da bacin ran yagana domin ita ce ainahin sanadin faruwar kome ," amma ai yagana cewa kika da farko an gwada miki can wurin ne banɗakin ? Meyasa kike haka tun farkon fara tafiyar mu tare zantukan ki dayawa ba gaskiƴa kike faɗa ba, haka kika ce mana kin san hanyar maiduguri ? Ba domin Allah ya haɗa mu da mutanen dajin nan ba(fulanin da suka taimake su ) da ba mu san halin da zamu shiga ba ," yagana yana da kyau mutum ya dunga faɗin gaskiya kome wuyan ta . Cikin takaici yagana take kallon falmata wacce take daga zaune idanun ta suna kallon gefe ," tayaya za'a yi ƴar karamar yarinyar da ta girmewa , ta zauna tana gaya mata magana son ran ta ? Tana yi mata tsawa da ihu irin haka kuma ƙarin abun takaicin ma makauniya ce miskiniya ," Dakata falmata daga yau sai yau ni ba sa'ar ki bace dan haka kar ki sake cewa zaki min faɗa da tsawa ," meyasa ku da kuka shiga wajen kuka ga ba banɗakin bane ba ku fito ba ,? Koh kuwa ba tare muka zo wurin ba ɗazun nan ? Da dan kawai nayi kuskure zaku hau kaina da faɗa yayar ki tana min ke ma kuma kice zaki min kamar ku kuka kawo ni garin ? Cikin sanyin jiki yakaka ta bi bayan yagana da kallo wacce bayan ta gama mayar musu da magana ta kaɗa kan ta ta bar wajen ba tare da ta sake ce musu ƙala ba , ta koma nesa da su ta zauna , alamu sun nuna taji haushin faɗa mata laifin ta da suka yi , Wanda ita kuma yakaka sam hakan bai mata daɗi ko babu kome cikin kwanaki biyun da suka yi tare da yagana taji daɗin samun ta a matsayin ƙawar da suka shigo sabuwar rayuwar su a tare , kuma ƙwarai yagana tana kokari wurin kyautata musu musamman ma dai falmata ," toh sai dai har ga Allah ita bata son hallayar da ta lura yagana ta na da ita na ƙarya , ba dan kome tayi mata magana ba sai dan tana son yagana ta bar hallayar dan ba hallaya bace mai kyau , duk da haka cikin ran ta ta ƙudurci aniyar bata hakuri tun da ta ga tayi fushi, sam ita baza ta so rabuwar su ba ,ƙwarai take bukatar ƙawa cikin rayuwar ta a yanzu wanda a tun tashin ta bata damu da ƙawaye ba , falmata ita ce ƙawar ta abokiyar wasan ta , amma a yanzu da girma ya hau kan ta ya zama dole ta nemi wata ƙawar bayan falmata da zata dunga taya ta koh da da shawarwari ne domin inganta rayuwar falmatan . ƙamshin abincin ne ya daki hancin su da ya sa ba shiri yakaka ta bi manyan farantan da aka wuce da su da kallo nan take yawun bakin ta ya tsinke ganin shinkafar da aka wadata kan ta da baƙar miyar da tashin farko ba za'a tantance jar miya ce koh kuwa wacce irin miya bace , amma da yake cikin su ya jima rabon sa da abinci sai abincin yayi kyau matuƙa a idon yakaka ," Yakaka ƙamshin abinci nake ji ? Muje mu ci mana koh ba namu bane ? Falmata ta ƙarasa zance tare da haɗiyar yawun da kamshin abincin nan ya sanya shi tsinkewa ," Wucewa aka yi da abincin inaga rabawa ake dan naga gashi sai kaiwa ake wuri-wuri ," inaga mu ɗan jira za'a zo kan mu ," Miƙewa tsaye yagana tayi tare da ƙarasawa bakin kofar ɗakin da ɗazu ta shiga tayi tambaya wanda yanzu ta ga an shiga da farantan abinci huɗu ," Dogarewa tayi daga bakin ƙofar tana ganin yadda matan nan kusan su arba'in da ƴaƴan su ,suka tasamman farantan abincin nan huɗu haiƙan da suke tashin tiririn zafi . Hannu baka hannun ƙwarya suke auna abincin nan zuwa cikin bakunan su yayin da ƴaƴan su waɗan da wasun su basu wuce ƴan shekaru biyu ba zuwa ƙasa , su ma ba'a bar su a baya ba, kokawa