Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
dadin abincin ,     Ƙarar wayar rahima ita ta dawo da sofi duniyar tunanin da ta lula na son hasaso meye ne a tsakanin doctor hamza da waɗannan yakubayin talakawan ƴan gudun hijirar da har yayi musu matsauki a cikin gidan su ya kuma jiɓanci lamuran su da matukar muhimmanci haka ?? ," Hello big bro ,"   Gasu nan muna tare ma ," cin abinci suke ,"    Rahimar ta kai kallon ta ga yakaka wacce kan ta yake sunkuye ,"    Eh tana ci sosai ma ," to idan sun gama zamu zo yanzu ,"toh !        Yakaka wai inji yayan mu idan kun gama cin abincin muje yana ƙiran ku ,"    Toh suka haɗa baki wurin amsa mata ,"      Ba'a kai mintuna uku ba falmata ta zare hannun ta tare da faɗin ta ƙoshi , ita kuwa yakaka daman ba wani na kirki take ci ba ," dan haka ita ma ta miƙe bayan ta tattare ɗan abincin da falmata ta zubar ,"    Ƙarƙashin rakiyar kallon rainin da mafi akasarin ƴan matan wurin ke bin su da shi suka ƙarasa barin falon suna jin su wasai tamkar an cire musu wani mugun dafi da idanun jama'ar suka zuba musu ," daga yakaka har falmatan ba masu son mutane bane ," rahima ta jagorance su zuwa wurin da doctor hamza ya ce su same shi ," daga kusa da kofar sashin sa ,"     Tun kafin su ƙaraso ya nacewa kallon fuskar ta , da ita kuma ta shagaltu da kallon haɗaɗɗun motocin da suka cika harabar gidan wannan tana wace waccen a haɗuwa ,",   Suna ƙarasowa suka gaishe da shi , ya amsa tare da haɗa musu da tambayar babu dai wata matsala ko ? Kuma sun ci abinci sosai ko ?  Suka tabbatar masa da basu da matsalar kome sannan a ƙoshe suke ,"    Manyan ledojin da aka zubo musu kayayayyakin su da ya saya musu na fitar bikin ya miƙa wa rahima , gami da wata madaidaiciyar leda mai ɗauke da tambarin ', down town, "     Ungo rahima wannan kayan nasu ne na fitar biki , ki dunga taya su shiryawa ,    Ta sanya hannuwan ta biyu ta karɓa tana ƴar dariya ,"    Eyeeh gobe su fatima za'a chanchare  gaskiya fatima kin kwace min fada wurin big bro ," ta ƙarasa zancen da sigar zolaya , tana kashe idon ta ɗaya ,"       Ɗan murmushi su duk biyun suka yi cikin ran su suna jin daɗin kulawar da yake basu tare da kyautatawa , hakan ke ƙara sa yana sake girma da ƙima a idon su ,"      Ba tare da ya kula da zantukan ta ba yace ,"     Ga shi tare da miƙa mata ƴan mukullayen sashin sa , daga yau zuwa lokacin da za'a kammala bikin ku dunga kwana ke da su a sashi ne , daga ke sai su , bance ki haɗo min gayyar ƙawayen ki su ɓata min waje ba , ki kiyaye ,"      Ya ƙarasa zancen da sigar gargaɗi fuskar sa babu alamun wasa ,"    Toh    Kai kuma aina zaka dunga kwana ?   Tare da baƙi a sashin baba ya amsa mata yana barin wajen ," bayan ya basu umarnin su tafi su kwanta dare ya soma shiga ,"    Da zumuɗi rahima tayi gaba suka bi ta a baya ,    Tab lalle yakaka ku ƴan gatan big bro ne , baya fa son kowa ya shigar masa sashi , kana shiga zai fara korar ka kar ka kai masa datti , daga ka fita kuma sai yayi shara ya goge kujerun sa , bala'in tsafta ce da shi kamar mai aljanun tsafta ," ta furta hakan daidai lokacin da ta sanya mukulli ta buɗe ƴar babbar kofar mashigar sashin nasa ,"      Suna sanya kafafun su ciki ," kowaccen su tana gaskata kalaman rahima da ta ce yayan ta mai bala'in tsafta ne , saboda tuno haɗuwar su ta farko yadda ta