bai iya amsawa ba saima muzurai da yake ci gaba da yi...! Lokaci guda yaci gaba da ‘yan waige waige kana ya had’e hannayensa biyu waje guda yana duban Ubandoma yake furta “Dan Allah.! Dan darajan manzo salallahu alaihi wasallama... Kayi min sutura kaman yanda Allah yayi maka, ka rufa min asiri...!!”
Ubandoma ya kuma murmusawa yana azawa Waziri rawaninsa akai yake furta “Haba Mai Girma Waziri..!!”
Waziri ya katsesa da fad’in “Banida wani girma wllhi..! K’ila ma ka fini girma a halin yanzu..!!”
Ubandoma ya girgiza kai yace “Yau nida nake duk’a maka kaine kake duk’a min Waziri..? Tabbas na yarda da hausan da ake cewa RUWA YA K’AREWA D’AN KADA..! Ruwa ya k’are maku Waziri bakuda wajen guduwa... Watan tonuwan asirinku da duk wani mummunan aiki da kuka jima kunayi cikin Masarautar nan ne ya tsaya...! Shige muje ai bazaka bar cikin Masarautar nan ba sai ka bada shaidar cewa ba Giwa bace Ta haifi Yarima Mahmooda kaman yanda Yarima Yazeed yace..!!” Ya k’arashe yana mai dank’wafo Waziri dake kuma duk’awa yana d’ago hannu yana rok’on Ubandoma ya rufa masa asiri..!
Ubandoma ya shiga janyo Waziri yana furta “Da ka tuna haka tinda wuri ka rufa ma kanka asiri kayi abinda ya dace da bai kawomu ga wannan munzani ba..! Ka sani Waziri kaida kanka ka toni asirin kanka babu wanda ya tona maka asiri..! Shige muje..!!” Ya k’arashe yana mai kuma hankad’o Waziri...
Rik’e gaskiya domin itace take fitar da tsirrai har tayi ‘ya’ya... K’arya fure take bazata Tab’a yin ‘ya’ya har a amfana da ita ba...! Ba’a tab’a cewa gaskiyarka Ta k’are saidai ace k’aryarka Ta k’are... Babu k’ask’antacce sai wanda ya k’ask’antar da kansa... Yau ga Waziri yana duk’awa gaban Bawan da a baya shi yake duk’a masa dan asirinsa ya rufu... Allah ka rabamu da jin kunya duniya da lahira Ameen..!
Cikeda isa da gadara Yazeed ya dakatar da Ja’afar da fad’in “The drama is over kai k’ask’antacce Bawa..! Idan ma banda lalacewa Ta yaya za’a ce Basarake yana rungumar Bawa..! Wannan ya tabbatar da abinda nake fad’i cewa Mahaifiyata ba ita ta haifi Mahmooda ba, shid’in jinin Bauta ne gashi nan kuna gani Bawa d’an uwansa na rungumarsa... Watak’ila sud’in sun had’a jini.. Wannan shine kuke so ya zamto Sarkinku..! Ace Sarki yana rungume rungumen bayi..?! Wace masarauta ce kuka tab’a ganin anyi haka..! Lallai lalacewa yakai lalacewa..! Har abada jinin Bauta bazai tab’a mulkanmu ba..!” Ya k’arashe yana fidda huci...
Daidai nan Ja’afar da idanunsa suka gama kad’awa ya juyo ya Yazeed yana takowa gaba garesa cikeda izza da isa shima wanda sam baisan yanada irinta ba, nan yake furta “Tabbas kayi gaskiya mud’in ‘yan uwan juna ne wanda suka fito ciki guda..! Tabbas kayi gaskiya shid’in bai fito daga tsatson mahaifiyarka ba ..! Tabbas kayi gaskiya jinin Bauta bazai tab’a mulkin Masarautar nan ba..! Wanda hakan ya tabbar da kaid’in har abada bazaka tab’a d’ale Karagar mulkin gidan nan ba a matsayinka na D’AN BAIWA..!!” Ya k’arashe yana mai matso da fuskarsa dab na Yazeed zuciyarsa naci gaba da wane irin tafarfasa...!!