suke da tiren abincin nan wasun su hannu bi-biyu suke jefawa cikin tiren basa koh nuna alamun jin zafin abincin , na bakin su yana komawa ciki sakamakon ƙona musu harcen da abincin ya ke , Cikin mintocin da suke ƙasa da biyar babu abincin nan babu alamun sa tamkar dai gonar hatsin da mayunwatan tsuntsaye suka sauka a kai suka tashi , haka kan farantan nan suke babu koh ƙwarar shinkafa ɗai , sai tashin tiririn da har yanzu da suka kammala cin abincin bai kai ga hucewa ba , ƴaƴan su suna ta sanya harce suna tanɗar jikin faranti tamkar zasu haɗa da farantin su lanƙwame . Sauke ajiyar zuci yagana tayi lokacin da suka haɗa ido huɗu da matar da ta yi mata kwatancen banɗaki a ɗazu "tana ta faman tanɗar yatsun hannun ta lungu da sako tana zura harshe tana zaƙulo duk wata guntuwar miyar da ta rage mata a hannu ," yarinya ke ba anan za ki ci abinci ba ki tafi ta can bayan tantunan da suke farfajiya anan ƴan mata sa'o'in ki suke kiyi sauri ki tafi kar a cinye a bar ki , cewar matar nan da yanzu ta kammala suɗe hannun nata ta goge hannun akan ta . Ba tare da tace kome ba ta juya gami da kai hangen ta ga harabar wajen can ta hango masu rabon abincin nan sun nufi manyan tantuna biyun da suke haɗe da junan su daga gefe ," da sauri ta ɗiro daga kan dakalin barandar har ta ɗaga kafafun tayi taku biyu sai ta waiwaya karaf suka haɗa idanu da yakaka wacce duk ta bi ta damu da fushin yagana , hakan ya sa duk wani motsin yaganan yake kan idanun ta ," Yafitar su tayi da hannu lokaci guda ta buɗe murya ", Yakaka ku zo mu je mu ci abinci a can ," ba tare da ta jira amsar su ba ta ɗaga ƙafafun ta cikin sauri ta nufi tantin da ta ga an kai abincin nan cikin ran ta cike da addu'ar Allah ya sa ba'a riga an fara ci ba . Da sauri ta ruƙo hannun falmata da jin zancen abincin nan ya sa cikin ta ya sake yin ƙarar yunwa , Mu yi sauri mu je falmata ! [6/24, 9:58 AM] +234 701 013 7848: Fikrah writers association *MAFARI......* ( _Hargitsin rayuwa_ ) *umm'muaz* 6 Jugum suka yi a ɗosane tsakankanin matsin ƴan mata sa'o'in su da waɗanda suka fi su , da ma ƙasa da shekarun falmata kaɗan "bayan kammala baɗakalar wawason abincin,. Yakaka ni fa koh rabin-rabin yunwar da nake ji bata mutu ba ,wannan abincin sam bai isa ga uwar hanji na ba , me zai hana mu nemi wurin sayar da abinci mu sayi wani da kuɗin hannun mu ? Kiyi hakuri falmata mu jira na dare tun da kin ga yanzu la'asar yayi ,idan yaso da daren sai mu shirya salon cin abinci , tun da kin ga dai yadda muka sha gumurzun kokuwa kafin mu samu ƴan lomomin da yanzu suke cikin mu . Toh yakaka ,Allah ya kaimu ɗaren . Cikin wani irin yanayi na tausayawa yagana take kallon yakaka wacce koh lomar abinci ɗaya bata sa cikin bakin ta ba , domin duk kokuwar da ta sha idan ta ɗebo abincin maimakon ta sanya a bakin ta , lalubar hannun ƙanwar ta take ta zuba mata , Cikin neman son su shirya bayan ƴar hatsaniyar da ta shiga tsakanin su ,"yakaka ta sakarwa yagana murmushi tare da riƙo hannun ta , mun gode yagana ba domin kin kira mu ba ,"da baza mu samu abincin ba" Murmushi yagana ta mayar mata ,"babu kome yakaka mun riga mun zama ƴan uwa " Waiwayawa tayi ga wata budurwar da take zaune kusa da ita "ta ɗuƙufa sosai wurin soka allura da zarewa a jikin hular da take ɗinkawa ", Dan Allah kawata koh zaki gwada mana banɗaki muna so muyi sallah? Cewar yagana Ba tare da ta ɗago daga yin ɗinkin da