kaya a tsakanin su , ta yadda ya fututtuke ya ci mutuncin su akan ƙazantar da falmata tayi masa a ofishin sa , wanda a lokacin da za'a faɗa musu doctor hamza mutumin kirki ne mai tausayi da kyautatawa irin yadda yake musu a yanzu zasu ce ,"ƙarya ne ," to ashe aljannu tsafta ne da shi , kamar yadda suka ji daga bakin ƙanwar sa ,"   Ƙamshin furanni tare da sanyin ban ruwa da aka yi a wurin zuwa wani ƙamshi na musamman da yake tashi a ƴar harabar sashin nasa suka haɗu suka bayar da wani irin yanayi mai daɗi tare da samar da nutsuwa ga zukata , "     Lumshe idanun ta yakaka tayi ta buɗe tana mai yawo da idanun ta a kowanne kusurwa ta wurin , ƙwarai yanayin wajen da tsarin sa suka burge ta ,"     Ƴar barandar da take ɗauke da ƙofar falon nasa rahima ta taka ta buɗe kofar tare da tura ta ta sanya kai tana cewa su yakaka ," su shigo ," Sanyi da kalolin ƙamshin da ɗakin yake suka sa falmata sakin wani gauron numfashi da tun shigowar su sashin take ta jaan iska ta hancin ta tana jin wata nutsuwa ta musamman na ratsa ta ," tsafta tayi a rayuwa ," Cikin shauƙin yakaka ta dunga bin falon da kallo ɗan madaidaicin falon da baya ɗauke da duk wani nau'in tarkace , kome ka gani a falon amfanin sa mai muhimmanci ne kuma yana bigiren da ya dace , Tun daga kan ƴan madaidaitan kujerun da suka kewaye falon tare da lallausan kafet har zuwa kan labulayen duk suna ɗauke da launi guda ne ,"ruwan madara ,"  sai gefe guda kuma girkakken gogaggen teburin katako ne shima ruwan madarar da ƴar kujerar sa wanda aka ajiye wata ƴar computer tare da tulin littatafai akan sa ," daga ɗaya sashin kuma ƙaramin firiji ne ,' daga haka babu kome a cikin falon sai sanyin AC da yake daga jikin bangon ɗakin sai kuma ƙamshin mai ɗakin da ya riga ya kama ko'ina na wajen ," A ƙasa suka zauna daga su har rahimar da take ta basu labarin party da suka halarta yau , " lokacin da take zazzage kayan da suke cikin leda ta ɗora da basu labarin , bikin da za'a yi na gobe har sai ya fi na yau haɗuwa da yin kyau domin a na goben har da tawagar ango da abokai/dangin sa waɗanda zasu iso a gobe da safe ,'    Woww wayyo Allah  yakaka wanɗannan ɗanɗasa ɗanɗasan rigunan dan Allah aina big bro ya sayo muku ,? Wayyo Allah ,"     Haƙoran ta a buɗe falmata ta fara bata labarin shagon da suka je ,' a ƙarshe ta zame ɗankwalin ta , baki siɗik ɗin gashin ta mai cika da tsawo tare da ƙauri ya bayyana ,"     Kin ga ma har kai sai da aka wanke mana ," ta ɗora da tambayar kin ga takalman da ya saya mana koh ? Su ma masu kyau amma ni dai kamar bazan iya sawa ba dana gwada Su naji  sun min tudu ,"    haba ! zaki iya sawa mana fatima , kuma wallahi ba ƙaramin kyau zaki yi ba ,     Wanne ne naki yakaka , wanne ne na fatima ,?    Ware mata su tayi Rahimar ta cigaba da santin kyaun kayan , a ƙarshe tayi alƙawarin taya su ƙwalliya tare da shiryawa ," inda har ta zaɓar musu waɗannan dogayen rigunan a matsayin kayan da zasu sa a gobe da yamma dai-dai lokacin da za'a fara gudanar da wushe-wushe a ɗora da sanya lalle ," ɗaya ledar ta jawo ta cire musu shawarman da take ciki naɗi uku kowacce ta ɗau ɗaya suƙa fara ci suna ƴar hirar su , har zuwa Lokacin da bacci ya ɗauke su ,"! ******** Misalin sha ɗaya na daren Alhamis biyamuradi youssouf ya samu shigowa cikin gari ƙarƙashin umarni da ya samu daga babbar