Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
mu ," Ƙai hannunta tayi ta lalubo fuskar yakaka jin tayi shiru bata cewa kome duk bayanin da take yi , nan taji ruwan hawayen da suka faca-faca akan fuskar ta ," share mata hawayen tayi kafin a hankali ta kai kanta ta ɗora akan kafaɗun ƴar uwar ta , idan ke kika yi kuka a halin yanzu ni me kike so nayi yakaka ? ,kiyi haƙuri ki daina kuka insha Allah zamu haɗu da maman mu ," Nemo yatsun hannun falmatan tayi ta sarƙe su cikin nata hannun "falmata ba ina kuka bane a domin wahala koh raunin zuciya akan halin da muke ciki ba," ina kuka ne akan tunanin halin da mama da ƙannena suke ciki ina kuka akan wahalar rayuwar da kike ciki a halin yanzu alhalin bani da karfin taimakon ki ,"dubi kafar ki falmata ta ɗago kafar falmatan da take ɗaure da ɗankwalin ita yakaka," Duk ƙafar ta soke da kayoyi daga idon sawun ƙafar kuma a kumbure yake in da ta faɗa rami a jiya ," Falmata tun tasowar mu ban taɓa ganin ciwo irin wannan a jikin ki ba ,"duk da cewa muna rayuwa cikin talauci amma iyayen mu suna tattalin mu ,da lafiyar mu" amma ki duba daga shekaranjiya zuwa yau da rikon ki ya dawo kaina na gaza wurin baki kulawa gashi duk kin ji rauni ," sai nake ganin laifin kaina da zan iya falmata da goyon ki zan yi nasan da mama ce da ta sauke Bulama ta goye ki amm dubi ni ... Ɗago kan ta tayi tare da toshe mata bakin ta da hannun ta ," fuskar ta babu walwala tace yakaka daga yanzu ki daina ganin laifin kan ki akan duk wani abun da kaddara zata ɗoramin ," Sannan ki daina ganin kamar ni a dalilin bani da ido bazan iya yi wa kaina kome ba ," wasu abubuwan zan iya yakaka ,"a yanzu rayuwa ta sauya min ta inda nake ganin dukkanin wasu abubuwan da a baya bazan iya su ba a cikin sabuwar rayuwar da zamu fuskanta zan iya su ," abun da nake so kawai kar ki taɓa ɗauke matsayin ki na wacce take gaba da ni a koyaushe kika ga zan faɗa rami ki taro ni kin ji yakaka ? Naji Falmata sai dai nima ina son ki bar min matsayina na yayar ki a duk lokacin da na nuna cewa nice gaba da ke wurin baki kulawa ,"kin ji koh ? Ɗan siririn murmushi tayi " naji yaa yakaka ," A hankali yagana ta sanya babban ɗan yatsan ta, ta ɗauke ƙwallar da ta gangaro mata daga cikin ido ," tana tausayin kan ta sosai da sosai tun tasowar ta kasancewar ta tashi ne ba tare da mahaifan ta ba mahaifiyar ta rasu tun tana yarinya yayin da mahaifin ta ya tafi ci rani ,"tun tana shekaru goma har yau bai dawo ba "dan haka a hannun kakar ta mahaifiyar Baban ta ta girma" sai dai daga jiya zuwa yau ta sake tausayawa kan ta a sanadin ganin tsaftatatciyar soyayyar ƴan uwan taka da take gudana tsakanin yakaka da falmata , wanda ya sa ta fahimci ba ƙaramin gibi take da shi a cikin rayuwar ta a sakamakon rashin dan uwa koh ƴar uwa da take da shi ba ," sosai soyayyar da ta lura tana gudana a tsakanin ƴan uwan biyu ta birge ta tare da bata sha'awa . Ajiye ƙoƙon ta"wanda ta riga ta shanye madarar ciki tas " tayi a gefe tare da miƙewa ta nufi wurin da har yanzu yakaka da falmata suke zaune ,"sai dai saɓanin ɗazu yanzu a jere suke a zaune inda falmata ta matsawa yakaka ta zauna a gefen ta suna fuskantar mahuɗar rana da ta fara ɗagowa tana keto tsakankanin ciyayin , ranar ta bada wani haske mai kyau ," Dafa kafaɗun su tayi da hanun ta ɗai ɗaya ," idan an gama tattaunawar sirrin tsakanin ƴan uwa a tashi mu tafi mu mayar musu da ƙoran nasu kafi su gama shiri su fara jiran mu kuma ,"kun san dai sun ce da wuri zamu kama hanya saboda miƙaƙƙiyar tafiyar da ke gaban mu ," murmushi yakaka tayi ," yagana baki da dama ," Satar kallon falmata yagana tayi wacce ko alama bata nuna ma taji abun da yaganan ta ce ba ," Kamo hannun falmata ," yakaka tayi da sauri yagana ta zagayo tare da kama mata ɗayan hannun ,"amma ga mamakin su sai ji suka yi tace "zan iya tashi da kaina ,! Yunƙurawa tayi amma sai suka ga ta kai hannun ta gami da lalubar hannun yakaka ta rike gam gami da miƙewa a hankali ,"hakan da yagana ta gani ya sa ta fahimci falmata bata so ta ita ta taimaka mata sai ƴar uwar ta "ɗan tabe baki tayi cikin nuna ko oho ", ***** To kun ga nan shine karshen dajin konduga daga nan ai gashi kuna iya hango gidajen da suke ta cikin yankin unguwannin Birnin Maiduguri ,"wadancen gidajen da kuke iya hangowa daga nan suna cikin unguwar da ake kira dalori ne , kuna ƙarasawa can kun riga kun shiga birnin Maiduguri ," mu daga nan muke sake komawa mu ɗauki hanyar in da muka nufa ," wannan dogon bayanin yana fitowa ne daga bakin bafullatanin mutumin nan ,"bayan sun kawo su yakaka iyakar dajin yankin konduga da cikin garin maiduguri ," Nan take su yakaka suka durkusa akan guiwowin su suna masu jero godiya da tarin addu'o'i ", zuciyoyin su kuwa ƙwal kamar an musu bishara da wani babban abun Alkairi," Da murmushi ɗauke akan fuskokin fulanin nan su biyar "da alama sun baro sauran a daji tare da dukiyoyin su (shanun su ) suke amsa jerun gwanon addu'o'in su yakaka ," kafin mutumin ya ɗora da cewa toh yaro sai ku kula da kan ku sosai ,maiduguri babban gari ne sosai domin haka sai kun yi taka tsantsan da kome , da mu ƴan gari ne da zamu sanya ku a hannun wasu da muka sani to mu ma bamu san kowa ba cikin maiduguri," Sanya hannun sa yayi a aljihu ya zaro wata tsohuwar naira ɗari biyu ya damƙa a hannun falmata wacce ya lura bata gani ," daga haka suka yi musu sallama tare da juyawa suka ɗau hanya abun su ba tare da sun sake waiwayawa ba ," Shirun dakikai biyu zuwa uku ne ya gitta tsakanin ƴan matan uku bayan juyawar fulanin zuwa inda suka fito ,"ga su dai ga birnin maiduguri bayan doguwar tafiyar da suka yi na kimanin kilomita 74-76, akan kafafun su daga ainahin garuruwan su , da kuma tarin ƙalubale da hatsarin da suka shiga a yayin tafiyar ," wanda ya kamata ace a yanzu da maɗaukakin farin ciki za su durfafi birnin na maiduguri , to sai dai a halin yanzu da fulanin nan suka juya tare da tafiya suka bar su a faffaɗan fili sararin Allah da ya tafi ɗoɗar daga nesa suna hango gidajen jama'a da fulanin nan suka tabbatar musu gidajen cikin birnin maiduguri suke ," sai duk suka ji zuciyoyin su sun raurawa ,'akan tunanin ina kuma suka dosa ? Ina zasu nufa ? Falmata ce ta katse shirun nasu a yayin da ta tattaro gutun yawun bakin ta da ya gama bushewa a sakamakon ranar damina da aka bude a yau ", Yakaka tsayuwar me muke yi ne kuma ? Kamata yayi mu ƙarasa cikin garin mu fara da neman maman mu a yau ɗin nan kin ga idan Allah ya sa muka ganta kafin dare ,"yau baza ta shiga cikin lissafin ranakun da zamu ƙara kwana ba tare da ita ba ko kuwa ? Mukut ! Yakaka ta haɗiye guntun yawun da ya saura mata a baki ," Falmata a yadda fa nake hango girma da yawan gidajen da suke cikin Birnin Maiduguri ya sha banbam da irin na garin mu" amma dai bari mu ƙarasa mu gani ," Yunkurawa suka yi tare da kama hanyar suna tafe babu me cewa ƙala ," sun yi tafiya me ɗan tsawo zuwa