take ba tace ,idan kuka fita kuyi hannun ku na dama ku miƙe sosai zaku tarar da banɗaki a jere amma ku kula hudu daga cikin takwas ɗin basu da kyau duk sun tsage sun farfashe ba'a amfani da su dan gudun su rufta da mutum . Godiya sosai suka yi mata dai-dai lokacin da suke miƙewa . Da ido yakaka take bin farfajiyar da take dauke da banɗakunan da kallo cikin wani irin yanayi na tsantsar kyankami domin duk da kasancewar su mutanen ƙauye ," suna da wadatar tsafta basa barin muhallin su cikin dagwalon ƙazanta ," Cikin ɗaukewar numfashi falmata tace kai yakaka wannan banɗaki da wari yake da alama babu wadatuwar tsafta , ni dai gwada min inda zan yi alwalar . Koh kafin ta buɗe baki "yagana ta karaso wurin hannun ta riƙe da manyan gorar ruwan roba wanda mafi akasarin mutanen wurin suke amfani da ita a madadin buta . Itama turus tayi ganin tsimi-tsimin "bahaya" a farfajiyar wurin wasu an turbuɗe da ƙasa wasu kuwa muraran suke a sarari ƙudaje tare da sauran ƙwari suna sukuwa a kai . Da sauri ta kawar da kai tare da tsirtar da wani mugun yawun da taji ya taru mata a baki tace ,"yakaka anya wurin nan kuwa ya dace da wajen alwala ? Gaskiya ku zo mu koma Bata gama rufe baki ba ,"taga wata mata da goyon ƴar ta,  ta zo tayi ƴar tsallaƙe ta tsallake tarin kazantar dake wurin tare da shiga ɗaya daga cikin banɗakin wajen ,"cikin ƴan dakikai kuma wata mace ta fito daga ɗayan banɗakin . Yagana babu yadda zamu yi kin ga kowa dake nan wurin da nan ɗin suke amfani , dan haka muma dole mu bi ayari . Tana rufe baki ta saki hannun falmata gami da tattare zanen ta , ta tsallaƙa cikin dauke numfashi ta nufi bandakin ,"tare da cewa falmata ki jira ni anan kar ki motsa ", Bayan sun idar da sallolin da ke kan su da suka yi ta a ɗanɗaryar ƙasar kan baranda ,cikin rashin wadatuwar suturar da zasu suturce jikin su kamar yadda ya kamata a yayin sallar ," duk da daman ba wani sani suke da shi sosai game da ibadar ba . Tsumu suka yi kowaccen su cikin taɗin zuci ," Ƙarar jiniya da tayi musu kama da ta motar sojojin nan da suka ji ya dumfaro farfajiyar masaukin nasu ,shi ya firgitar da su suka miƙe ba shiri cikin ransu kuwa cike da taraddadin da me jiniyar ta sake zuwa musu a karo na biyu cikin ƙasa da sa'o'in su biyar a cikin birnin na maiduguri ? Sai dai sabanin tunanin su a yanzu ba daga motar sojojin da suke zato bane ƙarar jiniyar take fitowa ba ," daga wasu jerun gwanon manyan bakaƙen motoci masu daukar ido tare da kyallin sabuntar dake nuni da tsadar su , karar take fitowa ", Buɗe baki da hanci yakaka,da yagana suka yi suna bin motocin da kallo waɗanda har matukan su suka riga suka sama masu matsaya ," Sai dai basu kai ga sauke numfashin farin cikin da suka riƙe na ganin cewa ba waɗannan sojojin da ganin su ba alheri bane a wurin su ,suka dawo ba , idanun su suka yi arangama da jerin gwanon motocin sojojin daga baya da ma na wasu jami'an tsaron masu mabanbantan kayan sawa wadanda basu kai ga rarrabewa da banbancin su da sojojin ba  ," Mukut ! Yakaka ta haɗiye yawun tsoron da ya cika mata zuciya fal ! Lalubar hannun ta falmata tayi cikin maƙyarkyatar murya take cewa " yakaka, yagana kun ga abun da nake faɗa muku koh ? Ni daman nasan da kyar idan ba gidan bayar da horo sojojin nan suka kawo mu ba ," ai tun daga horon yunwar da aka fara yi mana ɗazu ya ci ace kun fahimci irin kurkukun da muka shigo ," kawai ban faɗa miki