bayan ta da kallo , cikin ran ta cike da tausayin ƙuruciyar dake ɗiban ta tana shirin sanyata yiwa kanta sakiyar da ba ruwa , ita a karan kanta ba ƙaramin damuwa tayi ba da rashin ji daga wajen Youssouf kamar yadda yace kafin rabuwar su zai ƙira domin jin labarin halin da suke ciki , rashin ƙiran nasa ya ɗaure mata kai , tsoron ta ɗaya kada ace ya sau auren Falmata , ko kaɗan bata fatan hakan , tayi ƙiran wayar sa aƙalla sau goma bayan tahowar su amma bata shiga fatan ta Allah yasa lafiya .
Haka kawai ta ji damuwa tana mamayar ta kan cewa da Hajja tayi tunda suka taho wai bai ƙira ba , ita a nata zaton su na gaisawa da Hajja ta waya , kawai bai neme ta bane sanin da yayi tana fushi sosai da shi dan haka ko an kawo mata wayar ma ba karɓa zata yi ba kamar yadda ita ma ta kuɗurce a ran ta ,
To ashe ma ita take zaton haka shi yana can ko tunawa da sha'anin da ya shafe ta baya yi , ya riga ya yada da ita da abunda ke tare da ita , duk sai jikin ta ya sake yin sanyi ƴar hirar da suke yi ma ita da Yakaka da Rahima ƙarama kafin tashin ta zuwa ɗakin Hajja, sai ta gagara cigaba da sa baki tayi lamo a kwance tana jin yadda abunda ke cikinta yake dunƙulewa waje guda ,
Yakaka ita ta lura da shirun da tayi dan haka ta kai hannu ta jaa yatsar ƙafar falmata tare da cewa ,
" Maman baby yaya ne ? Akwai damuwa ne ?
Janye ƙafar ta tayi ba walwala a muryar ta tace ,
" Maman mama kin san dai na ce ku daina ƙirana da sunan nan bana so ,
Rahima ta kwashe da dariya " to Yakaka mu daina cewa Maman Baby , mu koma ƙiran ta da Matar soja yafi daɗi ko Hajja Falta ?
Kuka ta fashe da shi da a farko suka yi zaton na wasa ne , sai da suka ji har tana jaan hanci tukun suka tsahirta daga dariyar da suke duk kuma sai hankalin su ya tashi jikin Yakaka har rawa yake ta tallafo Falmatan zuwa jikin ta suna rige-rigen tambayar ta " me ya same ta take kuka ??
Ba tare da ta daina kukan ba tace ," Nace muku bana so , bana so bana so , kun ƙi dainawa .
Da sauri Rahima tace , " Yi hakuri ba zamu sake ba dan Allah ki daina kuka daga wasa ? Haba Fatima-zahra Maman Baby ,
Da sauri Yakaka ta ɗago tana hararar Rahima ,
Dariyar da Rahima take bata tuƙe ba ta dafe baki tare da cewa
" Au So nake nace Mamar Mama ta biyu , yi haƙuri ba zamu sake ba kin ji ƴar ƙanwata ?
Batare da ta amsa ba ta zame daga riƙon da Yakaka tayi mata ta koma ta kwanta a inda ta tashi , wani irin yanayi marar daɗi na sake mamayar ta baki ɗaya bata jin daɗin kome , abu kaɗan sai ya ɗaga mata hankali ya ƙara mata damuwa .
Fuskar Yakaka cike da damuwa take kallon ta , damuwar da ta hango tare da ita ya ɓata mata walwalar da take ciki mai daɗi , cikin ran ta ta haƙiƙance akwai abunda ke damun Falmata haka kawai ba zata yi kuka ba daga ɗan wannan wasan , ji tayi ta damu da son sanin damuwar ƙanwar ta .
Tun daga ranar sai duk walwalar ta ta ragu damuwa ta bayyana a cikin suffa da mu'amalar ta , kome take yi babu nishaɗi duk kuwa da cewar basu taɓa tsintar kan su a cikin gata da riritawa irin na wannan lokacin ba , daga kan Mamar su har zuwa Amnee da Baa , Rahima da kusan kowa na gidan nan-nan ake da su ,
Sai dai damuwar ta mai zurfi ce , kullum cikin kasa kunne take ta ji ko Hajja zata ƙira ta tace ga Youssouf ya ƙira su yi magana ko kuwa ma tace ya ƙirata ita sun gaisa amma ko alama ta yin ƙiran nasa bata ji ba , ita kuma tsoron surutun Hajja ya sa ta kasa tambayar ta .
