Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
aka ɗaura auren zainab da angon ta colonel Tahir Ma'aji , inda aka zarce da walima wanda mahaifin Amarya ya shirya ƙarƙashin jagoranci tare da kulawar Hamza , A daddafe Biyamuradi Youssouf ya tsaya aka ɗaura auren tare da shi , saboda hankalin sa da yake a tashe da son tafiya gidan madam saly dan jin ko an kai ga samun ta ,? "  A gurguje yayi wa ango gaisuwar taya murna , sannan ya jaa Tafeeda gefe , Ɗan ouwa ni zani koma bakin aiki ,ils ne me donnent que quarante huit heures , zuwa lokacin da nake issa bakin aiki , awanni sun kai ga cika ," Bai damu da kallon tuhumar da Tafeeda ke bin sa da shi ba , ya miƙa masa hannu suka yi musabaha , Idan ka cimma gidaa ka kiraye ni ɗan  ouwa ,' Allah shi kiyaye hanya ,saduwar Alheri Zame hannun sa daga cikin na Tafeeda yayi tare da juyawa ya fara taku domin barin wurin ," A takaice Tafeeda yace da shi ," me zan ce ga hajiya umma tare da mai martaba idan sun ka tambayeni halin da na riske ka ciki ??   Juyowa yayi da wani guntun murmushi a fuskar ka kace da su ,"    Yarima na a halin lafiya a bigire mai tsaro ,! Sannan ina miƙa gaisuwa ta a gare su tare da fatan Alheri ! Gyaɗa kai Tafeeda yayi yana mai juyawa ya shige taron jama'a cikin ran sa ya ƙudurce dawowa ya cimma youssouf su fuskanci matsalar sa tare , yanzu ma domin yana cikin ujila ne shi da kan sa awanni arba'in da takwas ɗin aka ba shi , dan haka su dukkanin su basu da isasshen lokaci a halin yanzu  ! Motar sa ya jaa da gudun gaske ya ɗauki gwadaben da zai sada shi da unguwar madam saly , Bai ko rufe motar ba ya taka ya shiga gidan , " a ƙufule ," sai dai tun daga bakin rumfar ya fara fahimtar sauyin da yake wurin domin dai babu kowa a cikin rumfar hatta kujerun cikin rumfar a tattare suke a gefe , da alamu yau ba'a shirin yin aiki ," Kai tsaye ya sa kan sa cikin gidan hanyar da ya bi jiya ita yau ya bi ya zo har bakin ƙofar ɗakin madam saly , har lau bai ga giftawa kowa ba tamkar gidan ba kowa ,"    Garam ! Ya ga ƙofar ɗakin madam saly garƙame da ƙwaɗo har biyu ƙarami da wani fankacece iri na rufe ƙofar babban gareji ,"   Duka ya kaiwa ƙofar ɗakin da ƙafar sa da matuƙar ƙarfi wanda ba domin ƙofar ta ƙarfe bace da ta karye,   Ya ɗaga murya yana cewa   Ina masu gidan ??   Ina masu gidan ?? Ko giftawar kadangare bai gani ba , bai buƙatar a sanar da shi , ya fahimci sun gudu ne ," nan take wani malolon bakin ciki ya maƙale masa a maƙoshi ," Murza fatar goshin sa yake yana kokarin saita kan sa lokacin da yake kan hanyar barin gidan cikin ran sa yana aiyana zai dawo kuma haɗuwar su ta gaba baza ta taɓa yiwa madam saly kai dama duk mutanen gidan kyau ba ,     Cikin takun da bai ko duba inda yake jefa kafafun sa ya bar gidan yana jin yadda zuciyar sa ke azalzalar sa da ya ɗan kora ruwa ko zai samu sa'ida azabar damuwa da yake ciki ta isa haka , amma tunowa da tafiyar ratsa daji da take gaban sa ya sa shi yakice tunanin shan barasa a wannan lokacin , ya fisgi motar da matsanancin haushin rashin cikar buri ya bar wajen bai ko kula da taron ƴan cha-chan da suke baje akan wata babbar tabarma daga ƙarƙashin bishiya a gefe suna faman yin karta tare da dara , da ya watsawa ruwan kwatami daga jikin su har zuwa fuskokin su