yanzu Allah yayi na dawo hayyacina..! Da wannan shawari muka nufo tsakar gida dan soma shiryawa....Wani ikon Allah muna fitowa tsakar gidan muka tadda Izzatu cikin bak’ak’en tufafi Alkyabba da rufin kai, hannunta rik’eda fitila jan wuta naci a cikin fitilar, Ta kafe mu da idanu cikin yanayi na ban tsoro ga wani k’aton bak’in tulu gabanta bak’in hayak’i na fitowa daga cikin tulun....!”
Jikinmu ya d’auki rawa sabida tsananin firgici da tsoron yanayin da mukaga Izzatu ciki wacce bamusan da zuwanta ba sai bayyanarta....
Murmushi ta sakar min tace “Gimbiya Turai k’araso mana, ki k’araso ga Hadimarki Izzatu kuma Aminiya a gareki...!” Tana maganar tana duban bak’in tulun dake ajiye gabanta yana fidda bak’in hayak’i...
Fattu jiki na rawa yake furta “Rankidad’e kada ki k’arasa...!” Fattu batakai aya ba Ta had’iyi kalamanta sakamakon wani garin magani da Izzatu ta busa mata..
Jikina na rawa na isaga Izzatu dake tsaye gaban tulun...
Ta kuma murmusawa tace “Turai lek’a cikin tukunyar nan ki gani..!”
Jikina bai daina rawa ba sabida tsananin tsoro na lek’a tukunyar mai fitarda hayak’i.... Wani ikon Allah Magidancin mutumi na gani mai kamanni irinta mahaifinmu saidai baikai Mahaifina a shekare ba..!”
Na d’ago a tsorace ina dubanta, murmusawa ta kumayi tace “Wannan shine d’anuwanki Alfah da ya shiga duniya nemanki...! Lek’a ki gani ya girma... Yayi aure aure har yanada iyali wanda ya aura a yawonsa Ta duniya da sunan yana nemanki...! Kar ki damu basai kin sha wahala ba ni nasan yanda yake... Fitilar tsafi ya hasko min hakan... Ta kuma tura fitilar cikin Tulun tana dariya take furta “Kinga gashi har matar tasa ta haihu, matar da ya aura a yawon nemanki... Kin gani lek’o ki gani Turai..!” Ta k’arashe tana mai kuma tura kaina cikin tukunyar yanda naga mutumin rik’eda jaririya sabuwar haihuwa..!
Hawaye na zubo min nake k’ok’arin kai hannuna Ina furta “Alfah..! Alfah d’an uwana..!”
Maidodani baya Izzatu tayi tana mai ci gaba da sakin wane irin dariya lokaci guda take ci gaba da furta “Wannan basu kad’ai bane ahalinsa, wad’annan a yawon nemanki ya samesu, akwai ahalinsa da ya baro ya fito yawon nemanki wanda fitilar tsafi bai hasko mana duniyar da suke ba...! Amma zamu fara da wannan ahalin nasa kafin sauran su bayyana mana...!” Tana ida fad’in haka ta danna hannunta cikin tulun wanda tuni jan wuta ya soma fitowa daga ciki... K’ara ta saki wanda take mukaga gidan da muke ciki ya soma cida wuta... Tana kuma danna hannunta wutan na kuma kama ko wani kafa na cikin gidan... Dukda azaba da take sha hakan bai hanata tura hannunta cikin tukunyar ba... Muna a haka Giro ya shigo ya tadda wanann tashin hankalin... Take muka hango wannan matsafin ya bugawa Giro wata Sanda akansa... Tinda ya buga masa sandar bai kuma koda shurawa ba, Giro ya fad’I macecce a wajen... Fattu ta yunk’ura zatayo kan mijinta matsafin mutumin ya nunata da sandar hannunsa tuni Fattu ta komada baya jikinta na wane irin rawa...