***
Yau tana zaune a tsakanin mamar su da Amnee suna ƴar hira , su ukun ne kawai a wajen , Rahima da Yakaka sun tafi amso sabbin ɗinkunan su da Baa ya bayar da kuɗi aka kawo musu atamfofi da lesika aka kai ɗinki domin su yi amfani da su wajen bikin auren Rahima da yanzu bai fi kwanaki goma sha biyu ba suka rage .
Amnee ta ɗan dube ta tana murmushi tace ,
" Fatima zahra , cikin nan naki wata nawa yake ciki ne ? Anya bai kamata ki fara zuwa awo ba ?
Da sauri ta ɗago kai ta dubi Amnee sai kuma ta sunkui da kai batare da tace kome ba ,
Khaalty Rahima ta ɗan dube ta , tace Fatima ba dake ake ba ?
A hankali tace , " Nima ban sani ba Amnee ,
Jimm Amnee tayi kafin ta ce , " to ai ya kamata ki fara zuwa awo banda ma dai shirme irin naki Fatima cikin fari da ake ɗokin sa da yi masa ƙirgen ƙwaƙwaf amma ke kyace baki san watannin sa ba ?
Hajja wacce take ƙarasowa falon daga waje inda ta gyara shanyar alkamar da ta wanke ta yin kunun Baa , sarai ta ji wasu daga kalaman Amnee , tace
" Wallahi uwar masu gida ke ma dai kya faɗa , wannan uwarɗakin tawa da kike gani kome nata daban ne bata ajiye kome ba sai wauta , cikin nata yana gaf da cika watanni huɗu a yadda lissafi na ya nuna min , sai dai kuma kin san cikin fari ɓuya ce da shi amma lokacin da suka dawo dai daga can turai cikin bai wuce watanni biyu ba da ƴan ɗoriya , daga can ta yo cikin , yanzu kuma kin ga dawowar tasu kusan kwanaki talatin .
Dariya ce ta so kama Khaalty Rahima jin wannan ƙokari na Hajja na ƙididdige kwanakin cikin Falmata da ko ita kakar ɗan ko ƴar ba ta iya haka ba ,
Ran ta cike da jin daɗin tsantsar ƙaunar da ta lura Hajja na yiwa ƴa ƴan ta tace ,
" Hajja baki da dama ke da Uwarɗakin ki ba mai shiga tsakanin ku , wannan zuwa awon ma ai ke zaki dunga raka ta .
Ƴar dariya Hajja tayi kafin ta harari Falmata tace ,
" can dai su ƙarata ita da Babba Uwar Mama ita zata raka ta bana iya miskilancin fatima ba .
Dariya Amnee tayi kafin tace,
" zan yi maganar da Baa Alaji idan ya so sai ya nema mata iznin mijin nata , kan fara zuwa asibiti saboda kuwa zuwa awo abune mai matuƙar muhimmanci ga mata masu ciki , yadda duk muka yi sai ki shirya a fara kai ki kin ji ko ƴata ?
A hankali ta gyaɗa kai kurum , tausayin abunda ke cikin ta kan yadda Mahaifin sa yayi banza da su ya fara kamata .
Daga haka Amnee da Mama suka cigaba da yin hirar su , a hankali ta miƙe ta nufi ɗakin su , domin kuka da take jin yana taso mata ,
Tana shiga ɗakin ta sanya tafukan ta duk biyu ta rufe fuskar ta tana fashewa da kuka marar sauti .
Tana tsakiya da yin kukan ta tsinkayo Sallamar Doctor Hamza , shuru tayi tana saurarawa jin tashin muryar gaisawar da suke shi da iyayen su ,
Jin sun gama gaisawa sai ta miƙe tan share hawayen ta , Doctor Hamza yana sawun gaba na mutanen da ba zata manta alherun su ba a rayuwar ta ,dan haka ya zama dole duk inda ta ji shi ta je ta gaishe shi ko da kuwa babu ƴan uwantaka a tsakanin su bare yanzu da suke ƴan uwan juna makusanta ,
A hankali ta fito , ta tako zuwa tsakiyar falon ta zauna tana gaishe shi ,
Da murmushi yake amsawa yana jin daɗin ganin ta samu lafiya , yace
" Fatima ƙanwata ke ce haka kika girma ? Alhamdulillah lafiya ta samu .
