kanki...? Kema kinsan bazan tab’a yin haka ba... Idan bakiso naci gaba da kiranki on and on, then always keep me updated... I need to know everything that’s going on with you there...!”
D’an rausayar da idanu tai kana tace “Alright fine... Kana so ka sani..?” Lokaci guda Ta soma sanar dashi abubuwan da suka faru tiryan tiryan a d’an shigowarta gidan da tai....Saidai tin bata gama bashi labarin abubuwan data gani ba ya mik’e daga zaunen da yake yana mai furta “No Muhibbah, you’re not pushing through with your plans... You know what..? This is over... Park your things gobe gobe zanzo na d’aukeki mu dawo gida... Bazan iya barinki tsakankanin wad’annan Animals d’in kici gaba da rayuwa ba... Who knows, wa yasan abinda zasu miki...?!” Ya k’arashe cikin tsananin k’unan rai...
A d’an tsawace itama ta soma fad’in “Do you really think I like it here... Kana tunanin Ina jin dad’in zama cikin wad’annan azzaluman ne...? Do you think it’s easy for me facing them bayan dik abinda sukai min...? This isn’t easy for me.... Each time idan naga fuskokinsu sai na tuna wancan lokacin... So please idan bazaka ci gaba da k’arfafa min gwiwa ba ka daina sarar min da gwiwa...!!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya irinta mai kuka....
Cikin sanyin jiki Ansar ke furta “I’m sorry... Ba nufi na ba kenan Muhibbah.... Na damu dake ne Muhibbah, you know how much I love you right...? So please kar kiga laifina dan na nuna damuwata, Kawai gangan jikina ne a nan but gaba d’aya zuciyata da ruhina suna taredake Muhibbah.... I’m sorry I made you feel that way...!” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya..
Tsaye ta mik’e had’ida dafe kanta kad’an tana mai furta “Ansar shiyasa banso sanar dakai ba, ya kamata ka gane da da yanzu ba d’aya bane... Babban kuskuren da sukai shine da suka barni da rai... Allah bazai kuma basu daman cutar dani ba... Kuma yanzu da na tabbata akwai abubuwa da dama da suke rufe cikin Masarautar bazan tafi ba Ansar har sai nakai mak’uran bincikena da yardar Allah... Kawai kaci gaba da min addu’a kaji...!”
Shiru yai tamkar mai nazari kana ya fuzar da fuci a hankali “Shikenan... Amma ki sani ba wai dan inaso ba na k’yaleki cikin Masarautar nan sai don Babu yanda na iya ne.... I love you so much Muhibbah... And ina kewarki sosai..!” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya..
Jiki a matuk’ar sanyaye tace dashi “Ka gaisar min da Mummy, nima ina kewarku sosai... Sai mun sake magana...!”
Sukai sallama su duka biyun jikkunansu matuk’ar sanyaye...
Mik’ewa tai ta soma zarya a d’akin tana tunani abinyi gaba... Ta d’auko sark’ar tana ci gaba da juyawa... Tabbas ya kamata Washe gari juma’a takai ziyara k’ofar Yarima Yazeed.... Da wannan tunanin ta bud’e drawer ta linke sark’ar cikin k’aramar farar k’yalle kana ta fad’a bathroom ta d’auro alwala...
**
Yauma da salati saman bakinsa ya bud’e idanu daga baccin da yake mai cikeda mafarkai marassa dad’i... Tabbas abin ya soma damunsa sosai, hardai zai kwanta toh sai yayi marfkin wani abin k’i.... Yau mafarkin nasa gameda Ja’afar ne... Ja’afar bawa d’ah ga sarkin dawakai na cikin masarautarsu...