lokacin da suka fara cin karo da gidajen da suke farko-farkon unguwar dalori Qaurters . Ware ido sosai yakaka tayi tana kallon tsarin gidajen tare da yawan mutanen da ta gani suna ta kai kawon su ," nan take taji zuciyar ta buga da tunanin ina zasu fara bi su nemo mahaifiyar su a cikin wannan faffaɗan birnin ? Ta bangaren yagana kuwa yawan jama'a da tsarin gine-ginen , bai wani zama baƙon abu ba a saboda babu laifi garin su "Bama" shima babbar Alkarya ce wacce take cike da Al'umma da kuma cigaba dai-dai da zamani ," tunanin ta ya fi karkata ga inda zasu je su samu mafaka kamar yadda kafin su fito daga gida a lokacin da labarin shigowar ƴan tawayen boko haram ya baza garin su aka fara guje guje da ƙokarin barin garin ɗaya daga cikin ƙannen mahaifin ta shi ya basu tabbacin idan suka tafi birnin maiduguri akwai mafaka agaresu da musamman gwamnati ta tanada ," Dan haka take taku zuciyar ta cike da son ganin sun isa mafakar ta su ," Ga bangaren Falmata kuwa ita ba ganin garin take yi ba amma hayaniyar muryoyin jama'a tare da ƙarar wucewar ababen hawa da suka cika mata kunnuwa sun isa sanar mata cewa ta shigo wani wuri da ya sha bamban da mahaifar ta me rangwamen hayaniyar jama'ah , ƙarar ababen hawa kuwa sai ranar cin kasuwar garin su take iya jiyo su daga nesa-nesa ," nan take taji tsoro ya kamata sakamakon tunowa da tayi da fannah ƴar makotar su wacce mota ta taɓa bigewa ta karya mata kafafu " , nan take ta lalubo jikin rigar yakaka ta haɗa da jikin tata rigar ta sake ƙullewa ," sannan ta sake jefa hannun ta cikin na yakakar wacce ita ma ta rike hannun falmatan gam-gam . Cikin mutuwar jiki suke tafiya a lokaci guda yunwar da take ƙwaƙular cikin su tana tuno musu da rabon su da sanya wani abu a cikin su tun madarar da suka sha da safe ga shi dai yanzu azahar ta yi domin suna iya jin kiran sallah daga massalatan da suke cikin unguwar,"Yakaka idan muka samu wurin da ake sayar da abinci mu tsaya mu saya kafin mu isa ga masaukin mu ," Uhm yagana wane masauki kike zance a yanzu bayan duk alamu sun bayyana a garemu bamu da hanyar da zamu bi ta sada mu da gidan gwamnatin ,"idan kuma kina da hanyar sai ki faɗa ," cewar falmata , Yagana Jaan bakin ta tayi ta tsuƙe domin ta lura ba wani birge falmata take yi ba a kome ," a gefe guda kuma na zuciyar ta ,tana me gaskata zancen falmatan tabbas , ganin kitse take yi wa rogo a duk zaton ta suna tako kafafun su cikin garin maiduguri zasu tadda jami'an da aka ce suna bada tsaro ga mutanen maiduguri zasu chafe su ,tare da sada su da masaukin su cikin farin ciki da walwala ," Sai dai tabbas a yanzu tana iya hango yiwuwar sauyawar tunanin ta "wanda ya sanya ta hango kanta a matsayin wacce tayi masauki a kan bola " da hakan ya sanya ba shiri ta fara zare idanu tana kallon mutanen da ta lura su ma a halin yanzu kallo suke bin su da shi a duk inda suka gifta . Duk ba wannan ba yanzu abun da yakamata mu fara yi shine mu samu wuri muyi sallah daga nan sai mu fara tambayar mutane hanyar masaukin da kika ce an tanada ga irin mu ,"koh me kuka ce ,"Yakaka ke furta hakan bayan ƴar gajeruwar muhawar da taji falmata da yagana suna yi , Cigaba suka yi da kutsawa cikin unguwar suna neman wurin yin alwala har dai suka yanke shawarar tsayawa a dai-dai wata mahaɗar da ta fi kama da tashar tsayuwar motoci saboda yawan ababen hawan da suka gani a wurin ,"sai dai yawan masu saye da sayar a wurin kama tun daga kan masu ɗanyen