Ni kuwa inaji Ina gani Izzatu ta janyoni waje ta turani cikin wani mota irin wanda ake zuba awakai, ta koma cikin gidan tana kallon yanda wutan Ke ci, Mutumi mai tuk’a motar ba kowa bane illa Wambai, Ina kuka Ina dubansa dan na ganesa shine Yayan AbdulJabbar da ya soma zuwa neman aurena a Masarautar mu kafin isowar AbdulJabbar... Ina hawaye na hango hawaye kwance shima cikin idanunsa,cikin rawar murya yake furta “Kiyi hak’uri babu yanda na iya ne, sun d’aureni ta ko ta ina... Amma ga wannan Taswiran zan baki ki adana duk daren dad’ewa shine zai toni asirin wad’annan azzalumai.... Ki b’oye wannan Taswiran cikin jikinki duk yanda za’ayi kada ki bari su gani...!”
Jikina na rawa na amsa Taswiran da Wambai ya bani na tura jikin k’ullin gashina... Daga nan isowar Izzatu naji yanda Ta busa min wani garin magani.....Tin daga haka farkawa nayi na ganni a wane irin sunkurumin d’aki, da ita da matsafin mutumin nan suna tsaye gabana... Izzatu tana kan wani jan Darduma mai d’aukeda tambarin masarauta... Nan ta soma sanar dani abubuwan da suka faru
“Turai ko Ince Baiwa Izzatu mai k’wacen miji daga rana mai kaman ta yau kin fita daga rayuwar AbdulJabbar, kin fita daga rayuwar mijina kuma uban ‘ya’ya na, wannan waje da kike gani shine zai zamto ma’ajiyanki, Sarki AbdulJabbar ya zaci kin mutu a cikin gobaran da ya tashi a gidanki, Wuta ya cinyeku keda Mijin Hadimarki...! Amma kar Ki damu nayi mutunci tunda Hadimarki da d’iyarta sun rayu, suna cikin Masarautar nan a nan b’angaren bayi, tinanin Hadimarki ya shafe bazata iya tuna komai ba balle ta sanar da AbdulJabbar... Sannan d’an uwanki Alfah a lokacin da na isa gareshi ya tafi ya koma ga asalin iyalansa na farko, matarsa da babbar d’iyarsa mai shekaru biyu a duniya hakan yasa ban cimmasa a wannan gidan ba, zai koma ya samu wuta ya cinye iyalansa, koda shike nayi mutunci shima, na taho da gudan jininsa ciki Masarautar nan, jaririyar da amaryarsa Ta haifa wacce ya aurota a yawon nemanki na taho da ita cikin Masarautar nan, zan goyata a matsayin d’iyar d’an uwana daga k’arshe itama zanyi sadaukarwa na k’arahe da ita daga tsatson mahaifinki Sarki Jamaluddeen wanda ni ce nan nayi sanadiyar mutuwarsa...! Ko ba dad’e ko ba jima sauran ahalin Alfah zasu bayyana mun kuma sai nayi ajalinsu suma dan babu wani dangin Jamaludden da zasu rage a doron k’asa balle wataran suyi sanadin Mulkina..!!”
Ta kuma kecewa da dariya kana ta d’auko wata doguwar wuk’a tana fad’in zata cire harshena yanda bazan kuma yin magana ba... Wani ikon Allah wuk’an bai yanka harshena ba, gani nayi Ta ambato Jakadiya dake tsaye daga waje, Jakadiya ta shigo ta baiwa Jakadiya umarnin ta bud’e bakina da k’arfin gaske...! Haka sukayi tarayya itada Jakadiya suka bud’e bakina matsafin mutumin nan ya zuma min wani abinda bazan iya cewa gashi nan ba... Tin daga wannan lokacin naji harshena ya d’aure ban iya cewa komai, sannan ina fama da gushewan hankali na wasu lokuta wasu lokutan kuma nakan jini cikin hankalina, da alama asirin gushewan hankali da sukai min baiyi wani tasiri akaina ba... Na zauna cikin ukuba hannun wad’annan matsafa na tsawon shekaru dan har girma ya soma sauk’a min... Wata rana Izzatu ta shigo...!” Taja Burki ta d’aga kai tana duban Ubandoma wanda Ke duk’e gabanta yana hawaye...