ba ,     Wucewar sa kenan ɗan liti ya fito daga banɗaki inda yayi maɓoya , bayan ya tabbatarwa da su madam saly su watse kaf su bar shi shi kaɗai a gidan zai jira zuwan kurtun ɗan sandan , ayi wacce za'ayi ɓera ya zubda garin kyanwa! Banten uba ! Kuturi ai yau da na yadda ya ganni sai ɗan buzu na , ai wallahi da sai dai Baba malmo ya auro wata safara'un ta haifi wani ɗan litin ba dai ni ba ,! Chab kai ka ga mutum kamar safurarren doki ??? Yana tafiya haka - haka - haka ,"kamar jarumin sadauki a fagen daga ??    Ko a mafarki na gan ka ai nayi sadaka !      Ahayyeee saly fara ta zo ta lale min kuɗin gadin gida da nayi mata ta biya ni ,," kurtun ɗan sanda kuwa cewa zanyi na gama da shi ," ah to meye ?? Ko banza ai na shaƙi tsoro da bugun zuci, "  Rikicin duniya kuwa ai da me rai ake yin sa ehe ,! ****   Bayan kammala bikin zainab da sati guda doctor Hamza ya sanya yakaka a makarantar islamiyya da Rahima take zuwa , amma ta ta bangaren matan aure take zuwa kullum da safe karfe 8am.zuwa 12pm falmata kuma aka cigaba da koyar da ita arabi da bokon a gida ,' A makarantar yakaka ta san sabon sunan da doctor hamza ya laƙaba mata a matsayin sunan ta na yanka ,watau AMINA MUSTAPHA DILMARI , Sosai take mayar da hankalin ta kan karatun ta kamar yadda doctor hamza kullum yake gargaɗin su , a gefe guda kuma cikin ta na cigaba da bunƙasa ta yadda har girman sa ya so yin yawa dan haka a awun da ta je cikin satin nan aka hana ta shan su madara da sauran cimakar da take sa yaro ya girma sosai a cikin mamar sa ,"    Da wata safiya tayi shirin makaranta ta fito zata tafi sai ga motar samy baby ta tsaya a gaban ta , gaban kaɗan da gidan su doctor Hamza     Nan ta nemi ta shigo suyi wata maganar da take tafe da ita , tayi murna ma da suka haɗu anan waje ," ba musu yakaka ta shiga motar tana murna sake ganin samy baɓy a dai-dai wannan lokacin da ran ta yake cike taf da son sani game da youssouf    Nan cikin motar samy baby ta fara yiwa yakaka huɗubar da ta zamto kuskure na biyu da yakaka zata afkawa a rayuwar ta , A sanyaye ta fito daga motar bayan ƙarasowar su gaban makarantar , ta luluƙa a duniyar tunani , ta yadda har bata san lokacin da samy baby ta jaa motar ta tayi tafiyar ta ba ,"   Idan aka zo ga batun ƙaunar ta ga youssouf kome kunce mata yake , tana son shi sosai , yana birge ta fiye da kowanne mahalukin da ta taɓa cin karo da shi a rayuwar ta , amma anya ? Anya girman son da take masa ya kai mizanin da zata dai-daita shi da falmata ? Ƙanwar ta jinin ta ? Abar batun cikin jikin ta shi wani sabon abu ne da yanzu yake kan hanyar shigowar sa cikin rayuwar ta , duk da cewa akwai ƙauna irin ta ɗa da uwa a tsakanin ta da abinda yake cikin ta wanda tasirin son da take yiwa shi youssouf ɗin yake mamayar abun da yake cikin cikin nata tare da ninka mata ƙaunar son gudan jinin sa da ke tare da ita , To amma falmata ba ?? Falmata haske ce kuma sanyi ce sannan cikamakin farin ciki ce cikin rayuwar ta , tun asali akwai shaƙuwa da so mai tsanani a tsakanin su fiye da wanda aka saba sani tsakanin saƙo-da-saƙo na haihuwa , ya zarce ƙauna irin ta tsakanin ƴa da ƙanwa sai dai a kwatanta shi chakuɗuwar jini da soyayya irin ta tsakanin tagwaye wanda ƙarya ɗan adam ya zare wannan tsananin wannan