kaya ,da masu kayan abinci na awu ,"har ma zuwa masu saida dafaffen abinci da kuma masu toye-toye , ga kuma ƴan tebura nan dangin su masu saida biredi da sauran su ya sanya su hasashen ƙila kasuwa ce," tsayawa suka yi a wurin suna rarraba idon neman wurin da zasu samu damar Alwala , Daga gefe kaɗan da su , suka hango masallaci wanda rumfar kwano ta kare gaban sa mutane suna ta Alwala wasu kuwa sun kammala alwala suna sallolin su a cikin rumfar ," Ɗan yawatawa da idanun ta yakaka tayi tana neman ruwan Alwala ,"sai dai yawan idanun da ta gani akan su ya saka ta cikin firgici ,"kusan illahirin mutanen wurin hankulan su da idanuwan su akan su yake ," kuma idan ba idanun ta suke mata ƙarya ba kusan duk mutanen wuri ɗaya suke kallo a jikin su", daga kan kirjin su zuwa cikin su ,'! A hankali ta sauke idon ta tabi inda suke kallo a jikin su ta gani koh wani abun ne a jikin nasu ," Hannu ta kai tare da gyara wuyan rigar ta da ya ɗan saɓule lokaci ɗaya kuma tana kai hannu ta gyarawa falmata ita ma nata wuyar rigar , duban ta 'ta mayar kan yagana wacce ta fahimci ita ma ta lura da irin kallon rashin yaddar da illahirin mutanen wurin ke bin su da shi ," Ƙasa tayi da muryar ta "yagana kin lura da irin kallon da mutanen nan ke bin mu da shi ? Koh daman haka mutanen birni ke yin kallon su ? Ina lure da su nima ,"amma ina ga haka suke kallon su "dan yaakura na tace a lokacin da ta kawo ni asabitin tsatsareni da ido likitan nan yayi a cewar ta saura kaɗan ta ɗauke ni mu tafi dan tayi zaton ma koh karama ne (maye ) ɗan guntun tsaki ta jaa a lokacin da suka haɗa ido da wani matashi majiyi karfi yana kallon su tsakar ka, lokaci ɗaya kuma yana danna wayar sa tare da kara ta a kunne "," Jibe shi dan Allah ya wani tsare mutane da ido toh kurwar mu kur ," Falmata kawo kuɗin nan na ƙarasa can na sayo mana ƙosai da doya nan wurin ma jama'a sun yi yawa mun ƙara gaba kawai muyi sallar ," Falmata bata ce ƙala ba ta miƙa mata gudar ɗari biyun da take duƙunƙune a hannun ta "sashi guda na zuciyar ta! Yana gaskata mata zancen su yakaka na cewa da suka yi an zuba musu ido domin kuwa ita ta riga su sanin ana kallon su ,dan tun da suka nufo wurin jikin ta ya bata akwai wani abun cutarwa ko kuwa idanun mutane akan ta ,'duba da yadda taji tsikar jikin ta tana ta faman miƙewa,'hakan shine alamun da ita take fahimtar akwai matsala a wuri "baiwar ta kenan" , a gefe ɗaya cikin ranta kuwa cike fal! Da haushin yagana akan yadda take nuna ita fa ala dole ta fi su sanin maiduguri Alhalin kuwa su da ita duk sammakal tilo ," basu da wani bambanci. Taku biyu yagana ta yi suka fara jiyo tsuwwar wani abu wanda basu san ko meye bane ,"yayin da hankalin su ya kasu biyu ɗaya akan mutanen da suka ga sun fara guje guje wasu ma har suna barin kayayyakin sana'o'in su ,gefe guda na hankalin su na ga kan tsuwar nan da suke ji tana sake durfafo inda suke , so suke su fahimta akan wannan tsuwar ne mutanen ke gudu koh kuwa meye dalili ,? Yakaka ƙarar meye ne wannan ɗin kuma meyasa naji kamar takun gudun mutane ?falmata ta furta hakan a dai-dai lokacin da take lalubar jikin yakaka tana gyara ƙullin da ya haɗa bakin rigunan su 'da alamun shirin gudu take " Nima ban sani ba Falmta," Yunƙurin buɗe baki yagana take cikin cewa wani abu amma sai maganar ta maƙale mata a fatar baki.' sakamakon ganin manyan motocin da suke ɗauke da irin fentin da suka gani a jikin jirgin saman nan da yayi musu ɓarin