Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
. Yakaka ashe daman irin zaman da kike da ni kenan ??   Cewar lubna idanun ta na bayyana ɓacin rai , A kaikaice yakaka ta dube ta , kin ga sahiba bana ciki da rigima , daga kawai mutum ...   Hmm   Lubna ta katse ta , Wallahi sahiba abu ɗaya zan faɗa miki a matsayin ki na wacce na ɗauka ƴar uwa , Kar ki yadda kiyi wasa da damar da ta zo miki , idan har wannan mutumin da gaske yake ki bashi dama ku fahimci juna , aka yi bincike bashi da wani aibu wallahi ki bada dama kuyi auren ku shekarun mu sun fara tafiya ishirin da biyu mun rufa ta da uku muke hari ,wallahi wasa ba namu bane dama kuma sau ɗaya take zuwa a rayuwa ,   Shiru yakaka tayi Kalmar ,"Dama," na maimaituwa a cikin kan ta , ita har tana da wata dama da ta rage mata kuwa ? Ai damar guda ɗaya da take da ita ta riga ta zo ta wuce tun a shekarun baya , " damar da mahaluki ɗaya ya bata wanda ta tabbatar baza ta taɓa samun  makamancin sa ba, bata yi amfani da damar ba a maimakon haka ma sai tayi masa mummunan sakamo da har yau idan ta tuno shi kunya tare da nadama basa ƙasa a guiwa wajen danne ta , ina ma ina ma ina ma ?? Da ace dama zata dawo mata ? Da ace zai sake ba ta dama ko da gutsire daga irin damar da ya bata a baya ? Wataƙila da ta gyara kuskuren ta ta wata fuskar , , abunda ta sani shi ɗin ya riga ya mata nisa ita ta zama wata shuɗaɗɗɗan lamari da ya taɓa giftawa cikin rayuwar sa , Bata da wani shauƙi ko tunani mai armashi akan wani ɗa namiji har yau ta gaza sake son wani ɗa namiji , " zata iya cewa ta ƙi maza ," ƙi irin na wanda kunama ta taɓa harbin sa babu shakka idan ya ga gizo-gizo kakkaɓe shi yake , dangantakar nesa nesa ce ke tsakanin ta da maza , shiyasa har yau ta gaza samun saurayi ɗaya tak , ita ce bata saurarar su bata bada fuska , take boye kan ta tare da killace surar ta daidai da fuskar ta a rufe take , ta zaɓi hakan , ta kuma fi son tayi tsarayuwar ta a haka ba tare da wani ɗa namiji ya sake ratsa rayuwar ta , burin ta ɗaya ne shine tayi ilmi kuma tana godiya ga Allah tana godewa malama maryam tare da addu'ar Allah saka da alkhairi ga baki ɗayan zuri'ar ta , Ko da ko kusa bata sahun malumma amma kai tsaye a yau ta wuce a ƙira ta da jahila , ta nemi ilmi tana kan nema kuma zata cigaba da nema har.....    Har suka kawo gida bata cewa lubna ƙala ba ,    Sai da suka shigo gidan ta ruga da ɗan gudun ta ta rungume malama maryam wacce take tsaye daga ƙofar kitchen tana amsa sallamar su .   Ni bazan yi aure ba har sai nayi ilmi na zama kamar ummi malama ta , sai ki san yadda zaki yi da mutumin da kika ba wa phone number . Murmushi ummi tayi ,    Anya kuwa yakaka ? Aure ai shine cikar darajar ɗiya mace Lubna wacce take zama akan kujera ta shiga bada labari tiryan tiryan tana yi tana hararar yakaka wacce take yanka musu cabbage da zasu ci abincin rana da shi . Sosai malama maryam ta yiwa yakaka faɗa daga ƙarshe ta ƙarƙare da yi mata nasiha tare da faɗa mata fa'idojin aure da girman matsayin sa a addini . Jikin yakaka yayi sanyi har idanun ta na tara ƙwalla , ta gaza cin abinci na kirki . A ƙarshe ta jaa kunnen ta akan daga yau kar ta ƙara ƙin saurarar duk wani namijin da yake da kamala da ya nuna yana son ta , ta ƙoƙarta ta saurare shi na ɗan wani lokaci ta