son da shaƙuwar da ya samo asali tun daga ranar faruwar halitta a cikin mahaifiya , sai dai fa ikon rabbi ," Zata iya kome domin ganin ta samarwa da falmata farin ciki a kowanne bigire na rayuwa fatan ta a koyaushe ta hango farin ciki bisa fuskar miskiniyar ƙanwar ta , sai dai wannan lamarin da yau anty samy ta zo mata da shi , yarda da shi tare da yin aiki da shi tamkar ta ɗau takobi ne ta gille duk wani farin cikin da Falmata zata iya shinshinowa a rayuwar ta , tamkar ta kassara ruhi da gangar jikin falmata ne , wacece FALMATA idan babu YAKAKA ??? Ba ta san ta kawo karshen makarantar ba sai da ta ji ta kaiwa bango karo , Zamewa tayi ta zauna dirshan a cikin ƙasa gami da fashewa da kuka , a sarari take furta kalmar,"  bazan iya ba , bazan iya ba, ! **** Cikin satittikan da suka biyo baya samy baby ta cigaba da zirya tsakanin makarantar su yakaka inda take killace ta tana cigaba da cusa mata ra'ayin da take ganin zai iya tsallakar da yakaka daga faɗawa hannun sofi , ta hanyar yin amfani da kalaman yaudara da wayo ta cikin amfani da makahon son da yakaka take yiwa Youssouf , har ta kai ga nasarar samun haɗin kan yakakan ta wani ɓangare ba tare da ita yakakar ta san haƙiƙanin meke cikin ran samy baby ba, iyaka son youssouf tare da ƙwaɗayin son samun sa a matsayin miji ya sa ta fara amincewa da shawarar samy baby , ɓangaren zuciyar ta dake gargaɗin ta tare da tuno mata da so tare da tausayin dake tsakanin ta da falmata ya fara samun rauni , ! Soyayya tayi ƙarfi ta yadda ta fara rufe mata idanu ! Sannu sannu , yau da gobe zuciyar yakaka tare da taimakon huɗubar samy baby da ta shaiɗan , ta ƙeƙashe da son ganin cikar burin ta na mallakar youssouf a matsayin mijin ta , kamar yadda samy baby ta wanzu tana ƙara ƙwaɗaitar da ita , bata ko duban hidindumu tare da gatan da doctor hamza yake gwada masu ita da ƴar uwar ta musamman ma ita da komen ta yake mai matuƙar muhimmanci agare sa , ko sau ɗaya bai taɓa burge ta ba , Koyaushe ɗaukar sa take a matsayin me kirki me TAIMAKON SU, hankalin ta a kullum daɗa tafiya yake ga youssouf wanda a yanzu hoton sa ya zama abun ɗebe kewar ta kullum dare har ma ta kan ɗan zanta da hoton idan dare yayi nisa wutar so kuma ta ruru iya ruruwa , sai ta fara sakin sambatun so , Sai dai tana ƙoƙari wurin boyewa musamman ga doctor hamza , wanda watarana a cikin ranaku ya kamata tana kici-kicin ɗaura agogon da youssouf ɗin ya bar mata a tsintsiyar hannun ta , ta shagala cikin bege sai murmusawa take har haƙoran ta na bayyana , sakamakon yadda idan ta ɗaura agogon yake zamewa daga hannun ta idan ta sauke hannun ,  sai tayi maza ta taro agogon ta chafe shi ta sake mayarwa cikin hannun ta , tana lailaya shi kamar tana ganin fuskar youssouf ɗin a jiki , Ya ɗauki lokaci dogare a bakin kofar yana kallon ta cikin shauƙin ƙauna , sosai tayi kyau a idanun sa tana sanye da atamfa buɗaɗɗiyar riga da zane, tayi ƴar madaidaiciyar ƙiba ta buɗu kaɗan , sai ɗaukar ido take Hankalin sa ne ya koma kan agogon da take wasa da shi a hannun ta , yana iya hango girma tare da ƙƴallin agogon daga inda yake tsaye ," ya shaida agogon maza ne ,"  Takawa yayi ya ƙarasa cikin falon bata lura da zuwan sa ba , sai gani tayi hannun sa ya riga ɗayan hannun ta chafe agogon