Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
fi yi mata kyau , da hakan ba ƙaramin sanya ta takaici yake ba , sai dai tayi matuƙar koƙari wajen boye damuwar ta domin kar ta jefa yakaka cikin damuwa ita ma , duk wani abun da idon ƴakakar bai gani ba game da tozarcin da ake yi mata bata faɗa mata . Juyi yake ta yi akan katifar sa kaɗan-kaɗan yana jin wani sabon yanayi da ya fara ziyartar sa a tun lokacin da agogon wayar sa ya nuna masa sha biyun dare cib wanda a lokacin yana kan computer sa yana wani aiki sai dai wannan yanayi da ya fara ji yana taso masa ya sa shi rufe computer tare da wani irin bingirewa akan katifar sa tamkar dai an tunkuɗa shi ,' daran ranar ya zo dai-dai da cikar sa shekaru talatin cif a lissafin watanni turawa , Miƙewa yake so yayi ya fita ya ɗauro alwala , domin ya samu damar raya ƙarshen daren da ibada Kamar yadda yake aikata hakan jifa-jifa , sai dai ga mamakin sa ya kasa tashi , haka yake jin sa kamar an ɗaure shi ko kuma an aza masa wani abu mai nawi an danne shi , yana jin sa a wani yanayi mai cike da fargaba da tsoro zuciyar sa na wani irin bugu , yana jin sa ɗan mitsitsi kuma sakayau tamkar ba shi ba , shi ya san ba bacci yake ba ba kuma a farke yake ba sannan ba mafarki yake yi ba , yana jin sa kawai a wata duniya ta daban , duk yadda ya so yayi addu'a ya kasa , Haka ya shafe tsawon awannin karshen daren har zuwa lokacin da alarm ɗin da ya saita a wayar sa ya fara rangwaɗo sautin kiran sallah cikin zazzaƙar muryar balarabe , wanda cikin ikon Allah ya ji cimak wannan nawin da yake ji ya hana shi motsi , babu shi tamkar dai an sauka a kan sa , da gudu ya miƙe tsaye , jikin sa ya jiƙe sharaf da gumi , wannan tsoron da yake ji ya kau , sai dai har yanzu ɗan sauyin da yake ji a jikin sa yana nan , amma cikin ran sa sai ya dangan ta hakan da zamantowar sa cikakken ɗa namiji lafiyayye da ya kai minzalin da ya kamata ya buƙaci mace , duk da cewa shi youssouf ba manemin mata bane , bai taɓa zina ba , bai taɓa kusantar kowacce mace ba duk yadda ya kai ga cuɗanya da matan bariki matan banza , shi mutum ne mai tsantsani ta wannan fannin , Da sauri ya ɓude ruwan leda ya juye cikin ɗan bokatin da yake yin amfani da shi wurin yin wanka , ya cika shi taf da ruwa gami da sunkuta ya fito daga tantin sa zuwa ɗan bayan gidan da aka samar masa na wucin gadi wanda yake mallakin sa shi ɗaya ,' Ruwan na da sanyi sosai dan haka yayi tunanin zai taimaka wurin kawar masa da yanayin da yake ji a jikin sa , sai dai ga mamakin sa daga lokacin da ruwan ya sauka akan fatar jikin sa , ya ji tamkar an ƙara masa masifa ne domin gaba ɗaya tsikar jikin sa tashi tayi da ya sa dukkanin wasu jijiyoyi na jikin sai da suka taurara tare da fitowa baro-baro ,wani irin ƙullewa ya ji marar sa tayi , Ba shiri ya sanya tufafin sa gami da ɗauro alwala ya dawo cikin tantin sa , a daddafe ya idar da sallah saboda yadda marar sa take tamkewa tana sakewa , Kwanciya rub da ciki yayi bayan ya sanya ɗaya hannun sa ya riƙe marar sa ,tun da yake bai taɓa tsintar kansa cikin wani hali makamancin wannan ba, a hankali ya fara jin ciwon marar yana raguwa , wani ɗan daddaɗan bacci yana fisgar sa a sakamakon lafawa da ciwon yayi tare da daɗin ƴar sassayan iskar asuba da take shigowa ta tsakankanin rumfar tantin sa ,,' Bacci yake yi sosai da bai