Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kuwa kasan mai ka aikata..!!?” Rai b’ace shima yake fad’in “A gabana kike waya da wani k’aton banza... You know what Hibbah.? I was such a jerk da na yarda miki Ki tafi kiyi rayuwa cikin Masarautar nan in the first place... I shouldn’t have allowed you to go back to that place..!!” Katsesa tai da fad’in “And you think you can actually stop me now...? Well no, bazaka iya hanani ba...Those people turned my life into a nightmare, thay took everything away from me, basu cancanci rayuwa cikin Farin ciki ba... Gaba d’ayansu basu cancanci rayuwa cikin kwanciyan hankali ba... I promised to take them down, even if it will cost me my life, wllhi sai na d’aid’aitasu...!” Ta k’arashe hawayen k’unan rai na gangaro mata... Lokaci guda Ta koma ta zauna cikin kujeran tana mai ci gaba da kuka maras sauti.... Ansar ya fuzar da fuci kad’an kana yan janyo kujeran ya zauna shima “Hibbah that too much resentment dake kwance cikin k’irjinki bazai haifar miki da komai ba face tarin dana sani... And do you know what’s worse..?, na tabbata gaba d’aya idanun Princes d’in akanki yake... Hibbah mai kike tinanin zanji...? Do you think this is fair for our relationship..? Please try to be a little bit considerate Hibbah...Zuciya batada k’ashi, kuma ita soyayya batasan sanda take shiga ba... What if you ended up falling in love with one of those princes..?” Da tsananin mamaki ta d’ago idanuwanta masu zuban hawaye tana dubansa, lokaci guda take girgiza cikin rashin yarda da abinda kunnuwanta Ke jiyo mata, murmushin takaici mai tsananin ciwo saman fuskarta take furta “Bayan dik abubuwan dana sanar dakai har kana tinanin ni Muhibbah zan afka soyayya da d’aya daga cikin mutanen dana fi tsana sama da komai a duniyar nan, mutanen da sukai jagoranci wajen ruguza rayuwata data ahalina... Ansar ban tsamman zanji haka daga gareka... Na zaci zakafi kowa fahimtata...” Batakai aya ba ya katseta da fad’in “Muhibbah abinda nake gani ne... Jiba fah kiga yanda kike waya da wannan d’an Sarkin kama wasu masoyan gaske..!” Wannan karon mik’ewa tai cikeda b’acin rai, ta dakatar dashi da fad’in “Cut the crap..! Ka kuwa San mai kake fad’i Ansar... Ni kake had’awa da wad’ann mutanen...?” Ta k’arashe hawaye na kuma gangaro mata.... D’an fuzar da fuci ya kumayi kana yace “I’m sorry Hibbah, please forgive me.... Hankalina bai kwance ne muddin kina taredasu...!” Hannu tasa Ta goge hawayen cikin zafin rai take fad’in “This should be the last time da zaka had’ani da wad’annan disgusting creatures din...!” Ansar ya jinjina kai a hankali yana mai furta “Bazan sake ba Muhibbah... So tell me mai da mai kika fahimta zuwa yanzu... How far have you gone..?” Zama tai cikin kujera had’ida k’urama waje guda idanu lokaci guda ta saki murmushi a hankali kana Ta soma furta “Dukansu da kake gani na karanci weakness d’insu, kuma dashi zanyi ruining d’insu.... Fu’ad da kaji muna waya dashi, a nashi haukan ya fad’a soyayya dani, wannan mahaukacin his weakness is his insecurity... Zanyi amfani da wannan daman to toy with his emotion and watch him crumble... Shi kuma Yazeed..!” Tai murmushi a hankali kana tace “Na riga dana fara bashi... His pride, son mulki had’ida son mata shi zai kaishi k’asa warwas, I’ll use that to ruin his marriage and make him look like a loser...And Yarima Mahmood...!” Ta d’an murmusa kad’an kana taci gaba da fad’in “His daughter will be his own downfall... Zanyi amfani da ita to bring