Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
girgiza fuskar ta ,"      Meƴe ya same ki falmata ?     Falmata ki tashi dan Allah     Ki tashi falmata ? Ki tashi Hasken tocila ne ya fara hasko su daga nesa kafin mutanen su ƙaraso ," tun kafin tayi magana suka yunƙuro da hanzari suna tambayar ta me ya samu ta kwancen kuma me suke anan ? Cikin kuka take rokon su akan su taimaka su ɗauki ƙanwar ta zuwa asibiti , basu yi ƙasa a guiwa ba suka ɗauki falmatan chak tare da kai ta ɗan ƙaramin ofishin da aka tanada a matsayin ƙaramin asibitin bada taimakon gaggawa ,' Yana zaune yana kammala shigar da wasu muhimman bayanai da suka shafi aikin sa ta computer suka faɗo masa duuu babu sallama bare neman izni ," Da ido ya bisu har suka shimfiɗe ta akan ɗan siririn gadon da aka tanadar domin marasa lafiya ," suka yi tsaye charko-charko sun tasamma mutane ishirin a cikin ofishin a tsai-tsaye banda waɗan da suke daga wajen baranda da idan aka haɗa zasu kai rai hamsi duk ƴan rakiya ne ," Cikin nazari yake kallon su ɗai-ɗaya ta cikin farin gilashin da yake manne akan fuskar sa bayan ya rufe computer gami da tokare hannuwan sa biyu akan teburin ya ɗago haɓar sa da su , cikin ranshi yana jimanta rashin hankali da gidadanci na wasu mutanen ƙauye ,"    Chan daga waje yake jiyo tashin ƴar siririyar muryar ta cikin kuka tana ambaton sunan "Falmata''wanda hakan ya sa da sassarfa ya nufo marar lafiyar da aka kwantar da bai kai ga sanin meye ya faru da ita ba ," Da taimakon hasken ƙwan lantarki fari sol da ya haske ofishin ya shaida fuskar ta duk da cewa ta ɗan kunbura a sakamakon shatin yatsu da suka kwanta tar a gefen da gefen fuskar ta ta da kuma laɓɓan ta da suka ɗan kumbura ,"amma hakan bai hana shi gane ta ba ," Me ya same ta ?? Ita ce tambayar da ya jefo musu a dai-dai lokacin da ya ɗauko abun auna bugun numfashi ya ɗaura shi a saitin kirjin ta ,' kallon-kallo aka shiga yi tsakanin mutanen da suke a cike a ɗakin domin duk cikin su babu wanda ya san takamaimai meye ya faru ga falmatan Ganin sun yi shiru ya sa shi sake cewa " ina ƴan uwan ta ?    Mutane biyun da suka ɗauko ta suka ce ƴar uwar ta tana waje ,"   " Ku ƙira ta" Da kyar ta samu hanya ta kutso cikin ɗakin idanun ta na yararin ruwan hawaye har ya jiƙe gaban hijabin ta , Gaban gadon da falmatan take kai ta zo ta tsaya ba tare da ta lura da wanene likitan ba ita dai babban burin ta ,  ta ga falmata ta motsa tsoron ta tare da taraddadin ta kar ace mata wani mummunan abu ya faru ga ƴar uwar ta , Tun da ta shigo yake bin ƴar siririyar fuskar ta da kallo , daga ƙarƙashin ruhin sa yana zumuɗin kallon cikin ƙwarar idanun ta ," Me ya same ta ? ,"   Itace tambayar da ya jefa mata bayan yaƴi umarnin ga sauran jama'ar akan su basu wuri zai yi aikin sa , maida duban ta tayi gare shi ,"karaf suka haɗa ido ," Tiryan-tiryan ta shiga bashi labari , yayin da shi kuma ya duƙufa wurin bada dukkanin taimakon gaggawar da yake ganin yakamata ga falmata sai dai falmata bata motsa ba ," Zama yayi tare da ɗaukar wayar sa kira yayi tare da bada umarnin tahowa da motar asibiti domin ya fahimci matsalar falmata ta zarce ƴan kayan aikin da suke nan ," kallon sa ya mayar ga fuskar yakaka wacce tayi jazir sakamakon kukan da take ta faman yi ,"     Kiyi hakuri ki daina kuka ƙanwar ki ta samu attack ne na ciwon ta a sakamakon toshe mata hanyar numfashi da aka yi wanda ya jawo