samu irin sa ba duk tsawon daren jiya , kafin sautin kiran wayar sa ya tashe shi , miƙa hannu yayi ya jawo wayar tare da miƙewa zaune saboda sautin kiran ya bayyana masa girma tare da muhimmancin mai kiran na sa Allô mama oui meilleur sava,? Daga chan ta amsa masa sava bien yaro na ya kwanan ka ? Da dama kou ? Ɗan jim yayi yana son faɗa mata yadda yake jin jikin sa saboda ya saba bayyana mata duk wata damuwar sa , sai dai kuma yanayin da yake jin yayi masa nawin faɗi a kan harshe musamman ma ga mahaifiyar sa * Daga bangaren ta kuwa zuciyar ta ce ta buga a sakamakon tunowa da mummunan mafarkin da tayi akan sa asubahin daren jiya da ya haddasa mata rashin nutsuwa , da ya sa tun asubah take neman layukan sa domin ta ji lafiyar sa kou ta samu kwanciyar rai amma rashin kyaun hanyoyin sadarwa ya sa sai yanzu da safe ta cimma nasarar samun sa a wayar ," Yaro na yi min magana mana hankalina ya tashi , Da sauri ya katse ta ," da dama umma ya ɗaura da tambayar ta ina merama ? Ta amsa masa da lafiya take , " Cigaba tayi da tambayar sa lamuran da suke gudana daga wurin sa , yana bata cikakkun amsoshin da suka gaza wurin gamsar da ita , zuciyar ta ta gaza nutsuwa duk lokacin da ta tuno da mafarkin da tayi sai ta ji bata son ta daina jin sa a waya , inda da hali so take ya kasance a idanun ta cikin waɗannan kwanakin dan tana jin kamar wani abu marar daɗi zai faru da su, duk da ta san sau dayawa mafarki bai zama gaskiya a mafi yawan lokuta daga shaiɗan yake , kuma ita bata da ikon kare kan ta ma bare wanin ta , ta san ko da agaban idanun ta yake , bata isa ta bashi kariya ba , illah addu'ar ta da ka iya yin tasiri akan ko ma menene , kuma duk nisan tazarar da ke tsakanin su ta san addu'ar zata isar masa , sanin da tayi youssouf ba sosai sosai yake tsayuwa yayi addu'a ba , shi dai mai tsayar da ibadun sa na farillah ne , bayan su sauran lokutan sa ƙorafi yake aiki ya cinye su ,wanda ita kuma hakan bai mata daɗi , ta san duk wata nasar da kariya daga wurin ubangiji ake samun su , dan haka a yanzu ma sai ta sake tunasasshe sa game da girman addu'a inda shi kuma ya tabbatar mata da yana yi ,' Sallama yake shirin yi mata , sai kalaman ta suka katse shi ,"Tu es notre lumière, notre joie, et pour toi nous donnerons le meilleur. En te souhaitant une vie abondante et en bonne santé.Joyeux anniversaire mon fils!,' Allah shi yi maka Albarka shi kare ka du inda kake yaro na , Murmushi ne ya suɓce masa halin da ya wayi gari cikin sa ya sa ya ma mance da yau take ranar zagayowar haihuwar sa kalaman ta na yanxu suka suka tunassashe sa,'amsa ya maida mata cikin tsantsar ƙaunar ta da yake ji cikin ran sa ," merci mama je t'aime," Daga bangaren ta ajiyar zuciya ta sauke bayan kammala wayar su , babu laifi ta ɗan samu nutsuwar zuciya , sai dai ta kuɗurce a ran ta zata ƙara ƙaimi wurin neman kariyar ubangiji akan ta da ƴaƴan ta , daga makiyan su da ta san suna kewaye da su , Juyowar da zata yi domin nufin ta shiga ɗaki ta fara sallar walha , idanun ta suka sauka akan hajiya uwa wacce take yi mata wani irin hargitsattsen murmushin da baza ta iya hasashen nufin sa ba , bata san lokacin da ta wanzu a wurin ba domin baya ta bawa kofar shigowa falon nata na ciki , Tsawon zaman su baza ta iya tuna rana ta karshe da hajiya saratu ta tako kafafun ta sashin ta ba , basa