him down... Guda d’aya daga cikinsu shine har yau ban fahimci ko shi d’in wane irin mutum bane.. Yanada wahalan fasaltuwa, yafi kamanni da hawainiya mai canza kala, mutum ne da baka fahimtar gabansa ko bayansa balle ka gane ina ya dosa... Amma daga yanda tinana ke bani shid’in yafi kusanci da mahaifiyarsu.. Idan nayi nasaran d’aid’aita masa rayuwa ko shakka babu kaman na cakkawa Turai wuk’a ne a k’ahon zuciyarta... Sannan idan nai nasaran d’aid’aita rayuwar Turai kaman na cakkawa Jamal wuk’a ne a k’ok’on zuciyarsa... Su biyu d’in suna tafiya kafad’a da kafad’a ne... Kaga koda ace banyi nasaran karantar Jamal ba ruguza Mulkin Giwa da yaranta daidai yake da ruguza Giwa da d’anta Jamal...!” Ta k’arashe tana mai kuma sakin murmushi... Fuzar da fuci a hankali Ansar yai yana mai murza tafukan hannunsa kana yace “Must you really have to involve Mahmood’s daughter.. I mean she’s an innocent kid, she had nothing to do with what her father did in the past....Laifin na mahaifinta ne ba nata ba, karkizo kiyi abinda later on you will regret doing it..!” Ya k’arashe cikeda kulawa... Shiru tai tamkar mai tinani kana Ta fuzar da fuci a hankali lokaci guda taci gaba da fad’in “Ni kaina banso Zahra Ta shigo cikin shirin fansa na sabida yarinya ce mai hankali da kuma hangen nesa, Yanda kasan ba zuri’ar Sarki AbdulJabbar ba... But nasan abinda nakeyi, bazan bari Ta cutu ba... From what I learnt, her father’s been lying to her, he’s hiding something from her... Something very serious, Ina tsamman ya shafi mutuwar mahaifiyarta... Zan saka mata kokonto da shakkun mahaifinta cikin zuciyarta, after all dama shid’in mutumin banza ne, bai cancanci zama mahaifin Zahra ba...!” Ta k’arashe tana sakin huci... Ansar yai shiru kaman mai tinani kana yace “This is a very delicate matter Hibbah, we are talking about an innocent child here...Make sure she doesn’t get hurt..!” Fuzar da fuci tai a hankali tana mai dubansa damuwa k’arara saman fuskarta kana tace “Believe me sabon kwanaki kad’an da nai da ita I become very fond of her, bazan bari ta cutu ba da izinin Allah...!”Ta k’arashe damuwa kwance saman fuskarta... Mik’ewa tsaye Ansar yai yana mai furta “Bana fatan kiyi abinda zakizo kina dana sanine Muhibbah... Kodashike Na yarda dake... And I know you’re a good person, nasan dik abinda kikeyi saida kikayi tinani sosai ... And addu’ata da soyayyata na tareda Ke ko yaushe... I hope everything will soon come to an end, so that we can finally get the chance to be together... Forever..!” Ya k’arashe cikeda kulawa... Murmushi ta sakar masa cikeda tausayinsa kana tace “In sha Allah My Dr...!” Ya murmusa kad’an shima kana ya duba agogon dake d’aure hannunsa na hagu yace “Zanje asibit kafin la’asar zan dawo sai na shirya... Is it okay with you..?” Murmusawa tai a hankali kana tace “Sure... Take your time Likita, nima zan shige Kitchen ne na taya Larai da wasu aikace aikacen...” Lokaci guda take d’an masa waving tana fad’in a dawo lafia.. Tsaye yai hannayensa sakale cikin aljihun wando yana dubanta har Ta shige kana ya fuzar da fuci a hankali ya nufi ma’ajiyar motarsa... *** Suna tafe a hanyar komawa Jos take labartawa Ansar abinda ta gani gameda mahaukaciyar da suka soma arangama da ita farkon zuwansu Masarautar... Shima sosai yaji mamakin wannan lamari had’ida kuma tabbatarwa lallai akwai abubuwan dake b’oye cikin wannan masarauta, kuma idan har Muhibbah zata zamto silan warwarewan wasu al’amara a Masarautar tabbas now more