tare da makauniyar ƙanwar ta, bata idasa ba malama maryam ta katse ta ,
Kin yi kuskure yakaka , kin yi kuskure , kin yi kuskure ,! Kaicho
wani irin tausayi chakuɗe da bacin rai take ji cikin ran ta , tamkar wata makusanciya a gareta ce ta aikata abubuwan da yakaka ta aikata ,
tun farkon fara koyar da yarinyar ta fahimcin tana da raunin sani sosai da sosai game da addini , kusan ma bata san kome ba , shiyasa ta ɗaura aniyar ganin ta kawo sauyi ta fidda ta daga duhun jahilci , cikin rashin sanin ta ashe jahilci tare da rashin wayon yarinyar har ya kai haka ( Bata san menene zina ba ) ? Ta yadda aka yi amfani da jihilcin aka cutar da ita cuta mai tsanani irin haka ?
Kukan da yakaka take ya tsansnta ganin shirun malama falmata ya ɗau lokaci tare da bayyanuwar matsanancin tashin hankali bisa fuskar ta ,
ALLAH zai yafe miki yakaka , muddin kika nemi yafiyar sa tare da niyyar baza ki sake komawa ga aikata saɓo irin wannan ba , ALLAH me yawan gafara ne ga bayin sa ,
Duk da cewa akwai bayanai daga malamai game da mutumin da ya aikata saɓon Allah alhalin bai san cewa sabon nan me girma bane da zai iya kai me shi ga shiga wuta ,ko kuwa bai ma san saɓo bane baki ɗaya, akwai hukunce hukunce , hukunci na farko shine , Shi JAHILCI ba'a uzuri da shi, sai dai cikin wannan hukuncin akwai bayanai da suke nuna akan karbi uzurin JAHILI , idan ya kasance gurin da ka tashi babu addini , babu malamai masu koyarwa ,ko kuwa an hana ka damar fita neman ilmin kuma ba'a koyar da kai ba a gida , to za'a iya yi maka uzuri da wannan , amma idan gurin da kake akwai addini akwai malumma , sai kaƙi fita ka nemi ilmi kasan hukunce hukuncen addini kayi zaman ka cikin jahilci to wannan baka da uzuri a addini , jahilcin ka ba uzuri bane ,
to amma idan ka rasa damar samun ilmi ne , akwai hadisin manzon Allah sallalahu alaihi wa sallam da yake cewa :
Allah ya ƙetarar da Al'umma ta abu uku , ma'ana ya yi musu afuwa akan abu uku , na farko shine mutum yayi abu cikin rashin sani , na biyu mutumin da ya aikata wani kuskure akan mantuwa , sai na uku wanda aka tilasta ma sa aikata saɓo, !
To idan aka yi duba ga wannan hadisin za'a yiwa mutumin da duk ya aikata wani saɓo cikin rashin sani , uziri a sassauta masa , sannan shi kuma yayi tuba zuwa ga Allah , tsarkakaken tuba ,
Manzon Allah yana cewa : duk wanda yayi tuba na gaskiya to zai kasance kamar bai taɓa aikata wannan Zunubin ba , amma wanda yake tuba alhali yana komawa ga aikata zunubin sa to tamkar yana yiwa Allah izgili ne .
kiyi Tuba na gaskiya yakaka tare da niyyar baza ki sake kusanta kan ki ga aikata ZINA ba a rayuwar ki , Allah zai yafe miki ya wanke ki a idanun Al'umma domin Laifin shi kika yiwa ,
Sannan , ki tashi ki nemi ilmi ki kuma yi aiki da shi idan dama ta samu gare ki kome ƙanƙantar sa ki koyar da ilmin da yake gare ki domin sauran Al'umma su amfana ,
shiriya ta zo miki hasken ilmi ya zo miki ki sa hannu biyu ki karɓe su ƙwarai akwai falala tare da samun dacewa a cikin su , ki manta da rayuwar baya ki himmantu wajen neman gafarar ubangiji akan saɓon da kika wanzu kina aikatawa , da fatan kin fahimce ni ??