fahimci wanene shi , daga nan idan ta yarda da halayen sa na ƙwarai ta bashi dama ita ma tayi aure , ko kusa kar ta kawo aƙidar ƙin aure kusa da ran ta saboda wani shuɗaɗɗan dalili nata , . A ladabce ta amsa mata da zata yi yadda ta faɗa mata . Bata wani jima ba saboda yadda walwalar ta tayi ƙaura ta musu sallama tana barin gidan ƙarƙashin rakiyar lubna wacce duk ta damu da rashin walwalar ƙawar ta ta , sai faman jan ta da hirar raha take , Har ƙofar gida ta rako ta , Zata tura ƙofar gidan ta shige lubna ta riƙo hannun ta , ta waiwayo tana kallon ta da sakakkiyar fuska . Sahiba idan baƙya son sa idan ya ƙira insha Allah zan faɗa masa dan Allah ki bar damuwa . Murmushi yakaka tayi ,    Ni dai ban ce miki ba , kawai ....shiru tayi ,     Baza ki gane ba sahiba . Zan gane dan Allah ki faɗa min meye ne ? Duk banji daɗi ba da naga ranki a jagule Ni bana son kowanne ɗa namiji ilmi me zurfi nake da burin yi saboda ina da mummunan rauni a zuciyata wanda jahilci ne ya assasa min ina so na samu ilmin da zai warkar min da ciwon da na ji akan jahilci , A hankali lubna ta gyaɗa kai tana sakin hannun ta ,   na fahimta, ta furta hakan ba domin ta fahimce ta da gasken ba , abunda ta daɗe da sani cewa yakaka tana da wani binannen ƙuduri wanda take dakon sa boye cikin ran ta da ita bata riga ta san wanne irin kuɗiri ne ba . Daga cikin niƙab ta sake yin murmushi ,    Sahiba sai gobe zan zo ki bani labarin yadda kuka yi da ,"direba,"    Ta ƙarasa zancen da dariya cikin muryar ta , ko kafin lubna ta bata amsa wacce ta yamutsa fuska tare da ƙanƙance ido   Ta shige gidan da ɗan gudun ta tana jin lokacin da lubna ke cewa daɗin abun ma direban jirgin sama ne . Da sallama ta shiga falon duk da cewa tayi ne ba domin tana sanya ran za'a amsa mata ba sai dan sanin muhimmancin sallama a musulunci da ta riga tayi . Kamar yadda ta zata kuwa daga samira har hamshaƙiyar ƙawar ta da take haƙimce akan kujerar falon babu wanda ya amsa sallamar ta , hirar su suke cigaba da yi da take cike da shewa da dararraki irin na yaran matan da suke juya duniya a tafin hannun su . Rage tsawo tayi ta ɗan durƙusa , Anty samy sannu da hutawa , Ke ke yaks wanne irin iskanci ne wannan ?? So nawa zan faɗa miki bana son kina shigo min gida da wannan maya-mayan yadikan da kike yawo da su a jiki , musamman ma na fuskar nan taki kamar wata korarriya daga makka ? To na faɗa miki yau ce rana ta ƙarshe . A hankali yakaka ta kai hannu ta kunce niƙab ɗin fuskar ta , lokacin da sofi take kai ganin ta kan ta , Kiyi hakuri anty na cire . To ya dai fi miki , yo Allah na tuba na sanya wannan mayanin a fuskata ai ya shaƙe min numfashi ya sheƙa da ni barzahu ban shirya ba , Kallon kallo suka yi a tsakanin su , kafin sofi ta janye idanun ta tana yatsina fuskar da ya zama halittar ta , Kirjin yakaka yayi dakan lugude , tsawon shekaru biyar bai isa a ce ta manta fuskar sofi ba matar da ganin farko haɗuwar su ta fari ta ɗau karan tsana ta aza musu ita da ƙanwar ta falmata , dan haka cikin hanzari ta miƙe tare da haɗiye kalaman gaisuwar da tayi niyyar miƙa mata , ta juya tana nufar ɗakin ta  . Friend wannan wacece ? Aina kika samo ƴar ƙwara ? Ko dai ko dai .... Ta ƙarasa zancen tana sakin wata shashashar dariya . Ɗan murmushi samy baby tayi cikin ran ta bata