wuta a daji ," a take suka fahimci ƙarar nan da suke ji daga jikin motocin nan take fitowa . Ɗurum dum ,"bugun sautin zuciyoyin yakaka da yagana a lokacin da suka yi idanu huɗu da tarin motocin da suke da tabbacin na waɗannan mamallakan jirgin saman ne ,"shikenan mun mutu mun lalace yakaka , shikenan wallahi sun biyo mu ne su kashe mu ," Su waye suka biyo mu ? Yagana wai meke faruwa ne ,"cewar falmata da maganganun yagana suka yi mugun ruɗa ta ," Sojojin da suka biyo mu da jirgi a daji sune gasu nan a mota .... Sauran maganar maƙalewa tayi a fatar bakin yagana a lokacin da ta ga gungun sojojin nan suna durƙowa daga bayan manya manyan motocin su hannayen su duk riƙe da bindigogin su da ya sanya cikin yagana ba da wani sautin ƙululu lokacin da tayi arba da su ,"wannan fa shi ake cewa anyi gudun gara an tadda zago ," Jeruwa sojojin suka yi daga nesa kaɗan da inda su yakaka ke tsaye a sandare ko numfashi da ƙyar suke jaa ," Da gudu wani soja ya fito daga cikin gaban wata mota hannun sa riƙe da wata jibgegiyar bindiga ," ɗaga ta yayi gami da jaan kunamar bindigar ƙaraƙat ,'ya saita ta akan su yakaka da zuwa yanzu suke ta ɗigar gumi kamar an tsamo su daga rafi ," Remove your clothes all, " Sasarai su dukkanin su suka yi suna wulwulga idanu cikin rashin sanin takamaimai ɗin abun yi lokaci guda kuma tsoro ya sake cika zuciyoyin su a sakamakon lura da suka yi cewa duk yawan mutanen wurin nan a yanzu basu ga ko mutum guda ba daga su sai sojojin nan ,"ji suka yi zuciyoyin su na barazanar faso kirjin su ., Fahimta da sojojin nan suka yi su yakaka basa jin turanci ya sa ɗaya daga cikin su ɗaga murya ", Ku cire kayan jikin ku idan ba haka ba zamu harbe ku mu kashe ku ," Cikin tsananin firgita yakaka da yagana suka kalli juna lokaci ɗaya suka ji falmata ta rushe da kuka ," Ji suka yi an sake daka musu tsawa Zamu harbe ku idan kuka sake minti ɗaya ," Ba shiri yagana ta fara cire tun daga ɗangalallen hijabin ta har zuwa rigar ta da yanzu take kan cirewa ," Satar kallon yagana ,"yakaka tayi kafin cikin rawar jiki ta miƙa hannu tana warware kullin da yake tsakanin rigunan su ita da falmata lokaci guda tana me cewa falmata ki cire kayan ki idan ba haka ba zasu kashe mu ,: Tsaye suke daga su sai siket din ciki hannayen su rumgume da kirjin su ,fuskokin su kuwa shaɓe shaɓe da ruwan hawayen da ya chakuɗa da majina gami da gumi ," Magana sojojin suka yi a tsakanin su bayan sun gama ƙare musu kallo Daga wurin da suke ," Sir I think they're not Boko Haram girls , there was no bomb in their bodies," ( shugaba ina tunanin waɗan nan. ba ƴan matan boko haram bane , babu nakiya a jikin su ) Yes they're not , (ƙwarai ba su bane ) Daga inda sojan nan ya yake tsaye ya sake ɗaga murya tare da basu umarni su sanya suturun su ," Koh kafin ya ida rufe bakin sa har sun yi nisa wurin sanya kayan nasu ,"tsayawa suka yi suna jiran su sake jin umarni na gaba ,"idanuwan su kuwa basu bar zubar ruwan hawayen wannan tozarci da tashin hankalin da suke ciki ba ," ba ma dai kamar falmata wacce har karkarwa take tsabar kuka ," Gani suka yi ɗai ɗaya da ɗai ɗaya suna komawar su cikin motocin su ,"yayin da suka ga waɗan nan biyu da suke yi musu magana ɗaya da hausa ɗaya cikin yaren da basa fahimtar sa sun nufo inda suke bindigogin su saɓe akan kafaɗun su ," Suna ƙarasowa wannan me jin hausan yace musu ", daga ina kuke kuma ina zaku ? A wannan karon shiru yagana da ta kasance jaa gaba