headquarter su dake chan niemey inda aka bashi awanni arba'in da takwas akan ya je yayi uzurin da ya taso masa na gaugawa kamar yadda ya shida musu  ya dawo ,"   Shi ya tuƙo kan sa ya keto dazuzzukan da suke da matuƙar hatsari saboda ƴan tawayen boko haram da suka yi bigire a cikin sa ," À daren ya so yaje ya gan ta har ma su tattuna cikin awanni arba'in ɗin da yake da damar su yake sa ran zai iya fara gyara ɓarnar da ya tafka ,wanda idan ya samu haɗin kan yarinyar ya na san ran zai wanke hakkin ta da ya ɗauka  ya cigaba da istigfari ,  sai dai yadda garin ya ɗau shiru ya sanya shi barin tafiyar zuwa gobe da safe , ta yadda ko da bai same ta ba kai tsaye zai iya samun abokan hulɗar ta wanda su kuma kai tsaye zasu sada shi da ita ba tare da wata wahala ba , Da wannan tunanin ya samarwa da kan sa wurin kwana a hotel ɗin da ya saba zama a lokacin da yake sintirin a garin ,! ******* Tsabar jin daɗin bacci su yakaka ba su suka farka ba sai ƙarfe takwas da ƴan mintoci , hanzari yin sallah suka yi suna dariyar makarar su , duk yadda rahima ta so da suyi wanka a banɗakin dake cikin ɗakin nasa , ƙin shiga ɗakin suka yi , yakaka ta turje tace iyakar su falo nan inda suka kwana baza su shiga masa har uwarɗaki ba ,"cikin zuciyar ta tana gargaɗin kan ta akan su kiyaye zarmewa da yawa ," A gurguje rahima ta kintsa masa falon yakaka tana taya ta , suka kintsa falon tsaf tamkar yadda suka same shi ,rahima tayi musu umarnin da su bar kayayyakin nasu a ɗakin tun da nan ɗin yau ma zasu kwana ,!    Tana sanya mukulli tana rufe kofar falon nasa ƙiran sa ya shigo wayar ta ,"   Big bro ina kwana ,? lafiya rahima ,kun tashi ne ? Mun tashi big bro, " Gamu nan ma muna shirin fitowa ina rufe ƙofar falo ne ,"    Ki bar ƙofar a buɗe gani nan zuwa ku jira ni ," Toh tace tana sauƙe wayar daga kunnen ta ," A shiryen sa yake tsaf cikin ƙananun kayan da suka amshi matsakaicin jikin sa ," fuskar sa babu walwala sosai bayan ya amsa gaisuwar da suke mishi yace ,"    Ina zaku fita ku je da wuri haka ? Ku koma ku zauna a ciki har zuwa lokacin da za'a kammala abun breakfast sai rahima ta karbo muku ," Ba wani wuri zamu ba yaya dakta zamu shiga ciki ne , ko da aiki mu taya su ," ...   Ke da ba isasshiyar lafiya ce da ke ba shine zaki yi aiki ? Akwai masu aiki , ki kula da lafiyar ki ,' ku koma ciki ku zauna ban yadda ku fita daga nan ba ,' !    Big bro amma ni zan iya shiga ciki ko ? Saboda ka ga.... Sarkin surutu ke zaki iya tafiyar ki , amma ki bar musu mukullin a hannun su , idan anyi girki ki kawo musu , ban yadda ki ɗebo gayyar ƙawayen ki ba , ki kiyaye  . Toh big bro ta amsa tana jiran ta ji ya jerowa su yakaka sharuɗan kula masa da ɗakin sa , ga mamakin ta sai gani tayi ya juya yayi tafiyar sa ,      Da sassarfa ya isa ga motar sa ya buɗe ya shiga ya jaa yana mai barin harabar gidan ya nufi gidan da mahaifiyar sa tayi matsuguni cikin sa , zuciyar sa sam sam babu daɗi ,saboda saƙon da yake ɗauke  da shi akan harshen sa zuwa ga mahaifiyar ta sa ba mai daɗi bane    Ya rasa mai ya sauyawa mahaifin su ra'ayi bayan wahalar da ya sha kwana da kwanaki ,wurin roƙon sa akan ya amince mahaifiyar su ta tako gidan ayi bikin zainab ɗin tare da ita , da kyar ya samu nasarar shawo kan sa ya amince da ta zo tayi kwana biyu a kammala biki ta koma , sai dai a daren jiya