Kaman yanda ya gani cikin baccin nasa, Shida Ja’afar suna tafe cikin Bargan dawakan mahaifinsa su duka biyu Sun saka kaya irinta mulki da sarauta iri guda babu abinda ya raba, kwatsam abokan gaba suka far masu... A tare suka zaro takubbansu domin yak’an abokan gaban nan.... Cikin abokan gaban d’aya yayo kan Mahmood da takwabi saidai tuni Ja’afar ya tare masa saran kana ya mik’a masa hannu ya d’agosa tsaye, su biyu d’in hannayensu rik’e cikin na juna.... Yak’i sosai suke da abokan gaban nan har saida Suka kashe abokan gaban gaba d’aya hardai sukai nasaran kama shugaban abokan gaban nasu wanda ya jagoranci yak’in ...Babban abinda ya firgita Yarima Mahmood shine wannan shugaban abokan gaban da sukai nasaran capkewa k’afafunsa kawai Mahmood ya kalla ya gane d’aya ne daga cikin ‘yan uwansa.... Cikin tsananin tashin hankali yake bin k’afafun da kallo hardai ya kusan k’arasowa zuwa fuska... Saidai kash kafin ya k’araso zuwa fuskar ya farka daga baccin bai hangi ko wanene cikin k’annen nasa ya kawo masu wannan hari ba....
Yarima Mahmood ya fuzar da fuci a hankali yana mai shafe sumar kansa... Wannan mafarki da d’aure Kai yake... Waye cikin ‘yanuwansa yayi mafarki dashi...? Tambayar da ya tsaya masa a mak’oshi... Sannan mai yasa Ja’afar ya saka kaya na alfarma ba kayan bayi ba...? Sannan Maiyasa D’an uwansa ke k’ok’arin kashesa Ja’afar ya tare masa...? Shin ina Ja’afar...? Mai yasa zai tafi yabar Masarautar nan...? Sannan idan har Jafar ya cika bawa ai bazai tab’a barin Masarautar nan ba..? Toh ya akai ya sami k’arfin gwiwan barin Masarautar yana a matsayin bawa..? Wad’annan tunani sun kasa barin kwanyar Yarima Mahmood... Baccin da bai iya komawa ba, ya mik’e ya zira jallabiyarsa fara k’al kana ya fito waje....
A b’angaren Muhibbah kaw ma iya cewa da alama baccin ya k’aurace mata itama... Mafarkin mahaifanta taitayi, musamman mahaifinta da takeji can k’asar zuciyarta tamkar Yana nan a cikin Masarautar nan...
Mayafi ta d’auka ta rufa akanta kana ta fito haraban masauk’in nata... Tai jigum tana duban sararin samaniya tana hango taurari jefi jefi... Lokaci guda tunanin rayuwarta na baya na zuwa mata... Maiyasa takejin rauni cen k’asar zuciyarta...? Maiyasa takejin d’aukan fansa bai kamaceta ba...? Shin anya abu mai kyau takeyi...? Shin hak’uri da yawan afuwa baifi d’aukan fansa ba....? Toh amma ta yaya zata iya yafe masu Ta mance komai...? Wasu hawayen suka kuma gangaro mata wani b’angare na zuciyarta naci gaba da raya mata
“You’re not a bad person Saudatu... Ke ba muguwa bace, burinki na d’aukan fansa na nufin kema kin zamto daidai dasu... Ask yourself, Ki tambayi kanki Maiyasa cen k’asar zuciyarki kikejin rauni da fad’uwan gaba..?
A fili ta baiwa zuciyar tata amsa “Sabida ni mace ce wacce a halittana tun fil azal akwai rauni....!”
Take taji zuciyar nata na kuma bata amsa da fad’in “Ba haka bane... Sabida Ke ba muguwa bace, bazaki iya cutar da d’an adam kaman yanda su suka cutar dake... Saudatu Ki aje makamanki Ki bi shawarin Ansar ki komaga sabon ahalinki wanda Allah ya maye maki gurbinsu da iyayenki da ya d’auka daga gareki...!
Cikin kuka take girgiza kai tana mai furta “Toh mahaifina fah da nakeji a ajikina Yana nan raye cikin Masarautar nan... Bazan iya tafiya ba tareda na tabbatar da zargina ba...!”
Zuciyar tata taci gaba da fad’i mata “Mahaifinki baya raye Saudatu... Kawai kinsa ma ranki haka d’in ne shiyasa kike zaton hakan ne....!”
