d’in d’ah na ne... Domin kuwa jikina ya bani akwai abuna mai mahimmanci a gefen d’akinda Ubandoma ya rufe ni.. Ban fasa kankare jikin ginin ba, ban kuma amince na tafi na barka hannun azzaluman nan ba har saida na tabbatar Allah ya kub’utar damu tare...! D’anah.! Jaririna..!!!” Wane irin kuka mai k’arfi ya kufce mata tana mai janyo Ja’afar d’in cikin jikinta da tuni ya koma tamkar wanda yayi sumar tsaye..! Jijiyoyin jikinsa sai mimmik’ewa yake ba komai yake tunawa ba face irin wulak’ancin da yaran Giwa sukai masa musamman Yazeed da Jamal, Yazeed akan tsananin son Mulki da izza shi kuwa Jamal akan Umaima ne... Ya tuna akwai wani rana da Yazeed ya take gadon bayansa ya d’ale doki, ya tuna akwai wata rana da Jamal ya sakasa ya sumbaci takalminsa dan ya gansu da Umaima kawai don ya nuna masa cewa shid’in k’ask’antacce ne bai dace da basarakiya jinin sarauta kaman Umaima ba....Dan ma shid’in Allah yayisa mai taurin kai da kafiya ne tun a baya lokacin yana matsayin Bawa, yakanyi abu tamkar ba Bawa ba musamman idan ka tasamma tab’a mutuncinsa sam bazai barka ka k’ask’antashi ba a matsayinsa na d’anAdam wanda Ubangijin talikai gaba d’aya ya d’aga darajan d’an adam kan sauran halittun duniya..! Shi mutum ko yaya ka gansa ba abun wulak’antawa bane, baka San kalan Baiwar da Ubangijinsa yai masa ba, kuma bakasan koma ya fika daraja a wajen mahaliccinku ba, idan yafika tsoron Allah sai ya fika daraja..! Sam Shari’a bata bama kowa daman kaci zarafin wani wanda yake k’arashinka ba koda kuwa bawanka ne...!
Ya dinga tuna ire iren cin mutunci da wulak’anci da ya fuskanta daga wajen wannan ahali... Sai yanzu komai yake dawo masa daki daki, watak’ila Mai Martaba ya fahimci shine mahaifinsa na asali da Giwa ta fahimci hakan shine ta kashe mai Martaba shima kuma Ta nemesa zata kashesa.. Wannan mata takai mak’ura wajen zalunci... Shi ko a labarun hikayoyi da ake karanto masu da cikin Fada bai tab’a cin karo da labarin azzaluman Baiwa irin Izzatu ba...! Amma zuluncinta yazo k’arshe da izinin Allah, sai ta girbi duk abinda ta shuka daga ita har yaranta guda biyu...! Yana mamakin yanda Yarima Mahmood ya kasance daga cikin ahalin wannan azzalumar mata domin kuwa shid’in ya banbanta da muguwar ahali irin wannan.. Kodashike Allah yakan fidda rayayye daga cikin macecce sannan ya kan fidda macecce daga rayeyye... Domin kuwa babu abinda yafi k’arfin buwayarsa...! Ja’afar ya lumshe idanunsa a hankali sanda yaji hannun Gimbiya Turai tana shafe fuskarsa da ruwa dan su duk a zatonsu suma yayi...! Yaja wane irin dogon numfashi had’ida sauk’e idanunsa kan matar, yai mata K’uri bayanan kalan azabtarwa da muzgunawa had’ida mummunan cin amanan da Baiwar ta tai mata na kuma yawo a kwanyarsa...!