Yazeed d’inma da wasu irin idanu yake duban Ja’afar d’in yana jin inama yanada hannuwa ya shak’o wuyan wannan bawa ya saka sa a yanda ya kamacesa..!!
Cikin tsananin huci Yazeed Ke furta “Kai k’ask’antacce Bawa..! Wa ya baka daman ka gaya min maganganu haka..! Kai har ka isa ka kira Mahaifiyata da Baiwa.. K’ask’antacce kaman Kai..!!!”
Muryar Ubandoma Yazeed ya sinkaya yana fad’in “Waziri shi zai tabbatar da abinda Yarima Ja’afar yake fad’i..!!”
Gaba d’aya mutanen dake wajen suka shiga juya sunan da Ubandoma ya kirawo Jafar dashi.. Yarima Ja’afar..! Yarima Ja’afar dai..! Shin yaushe Ja’afar ya zamto Yarima..? A Iya sanin kowa JA’AFARU D’an Bawa ne wanda bai gaji komai ba sai Bauta toh a ina ya samo title d’in ‘ya’yan Saraki..!!
Da tsananin mamaki Yazeed yai k’ok’arin kaikaitowa yana duban Ubandoma dake tafe tareda Waziri wanda ko d’aga Kai baiyi..!
Shikam Mahmood badon Allah ya taimaka yanada k’arfin zuciya ba tabbas da tuni ya silale k’asa sumamme da irin abubuwan da yake gani suna faruwa gaba gareshi wanda yafi kamanceceniya da ire iren mafarkan da yake..!
Yazeed ya dubi Ubandoma ya dubi Waziri..! Ubandoma ya kuma duba yace “Kai k’ask’antacce Bawa..! Ka kuwa San abinda kake fad’i..?!!”
Ubandoma ya risina gaban Yazeed yace “K’warai Rankaidad’e abinda nake fad’i gaskiya ne..! Mai girma Waziri shi ne zai bada shaida..!!!”
Wane irin k’asaitaccen murmushi Yazeed yayi ya dubi Waziri yace “Waziri inaso ka k’aryata wad’annan mak’aryatan a bainal jama’a..! Ina so ka bud’e baki ka bada shaidar cewa Mahmood d’an Baiwa ce bai gaji sarauta ba..! Domin kuwa D’an Bawa baya sarauta..!! Ina so ka bud’e bakinka Waziri ka sanar da d’aukacin ahalin Masarauta yanda Hadimar Mahaifiyata Ta yaudari Mai Martaba ya fad’a tarkonta har Ta haifo masa d’ansa Mahmood..!!”
Shidai Waziri banda rawa babu abinda jikinsa keyi, ga wane irin gumi dake tsartsafo masa babu k’akk’autawa..! Gaba d’aya saima silalewa saman gwiwoyinsa da yayi...!
Al’ajabi ya kuma cika mutane, Yazeed ya tsaresa da idanu yana mamakin yanda ya zube k’asa yana mai farawa da neman gafara..!
Lokaci guda Waziri yaci gaba da furta “Nidai amin aikin gafara..! Wllhi sharrin shaid’an ne da kuma sharrin zuciya had’ida rud’in duniya..!!”
A wane irin zuciye Yazeed ya katsesa da fad’in “Kai Old man ba wannan aka tambayeka ba..! Babu wanda yace kayi ma kanka tonan asiri..! Ba asirinka nace ka tona ba..! Asirin Mahmood nace ka tona..! Ka tona asirin Mahmood kowa yasan shid’in d’an Baiwa ce k’ask’antacciya..!!!” Ya k’arashe yana mai shure Waziri da k’afafunsa..!