mamakin rashin gane yakaka da sofi ta yi , ko ita da kan ta bata gajiya da kallon yakaka , wata irin fata ce da ita wacce bayan haske tana ɗauke da wani irin taushi tare da ƙyalli a idanu , ya haɗu da gyara tare da jimaka me kyau da take samu daga ita samy baby , haɗi da girma tare da cikar macen da take kan ganiyar ƙuruciyar ta , sai ta zama tamkar farin wata idan ta gifta dole ta ɗau hankali , ɗan tsararren jikin ta da yake a murmure kowanne irin kaya ta sanya masa kyau yake . Ai ba domin tirjiya da yakakar take gwada mata ba da tuni maƙudan kuɗaɗe sun fara shigo mata ta hanyar yaks , amma wani ɗan lokaci kaɗan take jira wanda zata kammala aiwatar da nufin ta , ta kuma fara kwasar adashen da ta dunga zubawa a dalilin ta ,   Friend wannan wata haja ce da nayi tsintuwar ta a gari  ,     Kalaman samy baby suka zo daidai da zaman yakaka a bakin ɗan gadon ta , daga inda take tana iya jin muryoyin su ,    Daɗi ta ji da samy baby bata jaa dogon bayani ta sanar da sofi ko ita ɗin wacece ba . Taɓ kina nufin wanna ƙatotuwar budurwar kika bawa mafaka a gidan ki ? Ah lalle ,   ta ƙuta      Kawai dai dan ke ma ba miji ke gare ki ba , idan ba haka ba ina ke ina kawo annoba muhallin ki ?    Ai ni tsakanina da ire-iren waɗannan matan masu kama da barbarar yanyawa ko gaisuwar kan titi babu ,     Ai ko sama da ƙasa zasu haɗu bazan bar ido irin na yarinyar nan ya gauraya da na doctor na ba ,     Wai Allah har bugun numfashi na ya fara sassarfa bala'i .   Dariya samy baby ta kwashe da shi , daɗi na da ke freind akwai bala'in kishi ,     Sha kurumin ki sanya ranki a sassanyar inuwa tunda har kika mallaki doctor hamza a matsayin miji ke da kan ki kin san naki ne ke kaɗai mutuniyar ,     Wata sakaryar dariya sofi ta sake tare da ba wa samy hannun suka tafa . Ni yanzu kin ƙi ki faɗa min sirrin friend wai tsakani da Allah wacce duniyar kika samu haka a Boston da har kika ajiye waɗannan manyan kayan haka ? Kin gan ki kuwa sofi cikin shekaru huɗu jal kin sauya ta jiki , ai wallahi wanda duk  ya san ki a da da kike bulugari bazai gane ki ba a yanzu da kika koma wata katafila, ke ni anya kuwa doctor yana iya yin nisa da ke wannan irin abebaɗan more rayuwa da kika haɗa a jiki ahayye duniya gidan daɗi ɗan Allah ƙawata bani sirrin !    Kalaman samy baby na kusa da ƙarshe ya sa fara'ar fuskar sofi raguwa , Cikin jimami tace ,    Ai lamarin doctor ajiye shi gefe guda friend , kullum jiya iya yau ke wataran ma jiya ta fi yau ɗin domin ko yanzu kafin su kawo ni nan su ajiye baki ga yadda ya nemi min cin fuska a gaban abokin sa ba , akan sutura , wai kayan da na sa sun matse ni , bazan hau masa mota a haka ba sai dai na tafi na hau taxi shi babu abunda ya dame shi , ya dunga balbalin bala'i da daman ƙiris yake jira tun kafin mu baro US yake kumburi shi ɗaya uwa fulawar da yis yayi mata yawa,  ina dai lallaɓa sa ne , Wallahi tsawon shekaru uku da muka yi a US da zan lissafa miki irin baƙin cikin bawan Allah nan da na ƙunsa sai kin ji tausayi na , gangar jikin sa kaɗai na mallaka , ruhin sa na wani waje wanda nake zaton ya min nisa duk kuwa  ƙoƙarina akan kome nasa , ke dai kin san yadda daman aka yi auren nan namu , to duk da haka ban zauna ba malamai da bokayen yi nake na ƙarƙare miki ƙanƙat ɗin tsafi dai har india na