Hawaye suka soma gangarowa daga idanunsa wanda tuni Sun kad’a sunyi jazir.... Ji yayi yakai hannunsa dake tsananin rawa saman fuskarta yana share mata hawayen dake kuma gangaro mata. Cikin rawar murya yake furta “Ta cutar dake..! Ta miki zalunci mafi muni Ummi tah... Ta maidaki Baiwa cikin gidan Mijinki sannan Ta maida d’anki Bawa cikin gidan mahaifinsa... Daga k’arshe ta haukataki ta kuma salwantar da sauran ahalinki..! Wannan matar bata cancanci yafiya ba domin idan na yafe mata ni kaina bazan iya yafewa kaina ba sabida abubuwan da tai miki Mahaifiyata..!!” Ya k’arashe cikin wane irin cazgan kuka..! Tuni Gimbiya ma kukan ya kufce mata suka had’e goshinsu itada d’anta Ja’afar waje guda suna yin mai isarsu...!!
Tirk’ashi..! Rayuwa mai bud’e ma Bawa shafuka daban daban, ko wanne da yanda yake zuwa maka, wad’annan bayin Allah rayuwa ta kuma bud’e masu sabbin shafuka.. Bayan tsawon shekarun nan gashi Allah ya had’a fuskokinsu, tabbas tsanani yana tareda sauk’i mai hak’uri shikeda riba...!
Bayan komai ya tsagaita Baba Nomau ya nusa had’ida furta “Alhamdulillahi..! Alhamdulillah...! Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Ubangijin da babu wani bayan shi, mai mulkin Sammai da k’assai da abinda ke cikinsu da abinda ke tsakaninsu, tsira da amincinsa su sake tabbata ga Annabinsa fiyayyen halitta wanda babu yashi, Manzon tsira (S.A.W)...!”
Ya juyo kad’an ya dubi Ubandoma yace “Hak’ik’a ka tapka kurakurai a baya, wanda a ajizancinmu na ‘yan adam zai wahala wani ya yafe maka..! Ubangijinmu ne zamuyi masa laifi duk girmanta duk yawanta ya kuma gafarta mana mu maimaita mu kuma sake rok’onsa ya yafe mana matuk’a bazamu masa tarayya wajen bauta masa ba... Shirka itace mafi munin zalunci da Bawa zai aikataga Ubangijinsa a doron k’asa, Shirka itace mafi girman laifi da mutum zai mutu yanayi Ubangiji bazai gafarta masa ba.. Amma duk wani laifi bayan shirka Ubangiji mai iya gafartawa ne idan yaso domin shid’in shine Algaffar kuma Arraheem..! Ka tapka kurakurai a baya amma daga k’arshe ka gane kuskurenka kuma kayi abinda ya dace sannan ka rok’i Ubangijinka gafara, Muna fata ya gafarta mana baki d’aya... Sannan muna fata wad’anda kaima wannan aika aika su gafarta maka domin shi addu’an wanda aka zalunta babu hijabi tsakaninsa da Ubanginsa..! Sannan ko a Shari’a idan an maka laifi ka rama gwargwadon abinda aka maka bakayi laifi ba amma saidai da zaka zamto mai afuwa da yafiya sai ya fi maka alkhairi... Allah yana son masu afuwa kuma yana tareda masu hak’uri..!”
Ya maidoda dubansa ga Ja’afar da mahaifiyarsa wanda kawunasu ke k’asa suna saurarensa, Baba Nomau yaci gaba da fad’in “An zalunceku kuma an cutar daku... Wannan mushirikar matar Ta maku zalunci mafi muni amma ku sani wani shari’ar sai a lahira..! Tinda Allah yasa duk mun fahimci haka kuma ya baki lafiya a halin yanzu ya kuma had’a fuskarki dana d’anki bayan kun d’ibe tsammanin sake had’uwa da juna.. Sai mu gode masa da wannan rahama nasa sannan gobe idan Allah yasa muna cikin masu nisan kwana mu d’unguma mu koma Masarauta a ida warware komai..!”
Gimbiya Turai ta jinjina kai tace “Haka ne Baba...!”
Ja’afar ma jinjina kansa yayi saidai kafin yakaiga furta wani kalma Ubandoma ya katsesu da fad’in “Bazan iya komawa Masarautar nan ba har sai na tabbata kun yafe min... Dan Allah ku yafe min duk abubuwan da nai maku a baya...!!”