Hannu tasa ta share hawayen da suka zubo mata, lokaci guda taci gaba da fad’in “Izzatu ta shigo tana fad’in d’an uwana Alfah yana wanann gari kuma kusada Masarautar nan, da alama bai jadadda da batun nemana ba... A lokacin ina cikin yanayi na hankali amma sanin halin wannan muguwar mata zata iya yin komai idan Ta fahimci a hayyacina nake hakan yasa na nuna mata a lokacin ma cikin hauka nake tuburan... Tinda naji tace Alfah na garin nake neman hanyar guduwa na sami yanda zan gana da d’an uwana domin na kub’utar dashi daga sharrin wanann azzalumar mata... Wata rana na samu na gudu, wannan mutumin ya mance bai d’aureni ba dan dama shine da Jakadiya masu lura da yanda nake... Shi yake d’aureni da sark’ok’i Jakadiya tana bani abinci, sun cutar dani sun d’aureni tsawon shekaru babu ibada ga mahiccina yanda ya kamata, saidai idan Ina cikin hankali nayi ishara a zuciyara tinda haukan nawa zuwa zuwa ne...Rayuwata haka taci gaba da tafiya cikin halin ha’ula’i a wannan kurkuku... Ranan dana samu na gudu domin na nemi d’an uwana Alfah a ranan bukin wata k’aramar sallah ne...!”
*MUHIBBAH*
*71*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Gimbiya Turai taci gaba da fad’in “Ranan bukin hawan doki na, Washe garin sallah kenan... kasancewar hankula sun karkata zuwaga shagulgulan bukin sallah ni kuma nayi amfani da wannan damar na gudu na fice cikin Masarauta da zummar neman d’an uwana Alfah dukda sanin cewa bansan ta yanda zan soma nemansa ba balle nayi tunanin samunsa, wani ikon Allah sai na hangi Jakadiya rungume da mutum saman kafad’arta sai faman waige waige take da alama wani hidiman yasha gabanta sunma mance Sun barni a kwance kuma a bud’e... Sannan akwai duhun dare a lokacin zai wahala a ganeni...Na dinga lallab’awa ina bin bayan Jakadiya a nawa tunanin itace zata kainiga d’anuwana Alfah... Aiko cikin wane ikon Allah sai na hangeta ta isaga Izzatu ta duk’a gabanta kana ta’aje wata ‘yar matashiyar yarinyar data aza a kafad’arta, cikin yanayi na firgici take furta “Rankidad’e munje har yanda Yarinyar take rayuwa da iyayenta saidai naga abin al’ajabi...!”
Cikin huci Izzatu taceda Jakadiya “Mai kika gani Jakadiya..?!”
Jiki na rawa Jakadiya take nuna yarinyar dake kwance tamkar gawa kana tace “Wannan yarinyar da za’ayi asirin gadon Mulkin su Yarima da ita d’iya ce ga wannan mutumi da kika nuna mana hotonsa a tukunyar tsafi kikace duk wanda ya gansa cikin garin nan ya sanar dake..!”
Izzatu ta zaro idanu waje tace “Kina nufin d’iyar Alfah ce..?!”
Jakadiya ta jinjina kai tace “K’warai Rankidad’e da idanuna naga mutumin...!!”