than ever bazai hanata ba dan wannan dangin jihadi ne saidaima yaci gaba da mata add’uan samun nasara.... Nan take kuma tabbatar masa hakan ya nuna k’ila tabbas mahaifinta na nan raye cikin Masarautar, k’ila Giwa bata kashesa ba, k’ila Yana nan raye tanai masa uk’uba kaman yanda takeyiwa mahaukaciyar nan... And now more than ever bazata janye k’udirnta ba har sai ta ceto mahaifinta da duk wani rai da ahalin AbdulJabbar ke zalinta.... Yamma lis goshin magrib suka iso Masarautar saidai Ansar bai shiga ba hasalima daga cen nesa da ginin masarautar ya ijiyeta kana ya shige masauk’i da zummar Washe gari da sassafe idan Allah yakai rai zai d’auki hanyar gida... ** MASARAUTA Zaune suke a hamshak’in parlorn na alfarma... Raheema an ci gayu cikin kaya na mulki da sarauta, kan nan a k’asa yawa mutuniyar arziki, sai faman sakin murmushin yak’e take, itafa wannan yarinyar tasa mugun shiga hakkinta take, tama kula tsaban Mahmood baison kasancewa da ita dik randa zasuyi zance dole Zahra na wajen.. Ta lura da biyu yake barin d’iyar tasa Ta kasance wajen tsaban baison keb’ewa da ita.... Kuma shi ba komai yake ce mata a hiran ba saidai tayita faman sakin murmushin k’arya a barta da ciwon kumatu tinda murmushin na dole take... Ta gaji ta gaji da wannan shegiyar d’iyar tasa da tai mata k’ebebe a mak’ogoro take neman Ta hanata rawar gaban hantsi.... Ga wani uban sakalta yarinyar da yakeyi saikace kansa aka fara haihuwa... Shi ko irin hallayan gidan sarautar nan ma baiyi yanda masu sarauta Ke son yara maza Dan su zamto magadansu amma shi kacaukam hankalinsa kan wannan yarinyar...Kodashike dan yaga baida wasu yaran ne sai ita, da zaran ta shiga gidansa ta haifa masa yara maza ‘yan tagwayen zai mance wannan tsinanniyar yarinyar ya watsar da tashanta, sannan ya koma yayinta itada yaranta da zata haifa masa...! Ta k’arashe tinanin nata tana sakin murmushin cin nasara.... Tana tsaka da murmushin ne taga Zahra ta mik’e ta nufi cen bayan parlorn tana k’ok’arin amsa waya.. Umaima ce mai kiran nata “Seriously Aunty Umaima... Tia ta dawo, please kice mata Ta k’araso sashen Paa d’ina Ina cen Ina jiranta.. Please please kar tace no...And tell her Zanyi fushi yanzu kam idan tak’i amsar gayyatana..!” Bata jira amsar Umaima ba ta katse kiran dan tasan Muhibbah na iya cewa bazata ba kaman yanda tai mata jiya da safe na maganan breakfast... Tana ida wayar ta juyo ta komo cikin parlorn,tana duban Babanta take fad’i cikin harshen Spanish “Paa este lugar es aburrido..Por eso le pedí a la tia que viniera... Espero que no te importe Paa (Wajen nan babu dad’i Paa, is kind of boring.. Shisa nace Tia tazo... I hope you don’t mind Paa) K’asaitaccen murmushi ya sakar mata kana shima ya amsa cikin harshen spanish “Cualquier cosa por mi princesa..” (Duk abinda Gimbiyata take so) Itadai Raheema sai dubansu take tana faman ci gaba da murmushin yak’e dan bama tasan mai suke fad’i ba.... Lokaci guda ta d’an gyara zamanta cikeda k’issa kana Ta dubi Zahra tace “Daughter nima dai za’a koya min Spanish d’in nan yanda nan gaba za’ake tattaunawar dani...!” Murmushin da yafi kama da yak’e Zahra tai kana tace “Sí Señora, I don’t have problem with that..!” Raheema ta kuma sakin murmushin yak’e kana tace “Toh yanzu dai a fassara min mai Daughter da Paa suka tattauna..” Murmusawan Zahra Ta kumayi dan already Mahmood ya tashi daga parlorn ya shige wani k’ofan yana amsa kiran Turaki Zahra Ta d’an gyara zamanta kana tace “Pronto lo verás con tus