Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yana iya jiyo sautin murmushin laɓɓan Maimounatou , so yake ya buɗe baki yayi ko da addu'a ne amma ya gaza , Wani ciwo mai kaifi da ya yanki uwar hanjin sa shi yasa shi burtso da Amai ta hanci da bakin sa , da yasa duhun da yake sabko masa hanzarin ƙarasa saukowa ya rufe masa ido ya daina ganin kome alhalin idanun sa na buɗe da hakan ya yi dai-dai da tsayuwar jijiyoyin jikinsa , kome kuma ya tsaya masa chak . Da gudu Maimounatou ta tsallake shi tana lalubar wayar ta , jikinta na rawa ta shiga ƙiran wata number ,     Ana ɗaga ƙiran bata jira ance kome ba tace       " ka tahou yanzou aiki ya cika sauran ka ƙarasa naka , ni nagama nawa .   Daga ɗayan ɓangaren Mammadou zuruf ya miƙe tsaye tare da kewaye matar sa ya fita ,      A harabar gidan sa ya tsaya , cikin yin ƙasa da murya yace     " kina nufin yau kin yi nasarar kashe Youssoufa ?   Jin jina kai tayi kafin tace "ƙwarai yau na cimma manufata ta amren sa .                     Assalamu Alaikum masu karatu da fatan kun wayi gari lafiya ? Alherin Allah ya sadu da mu baki ɗaya . Nagode    [12/25/2019, 9:11 AM] +234 706 503 6187: MAFARI ( Hargitsin Rayuwa) Umm'muaz 46 " Yakaka tana nan zuwa ita ma , Ita ce amsar da Falmata ta bawa Maman su , daga nan hira ce ta sarƙe a tsakanin su mai cike da labarin yadda rayuwa ta kasance musu bayan rabuwar su da juna . **** Tiryan-tiryan Falmata ta basu labarin duk wasu bala'o'in da suka afku ga rayuwar su bata ɓoye kome ba illa mummunar rayuwar da Yakaka tayi da har ta kai ga haihuwar Mama da take jin har abada laɓɓan bakin ta baza su taɓa iya bayyana wannan mummunan labarin ga kowa ba .    Ta cigaba da bata labarin ɓacewar Yakaka bayan haihuwar Mama ba tare da ta faɗi ainahin silar barin su da tayi ba har zuwa kan auren su ita da Youssouf yadda kome ya wakana , da rashin lafiyar Mama har zuwa tafiyar su USA da samuwar lafiyar idanun ta , komawar su Niger da kuma dawowar Yakaka , zuwa kan Mutuwar Mama .   Shiru su duka ukun suka yi bayan gama sauraron ta , zuciyar Khaalty Rahima ta girgiza da jin yadda rayuwa tayi walagigi da 'ya'yan ta mata , tsakanin ƙarya da gaskiya , rayuwar rashin gata ta tsantsar wahala abu ɗaya ne mafi ciwo a gareta yadda duk su biyun suka auri Miji guda a wannan ƙarancin shekarun nasu , lalle wannan ƙaddara ce mai girma .   Babu wanda ya fita sanin halayyar 'ya'yan ta duk kuwa da cewa sun jima da rabuwa daga yin rayuwa guri guda , amma ai ita ta haife su dan haka ta san halin kowaccen su tun kafin su mallaki hankalin da zasu iya boye abu a ran su .   Daga zaman Falmata a gabanta kawo yanzu ta fahimci lalle akwai wata damuwa mai girma da take cinta a rai , wanda farin-cikin haɗuwar su bai sa ta manta da damuwar ta ba , ji tayi hankalin yana neman tashi , tana jin kamar akwai wani abu da Falmata take ɓoye mata da tafi danganta shi da Yakaka , dan haka ta muskuɗa tana kallon fuskar ta cike da nazari tace ,   " Falmata kin samu labarin bayyana ta ne kika zo ?  Ko kuma kawai dai kin zo ne ? Murmushin yaƙe tayi kafin tace    " Maman mu ban san kin zo ba , ban San kina nan ba, ta cigaba da cewa Mama ina Yaana da Bulama suke ?  nayi kuka nayi kuka na damu akan sanin ina kike ko kina raye ko kin mutu ?  