Kame kanta tai sosai had’ida tak’urewa jikin garu tana kuka sosai take furta “No no no... Ya isa....ya isa haka...!!” Kuka sosai ya kufce mata... Tana mai k’unshe bakinta da duka tafukan hannayenta biyu...
Kaman sautin kukan mutum yake saurarowa daga nesa, ya d’an dakata da tafiyar nasa had’ida kasa kunnuwansa sosai, kasancewar dare ne komin k’ank’antan k’ara sai kaji dab kunnuwanka... A hankali yake bin hanyar da yake sauraron sautin kukan na fitowa daga nan....
Cen ya hangota tak’ure ta kifa kanta da gwiwa tana cazgan kuka....
Tsaye yai yana dubanta cikeda tausayawa.... A duniyarsa baison yaga mace na kuka irin haka koda kuwa baiwace ba d’iya ba, harga Allah yakanji babu dad’i cikin zuciyarsa... A hankali yaci gaba da takowa zuwa gareta, saida ya k’araso har yanda take kana yai sallama cikin muryarsa mai cikeda aminci....
D’if kukan nata ya d’auke tamkar anyi ruwa an d’auke, dikda k’irjinta dake bugawa a hankali hakan bai hanata k’ok’arin saita kanta ba.... Tai saurin gogewa hawayen fuskarta had’ida d’agowa... A karo na farko da sukai eye contact tin bayan dawowarta Masarautar....
Yau Yarima Mahmood ne tsaye a gabanta, tabbas abubuwan da suka faru wancan lokacin sun shiga dawo mata daki daki, saidai ya zama dole tai k’ok’arin saita kanta ta tattaro duka jarumtarta ta had’e waje guda...
Ta k’ak’aro murmushi a hankali kana ta mik’e tsaye tana mai gyara mayafinta..
“Barka da dare Rankashi dad’e..!” Tai maganar tana mai duban k’Asa...
Yarima Mahmood da har lokacin hannayensa Ke hard’e ta baya jinjina mata kai yai a hankali kana yace “Barkanki...! Ke kuwa mai kikeyi a nan cikin daren nan.....?”
Ta d’an saci dubansa jin tambayar da ya jefo mata kana Ta kuma k’ak’aro murmushi tace “Babu komai rankashi dad’e ni bak’uwa ce a Masarautar... I guess rashin sabo da wajene yasa bacci ya k’aurace min shisa na fito nan na zauna....!” Ta k’arashe tana wasa da ‘yan yatsun hannunta....
Jinjina kansa yai a hankali kana yace “Shiyasa kike kuka...? Ko kinsan sautin kukanki ka iya hana wasu halittu samun nitsatsen bacci cikin Masarautar nan...?”
Wannan karon d’agowa tai tana dubansa sosai kana ta d’an kauda fuskarta gefe....
Ganin tayi shiru babu amsa yasa Yarima Mahmood gyara tsayuwarsa had’ida d’aga kansa sama kad’an....
“Bakiyi kamanni da bayi ba... Shin wacece Ke...?!” Ya k’arashe yana mai sauk’e idanunsa akanta da alamun tuhuma...
Ji tai wani abu ya tokare mata mak’oshi, tai k’ok’arin daidaita natsuwarta
“Bak’uwar Umaima ce ni Rankashi dad’e....!” Tai maganar tana mai sadda kanta k’asa...
Sosai ya kaikaito wannan karon yana dubanta tamkar wanda ya tina wani abu kana yace “Muhibbah..?!”
Ta d’ago itama tana dubansa, lokaci guda ta sami kanta tana mai jinjina masa kai alamun eh....
Yarima Mahmood ya gyara tsayuwarsa kana yace “It was you then...Kece wacce kika taimaki d’iyata Zahra...”
Taji murmushi na zuwa saman fuskarta kana tace “Nayi abinda ya kamata ne your highness...!”
Tinda suka soma magana sai yanzu ya sinkayo wani zak’i cikin muryar nata bayan ya ambaci Zahra....
