shiyar gidan Youssouf , matar sa ita tayi ƙira na kan cewa na zo fa ga ɗan ouwana ya faɗi yana biɗar taimako na , shine na runtuma da niyyar kai masa ɗauki , da shigata na tadda shi a halin da ku ma kun ka zo ku ka taddo shi , wallahi ni iyakar abunda na shina kenan ban.....
Wata dariyar mai sauti da Maimounatu ta sanya , ita ta katse masa jawabin sa ya mayar da ganin sa kan ta yana ƙif-ƙifta ido , ba tare da ta dube shi ba tace
" Mammadou wallashi cikkin ragwaye kai na ƙurya ne , yo me kake tsoro idan ya tabbata gubar da shi wannan Azzalumin ya ci ta hannun ka ta fitto ? hukuncin kisa ta hanyar rataya ko kouwa ɗaurin rai da rai muddin rayuwa ?
" Burina labarin mutuwar sa ta jishe ni , daga nan koume shi faru dai-dai ne , ai hukuncin wadda ya kashe a kar shi , shi da kansa bisa turba nasa hukuncin yake , fansar ran Ghaddafi tare da gudan jina na da na rasa na ɗauka bissa kan sa , kai gudumawa ka bada bisa turbar naka cikar buri ko kouwa ?
Laɓɓan bakin Mammadou har rawa suke cikin in'ina yace ,
" kadda ki mini ɓakin sharri ɗiyar nan , ni yaushe na kawo miki gubar da kika ciyar da ɗan ouwa na da itta ? Ki yiwa Allah kadda ki tunkuɗa ni cikin masifa ,
Wani kallon banza Maimounatou ta wurga masa , idanun ta jajir tace .
" Yau ba rana ce ta yin wassan ƴar boye ba Mammadou ka daina yin kamar baka san kome ba , kamar kai da Mahaifiyar ka baku taya ni ba , bana son muyi rabuwar tsiya doumin kun bani taimako wajen biya hakkin Ghaddafi tukuici ya kamata na baku .
Ɗan sanda da yake rubuta duk wasu kalamai da suke yi , ya ɗan karkato ga Maimounatou , ganin kamar ta shirya bada wasu bayanai ,
" Wanene Ghaddafi menene kouma alaƙar sa da kashe Mijin ki da kika yi ta hanyar ciyar da shi guba .
" Ghaddafi masoyina ne .
****
Ghaddafi Yacouba Dango asalin iyayen sa ƴan ƙasar Mali ne da suka hauro sahara suka shigo ƙasar Niger , suka yada zango a yankin Agades , inda suka yi mazauni cikin wani kongon gida da yake daga baya sosai da Babban gidan sarkin Agades ( fadar Maimartaba sarkin Agades ) .
Bayan shi iyayensa suna da wasu 'ya'yan sai dai tsantsar talauci ya sanya su fantsama a cikin gari yin barace-barace , duk kuwa da cewa a lokacin shi Ghaddafi saurayi ne mai kimanin shekaru ashirin da ɗoriya ,
Lokacin da ya fara bara sai ya fahimci babu mai kula shi bare har a ba shi , dayawa daga cikin mutanen da yake roƙo ma ƙorar sa suke da zagi kowa na faɗin ya tafi ya nemi sana'a .
Ganin haka ya sanya shi daina bara ya koma tsince-tsincen matattun ƙarafuna a kan bola yana kaiwa yana sayarwa ,( jari bola ) babu laifi yana tallafawa iyayen sa da hakan .
a wannan yawon ya haɗu da wasu kangararrun yara sa'o'in sa da suke jeruwa bisa tsohon hanyar wucewar jirgin ƙasa wajen da aka mayar sa bola su kuma suka mayar da shi matattarar ƙananun shaye-shayen su da yin karta .
Su suka jawo sa cikin su ba ɗau lokaci ba ya zama ɗaya daga cikin su ya kangare , tsince-tsincen ƙarafunan ma ya daina , basu da wani aikin yi sai zaman banza a bakin layin jirgi ko kan katagun kwangayen gidaje , suna ƴan shaye-shayen su , babbar sana'ar su ita ce ƙananun sace-sace , daga sun ga gidan da ake barin sa galala sai su faɗa su yashe mutanen cikin sa , ƴan ƙananun dabbobin mutanen unguwa basu tsira ba , akuyoyi ,talo-talo kaji , agwagi , a taƙaice dai su Ghaddafi sun addabi mutane sun hana su sakewa .