ya sake birkice masa akan rashin amincewar zuwan ta gidan har ma yayi ikirarin idan har ya samu labarin ta zo zai mummunan saɓa mata ,    Fir yaƙi saurarar sa yaƙi yadda da duk wasu kalaman rarrashi da yake nufin yi masa ,'  yasan mahaifiyar su mai tarin laifuka ce , amma ƙwarai yadda mahaifin su yake nisanta su da ita yana matuƙar damun sa kome lalacewar uwa uwa ce ,"ba'a sauyawa tuwo suna ," Da wannan tunanin ya ƙaraso unguwar gami da karya kan motar sa ya gangara , kamar yadda yake a koyaushe unguwar cike take da yara ƙanana suna ta dawurwura a kan hanya , wasun su ko wondo babu , bare takalmi a kafafun su , batun wanka daman babu shi ," hakan ya sa yake tuƙa motar sannu a hankali yana sakin hon lokaci -lokaci saboda yaran da suke ƙaraƙaina , basa ko tsoron mota ,"    A ƙarƙashin ran sa kuwa har yau bai daina mamaki da son sanin dalilin da ya sa mahaifiyar su zaɓar rayuwar da take yi a wannan ƙazamtatciyar unguwar marar fasali ba , iyakar tunanin sa da tambayoyin da ya sha yi musu daga ita har abban su an rasa mai bashi amsa takamaimai , "   sai dai yasan koma menene ya faru ne bayan tafiyar sa makarantar gaba da primary ta gwamnatin tarayya ta kwana ,inda bayan dawowar sa hutun zango na farko na aji ɗaya , ya tarar da baki ɗayan rayuwar gidan nasu ta sauya , na farko dai bai tarar da auntie su RAHIMA a gidan ba sai sabuwar RAHIMA jaririyar ƙanwar sa ya tarar ,' abubuwa dayawa marasa daɗi ya tarar suna ta faruwa daki-daki wanda a ƙarshe ya jawo rabuwar auren iyayen nasu , da kawo karshen duk wata soyaƴyar da ya buɗi ido ya tarar iyayen su nayi wa junan su , hakan ya jefo mahaifiyar su cikin wannan rayuwar da take wanda yake jawo mata zagi da zargi tare da aibatawa daga dangin mahaifin su da shi kan sa ,," abun da hasashen sa yake bashi a koyaushe shine , koma menene ya jawo tarwatsewar rayuwar auren iyayen su yana da nasaba da auntie RAHIMA , wacce har zuwa yau da ake ɗiban shekaru wurin goma sha takwas babu wanda ya san ina take , a wane hali take cikin duniya ??? Wani ƙaƙƙarfan hon da wata mota dake biye da shi ta sakar masa shi yasa ba shiri ya kauce ya bashi hanya da mugun gudu motar ta wuce ,"hilux", ce baƙa mai ɗauke da baƙaƙen gilasan da ya sa ba'a iya hangen na cikin motar," Ɗan siririn tsaki hamza ya jaa yana aiyanawa a cikin ran sa wasu dai akwai su da wutar ciki ,    Parking yayi a gaban wani ɗan ƙaramin gida mai ƙaramar kofa dake ƙarshen layin ," ya kulle motar sa ya taka ya hau kan ɗan dandamalin  gaban gidan kafin ya leƙa da kan sa cikin ɗan siririn zauren ya rangaɗa sallama  har baki uku lokacin da yake kallon agogon hannun sa da yake nuna karfe tara dai-dai na safe  ," Karfe tara cif tayiwa biyamuradi youssouf a cikin rumfar madam saly , inda ya jaa ɗaya daga cikin kujerun wajen ya zauna ba tare da ya kula kowa ba ,  rarraba ido yake cikin nutsuwa yana neman fuskar ta a tsakanin fuskokin ƴan matan da suke ta kai kawo a gaban sa ," suna cigaba da gyaggyara tare da goge kujeru zuwa  kan teburan da suke cikin rumfar , domin ba'a riga an fara sayar da burkutu ba tukun , Karo na uku yagana ta ɗago kan ta tana sake kallon fuskar sa , tabbas shine wannan ɗan gayun balaraben mutumin da yakaka tace ɗan uwan ta ne ," Haɗa ido suka yi ta sakar masa murmushin da ke nuna alamun sanayya ,     Kallon ta yayi ya