shiga sassan juna iyakacin su , su haɗu a bangaren mai martaba idan haɗuwar ta kama dole , ko kuwa wurin gaishe da hajiya uwa ,' Sannan tayi mamakin ganin ta ita ɗaya kai tsaye har cikin bigiren ta da sai an nemi iznin ta kafin a shigo ,' a sanin ta tare da tawagar ta hajiya saratun zata iso kuma karƙashin jagorancin shugabar bayi ta bangaren ta ,' Da kallo ta bita lokacin da take yi wa kan ta mazauni akan shimfiɗar alfarma da ta tashi daga kan ta yanzu ,' Hala uwargidan mai martaba sarauniya tayi mamakin wanzuwa ta gaba gare ta a yau ,? Shi yassa aka gaza wurin taryaa ta kamar yadda ya kamaace ni , Fuskar ta babu walwala ta ce ," Ban yi mamakin zouwar ki nan ba saratu , shin ƙaƙa za'ai mamakin wanzuwar macce a kowanne bangare cikin gidan amren ta ? Sannun ki da isowa ina miki lale marhaban ,' zama tayi daga ɗaya bangaren shimfiɗar ,' Suka yi kallon kallo na tsakiyar ido , kafin saratu ta ce ,' Yau yariman maraɗi ke cikkace shekarun sa talatin cikkin duniya , kou ba hakka ba ? Kallon mamaki hajiya safiyya ta bi ta da shi tana jin bugun zuciyar ta na ƙaruwa a hankali mafarkin ta na jiya ke dawo mata da fuskar saratu da ta gani cikin mafarkin ," janye idanun ta tayi daga kan ta ," Ƙaƙa kin ka sani ? Kafin ta rufe baki saratu ta amsa mata cikin wani yanayi mai tattare da ma'anoni ,ƙaƙa uwa zata kasa sanin ranar haihuwan ɗiyan ta ,? ??? Guntun murmushin fatar bakin ta safiyya tayi ,'haka ne kin yi gaskiya ,! Kiraye ma ni shi na taya shi murna shine abu da ya kawo ni gaba gare ki ," Tsam hajiya safiyya tayi tun haihuwar youssouf yau shekaru talatin saratu bata taɓa taya shi murnar zagowar ranar haihuwar sa ba sai yau ,? Sama ta ka zata ce zata taya shi murna ? Wallah banza bata kai zomo kasuwa ,! Ta bangaren biyamuradi youssouf kuwa tun yana cikin yin waya da umma yake jin kira yana shigowa wayar , Yana gama magana da umma ya bi bayan kiran da ya gani daga wata bakuwar lamba daga ƙasar su , sai dai har kiran ya tsinke ba'a ɗaga ba , yana shirin ajiye wayar ɗan guntun sako daga lambar ya shigo wayar sa ," Mon frère, je t'aime tellement. Que toutes les meilleures bénédictions te parviennent aujourd'hui et pour toujours. !Bon anniversaire.! Sakon taya murnar zagayowar haihuwa ne ,duba lambar ya sake yi yaga bai san ta ba dan haka kawai sai ya share , ya fara koƙarin kiran layin maimouna kamar yadda suka saba kullum safe Neman iznin shigowa aka yi ya bada izni aka shigo , abincin karyawar sa ne , aka shigo masa da shi, Da hannu yayi nuni da a ajiye masa abincin , Allo ma jolie fille Allô joyeux anniversaire mon amour , Ɗan jim yayi yana tunanin ta yaya maimouna ta san yau ranar zagayowar haihuwar sa ,? Shi dai ba shi ya sanar da ita ba , ' Princesse wa ya fadi miki wagga batou ? Cikin dariya ta bashi amsa a iska ta ji , murmushi yayi tare da share batun , suka cigaba da hirar su cikin nutsuwa tare da ƙaunar junan su , Wayar su ba mai yankewa da wuri ba ce ,musamman yau da daɗin soyayar ya juyo , dan haka riƙe da wayar ya fita ya wanko bakin sa ya dawo ya zauna cin abincin sa , Tashin farko ya kai abincin bakin sa ba tare da bismillah ba , saboda hirar maimouna ta ɗauke hankalin sa , haka har ya cinye abincin tas tana zuba masa zantukan soyayya , sai dai me ? yana gama ci ya ji marar sa ta murɗa , ba shiri suka yi sallama ,' ga