shekaru suka yi ta tafiya ba tare da mun san halin da kike ciki ba , har na fitar da rai da sake haɗuwar mu a duniya , na koma yi miki addu'a iri ɗaya da wacce nake yiwa Baban mu , kan Allah ya jiƙan ku .    Ƙwallar tausayin ta ya taru a idanun Khaalty Rahima , kafin tace     " Yaana ta rasu a kan hanyar mu ta shigowa maiduguri , Bulama kuma yana nan ya girma , anjima kaɗan ma za ki gan shi ya dawo daga islamiya ,    Ta cigaba da cewa , " Falmata ni na wanke gawar Mahaifin ku a cikin gonar na binne shi , ban yarda gawar mutumin kirki irin sa ta walaƙanta a hannun dabbobin daji ba , bayan na koma neman ku ban same ku ba , na dawo wajen ƙabarin sa mun rayu kwana biyu ni da Yaana da Bulama ina yi ma sa addu'a , kafin mu bar gurin , Allah sarki Mutumin ƙwarai mai tawali'u Allah ya masa Rahama ,    " Amin Mama Amin ,    Falmata ta amsa tana share hawayen da suke zubo mata ,   Amnee ita ta katse musu hirar ganin duk fiye da rabin ta koke-koke suke yi da jimamin rayuwar su da ta wuce .     " Ukhtee Rahima ku bar koke-koken nan haka , Fatima mu tafi ɗaki kiyi wanka ki shirya kafin a kawo miki abinci , "me zaki ci 'ya ta ?   Ɗan murmushi Falmata tayi "kome ma zan ci , amma da zan samu tuwo miyar kuka da man shanu ,     Dariya Amnee tayi tana kama hannun ta " muje kiyi wanka ki shirya , abinda kike so shi zaki ci .   Bayan tayi wanka ta shirya cikin riga da zanen da Amne ta zaɓo mata daga cikin kayan Rahima , tsumu tayi zaune a kujerar gaban madubi ,    " wani irin yanayi take ciki marar kan gado , ga dai ta a gida ta dawo kamar yadda ta zaɓarwa kan ta , take kuma ganin hakan shine zai raba ta da ɓacin-ran da take ciki , daɗin-daɗawa ma ta dawo ta tarar da farin-ciki mafi ɗaukakuwa a wajenta watau haɗuwar ta da Mama , Amma sai farin-cikin nata ya gaza kaiwa ga matakin da take so , baki ɗaya a hagunce take jin zuciya da ƙwaƙwalwar ta sun gaza tsayuwa gu ɗaya bare su taya ta samun gamsasshen farin-cikin da zai wanke mata rai .    Ƙiran sallar La'asar da aka yi , yayi dai-dai da gilmawar tunanin da take ta yunƙurin danne sa tuntuni , wani sashi na zuciyar ta ya tunbuƙo da tambayar ta ƙarfi da yaji ,    " a wanne hali Yakaka da Youssouf suke ciki ? Wataƙila sunyi ta neman ta sun gaji , wataƙila kuma ba su ma wani neme ta ba , dama ce suka samu ta tsara yadda rayuwa zata musu a gaba , ƙila ma ya saki auren ta zuwa yanzu ,   Nan take ta runtse ido Zuciyar ta na tsananta bugu ,    Da sauri ta miƙe ta shiga banɗaki gami da ɗauro Alwalar La'asar , Har ƙarfe huɗu tana kan Sallaya tana addu'o'i domin yaƙi da tunane-tunane , sai da Amnee ta matsa mata ta zo ta ci abinci sannan ta tashi suka koma falon tare , inda suka tarar da Khaalty Rahima ita ma ta idar da sallar ta nan bisa darduma , idanun ta kan falmatan tana duban ta da murmushi irin na zallar farin-ciki ,da ƙauna , ita ma falmatan da murmushi ta tafi a hankali ta zauna a gefen ta , Farantin da aka jera abinci akai amnee ta tura mata gaban ta , " ki cinye duk kin ji ko ? Sama-sama take chakalar abincin duk kuwa da an girka shi yadda take so , miyar ta sha haɗin kayan ƙamshi na gargajiya , ga kuma man shanu gangariya , Sallamar Yakaka da ta sauka a kunnen ta daga bakin ƙofar falon shi yasa ta mayar da lomar da ta ɗauka da nufin kaiwa bakin ta , A hankali ta ɗago kan ta tana ganin shigowar ta ,da kai tsaye Yakaka ita ta doso bata kai ganin ta kan kowa da yake wajen ba , Ganin yadda ta taho yasa Falmata ta tsorata , dan haka ta janye kwanon abincin gaban ta , zuciyar ta na bugawa bata taɓa ganin Yakaka a fusace ya irin haka ba .    