Waziri da tuni ya ciro rawani ya nad’eta kan hannunsa, cikin rawar murya yake furta “Duk abinda Yarima Jafaru ya fad’i gaskiya ne babu k’arya ko d’aya cikinta..! Dashi da d’an uwansa Yarima Mahmooda Sune ‘ya’yan Sarauniya Turai kuma Giwar Amale ta asali..! Wacce kuka sani a matsayin Sarauniya Turai ba ta gaskiya bace... Hadimarta ce ta sace komai nata, ciki harda mijinta da kuma ‘ya’yanta guda biyu... Yarima Mahmood Ta maidasa nata don ta kashesa a gaba..! K’udirinta shine Bokanta ya sanar da ita cewa duk d’an Sarki da ya soma mulki zai mutu shiyasa Ta dage sai Yarima Mahmood ya soma hawa mulki..! Ta tilasta masa dawowa daga k’asar sifaniya Kawai domin Ta cika burinta akansa..! Shi kuma Ja’afaru Ta canzasa da d’an Bawa Almu, Ja’afaru d’an mai Martaba ne.. A lokacin da ta fahimci Ja’afaru ka iya sanin wani abu sai ta nemi rayuwar Jafaru wanda hakan ya sanyashi guduwa daga Masarautar..!”
Muryar shi na rawa yaci gaba da furta “Mun fahimci Mai Martaba yasan gaskiya duk abubuwan da suka faru dashi sabida wasik’a da muka tsinta wanda matar Mahmood Aliya Ta bar masa, cikin wasik’ar ba komai bane face duk wasu abubuwa da Giwa tayi wanda mahaifiyarta Ta sanar da ita a lokacin da tazo barin duniya..!”
Ya d’ago yana duban Mahmood wanda ya koma tamkar bashi a wajen kana yaci gaba da fad’in “Idan baka mance ba Rankaidad’e, ka kawo ziyara k’asar nan bada jimawa ba aka tura sak’on mutuwar mahaifinka..! A wannan kawo ziyarar da kayi a lokacin Aliya Ta rubuta wannan wasiya fa mai Martaba Wanda Mahaifiyarta da ta kasance Hadima ga mahaifiyarka Gimbiya Turai ta asali itace ta sanar da ita domin kuwa Mahaifiyar tata a gabata komai ya faru duk abubuwan da suka faru da Gimbiya da yanda aka salwantar da ‘ya’yanta...!”
Zuciyar Mahmood taci gaba da bugawa yana tuna tun bayan da suka kawo ziyarar da Waziri yake fad’i bai kuma gane kan Aliya ba har kawo zuwansu sanda Mai Martaba ya rasu wanda a lokacin itama aka tsinci gawarta a d’aki..! Ashe Giwa ce ta kasheta sabida tasan wani dark secret nata..!
Turaki dake jin abin kaman a shirin finafinai, saurin tsayawa a gefensa yayi dan yasan komai ka iya faruwa dudka k’arfin zuciya na abokin nasa..! Abu ne mai matuk’ar tayar da hankali komin k’arfin hali da mutum yakedashi..! Ta yaya za’ace matar da ka girma ka santa matsayin mahaifiya k’arya ta jima tana shera maka tsawon rayuwarka...! Babu komai cikin Rayuwar face k’Arya da zalunci..!! Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un..!!
Muryar Waziri ya sinkaya yana mai ci gaba da furta “A lokacin da kuka Zo k’asar sanda mahaifinka Sarki ya rasu a lokacin Giwa Ta fahimci cewa matarka Aliya ita ta sanar da Mai Martaba ta hanyar ajiye masa wasik’a.. Kuma kaima zata iya sanar dakai shiyasa ta kasheta..!!”
Baikai aya ba yaji sauk’an naushi ta ko ta ina Yazeed dake tsananin kuka yana naushinsa da duka k’afafunsa yake furta “K’arya kake..! Mahaifiyata itace Gimbiya Turai..! K’arya kake Mahaifiyata Gimbiya ce kuma sarauniya ce..!!! Ka bud’e baki kace k’Arya kake Waziri..! Har abada bazan tab’a zama jinin Bauta ba..! K’arya kake Waziri..!!”
Waziri na hawaye yake furta “Gaskiyar kenan Yazeed Mahaifiyarka Baiwa ce datayi k’wace da fin k’arfiwa Uwargijiyarta wacce ta aminta da ita bata kuma nufeta da komai ba face alkhairi..! Mahaifiyarka butulu ce mai saka alkhairi da sharri..!!”