huhunta ya wahalta kasantuwar daman tana ɗauke da cutar asthma amma insha Allah zata samu sauki numfashin ta zai dai-daita yanzu motar asibiti zata zo akai ta babban asibiti domin bata cikakkiyar kulawar da ta dace da masu irin ciwon ta sannan kuma jami'an kiwon lafiya mata su duba ta domin cikin bayanin ki ina zargin ta faɗa hannun ƴan ɓata gari ne," Tun da ya fara bayani yakaka take ƙara sautin kukan ta zuwa lokacin da ya gama mata bayani kuwa sosai take kuka har tana shiɗewa sakamakon ji da tayi falmata tana ɗauke da wata cutar da har sai an dangana ga babban asibiti ,'kuka take bilhakk . Komawa yayi ya zauna tare da jingina da jikin kujerar sa bayan ya rintse ƙwarar idanun sa , saboda sosai kukan ta yake taɓa masa ruhi , gashi kuma bai san yaya zai yi da ita tayi shiru ba , Cikin abunda yake ƙasa da mintuna sha biyar motar asibitin ta iso aka shigar da falmata cikin motar tare da yakaka wacce taƙi fur ta saki jikin falmatan da zuwa yanzu numfashin ta ya fara komowa amma sama-sama , Suna zuwa babban asibitin gwamnatin jaha ,aka ƙarbe ta tare da shigar da ita ɗakin bada taimakon gaggawa karkashin ƙulawar dakta hamza da daman ya kasance babban likita ne shi a asibitin , zama dirshan yakaka tayi akan tiles ɗin wurin tare da dunƙulewa wuri guda ,bata ko damu da mutanen da ta zo ta tadda a wurin da su ma suka kawo marasa lafiyan su da kuma sauran mutane masu wucewa da suke mata kallon tausayawa ba , Bayan share zaman mintoci arba'in da ƴan kai , wanda yakaka baza ta iya fasalta iyakacin ruɗani da hargitsin rayuwar da ta shiga ba a ƴan mintocin , dakta hamza ya fito cikin alhini da rashin kuzarin da fargaba suka haddasa mata ta ɗago idanun ta da suka kumbura tana tuhumar sa da su domin ta gaza buɗe baki ma tayi magana ," Ɗan lallausan murmushi yayi tare da yafitar ta da hannu ," a sanyaye ta miƙe tana gama hanya ta bi bayan sa zuwa cikin ainahin ɗakin ," Daga bakin kofar ta jaa ta tsaya lokacin da ta hango falmatan ras a zaune a bakin gadon asibitin,wata irin dariyar murna ce ta subce mata kafin ta taka da gudu ta tsalleƙe ƴar tazarar da take tsakanin su tare da rungumo falmatan wacce ita ma ta washe ƴan haƙoran tana dariya da jin sautin dariyar yakakan da take nema tun da ta farfaɗo , fuskar ta sayau da alamun rashin kuzari a tare da ita sakamakon allurorin da ta shaa har da ƙarin ruwa ," Falmata nah sannu , sannu sannu dan Allah me suka miki ?? Wacce irin cuta ce take damun ki falmata ciwon ki ya tsorata ni , irin tsoron da zan iya mutuwa idan ya zarta haka dan Allah falmata kar ki sake irin wannan rashin lafiyar ," gaya min ina ne yake yi miki ciwo yanzu , meye suka miki ?? Dakta hamza wanda yake tsaye ya harɗe hannunwan sa a kirji yana kallon su , karon farko da yaga wata irin tsaftatatciyar zallar ƙauna a tsakanin ƴan uwan biyu ,"shi ya amsa mata dukkan tambayoyin ta . Cutar asthma ce take damun ta , asthma cuta ce da take kama huhun mutum ya zamana huhun mutum yana kumburi tsokar huhun tana matsewa tare da rurrufe hanyoyin da iska take shiga wanda hakan yake bada matsala wurin shiga da fitar iska / numfashin ɗan adam , alamomin cutar sun haɗa da tsananin tari musamman cikin dare zuwa wayewar gari , gwarnaki , da kuma ɗaukewar numfashi ko kuma yin ƙarancin sa , ana iya gadon cutar asthma ta iyaye , ana kuma iya samun cutar ta hanyar ƙura idan tayi yawa , ko ta hanyar shaƙar iskar gas , ko kuma