Yai murmushi for the first time tin bayan had’uwarsu a nan wajen... Lokaci guda kuma ya d’aure fuska kaman wanda ya tina wani abu... Ita kaw Muhibbah zuciyarta sai ci gaba da tabbatar mata take, tabbas weakness d’in Yarima Mahmood d’iyarsa Zahra ce, hanyar da zata sami yardarsa kenan shine ta shiga jikin d’iyarsa sosai... Muryarsa ne ya katse mata tinanin nata
“Kin min laifi...!”
Ta d’an d’ago da alamun firgici wannan karon kana tace “Laifi kuma Rankashi dad’e...?!”
SameenaAleeyou 📚
[6/8, 8:31 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH*
*016*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Yarima Mahmood ya jinjina kai kana yace “K’warai kuwa... Kinmin laifi...”
D’an sadda kanta ta kumayi kana tace “Dikda bansan laifin ba, tuba nake Rankashi dad’e...!” Cikeda risinawa tai maganar...
Ya d’an gyara tsayuwarsa a karo na UKU had’ida yin gyaran murya kad’an “Baki San laifin ba....?”
Ta d’ago kad’an tana duban fuskarsa da security light ya haske tarau... Lokaci guda ta kuma maida nata fuskar k’asa tana mai furta “Tuba nike Rankashi dad’e...!” Yanda tai maganar sai yai masa tamkar ya tab’a sanin mai irin wannan muryar shekaru da jimawa...
Ya d’an d’auke idanunsa daga dubanta kana yace “Umaima bata sanar dake sak’o na ba...?!”
Sai yanzu ta tina ashe fah Wai tin jiya Umaima ta sanar da ita Yarima Mahmood na kiranta... Ta d’an daburce kad’an kai kace har cikin zuciyarta hakan ne kana tace “Allah ya huci zuciyarka Rankashi dad’e...!”
“Baki amsa min tambayata ba... Sannan cikinku waye zan hukunta Ke ko Umaima...?!” Ya k’arashe Murya a dake...
Dubansa kad’an tai kana ta shiga girgiza kai a hankali “Ta sanar dani Rankashi dad’e... A gafarceni laifin nawa ne... And please kar a hukunta Umaima batada laifi... !”
Bai amsata ba sai jefo mata tambaya da yai.. “Kinada alak’a da gidan sarauta ne...?”
Taji tambayar a bazata...
Gyara tsayuwarta ta d’anyi alamun gajiya da tsayuwa kana tace “A’a Rankashi dad’e wannan shine karona na farko a gidan Sarauta...!”
Ya jinjina kai a hankali yana jinjina d’abi’u irinta babban gida da take dashi, lokaci guda yana karantar ta da alama ta soma gajiya da tsayuwar..
Shiru ya gifta tsakaninsu har kaman babu mai yin magana cikinsu kana Yarima Mahmood yace “Baki sanar dani ba.. Kukan mai kike a nan...?”
Ta k’ak’aro murmushi kana tace “Kewar gida nake Rankashi dad’e... Kaifa mai ya fito dakai cikin daren nan....?!”
Saida tai tambayar sai kuma taga rashin dacewar tambayar tata, musamman da ta hangi irin duban mamakin da yake mata...
Lokaci guda ta kuma risinawa tana mai furta “Tuba nake Rankashi dad’e... A gafarceni....!”
Yanda tai maganan ya sanayasa sakin k’asaitaccen murmushi a hankali kana yace “Na kasa bacci ne kaman yanda kema kika kasa....”
Mamaki ya cikata ganin ya amsata Kai tsaye, Ta d’an jinjina kai a hankali kana tace “Kai hak’uri Rankashi dad’e, not being nosy, har kuma masu mulki kunada damuwar da take hanaku bacci....?”
Dariya taso basa wannan karon jin kalamanta tamkar ta k’aramar yarinya, saikace Zahra ce tai maganar...
Gyaran murya ya kumayi kad’an bayan ya murmusa a tak’aice kana ya isa gefen dakali ya d’an zauna...
