Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
irin mutanen da ƙwaya ta gama musu illa a rayuwa suka zama marasa amfanin da ba zasu iya yiwa kan su ba ma bare su yiwa wani . To ai daman a rayuwa muddin Shaiɗan ya zama jagorar ka ba zai kauce ba har sai ya kai ka tsakiyar kogin nadama da ba kuma za ka iya fiddo da kan ka ba. *** Yakaka da Doctor Hamza kamar kullum suna kitchen da safe suna aikin su tare da dai mafi yawan aikin Doctor Hamza ne ke yi saboda kome Yakaka ta ɗauka za tayi sai ya hana yace kar ta wahalar da kan ta da Babyn sa . Suna gaf da kammala haɗa abun Breakfast ɗin su tattabarun rannan suka sauƙo sai dai a yau su uku ne tare da su da 'yar wata matashiyar tattabara da duk alamu ba'a jima da fara fita da ita kiwo ba. Da sauri Yakaka ta nuna masa su tana cewa "Laa Habibi ka ga tattabarun mu na rannan har sun samu baby ko ba su bane .? Da sauri Doctor Hamza ya mayar da ganin su kan sa yama dariya yace "ai kuwa sune wai har sun haihu ? Gaskiya sun yi ƙoƙari . "Ba dan nima dai ga nawa Babyn yana hanya ba ai da sai nace sun cinye mu a wasan . Dariya Yakaka tayi tana ɗiban 'yar shinkafa ta watsa musu kafin ta taya shi su kwashe abincin karyarwar su kai falo . Bayan sun gama brakfast suka yi wanka Yakaka ta taya shi ya shirya suna yi suna 'yar soyayyar su da ba'a cika magana a cikin ta sai da suka fito za ta masa rakiya yana riƙe da kunkumin ta sannan yace "Wafaa  kin ga na manta har zan fita ban sanar da ke ba ƙanwar abokin aikina da yake nan unguwar ai kin san shi ko Doctor Abdallah ? Gyaɗa kai Yakaka tayi tana jin zuciyar ta na sauya bugu da ba ma zata iya bada amsa da baki ba. Murmushi Doctor Hamza yayi yana mayar da ƙofa ya rufe ya jawo ta jikin sa ya matso da ita Sosai cikin ta ne kawai ya tokare ya hana haɗuwar ƙirjin su . Muryar sa a ƙasa-ƙasa yace faɗa min meye a zuciyar ki na ji ta sauya bugu me kike tunani ? Girgiza kai ta sake yi cike da ƙagautuwa ta ji ƙarshen zance tace "ba kome , habibi me ya faru da ƙanwar Doctor Abdallah ? 'Yar sassauƙar dariya yayi ya jaa karan hancin ta kafin yace " sunan ta Madina ma'aikaciya ce a ƙungiya mai zaman kanta da take bada tallafi ga kasashen da annoba ta fadawa a sakamkon yaki ko na ɓullar cutuka watau NGOs babbar ma'aikaciya ce a kungiyar da bata dade da da dawowa daga... Cike da gundura Yakaka ta Katse shi "Habibi mana to ni meye alakata da ita? Wannan karon dariyar da yake gintsewa ita ce ta bayyana ya shiga kyakyatawa ganin haka yasa idanun Yakaka cika da ƙwalla ta fara ƙoƙarin zamewa ta bar gurin . Da sauri ya riƙo ta gaba ɗaya ya rungume ta a jikin sa yana dai-daita nutsuwar sa daga barin yin dariyar da yake yace "Wafaa aina kika koyi kishi haka un ?? Haka kike sona ashe ? Ki kwantar da hankalin ki Wafaa ni naki ne ke kaɗai da yardar Allah babu wacce zata sake ratsa tsakanin mu ke kaɗai kin isheni rayuwar duniya kin ji ko ? A tare suka yi ajiyar zuciya kafin ya cigaba da cewa "Abdallah shine ya bani labarin ƙanwar sa da shirin da take yi na tafiya Maiduguri domin yin aiki dalilin da yasa ya min zancen domin ya ji yaya lafiyar garin yake ? To bayan na ba shi amsar da ta dace shine har ma na ɗan ba shi bayani akan labarin rayuwar ku yadda kuka kasance a matsayin 'yan gudun Hijira har ma ya sake jimantawa to ashe ya faɗawa ita ƙanwar ta shi sai jiya yake shaida min cewar wai na nemawar Madina izni idan har kin amince tana so ta zo yau ta ɗan tattauna da ke kan yadda rayuwa ta kasance muku a Sanadin Boko Haram . Ya ɗan tsahirta