Yazeed dake cazgan kuka ya kuma kai masa naushi yana furta “K’arya kake mak’aryaci..! Babu wanda zai yarda da kalamanka sabida kaid’in maci amana ne kuma mayaudari..! Kaci amanan abokinka Sarki AbdulJabbar ka nemi Mahaifiyata da aurensa akanta.. Wazai yarda da kalamanka..!!”
Cikin kuka Waziri ya katsesa da fad’in “Banci amanan Abokina ba..! Mahaifiyarka babu aurensa akanta, bai aureta ba makircinta kawai tayi Ta rabasa da matarsa da ‘ya’yansa Ta haukatar da ita.. Kai a Naka tunanin Yazeed matar Sarki zatabi wani namijin ne..! Mahaifiyarka ba matar Sarki bace Baiwa ce k’ask’antacciya wacce ni nai mata sutura cikin Masarautar nan har Ta haifoka gudan jinina Ta kuma dangantaka ga Sarki AbdulJabbar..! Badon ni ba da bata haifoka ma Sarki ba..!!”
Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un..! Wad’annan bayin Allah haka sukayita kwance ma kansu zannuwa a kasuwa, sunzo wajen domin su kwancewa Mahmood zani a kasuwa su sanyashi yaji kunyar duniya sai gashi reshe ta juya da mujiya sai bankad’o asirai suke Wanda suka jima a bisne babu wanda yasan dasu saiko su sai mahaliccinsu... wannan rayuwa da mai yayi kama..! Shuka kirki domin ka girba gobenka..!!
Haka aka dinga silalewa a wajen cikeda wane irin Al’ajabi, Yazeed bai daina naushin Waziri yana fad’in har abada bazai tab’a zama mahaifinsa ba shid’in d’an Sarki AbdulJabbar ne..!
Raheemah da Gimbiya Zeenat sukaga tashin hankalin da yafi k’arfinsu, sosai Raheema Ke kuka tana fad’in Ta cuci kanta ta zalunci kanta, Tabbas Zina babban laifi ne wanda tin daga duniya zai kaika ga k’ask’anci, dukda kasancewarta d’iyar masu mulki gashi zina ya janyo mata Ta auri mutumin da aka haifesa ba Ta hanyar aure ba sannan kuma ba d’an sarauta ba d’an k’ask’antacciyar Baiwa maciya amana..! Laifin zina duk shine ya janyo mata wannan k’ask’anci da tozarci a rayuwa, yau ko da wanann tashin hankali aka barta tana cikin tsaka mai wuya, a duniya kenan balle ka isa masauk’i na har abada lahira..! Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un..! Ya Allah kai mana katangar k’arfe da manyan alkaba’irai harma da k’ananan wanda bazasu kai mutum ga komai ba face halak’a..!
Ja’afar ya isa gaban Yazeed da Waziri yanda suke zube a k’asa Yazeed na kuma tsinewa mahaifinsa Waziri albarka su duka biyun suna kuka suna nadamar rayuwa..!
Ja’afar ya dubesu gaba d’aya sai kuma ya dubi Waziri yace “Dukda laifukan da ka aikata bazanso asirinka ya bankad’u haka a idon duniyaba amma saidai ka sani daga cikin sharrin zina da illolin Sa yana janyo jin kunya da zubar da mutunci tin daga duniya har izuwa lahira..! Da wannan kawai aka barka ya isheka hukuncin duniya Waziri..
Ya kuma maida dubansaga Yazeed yace “Toh Yarima Yazeed ko ince Bawa d’an Baiwa Yazeed..! K’arshen tikatiki tik Inji masu iya magana..! Yau gaka nan a k’asa dani kana duk’e gabana, babu hannuwa babu mulki babu sarauta babu asali balle Tushe..! Babu babunka sunyi yawa Yazeed..! Ka sani Allah shi yake bada mulki ga wanda yaso ya kuma hana wanda yaso..! Bayan duk kalan abubuwan da mahaifiyarka ta aikata dan ta tarwatsa mahaifiyarmu da zuri’arta tayi iya k’ok’arinta wajen ganin Ta fitar dani da d’an uwana daga gidan mahaifinmu da sarautar da take gadonmu ne yau gashi nata ahalin sune suka tozarta..! Babu komai a cikin tsananin son mulki face halak’a..!”