Yakaka tana ƙarasowa ta riƙo kafaɗun Falmata da karfi ta jijjigata , muryarta a tsaurare tace ,      " Falmata me yasa kika min haka ? Meyasa kika tafi ki ka barni ? Ashe kinyi girman da za ki iya yin gaban kan ki a rayuwa ? Ashe ni matsayina a wajen ki daman bai wuce na ƴar jagora ba da yanzu kuma lafiya ta samu wajen ki shine kika sanya kan ki a hatsari wajen yin gaban kan ki ? Wallahi da wani abu mummuna ya same ki bazan yafe miki ba Falmata .    Kukan da take riƙewa ya taho mata , sakin kafaɗun ta tayi ta zauna daɓas akan kujerar gefen ta ,  muryar ta cikin kuka ta cigaba da cewa ,      " Falmata kin manta ne da kusancin dake tsakanin mu ? Ashe har akwai wani laifin da ni zan miki ki kasa yafe min ?    Zuwa lokacin ita ma falmatan hawaye ke sauƙa a idanun ta , ganin kukan Yakaka ya karya mata zuciya , a hankali ta zauna a gefen Yakaka , muryar ta na ɗan rawa tace  " Yakaka , kiyi haƙuri ba yadda zan yi ne , kin san... Kawai bazan iya zama bane .   Da wani irin yanayi Yakaka ta ɗago tana kallon ta , baza ki iya zama a gidan auren ki ba saboda ni ko Falmata ? Saboda mummunan kuskuren da na aikata ko ? Saboda...     Da sauri Falmata ta katse ta tana nuno mata inda Khaalty Rahima da Amnee har da Hajja duk suna tsaye suna bin su da kallo ,    "Yakaka kin ga fa Maman mu a tsaye , ga ta nan tana kallon ki , bata mutu ba ,ga Maman mu Yakaka .    A hankali Yakaka ta bi inda take nuna mata da kallo cikin ran ta da ɗarsuwar tunanin ko dai Falmata ta samu jirkituwar tunani ne ? Tunanin ta ya tsaya chak na wasu ƴan daƙiƙoƙi lokacin da idanun ta suka kai kan fuskar Khaalty Rahima wacce take murmushi tana raba ganin ta a tsakanin su biyun cike da nishaɗin sake samun damar ganin su tare a gaban ta . A hankali Yakaka ta mike tana kusantar inda take bayan tsayuwar kukan ta chak , zuciyarta cike da wasi-wasin gaskanta sake ganin ta , sai dai kuma ko a cikin mafarki ta ga Mahaifiyar su ai ba zata gagara gane ta ba ko me kuwa jirkituwar kamanni da ta samu mai-kyau ko mai-muni . Tana ƙarasowa gurinta ta kai hannu a hankali tana tattaɓa jikin Khaalty Rahima, muryar ta a dishe da kukan da tayi tace ,    "Maama ke ce ? Ke ce Mama ?    Hannun ta da yake taɓa jikinta khaalty Rahima ta riƙe , tana cewa , "Ni ce Aminatu , Yakaka na , ni ce ,   Yakaka tana wata ƴar Dariya-dariya , kuka-kukan da yake fallasa tsantsar ruɗanin farin-cikin da take ciki , ta waigo ga Falmata tana mai mancewa da Falmatan ta riga ta haɗuwa da Mama , ɓakin-cikin da ta shigo da shi yana zagwanyewa tace ,     "Falmata wallahi Maman mu ce , kin ga Maman mu ? Zo ki gan ta , ta ƙarasa magana tare da yafito Falmatan da hannu ,    Sai kuma ta juya ta rungume ta da ƙarfi tana cewa ,"Mama na, Alhamdulillah , Alhamdulillahi . **** Daren ranar ba suyi wani baccin kirki ba su duk huɗun hira kawai suke yi inda cikin labarin da Yakaka ta basu ta bayyana musu ainahin yadda haɗuwar ta da