Murmusawa Gimbiya Turai tai tace “Na yafeka tuntuni tun lokacin da ka zab’i kayi abinda ya dace bayan kanada damar da zaka kuma mik’ani hannun wannan azzalumar Baiwar, amma ka zab’i kayi abinda ya dace kayi sanadiyar kub’utarmu nida d’ah na ka kuma kawo mu yanda maganinmu yake cikin hukuncin Ubangiji da ikonsa..! Kaima abin mu maka godiya ne Ubandoma... Allah Ubangiji ya saka maka da mafificin alkhair bisa abinda kayi...!”
Ubandoma ya duk’a yana hawaye yake furta “Na gode na gode Rankidad’e..! Ubangiji ya k’ara girma..!”
Ya kaikaito kad’an yana duban Ja’afar... Kafin yayi magana Ja’afar yayi saurin d’agosa ya rungumesa, lokaci guda yake furta “Tun zamanin da nake na matsayin Bawa cikin Masarauta baka tab’a muzguna mun ba hasalima kai d’in kana d’aya daga cikin masu kwatanta alkhairi a gareni.. Sannan daga k’arshe kamin abinda bazan iya saka maka ba koda kuwa daga farko ka zamto silan shiga rayuwar da na girma na tsinci kaina ciki..! Na gode maka Baba..!”
Ubandoma na hawaye yake furta “Rankaidad’e nifa Bawanka ne ka daina furta min kalman godiya.. Ka barni na duk’a gabanka..!”
Ja’afar na murmushi yake furta “Ni dakai duk d’aya muke wajen Allah mu duka bayinsa ne kuma har kullum kai d’in tamkar Uba ne a gareni dan bazan mance yanda ka kula dani ba bayan babu iyayen da na girma na sansu matsayin iyayena.. Babu k’ask’antacce sai wanda ya k’ask’antar da kanshi kaji koh..!”
Cikin sauri Ubandoma ya shiga jinjina kai cikeda jin dad’i yana kuma godiya... Fuskoki suka cika da annuri da Farin ciki... Ja’afar da mahaifiyarsa suka kasa sakin juna sabida Farin ciki.. Gani take kaman wani abu zai kuma giftawa ya raba tsakaninta da d’anta...!
Baba Nomau ya kuma basu wasu add’u’o’i yace suyita nanatawa suna ambaton Allah domin kuwa duk yanda wad’anda suka cutar dasu suke suna cikin tashin hankali...
**
Tinda suka baro asibitin wajen Yazeed yake shek’a gudu saman kwalta daga gani zaka fahimci neman hanyar fitar da b’acin ransa kurum yake, ya kasa yarda ‘yan uwansa da mahaifiyarsa zasu aikata irin mugun abinda yaji sun aikata, Allah ya gani ko k’aunar ganin fuskokinsu baya yi shiyasa ma koda suka iso asibitin yake alla alla ya fice daga cikin asibtin... Babu yanda Turaki bai ba ya basa motar ya tuk’a amma yak’i sai zuba gudu dasu yake saman kwalta... Bai cewa uffan sai shek’a gudu yake jijiyoyin jikinsa suna kuma fitowa duk sanda kalman fyad’e da k’annensa suka aikata ma k’aramar yarinyar nan zaizo zuciyarsa.. Idanunsa suna kuma kad’awa...! Turaki kansa ya rasa gane kan abokin nasa, tashin hankalin da yake hangowa tattareda Mahmood d’in yafi k’arfin ace dan sabida iftila’in da ya aukawa Yazeed da ahalinsa yake ciki tinda yasan abokin masa musulmi ne kuma yayi imani da K’addara mai kyau ko akasinta... Amma ya rasa gane ina tauhidin abokin nasa ya tafi yake neman yin wasa da rayuwarsu saman kwalta... Shi kansa Turaki bai iya cewa komai sai ambaton Allah kurum da yake cikin zuciyarsa....