lokacin da yake silmiyowa daga tsintsiyar hannun ta ," Ɗaga agogon yayi yana ƙare masa kallo daga gani ba tambaya agogon mai matuƙar tsada ne , da samun irin sa sai a hannun goggagun attajirai ," Cikin taushin murya da nutsuwar da take mahaɗin cikar kamalar halittar sa yace ,"     Agogon waye ? Shiru tayi tare da sunkui da kai, tun usul ƙarya bata cikin halayyar su , basu ma san yadda ake yin ta ba idan ba yanzu da duniya take ƙoƙarin koya musu ba ,"   Ganin sa ya janye daga kan agogon ya maida kan ta , tare da ɗan ƙara sautin muryar sa ,    Wannan agogon na waye ne ?? A firgice ta ɗago kan ta jin kamar ya mata tsawa , matuƙa take shakkar sa tare da gwada yi masa biyayyah Ba-ba-baba Agogon - agogon Baba ne !   Ta harhaɗo kalaman da suka fito a baibai ,"  idanun ta na yin ƙwalƙwal . Agogon Baba ?   Hamza da Falmata suka haɗa baki wurin tambayar ta ! wacce take ƙarasowa wajen da lalube daga cikin ɗakin saboda jin tashin muryar doctor hamza domin ta gaishe shi , Agogon Baba ? Yakaka ina agogon Baban mu ? Daman Baa yana da agogo  ,       Falmata ta furta hakan cikin tsananin murna kasantuwar ta mai matuƙar ƙwalafacin iyayen ta , hakan ya sa ta ma manta da abun da ta fito yi ,"gaishe da doctor hamza ," ta himmantu wurin son a bata agogon ta riƙe , doctor hamza ne ya ɗaura mata agogon bisa hannun ta , bai sake cewa kome ba ya juya yana barin falon zuciyar sa cike da wasi-wasi akan kalaman da yakaka ta furta na dangana wannan tsadadden agogon ga mallakar mahaifin su , A sanyaye falmata ta ɗago kai daga barin shafa agogon da take yi ta saita idanun ta a inda take zaton yakaka na zaune ,     Yakaka kika ce wannan agogon Baa ??     Da ido yakaka ta kafe ta kamar tana son ta gyara mata sokuwar ƙaryar da tayi ," wanda ta hango rashin yarda da zancen nata ƙarara a idanun doctor hamza    Miƙa hannu tayi ta zare agogon daga hannun falmata ,    Falmata muje ɗaki na kwanta ki ɗan danna min kafafuna ciwo suke min ,   Da sauri ta amsa da   toh sannu yakaka Tun daga ranar yakaka take koƙari wurin boyewa kowa duk wani abinda ya shafi soyayyar da take yiwa youssouf ciki kuwa har da Falmata , Da samy baby kaɗai take hirar sambatun soyayyar youssouf , wacce take daɗa ƙaimi wurin shiryawa yakaka gadar zare , tare da bugun cikin ta a koyaushe tana jin tsakanin ta da doctor hamza , irin kulawar tare da hidimar da yake yiwa yakaka yake sake bata tabbacin zaton ta gaskiya ne , doctor hamza son yakaka yake , soyayyar kuma mai tsanani ta aure , wanda a koyaushe idan ta tuno sofi da irin mahaukacin son da take yi masa da irin mummunan alwashin da ta sha a kan sa , sai taji abinda take kokarin yi da nufin raba tsakanin sa da yakaka dai-dai ne, a ganin ta taimakon yakakar zata yi , har ma tana danganta yunƙurin ta a matsayin CETON RAI ,"  Lokacin da yakaka ta shiga watan haihuwar ta hamza ke sanar da ita daga wannan satin zata daina zuwa makaranta , baza ta dunga zuwa ko'ina ba daga awu , sai dai ta fita motsa jiki da dare , Da farko ta shiga damuwa , da hukuncin da ya yanke na hana ta zuwa makaranta ganin cewa a makarantar take samun damar haɗuwa da samy baby duk lokacin da samy baby ta so ," Amma lokacin da ta sanar da samy baby sai ta ga bata wani damu ba , suka cigaba da hirar su da fiye