Ya d’an tsagaita sai ya kuma duk’awa saitin kunnen Yazeed yake furta “Kai k’ask’antacce Bawa, namu dakai bata k’are ba bari duk wata k’ura Ta lafa..! Yarima zai kuma waiwayanka..!!” Ya k’arashe yana mai sakin murmushi saman fuskar Yazeed dake zuban hawaye..!
Ya dubi Waziri a hankali yace “Baba Kwarto ashe anko kukayi da d’an Naka shima d’in wani k’Aton Kwarto ne mai danne ‘ya’yan mutane aje gida a masa tarbiya akwai ‘ya’yan bayi cikin Masarautar nan, Masarautar bazata lamunci mummunan d’abi’a irin wannan daga d’aya cikin Bayinta ba..!” Ya k’arashe yana mai had’e girnsa had’ida tsimewa sosai wanda tuni yasa Waziri soma jinjina kai yana mai ci gaba da matsan k’walla..!
Ya mik’e yana gyara rigarsa Ta sarauta had’ida daidaita tsayuwarsa...
Har ya soma tafiya ya juyo ya dubi Dakarun dake gefe yace su kame Waziri su rufe a nan fursunan cikin Masarauta dan sai yazo ya sanar dashi yanda akai ya kashe mahaifinsa Sarki in details..!
Dakaru suka risina suna furta “An gama Rankaidad’e Yarima..!!”
Suka k’arashe suna masu tattaro Waziri dake faman magiya yana Baiwa Yarima Ja’afar hak’uri...
Yazeed dake duk’e wajen bayan Ja’afar yabi da kallo Hawaye na kuma gangaro masa yana tuna babu irin cin kashin da baiyiwa Ja’afar d’in ba a matsayinsa na d’an Sarki wanda Ja’afar d’in Ke k’asansa, yau sai gashi Wai Ja’afar shine a sama dashi shine suka canza title shi ya koma Bawa wanda yake k’asa da J’afar yayinda Ja’afar d’in ya Koma jinin Saraki wanda yake sama dashi..! Da rarrafe Yazeed yake k’ok’arin mik’ewa yana huci yana dararawa bayin dake tsaye wajen suna kallonsa tsawa..!
Bawa guda ya bud’e murya yace “Kai billahillazim idan ka kuma zaginmu zakaji a jikinka dan damu da kai babu banbanci, kai gwara mu ma da aure aka haifo mu..! Duk fad’in Masarautar nan babu wulak’antaccen Bawa irinka dan haka kana kuma cewa fit wllhi zamu tara maka na gajiyya mu k’arasa karya sauran k’afafunka..! Tashi ka b’ace mana a nan kafin mu k’arasa ka..!!”
Yazeed ya soma jada baya ganin gungun bayin na yunk’urin nufosa..! Cikin wane irin tashin hankali ya nufi b’angarensa wanda bai tab’a tsintar kansa ciki ba tsawon rayuwarsa..!
**
Zahra da har wannan lokaci bata dawo hayyacinta ba kwance take zazzabi na neman rufeta, Umaima wacce itama k’arfin hali kurum take itace a gefen Zahran tana kula da ita.. Bacci har ya soma d’aikam Zahra Ta farka a firgice tana ambaton sunan Muhibbah da k’arfin gaske, mafarki take Jamal na binsu itada Muhibbah, suna gudu ya kama Muhibbah dake ambata mata sunan takarda da yaren Spanish..!
Take ta nanata sunan takardan a fili “Papel..!!” Ta shiga tuno kalaman Muhibbah a gareta cewa Ta baiwa Paa d’inta Takardun data d’auka cikin rigarta..!
Babu shiri Zahra Ta zira hannu cikin rigarta Ta ciro takardun wanda har sun soma d’an diddigewa sabida damshin ruwa da ya tab’a su...