**
A b’angare guda tun fitowar da yayi daga Bauchi sai yanzu Allah yayi isowarsa, mota ta b’aci masa a hanya sannan ya rasa mai gyara ya kuma rasa wanda zai tsaya ya taimaka masa, gashi dama ba isasshen lafiya bane dashi tinda daga asibiti ya cire ruwan drip ya fito sam babu wani k’arfi jikinsa, bashi ya samu isowa garin Jos ba sai wannan lokaci dan da kam ma ya yanke shawarin tsayawa a Toro ya kwana ne amma sai yaji inaa bazai Iya kwana baisan halinda Muhibbah ke ciki a wannan masarauta ba hakan yasa ya k’udiri niyyan komin dare sai ya shiga Jos da izinin Allah... Daidai yanda suka saba parking idan ya kawota a wajen yayi parking can tsallake da Masarautar... Yayi tsaye yana tinanin abinyi, ta yaya zai doshi Masarautar ba tareda an tambayesa wanene shi daga ina yake kuma wajen waye zai jesa, yasan by now Umaima zata iya fahimtar shid’in ya mata k’arya, Toh ta yaya zai shige Masarautar bata hanyar Umaima ba... Kodashike ita d’in tana da zuciya mai kyau watak’ila tansauraresa ta kuma basa uzuri... Take ya lalaumo wayarsa cikin mota ya soma dialing layin Umaima..! Saidai sam wayar tata bata shiga... Dafe kansa yayi a hankali had’ida jefa wayar cikin mota dan shima wayar tasa chaji gab take da k’arewa... Ya fuzar da fuci yana tunanin abinyi ya wane irin jiri dake neman kaisa k’asa dan tun bayan drip d’in babu wani abu da ya saka cikinsa..! Wata zuciya tace tsayuwa a nan bai ganka ba Ansar Muhibbah tana cikin Masarautar nan kuma tana tsananin buk’atarka ka shiga kawai ka fito da ita komai ta fanjama fanjam, komai zai faru kawai saidai ya faru but ya zama dole ka shiga ka ceto masoyiyarka...! Da wannan tunani Ansar ya nufi Masarautar yana tafe ko ganin gabansa baiyi....
A daidai lokacinda su Mahmood suka doso Masarautar suma.. Turaki ne kawai ya hango mutum yana tafe bisa kwalta tamkar mai tab’in hankali shikam Mahmood sam baiga mutum ba dukda cewa hasken wutan streetlights sun haske ko ina... Turaki fad’i yake “Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un..! Watch out your Highness..!!” Inaaa sam Mahmood baima saurari abinda Turaki Ke fad’i masa ba saiji yayi ya d’auke mutum da k’arfin gaske...! Ya taka burki babu shiri Allah yasa babu wata motar ma bayanshi da shike wannan close d’in babu gidan kowa wajen ba kuma hanyar wucewa zallan Masarauta ce kawai a wajen...!
A tare suka fito suna duba mutumin da suka bige... Turaki ya d’an tab’asa yana furta “Kaman yana numfashi Your Highness.. Muyi gaggawan kaisa asibiti mafi kusa..!”
Cikin sauri Mahmood d’in ya taimakawa Turaki suka ciccib’i mutumin suka saka bayan Mota... Babu shiri Turaki ya amshi makullin motar suka nufi wani privare hospital da baida nisa sosai da Masarautar...
**
A can asibiti wajen Yazeed kuwa gaba d’aya Giwa ji take kaman an mintsileta, Ta kasa zaman asibitin Ta kuma kasa komawa Masarauta, batasan dalili ba amma zuciyarta sai yankewa yake yana bugawa yanda kasan ana sauk’e mata shirgegen guduma saman k’irjinta haka takeji... Ga wani irin muguwar k’aik’ayi da bata tab’a jin irinsa ba tsawon rayuwarta, hannunta nayi kanta nayi... Ta gaza zama ta gaza tsayuwa, gaba d’aya Giwa ba a hayyacinta take ba ta alak’anta hakan da asirinsu da Fu’ad ya tona wajen Mahmood..!