bane yakaka , amma tun sanya kafafuna cikin garin maiduguri naji ajikina babu alheri cikin sa , naji cewa akwai wani babban al'amari marar daɗi da zai same mu a cikin sa ," Kuwwar mutane tare da dararrakin su da ya cika musu kunnuwa shi ya katse surutun da falmata take yi cikin ɗimaucewa ta koma cewa "menene yakaka ? Harbi ake ? Kashe mu muma zasu yi ? Toh ku zo mu gudu mana tsayuwar me muke ? Ki nutsu falmata ! Yagana ta furta "cikin ɗan ɗaga murya" a sakamakon surutun da hargowar da falmatan take yi musu cikin ruɗewa ya hana ta , ta gano abun da take hasashe , ganin yadda taga fuskokin kowa a wurin ya yalwatu da fara ,"ta ko'ina bullowa jama'a suke suna tururuwa a harabar wajen ," Da gudu yagana ta dira daga kan baranda kafin ta waiwayo cikin tsantsar farin cikin da kamar anyi mata babban bisharara ,"yakaka falmata ga gwamna wallahi gwamna ne yazo ,gwamnan jahar borno ", kuyi sauri ku taho kar wajen tsayuwa ya cika ," daga haka ta kara da gudu kamar yadda taga sauran jama'a maza da mata suna kwasar gudun zuwa gaban dandamalin da jami'an tsaro suka kewaye ta ko'ina wanda da alama anan gwamnan yake tsaye . Saƙare suka yi a tsaye  cikin rashin sanin takamaimai halin da suke ciki na farin ciki koh saɓanin hakan , a zahiri basa jin wani farin ciki a dan saboda zuwan gwamnan musamman ma ga falmata ," wacce ta sauke boyayyar ajiyar zuciyar samun kwanciyar hankali jin ba zuwa aka yi domin azabtar da su ba kamar yadda ta zata ," sai dai ita bata wani farin ciki da zuwan gwamnan domin rashin sanin muhimmancin zuwan nasa . A hankali yakaka ta fara jaan hannun falmata cikin cewa mu ma muje falmata muga gwamnan kuma muji bayanin sa kin ga duk mutane sun tafi . Bayan gajeren bayanin da gwamnan ya gabatar musu cikin yaren su wanda duk na ban hakuri ne game da halin da suke ciki tare da yi musu alkawurwukan kyautata musu da ababen more rayuwa , sannan a karshe yayi musu albishirin tarin kayan abinci da suke tafe da shi , gidajen sauro , butoci da kuma bargunan rufuwa , ya kuma ƙara da albishirin za'a ƙara musu matakan kula da lafiyar su da sauran bukatun su na yau da kullum, a karshe kuma ya basu dama wasu daga cikin su suka faɗi irin matsalolin da suke ciki a sansanin nasu , inda mafi yawan korafe-korafen nasu ya tafi akan ƙarancin abinci da ruwan shaa,  uwa uba da cizon da sauro da ƙwarin gurin suke musu wanda cizon sauron yake kawo musu mummunar masassarar da har take iya kaiwa ga rasa rayuka idan ya zo da ajali musamman ga mata masu ciki da kananan yara . Bankwana yayi musu bayan da ya basu tabbacin za'a samu sauyi daga yanzu inda ya nemi da a naɗa kwamiti da shuwagabanni a tsakanin su kashi-kashi domin lura da matsalolin su . Nan take aka shiga ihu da kalmomin yabo ga gwamna da tawagar sa har zuwa lokacin da ƙurar motocin su suka bace . Babu laifi , ziyartar da gwamna ya kawo musu sosai ta saisaita ciwukan da suke cikin rayukan al'ummar sansanin yayin da ya haifar da farin ciki a cikin zukatan kashi tamanin na cikin ɗarin mutanen. Idan aka ɗauke falmata wacce har kawo yanzu da ake kammala raba musu gidajen sauro tare da barguna, inda ake haɗa mutum biyu da gidan sauro guda bayan an damƙa musu bargunan su ɗai-ɗaya da buta ɗaya ," dukkanin su ba'a haɗa su da juna ba ,an ware su ne daban-daban yayin da aka haɗa yagana da wannan budurwar wacce ta basu kwatancen inda banɗaki yake , yakaka kuwa da