Juya takardun ta shigayi tana duban Umaima take fad’in “Paa..! I need to give this to Paa..! I need to go Paa right now..!!” Bata kuma tsayawa sauraren Umaima ba Ta fice a guje tana neman Mahaifinta, Umaima na d’ingisawa take k’ok’arin bin bayanta saidai bazata iya ba sabida gurd’a mata k’afa da Jamal sabida d’aureta da yayi Ta jima a d’aure.. Haka Ta koma ta zauna da k’yar tana kame k’afarta...
Zahra kaw tuni ta fantsama Masarauta a guje...!
**
A hankali Mahmood Ke takowa yanda take zaune Ta bada baya tana duban fad’in Masarautar da irin rayuwar da tayi ciki... Al’amarin mahaifiya ya wuce wasa, tabbas shiyasa yaji wani al’amari mai girma a tattareda matar sanda suka soma had’uwa a lokacin tana cikin halin hauka wanda Giwa tai sanadiyar kasancewarta ciki..! Rauni sosai ya bayyana tattare dashi, dole ma yaji rauni domin kuwa mahaifiya ba abin wasa bace..! Tsawon rayuwarsa yayi ne yana yima wancan azzalumar matar biyayya.. Ashe ba itace Ta haifesa ba rabasa tayi da mahaifiyarsa..! Ko mai zai ma Giwa baijin zai huce domin kuwa Ta masa abubuwa da dama wanda duniyar nan tayi kad’an yace zai rama a cikinta saidai ya barwa wanda ya haliccesa ya kuma hicceta yayi hukunci tsakaninsu domin shi kad’ai ne zai iya hukunci ma wannan azzalumar matar wacce babu d’igon imani ko rahama cikin zuciyarta..!
Ya duk’a a hankali gijif saitin k’afafunta yana jin wani irin kuka mai k’arfin gaske na zuwa masa..! A hankali ya saka yatsun hannunsa yana shafa yatsun k’afafunta dasu.. Hawayensa na d’iga saman k’afafun nata..! Baisan sanda ya kifa fuskarsa saman k’afafun nata yana kuka sosai..! Itama kukan take tana dafe dashi..!!
Ta kasa aminta shid’in d’anta na fari ne data rasa tsawon shekaru... Su duka biyun babu mai iya cewa komai sai kukan rahama da suke, hak’ik’a Ubangijinsu ya cika rahamarsa a garesu, bayan d’ebe tsammani na tsawon shekaru yau sai gashi ya kuma had’e fuskokinsu matsayin d’ah da uwa..! Allahu Akbar komai yayi tsanani yana tare da sauk’i, duk tsananin da ka tsinci kanka ciki, kada ka karaya, ka yarda da Ubangijinka kayi imani cewa zai kawo maka sauk’i...!
Hannayenta na rawa ta d’ago fuskarsa dake jik’e sharkaf da hawaye wanda ya rine zuwa ja sabida tsananin kuka..!
Turaki da Ansar dake gefe guda suna kallon wannan kayan Farin ciki da Al’ajabi duban juna sukai had’ida sakar ma juna murmushi lokaci guda Turaki na labartawa Ansar d’in wanene Mahmood, d’abi’unsa tsakanin mutane kama daga ahalinsa har zuwa al’ummarsa..!
Ansar na duban reunion d’in Mahmood da mahaifiyarsa yake furta “Ban tab’a cin karo da labari irin na wad’Annan bayin Allah ba..! Hak’ik’a an masu zalunci mafi muni a doron k’asa..! Daga k’arshe Allah ya kuma had’e fuskokinsu.. Sun cancanci farin ciki a sauran rayuwar da Ta rage garesu..!!”
Turaki ya jinjina kai a hankali yana mai furta “Wannan haka ne..!”
Ubandoma ne ya k’araso yana kuma sanar dasu yanda al’Amara suka kasance..! Nan su Turaki ma Ke sanar dashi yanda al’amaran suke a Masarauta, sosai hankalin Ubandoma ya tashi jin Muhibbah na hannun Giwa, ya tuna sanda suka rabu tai masu sallama..! Tabbas idan Giwa ta gane itace Saudatu bazata barta da rai ba...! Hankali tashe yake tambayar su Turaki ina ake zaton Giwa takai Muhibbah..!