da rabin hirar maimaici ne tare da tisawa akan yadda tsarin samy baby yake da yadda kome zai kasance , har zuwa gamuwar ta da muradin zuciyar ta kamar koyaushe yakaka ke ƙarasa hirar da sambatun yadda haɗuwar tasu zata kasance da youssouf da ɗokin zuwan ranar , Bayan gama hirar su , sai samy baby ta ciro ƙaramar wayar ta , ta kamo hannun yakaka ta danƙa mata ,"     Zamu cigaba da tattaunawa akan waya yaks , saboda kin ga bana son mutanen gidan su san da alaƙar mu domin kar a zarge ni har a bibiye ni bayan kammaluwar kome , ki tabbatar babu kowa a wurin a duk lokacin da zamu yi waya , ki dunga min flashing idan kina son magana da ni , sannan kuma daga mun gama magana ki dunga kashe wayar , kar ki bari kowa ya san da wayar , Idan chaji ya kusa ƙarewa ki sanar da ni , ni zan san hanyar da zan yi na karɓi wayar nayi mata chaji ," Abu na ƙarshe shine kar ki manta da tsarin mu ko cikin dare kika ji ciwon haihuwa na zama mutum na farko da zaki fara sanarwa kafin kowa , kin san dai shirin mu zai fara ne daga haihuwar ki ,  ai kin gane ko ?   Naji anty samy kuma bazan manta duk tsarin da kika shirya min ba , nagode sosai da taimakon da kike min a kullum tunda muka haɗu , Allah ya saka miki da Alheri ,! Murmushi mai wuyar fassara samy baby tayi,     Ameen yaks , Tun bayan da doctor hamza ya sawa yakaka dokar hana fita unguwa , ya zama kullum da dare tare suke fita ita da Rahima , da misalin karfe 8pm , su ɗan yi tattaki su zagaya unguwar zuwa 9pm sai su dawo gida , Ƙwarai yakaka take jin daɗin fitar tasu saboda yadda a kwanakin take jin nawin cikin kafafun ta duk sun ɗan kumbura , ga kwonkwason yana mata tsuku idan ta daɗe ," Tare suka fito da Rahima daga sashin su , Rahimar tana ta mitar Yakaka ta katse mata kallon TV da take ta dame ta akan tazo su fita ta raka ta motsa jiki ,"      Yakaka ni fa yau baza mu yi wani nisa ba , zamu dawo kin ga dai garin da sanyi ma , ga duk hazo ya rufe sama , ni ba dan kin nace ba ma wallahi yau baza mu fita motsa jikin nan ba duk ƙura ta bi ta shigewa mutum hanci ta sa mura ,"   Gyara zaman burmemen hijabin ta yakaka tayi tana murmushin jin daɗi domin tun basu yi nisa ba ma ta fara jin kafafun ta na warwarewa ,"      Ni kuwa Rahima daɗin yanayin ma nake ji , kiyi haƙuri kin san ba laifi na bane yaya dakta ne ya ce kar na dunga fashin fita motsa jikin ,"    Doctor hamza ne ya shigo ta ƙaramar ƙofar gidan jikin sa sanye da ƙananan kaya ya rufe bakin sa da hancin sa da abun tare ƙura ,"Mask ," Idon sa ya sauke a ƙan su lokacin da suke ƙarasowa ,"      Gaishe shi suka yi ya amsa musu ya ɗora da     Za'a je motsa jiki ko ? Da sauri Rahima ta tari numfashin sa , big bro daman an bar zuwa motsa jikin nan yau sai gobe , ji fa garin duk hazo wallah ,"        Rahima dan Allah kiyi haƙuri muje yakaka ta ce , tana marairaicewa ,"       Cuno baki Rahimar tayi taƙi cewa kome , "      Murmushi hamza yayi ,    Koma ciki abin ki Rahima yau an ɗaga miki ƙafa sai gobe ,      Da sauri Rahimar tayi juya tana dariyar murna , dan kar yace ta dawo ma har da ɗan gudun ta , ta ƙarasa shigewa sashin su , "    Ganin sa ya mayar kan Yakaka , wacce ta sunkui da kai tana wasa da hannun ta ,"       Noori   Ya ƙira ta    Na'am   Tace tana ɗago kan ta ta dube shi kafin ta sake sunkui da kan ," ba wani sanin ma'anar sunan tayi ba , ita dai tasan yakan ƙira ta da kalmar a irin lokuta haka da suke su biyu kaɗai !          