bata amsa ba illa hannu da ta kai ta rungume malama maryam , idanun ta na zubar ƙwallar da ita kaɗai ta san dalilin sauƙar su a daidai wannan lokacin
Godiya ta dunga jerowa malama maryam har lokacin da ta sanya ƙafar ta tana barin gidan lokacin dare ya fara shiga karfe goma saura ,
kan titi babu kowa garin ya sake ɗaukar sanyi , a hankali take tafe iska yana ɗaga hijabin ta , tayi zurfi cikin tunani , daki-daki take tuno kome da ya dunga faruwa a rayuwar su ita da ƙanwar ta ,
tana so ta zargi iyayen su akan killace su a gida da suka yi suka hana su neman ilmi , sai dai so irin na tsakanin ɗa da iyayen sa ya mata dabaibaiyi yaƙi bata dama , ji take suna da wata hujjar su , babu shakka akwai dalili ,
tunanin falmata da baby mama yayi mata dirar mikiya , wata irin kunyar falmata ta ji tana nuƙurƙusar ta , yaya zata Ji ranar da duk ta san irin kuskuren da tayi har ta samar da baby mama ta gudu ta bar mata ita ? Wataƙila daga ranar zata fara tsanar ta ,
tsoro take ji tsoron girma ya zowa baby mama ta samu sani akan irin ta hanyar da aka samar da ita , ? Me zata cewa waɗannan bayin Allah biyu ??
Lalle wajibi ne a gare ta ta nemi ilmin addini ko domin ta samun ƙarfin guiwar da zata iya fuskantar su tare da tarin hujjoji da bayanan da addinin ya tanadar domin ta gamsar da su ta kuma wanke kan ta a idanun su su san cewa ta aikata kome ne cikin DUHUN JAHILCI ,!
Ko zasu fahimce ta ? Ko falmata zata yadda ta cigaba da riƙe ta a matsayin ƴar uwa masoyiya ? Ko baby mama zata yadda da ita a matsayin uwa ?? Yaushe wannan ranar zata zo ? Zata zo nan kurkusa , ko sai bayan shuɗewar tsawon wani lokaci ? Abun da ta riga ta sani muddin su na raye wannan ranar zata zo ,
YARIMAN MARAƊI ,
Zuciyar ta ta auno mata da sunan sa da kome da ya wakana cikin rayuwar ta a wannan gaɓar shine sanadi ,
bata gan shi ko kusa tare da duhun jahilci makamancin nata ba , kome da shi yayi mata yayi ne cikin ilmin sa ,da sanin sa ya aikata Zina da ita ,
zuciyar ta take ji tana wani irin buɗawa da sabon yanayin da yake shigar ta akan sa da sabon matsayin da ya kamata ta ajiye shi tun farko a ran ta ,
Tunowa ta fara yi filla filla da farkon haɗuwar su har zuwa ranar ƙarshe da ya kore ta daga motar sa a tsakiyar titi tana kuka , yayi tafiyar sa ya bar ta har yau bai sake waiwaiyar ta ba ,
tabbas shi macuci ne azzalumi agare ta bai chanchanta da samun soyayyar ta ba ko kaɗan ,
bai taɓa son ta ba , kawai amfani yayi da jahilcin ta ya ribaci gangar jikin ta ya yasar da ita tare da cikin da yayi mata , wani irin yanayi mai ƙarfi da kaifi ta ji yana keta zuciyar ta a game da shi , hannun ta ta kai ta tattaro bakin hijabin ta ta riƙe tare da cije gefen leɓen ta na ƙasa da ya zo daidai da zubowar hawayen ta da yake nuni da mummunan ƘULLACIN da tayi masa .... !!!!!!
[9/3, 10:13 PM] +234 806 122 1116: Fikrah writers association
MAFARI
( Hargitsin Rayuwa )
umm'muaz
31
Ba ƙaramin kaɗuwa Youssouf ya yi ba lokacin da Maimartaba yake shaida masa zancen auren sa da Siyama , da har an riga an miƙa dukiyar auren ta ga mahaifin ta dake niamey , za'a yi ɗaurin auren sa da ƴan matan duk biyu a rana guda kamar yadda ya buƙata ,
Ya jima a zaune gaban Maimartaba yana jin yadda zuciyar sa take cunkushewa da tarin takaici ,
Ba tun yau ba ya gama lura da take-taken yarinyar , shi yasa sam baya sakar mata fuska ashe bai sani ba har tayi girman da zata iya yin tsaurin ido irin haka a matsayin ta na mace ta doshi iyayen sa da buƙatar son a haɗa su aure ? Babu shakka zata ɗanɗani kuɗar ta a hannun sa , sai tayi danasanin wannan mummunan shisshigi da tayi ta kutso kan ta cikin rayuwar sa da take a hargitse a halin yanzu ,
Ganin shirun sa ya tsawaita ba tare da ya amsa da amincewar auren ba , ya sa me maimartaba yin gyaran murya
Da fatan ba zaka bijirewa oumarnin mu ba ? Bisa ga wannan haɗi da munka yi na amre tsakanin ka da ƴar ouwar ka , saboda ba muyi haka ba face sai da munka hango tarin alkhaire tare da dacewa sannan munka so ƙulla igiyar amre a tsakankanin ku , wannan ɗiya ɗiyar ƴar uwa ta ce , kai ma kuma ƴar ouwa take gare ka , ina yi maka oumarni ka karɓi amren nan da hannu biyu da ikon Allah gaba kai zaka yi farin ciki .