Turaki yace ai babu irin neman da basuyi ba cikin Masarautar, har dai Sun soma tunanin ko ta fice da ita daga cikin Masarautar ne..!
Ubandoma ya nusa kaman mai tunani sai kuma ya girgiza kai yace “Giwa bazata tab’a fitar da Saudatu daga cikin Masarautar nan ba, ita d’in ta jima da k’udirin tsafi akan yarinyar..!”
Turaki da Ansar suka dubi juna suka kuma duban Ubandoma cikeda mamaki lokaci guda suka maida dubansu gaba d’aya ga su Mahmood..
Hannayen Mahmood ta shiga warwarewa kaman tana neman wani abu, nan tsakanin yatsun hannunsa na dama ta hango irin alaman dake nata hannu Wanda ashe shima yanada irinta, take ta ware hannunta itama Ta jera da nasa hannun, alaman tabon ya bayyana saman tafukan hannayensu, su duka biyu sukai K’uri suna duban irin alama guda da Allah ya halitta masu, ko shakka babu su d’in d’ah ne da mahaifiya..! Wani sabon kuka ya kufce mata.. Take Ta rungume d’anta tana kuka sosai..! J’afar da k’arasowar kenan shika cikin tsananin sanyin jiki ya isa ya rungumesu gaba d’aya..! Su duka ukun suka rungume junansu kaman masu tsoron kada a kuma raba tsakaninsu.. Sosai suke kuka mai ban tausayi da tab’a zuciyar duk wani mai imani...
Dattijo Baba Nomau dake zaune daga gefe shima saida ya kamo bakin babbar rigarsa yana tsane k’wallan da suka gangaro masa..!
Toh daga nan fah bayan wanann ya lafa aka sako batun neman Muhibbah..!
Yasu yasu ne zaune k’asan Rumfar yanda suke tattauna ta inda zasu b’ullowa al’amarin tinda an bincika ko ina ba’a sami su Giwa ba..!
Gimbiya Turai ta dubi Mahmood tace “Izzatu bazata tab’a fitar da Saudatu daga cikin Masarautar nan ba, domin kaman yanda na baku labari ita d’in ta jima da k’udirin yin tsafi da d’iyar d’an uwana..! Amma saidai akwai abinda nake tunani shine zai kaimu ga yanda Izzatu Takai Saudah..!”
Mahmood ya d’ago a firgice yana dubanta duk ya jigata a d’an tsawon yini guda da wannan al’amari Ke faruwa..!
Gimbiya taci gaba da fad’in “Wambai ya bani wani Taswira yace na adana shine zai toni asirin Izzatu duk daren dad’ewa..! Kuma na baiwa Saudah wannan Taswiran..!!”
Zuciyar Mahmood bata daina bugawa ba yake tuno abubuwan da suka faru... Sai yanzu zanen ginin gidan sarauta da Wambai ya basa da kuma wanda ya tsinta hannun Muhibbah ya fad’o masa..! Ya mik’e babu shiri yana furta “Nasan yanda Taswiran suke nima Wambai ya bai guda d’aya kafin ya bar duniya..! Amma fallen zanen guda uku ne.. Bazamu iya gane inda zanen ya dosa ba da abinda yake nufi sai mun cika guda ukun... Ina zuwa..!!” Bai kuma tsayawa sauraren kowa ba ya shiga cikin sassarfa ya nufi d’akin da aka aje Muhibbah..! Saidai babu zanen babu dalilinsu..!
Hankali tashe ya dawo ya sanar dasu babu zanen bai gansu ba...!!
Kaman daga sama ya sinkayo muryar Zahra ta nufosa a guje tana ambatonsa.. Ya waigo yana dubanta, bata daina haki ba take mik’a masa Takardun dake hannunta, lokaci guda take furta “Paa Aunty Muhibbah tace na baka wannan..!!”