Ganin haka yasa Mutane suka yi ɗango suka kai ƙarar su wajen Maimartaba ,
Da kansa Maimartaba ya sa aka kamo su , aka basu horo tare da haɗa su da aiyuka a cikin gidan sarkin mai wahalarwa na tsawon satika biyu duk saboda a hora su
Ghaddafi yana cikin samari huɗun da aka tura bargar dawakai domin kula da su da share musu waje gami da basu abinci .
Kafin kwanaki huɗu Ghaddafi ya saba da aikin yana kuma jin daɗin aikin saboda ko babu kome yana ci ya ƙoshi fiye da sau uku a rana
Ranar da yake cika sati a kan aikin sa , Babban bawan da ainahin kula da bargar yake ƙarƙashin sa , ya danƙa masa linzamin wani kyakkyawan matashin jan doki ,
Yace ya kaɗe jikin sa da kyau dokin gimbiya ne , yau zata ɗan hau ta kewa akan sa nan cikin filin dake gaban bargar .
Zuwa la'asar sakaliya , gimbiya Maimounatou tare da bayunta biyu suka iso
Ba ɓata lokaci ya jaa limzamin dokin zuwa gaban ta yana mai tsare ta da kallo ganin ta da yayi yarinya ƙarama da bata wuce sa'ar ƙanwar sa ta uku ba ,
Gimbiya Maimounatou tana ɗago kai ta sauke ganin ta a kan sa , zuciyar ta ta wani irin bugawa , a iyakar shekarun ta goma sha shidda alokacin bata taɓa ganin wani ɗa Namiji mai kyaun sura irin sa ba , kasancewar Ghaddafi kyakkyawan balarabe ne na sosai jazur da shi .
Tun daga wannan lokacin sai ta faɗa jarabar ƙaunar sa , bata da aiki sai zuwa barga dan kawai ta kalle shi , a lokacin ita tana hutun kammala makarantar ta ta secondry ,
Sai dai kamar ɗaukewar ruwan sama sai ta rabu da sake ganin sa bayan wasu ƴan kwanaki , duk yadda ta so ta daure ta manta da shi , ta gagara a hankali damuwar rashin cigaba da ganin sa ta fara duƙushe walwalar ta , saboda wannan ne karo na farko da zuciyar ta ta fara son wani ɗa namiji ,
Ganin damuwar ta na neman kai ta ƙasa , sai ta nemi Gnala da ta bincika mata wanene wannan sabon balaraben bawa ? me kuma yasa ta daina ganin sa ? Ko an sauya masa shiyar aiki ne ?
Ba'a ɗauki wasu kwanaki ba ta samu duk wasu bayanai game da Ghaddafi , sunan sa , asalin sa , iyayen sa da laifin da suka yi har aka kawo ƙarar su ga Maimartaba aka hukunta su .
Kuka ta zauna tana yi sosai , so take ta tunbuƙe son shi daga ran ta ji da tayi ko kusa basu dace da juna ba , shi ɗin maƙasƙanci ne ko a cikin maƙasƙanta ko ɗaya ba shi da nagarta da ya dace da samun soyayyar ta .
To sai dai ita zuciyar da so na farko ya fara fasawa ya dasu a cikin ta tauri ne da ita tare da ƙwalafaci , dan haka bayan wasu kwanaki kaɗan sai ciwon son shi ya dawo mata sabo fil ,
Jin ba zata jure rashin ganin sa ba yasa bayan ta samu tabbacin inda yake zama da la'asar sai kawai tayi badda-kama cikin baƙaƙen kayan su na buzaye ta rufe rabin fuskar ta da mayafin ta , ta ratsa sorayen gidan su ba tare da ta bari kowa ya gane ta ba ta fice daga gidan su rana tana daf da faɗuwa , bata ko damu da iskar hunturu wacce ke tayar da rai-rayi da take ta busawa tana tila ƙasa a idanu hanci har ma da kunnuwan al'umma ba ,
Kasantuwar bata saba fita ita kaɗai ba hasalima yau ce rana ta farko da ta taɓa tako ƙafafun ta shiyar unguwar da take baya da Masarautar su da take ta talakawan liƙis , sai tayi ɓatan kai , ta gagara gane kwatancen da Gnala ta yi na inda aka ce Ghaddafi yana zama , ta nemi hanyar jirgin ƙasa ta rasa .