Kalmar 'Umarni, ta daƙile dukkanin wani yunƙuri da zai iya yi , domin shi ɗin me yawan biyayya ne ga iyayen sa , haɗi da sanin da yayi a yanzu shi me tarin laifuka ne , wanda yake neman wata kafa ko yaya ne da zai iya faranta ran iyayen sa ta dalilin ta, ko domin su iya masa uzuri a duk ranar da laifukan sa suka bayyana a gare su , su duba irin faranta mu su da yayi su sassauta masa hukunci ,
Cikin harhaɗa kalmomin da suke suɓcewa daga harshen sa saboda kaifin su da yake iya ji ya furta ,
Na Amince , Allah shi ƙara girma da ɗaukaka .
Da murmushi bisa fuskar sa yace
Madallah da kai , Allah shi maka Albarka , Ya Albarkaci zuri'ar ka , Allah shi yi katanga tsakanin ka da miƙiya , kana iya tafiya ka fara shiri doumin nan da sati biyu da ranar tayi dai-dai da gomma ga watan gobe ake ɗaurin amre .
Godiya yayi ya miƙe yana barin shigifar sarki , kai tsaye gidan da zai tarar da Tafeeda ya nufa ,
Cikin sa'a ya same shi dawowar sa kenan daga aiki da sanyin la'asar ,
Babu walwala a fuskar sa ya samu wajen zama bisa kujerun shan iska ,
Ɗan ouwa ka kuwa san me ke shirin farouwa gare ni ?
Maida ganin sa yayi kan sa , bayan ya miƙa masa sassanyan lemun da ya tsiyayo masa a kofin gilashi ,
Sanar da ni ɗan ouwa
Wai amren mataye biyu a rana gouda , kuma amre tare da yarinyar nan siyama da ko ƙamnar duban ta bana yi , shin baka yi tounanin akwai wani dalili da ya sa maimartaba haɗa min amren mataye biyu a rana gouda ba ?
Ɗan guntun murmushi tafeeda yayi
Banda abun ka Yarima shin amren mataye biyu a rana gouda ba gata bane ?
Ita siyama ai duk inda ake neman macen amre ta zarta ,
Maimartaba bashi da sani kan kome wataƙila hasashe ne yayi irin nasu na manya ya sanya shi yi maka gatan amra maka mataye biyu a rana gouda ,
Juyar da kan sa gefe yayi yana jin yadda ran sa ke sake ɓaci , kan batun auren , ga kuma ya lura Tafeeda ba shi da niyyar taya shi jimami , shi ina zai kai mata har uku a shekarun nan nasa ??
Kurɓar lemun sa tafeeda yake yi yana satar kallon youssouf da yayi tagumi hannu biyu ya nisa cikin tunani ,
So yake ya masa tambaya game da al'amuran sa na ƙasar nigeria , ɗiyar sa da take can , ƙaƙa ya ƙarƙare da barin ta a chan ? Hannun wa ya baro ta ? Sai dai rashin son tuno masa da ita ya sanya shi haɗiye tambayoyin sa , ga zaton sa Biyamuradi yayi amfani da shawarwarin sa , ya baro duk wasu kuskuren da ya aikata a inda ya aikata su !
Farin cikin da Siyama ta tsinci kan ta cikin sa bai misaltuwa , domin duk wani da ke mu'amala ta kusa ko ta nesa da ita zai iya shaida farin cikin tare da walwalar da ke tare da ita , da ɗai bata taɓa farin ciki me yawan haka ba cikin rayuwar ta ,
Ƙulluwar aure a tsakanin ta da Youssouf wani abu ne da tayi shekaru tana mafarkin sa a bacci ko a farke , bata taɓa zaton zata samu damar mallaƙar sa a matsayin miji a sauƙaƙe haka ba , a kuma daidai lokacin da take zaton ya sulluɓe mata zai zama malakin wata ba ita ba , duk tunanin ta na bata sai wani nisan shekaru wataƙila idan da rabo suyi aure , ga haɓakar farin cikin ta ashe tabbatuwar mafarkin ta zuwa gaske yana kurkusa , ashe tare zasu mallake shi ita da wacce take tunanin ta fita sa'a , ashe sa'ar na gare ne su biyu ,?