ojos” Raheema Ta kuma yin yak’e kana tace “Ai kin kuma shigar dani duhu daughter...!” Murmusawa Zahra tai kad’an kana tace “Cewa nai da sannu idanunki zasu gane miki...!” Raheema Ta kuma sakin murmushi kana tace “Oh I guess babban surprise za’a min...!” Zahra Ta murmusa da gefen baki kana tace “Créeme uno muy grande” (Ki yarda dani, Babba ma kuwa)... Raheema Ta kuma sakin murmushi cikeda jin dad’in babban surprise d’in da Zahra zatai mata, watak’ila Zahra ta fara sonta da mahaifinta ne... Ta kuma sakin murmushi tana mai gyara zamanta, lokaci guda tana mai kuma initiating fira tsakaninsu da Zahra... ** Muhibbah ta dubi Umaima tana mai girgiza kai “What..! No gaskiya ni bazanje sashen Yarima Mahmood ba, mai kike tinanin za’a d’auken a Masarautar nan... Zahra yarinya ce bazata fahimci komai ba... Ki k’yale zancenta kawai...” Ta k’arashe tana mai tufke sumarta data ida tajewa cikin ribbon... Umaima ta zauna saman stool kana tace “Babu wanda zai kawo komai, besides Raheema na cen... Kika sani ko da amincewarsu gaba d’aya suke so kije cen... It is not as if kin aikata wani abu maras kyau ne, ga Zahra ga kuma Raheema duka suna cen ba Ke kad’ai bace...” Muhibbah ta kaikaito tana dubanta kana tace “Raheema na cen..?” Jinjina mata kai Umaima tai kana tace “K’warai kuwa...!” Lokaci guda Muhibbah ta juyo tana kuma duban kanta a madubi, ta saki murmushi mai k’unshe da ma’anoni kana ta juyo taceda Umaima “Alright fine... Kunci gari Keda Zahra...!” Umaima ta murmusa cikeda jin dad’i kana tace “Yauwa ko ke fah, maza tashi tashi ki shirya.. I’ll help you get ready....” Take Umaima ta tayata shiryawa cikin kaya na alfarma, dikda babu wani kwalliya saman fuskrta tayi kyau har ta gaji... Umaima tai mata K’uri kana tace “Inama ku had’uda Prince F a hanya sai ya kusan sumewa ina fad’i maki.... Hararan wasa Muhibbah Ta aika mata kana tace “Kedai kinji dashi.. Must I have to wear all this...? Ni fah ba d’iyar Saraki bace....” Umaima na kuma sakin murmushi take fad’in “Soon zaki zama matar Saraki, so better get used to it...” Muhibbah ta girgiza kai a hankali kana tace “Au har kin yanke...?” Umaima Ta jinjina kai tace “K’warai kuwa d’an sarki ma Sarki ne...!” D’an murmusawa sukai gaba d’aya a tare kana suka nufo k’ofa.... Suna isowa k’ofar Yarima Mahmood Umaima ta juya tana fad’in “Ai Ke kad’ai zaki shige dan ni ba’a bani izinin shigowa ba...!” Muhibbah ta dubeta baki sake kana tace “Wai da gaske kike..?” Umaima ta d’aga mata gira tana fad’in “Sosai kuwa... A fito lafiya Rankishi dad’e..!” Tana ida fad’in haka ta juya tana murmushi Sauk’e fuci Muhibbah tai a hankali tana duban k’ofar sashen..... SameenaAleeyou 📚 [6/29, 4:49 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* *025* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Daga yanda yake tsaye ya baiwa k’ofa baya yana fuskantar tanfatsetsen window dake gabansa tai tsaye tana dubansa... Wani irin muguwar fad’uwan gaba taji sanda ta hangi gadon bayan Mahmood, yanda kasan mai laifi yaga wanda yaima laifi hakan nan ta tsinci zuciyarta cikin wannan yanayi... Maiyasa dik sanda ta kasance taredashi takeji wane irin al’amari na daban, maiyasa dik irin tsanar da tai masa yafi k’ullatanta a bayan idanunsa, maiyasa da zaran tai arangama dashi sai ta nemi wannan tsanar ta rasa, sai ta rasa control ta kuma rasa wane irin yanayi ne take tsintar zuciyarta ciki.... Wayar da yakeyi ne ya tafi da hankalinta... Ta d’an lab’ab’e kad’an jikin k’ofar tana sauraron abinda