Jamal ya da shima hankalinsa ba’a kwance yake ba ya k’araso ga mahaifiyar tasa cikin cangwala sandarsa, ya tsaya dab da ita yana muzurai yake furta “Maami meye abinyi yanzu da Yaya yasan laifin da muka aikata shekarun baya... Maami jikina na bani Yaya bazai dakata ba until he seek justice for what happened to that girl, koda kuwa mu d’in ahalinsa ne.. Maami kin sanshi kinfi kowa saninsa tinda Ke kika haifesa...!”
Cikin tashin hankali Giwa dake faman soshe soshe Ta katse Jamal da fad’in “Bani na haifesa ba kar ka sake cewa ni na haifi wannan tsinannen yaron... D’anda na haifa bazai tab’a kiranada ‘yar ta’adda ba...!!!”
Cikin rashin gane ina kalamanta suka dosa Jamal yace “Maami ban gane ba... Ban fahimta ba...! Yaya ne fah..! Yaya Mahmood nake nufi..!!”
Cikin daka tsawa Giwa tace “Uban Yaya Mahmood ne ba Yaya Mahmood ba... Allah yasa Mahmooda Uban AbdulJabbar ne..! Kai nace maka bani na haifesa ba kar ka sake cewa d’ah na ne..!!” Ta k’arashe tana mai ci gaba da susa...!
Jamal yasha jinin jikinsa yana dubanta cikeda tsoro saikace wata sabuwar kamu..! Koda shike k’ila fushi take da Mahmood d’in shisa take ambatonsa da cewa ba ita ta haifesa ba..! Ya d’anyi shiru sai kuma yace “Maami ya kamata mu koma masarauta Kinsan akwai aikin da bamu k’arasa ba can Masarautar..!”
Nan ma katsesa Giwa tayi da fad’in “Kai nace maka bazamu bar asibtin nan ba sai Yazeed ya farka..! ko ni ko kai babu mai barin asibitin nan sai mun tabbata d’an uwanka ya farfad’o, ince da handcuffs ka d’aure yarinyar toh uban waye zai kwanceta...!!”
Jamal ya kuma jinjina kai a hankali yana kallon bak’on lamari daga mahaifiyar tasa... Bai kuma cewa komai ba sai komawa gefe da yayi...!
Can Giwa ta hango Waziri ashe Shima ya kasa tafiya yana nan yana jiran farfad’owar Yazeed... Giwa tana ganin giftawarsa tai saurin bin hanyar da yabi...
Koda Jamal dake fakaice da ita yaga tabi bayan Waziri sai shima ya saci idon Jakadiya yabi bayan mahaifiyarsa a hankali...
Tsaye yayi ya lab’e yana sauraren tattaunawar Giwa da Waziri...
Cikin k’unan rai Giwa ke ci gaba da fad’in “Saida nace kabi bayansa ka dakatar dashi, Wannan duk laifinka ne... Ka kasa dakatar dashi... Da ace ka dakatar dashi da yanzu d’anmu yana nan da lafiyarsa, da yanzu bai rasa hannayensa ba balle ‘ya’yansa... Idan Yazeed ya farka bazai tab’a yafe maka ba kuma bazai tab’a amsarka a matsayin mahaifi ba...!”
Cikin tashin hankali Waziri Ke fad’in “Ki dakata ki saurareni Turai, Yazeed ni na basa jini ni na taimaki d’anmu na basa jini akai masa aiki, da ace banyi gaggawan basa jinina ba k’ila da yanzu mun rasashi gaba d’aya.. Ki gode ma Allah ki gode min har yanzu Yazeed yana numfashi...!”