wata yarinyar mace mai yara biyu ƙanana aka haɗa ta , falmata kuma da wata mata wacce take yanayi da zaurawa ,"domin ta wuce a sata sawun ƴan mata ƙanana irin su ,"kuma ita bata da ɗa ," babbar budurwa dai . Babu yadda yakaka bata yi da wannan babbar budurwa da aka haɗa su da falmata akan tayi musu lamini ta bar musu ita da falmata gidan sauron idan ya so sai itama yakaka ta bar mata wajen ta ,"ma'ana suyi musanye wuri," saboda a zahiri ta shiga tashin hankali ganin za'a raba musu wurin kwana da ƙanwar ta ," Amma fir budurwar nan taƙi ,tace ita gaskiya baza ta iya kwana cikin gidan sauro guda tare da mai yara ba , karshe ma ta fatattaki yakaka ta kuma ce idan har ta matsa toh fa sai dai falmatan ta bita su tafi chan su ƙarata "ta bar mata gidan sauron ita ɗaya " Da farko yakaka tayi tunanin su haƙura kawai da kwanan cikin gidan sauron su haɗu su dunga kwanan su tare, sai dai tunowa da korafe korafen da taji ɗazu sun yi da suke faɗin illar da cizon sauron yake yi da har yake iya kisa , yasa taji babu yadda zasu yi dole ta kiyaye lafiyar falmata , dan haka tana ji tana gani aka raba musu wurin kwana da ɗaki ita da ƙanwar ta . Dare ya raba tsakiya idan banda juyi babu abun da falmata take yi gaba daya ta kasa bacci saboda tsananin takurar ta da budurwar da ake kira da "ajus" taƴi duk ta bi ta ture ta, tare da janye mata bargonta ta rufu da shi ,sakamakon sanyin damina tare da raɓa irin na tsakiyar daren yanayin damina ," sakamakon turo ta da ta dunga yi yasa gidan sauron nasu duk ya buɗe sauro da cinnaku masu fiffike sun samu damar shiga ciki sai faman ɗallara mata cizo suke ,"sau biyu tana yunƙurin jaan bargon ta amma sai ajus ta ɗallara mata mintsini tare da haure ta da ƙafa ," Lalubawa tayi ta tashi ta zauna tayi tsumu , gefe ɗaya na zuciyar ta cike taf ! da kewar mahaifan ta da ƴan uwan ta ,"kamar yadda take sake ganin daren na yau ma kamar sauran ukun da suka wuce babu mahaifiyar ta babu mahaifin ta babu ƙannen ta ," duk wani buri da take da shi na samun gamuwa da mahaifiyar ta da sauran ƴan uwan ta taji yana barin ran ta , wani sashi na ranta yana raɗa mata tare da bata tabbacin sun rabu kenan har abada," fashewa tayi da kuka dai-dai lokacin da wata gwarzuwar cinnaka ta sake mallara mata cizo a dokin wuya ,"cikin zubar hawaye take tuno irin kulawar da mahaifiyar su ke basu a irin wannan yanayin na yawaitar muggan kananan kwarin damina sam bata bari su cutar da su ,"toshe kunnuwan ta tayi da hannayen ta biyu a sakamakon rugugin hadarin da taji wanda take da tabbacin ruwan sama gaf yake da tsinkewa A hankali yakaka ta sauke ɗan jaririn mai kimanin watanni biyu zuwa uku daga kan kafaɗun ta a yadda take durƙushe cikin gidan sauron tana ta faman jijjiga shi ,"tayi niyyar kwantar da shi a gaban uwar sa wacce take bararraje , tayi wawiyar kwanciya cinyoyi duk a buɗe kai ba ɗankwali ," cikin addu'ar Allah yasa kar ya farka domin hakika ta gaji da rainon sa tun farkon dare yake hannun ta lokacin da uwar sa ta dungura mata shi tace ta jijjiga shi yayi bacci,  ita ta gaji bacci take ji ,ta jaa ɗayan ɗan nata gaban ta suke shaƙar baccin su ,"sau uku tana ajiye shi amma daga yaji an ajiye shi baya yin minti ɗaya yake sake challara kuka ," cikin gigin bacci da hargowa uwar sa zata ce dallah ta ɗauke sa zai hana sauran mutane bacci . Cikin sa'a har ta kwantar da shi bai tashi ba

Chapter 8 of 111