Cikin wane irin daka tsawa taceda Jakadiya “Maza ki koma ki tabbata Alfah ya mutu wannan karon daga shi har matar tasa ku k’onesu da wuta, kada ki bari ya kufce..!! Ita kuma wannan yarinyar zan mik’ata ga boka Tal’udu domin ya sanar dani duk yarinyar da ‘ya’yana suka lalata ma rayuwa itace gudan jinin da K’addarar Masarautar nan zai rayu a wuyatan, itace zai tsafi da ita domin ya tabbatar da dawamammiyar mulki na data ‘ya’yana cikin Masarautar nan...! Wannan yarinya SAUDATU itace makullin mulki na data ‘ya’yana...!!!” Ta k’arashe tana sakin wane irin shewa, ni kuma a lokacin naji jikina na wane irin karkarwa, naga wannan yarinyar d’iyar d’anuwana kaman yanda Izzatu tace tana buk’atar taimako daga gareni dan idan na barta Izzatu zata halak’ata, koda ba d’iyar d’anuwana bace rai ne mai buk’atan taimako daga hannun wannan azzalumar Baiwa da babu Allah cikin zuciyarta... Na isaga yarinya SAUDATU na tallafota na k’urama fuskarta idanu sai na hango kamannin d’anuwana a tattareda ita, naji wasu irin hawaye suna zuwa min, jikina ya d’auki rawa... Duk wannan abinda nake Izzatu bata lura dani ba sai sakin wane irin muguwar dariya take tana furta a yau burinta zai cika za’a kulle k’ofar sarautun Masarautar nan akanta da ahalinta da jinin wannan yarinyar... Cikin rawar jiki na soma k’ok’arin gudu rungume da yarinyar saidai ashe bokan Izzatu tuni ya hangoni sai ganinsa nayi gaba gareni cikin wane irin yanayi maras kyan gani.... Kafin nayi wani aune ya nunani da sandar tsafinsa sai gani nayi kaman an finciki yarinyar daga hannuna ta fad’a hannunsa, naji mummunar muryarsa yana furta “Wannan tamu ce, ita d’in an d’aura mata aure da Sarauniya, Amaryarmu ce wacce sarauniya zata zuk’i jininta..!” Take naji kaman an kifar dani k’asa tin daga lokacin ban kuma sake sanin komai gameda Alfah da ahalinsa ba domin kaw farkawa kawai nayi na ganni a d’akina wannan mutumin ya d’aureni da sark’ok’i... Hakan yasa nasan Fuskar d’iyar Alfah... Kuma ko bayan shekaru da na sake ganinta sai na fahimci itace, kenan Allah bai ida nufin Izzatu da Bokanta akan d’iyar Alfah ba, ya kub’utar da ita da buwayarsa daga hannun wad’annan azzaluman bayi nasa... Shiyasa na k’udiri niyyan mallaka mata wannan Taswira da Wambai ya bani shekara da shekaru Ina ajiye dashi, domin kuwa jikina ya bani itace zata zamto silan tonon asirin Izzatu...!!”Tana hawaye taci gaba da basu labari har kawo zuwa yanda Muhibbah ta taimakesu itada Ja’afar da taimakon da Ubandoma yayi masu bayan duk abubuwan da yayi mata a baya wanda Muhibbah itace Ta matso masa da tsoron mahaliccinsa kusa har ya karyar masa da zuciya yayi abinda ya dace..!!
Gaba d’aya baka jin sautin komai sai ajiyan zuciya da zuban hawaye... Sosai Ja’afar yake kuka ya matso kusan Gimbiya Turai ya duk’a yace “Rankidad’e kikace budurwar data taimaka mana sunanata Muhibbah Kuma Ta ambaci sunana tace ta sanni..?!”
Gimbiya Turai ta jinjina kai tace “K’warai ta ambato sunanka J’afar, kuma ta sanka, kuma wanann budurwar itace SAUDATU d’iyar d’anuwana Alfah wanda Izzatu ta halak’asa...!!”
Hawaye suka kasa daina zubowa daga idanun Ja’afar, lokaci guda yake furta “Saudah ta dawo, ta dawo cikin Masarautar nan...!!”