Cikin karaji Giwa Ke fad’in “Meye abin godiya a nan bayan kasa d’anmu ya zama muskini shikenan haka zai tashi yaga ya rasa hannayensa.. Duk burin sarautar da naci masa yanzu bazai samu ba..! Ka cuceni Waziri... Ka cuci D’anka Yazeed..!!”
Kaman daga sama suka sinkayo muryar Jamal cikin wane irin yanayi yana furta “Maami did I hear it right..! Naji da kyau cewa Yazeed d’an Waziri ne..?!!”
Daga Giwa har Waziri aka rasa mai basa amsa...Jamal dake ci gaba da sakin huci ya k’araso gaban Giwa sosai yana furta “Answer me..! Ki amsa min...! Yazeed d’an Waziri ne..?!”
Giwa bata iya furta komai ba sai muzurai.. Ya kuma d’aga murya yana jefo mata tambayar... Waziri ne ya basa amsa da fad’in “K’warai abinda kaji haka ne Jamal... Yazeed d’ah na ne da mahaifiyarka....!!”
Cikin tsananin Shock yake duban Giwa zuciyarsa na kuma tsinkewa har wani irin rawa jikinsa keyi, kana iya hango hakan daga sandar crotchets d’insa yanda sandar ke rawa kaman zai dungurar da Jamal d’in k’asa..!
Cikin wane irin yanayi yake girgiza kai yana duban Giwa “You tell me what really happened..! You tell me ta yaya wannan mutumin ya zamto mahaifin d’an uwana da muka fito ciki guda muka girma a matsayin ‘yan uwa da suka had’a duka iyaye biyu..! Maami ki bud’e baki ki sanar dani..!!” Ya k’arashe hawaye na gangaro masa cikin tsananin k’unan rai...!
Giwa dake danne kukanta tace “Ya faru ne hakan..! Domin kuwa Waziri shi yake taimaka min da komai wajen ganin na kafa mulki na cikin gidan nan..!”
Jamal ya katseta da fad’in “Shiyasa kikaci amanan mahaifina kika basa kanki...! Maami how could you do this..! Ke fah mai sarauta ce mai Martaba..! Ta yaya zaki aikata k’ask’antaccen laifi irin wannan..!”
Giwa ta katsesa da fad’in “Kada ka yarda ka yanke hukunci akaina domin kuwa baka San kalan rayuwar dana fuskanta a baya ba dan na tabbatar da mulkin nan bai kufce min ba..!”
Cikin huci Jamal d’inma ke furta “Wane mulki kike magana bayan d’an naki ba Magajin mahaifinmu bane... Ince Yazeed kike maganan d’aurawa saman Karagar..? Ashe dama duk son Yaya da kike na k’Arya ne..? Toh idan ba ke kika haifesa ba wacece Ta haifesa..?!”
Giwa Ta basa amsa da fad’in “Wannan ba matsalarka bace a halin yanzu.. Kaidai tinda kasan kaid’in d’ah ne magana ya k’are..!”
Waziri ya katseta da fad’in “Ina magana ya k’are tinda shi baisan waye nasa mahaifin ba..!!”
Ya karkata ya dubi Waziri da tsananin mamaki hawaye naci gaba da gangaro masa lokaci guda ya maidoda dubansaga Giwa yace “Answer his question... Waye mahaifina Giwa...?!”
Hararan Waziri kurum Giwa take kana tace “Mahaifinka Sarki AbdulJabbar ne..!!”
Waziri ya bud’e murya yace “K’arya take maka ita kanta batasan waye mahaifinka ba domin kuwa Ta shiga rud’u a lokacin..!!”
Jamal ya fiddo idanu waje yana duban Giwa lokaci guda yake girgiza kai yana mai furta “You’re unbelievable..! Shin abinda yake fad’i gaskiya ne Giwa..?! Do I need to take a DNA test for me to know who my father is..?!! Answer me Giwa..?! Ki amsa min nace..!!”