Ganin tai tsaye wajen ya sanyashi nuna mata d’aya dakalin dake gefe kana yace “Bismillah..!”
Babu musu ta isa ta zauna...
Mahmood yaci gaba da fad’in “Baki San masu mulki sukeda damuwa ba... Shin baki San duk wanda Allah ya jarabcesa da jagoranci wasu Al’umma ya d’aura masa babban nauyi bane...? Ta yaya shugaba zaiyi bacci hankalinsa kwance bayan baisan halinda d’aukacin al’ummarsa suka kwana ba..?”
Tai shiru ba tareda ta iya amsa masa tambayar ba...
Yarima Mahmood ya jinjina kansa kana yace “Dik yanda bawa yakai da samun wani d’an Kaso na mulki daga cikin mulkin duniya da Allah ke rabawa tsakanin bayinsa bazai tsallake matsaloli na rayuwa ba... In one way or the other dole yanada matsalarsa... Cikan d’an adam kenan...!”
Tai shiru tana jinjina kalamansa lokaci guda tana jin natsuwa na sauk’ar mata cikin zuciyarta a hankali... Sai takejin kaman she’s safe around him....
Lokaci guda taga ya mik’e hannayensa hard’e Ta baya kana yace “Kije kwanta dare yaja sosai, kokuma Ki tausashi zuciyarki da ambaton mahaliccinki, zaki samu natsuwa a cikin yin hakan....!”
Daga haka bai kuma cewa komai ba sai sa kai da yai ya soma takawa a hankali....
Muhibbah tabi bayansa da kallo tamkar mai tinanin wani abu.... Cikin sauri ta mik’e tabi bayansa kana tace “Rankashi dad’e.... Na gode....!”
Bai juyo ya dubeta ba saima sa kai da yai yaci gaba da tafiya...
Muhibbah tabi bayansa da muguwar kallo cikeda tsana da k’yama har ya b’acewa ganinta, lokaci guda hawaye na kuma gangaro mata... Tasa bayan hannunta tana goge hawayen da suka wanke mata fuska... Zuciyarta naci gaba da mata zogi.... Lokaci guda kuma ta tsinci kanta tana mai bin shawarin Yarima Mahmood, Ta nufi d’aki ta d’auro alwala kana ta fito ta tada sallah kaman yanda ya bata shawarin yin hakan..
**
Washe gari Ta kama juma’a babban rana, sannan a wannan ranan Muhibbah ta sami ganawa da Giwa tun bayan zuwanta Masarautar... Wani ikon Allah had’uwa ta farko da Giwa da Muhibbah sukai Allah ya jefa k’aunar Muhibbah cikin zuciyar Giwa... K’awayen Umaima sunsha zuwa Masarautar amma bata tab’a gamo da wacce jininsu yazo d’aya irin Muhibbah ba, har tambayarta take gameda rayuwarta musamman da taji makaranta ya kawota garin...
Giwa ta kuma gyarawa daga kishingid’en da take tana duban Muhibbah dake risine gabanta a k’asa kana tace “Kikace ke ‘yar asalin garin Bauchi ne...?”
Muhibbah ta jinjina kai kana tace “Eh Allah shi taimakeki, ni ‘yar asalin garin Giad’e ne dake nan jihar Bauchi amma cikin Bauchi muke zama, mahaifina Alhaji Iro Datti ya kwana biyu da rasuwa....” Ta k’arashe cikeda girmamawa...
Giwa ta jinina Kai tana mai furta “Allah sarki ashe ked’in Marainiya ce... Toh ki saki jikinki kinji koh domin kaw kinzo gidan goya marayu... Ki zauna a Masarautar nan har iyaka lokacinda zaki kammala karatunki kinji koh...!”
Muhibbah Ta d’ago cikeda jin dad’i tana duban Giwa dake ci gaba da sakin murmushi a hankali kana tace “Godiya nake Rankishi dad’e... Na gode na gode K’warai Allah ya k’ara girma...!”