Ƴar dariya tayi , kafin tace " Ni ce Yaa dakta ,
Dariya shi ma yayi yace " lalle girman 'ya mace ba wuya , Al'amarin Ubangiji kuma ya zarta yadda duk muke zato , Khaalty lokacin da na kawo yaran nan gidan nan ko kusa bani da masaniyar muna da wata alaƙa tsakanina da su , kawai nayi niyyar taimakon su ne domin Allah , ashe kin ga ma abun farin-ciki ƙannena ne su , lokacin da Amnee take sanar da ni ba ƙaramin mamaki nayi ba da farko ma ni na shiga ruɗani ne su waye Amina da Fatima ? Sai da ta min bayani sosai ,
Ya nisa kafin ya cigaba da cewa , " Khaalty nayi murna da Allah ya haɗa ki da ƴaƴan ki , Allah ya kuma kare ku baki ɗaya , ya sa bakin wahalar ku kenan .
" Amin Amin ɗana , tace da sigar zolaya ,
Shima dariyar yayi da sauti sanin cewa ta ƙira shi da ɗanta ne dan tasan bai son haka tun yana ƙaramin sa a cewar sa tayi ƙanƙanta ta ƙira kanta Mamar sa ina ma laifin tace ita yayar sa ce ?
Khaalty Rahima ta cigaba da cewa , " kawai sai muka gan ka babu sanarwar zuwa ? Ko wani aikin ka zo yi ?
Jingina kansa yayi da kafaɗun kujerar da yake kai , yace
" Baa ne ya ƙirani tun shekaran jiya , yace lalle na zo cikin kwanaki biyun nan , to nima daman kuma ina shirin zuwa saboda shirye-shiryen bikin nan ban sani ba ko akwai abunda za'a iya buƙata mai muhimmanci ayi a gama akan lokaci tunda ga ku , kar ya zama irin na bikin su zainab kome a hagunce , aiki ne ya tsare ni ban iso da wuri ba .
" Na fara shiga wajen Baa ɗin amma na tarar da shi da mutanen nasa kin san sai kuma ya sallame su da abunda suka saba , kai mutanen mu sai a hankali , wai kawai sai ku mayar da wani mutum ɗaya wajen zuwa ku faɗi buƙatun ku da damuwar ku kamar wani shi ɗin injin buga kuɗi gare shi ? To wai wanene bashi da buƙatu da damuwowi ?
Sallamar Rahima da ta shigo da ɗan gudun ta , ya sa shi mayar da ganin sa kan ƙofar , dai-dai da shigowar Yakaka , wacce tunda ta ji Rahima na murna tana cewa ga motar Company ya zo , ta ji jikinta yayi sanyi duk taku ɗaya na kafafun ta da jin ƙarin hauhawar bugun zuciyar ta ,
Idanun ta ta sauƙe kansa da shigowarta falon , karaf suka haɗa ido ,
Kowanne su yayi saurin janye ido Doctor Hamza ya haɗa da kawar da kai ita kuma ta sunkui da kan ta , cikin raggon taku ta ƙaraso ta bayan kujerar da Amnee take kai , tayi durƙuso da kyar ta haɗo kalmomin ,
" Ina wuni ,
Kamar bai ji ta ba haka ya cigaba da zolayar Rahima da yake cewa " ke little idan ana shirye-shiryen aure ramewa ake yi ke kuwa ga ki sai sake kumbura kike , me takwarar ki take baki haka hala ɗure take miki ??
Dariya Khaalty Rahima da Rahima ƙarama suka sa a tare , kafin Rahima ta zagaya ta kujerar da Amnee take ta saƙalo hannuwanta a wuyan ta , tana haɗa fuskokin su tace ,
" Khaalty kar ki faɗa masa , abun sirri ne ko ?
Amnee wacce ta lura da yadda yayi watsi da Yakaka , kuma bata ji daɗin hakan ba sai ta ce ,
" Takwarata tana gaishe ka fa ?
Wani wur-wur yayi da ido , sai kuma yace " Ok Lafiya , ba tare da ya dube ta ba illa haɗe girar sa da yayi , ya zaro wayar sa daga Aljihunsa , kaf fara'ar fuskar sa ta ɗauke .