Cikin zuban hawaye Giwa Ke jinjina kai tana furta “Gaskiya ne Jamal bansan waye mahaifinka ba...!”
Dakatar da ita yayi ta hanyar d’aga mata hannu yana mai sakin huci yake furta “No..! My father is dead..! My father was King AbdulJabbar... Shine mahaifina... Bazan tab’a zama product na cin amanar da kika masa ba..! You’re a worthless mother..! Mujiyar uwace Ke mai kashe ‘ya’yanta..! Ko baki d’auki wuk’a kin dab’a mana ba kin kashe mu da abinda kika mana... Gaba d’aya rayuwana nayisa ne wajen miki biyayya..! Ashe duka rayuwan nawa k’Arya ne... Babu komai cikinta face k’arya...! Duk fad’i tashin da Kike wajen ganin kin kafa mulkin babu komai a cikin labarin face k’arya..! Kina neman ki d’aura ‘ya’yanki saman Karagar da basuda gado..! Maami kin cuceni kin zalunceni..! Nayi nadaman miki biyayya da nayi a baya dukda ire iren muggan abubuwan da kika sa na dingayi.. Allah ya isa tsakanina dake Giwa.. Kuma yanzu basai anjima ba zanje na kwance yarinyar nan bazan sake miki biyayya ba daidai da dak’ik’a guda..!”
Ai bata bari ya fice ta shiga janyosa tana basa hak’uri yana fuzgewa.. Ya juyo yace “Kika kuma tab’ani wllhi zan rabza miki sandar nan kinji na rantse..!!”
Giwa na kuka taceda Waziri ya dakatar dashi yana hanasa ficewa...!
Da k’yar Waziri ya rik’o Jamal dake faman bige bige yana kuka yana fad’in ya tsani Giwa...!
Saman wata kujera Waziri ya zaunar dashi ya rik’e sandar nasa wanda babu hali yayi tafiya babu ita..
Waziri ya duk’a gaban Jamal dake ci gaba da sakin huci yana murza tafukan hannayensa sabida tsananin b’acin rai... Lokaci guda Waziri Ke furta “Jamal basai kayi gwajin k’wayoyin halitta ba dan kasan wanene mahaifinka... Kasa a ranka cewa mahaifiyarka itace k’wal d’aya taka domin kuwa tayi sadaukarwa da dama a sabida ku ‘ya’yanta...Duk abubuwan da take, duk fad’i tashin nan sabida kai da ‘yan uwanka take..!”
Cikin karaji Jamal ya katsesa da fad’in “Can’t you see she’s ruining us... Duk abubuwan da take babu wani alfanun da suka mana saima d’aid’aita rayuwarmu da sukayi... Ka gaya min cikin yaran nata wanene ya taka matakin nasara,,, Yazeed dake kwance babu hannuwa babu iyali ne..? Ko kuwa ni da nake dogarawa da wannan sandar ko Fu’ad dake kwance gadon asibiti wanda tasa muka maidasa mahaukaci da k’arfin gaske..! Ka gaya min wanene zai gaji kujeran dataci burin cikinmu..?!!” Ya k’arashe sabbin hawaye na gangaro masa..!
Waziri yace “Dukda haka dai, yanzu idan ka juya mata baya zaku tafi k’aaa tare ne gaba d’aya ko ince dukanmu gaba d’aya..!”
Giwa dake gefe tana hawaye Ta shiga jinjina a masa kai tana furta “Ni d’in mahaifiyarka ce Gwarzona, ko mai Nayi bazaka gujeni ba, domin kuwa ba’a sake mahaifiya, bamu San waye mahaifinka ba amma nid’in nice mahaifiyarka..! Jamal karka guje ni da bazan iya k’arasa yak’in nan ba tareda kai ba d’ah nah..!!” Ta k’arashe cikeda kissa tana kuka tana dafe k’afan d’an nata...