mamakin sa sai kuma ya nemi ciwon ya rasa , Dan haka ya tashi yayi shirin sa tsaf cikin kayan sa na soji , ya fito Ya tarar da duk sauran da ke ƙarƙashin sa ma sun shirya domin a yau zasu ɗan yawata ne cikin daji ta sama ta hanyar jirgi mai saukar ungulu,'helicopter"domin su ga wuraren da ƴan tawayen boko haram suke da mafaka su tabbatar basu tsallaka iyaka sun shiga yankin ƙasar su ba ,' Suka hau jirgi ya ɗaga da su , sun ga wuraren da boko haram suka yi bigire na dindin-din cikin dazuzzuka tare da matan su da ƴaƴa suna rayuwar su cikin walwala tare da jin daɗi fiye ma da al'ummar cikin gari , abun da ya ɗaure kan youssouf kenan , ƙaƙa ƴan ta'adda irin wannan suka samu bigire cikin ƙasa kamar nigeria ? Shin wake ciyar da su ? Wake kai musu makamai ? Waye ke da alhakin basu magunguna zuwa kaƴan bukatun yau da kullum ?? Tabbas akwai lauje cikin naɗi ,' Sun samu kimanin awa guda a sama suna shawagi kafin suka sauko , kai tsaye ya wuce cikin tantin sa ya kwanta , gaba ɗaya yau ya gaza gane kan sa wani iri yake jin sa tamkar akwai wanda ke sarrafa shi a gefe , yana ji kamar su biyu suke gudanar da kome , amma kuma shi baya ganin kowa ," Haka ya yini babu walwala , sun yi waya sau biyu da umma wacce take sake jaddada masa ya riƙe addu"a tare da yawaita karatun kur'ani sai dai kuma abun da bata sani ba shine yau sam-sam ya gaza yin addu'a a yanzu haka da yake kwance ya gagara tashi yayi sallar azahar alhalin kuma la'asar har ta gota , karfe huɗu ma ta wuce , sannu sannu ya fara jin wannan yanayin da yake ji na safe yana sake tado masa , " wata irin mahaukaciyar sha'awa yake ji kamar zai fidda wani sashi na jikin sa ya ajiye koh ya huta ," shi kuwa yau wacce irin masifa ce ta same shi ? Ita ce tambayar da yake yiwa kan sa ," Sau biyu sojojin da ke da alhakin kula da lafiyar sa suna leƙowa su duba shi domin sun ji shirun yayi yawa , koh ɗan masallacin da suka tayar suke jam'i cikin sa bai zo yayi sallah tare da su ba a yau baki ɗaya , Ga mamakin su duk shigar su a zaune suke tadda shi , sannan kuma yana tabbatar musu da lafiyar sa lau babu abun da ke damun sa , dan haka sai suka kƴale shi , Zuwa magariba youssouf ya fara gagara iya riƙe kan sa domin tashin hankalin da yake jin kan sa a ciki ya wuce tunanin sa ya wuce yadda yake ji idan bai sha burkutu ba , wannan karon ji yake yana gab da mutuwa idan bai samu biyan bukatar sa ba , Ina zai samu mace a yanzu alhalin yana cikin jeji ? Yaya zai yi ? Dama a cikin gari yake sai ya fita ko'ina ne ya samo wacce zata taya shi ya kauda bala'in da yake ji ,' miƙewa yayi a dudduƙe ya ɗauki walet ɗin sa tare da ID card ɗin sa , har yayi nufin fita sai kuma ya fasa lokacin da ya kalli jikin sa ya ga yadda ya ke , wani kunya da takaici suka dirar masa , lokaci guda wani duhu ya mamaye masa kwakwalwa da ya sa nan take ya mance da wani batun kunya illah umarni da yaji ana bashi akan ya tafi , Yana daga cikin ɗakin ya danna kiran masu kula da shi ta wayar hannun sa , ba tare da jinkiri ba suka zo , yace su kawo masa mukullin mota zak ɗan fita , " jim suka yi ,toh sai dai basu da ikon musa umarnin sa dan haka suka kawo masa mukullin motar suna jiran su ji yayi musu umarnin su mishi rakiya wani wurin , sai suka ji ya sallame su , ficewa suka yi suka bar shi ," suka nufi bakin masallaci domin yin shirin