A hankali Yakaka ta miƙe tana murmushin yaƙen akan wasan da Mamar su da Rahima suke yi , sum-sum ta wuce ɗakin su .
Ƙiran wayar Amnee da aka yi yasa suka ɗan tsahirta daga hayaniya , bayan ta ɗaga wayar sai ta saurara ,
" to Baa Alaji tace.
Duban Khaalty Rahima tayi , tace
" Ukhtee , da ke da Ɗan ki ku zo muje Baa alaji yana ƙiran mu .
***
Bayan sun sake gaisawa a tsakanin su ,a ƙagauce Amnee da take zaune daga gefen sa tace
" Baa Alaji lafiya dai ko ? Wannan ƙiran Allah ya sa Alheri ne.
Prof ya dube ta da ɗan murmushi , yace " inshaAllah Alheri ne Aminatu ,
ganin ya mayar kan Hamza da Khaalty Rahima da suke zaune a ƙasa kafin ya fara cewa .
" Dalilin da yasa na ƙira ku ba kome bane sai kan wata magana ko kuwa nace shawarar da na yanke tun watanni baya , amma ban sake haƙaƙewa akan abunda nake niyyar yi ba na haɗa Aure tsakanin Ƴaƴa na biyu kai Hamza da kuma ƙanwar ka Amina ba , sai da tabbatuwar yaran nan ƴan uwan ka ne ba wasu bare ba da ba'a san asalin su ba , hakan ya sa na sake ganin dacewar lamarin fiye da farko ,
" Duk da cewa batun ƙarin auren da nace kayi ba sabon abu bane a wajen ka , tun kwanaki na sanar da kai ka kuma yi na'am kawai wacce nake burin ka aura ɗin ne baka kai ga sani ba , sai a yanzu nake sanar da kai Aminatu ƴar Rahima ƙanwar Mahaifiyar ka ita ce matar da nake son ka aura a matsayin matar ka ta biyu , da fatan ba zaka yi gardama ba ??
Daga Khaalty Rahima har Doctor Hamza baki ɗaya idanu suka zuba suna kallon sa , a hargitse sosai ƙwaƙwaƙwar Doctor Hamza take , meke nan yake ji ? Yaya Baa zai masa haka ?
A hankali ya sauƙe ganin sa daga kan prof ya sunkuyar da kansa ƙasa , ta wutsiyar ido yake hango yadda Khaalty Rahima ta dawo da ganin ta kan sa , zuciyar sa na shaida masa cewa amsar sa kowa a wajen yake jira , kan ya amince ko kuwa a ah ?
abunda ya bi duk wasu gaɓɓai na jikinsa ya kassara bai wuce kaifin idanun Khaalty Rahima ba , matar da tunda ya buɗi ido ya gansu tare da Mahaifiyar sa a matsayin shaƙiƙan juna , ƙaunar ta a gare shi kuma mai tarin yawa ce , jin daɗin wasannin ƙuruciyar sa duk ya yi tare da ita , shi kuwa ta yaya zai iya cewa yaƙi ƴar da ta haifa daga cikin ta a tsatson idanun ta ? wallahi ba zai iya ba , Baa ai bai kyauta masa ba da ya titsiye shi da wannan batun a gaban idanun Khaalty Rahima ,
Satar kallon Amnee yayi yaga yadda ta nutsu fuskar ta da wani irin yanayi na nuna zaƙuwa tana kallon sa .
Yawan ƙaunar da Amnee ke yiwa Rahima ya san kuskure kaɗan idan yayi kan lamarin nan zai matuƙar sanyata a ɓacin rai , shi yaya zai yi ne ?
Muryar Khaalty Rahima da ta ratso shirun wajen ya katse masa tunani ,
Da wani yanayi cikin muryar ta da ya sha banban da murmushin yaƙen da yake fuskar ta a lokacin tace ,
" Yaya , mun ji daɗi mun kuma yi farin-ciki da wannan haɗin da kayi niyyar yi , Sai dai Yaya , Hamza ai tuni ya riga ya zaɓi abokiyar zaman sa har kuma tafiyar su ta fara miƙawa cikin kwanciyar hankali da fahimtar juna ba tare da yana da niyyar ƙara yin wani auren ba , dan haka ni ina ganin Yaya da dai an bar yarona ya zauna da matar sa ɗaya kar a ɗaura masa nawin mata har biyu da bai shirya ba .