Lokaci guda Jamal yasa hannuwansa ya d’agota zaune... A hankali yake furta “What’s done is done Maami...! Naji zan tsaya tareda Ke mu k’arabs abinda kika riga kika soma... Nima ina cikin yak’in nan already...! Now that I know sarautar na namu bane zanyi komai domin naga ahalinmu basu tagayyara ba..!!” Ya k’arashe cikin tsananin huci da zafin zuciya...
Giwa Ta saki murmushi tana dubansa, lokaci guda take furta “Hak’ik’a kai d’in ka cika d’ah na kuma jinina..!!”
**
Iyaka jigata Umaima Ta gama yi, da k’yar da tura k’afa da nishi da komai ta samu ta janyo wayar da babban yatsarta.... Ta had’e k’afafunta tana k’ok’arin d’ago wayar zuwa hannunta, nanma wani jan aiki... Sai ta kama kaman zata iya d’aukowa sai ya fad’I k’asa... Ga dare na kumayi, k’arshe haka ta hak’ura ta maida jikinta baya tana nishin wahala da k’yar... Firgit Ta farka Ta hango hasken hantsi alamun gari ya soma wayewa.... Taci gaba da k’ok’arin d’aukan wayar da k’afafunta har Allah ya bata sa’an d’aukan wayan... Saidai tana samun nasaran d’aukar wayar taji kaman shigowarsa, zuciyarta ta yanke... Cikin Sauri ta tura wayar ta zauna bisa... Tai saurin gyaran kwanciyarta ta lumshe idanu tamkar mai bacci zuciyarta bata daina tsinkewa ba...!
K’arasowa gareta yayi ya zauna gefenta had’ida k’ura mata idanu... Yakai hannunsa a hankali yana shafa goshinta zuwa fuskarta, lokaci guda yake furta “I’m sorry my love..! Ba’a son raina na d’aureki na barki kika kwana d’aure daren da ya kamata mu rayasa cikin faranta ran juna... Please forgive me Umaima... I promise zan kula dake... Zan baki Farin ciki a gidan aurenki, zan zamto the most loving and caring husband da ko wace mace zatayi fatan samun irinsa....Dukda cewa a yau labarin rayuwana ya canza... Amma na miki alk’awari soyayyar da nake miki bazai tab’a canzawa ba..! I love you so much Umaima..!” Ya k’arashe yana mai sumbatar goshinta..!
Hawayen da take mak’alewa suka shiga gangaro mata... Lokaci guda Jamal yai k’ok’arin saita kansa yana dubanta... “My love kin tashi..! Akwai abinda kike so..! Tell me ko menene zan kawo miki..!”
Yananyin data gansa gaba d’aya kaman bashi ba harga Allah tun bayan abubuwan data gani mugun tsoronsa take.. Amma dole tasan yanda zatayi Ta kub’utar da kanta da kuma Muhibbah daga hannun wannan mahaukacin mutumin tinda har Allah ya bata Sa’an d’aukan wayar salulansa..! Dole tayi acting very smart idan tanaso Ta cimma burinta..!
Cikin rawar murya take furta “Ya Jamal meke faruwa..?! Maiyasa ka d’aureni..! Na gaji, bathroom nake son shiga dan Allah ka kwanceni kaga ko sallah banyi ba..!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya..!
Dubanta yayi duk a rikice sai yace “Are you sure..! Zafi kikeji da gaske.. where does it hurt.. Nuna min ina Ke miki ciwo.?!” Ya k’arashe yana kai hannunsa jikinta..
Ta had’iyi miyau da k’yar tace “Ko inama ciwo yake min a jikina... I spent the whole night like this.. Maiyasa ka d’aureni.. Ina sonka bazan tab’a gudunka ba... Please untie me..!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya...
Kaman wanda yaji maganarta ya soma yunk’urin kwanceta, sai kuma ya dakata yana furta “No... Zaki gujeni, sabida munafukar nan Ta fad’a miki k’Arya akaina... No Umaima bazan kwanceki ba har sai na tabbata ked’in kin
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 49 Chapter of 65