tsananin sanyi , cutar asthma bata da wani maganin warkar da ita baki ɗaya sai dai akwai magungunan hana samun farmaƙi daga cutar ," sannan ya zama dole me cutar ya kiyaye kan sa daga shaƙar ƙura ,shaƙar iskar gas ,zama cikin wurin da yake da tsananin sanyi ko kuwa shan abu mai matsanancin sanyi domin bawa kansa kariya daga samun farmaƙin ciwon ," Numfasawa yayi yana me gauraye idanun sa cikin na yakaka wacce tayi kasaƙe tana sauraran sa idanun ta tar akan fuskar sa , lumshe idanun sa ya sake yi lokacin da ya ji wani yanayin shauƙi yana fusgar sa a sakamakon kallon cikin idanun ta da hasken ƙaton farin ƙwan wutar da yake cikin ɗakin ya haska su suke wani irin sheƙi tamkar ba yanzu suka gama ambaliyar hawaye ruwan ba ," Sannan ƴan bata gari sun yi yunƙurin lalata ƴar uwar ki ta hanyar yi mata fyaɗe sai dai a binciken da muka gudanar basu riga sun cimma nasara ba ,Allah ya kiyaye ta sai ku kula da gaba ,  ga sister zahra zata sake yi muku bayani dalla-dalla , zaku kwana anan zuwa gobe da safe muga yanayin jikin nata sai mu sallame ku , Duk da cewa ba duka kalmomin sa yakaka da falmata suka gane ba amma sun fahimci dai falmata tana da wani ciwo wanda yake riƙe numfashi a irin fahimtar su , sai dai daga yakaka har falmata babu wacce ta wani damu sosai saboda suna ganin ta samu sauki saboda falmatan ta bada tabbacin bata jin kome a halin yanzu lafiyar ta ƙalau sai ko ɗan rashin karfin jiki dan haka su ran su yau ƙwal zasu yi kwanan sabon wuri kwanan ƴanci , kwanan cikin haske , ga falmata kwanan kan gado da katifa duk da ba wani taushi bane da katifar asibitin amma ga falmata abun daɗi ne tun da kuwa yau ne karon farko da ta hau gado da katifa a gaba ɗaya tarihin rayuwar ta ,"dan haka da walwala akan fuskokin su suke yiwa dakta hamza godiya wanda yake bin su kawai da ido tare da gƴaɗa kan sa ,"ya kuma juya yana mai sake jaddadawa wata ma'aikaciyar jinya wacce ya kira da suna zahra akan ta tabbatar tayi musu bayanin kalmar fyaɗe tare da nisantar hulɗa da duk wani ɗa namijin da ba muharramin su ba , "wanda shi da kan sa bai san dalilin da ya sa yaji ya damu akan son su nisanci hulɗa da maza har yake jin da yana da dama da ya killace yaran , sai dai kawai ya ɗauki hakan a zuwan tausaya musu da ya fara yi da fahimtar da yayi basu da wani gata bayan Allah sai su biyun da junan su suka dogara ,' Har ya taka ya nufi bakin kofar ficewa daga ɗakin bayan yayi musu sallama domin barin asibitin , sai kuma ya juyo gami da nufo wurin da yakaka take zaune akan kujera daga gaban gadon falmatan ," Janyo wata kujerar yayi tare da zama a daf da yakaka wacce tayi wuri wuri tana tunanin me kuma zai sake zaunar da shi ? Domin ita dai sam bata sakewa idan yana wurin wani irin nawi take ji daga ƙarƙashin ran ta da zuwa yanzu ta kasa fahimtar menene , abu ɗaya ta sani shine daga farkon haɗuwar su da tsiya suka faro ta tare da kullatar shi gami da jin tsanar sa cikin ruhin ta, sai dai daga ranar da ya fara taimakon ta zuwa yau ,ta kasa sanin takamaimai a wane mizani ta ajiye shi , ta dai san ƙwarai ta fara ganin girman sa daga haka baza ta ɗorar da kome ba bayan faɗuwar gaban da take ji a duk lokacin da idanun su suka sarƙe cikin na juna , shi yasa sam bata son kallon idon sa , Umarni ya bada aka miƙo masa ƴan kananun kayayyakin wankin ciwo idanun sa akan laɓɓan ta da na ƙasan ya kumbura ," Da kansa ya wanke mata ciwon