Prof da yake kallon duk su biyun , ya gyara zama , yana mayar da ganin sa gaba ɗaya kan Khaalty Rahima .
" Rahima wannan ba hujja bace da zata hana auren Hamza da Aminatu , sai dai idan kin nuna min Aminatu ba ɗaya take da sauran 'ya'yan da na haifa da nake da ikon zaɓa musu abokan rayuwa ba, ko kuwa har yanzu baki huce daga abunda ya gabata ba shiyasa zaki gwada hakan ta hanyar hana wannan al'amarin tabbatuwa ko Rahima ?
Da taruwar hawaye a idanun ta muryar ta cike da tashin hankali , ta shiga girgiza kanta tana cewa " Haram ko kusa ba haka bane Yaya , dan Allah kar kace haka , a tun kafin bayyanata Aminatu da ƴar uwarta suna da wani majiɓanci da ya wuce ka tsawon wannan shekarun ? kayi haƙuri ba nufina ba kenan , ni shi nake...
" idan ba haka bane to ki barni nayi abunda nake da manufar yi inshaAllah alheri ne a garemu baki ɗaya ,
Bai saurara ba ya juya ga Doctor hamza da zuwa lokacin gumi ke tsattsafo masa a goshi , da murya dake cike da gargaɗi Prof yace ,
" Likita kai nake saurare kai kuma me kace ?
Ɗago da kan sa yayi ya dubi iyayen sa , yanayin da ya gani a kan fuskokin su, su duka biyu ya razana shi musamman ma Amnee dake masa wani kallo mai kama da harara , da sauri ya mayar da kansa ƙasa kafin muryarsa cikin rashin amo sosai ta fito ,
" Na'amince Baba , Na Amince Baa .
Daga haka yayi shiru yana jin wani irin ɓacin-rai da ya taho masa tare da Amincewa auren yarinyar da ta gama yawon ta shekara da shekaru dan kawai tana ƴar uwar sa ,
Daga sama ya tsinkayo muryar Prof yana cigaba da cewa ,
" To Alhamdulillah Allah ya maka Albarka , ya baka 'ya'yan da zasu maka biyayya fiye da yadda ka min , Ubangiji Allah ya jiɓanci lamarin ka ya raba ka da sharrin duniya, Allah ya sa Albarka a zaman ku ya baku zuri'a masu yawa da Albarka , ka faranta min rai sosai .
Ya nisa lokacin da Amnee wacce haƙoranta ke washe tana ƴar dariyar dake nuni da zallar farin-cikin da take ciki take amsa addu'o'in sa ya cigaba da cewa ,
" za'a haɗa auren naku da na Rahima ayi shi duk a rana ɗaya dan a rage hidima idan ya so ko bayan sati guda ne idan ka samar mata muhallin da ya dace da ta zauna a can Abujan kusa da kai sai ka taho ka ɗauke ta hakan yayi ko ?
Yace yana mayar da ganin sa kan Amnee , wacce ta gyaɗa kai da sauri da maɗaukakin fara'a a fuskar ta tace , "Yayi sosai ma Baa Alaji , cikin sati uku masu zuwa ai su zainab sa iya zuwa Dubai yiwa takwarata kayan ɗaki .
Da wani irin bahagon yanayi Doctor hamza ya ɗago yana kallon su ,
Khaalty Rahima da duk hankalinta ke kan sa ta yi gyaran murya kaɗan , cikin ƙanƙan da kai tace ,
"Yaa ka min izni nayi magana wannan karon a matsayina na innar ango madadin uwa ,
Murmushi Prof yayi , "An miki izni , yace
" Yaya Dan Allah a mana alfarma , bayan an ɗaura auren a bamu ko da watanni biyu ne ya kammala shirin sa , kamar samar da wajen zama a tsanake , ya kuma sanar da uwargidan sa cikin kwanciyar rai , ya ɗan samu ya dai-daita lamuransa ,tunda nawi ne zai ƙaru masa kar a tsawwala yafi kyau yayi kome cikin lumana tunda indai ta zama matar sa ai kome ya kammala .