Giwa ta girgiza kai a hankali murmushi bai bar saman fuskarta ba take ci gaba da fad’in “Babu komai Muhibbah ki saki jikinki tamkar Umaima nan gidanku ne kinji koh...!”
Muhibbah Ta kuma risinawa tana godiya yayinda Umaima Ke tayata godiyan cikeda jin dad’i...
Har Giwa tai masu izinin ficewa Jakadiya bata daina jifarsu da muguwar kallo ba...
Suna fita Jakadiya Ta gyara zama tana duban Giwa “Allah shi taimakeki anya baki gaggawan maraba da wannan yarinyar ba, bansan dalili ba amma sam bata kwanta min ba....Allah shi baki yawan rai a duba lamarin...!”
“Jakadiya yaushe kika fara samun ra’ayin kanki a gidan nan banida labari”Giwa tace tana mai aikata mata wulak’antaccen kallo...
Jakadiya yada kai k’asa tana neman afuwa da tuba...
K’asaitaccen murmushi saman fuskar Giwa kana taci gaba da fad’in “Jakadiya kenan... Kaman baki san ko ni wacece ba har yanzu... Duk abinda nayi Jakadiya yanada manufansa... Kin tab’a tambayata Maiyasa dik abinda Umaima zatayi ko zatazo dashi cikin Masarautar nan bana dakatar da ita...?!”
Jakadiya ta girgiza kai a hankali alamun a’a...
Giwa Ta jinjina kai cikeda k’asaita kana taci gaba da fad’in “Umaima zata min amfani nan gaba kad’an a shirina Jakadiya... A halin yanzu Umaima ta gama aminta ni d’in Sarauniyar K’warai ce mai kimanta adalci da k’aunan jama’a... Dik abinda zan bijiro mata dashi nan gaba kad’an bazata watsa min k’asa a idanu ba, dan Haka Jakadiya koda wasa kar na sake zartar da hukunci cikin Masarautar nan mu samu sab’anin ra’ayi, duk abinda nayi ko zanyi ki ya zama wajibi akanki ya zama dole Ki aminta dashi... Da ace wata ce cikin bayi tayi wannan magana ba ke ba Jakadiya da yanzu ta jima a barzahu...!”
Jakadiya Jiki na matuk’ar rawa take fad’in “Tuba nake Allah ya taimakeki... Allah ya huci ran Giwar Amale... Jakadiya tana neman afuwanki Allah ya baki yawan rai...!” Ta k’arashe tana mai d’ago hannu daga nan durk’ushe alamun jinjina...
Shigowar Jamal ya sanya Jakadiya mik’ewa Ta basu waje bayan ta gama kwasan gaisuwa wajen Yarima Jamal....
Cen saman kujera na alfarma dake gefe cikin d’akin ya zauna... Mahaifiyar tasa ta dubesa kana tace “Baba na ya haka... Ya na ganka haka, akwai matsala ne...?”
Jamal ya fuzar da huci a hankali kana yace “Maami magana ce kan Ya Mahmood...!”
Ta gyara zama sosai tana duban Jamal kana tace “Umhum Ina saurarenka, mai kuma ya faru da Mahmood d’in...?”
Shafe fuskarsa Jamal yai da duka tafukan hannayensa kana yace “Maami Wai kinsan d’iyarsa Zahra ba Aliya bace ta haifeta... Yarinyar bada aure ya haifeta ba...!”
Shiru Giwa tai tamkar mai nazari tana mai kuma tabbatar da zarginta kan lamarin yarinyar, Toh amma saidai abu ne mai kaman wuya ace Mahmood zai aikata wani abu makamancin wannan, idan za’a saka mata takwabi zata iya rantsuwa d’anta Mahmood bazai tab’a aikata mummunan sab’o irin wannan ba... Ance ba’a shaidan d’an adam amma ita tayi shaidan Mahmood... Toh yaya akai hakan ta kansance...?
Muryar Jamal ya dawo da ita daga Duniyar tunani yanda yake fad’in “Maami abin ya matuk’ar bani tsoro da mamaki... Ya za’ace Yaya ya aikata babban abin kunya irin wannan, Maami bayyanar wannan magana barazanace garemu baki d’aya....!”