Bata ji ko ɗar ba akan sanin da tayi auren su auren haɗin iyaye ne , tare da sanin da take da shi akan irin tsanar da shi yake gwada mata , ta ji ta gani ta amince ta kuma shirya yin zaman aure da shi da gasken gaske , cikin kowanne irin hali , tana jin son da ita take masa zai ishe su rayuwa ita da shi ,
Soyayyar sa ga gimbiya maimouna bata razana ta , illa kishi da ke nuƙurƙusa ran ta , dan haka ta sha alwashin ko da ƙaƙa , sai sun raba soyayyar youssouf biyu ita da maimouna kamar yadda zasu mallake shi a matsayin miji su biyu a lokaci guda , idan ya so ita na ta kason soyayyar idan ya so ya zubda a rariya , bata da damuwa son da take yi masa ya ishe su , .
Shiri take ka'in da na'in ubbo tana taya ta haiƙan , gefe guda hajiya umma na bada ta ta gudummawar a matsayin siyama na ɗiya a gare ta , ɗiyar da ta goya tayi rainon ta tun tana tsumman goyo ,
Lokacin da gnala take sanar da gimbiya maimuna dangantakar dake tsakanin youssouf da siyama har ma da zantukan da ta ji siyama na tattaunawa da ubbo , bata wani ɗau batun da muhimmanci ba , saboda wasu dalilai nata da take ganin ko da ace zai aure su su biyun ita bata jin hakan zai dame ta , burin ta ɗaya tal , shine ta samu nasarar aiwatar da ƙudurin da zai sa ta aure shi .
Dan haka ko da yake kame-kamen sanar da ita batun auren sa da siyamar yana bin ta da kalaman rarrashi , kwantar da murya tayi ta dunga zuba masa sassanyan rikicin da ya sake ɗaga darajar ta a idanun sa tare da sake dilmiyar da shi cikin ƙaunar ta ,
Ya dunga jin yayi sa'ar samun nutsattsiyar mace kuma me haƙuri, wacce mace ce a zamanin yanzu da za'a yiwa kishiya gab da lokacin auren ta , a kuma haɗa su aure rana guda , ba'a yi danbarwa da ita ba ? Ƙwarai ƙwarai maimouna ta ƙara ƙima a idanun sa ,
Samun haɗin kan ta farad ɗaya ya lafa guguwar ƙin auren a cikin ran sa , sai ya samu nutsuwar fuskantar shirye-shiryen auren tare da cigaba da zarya wajen sabon gurin aikin sa da aka tura shi Dosso , inda zai zama shugaban soji na baki ɗayan yankin na jahar Dosso ,
Tafkeken gida aka mallaka masa tare da motocin hawa biyu , ƙari da tarin hadimai sojoji tun daga kan masu gadi , direba , har zuwa kan me girki .
Tsakanin jahar Maraɗi da jahar Dosso babu tazara me yawa , dan haka lokacin da yake da samun tabbacin wajen zama a dosso , sai yayi niyyar bayan bikin su , zai dawo da gimbiya maimouna nan gidan sa na dosso , kusa da shi , ita kuwa siyama ta cigaba da zama can a maraɗi , tunda ita ta zaɓi auren cikin gida sai ta samu matabbata a cikin gidan , !
Sai dai yana sanar da hajiya umma niyyar sa , a take ya ga sauyin fuskar ta ,
Abu guda ta ce da shi .
Kome tsanani kayi ƙoƙarin kwatanta adalci tsakankanin matayen da Allah ya baka amanar riƙon amren su , kar ka kuskura ka karkata ga ɗaya daga cikin su , saboda gujewa fushin Allah da azabar sa ka kiyaye , siyama da maimouna duk su biyun matan amren ka ne .