je akan a min yadda zan yi na samu mazauni na dindin a gurin sa na amshi sararin zuciyar sa, Zuwa na karnataka india ne ma fa da aka min wani mugumugun aiki aka min filla filla da tunanin sa na samu yake kula ni har muke iya haɗa shimfiɗa , A hakan ban zauna ba kullum ni ce a gyara saƙo da lungu na jikina tare da matso kyau , rana ɗaya na lura kamar Yana son mace me manyan kaya , saboda bin wata mata da kallo da na ga yana ta yi a gidan cin abinci a boston , na dubi matar na ga idan banda himilin cinya da ɗuwawu bata fi ni kome ba , tun daga ranar na shiga faɗi ta shi ganin yadda zan yi nima na ajiye manyan kayan nan , magungunan ɗago ɗuwaiwai da ƙara faɗin cinya babu irin wanda ban afa ba , amma da yake jikin nan nawa marke ne , shiru maƙatau bulunbuƙui , jiya iya yau , na kasa haƙuri na faɗa miki tare da jagorar wata ƴar * ƙawa da nayi a boston balarabiya ce ƴar duniya ta ƙarshen ƙarshe  , ita ta kai ni aka min aiki me ƙanƙat , aka tatso tare da ɗago tudun bayan nan da kike gani , azaba babu irin wacce ban sha ba a lokacin aikin nan da bayan gama yin sa , amma na shanye , kuma babu shakka ƙwalliya ta biya kuɗin sabulu , domin wasu cin kashin da yake min da yawan fushin sun ragu , duk da dai da farko ya tada ɓallin sai na faɗa masa me naje nayi jikina ya koma haka ya dunga bincikata , da yake lokacin aikin nan na karnataka na kan zafin sa , zancen bai yi nisa ba ya manta ya kuma haɗu da shima yana son manyan kayan ai hajiyata shiru kike ji malam ya haɗiyi shirwa !    Sai dai ki ga idan na gifta yana zaune yana haka da ido ,"ta wani yi ƙasa-ƙasa da ido tana kwatance , " yana bin abebaɗan da kallo , ni kuwa sai na sake jujjuya masa su da kyau yadda zan sake kamo sa , a raina ina "faɗin kai da abubuwan ka ai daman sakin jiki kayi ka ƙure musu kallo meye na wahalar satan kallo kamar ba naka ba " ah to abun duniya menene ?? Sarkin fawa da kyautar ƙaho !     Wata ƙatuwar dariya me ɗauke da haniniya samy baby ta kwasa sofi tana taya , suka chafke   Shegiya tawan baki da kyau ! Watau shi tsuntsu me wayo ta wuya ake danƙar sa ,     Charaf kuwa     Ah to ai na faɗa miki friend babu abunda bazan yi ba babu kuma inda bazan shiga ba akan soyayyar doctor buri na ɗaya , shine ya kasance nawa ni ɗaya har abada ..    Kin kuwa kamo hanyar , ko ma nace kin isa ga matakin .!    Wata dariyar suka sake saki kamar sabbin mahauk.... Yakaka wacce dararrakin su ya mugun takurawa , saboda rabo da tayi da jin hayaniya sosai ya haka da kuma kalmomin su da basu mata daɗin saurare ta sanya ƴan yatsun ta biyu ta toshe kunnuwan ta , hakan bai mata ba sai ta ɗauko ƴar ƙaramar wayar ta wacce samy baby ce ta saya mata tana da memory a ciki wanda yake ɗauke da ƙira'o'in Alqur'ani izifi sittin tare da wa'azizzikan manyan malamai ta jawo ear plugs ta maƙala a kunnuwan ta , ta sanya ƙira'ar AlQur'ani ta fara saurara bayan ta jingina da jikin gadon nata . Niamey A ɗakin zaman marasa lafiya na musamman dake cikin national hospitalisé , mata biyu ne bisa kan ɗan gadon marasa lafiya , babbar ta jinginu da jikin sa ƙarfen gadon yayin da ƴar ƙaramar take kwance a jikin ta kan ta na bisa ƙirjin babbar dukkanin su biyu idanun su a rufe suke , Ɗan motsawa ƙaramar tayi tana yamutsa ƴar fuskar ta da take fayau ! Kafin ƴan daƙiƙai babbar ta buɗe nata idanun tare da tallafo ƙaramar ta miƙe zaune da ita sosai daga kishingiɗar da tayi ,     Sannu Mama , ya kike ji yanzu jiki ya daina ciwo ?     