kafin ya ɗora da cigaba da cewa "Wafaa da fatan ban saɓa miki ba da na bada wani ɓangare na labarin ku ba tare da amin.... Da sauri Yakaka ta rufe masa baki da lallausan hannun ta tana girgiza masa kai  tace "Habibi kar kace haka ni wallahi baka min laifin kome ba ina maraba da Madina kace ta zo insha Allah za ta iya samun duk wasu bayanai daga bakina daidai gwargawdon yadda rayuwar mu ta kasance . Sumbatar ta yayi a goshi kafin ya sake ta yana jin yadda take ƙara shiga ransa saboda sanyin halin ta . Daga nan rakiya ta masa ya tafi cike da kewar juna da suke ji a koyaushe idan zasu yi rabo da juna ko da na awa guda ne . Bayan ta dawo cikin gidan da ƙwazo irin nata ta gyara gidan tsaf tana yi tana hanzari tana duba waya dan kar lokacin ƙiran ta kula da Ukhtee yayi . Ta gama ƙarfe tara cif tana zama kuma Falmata ta ƙira ta a skype bayan sun gaisa Falmata tana tsokanar ta Maman biyu sai ta haɗa Su da Ukhtee ita ta shiga lectures. Da kamar kullum idan za ta shiga lectures da take yi a sati sau uku Ukhtee bata yarda da mai rainon ta ta riƙe ta har Falmata ta gama ihu za tayi ta yi tana kuka . Sai fa idan an ƙira Yakaka a Skype an haɗa su nan ne kuma babu ruwan ta da Falmata bare wata mai raino za tayi ta damuƙar wayar tana gwalatu da dariya Yakaka na biye mata tana mata wasa har tayi bacci idan ta farka kafin Falmata ta fito Yakaka za'a sake ƙira ta kula da ita ta waya . Wata irin ƙauna da shaƙuwa ce ta ban mamaki a tsakanin Su biyu yadda Ukhtee ta gane da Falmata da Baban ta haka ta gane da Yakaka haka kuma take son ta . Sai da ta gama mata wasa ta samu tayi bacci sannan suka yi sallama da mai rainon ta ajiye wayar fuskarta ɗauke da murmushi tana jin ƙarin ƙaunar Ukhtee na bin jikin ta "daga an yaye ki zan je na ɗauko ki takwara koda kuwa Baban ki baya so sai dai yayi haƙuri sa samu wasu bayan ke amma ke kam tawa ce 'yata 'yar gidana. Ta furta hakan a sarari dai-dai lokacin da aka ƙwanƙwasa ƙofar gidan. A hankali ta miƙe tana ɗan tura cikin ta gaba da duk cikin watannin sa biyar amma yayi girma sosai "Matar likita ko 'yan tagwaye zata haifa ? Lokacin da ta buɗe ƙofar sai ta ci karo da wata kyakkyawar mace da zata girme mata da kaɗan a shekaru wacce kallo ɗaya tal za'a mata a hango tarin ilmin Boko da wayewar da suka samun wajen zama na dindin a tare da ita bayan hutu da yake numfasawa a jikin ta . Daga kan takalman ƙafafun ta marasa tudu har kan ɗan farin gilashin da yake saƙale akan doron siririn karan hancin suna nuni ne da irin tsadaddiyar rayuwar da take yi ta 'ya'yan gata 'ya'yan manya. "Madina ce . Yakaka ta aiyana hakan a cikin ran ta kafin ta ɗan sake faɗaɗa fuskar ta da murmushi  cikin muryar ta mai sanyin ta ce "sannu da zuwa ki shigo mana . Da taƙaitatciyar Sallama ta shiga gidan kamar yadda fuskar ta ma ke ɗauke da taƙaitatcen murmushi. Bayan sun gaisa Yakaka ta kawo mata zoɓo mai sanyi da yake tashin ƙamshin kayan shai irin na mutan Ndjamena da take ƙamshin ya ɗau hankalin Madina ' Bayan sun ɗan taɓa hira lokacin da Madina take shan Zoɓon da daɗin sa yake ratsa ta "bata taɓa zaton irin wannan local juice ɗin yana da daɗi haka ba , ta aiyana hakan a cikin ranta. Da ta gama sha sai ta fuskanci Yakaka sosai ta sake gabatar da kan ta tare da yi mata godiya da amincewar da tayi ta bata damar tattaunawa da ita . Cikin jin daɗi Yakaka ta ce ita ma tana godiya daga haka shiru suka ɗan yi Yakaka tana ɗan satar kallon Madina wacce take shafa fuskar haɗaɗɗiyar ipad ɗin ta har dai ta kai inda take son zuwa ta ɗago kanta. Fuskar ta a sake tace "Amina zan so ki bani labarin yadda rayuwa ta kasance muku bayan da 'yan tawayen Boko-haram suka tarwatsa garin ku wanne irin tallafi kuka samu daga ƙungiyoyin bada agaji na ƙasa da ƙasa ? shin kun samu taimako ?  