sallar isha'i Suna tafiya shima ya fito ya buɗe motar ya faɗa ,' ya jaa ta da mugun gudu , ya hau titi tare da nufar cikin garin maiduguri a wannan daren ,' Gudun da yake ba na hankali bane , bai ko tsoron dare da yadda garin yake haɗe da hadari sai walƙiya ake yi, bai tsagaita ba sai da ya shigo da'irar birnin maiduguri lokacin sha ɗaya da rabi na ɗare har ta gota, cikin garin babu kowa kan titi sai sojoji ƴan uwan sa da suna hango motar ta sa mai ɗauke da fentin launin kakin soja suke buɗe hanyoyin da suka bi suka tottoshe saboda tsaro, shawagi ya fara yi da motar marar sa na cigaba da karta masa har yana ganin duhu-duhu , ya haɗa zufa sai tsuma yake yi, ina zashi ? Shi ba wani sanin kan garin yayi ba guri ɗaya zuwa biyu ya sani , daga barikin garin wurin abokin sa , sai kuma wurin sayar da burkutu , karya kan motar yayi ya lokacin da ya ji kamar an umarce shi da ya tafi zuwa wurin sayar da burkutun , a chan zai samu wacce zata iya kula da shi , Yana yin fakin ɗin motar ya fito ba tare da ya damu ya rufe murfin ba ya fara taku yana bin hanyar da zai sada shi da cikin gidan hannun sa ɗaya ya riƙe marar sa , da layii ya ƙaraso cikin rumfar , sai dai bakikkirin ya tadda wurin , babu kowa an watse kujerun gurin kansu a tattare suke, wani irin jiri ya ji yana kwasar sa , ya tabbata yau mutuwa zai yi , Tun shigowar sa yakaka wacce bata daɗe da kwanciya ba, bayan ta tattara cikin shagon ta kintsa kome, sai dai ta gagara bacci saboda tsinkewar da zuciyar ta ke yi wanda ta danganta hakan da tsoron tsawa da walkiyar da ake yi , Taji shigowar sa a tun takun sa na farko a cikin shagon , tsumu tayi cikin zanin rufuwar ta , tana sake jin bugun zuciyar ta na ƙaruwa da duk wani motsi da yake ,wanene cikin daren nan ? Koh wani ne yayi mantuwa ? kaƙƙarfan kamshin turaren sa shi ya ziyarci hancin ta , kamshin da ya ɗauki tsawon kwanaki a hancin ta kafin ta daina jin sa a wancen haɗuwar ta su ,' Kamshin na musamman ne dan haka sai ta zame abun rufuwar daga kan ta dan ta samu damar shaƙar ƙamshin da kyau cikin ran ta kuma tana ƙwaɗayin ganin fuskar sa , Da ɗan tazara a tsakanin su domin shi yana tsaye daga bakin kofar ta ciki yana fuskantar inda yakaka ke kwance sai dai bai kai ga fahimtar mutum ba ce saboda babu wadatar haske kuma baki ɗaya bai cikin hayyacin sa , Sosai ta buɗe fuskar ta tana ƙare masa kallo ta cikin ɗan hasken da yake shigowa ɗakin da taimakon hasken hadarin da ya gangamo cikin duhun daren , bata gani ainahin kamannin fuskar sa sai dai siffar jikin sa da take gani , gani tayi ya sunkuya yana riƙe da cikin sa Tsawa aka yi tare da walƙiya da ya haddasa yakaka tsorata har ta miƙe zaune , motsin ta ya sanya shi ɗago kan sa ,walƙiyar da aka sake yi ta hasko masa farar fuskar ta ta zuba masa ido tana kallon sa daga inda take zaune ,' Wani tsallen farin ciki zuciyar sa tayi, da sassarfa ya fara takawa yana nufar ta tamkar mayunwacin zakin da ya kwan uku ba abinci , Baya ta fara yi akan bencin tana matsawa , cikin in'ina tace ,' Babu ruwa ya ƙare ,mun ruga mun tashi an gama aiki sai gobe da rana ,' Kalaman ta sun zo dai-dai da ƙarasowar sa gaban ta , baiyi wata wata ba ya miƙa hannu ya ɗago ta daga kan bencin ta hanyar ɗago kafaɗun ta ya tsaida ta akan kafafun ta , ba kuma tare da ya ce da ita ƙala ba ya juya tare da jaan hannun