yake fad’i cikin wayar “I can’t be mistaken Turaki, na tabbata naga wannan mutumin, kuma ka sanni I won’t rest har sai na isa k’arshen al’amarin nan.. Dole za’a k’ara tsaro cikin gidan sannan za’ai installing CCTV cameras all over the Palace koda hakan na nufin karya k’a’idan Masarautar ne, hakan ne kawai zai bamu daman warware wasu al’amara dake faruwa cikin gidan cikin sauk’i.... Gabanta ya yanke ya fad’i, cikin zuciyarta take kuma nanatawa CCTV cameras, hakan na nufin za’a ganta kenan... Kai no no way bata fara komai ba, maiyasa Mahmood ke shirin ruguza mata shirinta... Idan tai sake tabbas Mahmood zai lalata mata dik wasu shirinta tun kafinma Ta fara... Fuzar da fuci tai a hankali sanda muryarsa ya kuma dawo da ita daga duniyar tinanin da ta tafi... Da mamaki saman fusakarsa yake dubanta... Tai k’ok’arin dawowa cikin hayyacinta, murmushin da yafi kama da yak’e saman fuskarta... “Your Highness, barka da dare...!” Ta fad’i murmushin saman fuskarta... Har lokacin dubanta yake fuskarsa babu alamun walwala, baice da ita komai ba saima had’e hannayensa da yai waje guda yana dubanta, wane irin duba yake mata tamkar duba na tuhuma ko na mai laifi, take taji jikinta yayi sanyi sosai, domin kaw sosai ya tsareta da wannan idanun nasa masu firgitar da dik wani mai laifi... Ta had’iyi miyau da k’yar tana kuma satan kallonsa... Tamkar ta juya ta koma a guje haka taji... Neman kalamai ta soma saman harshenta dake faman sark’ewa tana furta “Am...Am... I’m sorry your Highness, I... I was told that..!” Muryar Zahra ta sinkayo kaman daga sama ne ya katse mata bayanin da take da k’yar da baki da hannaye “Tia Hibbah...! I thought you wouldn’t come... Sannu da shigowa... k’araso, shigo...!” Ta k’arashe tana mai kamo hannun Muhibbar suka shige cikin parlorn... Ita dai Muhibbah gaba d’aya jikinta ba’a sake yake ba, sai faman waigowa take tana kuma duban Mahmood da yai tamkar baisan suna wajen ba.... Ga mamakinta sai kuma taga bai nan da alama k’ila saman bene ya haye ko ficewa yai gaba d’aya.... What if ya ganeta ne... What if ya fara saka shakku da kokonto akanta... Tabbas gaining trust d’in Zahra kawai yayi kad’an dole ta sami yardar Mahmood... Bazata bari ya saka shakku akanta ba, sannan wannan cameras da yake maganan installing ko ina cikin gidan babban barazana ne ga shririnta.... Raheema dake faman zuba had’edd’en soup cikin bowl tana fad’in “Ehen Daughter you need to taste this soup kafin Paa ya tasting, I cooked it myself... I really want to hear your opinion....!!” Burki taiwa kalaman nata sanda ta juyo rik’eda bowl d’in tana duban abin mamaki... Wai dama wannan shegiyar uwar shishigince surprise d’in da Zahra Ke fad’i... Baki sake take dubansu... Bata ankara ba saiji tai bowl d’in ya fad’i tauu saman k’afarta, soup mai zafi dake ciki ya k’ona mata k’afa ga tangaran d’in ya yanka mata fata... Ta saki k’aran azaba daidai lokacinda Muhibbah ta isa da sauri tana k’ok’arin taimaka mata... Raheema ta finciki k’afarta tana fad’in “Don’t you dare.... How dare you..!! Mai ya kawoki nan... You’ll pay for this munafuka algunguma mayya...!!” Daga Zahra har Muhibbah tsaye sukai suna mata duban mamaki... Zahra da tsoro ya nuna saman fuskarta tace “Aunty Raheema meke faruwa, Mai Tia taimaki... Taimakonki fah take son yi... Look you’re wounded, Deja que ella te trate la herida ... es su profesión” (Ki k’yaleta ta duba ciwonki fanninda ta k’ware ne...) A zuciye Raheema dake tsananin fuci ta juyo tana duban