Dubansa ta d’anyi kana tace “Babu wanda zai sani, kuma kaima banaso ka nuna masa kasan komai, maganan zai zauna a haka kaman ba’ayi ba....!”
Su duka biyu sukai shiru kowa na sak’awa da warwarewa cikin zuciyarsa....
**
A b’angaren Mahmood kaw tinda aka fito daga masallacin Juma’a ya b’adda kama ya fice ya nufi gidan D’an uwan mahaifinsa Dattijo Baba Wambai, ko Ubandoma baisan ya fice ba, sannan ko motar Masarautar bai d’auka ba, hasalima motar haya ya shige ya nufi gidan Baba Wambai....
Tamkar wani buzu haka yasha rawani ya nad’e fuskarsa, a k’ofar gidan ya tsaya yanda ya tadda wani yaro ya taho zai shige k’ofar gidan..
Yarima Mahmood yai kiransa kana yace “Kai yaro shin kana shiga wannan gidan...?”
Yaron ya jinjina kai alamun eh kana ya k’arada “Amma matar gidan masifaffiya ce tana koranmu idan mun shiga d’iban ruwa....”
Yarima Mahmood da ya b’adda kama zuwa bak’on Buzu yace “Ka shiga ciki kace ana sallama da Baba Wambai.... Idan an tambayeka inji Wanene kace bak’on Buzu ne...”
Yaron ya jinjina kai yana mai amsawa kana ya nufi cikin gidan...
Jim kad’an saiga Baba Wambai ya fito a daddafe yana rik’eda yaron yake fad’in “Kai Muntaqa ka faye wasa gaban famfo shiyasa Innani Ke korinka, muje naga bak’on Buzun....!”
Yaron yai masa nunida yanda Yarima Mahmood ke tsaye kana yace “Gashi nan ai Baba...!”
Baba Wambai yakai dubansa ga mutumin saidai duba d’aya yai ma k’wayar idanunsa ya fahimci Mahmood ne...
Ya saki murmushi a hankali kana yace “Mahmuda kaine tafe da tsakar ranan nan...?”
Yarima Mahmood ya d’an murmusa kad’an yana mai jinjina kai yake furta “Ai nayi zaton bazaka ganeni ba Baba...”
Murmushin Baba Wambai ma yayi kana yace “Yo banda abinka Mahmooda dik yanda zaka kai ga canza kamanni ai bazaka b’ace min ba... Wannan idanu nawa da kake gani tarau yake, gashi gidanmu munyi gadon ciwon ido amma ni nawa har yafi Naka mai cikeda k’uruciya.... K’araso daga ciki....!”
Mahmood ya d’anyi still a wajen yana mai rik’o hannun Baba Wambai yake fad’in “A’a Baba Wai da nafiso mu zauna daga waje don banaso wani ma yasan nazo shiyasa na b’adda kamanni....”
Baba Wambai ya jinjina kai kana yace “Kayi gaskiya Mahmuda, hakan da kayi kayi daidai, mu k’arasa k’arkashin bishiyar Gamjin cen....!”
Mahmood ya jinjina kai yana mai taimakawa Baba Wambai har suka isa k’ark’ashin bishiyar, suka zauna saman manyan reshen bishiyar da suka sauk’o k’asa.....
Bayan sun gaisa Baba Wambai yace “Ina saurarenka Mahamuda, meke tafe dakai...?”
Mahmood ya d’an gyara zamansa had’ida kwance rawanin kad’an kana ya soma fad’in “Wato Baba kan mafarkan nan ne da suka addabeni wanda babu daren da zaiyi na kwanta bacci na tashi ba tareda nayisu ba... Abun ya fara damuna sosai Baba....!” Ya k’arashe cikeda kulawa...