Ƙura tayi buɗu-buɗu da baƙaken kayan jikin ta , magariba kuma ta kawo kai , da kyar ta samu ta tsayar da wata budurwa ta tambaye ta ina ne tsohon hanyar jirgin ƙasa ?
Budurwar ta gwada mata hanyar da hannu, juyawa tayi da sauri ba tare da ta ko yi mata godiya ba ta fara taku zuwa kan hanyar da ta mata nuni ,
" hala can kike noufin zouwa ? Ko kouwa kin san da kwai hatsari bissa hanyar kou ? Kin san fa an sau waɗannan tsinananan samari da suke ratse bissa hanya nan , a shawarce kadda ki bi ta wannan hanyar war hakka .
Tsayawa tayi cak , ba ta juyo bata kuma ce ƙala ba , sai ta sake kaɗa kan ta tayi gaba ta miƙa sosai a hanyar har ta tarar da matattciyar hanyar jirgin ƙasan da duk bola ta mamaye ta ,
Warin da yake wajen ya sanyata rufe hancin ta tana tsallaka tsumi-tsumin bolar da take wajen ,
Shal hanyar take babu kowa ko ƴan dabbobin da suke kiwo akan bolar babu kowa ya kaɗa dabbar sa gida kafin a sibare masa ita gobe kasuwa .
Sai hange-hange take yi cike da burin son ganin sa ,
Taku ta fara ji daga bayan ta kafin warin taba ya mamaye ƙofofin hancin ta ,
Da sauri ta juyo karaf suka haɗa ido da shi tare da waɗansu samari biyu daga dama da hagun sa ,
Daga cikin mayafin ta ta saki tattausan murmushi zuciyar ta na cika da farin-cikin sake ganin sa ,
Warware mayafin fuskar ta tayi , ranar da tayi jazur gaf da faɗuwa ta haske ta tana ƙarawa farar fuskar ta jaa da kyau , cikin siririyar muryar ta tace " Ghaddafi wajen ka na taho .
Zaro ido yayi yana daɗa kallon ta , babu shakka wannan gimbiyar nan ce ɗiyar sarki to me ya kawo ta wajen nan me kuma take nema a wajen sa ?? Hayaƙin tabar da ya cika bakin sa da ita ya fesar ta hanci ta baki .
Tun bayan wannan ranar sai soyayya mai ƙarfi ta ƙullu tsakanin ƙananan matasan biyu ba tare da tunanin me ke je ya dawo ba , soyayyar junan su ta rufe musu ido daga hango tarin banbancin dake tsakanin su ,
Cikin watanni shidda sun yi wata irin shaƙuwa ta ban mamaki duk kuwa da cewa daga ɓangaren ita Gimbiya maimounatou babu wanda yasan da batun soyayyar su ita da Ghaddafi , sau biyu kawai suka taɓa haɗuwa , rana ta farko da ta je wajen sa sai kuma rana ta biyu da ta kai masa kyautar wayar tafi da gidanka sabuwa dal , da ta sa Mahaifiyar ta ta saya mata lokacin ma wayar sai hannun wane-da-wane tare da wasu kuɗaɗe masu yawa .
Zancen tafiyar ta makarantar jami'a ta babbar birnin Niamey shine ya tayar da hankalin su , saboda nisa da zasu yi da juna .
A gobe zata tafi makaranta , ta saci jiki kamar yadda ta saba ta je wajen sa da hantsi ,
Akan ƴar rusasshiyar katangar wani kangon gida ta tarar da shi , a shirye tsaf yake cikin wandon gonjo da rigar sanyi mai haɗe da hula da ya saya daga cikin kuɗin da ta masa kyautar su .
Yana daga sama yayi mata nuni da gefen sa kan katangar akan ta hauro ta zauna ,
Dariya tayi da haƙoranta tana kaɗa kai tace
" Bani iya hawa bissa nan ai kaima ka sani ,
Murmushi yayi ya diro ƙasa bata ankara ba ya ɗaga ta ya ɗora ta kan katangar runtse ido tayi zuciyar ta cike da tsoro ,
Bata san zaman sa a gefen ta ba sai da ya zunguri kafaɗar ta , a hankali ta wara ido tana kallon sa , sam ta kasa sabo da takaɗarancin Ghaddafi ita bata saba irin wannan rayuwar ta ƙarancin tarbiyya ba .