Gimbiya Turai ta jinjina masa kai tace “K’warai Jafar ta dawo kuma nasan duk yanda take cikin Masarautar nan tana buk’atar taimakonmu domin kuwa idan har Izzatu ta fahimci wacece ita toh rayuwarta ka iya kasancewa cikin had’ari mafi muni fiyema da wanda ta shiga a baya...! Amma ya akayi kasan SAUDATU..?!”
Ja’afar da idanunsa suka kad’a sukai jazir bayan hannunsa yasa ya share hawayen da suka zubo masa lokaci guda ya soma furta “SAUDATU wata yarinya ce da muke had’uwa da ita a k’aramar Kasuwar dake gabashin Masarautarmu, nakan shiga kasuwa duk ranan asabar domin nayi cinikin harawan dawakan Sarki na musamman, kaman yanda kuka sani ni d’in dah ne d’aya tol ga Sarkin Bargan Dawakan Sarki mai rasuwa mai suna Almu, mahaifiyata kuwa mai suna Kumbo tun lokacin data haifeni Allah yayi mata cikawa kaman yanda mahaifina ya bani labari, tun tasowata bansan komai ba face kulada dawakan Sarki kaman yanda mahaifina ya d’aurani akai, hakan yasa har bayan rasuwar mahaifina Mai Martaba bai yarda da kowa yaci gaba da kula masa da dawakansa ba sai ni dukda kuwa k’arancin shekaruna a wancan lokacin, tun ina k’arami na iya zuwa kasuwa nayi cinikayyan abincin Dawakan Sarki da kaina sabida nid’in nasan kan kalolin ciyayi abinci Dawakai wanda yafi kyau ma Dawakai... Wannan dalili na d’aya daga cikin abinda ya kuma jefa shak’uwa da Sabo tsakanina da Sarki AbdulJabbar... Toh Kasuwar da nake zuwa nakan had’u da yarinya Saudatu wasu lokutan da ‘yar jakanta Ta kayan data saye a kasuwa... Na lura yarinyar kaman tanada tsoron mutane dan ko kallo idan ka faye mata zakaga ta soma jada baya kaman zata gudu, da shike kasuwa ne k’arami hakan yasa yawancin mutanen da suke halartan kasuwan akai akai sukan iya sanin juna... Wata rana ta gama sayyayan kayan lambu dangin su tumatur ni kuma na d’auko harawata ta Dawakai na yunk’ura zan mik’e d’aukeda harawa a gadon bayana kwatsam mik’ewar da zanyi naji nayi fatali da abu ashe kayan miyanta na watsar mata... Ta durk’usa a wajen tana duban kayan miyan tana kuka...!
Akaita bata hak’uri tak’i tayi shiru, nima da naji haushi nayi zuciya nace kar Allah Sa kiyi hak’uri Ke wannan yarinyar dama haka kike ko yaushe kina yawan zuwa kasuwa amma kaman akwai abinda kike b’oyewa, wasu irin iyaye ne gareki ma da bazasu Zo kasuwa da kansu ba sai su turo k’aramar yarinya kaman ke...!! Haka nayita mata masifa a wajen har ta tsagaita da kukan da take ta tsaya tana dubana... Ashe itama taji haushi matuk’a ai kuwa tuni naga ta daka tsalle ta finciko harawana ya tsinke gaba d’aya k’ullun dakai masa ya watse a wajen... Sai faman sakin huci take tana hararata... K’arshe jama’an dake wajen suka shiga bamu hak’uri da ni ita, aka tattara mata kayan miyanta nima aka tattara min nawa harawan..! Sosai rashin tsoronta ya bani mamaki... Ni kuwa nace wannan yarinyar batada tsoro kuma ban santa a fad’in yankin ba, bansan su waye iyayenta ba, amma wannan rashin tsoro nata yayi min kamada d’iyar manyan mutane ko masu mulki, nace sai nabi yarinyar naga inane gidansu... Tana tafe ina biye da ita har ta fahimci Ina biye da ita... Taja ta tsaya ta rik’e kunkumi tanaci gaba da sakin huci, lokaci guda kuma naga Ta auna a guje tana k’ok’arin canza hanya.. Nayi saurin shan gabanta nace “Ki tafi a hankali kada ki kuma zubar da kayan miyanki, ni babu abinda zan miki...!”