Cike da amincewa Prof yace , " To shikenan tunda kun nemi wannan Alfarmar an muku , amma ya tabbar kafin cikar watanni biyun ya kammala duk wasu shirye-shirye tunda ɗan naki ai Babban likita ne albashin sa ya kai wani mizani amma duk da haka na ɗauke mar nawin sadaki da duk wasu hidindumu da suka shafi biki na shi hidimar shine ya samar mata da muhalli mai kyau tare da ɗaura aniyar kulawa da duk wasu hakoki nata da suke kan shi daga ranar da zata shiga gidan sa har zuwa ranar da mutuwa zata ɗauki ɗayan su , kaji ko ?
Ya ƙarasa zancen yana juya akalar tambayar sa ga Hamza ,
" Gyaɗa kai yayi nagode Baa Allah ya ƙara girma ya furta hakan yana miƙewa yayi hanyar ficewa daga falon , Khaalty Rahima ma godiyar tayi musu sosai kamar zata zubda ƙwalla dan farin-cikin gatan da ake shirin yiwa ƴar ta ,
Tafe yake baya sanin ina yake ajiye ƙafar sa , Jacket ɗin sa riƙe a hannun sa saboda zafi da yake ji yana damunsa kota'ina cikin jikin sa tsabar tashin hankali , abunda ya faru yanzu a falon Baa so yake ace wani rarraunan mafarki ne daga cikin jerin shuɗaɗɗun mafarkan da ya dunga yi a shekarun baya , domin tuntuni ya wanke tabbatuwa hakan daga zuciya da tunanin sa .
Har ya kusa sashin sa ya tsinkayo muryar Khaalty Rahima tana ƙiran sa , juyowa yayi yana ƙirkiro wani rarraunan murmushi ya ɗora a fuskar sa ,
Ta ƙaraso idanun ta akan fuskar sa tana nazarin sa , muryar ta cike da nutsuwa tace
" Hamza kada fa ka damu kan ka wajen yin duk wasu hidindimu ko da gidan da zata zauna ɗin ma ka kama muku mai sauƙi idan ma ba hali ko ɗaki guda sai a bata a cikin gidan da kuke zaune nasan 'yata safiya ba zata ƙi ba , idan kuma duk hakan bata samu ba , zan sa Ukhtee ta roƙi Yaya ko anan sashin naka na gidan nan ai sai a barta tayi zaman ta ba ma sai ta tafi can Abujan ba , shi zaman aure ai bautar Ubangiji ce wurin Mace da Namiji baki ɗaya .
Tausayin ta ya kama shi , bai bar murmushin da yake yi ba yace " kar ki damu Khaalty yadda duk Baa ya ce haka za'a yi inshaAllah babu abunda zai gagara ,
Murmushi tayi , sannan ta cigaba da cewa , "Nagode, Nagode , yadda ka rufa min asiri kaima Allah ya rufa maka, ya baka 'ya'yan da zasu maka fiye da abunda kayi ga iyayen ka , nagode nag...
Hannunta ya riƙo ," haba Khaalty godiyar me kike min haka , ai ni...
Da sauri ta katse shi , tana cewa "Godiyar kome ma , ka yi kome da yakamata nayi ta gode ma Hamza Allah ya ma Albarka ,
" Amin ya amsa yana sakin hannun ta ya juya ya nufi sashin sa ,
A hanya komawa ciki Khaalty Rahima da Amnee suka haɗu , cike da farin-ciki suka rungume juna ba sai bakunan su sun furtawa junan su ba babu makawa sun san zucoyoyin su cike suke da farin-cikin faruwar wannan lamari.
" Baa Alaji yace a tambayi takwarata ita ma, ko ta amince ? Ko kuwa tana da wani wanda take so ya shirya yin aure , dan fa ba za'a mata dole ba ,
Ɗaure fuska Khaalty Rahima tayi , " wanne irin ma a nemi amincewar ta Ukhtee ? Shi namiji ma aka masa dole bare ita mace ?ai koma waye take so dole ta haƙura tunda Yaya ya yanke hukunci .
Murmushi Amnee tayi , " wa yace miki dole aka yiwa ɗan ki ? Ba soyayya bace ya sa ya ɗauko ta ya kawo ta gidan nan lokacin ma bai san ko suwaye su ba ? Ai kawai dan dai kaddara ta gifta tsakani badan haka ba da auren su
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Chapter 110
Chapter 111
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 86 Chapter of 111