Cikin muryar sa mai sanyi sosai ba'a ce daga bakin sa amon ta ke tasowa ba yace ,
" ranki shi daɗe ai bashi kamata ba ke kina ƙasa ni ina sama tsololo , ke ai gimbiya ce ɗiyar sarki ni tamkar bawa nake a gare ki ,
Hararar sa tayi sai kuma tayi murmushi , a hankali tace
" bana so kana taɓa min jikina , kuma kai baka cikin jerun bayun gangar jikina amma zan yi farin ciki da zaka zama bawan zuciyata .
Murmushi yayi mai sauti , " ai tun-tuni nake hadimi ga zuciyar ki gimbiyata , amma meyasa bakya son ina taɓa ki ? Ya tambaye ta yana kallon gefen fuskar ta
" kawai ba yanzou ba , ta bashi amsa
" sai yaushe , yace yana shilla ƙafar sa
" sai mun yi amre kou ? Ta ce tana rufe fuskar ta da tafukan hannun ta duk biyu .
Ganin sa ya dawo kan ta , kafin ya ɗauke kan sa zuwa sama kaɗan da wata muryar dake bayyana ciwon zuci yace
" Maimounatou bani da matsayi , nagarta , kyaun asali kou dukiyar amren ki , ke ɗin kouma ai shaida ce bisa hakka .
Ganin ta ta mayar kan sa , tana jin yanayin ta na nishaɗi na jirkituwa zuwa tashin hankali da damuwa tace ,
" Amma ai muna ƙamnar juna , abunda ka lissafa bai issa hana amren mou ba , tunda ai zaka iya sauya halaye sannan kouma kai Namiji ne kana da ƙarfi neman dukiya ko baka iya zage damtse wajen neman dukiyar amre na ?
Idanun sa da suka fara yin jaa ya nitsar cikin nata raunanan idanun ,
" ta wacce hanya zan nemi dukiyar amren ki maimounatou baya.....
Katse shi tayi jin yana shirin ɓata mata walwalar ta ta yau baki ɗaya alhalin kuma bankwana ta zo su yi , tace da shi
" ka nemi dukiyar Amren Maimounatou ko ta wacce hanya Ghaddafi , buƙatata kawai muyi aure dagga na kammala ecole .
****
Bayan tafiyar Maimounatou sun cigaba da kasancewa a waya ita da Ghaddafi suna sake cinye zuciyoyin juna da so da ƙaunar juna ,
Basu sake haɗuwa ba sai bayan shekara guda a ranar da take ta zagayowar haihuwar Maimounatou ,
Babu zato aka sanar mata da sakon ƙiran da wani baƙo ke yi mata a can filin makaranta , tayi mamaki sosai saboda duk cikar jami'ar babu wani ɗa namiji ɗaya da suke ko da gaisuwar kirki ne .
Amma haka kawai ta ji zuciyar ta na son zuwa amsa ƙiran koma wanene , dan haka ta kama hanyar inda aka kwatanta mata
A tsaye ta tarar da mai ƙiran nata ya bada baya a jikin wata ƴar ƙaramar mota ƙirar golf da ta sha jaan fenti tana ta ɗaukar ido .
Daga sama har ƙasa take kallon sa zuciyar ta na kai-kawo wajen tantance shi ɗin ne ko ba shi bane ?
Juyowar da yayi ya hutatshe da zuciyar ta daga tunanin tantance shi , saɓanin haka zallar farin ciki ta ji yana tunbuƙowa daga ƙasan ranta , tamkar tayi tsalle ta rungume shi take ji a lokacin
Hannunta biyu ta kai tana rufe bakin ta da haƙoranta ke buɗe tana dariya , sai kuma tayi ɗan tsalle tana matsawa daf da shi ta haɗo haruffan sunan sa cikin wani irin sauti mai nuni da ɗoki da farin-ciki da take ciki tace.