watsar gami da sake musƙutawa bayan ya daɗa ɗaure fuska tamau , cikin abun da bai fi mintuna biyar ba ya fara gundura da zaman , shi mutum ne wanda bai ƙaunar jira , yafi son daga ya buƙaci abu to ya samu ," Ajiye ɗan tsumman goge-gogen da yake hannun ta yagana tayi gami da nufo inda yake ," Sannu da zuwa malam. Yi yayi kamar bai ji ta ba yana nacewa kallon ɗaya daga cikin sabbin ƴan aikin da madam saly ta maye gurbin su yakaka da su ," farin ta ya jaa hankalin sa daga nesa yayi zaton ko wacce yake nema ce , sai da ta matso kusa ya fahimci ba ita bace domin wannan daga ganin ta ma hasken na bilicin ne ga fuskar tata wani wuri jaa wani wuri ruwan hoda wani gun kuwa brown ne ma , haka take dai dabbare-dabbare , ɗauke kan sa yayi dai-dai lokacin da ita kuma take farga da kallon da yake bin ta da shi nan take ta watsa masa signal da ido tana wani mokaɗe baki ! Gyara tsuyuwar ta yagana tayi ," Unm nace ka zo wurin yakaka ne ?? Maida hankalin sa yayi kan ta ji da yayi kamar ta ambaci sunan ta , sai dai matsalar shi bai wani riƙe sunan nata ba , amma tabbas kamar ya ji ta taɓa ambatar sunan ," Wata ɗiya nake nema , tana aiki anan doguwaa ce fara , tana da tsaga bisa ƙuncin ta , idan kin san ta ki sada ni da ita zan biya ki ," Karkaɗe jikin kayan ta yagana take lokacin da ta fahimci bayanin sa wanda yake sake tabbatar mata da zaton ta na ƙarya yakaka tayi mata da tace wai ɗan uwan su ne , domin ga shi ko sunan ta bai sani ba tabbas  wata alaƙa ce ta daban a tsakanin su ," YAKAKA TAYI CIKIN SHEGE MADAM SALY TA KORE TA DAGA GIDAN NAN, BABU WANDA YA SAN INDA TAKE . Ta furta hakan lokacin da take gyara zaman rigar ta cikin halin ko in kula , Wani irin abu biyamuradi ya ji tsuwww yana yawo a cikin kan sa tare da kalaman da yarinyar nan ta furta masa ," kusan bai ma fahimce ta sosai ba , dan haka ya saita idanun sa cikin nata tare da tattaro duk wata nutsuwa da yake da ita ya sake maimaita mata kalmomin da yayi amfani da su wurin tambayar ta ɗaya bayan ɗaya dalla-dallah kamar mai koya mata karatu ," Sake maimaita masa amsar tayi kamar farko ," lokacin da take taka kafafun ta tana barin wurin , tare da turniƙin kishin da ya tattare mata a ƙahon zuci , saboda tashin hankalin da ta gani a fuskar sa baro-baro yana nuni ne da kowacce irin alaƙa ce a tsakanin sa da yakaka mai girma ce ta kuma taka wani matsayi mai muhimmanci a wurin sa , " tare suka zo maiduguri da yakaka amma a sarari yake bayyanuwa yakaka ta fita sa'ar shigowa garin ,' tun akan wannan kyakkyawan ɗan gayun likitan da ya gigice a neman ta ta fahimci hakan ," wannan mai kama da larabawan kuma ko menene alaƙar sa da yakakar  oho ?? Ko ma menene ta sha alwashin sai ta rusa duk wani tubalin nasara a rayuwar yakaka ," Wani irin yanayi na ruɗani ya shiga da tunanin sa yake kufce masa da hakan har ya sa bai ma san lokacin da yagana ta bar gaban sa ba ," kalmar cikin shege kawai ita ke maimaituwa a ƙwaƙwalwar sa tana fasa kan ta tana sake dunƙulewa wuri guda tare da yin wajajjawa cikin tunanin sa ," wani irin ƙugi cikin sa yayi da yake bayyana halin tsoro da ya shiga lokacin da tunanin sa ya tattaru wuri ɗaya ya chanko masa yarinyar tana ɗauke da cikin sa ne ba cikin shege ba ," Kamar wanda aka tsikara ya miƙe tsaye akan kafafun sa yana wurga idanun sa kowanne lungu da saƙo yana neman yarinyar sai dai ko alamun ta bai gani ba kamar wacce ta ɓace , Wata irin damƙa ya kaiwa kafaɗun wannan koɗaɗɗiyar yarinyar da barin yagana wurin ya sanya ta tahowa gaban sa tana wata ƙwarƙwasa , Ƴar ƙara ta saki saboda yadda ƙasusuwan kafaɗar ta suka amsa da jin ruƙon soja ba da wasa ba ," muryar sa ta tsinkayo da wani irin yanayi da amon ta yake bayyana tsantsar tashin hankalin sa ," Ke wacece madam saly  ?  