Sai naga taja Ta tsaya amma dai tsoro bai rabu da ita ba... Na aje harawana gefe nace “Ke kuwa yarinya menene sunanki kuma daga ina kike dan ni ban tab’a ganinki a yankin nan ba sai tsakanin kwanakin nan..!”
Ta kauda kanta gefe kaman bazata min magana ba sai kuma tace “Abbah na ya hanani magana da kowa a garin nan..!”
Mamaki ya kamani nace “Ya hanaki magana da kowa kuma shine yake turoki Kasuwa kiyi sayayya..?!”
Ta jinjina kai tace “Eh ya hanani magana da kowa yace akwai dalilin da ya kawo mu garin nan da zaran mun sami dalilin zamu tafi mu bar garin nan, Abbah na baya fitowa daga gida sai dare sabida yace akwai wasu mugaye a garin nan da zasu iya cutar dashi shiyasa baya iya zuwa kasuwa saidai ya turani...!”
“Sosai mamaki ya kamani jin irin kalaman da take fad’i, na jinjina kai nace “Toh Ummanki fah.. Maiyasa bazata miki rakiya zuwa Kasuwar ba..?!”
Ta d’an dubeni kad’an sai kuma tace “Ummah ta batada lafiya, ta kusa haifa min k’aramin k’ani bazata jure fitowa kasuwa ba..!”
“Na jinjina kai nace toh inane gidanku..?! Daga yanda muke tsaye tamin nuni da wani gida can da yake arewa da yanda muke tsaye, gidan shi kad’ai ne a wajen tol ko mak’ota basu dashi..! Na jinjina kai nace ni kuma cikin Masarauta ne gidanmu kuma sunana Ja’afar...! Ni ba mugu bane kaman yanda kikayi zato, kiyi hak’uri da zubar miki kayan miya da nayi..! Wani ikon Allah sai gani nayi ta murmusa tace “Shikenan Babu komai nima kayi hak’uri da zubar maka harawarka da nayi..!”
“Na kuma murmusawa Ina dubanta sai kuma nace “Basai kin bani hak’uri ba ni na hak’ura... Ki tafi gida kar a soma nemanki..! Ki wuce har ki shige gida ina kallonki bazan bari wani ya cutar dake ba..! Ta murmusa tace min na gode, zan iya kiranka Yaya Ja’afar tunda banida kowa a garin nan kuma ba’a barina na fita ko ina sai kasuwa kasuwan ma sai ranakun sati..!”
“Na kuma murmusawa nace “Toh ai ban wani girmeki sosai ba ni kar ki tsufar dani ki kirani Yaya..! Ta kuma murmusawa tace “Amma ai ka girmeni, kuma nasan k’anwarka ce tsarata kaga ni banida wani Yaya banida kowa sai Ummah na da Abbah na saiko k’aramin k’anin da zata haifo min..!”
“Tayi maganan cikeda yarinta, na murmusa nace “Toh shikenan tinda bakida Yaya Ki kirani Yaya nima tinda banida k’anwa kin zamto k’anwata...Hakan yayi miki..!?”
“Ta jinjina kai tana kuma murmusawa tace yayi min.. Yaya Ja’afar..! Daga haka d’aga min hannu tayi ta shige tana waigowa har ta kusan isa gida Ina nan tsaye Ina dubanta, sai kuma na dakatar da ita nace “Gashi kuma Yaya baisan sunan k’awarsa ba har zata shige..!” Ta murmusa kad’an tace “Sunana SAUDATU..!”