Zahra kana Ta soma fad’in “Shut your mouth you little brat, this is all your fault...How could you... Ta yaya zaki katse min hira da mijina ki kirawo mana wannan shu’umar wajen nan... Just who do you think you are..!? Na jima da sanin baki so na auri mahaifinki, but ban zaci munafuncinki yakai har haka ba, tell me so kike Ki lik’awa babanki ita ko mai da zaki gayyato mana ita...? Toh bari kiji na fad’a miki, Yarima Mahmood is mine, he’s mine... I don’t care if you’re his daughter... The next time da kika sake yunk’urin aikata wani abu mai kama da haka ni da kaina zan hukuntaki, maras kunya kawai...!” Zahra da tuni ta soma huci da hawaye, lokaci guda take furta “You’ve no right to talk to me that way..! You are not my mother, you can’t punish me... You’ve no right over me...I hate you, I hate you.... And yes I never liked you, I don’t want you for my father... To hell with you..!!!” Ta k’arashe cikin tsananin daka tsawa hawaye na sauk’o mata.... A zuciye Raheem Ta mik’e zatakaiwa yarinyar mari Muhibbah tai saurin rik’e hannun Raheema tana mai sakin huci itama... “Don’t you dare lay a finger on her...!!” A guje Zahra ta nufi upstairs tana kuka sosai take kiran mahaifinta.... Raheema ta dube Muhibbah shaye da mamaki kana tace “Excuse me...! Wacece Ke... How dare you interfere..! Sakar min hannuna kafin na sakaki kiyi nadaman da baki tab’a irinsa ba tsawon rayuwarki.... Munafuka mai bin mazan mutane..!!” Wannan karon murmushi Muhibbah tai kana tace “Why...? Tsoro kikeji...? Baki yarda da kanki bane...? How many times do I have to tell you babu abinda zanyi da Yarimanki... Ni inada Sarki already... Bana buk’atan Yarima, amma ga shawari guda d’aya... If you’re scared of losing your prince... Then ki sami igiya mai k’arfi ki d’aure zuciyarki dana d’iyarsa waje guda... Aikin banza kike idan har yarinyar nan bata k’aunarki... Shawari ce..!!” Ta k’arashe tana mai sakin murmushi saitin fuskar Raheema... Tana ida fad’in haka tasa kai tai ficewarta daga sashen gaba d’aya, tana tinanin mai zatai gameda batun dasa cameras a cikin gidan da Mahmood Ke k’ok’arin yi, she really needs to come up with something, dole tasan yanda zatai tasa a datse batun saka cameras cikin gidan.... Haka Raheema tabi bayan Muhibbah da kallo har ta b’acewa ganinta, kumafa abinda Muhibbah ta fad’i mata gaskiya ne... Idan har tana son samun kan Mahmood da gaske toh fah dole tai hak’uri da wannan sangartacciyar yarinyar har ta samu ta mallakesa, idan yaso daga baya sai tasan yanda zatai da yarinyar.... Tana ida tinanin ta d’aga idanu tana duban benen, lokaci guda ta kuma sauk’e huci a hankali kana ta soma jan k’afarta mai ciwo ta nufi benen da d’ingishi... Tana haurawa ta hango Zahra zaune parlorn saman ta tak’ure waje guda ta kifa kanta cikin gwiwarta tana kuka mai tsuma zuciya.... Ta gallawa yarinyar harara tana mai yatsina fuska, lokaci guda tai k’ok’arin saita kanta kana ta nufi cikin parlorn cikeda k’issa, gefe da Zahra ta isa ta zauna had’ida kwantar da murya “Daughter I’m sorry... Believe me I didn’t mean to... Kiyi hak’uri dan Allah... Please don’t tell your Paa about this... Kiyi hak’uri rainane ya b’aci amma bana nufin dik abinda na fad’i kinji koh....!” Ta k’arashe tana mai k’ok’arin rungumo Zahra... Idanunta masu zuban hawaye ta d’ago tana duban Raheema dashi kana tace “Don’t touch me... Karkizo kusa dani... Bana sonki da Paa d’ina... Bana so ya aureki... Ke muguwa ce... Ni Ki k’yaleni... Just go away..!!” Ta