ta da ya riƙe nufin sa ta biyo shi ,' Waiwayowa yayi jin ta turje tana ƙokarin zame hannun ta da ya riƙe tamau , Cikin wata irin dusasshiyar murya da take fitowa daga ƙarƙashin maƙoshin sa yace ," Ki taimaka min kar na mutu ko nawa ne zan biya ki ki taimake ni ," Daga haka ya juya yana jaan hannun ta , bata yi turjiya ba ta fara bin sa kafafun ta ko takalma babu ," kalmar taimako da ya ambata tare da wani abu da take ji yana fisgar ta a game da shi ya sa ta bi shi ,' Sun zo tsakiyar filin gidan aka fara yayyafi ,' yakaka ta sake tsayawa saboda gargaɗin da zuciyar ta ke yi mata akan yunƙurin bin mutumin da bata sani ba cikin dare zuwa wurin da bata kai ga sani ba wai shin ina hankalin ta yake ne ?? Juyowa yayi aka saki tsawa da walkiya tare da ƙaruwar ƙarfin ruwan sama , haɗa ido suka yi ta hasken walkiyar suka kalli juna na wasu dakikai ba tare da kowannen su ya samu damar magana ba ," Cikin idanun sa ta hango ruɗanin da yake ciki , tare da wani abu da ya taɓa zuciyar ta da bata kai ga fahimtar yanayin sa ba , sai dai koma menene yayi tasiri matuƙa wurin raunana mata zuciya ta yadda ta ji kowanne irin taimako ne zata iya yi masa , zata mishi kome yake so , tana nufin kome , A bangaren biyamuradi youssouf kuwa shi ma kallon cikin idanun ta ya taɓa shi , ya hango rauni tare da zallar ƙuruciyar da ke tattare da ita ,sai dai sun gaza tasiri agare shi domin daga lokacin da ya riƙo hannun ta ya fara jin wani irin nutsuwa tare da ɗaukewar ciwon da yake ji ,har da wani danshi danshi yake ji a ƙasan ran sa wanda ya tabbatar masa ita zata iya fidda shi halin da ya ɗauki tsawo awanni ashirin da huɗu cikin sa , yana jin zai iya biyan ta ko nawa ne domin ta yadda da shi , Ganin bata ce kome ba ya sa shi ya cigaba da tafiya riƙe da hannun ta sai dai wannan karon tare suke jefa kafafun su a jere tamkar sabbin masoya cikin samun amincewar yakaka da ta hakiƙance zata taimaka masa , " Bai saki hannun ta ba sai da ya dangana ta da cikin motar sa ba tare da fargaban kome ba yakaka ta shiga ta zauna tana shaƙar ƙamshin turaren sa da ke da matuƙar tasiri agare ta ," Da ƙarfi ya fisga motar wanda yayi dai-dai da fara saukar ruwan sama da matuƙar ƙarfi , wani ƙaramin Guest house ya nufa wanda yake ganin sa akan hanyar shigowa gari , cikin su babu wanda yake ce da ɗan uwan sa ƙala ba har suka isa , bai wani sha wahala ba wurinnsamar musu da ɗaki zamantowar sa jami'in tsaro , Riƙe da hannun yakaka wacce ta zamto tamkar rakumi da akala ya danna kai cikin ɗakin ,' Daga lokacin da suka sanya ƙafa cikin ɗakin kome ya fara kasancewa nan ne mafarin hargitsin rayuwar su , sun gudanar da kome cikin amincewa tare da tallafin junan su , yakaka bata hana biyamuradi kan ta ba wanda ita da kan ta baza ta iya faɗin dalilin ta na sadauƙar masa da mutuncin ta ba ita dai ta san koma wanene wannan mutumin da ya kasance mutum na farko da ya fara kasancewa da ita a wani bigire kuma cikin wani yanayi irin wannan ,akwai wani al'amari mai girma a tare da shi .' A bangaren biyamuradi kuwa tsintar kan sa yayi a wata duniya mai nisa wacce take tare da wani irin daɗi da sanya nishaɗi da bai taɓa jin makamancin sa ba , ji yayi ko da dakika guda baya fatan wani abu ya gifta da zai katse masa jin daɗin sa , Yana jin zai iya mallakawa yarinyar nan kome ta buƙata

Chapter 21 of 111