Duban fuskar maman ta tayi da raunanan idanun ta , ta kai ƴan hannuwan ta duk biyu ta ɗaura bisa fuskar mamar ta shafa tun daga goshin ta zuwa haɓar ta ,kafin cikin ƴar muryar ta me zaƙi irin ta yara masu wayo tace          Na ji sauƙi maama kin ji ko ? Da ɗan raunannan murmushi a fusksr falmata ita ma ta sanya hannu ta shafi fuskar mama yadda tayi mata ,    Naji daɗi mama na ta ji sauƙi ,Allah ya ƙara miki rangwame tare da sassauci , me zaki ci kafin ki sha magungunam ki ? ,    Mayar da kan ta tayi ta kwantar bisa ƙirjin mamar ta ,      Maama bana cin kome , ! Idanun falmata suka kawo ruwa tana jin wani irin ciwo daga ƙasan ran ta , ƙaƙƙarfan tausayin mama kamar kullum yana sake cin ran ta , da ace tana da dama da tayi musanyan jinin jikin ta da na mama wanda ke gauraye da ƙwayoyin ciwon da a kullum yake barazana ga rayuwar ta tare da sanya ta a tsananin ciwo , to sai dai bata da dama ciwon mama muƙaddari ne daga Allah tun lokacin samuwar halittar ta . Bai tare da cikakkiyar nutsuwa ya turo ƙofar bakin sa ɗauke da sallama , jin muryar sa ya sanya mama ɗagowa daga jikin falmata , ta waigo shi da buɗaɗɗun haƙoran ta ,   Papa !   Da sassarfa ya ƙaraso , ciɗak ya ɗaga ta tare da rungume ta tsama cikin jikin sa yana shafar lallausar sumar ƙan ta da take a tsefa an tufke mata ita a ƙeya . A hankali yayi baya yana zama kan kujera ɗakin ya tare da ajiye ta kan ƙafafun sa ya riƙo fuskar ta da hannayen sa biyu idanun sa na bayyana tsantsar damuwa da soyayya yace mata .    désolé ma chérie comment tu te sens maintenant ? ( sannu my dear ? Me kike ji yanzu?  Je me sens mieux maintenant papa!  ( naji sauƙi yanzu papa )     Ta furta hakan tana me shigar da kan ta zuwa ƙirjin sa ta kwantar da alamun rashin ƙarfi a tare da ita ,   Runtse idanun sa yayi da ƙarfi yana jin yanayin da ya gan ta a ciki na narkar da ruhin sa ,   A hankali ya ɗago kan sa yana duban sashin falmata daidai lokacin da ta kai ƴan yatsun ta tana ɗauke hawayen da ya biyo kan kumatun ta ,           Tausayin ta me ƙarfi ya taso masa ,      Fatimah , Ya ƙira sunan ta a ƙasan maƙoshi   Sashin da take jin tashin muryar sa ta waiga ba tare da ta amsa ba .   Meyyasa ba'a sanar da ni tashin ciwon mama ba ? Sai doctor ta ne daga nan ya ƙira ni yake sanar min ? Muryata ƙasa-ƙasa ta ce     Hajja ce ta hana a faɗa ma tace duk shekaranjiya ka tafi daga niamey , !      Miƙewa yayi tare da ƴar sa a kafaɗa bai ce kome ba , sai da ya kai bakin ƙofa yace mata     Bari mu tai ga likitan ta !      Bai jira amsar ta ba ya fice daga ɗakin .    Kichiɓus suka yi da hajja wacce take kan hanyar dawowa ɗakin bayan ta ɗan zaga ta motsa ƙafafun ta. Riƙe baki tayi nuna alamun mamaki ! O Ni , yanzu ashe Babban soja sai da ka taho ? Kai da shekaranjiya jiyan nan ka tafi bakin aiki ? Banda abunka ai mun riga mun saba mun kuma fahimci kan ciwon mama tana fara nuna alamun rashin lafiya da hanzari muke zowa da ita asibiti , ai da kayi zaman ka bakin aiki . Gaishe ta yayi a ladabce    ta amsa da sakakkiyar fuska .   Babu kome hajja ai lafiyar mama ta sa'a wuce aiki muhimmanci bari mu je ga likitan ta .    