wurin mayar da amsa tayi tana zazzare idanu tare da satar kallon bindigogin hannun su ," Jin yagana tayi shiru ya sanya yakaka ta buɗe bakin ta cikin maƙyarƙyatar murya tare da gurbatatciyar hausar ta tace ", :Umh daman mu ƴan hijira ne daga garin mu shine-shine muka zo nan neman gwamnati ta taimaka mana da masauki ," Inane garin naku ? Ƙauyen mairambiri Magana sojojin nan biyu suka yi a tsakanin su cikin harshen turanci ," Ku zo mu kai ku camp mu ajiye ku saboda idan kun cigaba da yawo haka a gari mutane baza su yadda da ku ba a karshe ma ana iya yi muku dukan tsiya da tunanin ku irin ƴan matan da boko haram suke ɗaura musu nakiya ne , su shiga cikin kasuwa koh taron jama'a su yi ƙunar baƙin wake ," bayanin da sojojin nan suka yi musu kenan bayan sun gama shawara a tsakanin su Nan fa aka shiga kallon-kallo tsakanin yakaka da yagana ," camp ina ne camp ?koh dai gidan horar da mutane ne sojojin nan zasu tafi da mu ? Wannan ne zancen da yake ta kai kawo cikin zuciyoyin su dukkanin su uku lokaci guda kuma suka ji wata sabuwar nadama baki daya ta kama su ,"daman haka mutanen cikin birni suke azzalumai haka kawai sai su hau jibgar mutum ? Tsawar da aka daka musu ita ta sanya ba shiri yakaka ta kama hannun falmata suka bi bayan sojojin nan da su har sun yi juyawar su sun kusa isa ga motocin su tun bayan da suka basu umarni ," Wani irin mahaukacin gudu motocin sojojin nan suke akan tsakiyar titin na Maiduguri ," duk inda suka gifta motoci da sauran ababen hawa darewa suke suna basu hanya ," Tsugunne su yakaka suke a bayan hilux ɗin, sojoji biyu sun sanya su a tsakiya a zaune a kan ɗan tudun da aka tanada domin zama ," ji suka yi iskar shaƙa ta musu yawa a saboda gudun da motar ke yi ,"nan take maƙoshin su ya bushe ƙemas , idan ban da sharar hawaye babu abun da suke yi ,tun da suka hau motar babu me cewa ƙala ," Gware yakaka da falmata suka yi ," a sakamakon wani irin birki da motar da suke ciki ta jaa," wani marayan kuka falmata ta fashe da shi a dalilin zafin da ya ziyarci ƙwaƙwalwar ta a dalilin gwaren da suka yi ", Dira sojojin da su ke tare da su a bayan motar su ka yi kafin su yi musu umarni akan su sauƙo , Tsayawa yakaka-da-yagana suka yi suna ƙarewa wurin da aka kawo su kallo ,"wata babbar kofa ce a gaban su me kama da kofar gari a ganin su, sai da ƴaƴan hanjin cikin su yakaka ya kaɗa sakamakon ganin wasu gungun sojoji da suka yi daga cikin wata rumfa a gefen kofar ," Yakaka ina aka kawo mu ,? Inji falmata ," Nima ban sani ba falmata ,amma dai kamar wani babban gari ne shima gashi dai har da wata babbar kofar sa ," ta furta hakan tana me satar kallon sojojin da koh kula da su basu yi ba," Ku zo mu je nan shine camp (sansanin ƴan gudun hijira ) inda gwamnati ta tanadar ga ire-iren ku ," a cewar wannan sojan da ya wuce gaba ," Da sauri su ka bishi ransu yana wani ɗan motsin daɗi-daɗi ! Duk da cewar dai basu gama aminta da zancen sa ba domin basu tabbatar ba ,' Yakaka da yagana su na sanya kafa cikin wurin suka fahimci ba ƙaramin babban fili bane ta ciki , a yayin da suka fara yawata idanun su zuciyoyin su cike da mamakin ganin mutane birjik fululu iyakar ganin su suna ta harkokin su ," Hayaniyar jama'ar da falmata ta fara ji yana tashi cikin yaren su , shi ya sanya ta ji kaso goma na tsoron da yake cike da ranta ya kau ,! Bayan ƴar gajeruwar tafiyar da suka yi , bakin wani gini sojan nan ya tsayar da su yayin da shi

Chapter 6 of 111