da ta ji a sanadin dartse laɓɓan , yana yi yana kallon idanun ta da suke runtse gam a saboda ɗan radaɗin maganin wanke ciwo , a hankali kalmar , "sannu" ta subto daga bakin sa bayan da ya gama wanke mata ciwon ,yana bin fuskar ta da kallo ," ya daina zafi ko ? A hankali tana me kaucewa kallon idanun sa ta 'gyaɗa kan ta ," nagode Miƙewa yayi ,"ki zo ki sayo muku wani abinda zaku ɗan ci a waje ," Tare suka jero duk inda suka wuce tsirarun ma'aikatan asibitin da suke aikin dare , sai sun isar da gaisuwar su , har suka fito bakin asibitin babu me cewa ƙala a tsakanin su ," zaro gudan dubu ɗaya yayi a aljihun sa ya miƙa mata tare da gwada mata tsallaken titi wurin wasu mata masu toye-toye da kuma masu sayar da shayi ,     Tare da ɗan durkusawa ta miƙa hannu biyu ta karbi kuɗin tana godiya , bin bayan ta yayi da kallo har sai da ta tsallaka titin kafin ya juya cikin asibitin inda ya ajiye motar sa ya shiga gami da bata wuta ya bar harabar asibitin ,' Bayan sun ci masa/waina tare da ruwan bunu shayin da yakaka ta sayo musu a waje , sai suka tattara hankulan su baki ɗaya ga sister zahra da take yi musu bayani dallah-dallah game da fyaɗe ta kuma tsoratar da su sosai game da yin tarayya koh wasannin banza da maza , sun kuwa tsoratu har cikin rayukan su fiye da zaton ta domin su dukkanin su biyu kwana suka yi tare da tunanin maganganun da ta faɗa musu , wanda ya sa suka ji baki ɗaya zaman sansanin nasu ya fita akan su , ga zaton falmata mazan sansanin su ne kaɗai suke iya yiwa mace fyaɗe su yi mata ciki ,"     Yakaka nikam bazan koma sansanin mu ba dan Allah mu samu wani waje mu dunga kwana koh aina ne ' cewar falmata kenan lokacin da gari ya waye likitocin aikin safe suka zo suka duba su tare da basu sallama bayan sun tabbatar da ta samu lafiya ,bata kuma cikin hatsari ," Nisawa yakaka tayi wacce itama har ga Allah bata son komawar sun sansanin su , ko kusa bata son abun da zai ɓata rayuwar falmata , duk wani abun da ya shafi falmata bata ɗaukar sa da wasa ," Falmata nima bana so mu koma sansanin mu , toh amma bamu da wurin zuwa da ya fi chan ɗin , bamu da kowa ba mu san kowa ba ," Mu tafi wurin uwarɗakin ku yakaka , mu roƙe ta  , ta yadda ta bamu wurin kwana koh da a zaure ne , Zubawa falmata ido tayi tana juya shawarar ta ta cikin nazari , tana hasashen madam saly baza ta ƙi taimakon su ba toh amma gidan madam saly ma ai sansanin maza ne , mazan ma tambaɗaɗɗu ƴan iska , har ma gwara na sansanin su ," Girgiza hannun ta falmata tayi , ta ɗago ta dubi fuskar falmatan da hawaye ya silmiyo ,"   Yakaka dan Allah kar mu koma sansani , ajus baza ta daina aikena wurin ƴan maza ba ni kuma tsoro nake ji yakaka dan Allah kar mu koma ," Da sauri ta sanya hannu ta goge mata hawayen ,"kiyi shiru falmata baza mu koma ba ," A hankali suka tako zuwa wajen asibitin , duk da cewa yakaka ta so su jira dawowar dakta hamza domin ta bashi chanjin sa naira ɗari takwas da yake hannun ta , toh amma kukan falmata ya kaɗa mata hankali bata jure damuwar falmata , sai dai har zuwa yanzu da suka fito bakin titin suka jaa suka tsaya hankalin ta ya kasa kwanciya da zama a gidan madam saly tare da ƙanwar ta , Kamo hannun falmatan tayi ta zaunar da ita lokacin da wani tunani ya ɗarsu a ran ta ,"    Zamu je gidan madam saly mu roƙe ta mu zauna zuwa wani ɗan lokaci , sai dai da sharaɗi falmata , Sharaɗi ?   