*****
Tun farkon satin aka fara gudanar da shagulgula da wasannin daga bangaren masarautar maraɗi har da ta Agades wanda suke da tarin wasannani da al'adun gargajiya fiye da na maraɗi , haɗi da shiri sosai da suka yi na bikin kasantuwar kowa ya san gimbiya maimouna ɗiyar gata ce ta sosai ,
Har zuwa yau da take ranar sakun lalle ga amare , gobe juma'a za'a ɗaura auren
Kamar yadda al'adar masarautar maraɗi take , duk lokacin da za'a yi sakun lalle ba'a yi a cikin masarauta ,
can tsibirin maraɗi ake tafiya da amayar ,"wani ƙaramin gari ne da yake ƙarƙashin jahar maraɗi da ake ƙiran sa tsibiri bashi da nisa sosai da ainahin cikin garin maraɗi ,
Gidan sarkin tsibirin nan ake sakun lallen a cikin gidan akwai wata mace da ake ƙira ,inna , wacce sunan sarautar ta ce ,inna ɗin ," ita take sakun lalle ga amaren da duk za'a shigar ko za'a fitar daga masarautar maraɗi,
Karfe ɗaya na rana gimbiya maimouna tare da ƙanwar mahaifiyar ta da ƙanwar mahaifin ta da matar maimartaba sarkin agades ta biyu tare da wasu daga cikin matan ƴan uwa na ƙurƙusa tare da rakiyar amintattun hadiman ta mata biyu da bayu maza uku sai kuma ƙaramar jakaɗiyar agades, jirgin su ya iso tashar jirgin sama na maraɗi daga agades ,inda nan take motocin da suke jiran su domin kai su tsibiri suka ɗauke su kai tsaye zuwa tsibirin maradi ,
Tarɓa me cike da girmamawa aka yi musu , inda suka tarar da gidan cike da manyan mata masu sarauta na kurkusa da fada cikin su har da manyan yayun biyamuradi ,"Ammi da Dada da Asma'u da ake ƙira ma'u ƴar wajen hajiya mama ta farko . ," da kuma ƙaramar jakadiya .
Tsakanin su bai cika awanni biyu ba siyama ta iso ƙarƙashin rakiyar ƙannen maimartaba sarkin maraɗi su biyu tare da hajiya mama da ubbo sai kuma ƙannen baban ta su biyu ,
Ta ko'ina buɗa da ƙirari ne yake tashi saboda makaɗa da maroƙa da suka cika faɗar sarkin tsibiri duk da cewa an dakatar da su daga shiga cikin gidan inda aka fara shirin sakun lallen amaren
Shimfiɗa ce aka yi da manyan jajayen dardumai , a tsakiyar babban ɗakin , inda aka ajiye babban tum-tum na zama a tsakiyar shimfiɗar ,
Inna tayi umarni da a shigo da siyama za'a sanya ta a lalle ,
Ko kafin bangaren gimbiya maimouna su ce kome , hajiya mama ta yunƙuro ,
Wacce siyama kouwa ? Ai ita maimouna ita ce matar farko dan haka ita za'a fara sanyawa ga lalle ko kouwa ?
Hakka zance yake ranki ya dade uwagijiya ta ,
cewar ƙaramar jakadiyar Maraɗi
Aiyuriyuriyyyy ayuririyyyyyy ayyuririyyyy !!
Wata zazzaƙar guɗa ta fito daga hancin jakaɗiyar agades , saboda jin babban matsayin da uwargiyar su ta samu ,
Taka a sannou-sannou ƴar sarki jikar sarki , matar yarima ɗan sarki surikar sarki , gaban ki salama bayan ki lafiya farar macce fitila gida , tauraruowar ki me ƙarfi ce wacce hasken ta ya tarwatsa ya zagaya nahiya tun dagga birnin agades har yankin maraɗi , wouce gabba kin yiwa sauran mata zarra , kin yi gado ba haye kika yi ba mahaifiyar ki ai ita shugaba ta matayen agades ,
A hankali ta sanya kan ta cikin ɗakin tana jin yadda ginshiri irin na sarauta yake sanya ta ƙasaita da jin faɗi.
Bayan shigar ta guda daga bangaren mahaifin ta tare da guda daga bangaren mahaifiyar ta suka rufa mata baya , ubbo ta yunƙura zata shiga hajiya mama ta dakatar da ita tare da yiwa ma'u umarni da ta bisu kamar yadda al'adar take mutum ɗaya daga bangaren dangin miji ke shiga ɗakin sakun lallen .