“Na jinina kai nace “K’anwata Saudatu..! Tai gajeren murmushi Ta kuma d’ago min hannu tace sai anjima...! Har saida naga shigarta gida kafin nasa kai nima na d’auki ciyawata na shige...! Toh tin daga wanann lokacin Sabo ya shiga tsakaninmu da Saudatu, nakan mata rakiya har zuwa gida, a haka bukin sallah ya k’arato na kula tana son zuwa taga hawan Dawakai amma baza’a barta ba a gida tinda ba’a barinta taje ko ina... Nayita bata labarin yanda hawan bukin sallah yake kasancewa, sosai yake sakata nishad’i yanda kasan ta had’a jini da sarauta... Kullum bata da labari da ya wuce na Dawakai da gidan sarauta... Tace min tana son ta shigo Masarautar nan wata ran taga yanda ginin gidan sarauta yake.. sabida idan tanama Abbanta labarin sarauta da abinda ya shafi gidan sarauta sai yayita mata fad’a yace koda wasa babu abinda ya had’ata da sarauta, babu komai cikin gidan sarauta sai zalunci... Dukda kuwa tsananin son kasancewa gidan sarauta da Saudatu keyi... Wata Rana Nace ta biyoni na shiga da ita taga yanda gidan sarauta yake ko sau d’aya ne a rayuwarta...haka kuwa akayi wani rana ta biyoni a tsorace na nuna mata cikin Masarauta, tayita mamakin girman gidan sarauta da yanda ake gudanar da al’amaran cikin Masarauta.. Naga yanda take matuk’ar son gidan sarauta da abinda ya shafi sarauta... Nace tinda ga k’aramar Sallah ta gabato ta fita taga yanda ake wasan Dawakai masu mulki suna hawa dawaki kuma suyi wasan saman dawaki su nuna bajintarsu.. Tace dani Aiko duk yanda za’ayi zata nemi hanya ta fito dukda ba sanin gari tayi ba, amma tana matuk’ar son ganin wasan doki... Nace zanso nayi mata rakiya tinda batasan kan gari ba amma saidai nid’in Bawa ne banida iko sai abinda Iyayen gidana sukace.. Na bata hak’uri nace bazan samu mata rakiya ba domin kuwa ni ne nake jan linzamin dokin D’an Sarki k’arami Wato Yarima Fu’ad sabida bai iya rik’e linzami..! A haka dai tace toh shikenan amma tabbas zata fita taga yanda wasan Doki yake kasancewa...!”
J’afar ya sauk’e nannauyan ajiyan zuciya hawaye naci gaba da gangaro masa yake furta “A ranan bukin wannan sallan tabbas wani al’amari ya faru... A hanyarmu ta komawa dani da yaran Sarki gaba d’aya wanda mune mukai dare sabida wasan doki da yaran sarki suka tsaya yi... A hanyarmu muka tsinci Saudatu ta b’ata sabida batasan kan gari ba... Yarima Mahmood wanda duk cikin yaran Sarki yafisu jin k’an mutane shi yayi umarni mu d’auketa mu maidota gida dan na sanar dashi na santa kuma har gidansu na sani.. Hakan yasa muka d’aukota muka nufo Masarauta... Na tafi na barta tareda yaran Sarki..!!” Muryarsa ya carke hawaye naci gaba da zubo masa...! Lokaci guda ya kuma d’agowa yana duban Gimbiya Turai wacce itama hawayen take... Cikin rawar murya yake furta “Kenan sun lalata rayuwar Saudatu..! Sunci zarfinta.. Sun tarwatsa ahalinta..!!! Tabbas daga baya na daina ganinta a kasuwa na kuma tadda gidansu su Saudatu ya k’one babu kowa cikinsa ya zama kango... Kuma babu wanda ya sansu balle naji labarun ina suka koma.! Ashe abinda Giwa da ‘ya’yanta suka aikata ma Saudatu kenan..!!” Ya k’arashe cikin wane irin huci lokaci guda ya mik’e yana furta “Wllhi sai na d’au fansa akan abinda suka mata..! Sai nayi ajalinsu d’aya bayan d’aya koda nima za’a d’auki nawa a matsayina na k’ask’antaccen Bawa..!!” Ya k’arashe cikin wane irin karaji...