Tunanin ta ya katse lokacin da ta ji yace mata ,   Bismillah mu tafi ,' ya buɗe mata ƴar ƙaramar ƙofar   Tare da shi zan tafi ? Ta tambayi kan ta lokacin da take sanya ƙafafun ta da ta cusa wasu ƴan takalman roba na mata ," kumburin da ƙafar ta ta tayi ya sa takalman suka ɗan kama kafar ,"     Ta ina-da-ina kuke bi idan kuka fito ?       Ta nan muke bi tace da shi da ƴar siririyar murya ,"     To yau ba nan zamu bi ba , zo mu bi ta nan , ya ce mata haka yana nuna mata hanyar da tayi baya wacce take da rangwamen mutane da hayaniya ,"    Ba musu ta bishi ,   Suka fara tafiya sannu ,sannu ,  rabin hankalin sa baki ɗaya na ga inda take sanya kafafun ta , "     Ɗan takaitatcen shiru ne ya biyo bayan fara tafiyar ta su ,"    Kafin Hamza ya lalubo hirar da yake ganin zata fi armashi ga yakaka ,"     Noori , ya ƙira ta ,"     Wanne suna kike tunanin zamu sawa baby ?      Yana hango lallausan murmushin da ya bayyana a fuskar ta da taimakon hasken fitulun bakin hanya, kafin ta ɗan sunkui da kan ta ,"     Nima ban sani ba yaya dakta , kawai duk wanda ka zaɓar mata ,"     Ɗan murmushi yayi kafin yace ai uwa ita ce mafi soyuwa ta zaɓarwa ƴaƴan ta suna ,     Ni mata ta duk ita zata dunga zaɓarwa yaran mu suna , dan haka mu fara da wannan babyn , ki tuno suna mai kyau da asali a addini da za'a sa mata , "   Kasaƙe tayi ita a dole tana son tuno da sunan ,!      Mama ? tace masa da sigar tambaya ,"     Mama!  shima ya maimaita yana kallon kwarar idanun ta ,"     Eh tace da shi tana sunkui da kai ," Toh kin samar mata da laƙabi ," ya furta hakan yana mai yi mata murmushin da ke bayyana sautin sa ,     Ita ma ƴar dariya tayi , tana jin yadda farin ciki ke mamaye mata rai , kafi ta ɗan cije baki a hankali tace na gaji ,     Yawata idanun sa yayi , nan ya hsngo wani ɗan tudun da aka yi da siminti a bakin hanya , domin zama ,      Muje ki zauna a chan yace da ita , Ƙarasawa suka yi ta zauna shi kuma ya tsaya daga gefe ," , ƙura ta taso tare da ƙasa ba shiri suka kare fuskokin su ,"     Sai bayan da ta lafa ya mayar kallon sa kan ta ," mask ɗin fuskar sa ya sanya hannu ya ƙunce , " a hankali ya miƙa mata ,"           Karɓi noori , ki saka ƙura tayi yawa ," kar ya cutar da ke ,"       Da hannu biyu ta karɓa , ta fara juya mask ɗin a hannu bata san yadda ake sawa ba ,"        Fahimtar hakan da yayi , yasa yace mata yana mai kwatantawa da hannun sa,     Haka zaki sa ,   Sake juyawa shi tayi ta fara ƙoƙarin ɗaura shi ba dai-dai ba ,"    Bani ki ga   Ya zare mask ɗin daga hannun ta ,  Zagayawa yayi ta bayan ta ya daidaita mask ɗin a fuskar ta tare da ɗaura mata shi , dai-dai kan hamcin ta zuwa haɓar ta ,"     Ya dawo ya tsaya , yana kallon fuskar ta , suna haɗa ido ta sunkui da kan ta tana jin wani irin yanayi marar ƙarfi chan a gefen ran ta ,"   A hankali ta motsa laɓɓan ta   Nagode ,! Bai amsa mata ba illa zura hannun sa da yayi a aljihun sa tare da kai kallon sa sama yana ganin yadda garin yayi jaa hazo ya lulluɓe sararin samaniya , Wani irin so da shauƙi mai ƙarfi yana fusgar sa bai ƙi ba suyi ta kasancewa

Chapter 36 of 111