Dattijo Wambai yai K’uri yana duban wani gefen kana yace “Mahamuda dik yanda akai wannan mafarkai naka da kake yawanyi sunada manufarsu... Banida ilimin fassarar mafarki amma koma minene Allah shi yasan maiyasa yake nuna maka abu makamancin haka cikin baccinka.... Wasilci na farko da zanyi maka shine kaci gaba da k’ok’arin kwatanta rik’o da addini... Sannan abu na gaba kaci gaba da taka tsan tsan cikin wannan gida D’ah na...! Gidan sarauta gida mai kafi da abubuwa na ban mamaki had’ida tarihi.... Kasa ma ranka babu wanda ya isa ya cutar dakai face da izinin mahaliccinka... Sannan ka tausaya ma wad’anda suke k’asa dakai domin ka samu sauk’in gudanar da al’amara daga wajen mahaliccinka....”
Yarima Mahmood ya jinjina kansa a hankali kana yace “In sha Allah zan yi k’ok’arin kwatanta dik abinda ka umarta Baba...”
Baba Wambai ya jinjina kansa alamun gamsuwa kana yace “Sannan abu na gaba shine tunda yanzu Allah yasa ka dawo, kaci gaba da abinda iyayenmu suka rik’e gidan dashi, don na tabbata tun bayan rasuwar mahaifinmu Sarki Kakanka mai rasuwa aka daina wannan kyakkyawar d’abi’a a cikin gidan....!”
Ya d’an dubi Baba Wambai kana yace “Me kenan Baba...?”
“Duk ranan Juma’a akanyi sauk’an alkur’ani mai girma cikin fada sannan mahaifinmu yakan fita masallacin juma’a ya raba sadaka ma yara da gajiyayyu sannan yakan sauya kama ya zaga ya duba marassa lafiya wasu lokutan harma da gidajen marayu...da kuma kasuwanni domin yaga mai yake wakana a k’asarsa. yakan kuma kai ziyara gidan yari yaga halinda fursunoninsa Ke ciki....Duk wad’annan d’abi’u ne masu kyau wanda shugaba idan ya suffanta dasu tabbas yayi koyi da shugabbannin K’warai.... Tin bayan rasuwar mahaifinmu aka daina gudanar da irin wad'annn al'amara a Fada... Daga nan abubuwa suka rikice, domin kaw duk gidan da ba'a ambaton Allah cikinsa wannan gida tamkar kufai ne....”
Mahmood yai shiru yana mai jinjina kansa kana yace "Haka ne Baba, in sha Allah za’aci gaba da sauk’an alk’ur’ani mai Girma duk juma’a cikin gidan kaman yanda akeyi a baya....”
Baba Wambai ya jinjina kai yana mai furta “Masha Allahu... Hakan yayi kyau Mahmuda, Ubangiji ya maka Albarka ya tsareka da tsarewarsa daga dikkan sharri da zai tunk’aroka...”
Mahmood ya amsa da Ameen kana ya jefowa Baba Wambai tambayar da ya sanyashi d’agowa sosai yana dubansa...
“Baba nikam nace ba, shin kasan lokacin da Ja’afar ya tafi ya bar Masarautar nan..? Shin dama Bawa na iya tsallake Masarautar su ne ya tafi wani wajen....? Shin Baba mai yasa Ja’afar ya tafi rana tsaka yabar Masarautar nan...? Kanada wata masaniya akai ne Baba....?”
SameenaAleeyou 📚*MUHIBBAH*
*017*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
A hankali Baba Wambai ya sauk’e ajiyan zuciya kana ya kuma duban Yarima Mahmood a karo na biyu....
“Baba akwai wani abu ne...?” Mahmood d’in ya bid’a..
Baba Wambai ya girgiza kai a hankali alamun a’a kana yace “Banida masaniyar abinda ya fitar da Ja’afar daga Masarautar nan... Kaman yanda ka dawo ka tarar baya nan, nima kwatsam na fahimci baya nan, Mahmuda abubuwa da dama cikin Masarautar sai ayi ban sani ba... Inaga idan akwai wanda yafi cancanta ya amsa maka wannan tambaya taka toh ba kowa bace face mahaifiyarka, sai ko kuma Waziri....!”
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 65