Bayan zaman gimbiya maimouna inna ta janye hular alkƴabbar dake bisa kan ta , baƙin gashin ta da ya sha gyara ya bayyana , inna ta sanya wata ƴar kyakkyawar kibiyar kitso ta raba gashin biyu hagu da dama ,
Matar da take waziriyar inna ta miƙo mata wani ƙoƙo cike fal da madara sanuwa/nono , ta karkata ƙoƙon a sannu sannu ta fara zuba madarar a daidai tsakiyar tsagun ,
A hankali kakkauran nonon ya fara kwaranya , bisa tsagun kafin ya saki layi ya tarwatse a gaba ɗayan cikin gashin maimakon ya bi kan hanyar da aka masa ƙaɗai ,
Nan take inna da waziriyar ta suka haɗa ido suna masu gƴaɗa kai a hankali , yayin da fuskar ma'u ta sauya tana bayyana ɓacin rai a sarari , har aka gama zuba nono nan haka yayi faca-faca akan fuska da jikin kayan gimbiya maimouna ,
A fusace ma'u ta juya ta fita daga ɗakin gefen mahaifiyar ta ta je ta tsugunna ta mata raɗa , nan take fuskar hajiya mama ya bayyana wani sirrantatcen murmushi , kafin tayi gyran murya tayi wa jakadiya alama da ido ,
Nan take jeka ta karkace kai ta rangaɗa ƙaƙƙarfar guɗa da ta sanya , mutanen agades samun kwanciyar hankali musamman innonin gimbiya maimouna da duk suka sha jinin jikin su , kan shirun da suka ji daga ɗakin ko dai ƴar ta su tayi kuskure ne cikin rayuwar ta ?
Amma jin buɗa daga bakin jekadiyar maraɗi ya sa hankalun su ya kwanta yayin da tasu jakadiyar ma ta karkace kai ta dunga sakin zaƙaƙan buɗoɗi ,
Bayu mata biyu suka jawo wata ɗirkekiyar tunkiya fara sol suka ɗanka ta ga hannun matar sarkin agades ,
Tunkiyar gimbiya maimouna ce ta sakun lalle , nan take bayun agades suka kama igiyar tunkiyar suka riƙe gam .
Ma'u ta koma ɗakin ƙarƙashin umarnin hajiya mama ta sanya farin kyalen ta share fuskar gimbiya maimouna gami da jan hular alkyabbar ta ta rufa mata akan ta ,
Suka fito daga ɗakin ,
Bayan an sauya shinfiɗa da wajen zama aka yi umarni a shiga da siyama ,
Ƙanwar mahaifin ta ɗaya tare da hajiya mama sai kuma ubbo su ne suka shiga da ita ta zauna akan tum-tum
Inna ta tsaga gashin ta , ta karbi ƙoƙon madarar ta shiga tsiyayo mata shi daga tsakiyar kan ta sannu sannu ya shiga bin layin yana gangarawa har zuwa kan siririn karan hancin ta yana ɗiga a gaban rigar ta , har nono ya ƙare bai karkace hanya ba ,
Wata ƙarƙarfa guɗa ce ta taso daga hancin inna da tayi amsa kuwwa har fada da nan take makaɗa suka ƙara ƙarfin kiɗan su da ƙirari ,
Daga waje ma bayun masarautar maraɗi suka dunga sakin buɗa ba ƙaƙƙautawa ,
Zuciyar hajiya mama tayi bakikkirin lokacin da ubbo ta sunkuya ta ɗau farin kƴallen tana gogewa siyamar madarar fuskar ta idanun su suka gauraye cikin na juna sassanyar ƙaunar da take tsakanin su tayi tasiri idanun siyama suka ciko da ƙwallar murnar ganin wannan ranar me cike da ɗinbin tarihi a wajen ta , a hankali ubbo ta kai hannun ta duk biyu ta rungumo siyamar zuwa jikin ta , a hankali ta raɗa mata a kunne
Madallah da ke ƙauna ta ɗiyar kirki , me daraja ,Madallah da ke mace tagari abar alfaharin iyayen ta da mijin auren ta !
Ko kusa ran hajiya mama bai yi daɗi ba da cikar budurci da alamu suka bayyana ga siyamar kamar yadda al'adar daman take nuni ne da macen da take cikakkiyar budurwa ita ce wacce nonon ke bin dai-dai tsagun layin ba tare da ya karkace ba , ta so ƙwarai ace an samu matsala irin wacce aka samu ga gimbiya
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Chapter 110
Chapter 111
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 48 Chapter of 111