Eh sharaɗi falmata , gidan madam saly matattarar ƴan maza ne , ba kamar yadda kike zato bane falmata , gidan madam saly gidan ƴan iska ne , kin ga ke kuma falmata baki da lafiyar idanu zasu iya cutar da ke kamar yadda na sansanin mu suka so yi , dan haka na samo mana wata dabara , idan zaki yadda , Zan yadda koma menene yakaka idan har baza mu koma sansanin mu ba ," Zaki koma namiji falmata Zaki koma saka kayan maza Zan aske miki kan ki , domin ta haka ne kaɗai a yanzu zan iya kare ki daga ƴan maza kin yadda ?? Baki buɗe falmata ta ware manyan idanun ta tana juya su a saitin wurin da take jiyo sautin muryar yakaka tamkar dai tana kallon ta ,' !!!! .    Kar ku manta da kankaro mutunci , Iya adadin sharhi da nuna kulawar ku iya karfin da zan samu wurin cigaba da rubutu      Nagode. #umm'muaz #fikhr #son so[6/24, 10:57 AM] +234 701 013 7848: Fikrah writers association MAFARI... ( Hargitsin Rayuwa) umm'muaz 16 Tafe suke su biyu akan hanyar su ta zuwa gidan madam saly , idan ba wanda yayi musu farin sani tar-tar ba , babu ta yadda za'a yi a gane falmata mace ce , sakamakon askin tal kwabo da yakaka tayi mata da sabuwar rezar da ta saya , sai walwali da ƙƴalli mummulallen kan ta yake , jikin ta kuwa sanye take da wasu afarangiya da wondo na maza da suka yi mata bururum-bururum wanda yakaka ta saya mata a kasuwar tsaye da sauran chanjin dakta hamza , Fuskar falmata sam babu walwala saboda dole kawai yakaka tayi mata har ta amince kan ta ya sha askin da tun da aka yi mata shi take jin kan ta sakayau tamkar zai faɗo ga uwar ranar damina da ta fara ɗagawa "hantsi ya dubi ludayi" , wannan karon hantsin kan falmata ya duba ," Yakaka nikam gaskiya bazan iya sake yadda ki min wani askin ba idan har gashi na ya sake fitowa kamar yadda kika ce ,"saboda gaskiya zafin rana tana ƙona min fatar kai ,sannan kin ga kullum a rana nake wuni a zaune ," Cikin tausayawa tare da ganin laifin kan ta yakaka tace ,"    Ki daure kiyi hakuri falmata ni da kaina ba'a son raina ba ne na aske miki suma ,bamu da wani zaɓi ne bayan hakan ,kina sane dai da yadda mazan gari nan suke ƴan iska ," kiyi hakuri nan gaba bazan sake suɗe miki kai tal kamar haka ba zan dunga bar miki kaɗan ,"     Me zai hana ki saya min hula kawai ?? Ki barmin kaina ba tare da kin aske ba idan ya so na cigaba da sanya kayan mazan a zuwan ni tamiji ce , tunda ba wanda ya san mu a gidan madam ɗin sai yagana da kolo ," Yakaka bata samu zarafin amsa mata ba sobada sun kawo gidan madam saly ,       Cikin yin ƙasa-ƙasa da murya tace kiyi shiru falmata mun zo gidan , kar kiyi wani abun da zai sa wani ya fahimci ke mace ce ,"   Fuska a turɓune falmata tace " toh" Tun kafin su ƙaraso ainahin cikin gidan suka soma tsinkayo muryar madam saly wacce take ta bala'i da dure-duren ashariya akan satar da ta wayi gari an ɗunguma mata har ta naira duba ishirin ," Ƙarasowar su ta zo dai-dai da cewar madam saly ," kuma na rantse daga yau duk wasu ƴan zaman fara ƴan zaman alfarma su nemi inda dare yayi musu tun da abun ma ya zama haka , kayi wa mutum rana yayi maka sulusin dare , ji min ganin arhar gabas ? daga yau babu shegiyar ƙaramar karuwa da zata sake kwanan min cikin gida kun dai ji na rantse ai daman kome aka yi da sabara sai ta yi kere," ta karasa tana sake shigar da mici-micin idanun ta da suka yi jaa domin bala'i ! Duk da yakaka ba duk kalaman madam saly ta kai ga fahimta ba , amma ganin ta