Youssouf ya kasance da yadda ta haifi Mama , samy baby ta yaudare ta, da kuma duk abubuwan da suka kasance tsakanin ita da Youssouf da danginsa baki ɗaya bayan zuwan ta Niger har zuwa guduwar da Falmata tayi ta bar ta a Niger . A Zuciyar ta ta ƙudiri aniyar tsage gaskiya kome ɗacin ta , ita bata ga Alfanun ƙarya ba , babu wata rana da ƙarya zata iya yiwa mutum illa sada shi da ranar Nadama . Daga Khaalty Rahima har Amnee sun koka kan yadda mummunar kaddara ta faɗawa Yakaka sanadin duhun jahilci tare da zun-zurutun rashin wayo , haɗi da raunin wayewar mu'amalantar jama'ah , da kuma rashin wani babba majiɓanci a cikin rayuwar su . Yadda zuciyar Yakaka ta cika da tsoron ko zasu yi mata faɗa ko ma su yi fushi da ita sai ta ga akasin haka , domin daga mamar su har Amnee tausayi kaɗai take iya hangowa a fuskokin su , dan haka sai ta ji ta samu nutsuwar zuciya irin wanda bata taɓa samu ba tunda igiyar rayuwa ta fara jan ta .   A gareta yau ce rana ta farko da wasu nata makusanta na haƙiƙa suka fahimce ta ba tare da sun ƙalubalance ta ba , babu shakka babu kamar uwa Mahaifiya, ƙaunar ta ga abunda ta haifa daban ne , haka ma yawan sani da fahimtar ta ga 'ya'yan ta daban ne kamar yadda yawan uzuri da afuwar ta gare su ya hauhauwa .    Amnee ita ta katse shirun tsakanin su inda ta cigaba da cewa ,     "Amma takwarata , raba auren ƙanwar ki da Youssouf da kika so yi , ko kusa ba hanyar samar da mafita ba ce ba , idan kika duba yadda sharri ya biyo ta hannun sa haka nan ma Alkhairi ya zo ta hannun nasa , ki duba yadda ya riƙe auren ƙanwar ki har ma ya zama hanyar samar da lafiya a gare ta ? Bai walaƙanta ta ba duk kuwa da tazarar banbancin matakan matsayi ta kowacce fuska na rayuwa da yake tsakanin su , Baki ga yadda ya jajirce kan rayuwar ƴar sa ba har sai da Allah ya ɗauke ran ta ba tare da ya bari ta walaƙanta ba , kamar yadda sauran mafi akasarin ƴaƴan da aka samar ta wannan hanyar suke rasa tudun-dafawa iyayensu duk biyu na kƴamatar su musamman ma uba , amma sai shi ya kasance mai bata kariya da dukkanin ƙarfin sa , hatta a gaban dangi da Al'ummar sa . "Babu shakka laifin sa maigirma ne sannan alkhairin sa kuma mai yawa ne , na fahimci irin ciwon da kika ji , kike kuma kan ji bisa dalilin faruwar kome , ina nufin auren sa da Fatima , to amma kiyi haƙuri ki rungumi kaddarar ki , ki yafe masa domin 'yar uwar ki da ya alkintawa rayuwa , ki bari su cigaba da zaman su na aure , Ubangiji Allah zai dube ki kema takwara zai baki Miji nagari wanda zai tallafawa rayuwar ki , ya rufe duk wani aibunki , ya ƙi duba zuwa duk wasu shuɗaɗɗun laifukan ki , ya zamar miki abun Alfahari , Allah yana son bayun sa masu yawan yafiya kin ji ko ? Ta ɗago kan ta a hankali tana murmushin da iyakar sa bisa siraran laɓɓan ta , idanun ta na sheƙin hawayen da suka cika gurbin su ta ce , "Amnee nagode , nagode da addu'ar da ki ka min , kuma inshaAllah na yafe masa Allah ya yafe min nima ,    Hannu ta kai ta riƙo hannun Falmata wacce tayi lamo a kwance kusa da Mamar su , ta juya musu bayan ta , duk zaman su a ɗakin bata cika cewa kome ba , a sarari damuwa mai-yawa take bayyane a fuskar ta ,      Cikin sanyin murya Yakaka tace ,     " Falmata ke ma ki yafe min duk wasu laifukan da nayi miki da saka ki a damuwa da tashin hankalin da nayi , ki yi haƙuri kin ji ko ? ban yi da gangan ba .     