" Gha°ddafi ? Kai ne ? je ne peux pas croire mes yeux mon amour ,
Dariya yake lokacin da ya zare baƙin tabarau ɗin dake idanun sa , cike da murnar ganin ta ya kai hannu ya riƙo hannuwanta ya jaa ta yana ƙarasa rufe tazarar dake tsakanin su ya haɗa ta da jikin sa , cike da salon son ya burge ta ya harhaɗo kalmomin da ya shafe tsawon wata guda yana koyon su yace ,
" tu m'as tellement manqué chérie ,
Bayan sun gama ɗokin ganin juna , Maimounatou ta kasa ɗauke idanun ta daga kan sa duk wani motsin sa ƙara burge ta yake yana sake nutsar da ita cikin ƙaunar sa ,
Yadda yayi shar da shi yayi gayu ya sake fiddo tsantsar kyaun sa , da cikar zatin sa na matashin Namiji , kasa jurewa tayi ta tambaye shi ,
" Ghaddafi ina ne ka samou dukiya hakka mai yawa har ka sai moto ta hawa , ka gan ka kouwa yadda kayi gayu tamkar ɗiyan saraki wallahi ka burge ainun ,
Ƴar dariya yayi ,kafin yace da ita
" cikin dukiyar amren mu da na fara taru na ɗauki kaɗan na sayi suturu doumin nayi kwalliya na burge ki , kadda samarin jami'a ƴan gayu su kwace min ke ,
Ba tare da ta damu da ta tambaye shi wacce sana'a ya fara yi ba ta washe ƙaramin bakin ta tana cewa
" Duk faɗin babban birnin Niamey babu namijin da zai iya kwace maka ni Ghaddafi ,
Da murmushi a fuskar sa ya buɗe kujerar motar sa na baya ya shiga fiddo manyan kwalayen da yayi mata birthday gift yana jera mata a gaban ta ,
Zuciyar ta tana sake bunƙasa da ƙaunar sa take bin sa da kallo bata ƙi ba ace cikin wata mai kamawa a ɗaura auren su .
*****
Cikin shekaru huɗu na karatun ta Ghaddafi ya bunƙasa ya zama hamshaƙin attajiri , ya ma ɗauke iyayen sa da ƙannen sa daga Niger ya mayar da su can ƙasar su Mali ya gina musu sabuwar rayuwa ya ƙere musu gida na zamani .
Zuwa lokacin ita da kan ta Maimounatou tasan Ghaddafin ta ya sha kwana , ana kuma damawa da shi a harkokin masu dukiya , sai dai ita da kan ta ba zata ce ga takamaimai sana'ar sa ko aikin sa ba , baza ta ce ga inda yake samun kuɗaɗen da yake mata wasa da su cikin kyautuka na bajinta ba da har wasu lokutan takan yi masa faɗan kuɗaɗen sun yi yawa , amsar da kullum yake bata shine
" wannan kaɗan ne dagga cikin dukiyar Amren ki da nake biɗa ina tarawa Maimounatou,
Soyayyar su kuwa sai abunda yayi gaba kusan kowa da yasan Maimounatou yasan da soyayyar ta ga Ghaddafin ta , idan aka cire iyayen ta amma hatta ƴan uwanta makusanta kowa ya san sunan sa , sun kuma shaida wasu daga cikin manyan kyautukan da yake yi mata ,
Haka shi ma ta ɓangaren Ghaddafi tun daga kan iyayen sa da ƴan uwa zuwa abokanan sa tun na farko da suka riga daman suka san da Gimbiya Maimounatou har zuwa kan sabbin abokan sa babu wanda bai san labarin Gimbiya Maimounatou ba ,
A cikin shekarar ne kuma gwamnatin ƙasar Niger tayi hoɓɓasa kan gagararrun ƴan fashi da makamin da suka addabi baki ɗayan kusurwowin ƙasar ta Niger ta kan kowacce boda guda bakwai da kasar ke da su ta Nigeria, Chad, Algeria, Mali, Burkina Faso, Libya, da Benin. sun hana duk wani ɗan kasuwa shan ruwa ya tsirga masa cikin ƙasa da shekaru biyar , da har suna ne da su na musamman da ake ƙiran su da shi escouade de lions .
escouade de lions sun gagari kananun sojoji su waye kuma ƴan sanda ? bare kuma ma'aikatan hana safara da miyagun kaya , ƙananan ƙwari a wajen su kenan ,
Kisa suke tare da ɓarna yadda suka so suka ga dama , gwamnati ta rasa yadda zata yi da su , dayawa daga cikin su ɓoyayyun fuska ne da su babu takamaimai wanda ya san fuskokin su , sannan an gaza gano takamaimai madakatar su da za'a iya taƙile su ta nan .
Youssouf Abdoul-Azizou Baskore ,shine sojan da babban hafsin soja na ƙasar Niger ya wakilta a matsayin wanda zai ja tawagar aikin da zai kawo ƙarshen waɗannan gungun ƴan fashi da makamin , lokaci kaɗan bayan dawowar sa daga ƴakin da aka tura su Libya.
Cike da zuciyar jarumta da son kare hakkin ƴan ƙasar sa Youssouf ya karbi aikin da aka ba shi , inda ya nemi taimakon haɗin guiwar ƴan sandan ciki da dole sai da taimakon su za'a kai ma nasarar cafke ƴan fashi da makamin .