cikin maɗaukakin bacin rai ya haka , yayi matuƙar tsorata ta tare da dukushe mata ƴar ƙwarin guiwar tunkarar ta da batun dawowar su zama a wurin ta ," A fusace ta juya ga su yakaka lokacin da taji yakakan tana gaida ta bayan ta ɗurkusa guiwar ta biyu a ƙasa ,"        Ba tare da ta amsa mata ba ta maida ganin ta kan falmata wacce take tsaye kiƙam tana jujjuya idanun ta kan nan sai sheƙi yake tare da ɗaukar idanu.,' Wannan ɗan ƙolon fa ? Shi kuma daga ina ?? Cikin sanyin murya da inda-inda yakaka tace"  ƙani na ne " tana mai sanya hannu ta jawo hannu falmata ta ɗurkusar da ita ,"      Ina kwa..... Ko kafin falmata  ta ƙarasa kalmar gaisuwar da ta ɗauko nufin yiwa madam saly , tsawar ta ta katse mata hanzari ,"     Miƙe miƙe maza-maza ka kama gaban ka , ka tafi barar ka ni nan bani da buƙatar irin ku , ke yaks ɗan uwar ki wane ɗan iskan ne yace ki kawo min ƙanin ki nan ? Ko nace miki ina bukatar almajiri ne ? Oya kama hanyar ka kayi tafiyar ka kwa haɗu a mahaɗar ku kar na sake ganin ka a gidan nan ," Gaba ɗayan su sun firgita da tsawar da tayi musu musamman ma falmata wacce kalma korar da aka yi mata ta sanya ta jin ruwan hawaye ya fara taruwa a gurbin idanun ta ," Madam kiyi hakuri , shima na kawo shi ne ko akwai aikin da zai dunga yi miki ,?         Aikin ubanki wannan ɗan tatsitsin yaron zai min ? ,"     Kai tashi kayi naka guri nace ," ta furta hakan tana zazzarowa falmata ido ,wacce dirin muryar madam saly cikin faɗa duk ya bi ya diririta ta tare da dasa tsoron ta cikin ran ta anan take har ma ta ji ta fara nadamar zaɓar gidan ta a matsayin wurin mafakar ta , Cikin muryar kukan da ya bayyana kansa yakaka tace ,"      Makaho ne madam dan Allah ki taimaka mana ki bamu wurin da zamu dunga kwana wallahi zan dunga yi miki aiki daga safe har dare koh baki biyani ba ni dai kawai ki taimake mu ni da ƙani na ki bamu wurin kwana ,? Kallon hadarin kaji madam saly take yi ma ta ,"     Yau ji min gantalallun yara ke yanzu ni ce zan baku masauki ke da musaƙin ƙanin ki ?? Dan uban ki yaks kin ga gida na yayi kama da masaukin baƙin ƴan gudun hijira ?? Ciki ma har da muskinai ? Ke ma ai kin sa wanan abun bazai yi yu bane "auren mage da ɓera " an faɗa miki nan gidan sarkin unguwa ne koh kuwa gidan mai gari ?? To bari kiji ni bani da wurin ajiye ke kan ki bare miskinin ƙanin ki , toh na ci uwar me da ku ??gayyar na ayya gayyar tsiya gayyar ƙwarƙwata da tsumma, dan aikin da kike min daga na ɗaga murya nayi cigiya zan samu madadin ki , dan haka tun wuri ki maida ƙanin ki inda kika ɗauko sa ,ki zo ki kama min aiki na , kina cin lokacin aiki kin kuma san dai doka ta ban yadda da asara ba ," Ɗan liti wanda tun shigowar su yake tsaye a gefe ya kafe yakaka da falmatan da idanu ,yana nazarin ɗan dirarren yaron mai ƴar kyakkyawar zagayayyar fuska da yakaka ta kira da kanin ta ," yayi charaf ya chafe zancen jin ana shirin korar masa hanyar samun abebaɗan arziki ! Haba haba madam saly tayaya arziki yana bin ki kina guje masa ," kuma ai a so kare har bindin sa !      Ya furta hakan yana farfari da ido A harzuƙe madam saly wacce ta koma daga bakin kofar ɗakin da ƴan matan ciki ke tattataro ƴan kayayyakin su suna fitowa ta juyo ,' waɗan nan ne hanyar arzikin liti bana son ƙazamar kalma," wai me kuke jira ne ?? Ta wurga tambayar ga yakaka wacce zuwa lokacin kuka take yif-yif suna durkushe cikin rana ,"  

Chapter 16 of 111