Muryar Ubandoma suka sinkaya cikin zuban hawaye yana furta “Kai ba k’ask’antacce bane Ranakaidad’e..! Kai d’in Mai Martaba ne jinin mai Martaba..! Kai d’in D’ah ne ga Sarki AbdulJabbar mai rasuwa kuma mahaifiyarka tana nan a wajen nan tareda Kai...!!!”
K’irajai suka shiga bugawa..!! Gaba d’aya idanu suka koma kan Ubandoma....
SameenaAleeyou 📚
*MUHIBBAH*
*72*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Ubandoma ya d’an tsagaita da kukan da yake ya d’ago ya dubi Gimbiya Turai ya kuma duban Ja’afar wanda su duka biyun hawaye ne Ke gangarowa daga idanunsu ya kuma saita dubansaga Gimbiya Turai ya duk’a gabanta had’ida risinar da kansa “Rankidad’e Jaririn da Giwa ko ince Izzatu ta canza da naki shine jaririn Malam Almu Sarkin Barga... Izzatu itace Ta kashe matar Malam Almu ta kuma kashe jaririn, tazo da da wani jariri rayayye ta canza da jaririn matar Almu, ni....!” Muryarsa ta soma rawa sosai sanda Ja’afar da tuni jikinsa ya soma rawa sosai ya duk’a gaban Ubandoma yana mai furta “Da wani jariri ka canza..! Kayi magana, ka sanar damu wanene jaririn..!!?”
Ubandoma yaci gaba da hawaye yana mai furta “Gaba d’aya cikin laifukan da nayi a baya bisaga umarnin Izzatu babu wanda ya tsaya min a rai irin wannan sabida ya k’unshi jariri wanda baida hakkin kowa... Bansan daga yanda ta samo rayayyen jariri a wancan lokacin ba Ta bani nayi musayen jaririn da na matar Malam Almu wanda tuni tayi tsafi ta kashesu daga shi har uwarsa...!” Ya kuma d’agowa yana duban Ja’afar da Gimbiya Turai kana yaci gaba da fad’in “Rankidad’e wannan jaririn da aka kai miki matsayin naki tabbas ba naki bane kaman yanda Fattu Ta gani kuma ta fad’i maki... Jaririnki yana nan da raye..! Rankidad’e jaririnki ba kowa bane face JA’AFARU..!!!” Ya k’arashe cikin wani irin kuka yana mai zama dirshan a dandamalin k’asa...!
Innalillahi wa inna’ilaihi ilaihi raji’un..! Kalaman da zukatansu Ke iya nanatawa kenan...! Ja’afar da yaji batun a wane irin ba zata d’ago gajiyyayun idanunsa yai yana kuma duban matar da Ubandoma ya gama sanar dasu cewa itace mahaifiyarsa kuma shid’in ba Bawa bane d’ah ne ga Sarki AbdulJabbar mai rasuwa... Giwa itace ta rabasa da mahaifiyarsa ta kuma maidasa Bawa k’ask’antacce a gidan Mahaifinsa... Ya rayu a matsayin Bawa a cikin Masarautarsa..! Shin wannan zalunci da mai yayi kama...!! Sosai jikinsa yake rawa gumi na kuma karyo masa dukda iskan damuna dake hurawa, ji yake kaman numfashinsa na neman d’aukewa ya bar jikinsa.... Bai kuma fahimtar meke faruwa ba saida yaji hannun matar nan tana shafa fuskarsa cikin rawar murya take furta “Kaid’in d’ahna ne..! Tabbas kai
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 48 Chapter of 65