k’arashe tana mai kuma kifa kanta cikin k’afafunta... Takaici ya kuma turnuk’e Raheema a mak’oshi, batasan Mahmood da matarsa wane irin goyo sukaiwa d’iyarsu ba, shakka babu goyon turai Mahmood yai mata shisa bata ganin mutane da gashin ido, an gama sakalta yarinyar sai abinda take so... Ji take kaman ta d’add’auketa da mari amma sai tai k’ok’arin saita kanta sanda ta tuna kalaman Muhibbah... A hankali ta mik’e tana kuma duban Zahran kana ta fice daga parlorn ta nufo k’asa... Gimbiya Zeenatu na kwance saman kujera mai lilo na sarauta, gefe da ita kuyangace ke rik’eda parantin kayan marmari tana d’auka d’aya bayan d’aya tana ci cikeda kmasaita da mulki... Tamkar wacce aka jefota haka suka hango Raheema na shigowa na sakin huci... Kuyangin suka shiga sadda kawunansu suna gaidata, sai faman sakin huci take tana jan k’afarta dake ciwo... Gimbiya Zeenat ta tashi daga kishingid’en da take ta zauna sosai tana duban Raheema... “Ke kuma fah... Miye haka...?” Raheema taja Ta zauna kujera mai duban ‘yar uwarta kana tai alamawa bayin kan cewa su fice... Babu musu suka risina suka fice gaba d’aya.... Gimbiya Zeenat tace “Ke nake saurare Raheemah, mai kuma ya faru... Ya na ganki kin dawo cikin fushi keda kika tafi zance da masoyinki.... Sannan mai ya sami k’afarki na ganki haka nan...?” Huci kawai Raheema ke sakewa tamkar tafashesshen kunu.... Gimbiya Zeenat tace “Ke Raheema ki bud’e baki kimin magana Bana san shashashancin banza...!!” Tai maganar cikin hasala.... Raheemar ma a hasale take fad’in “Aunty ni fah na gaji, na gaji da wannan shed’aniyar d’iyar Mahmood d’in... Wannan yarinyar da kike gani sam babu alkhairi a tattare da ita....!!” Ta k’arashe tana mai kuma sakin huci... Mik’ewa tsaye wannan karon Gimbiya Zeenat tai kana tace “Bani labari mai ya faru...?!” Tas Raheema ta kwashe dik abinda ya faru ta sanar da ‘yar uwarta... Da mugun mamaki Gimbiya Zeenat ke dubanta kana ta d’an girgiza kai alamun rashin yarda tace “You mean to say Mahmood baisha miyar nan da muka gama masa had’i ba..?!!” Sai sannan Raheema ta tina ashe fah miyar da aka shirya musamman dan Mahmood an gama masa had’i da komai shine ta tuntsirar dalilin ganin Muhibbah... Ta dafe kanta cikin sauri tana mai furta “Na shiga uku Aunty wllhi baici ba...!” Saukan wane irin jahilin mari taji a k’uncinta, ta d’ago tana duban Auntyn tata dake sakin hucin b’acin rai... “Ashe ke shashasha ce ta bugawa a jarida ban sani ba... Ashe Ke doluwace Ta k’arshe.. Kinsan da yaya aka had’a maganin nan... Kinsan kwanakin maganin nan nawa a tsibirin iskokai... Shine dan dak’ik’anci da shashashanci zaki zubar kuma dik zaman nan baki San yanda duk kikai kika basa yaci ba..?? Dak’ik’iyar inace Ke Raheemah..!!?” Ta k’arashe tana mai jijjiga Raheema dake kuka dafe da k’uncinta.... Raheema na kuka take fad’in “Aunty wllhi ba laifina bane laifin shegiyar Muhibbar nan ne.... Aunty makirar nan ta shige dik tinaninki...!” Hankad’ata gefe Gimbiya Zeenat tai tana mai ci gaba da sakin tururi “Bazamu tab’a rasa Mahmood ba, dole ya zamto yana k’ark’ashin ikonmu.... Amma kafin nan sai mun b’atar da wannan yarinya Muhibbah dake k’ok’arin kutso Kai cikin rayuwarsa data d’iyarsa..!!” Raheema ta dubeta da mamaki kana tace “Aunty ya za’ai mu b’atar da ita, bayan ko idanunta tsoro suke bani...!” K’asaitaccen murmushi Gimbiya Zeenat tai kana tace “Na b’atadda wad’anda suka fita balle ita... Akan mulkin nan babu abinda bazanyi ba... Juwariyya..!!!” Raheema ta

Chapter 15 of 65