Cikin sauri Mahmood ya amshi takardun, jikinsa har na rawa yake warwaresu..! Ga tsananin mamakinsa Map d’in nan ne mai d’aukeda wani irin rikitaccen zane..! Ya d’ago yana dubansu kana yace “Gashi nan..! Alhamdulillah ya zanen nan..!!” Gaba d’aya suka mik’e sanda Mahmood ya k’urawa zanen idanu yana karantarta..! Babu shiri ya nufi saman benensa a guje su Ubandoma dasu Jafar na biye dashi..! Can saman tsauni ya hau ya tsaya yana karantar fad’in Masarautar da kuma zanen..!
Daga can b’angaren hagu daga Masarautar ya hango hanyar da yayi linking wannan Taswira..! Tabbas wani gini ne cikin Masarautar wanda hankalinka da tunaninka bazai baka akwai wani mihimmin abu wajen ba, anyi amfani da wad’anda sukeda ilimin sanin gini na zamanin da sai aka b’atar da ginin cikin ado da kwalliya wanda zakayi zaton ginin kwalliya ce kawai ga Masarautar..! Babu shiri ya nufo k’asa suka kuma biyo bayansa har saida ya tsaya gaban wannan ginin... Ya isa yana shafawa a hankali yana mai kuma bin diddigin zanen..! A daidai center ya hangi wani alamu kaman shatin kwbo wanda akai masa ado a tsakiyarsa da alamun tambarin masarauatr su..!
Ya saka hannunsa yana shafe shatin kwabon..! Baba Nomau da yayi masa k’uri tamkar mai nazari ya bud’e muryarsa da girma ya kama yace “Akwai wani sirrin k’unshe da wannan alama..! Mutanen zamanin da sun yarda da alama musamman mai d’aukeda tambari irin wannan na sarauta..!
Muryar Ubandoma da shima yayi nisa cikin zurfin tunani suka sinkaya yana fad’in “Mahaifina ya bani wani labari cewa akwai wani fursuna da aka ginata shekaru d’aruruka, tin zamanin wani Sarki can da jimawa..! Wannan fursunan ba’a tab’a rufe kowa cikinta ba ko shi Sarkin da ya ginata, ko wani sarki yakanyi zamaninsa ya shud’e ba tare da ya bud’e wannna fursunan ba, kuma ko wani Sarki kafin ya bar duniya yakan barwa Babban d’ansa mabud’in wannan bak’in fursunan... Kenan mahaifin Sarki AbdulJabbar bai barwa Sarki AbdulJabbar mabud’in wannan fursunan ba ya bar mabud’in hannun babban D’ansa Wambai tinda dama ko wani Sarki ma babban d’ansa yake barin mabud’in..! Kuma wannan fursunan Tanada mabud’i ne guda d’aya tak a duniya..!!”
Ya d’anyi fasali kaman mai tunani sai kuma yaci gaba da fad’in “Lokacin da hankalin Giwa ya tashi na neman wanene Bak’on Buzu da yake ziyartan gidan Wambai Tabbas naji tana maganan neman wani k’undi daga hannun Wambai wanda shine dalilin da yasa na zaga na shiga gidan Wambai Dan na samo wannan k’undi ganin irin mahimmancin da yake dashi a wajen Giwa..! Na tabbata wannan k’undin yanada alak’a da wannan zanen..!!”
Ai Ubandoma bai gama rufe baki ba Mahmood ya soma jada baya yana furta “Tabbas ni ne Bak’on Buzu, na b’atar da kama ne domin na samo amsoshin da na dawo k’Asar nan ina nemansu kuma Tabbas Wambai ya bada Bak’on Buzu wani k’undi wanda yace akwai lokacin da zan buk’aci bud’e wannan k’undin..! Tabbas mabud’in wannan Taswira yana cikin k’undin da Wambai ya bani..!!”
Daga haka ya nufi d’ajinsu a guje Dan d’auko k’undin da Wambai ya damk’a masa...
*MUHIBBAH*
*76*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Sharkaf Ta jik’e da gumi tana duban Giwa tana girgiza kai hawaye suna ci
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 52 Chapter of 65