Bayan dogon bayanin da kamar maimaici ne gare shi akan cutar ƴar ta sa wacce take ɗauke da ciwon Amosanin jini , " da a turance ake ƙiran sa da Sickle Cell Anemia, Ya ɗora da yi masa bayani akan binciken da shi youssouf ya sanya likitan ya yi masa akan wannne asibiti ne mafi kyaun kayan aiki tare da ƙwararrun likitoci da zai iya kai ƴar sa ayi mata aikin da ake sanya ran idan har anyi sa da dacewa masu cuta irin na ta kan iya warkewa baki ɗaya . Fitaccen asibitin nan a duniya da yake ɗauke da ƙwararrun likitoci dake ƙasar amurka ,"Mayo Clinic ," shine asibitin da likitan ya tabbatar da ƙwarewar su akan aikin dashen ɓargo  ga marassa lafiyan da ya shafi manyan cutukan cikin jini . Miƙawa likitan hannu yayi suka yi musabaha lokacin da yake miƙewa akan ƙafafun sa domin barin ofishin . Likitan ya kai duban sa ga mama wacce tayi luf a jikin baban ta tana wasa da adon gaban rigar sa na soji . Madame Safiyya Baskore sommes-nous bien maintenant? pas plus d'injection non?    dariya  tayi kafin ta amsawa likitan dai-dai lokacin da suke ƙarasa barin ofishin ita da baban ta .    oui je me sens mieux maintenant plus d'injections . Dariya likitan yayi yana ɗaga mata hannu alamun ! bye bye !      A hankali ta motsa laɓɓan ta tana kwantar da kan ta kan kafaɗun baban ta   au revoir ! ( Bye ) ..       Assalamu Alaikum kowa da kowa !    Surprise ??  😂 Ina gaisuwa agare ku baki daya masu karatun da suke faranta min wajen Danna dan tauraron nan tare da ajiye min sharhin su a karkashin kowanne shafi na rubutu na,  ina son Sanar da ku cewa ina godiya me dinbin yawa agare ku. Okay ghost readers, Makaho bai San Ana ganin sa ba sai an zungura shi ko ?? 😠 Kun san bakwa kyauta min koh?     Amma ba kome a dai juri zuwa rafi wataran tulu zai fashe,  😂 [9/3, 10:14 PM] +234 806 122 1116: Fikrah writers association MAFARI ( Hargitsin Rayuwa ) Umm'muaz 33 Wannan shafin na bada tukuicin sa baki daya ga " ZULAIHAT RANO " MEELAH " RALIYA GARBA. #I MORE THAN APPRECIATE YOU SISTERS# Bayan an sallami mama daga asibiti sun dawo gida , idan banda lelen ta babu abunda falmata take rabon ta da makarantar ta ma yau kusan sati guda kenan , Domin duk yadda hajja ta so falmata ta tafi makarantar ta bar mata kulawar mama ta ƙiya , gani take daga ta matsa daga kusa da ita ciwon nata zai iya tashi . A zaune suke a falo hajja tana kishingiɗe tana hutawa bayan ta gama ƴan kananun aiyukan ta na safe , Mama tana kalmashe bisa cinyar falmata , wacce take bin duk gaɓoɓin maman tana tausa mata su sannu a hankali , jikin ta sanye da ruwan hodan kayan sanyi na yara mata me adon ƴan ƙula-ƙulai farare , ƙafafun ta a ƙunshe cikin fararen safar ƙafa . Biyamuradi ya shigo falon , a shirye yake tsaf cikin kakin sa na soji , fitowar sa kenan daga sashin sa da yake sabon gidan da ya saya musu wanda ya fi wanda suka fara zaman haya a cikin sa girma da tsari , domin wannan sashi uku ne da shi ƴan madaidaita , sashin da su falmata suke da sashin baƙi wanda ba'a amfani da shi sai kuma sashin biyamuradi da idan ya zo garin yake sauƙa a cikin sa a wasu lokuta , musamman a lokacin da ya tarar da rashin lafiyar mama , wasu lokutan kuwa a hotel yake zaman sa . Mama tana jin sallamar sa ta miƙe daga jikin falmata wacce take ƙoƙarin riƙe

Chapter 58 of 111