Yi maza ki sada ni da ita a yanzu yanzu ," A tsorace take kallon sa har sai da ta firgita ganin yadda fuskar sa tayi jaa jijiyoyin kan sa suka fito tar kore-kore ,    Ma-ma-madam bata tashi.... Tsawar sa ta katse ta ," Ki gwada min inda take nace yanzu yanzu ,"   T-toh sake ni muje na kai ka wurin ta ," Wucewa tayi gaba ya bita , har zuwa cikin gidan ƙofar ɗakin madam saly , ta tsaya daga bakin kofar ,"   Madam ina kwana ? Kin yi baƙo ne yake son ganin ki ," Daga ciki ta amsa , Wanne ɗan»»» yake nema na da sassafen kamar naci bashin uwar sa ban biya ba to bill..... Wata irin fincika ta ji anyi mata kafin ta fahimci meke shirin faruwa ta ji an watso ta waje daga ita sai wata ƴar guntuwar rigar baccin ta iyakar guiwa irin gumamar makkah ɗin nan , sillalliyar ƙeyar ta sai ɗaukar ido yake a hasken hantsi ," Kutuma..... Tace tana ɗago kan ta tare da miƙewa tsaye daga dunguren da tayi ,"     Arba tayi da biyamuradi youssouf , fuskar nan tasa yariman sa sak ," A take ta gane shi dan haka ta ƙanƙance ido ,' !    Lalle toh sannu uban uba na da zaka zo ka wani figoni haka toh idan ma ita karuwar taka ce ta aiko ka kazo ka mun wannan rashin mutuncin toh daga ita har kai kun yi kaɗan aikin ban...... Marin da ya waske ta da shi ya hana ta cigaba da bayani sai ma ganin duhu duhu da ta fara , ba shiri tayi faɗuwar ƴan bori tare da sanya wani kakkarfan ihu ," Ihun ta ya sa duk mutanen gidan rugowa da gudu zuwa wajen,  Har da ɗan liti da shima yake sawo kan sa cikin gidan ,  ya ɗebo da gudu har yana bangaje yagana wacce ita kuma take komawa baya saɗaf-saɗaf bayan da ta leƙa ta ga mutumin nan ne tare da madam saly," Meke shirin faruwa ,ko kuwa ya faru ?  da nake jiyo ihun giwar mata , ai wallahi ramar giwa kunyar daji , ace muna nan tare da ke kike sakin irin wannan ihun uwa wacce maciji ya sara ina macijin yake ??   Ya ƙarasa zancen yana bangazo larki ya faɗo tsakiyar filin Daidai lokacin da youssouf ya ɗago kafaɗun madam saly tare da saita ƴar ƙaramar bindigar da ya fiddo daga aljihun wandon sa a kanta ," muryar sa a kausashe a tsaƙanin maƙoshin sa yace mata Ina kin ka kaita ? Tana ina ? Duk inda take ki nemo ta , Wata irin zilliya ɗan liti yayi ya koma  bayan hema ya ɓuya, yana cewa      Na shiga uku an fasa aure nah ! Wata irin karkawar tsoro madam saly take ganin mutuwa kusa ," laɓɓan ta suna rawa tace Wallahi billahil azeem ka dai ji rantsuwar musulma kenan ko ? ba ni na kori yaks ba ita da kan dare ɗaya ta haɗa kayan su ita da ƙanwar ta suka bar gidan nan cikin dare babu wanda ya ga tafiyar su , ko jama'a ? ta maida tambayar ga mutanen da suke tsaye charko-charko an rasa mai cewa uffan a cikin su Sake danna mata bakin binɗigar yayi aka ,tamkar zai nitsar mata da shi cikin ƙoƙon kan ta yace ,"     Ƙarya kike ke kika kore ta kin san inda take , na baki awanni ishirin da huɗu ,zuwa gobe iwar haka ki

Chapter 33 of 111