sannan a wane hali kuka kasance kafin taimako ya zo muku da kuma bayan taimakon ya riske ku.? Shiru Yakaka ta ɗan yi sannan ta mayar da ganin ta kan kyakkyawan agogon hannun Madina tamkar mai nazarin lokaci kafin ta buɗe bakin ta a hankali cikin sanyi muryar ta tace . "Mafarin Hargitsin Rayuwar mu ya fara ne ni da ƙanwata Falmata sanadin 'yan tawayen Boko haram da suka sa muka tsinci kan mu a matsayin 'yan gudun Hijira. Tammat Alhamdulillah . Alhamdulillahi.Alhamdulillah. Alhamdulillah Godiya ta tabbata Ga Allah Maɗaukakin Sarkin wanda ya bani ikon Farawa da gama litaffin nan da na ɗau tsawon watanni Ashirin da kwanaki shidda  ina rubutun sa tsakanin faɗi-tashi na rayuwar yau da kullum tare da juyin yanayi tsakanin zafi da sanyi da ruwa da iska babu shakka Allah shine abun godiya . Ina roƙon Allah ya yafe min daga abunda ya kasance kuskure na rubutu kasantuwa ta 'yar Adam mai cike da rauni da tarin laifuka ( Allah na tuba ) sannan abunda yake na lada Allah Ubangiji ya karɓa ya ɗora shi bisa mizanin kyawawan aiyukana ( Amin ) Sannan godiya ta marar yankewa ta tafi ne gare ku masoyan rubutu na da baki ba zai iya lissafa adadin ku ba Wattpidians wanda da kuka yi jimirin bibiyar rubutuna tsakanin lokaci mai tsawo da yake cike da tsaiko mai tarin yawa daga gareni , babu shakka ƙauna ce sila kaunar da ku ka nuna ita ta ban ƙwarin guiwar da har ta kai a yau muka kawo ƙarshen littafin tare da ku ,  hakika kalmar nagode tayi kaɗan wajen bayyana muku godiya ta sai dai nace Allah ya saka muku da alkhairi nima Ina ƙaunar ku saboda Allah . Godiya ta musamman ga ƙawa kuma 'yar uwa Fatima Salim aka Batul Mamma da ba domin ita da tarin gudumawa da alkhairin ta a bisa rubutun littafin nan ba da fa tafiyar bata miƙa ba nagode ƙwarai ƙwarai Sister Fatima Allah ya bar ƙauna. Yabo tare da Fatan Alherin ya tafi ne baki ɗaya ga Yayana kuma Malamina Sheikh Muktar Yaa Allah ya saka da alkhairi Yaa Mukhtar kalmar nagode tayi tsororo a tsakanin mu sai fatan Allah ya bar ƙauna . Sannan akwai tarin masoya masu daraja da littafin Mafari ya zama sanadin haɗuwar mu amma ƙaunar mu sai tayi ƙarƙon da ta zarce dalilin haɗuwar Littafi daga cikin su Akwai baki ɗayan jama'ar group ɗina na Mafari fans . Sannan  'Yar uwa kuma jagorata a harkar rubutu Sumayyah Abdulkhadir Takori , tare da ke da dukkanin jama'ar ki na Takorities ina godiya a gare ku tare da ƙaunar ku Allah ya bar zumunci . Jama'ar Batul Mamman na KDM ina godiya da yawan ƙaunar ku . Nafeesa Tafeeda tare da jama'ar ta na Maman Mama novels. Sister Amina Mafari fans Group admin Jameela aka Meela ,Raliya Garba Zulaihat rano , Zahra aka donutfairy ,Maryam Talba ,Auntie Aisha , Fadeela Khabeer godiyar ku ta musamman ce Allah ya bar Kauna. da da da da Masoya haƙiƙa kuna da yawan da ya wuce fa na ƙirga ku musamman dai da yake ai kun san ƙyuiya irin tawa ah to da ya muka sha a rubutun ma ? Lol. Masoya ga dama ta samu na tattaunawa akan duk wani abunda na rubuta daga farko har ƙarshen littafin Mafari . Ga masu min gyara ko domin gaba ina maraba . Ga masu ƙorafi domin gaba ina maraba . Ga masu neman ƙarin bayani/tambayoyi kowanne iri muddin b An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 111 of 111