A dai-dai lokacin rayuwa ta yiwa Ghaddafi da Maimounatou daɗi domin watanni uku kaɗai ya rage mata ta kammala karatu baki ɗaya ta bar makaranta , abu na gaba shine ta gabatar da Ghaddafi ga iyayen ta , a ɗaura musu aure daga nan su shilla zuwa ƙasar France da suka zaɓe ta a matsayin kasar da zasu barji amarcin su a can.
Kafin cikar watannin wani irin liƙewa Ghaddafi ya yiwa Maimounatou koyaushe yana sintiri tsakanin garin da yake da Niamey ,
Duk da cewa Maimounatou tana jin daɗin yadda yake yawan ziyartar ta a ganin ta ƙaunar da yake yi mata ne take sake hauhawa a zuciyar sa da daman take tantamar kamar ƙaunar da ita take yi masa yafi wanda yake yi mata yawa ,
Sai dai yadda yake yawan taɓa ta tare da bayyana mata cewa shi fa a sarari a matse yake da ita yana da muradin ta , lamarin yana damun ta , domin ita ta san bata cika ƙarfi ba muddin akan ƙaunar Ghaddafi ne , sannan.ta ɓangaren gangar jikin ta ma rarrauna ce .
Cikin haka abunda take ƙoƙarin gujewa ya auku , shaiɗan tare da tsantsar son da take yi masa ya sa ta bashi kan ta a wani dare ,
Daga lokacin kuma sai gurɓacewa ta shigo cikin soyayyar tasu domin tamkar busa ake musu ko umarni , koyaushe suka haɗu sai sun yi ta'asa kafin su rabu , a hakan daga zuciyoyin kowannen su niyyar auren juna bata sauya ba , a ganin su zinar da suke ba kome bace tunda aure zasu yi illa ƙarawa juna so tare da ƙoƙarin kiyaye juna daga zuwa ga waɗansu mutanen daban ( abunda matasa dayawa suke ta'alaƙa ƙazamtatciyar rayuwar su akai , ba kome bane illa tsagoron son zuciya da rashin shan tsabga da ace ana zane matasan mazinatan da duk aka kama da laifin zina a nahiyar mu kamar yadda addini ya tanadar da abun ya ɗan ragu ) .
Daren yau bayan sun gama fasiƙancin su a ɗakin otel ɗin da musamman Ghaddafi yake da ɗakin sa ,
Yake sanar da Maimounatou kan cewa tafiya ta kama shi zouwa Benin da zai iya kaiwa tsawon kwanaki goma kafin dawowar sa da zuwa lokacin kwanaki biyu kachal ya rage tayi jarabawar ta, ta ƙarshe .
Ba domin ran ta ya so ba suka yi bankwana washegari da safe da alƙawarin zasu dunga yin waya koyaushe , ya kama hanya bayan ya ajiye ta a bayan makarantar su .
Sun cigaba da yin waya har kwanaki uku bayan tafiyar sa kafin daga baya kuma ta daina samun wayar sa , shima kuma bai ƙira ta ba , ta damu ainun saboda hakan ɓakon lamari ne a gare ta su shafe tsawon wasu kwanaki ba tare da sun yi magana a waya ba ko da kuwa baya ƙasar .
Wasa-wasa sai da suka shafe tsawon kwanaki shida babu waya a tsakanin su zuwa lokacin hankalin maimounatou ya kai ƙurya wajen tashi , jarabawar ta ma sai tayi da gaske take iya rubutawa ,
Bata da aiki sai gwada ƙiran layukan sa da duk take da su , cike da fatan ko Allah zai sa ta same shi ,
Bayan ta fito daga jatabawar ta ta yau waje ta samu daga can gefe ta zauna tana cigaba da lalubar layin Ghaddafi , amma kamar koyaushe cikin kwanakin duk layukan sa basa tafiya ,
Tsumu tayi a zaune idanun ta cike da ƙwalla , hirar da ta ji wasu matasa na yi daga gefen ta ta ɗan ɗauki hankalin ta , inda ta ji suna labari akan jajirtatcen sojan ƙasa Youssouf ɗa a wajen sarkin Maraɗi wanda cikin watanni da basu cika uku ba , a kwanaki biyar da suka wuce tawagar sa da yake jagoran ta ta tarwatsa gungun ƴan fashi da makamin da suka yi mafaka
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Chapter 110
Chapter 111
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 84 Chapter of 111