Miƙewa zaune  tayi tana riƙo hannuwan Yakaka duk biyu , muryar ta na rawa ta ce ,    "Yakaka meyasa za ki bani haƙuri ? Bayan ke kika cike min gurbin Mahaifiya , Mahaifi ,dangin da kowa namu lokacin da muka rasa kowa ?Bayan ke ce kika dunga ɗawainiya dani Alhalin ina musaƙa ? Ke ce kike zama da yunwa domin ni naci , ke ce kika sadauƙar da rayuwa ƙarƙashin rufin ɗaki kan katifa kika zaɓi kwanan cikin zaure domin ni na kwanta ? Yakaka, ke ce fa Mamar Mama 'yar da dalilin ki samar muna da rayuwar jin daɗi kaddara ta sa aka samar da ita , 'yar da ni kuma ban so wata halitta sama da ita ba , dalilin Mama na samu lafiyar idanuna , tsawon zamana da shi Albarkacin Mama nake ci ,...   Hannu Yakaka ta kai da nufin rufe mata baki , " ya isa Falmata ki ce kawai kin yafe min nima ,    Janye hannun Yakaka tayi daga kan bakin ta hawayen idanun ta da suka taru suna zubowa tace ,     " Yakaka ai ni ce zan nemi yafiyar ki akan butulcin da nayi miki , shaiɗan ne ya min huɗuba da har ya sa nayi fushi da ke , ruɗewa nayi Yakaka ban taɓa zaton abinda ya cutar da ke ni kuma zai kyautata min ba , ban yi zaton sanadiyyar shan wahalar ki ni zan samu salama ba , ban so ba kika zamto mafarauciya ni kuma cima-zaune ba , Yakaka nima bazan iya cigaba da zama da shi ba ..     Kuka ya ci ƙarfin ta , zuciyar ta na mata zogi , Yakaka ma hawayen take yi a dai-dai lokacin bata da sauran kalmar da zata yi amfani da ita ta rarrashi Falmata , ta ta zuciyar ma jinya take . **** Washe gari da safe bayan sun shirya sun yi karin-kumallo Amnee ta musu jagora zuwa wajen Prof da daman tun a jiya labarin zuwan su ya same shi , haɗi da dangantakar su da Amnee da Rahima . Bayan ya amsa gaisuwar su , ya dunga bin su da kallo cike da tausayi , can daga ƙasan ran sa yana jin tamkar yana da kamasho mai yawa na kasancewar rayuwar su a haka , Ba domin shi da danginsa da suka ƙi auren  Rahima da ɗan uwan su ba da hakan ya kawo barin Rahimar gidan da wataƙila yaran basu tashi 'ya'yan ƙauye marasa galihu irin haka ba , Da ace ko da mahaifiyar su da sauran 'yan uwan su sun ƙi auren , shi bai biye musu wajen nuna tsanar lamarin ba da har ya kawo saɓani tsakanin sa da Matar sa ba , ya tsayawa Rahimar har ta samu wani mijin ko da ba ɗan uwansa ba , da Rahima da yaranta basu sha wahalar rayuwa irin haka ba , da suka faɗawa hatsararruka da dama mafi munin su hatsarin Ƴan tawayen Boko Haram , da ko babu kome mutumin birni zai aura mata mai daraja da ƙima kamar ta sa . Yana jin yanzu lokaci ne yayi da zai gyara kuskuren sa , har yanzu yana da damar sake zaɓowa Rahima wani mijin muddin ta amince , 'ya'yan ta kuwa daman Allah ya faɗo da taimakon su ta hannun sa , ashe akwai abunda Ubangiji ya ɓoye , Dan haka ƙudirin haɗin Auren Hamza da Yakaka da ya yi niyyar yi tuntuni ya ji ya sake kaurara a cikin ran sa , har ma ya ji dacewar matso da lamarin kusa , wataƙila da jajircewar da zai yi cikin Rayuwar Rahima da 'ya'yan ta a sauran rayuwar da ta yi masa saura zai samu ya ragewa kan sa girman laifin da yayi wajen tayawa a wargaza rayuwar Marainiyar yarinyar da take amana a wajen sa . Cike da nuna tsantsar kulawa ya shiga jan su da hira ba tare da ya shigo musu da wata tambayar da ta shafi ɓangare na rayuwar su ba , cikin hirar da kusan su biyun ke yin ta a tsakanin su Amnee tace ,     " Baa Alaji , a ƙira yaran nan duk a sanar da su dawowar ƴan uwan su , saboda a sa rana su zo su gana da juna ko kuwa ?   " Hakane , to amma tun da daman nan da ƙasa da sati huɗu ya rage bikin ita Rahima ƙarama kuma a halin yanzu ita da Zainab ɗin duk basa ƙasar suna can Dubai ko da an sanar da su dawowar ƴan uwan nasu sai a bar batun haɗuwar su har zuwa nan da sati biyu da duk zasu hallaru domin bikin Rahima .     " to shikenan Baa Alaji bari yanzu zan ƙira idan mun koma ciki idan ma ya kama a haɗa su a waya su fara gaisawa ,    " to babu laifi , ya zarce da cigaba da cewa,      " Rahima baku da wata damuwa ko ? Da sauri Khaalty Rahima ta amsa ,   " babu damuwar kome Yaya , Allah ya saka da Alheri ya ƙara nisan kwana .   Amin yace yana Gyaɗa kai ya mayar da ganin sa kan su Yakaka ,      " Yarana kuma babu wacce take da wata matsala ko ,? Idan kuna da ita ku sanar da ni , ni tamkar Mahaifi nake a wajen ku Mahaifiyar ku ƙanwata ce ,    Girgiza kai Yakaka tayi , a hankali tace "Baa babu matsalar kome mun gode , Falmata wacce kan ta yake sunkuye ta ɗago kai kamar zata yi magana sai kuma tayi shiru tana sake sunkui da kai ,    Prof da duk yake kallon su yace ,   "Fatima akwai matsala ko ? Meye kike son ki faɗa min , ina jinki ƙaramar 'yata ?   Dukkanin su sai suka mayar da ganin su kan Falmata wacce kan ta ke sunkuye ,   'Baa so nake Dan Allah ka raba auren mu , bana son cigaba da zama da shi ko kaɗan Dan Allah Baa ka sa ya sake ni .    Muryar Falmata ta ratsa wajen cikin alamun da take gaf da fashewa da kuka , Shiru ne ya ratsa falon , tamkar ruwa ya cinye su , kafin Prof yayi gyaran murya yana karantar yanayin ta yace ,    "Fatima shi mijin naki laifi ya yi miki ? Ko kuwa wani abu aka miki daga danginsa ? Ko kun samu saɓani ne da shi ?   Shiru tayi bata amsa ba , sake maimaita mata tambayar yayi nan ma tayi shiru , Khaalty Rahima zata yi magana ya dakatar da ita ,    Ya sake cewa    "ko kuwa kawai daina son shi kika yi ? Ko gajiya da zaman ku tare kika yi  ? Ko kuma can ƙasar tasu ce bakya so ?   Da sauri ta gyaɗa kai , murmushi mai sauti yayi , cike da tausasawa yace " to babu laifi , ki ƙira shi kice na ce ya zo ina son ganin shi , idan ya zo sai a yi miki yadda kike so kin ji ko ? " to Baa nagode . Murmushi yayi bai ce ƙala ba .     **** Niamey Police nationale Maimounatou wacce take zaune daga kan wani ɗan dandamali da aka tanada shi musamman domin zaman waɗanda ake tuhuma da laifi a cikin babban ofishin 'yan Sanda na ƙasar Niger baki ɗaya . Ta muskuɗa tana cigaba da wasa da awarwaron hannun ta , tayi kunnen uwar shegu da duk wasu manya da ƙananun tambayoyin da babban ɗan Sanda da yake tsaye daga kan ta yana jefo ma ta , Ganin taƙi yin magana ya sa ɗan Sandan ƙutawa cike da kaiwa maƙura a jin haushin ta , ya mayar da ganin sa kan Mammadou bayan ya ɗaga takun sa zuwa gaban sa ,    " Mammadou ko za ka iya faɗa mana dalilin da yasa ku ka ciyar da ɗan ouwan ka guba ?      Da sauri Mammadou ya ɗago da kansa ,    " Wallahi ni bani da wata masani kan abunda yake faruwa a

Chapter 83 of 111